You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng *BAK'AR TA'ADA*
*NA*
*Surayya Dahiru Gwaram*
*(Mrs M.I. Nashe)*
*Marubuciyar Halin yau da Sabo da kaza*.


•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


*Rok'on addu'arku*!
*A irin wannan ranar ta 09 ga wata 09 shekarar 2000. Ubangiji ya karbi ran
mahaifiyata. Dan haka ina baran addu'arku dan nema mata raham da gafarar Allah daga
bakunanku masu albarka dan Allah*.

*Haka nan ina mika sak'on ta'aziya ta ga dukkan musulmai bisa babban rashin da muka
yi na bijimin malaminmu kuma uba*.
*Sheikh Abubakar Giro Argugun*
*Allah ya jikan magabatanmu gabad'aya kwata.*

*JAN KUNNE*
*KADA A TA'BA MINI LABARIN NAN, KO KARANTA SHI A KOWACCE IRIN KAFA TA SADARWA BA
TARE DA IZININA A RUBUCE BA*.
*IDAN KUMA AKA YI KARAMBANIN TABAWA, ZA'A FUSKANCI TUHUMA DAGA LAUYANA BAR MUSTAPHA
ISA GWARAM*.


*GARGADI*.
*WANNAN LABARIN KIRKIRARREN LABARI NE*
*BA SHI DA ALAKA DA KO WANNE MAHALUKI*.
*IDAN KIN CI KARO DA RAYUWAR DA TA YI KAMANCECENIYA DA TA KI, KO WANINKI, TO ARASHI
NE*.
*DOMIN MANUFAR MARUBUCI ISAR DA SAKO DA HANNUNKA MAI SANDA A CIKIN ZAMANTAKEWARMU*.
*LITTAFAN SURAYYA BASA NUFIN HABAICI KO SHAGUBE GA RAYUWAR WANI KO WATA.*
*NA GODE*.

*GODIYA GA*
*SADIK ABUBAKAR*
*NA GODE MADALLAH*.

*GAISUWAR GIRMA GA IYAYENA KUMA MARUBUTA*
*HAJ SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI ZARIA*.
*HAJ HAFSAT C SODANGI*.
*HAJ MARYAM KABIR MASHI*.
*HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM*.


*YABO GA*
*K'AWATA JAMILA JANAFTY*
*IDAN DA WANDA NA GAMSU DA TULIN SOYAYYARTA GA RUBUTUNA DA CIGABANSA TO KE CE*
*DUK WATA KALMA TA YI KA'DAN TA FAYYACE GIRMAN SHA'ANINKI A WAJENA*
*INA FATAN UBANGIJI YA SHIGA AL'AMARIN KI, YA BAKI MIJI NA GARI*.

*GAISUWAR SADA ZUMUNCI GA MARUBUTA*
*Sumayayyah Takori*
*Binta Umar Abbale*
*Fadilah lamido*.
*Hassana D'anlarbawa*
*Zainab MAZAWAJE*
*Lubna Sufyan*
*Nazifa Nashe*
*Ayusha Muhd*
*Nana Diso*.
*Kulsum Baffah*.
*Safiyya Um Abdul*
*Umm Asghar*.
*Aisha Dansabo*
*Aisha jos*
*Zee Kumurya*
*Da dukkan y'an kungiyarmu ta lafazi*.

*FATAN ALHERI GA IYAYEN D'AKINA*.
*HAJ HALIMA D'ALHA SHEHU*
*HAJ RABI SANI*
*HAJIYA HALIMATUS SA'ADIYA*
*HAJIYA HADIZA FARI*.
*HAJIYA ZAINAB ABDULWAHAB*
*ALLAH YA HA'DA Y'AY'ENKU DA MUTANAN DA ZASU MUSU KARAMCI FIYE DA YADDA KUKE MINI,
INA MATU'KAR GODE MUKU*.

*TUKUICIN LABARIN SUKUTUM GA*
*AISHA MUHD LAME*
*ALLAH KA SO AISHA, KA FARANTA MATA, KA BIYA MATA BU'KATUN TA NA DUNIYA, KA BATA
BABBAN RABO A LAHIRA*.
*IDAN AKWAI WANDA JINI BAI HA'DAMU BA, NA KE DAKACEN INA MA JINI YA RATSA
TSAKANINMU TO AISHA LAME CE MAI KAYAN Y'AN GAYU TA ORIFLAME*
*SURAYYA DEE TA GODE, TA YABA MIKI, UBANGIJI YA TAYA NI GODE MIKI*.


*Doka mi lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha Babban laifine da yake dai-dai da
satar Dukiya*


*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*.

*1&2*.

*SHIMFI'DA*.
Sunana Asiya Sani Toro.
Amma mafi yawa da Yabi ake kira na a dalilin mahaifiyata ta yi aikin Hajj da ni a
cikinta.
Mama ce kawai bata kira na da hakan sai Asiya saboda tana adawa da Yabi tunda ana
nufin nima Hajiya ce.
Gidanmu babban gida ne a garin na Toro domin ko yaro k'arami ka tambayi gidan
Marina zai nuna maka. A dalilin asalin kakanmu da ya zo daga Kano ya fara kafa
wannan sana'ar a garin. Fiye da shekaru saba'in kenan, amma har yau ba'a juya wa
sana'ar baya ba, duk da dai an zamanantar da ita, ba kuma cikin gidan ake yin ta ba
saboda warinta.
Gidanmu babban gida ne k'warai da gaske.
Idan na ce babban gida ina nufin mai d'auke da ahali daban daban masu yawa.
Ko a k'ofar mahaifinmu Alh Sani (Baban Marina) da shi ne babba mata uku ne.
Hajiya Habiba ita ce uwargidan mahaifinmu, mace mai k'ifadi da kutunguila. Duk wani
rikicin da yake k'ofarmu, dama cikin gidan tana da sa hannu, ta tsani ta ga ko
wanne irin cigaban d'an wata sai nata yaran kawai.
Sannan komai cikin dabara da girma ta ke yinsa, ba kowa ne ya fahimci irin makircin
da take k'ullawa ba. Sai mu da mu ke rayuwa da ita kullu yaumin.
Ta kanka ne komai, ta yadda komai ta shimfi'da akan haka za'a tafi, sai dai ranar
da ta samu bacin rana Baba ya bijire mata.
Ya'yanta biyar.
Yaya Musa, Yaya Hadiza, Yaya Salamatu, Yaya Indo sai autarta da ta haifa bayan ta
shafe shekaru masu yawa Nazira, wacce ita ce sa'a ta ta girme ni da wata uku.
Sai Mahaifiyata Hajiya Àsma'u wacce muke kira da Goggo. Ba dan tana mahaifiyata ba,
amma mace ce mai sanyin hali da matsanancin ha'kuri. Idan na ce ha'kuri, ina nufin
ha'kuri gangariya, irin ha'kurin nan da mai yinsa kan saka a alummar da suke kewaye
da shi su halaka saboda hakkinsa da za suyi ta d'auka.
Yaranta takwas cif.
Yaya Salisu, Yaya Rabi'u, Yaya Ummi, Yaya Adnan, Yaya Ali, sai ni Yabi, duk dai
bani nake bin Yaya Ali ba, akwai wani ya rasu ne, sai Anas da kuma autarmu Ikilima.
Wannan yawan yara da mahaifiyata ta tara a d'akinta, kuma maza, ya sanya Mama ta
tisa ta a gaba da masifa da tuggu, kusan kowa a gidan ya tsani mahaifiyarmu, ba
kowa ne yake mua'amala da ita ba.
Duk gidan bakinsu daya ne a kanta. Duk kuma Mama ce ta b'ata ta, take adawa da duk
wanda zata ga ya mu'amalan ce ta
Shi yasa hatta mu yaranta bamu da wani kwarjini har a wajen Dada kakarmu da ita ma
tana cikin gidan bangarenta daban.
Sai Hajiya Sahura muna k'iranta da Innah. Yaranta biyar Na farkon ma mun dan girme
masa ka'dan Ubaid, Ubaida sai Abida, Hajara, Ismail da autarmu gaba'daya Saliha.
Duk yadda Mama ta so wajen raba zumunta a tsakaninmu bai yi tasiri a tsanina da
Nazira ba.
Duk yadda bata kula ni, bata sakar mini fuska hakan bai hana ni yin dabdala a
dakinta ba a dalilin Nazira.
Bare ita kuma da dakin Goggonmu take kwana..
Sau dubu gara Inna akan Mama. Domin dai ba yadda za'a yi Inna ta ha'da wa Goggo
sharri, ko ta tsokane ta da gangan, amma bata wani girmama ta a dalilin Mama ta
dabarbarce ta, ta hana ta yin mu'amala da Goggo ta hanyar fa'da mata Goggo ce da
gida, duk yaranta maza ne, idan Alhaji ya mutu duk su din y'an kallo ne.
Da na fara mallakar hankalina sai nake tambayar kaina wai mene ne mahaifinmu ya
mallaka da har ake fatan ya mutu?
A da kam ya yi arziki k'warai da gaske, domin duk girman Gidanmu shi ya zaga ye ya
gine shi, sannan mafi yawa na cikin zuri'arsu shine ya biya musu suka sauke farali.
Amma tun shekarar da aka haife ni ya ha'du da y'an damfara suka yi masa sanadin
karayar arziki, har yanzu da muke da shekaru goma sha biyar bai farfad'o ba.
Yan'uwansa kuma kowa ya zuba masa ido ya zama abin tausayi.
Amma a hakan Mama take fa'din Goggonmu ce zata ja komai.
Wannan kenan.
Sai k'ofar Alh Badamasi(Baban Tsakiya).
Matansa biyu da yara sha biyu.
Na uwargidan Hajiya guda bakwai . Babban d'anta Yaya Jabir, Zakiya, Jamila,
Hauwa, Firdausi, Aisha sai k'aramarsu , Basira. Nan Firdausi ce warinmu.
Sai amaryar Momi tana da yara biyar, Nasiru, Naziru, Sararu, Rumanatu da Kubrah.
Anan ma Saratu ce sa'armu.
Sai kofar k'arshe ta Alh Iliya (Baban kasuwa).
Matarsa daya da yaransu shida.
Amina, Aminu, Maijidda, Kaltume Abba andda Aliya.
Maijidda ce sa'armu
Sai wajen kakarmu Hajiya Binta! wadda Yaya Umminmu sunanta ta ci. Kowa Dada yake
ce mata, wata irin tsohuwa mai wahalar sha'anin gaske.
Tana daga zaune rikicin da take yi ba dan ka'dan bane, haka nan bata damu da ha'din
kai a tsakanin ahalin gidan ba.
Domin bayan su Babanmu akwai yan'uwansu mata biyu.
Bangaren Dada ma hawa biyu ne, domin akwai wata k'ofar a can ciki bayan ka wuce
k'ofarta ta farko, sannan ana iya fita waje ma ta wannan wajen Sai dai kofar a rufe
take. Amma ba kowa ciki sai kayan ajiye ajiye da dangin kayan noma da tarkace.
Babar Bulkachuwa(Hauwa) ita ta biyo Baban Tsakiya, tana aure a Bulkachuwa, mijinta
Alh Yusufu babban d'an kasuwa ne a kasuwar kayan miya ta Muda lawal a Bauchi.
Ita ce amarya amma sai a kanta ya samu haihuwa ta tsaya masa, uwargidan wabi take
yi, ma'ana idan ta haihu sai su koma.
Tijjani ne babba sai Aliyu, sai Nasir. Sai bayan haihuwar Nasir ne uwargidan ta
haifi Maryam da kuma Hafsa.
Daga nan sai Babah ta sake haifar Ihisan. Kenan yaranta hudu na uwargidan kuma
biyu.
Tijjani ya taso cikin wani irin gata a wajen mahaifinsa a dalilin tsawon lokacin da
ya shafe babu haihuwa.
Sai dai kash gatan ya zame masa d'an zani domin gaba'daya sai ya kangare, tun yana
karaminsa ya ko yi fitina iri iri, shine kame kaji da awakin jama'a yana siyar wa,
gaba'daya ya ki kar'bar tarbiyar da ake ba shi a sanadin duk abokansa lalattu ne.
Duk yadda Baba ta Bulkachuwa da mahaifinsa suke son fige masa wannan dabi'ar abin
ya ci tura.
Akan dole suka raba shi da garin, suka dawo da shi wajen Mahaifinmu da Baban
Tsakiya, tunda su din zafi ne da su ainun.
A lokacin bai fi shekaru sha biyar ba.
Sa'an Yaya Salisu ne, amma shiriritarsa ta mayar da shi cikin kannensa su Anwar,
duk dai su din ma sun raina shi, sun ware shi ba wanda yake son a ganshi da
Bulkachuwa saboda munanan TA'ADODIN sa.
Yayin da mu muke k'ananu sosai
Sai Baba Maryo ita ce autar Dada.
A nan Toro take aure, yaranta biyar amma biyun farko na wajen Dada da ta haifa da
mijinta na farko.
Anwar da Nasiba.
Yaya Jabir, Yaya Rabi'u, Yaya Abba da Yaya Anwar duk sa'annin juna ne tare suka
taso, fikon junansu mafi girma watanni biyar ne.
Kazalika muma y'anmatan tare muka taso. Duk da babu ha'din kai ko ka'dan a tsakanin
iyayenmu mata, hakanan ni da Nazira an fi mayar da mu banza da wofi a dalilin
mahaifinmu ba shi da shi, ga shi dai shine babba amma ya zama fanko, ya zama wofi
dai dai da shawara ba a yi da shi.
Duk yadda ba wani shakuwa a tsakaninmu irin na zumunci, in dai fita ne, to tare ake
tafiya zuwa makarantar boko ko Islamiya.
Haka za'a ganmu zaratan y'anmatan reras da mu.
Kusan ba'a ta'ba yin y'anmata da muke sa'anni da yawa a gidanmu irin akan mu ba.
Domin mun doshi bakwai
Ni Yabi, Nazira, Basira, Firdausi, Maijidda, saratu, Nasiba.
Dukkanmu kowa turbarakallah babu makusa, tunda asalin Kakarmu Dada Bafulatanar Lame
ce asalin fulanin Mali.
To kusan dukkanmu mun samu tsayi da gashinta.
Duk da ni din bani da tsayi, yar shafal ce, matsakaicin kyau ne da ni amma fara ce
sol, sannan kuguna a dan bude yake ka'dan, sai dai kirjina kam ko na kai shekarun
budurci sosai baza su yi wani girma ba.
Kowanne irin sutura na saka sai ta yi mini kyau.
Duk da kayan nawa mafi yawansu masu sau'kin farashi ne a dalilin mahaifinmu baya
samun sukunin yi mana sutura.
Abinci ma da wahalar gaske muke cinsa, duk da ga yan'uwansa nan suna cin duk abin
da suke so.
Amma ba'a yi mana kara ni da Nazira idan zasu yiwa y'ay'ensu sutura su ha'da da mu.
Ko da yake Nazira ta fini sutura a dalilin Mama tana sanya yayyenmu na d'aki suna
yi mata.
Yaya Salamatu tana d'an yin kara tana bada kuncen har da ni, da yake babu laifi
mijinta yana da rufin asiri, amma Mama bata bari a bani, sai dai da Yayar ta
fahimci hakan sai take bani a b'oye tana fa'din ba sai na fa'da ba.
Ni kuma bana iya yin shiru sai na nuna wa mahaifiyarrmu, ita kuma sai tasan yadda
ta yi ta yi mata godiya tana kuma jan hankalina na kula da ita.
Sosai nake ganin kirkin Yaya Salamatu duk da dai sai ta zab'e mafi kyau ta bawa
Nazira ni kuma ta bani saffa saffa, amma dai ta k'ok'arta a yadda mutanan yau suka
dauki y'an uban ci.
Yayata da muke d'aki d'aya ita ma tana cikin matsanancin babu, domin duk talaucin
gidanmu a hakan Goggo take tara mata k'anzo dan ta ci ita da yaranta.
Wani irin bahagon miji take aure, bai san hakkin komai ba sai hakkin auratayya
tunda kusan duk shekara biyu suke haihuwa ita da uwargidanta tamkar masu gasa. Dan
ma yanzu uwargidan ta daina yi.
Hatsin da za'a yi tuwon dare kawai zai bayar, dai-dai da cefanen miya mace ce zata
yi, da safe a yi dumame a ci yadda ya samu, ba dan an koshi ko dan da'di ba.
Da rana kuwa ko wacce ita zata ciyar da kanta da y'ay'anta.
Ba maganar sabulun wanki bare a je ga na wanka.
Yaya Ummi kyakkawar mace amma wahalar da miji ya sakar mata da muguntar kishiya ta
saka duk ta fita a hayyacinta.
Domin ita ce mai k'ananun yara, ita d'ayar al'amura sun fara saisaita mata, tunda
manyan ya'yanta sun kawo k'arfi, amma komai zasu kawo a boye ne, ita kawai zata
amfana.
Duk cikin yaran gidanmu tafi kowa shan wahala a gidan aure.
Shi yasa take a ware, sai idan Yaya Rabi'u ya d'an figi wani abu ya kai mata a
dalilin suma suna fama da rik'ewa Babanmu gidanmu.
Rayuwar ta yi mana tsananin gaske, mahaifiyarmu ha'kuri take yi kan ha'kuri.
Kuma wani abin mamaki da Mijin Yaya Ummi mai tarin dukiya ne amma fa baya iya ci,
sai dai ya yi ta lissafin kadarorin da ya tara.
Manyan yaransa sai fatan ya kauce su ci abin da bai bari sun ci ba suke.
Gaba'daya tausayin Yaya Ummi nake ji, abubuwa sun yi mata yawa, ga tashin hankalin
gidanta, ga azabar yan'ubancin da su Yaya Indo suke yi mata.
Sun wareta, Yaya Salamatu ce mai sassauci kawai.
Duk sadda ka je gidanta haka zaka ganta tamkar mahaukaciya.
Wankau take yi, kamar me? yini take tana wanki.
A hakan take samu ta wanke kayanta da na yaranta, ta kuma samu ku'din da zasu ci
abinci da rana.
Duk da dai bashi yafi yawa, sai ta yi wanki sau nawa ba a biya ba.
Na kan yi mamakin yadda mutanen yau suka shagala da fa'din Annabi (S.A.W.) na cewa
"Mafi adalcin mutum shine Wanda yake biyan hakkin Wanda ya yi masa aikin wahala
kafin guminsa ya bushe.
Amma a wannan zamanin sai mutum mai wadata ya bawa miskini aikin wahala amma
biyansa hakkin wai sai ya zama bashi, abin kaicon ma idan an yi masa aikar a bayar
da ku'din nan, sai ya zama laifi.
Mace ma'aikaciya sai ta bari ku'din mai wanki, ko markade, ko kuma mai dakan hannu
ya taru a kanta.
Ba tare da yarjejeniyar sai k'arshen wata zata biya ba.
Anya kuwa muna son ganin dai-dai jama'a?
Wannan wahalar data taru ta yi mana k'awanya ya sanya na mayar kitsona na ku'di.
Domin tun daga alhamis idan na fara k'itso har lahadi, amma ba wanda zai cire ko da
sisi ya bani a cikin matan gidanmu da duk kusan sati nake yi musu kitson su da
y'ay'ansu.
Kuma na sani hakan baya hana su karbin ku'din kitson a wajen mazajensu, ko
iyayensu.
Bisa shawarar Nazira na daina yiwa kowa kitso sai ta biya.
Iya y'an k'ofarmu kawai nake yiwa kitso kyauta.
Mama kuwa bata yarda ta ba ni kanta dama.
Amma ina yiwa Inna da Gwaggonmu.
Da kuma yan'uwana na k'ofarmu.
Ai wannan bijirewar da na yi akan sai an bani ku'din kitso ya sake jefa tsana a
tsakaninmu, domin duk inda Mama ta zauna sai ta ce "Uwarta ce ta kitsa mata, me
za'a yi da irin wannan haihuwar a ce ba zaka bari aci arzikinka ba?"
Iyayenmu maza da suka san suna biya basu dauki al'amarin a wani abu ba. Domin suna
k'yashin a ce mu d'in muna da mamorar da zamu yi musu alfarma.
Domin fa'di suke yi "Idan ku'di ne ku bata kudinta daidai da yadda na waje zasu
biya ta, ko kuma daidai da wanda idan kun je wajen bare zaku bayar. Ita ce bata
gaji arziki ba".
Yayin da muka k'udire a ranmu ni da Nazira ba wanda zai sa na yiwa yaransa ko
matarsa kitso akan dole domin suma basu taimake mu ba, dai-dai da ku'din islamiya
da bai taka kara ya karya ba, basu ta'ba ha'da mu da y'ay'ansu sun biya ba.
An sha koro mu da sauran k'annenmu, akan ku'din islamiya.
Yayin da sauran yaransu basu da wannan matsalar.
Idan zamu yi wata a zaune, Mahaifinmu ko iyayenmu mata basu samu sukunin biya ba,
ba wanda zai dube mu.
Dada kuma ba zata ce wane biya wa yaran nan ba.
Ita kanta ta manta irin da'din da Babanmu ya jiyar da ita.
A yanzu kam ta mayar da shi da dukkan ahalinsa tamkar wasu barori a cikin ahalinta.
Tarin Baban kasuwa ya fi maganar Babanmu sau dubu.
Tunda shine yafi kowa rufin asiri, sai Baban tsakiya.
A batun soyayya kuwa kowa shaida ne Dada bata ha'da lamarin Yaya Anwar, da Tijjani
da kuma Nasiba da kowa.
Sun fi kowa lasisi a gidan, gasu dai ba y'an gidan ba ne tunda iyayensu mata ta
haifa.
Amma sun fimu gata da gadara a gidan.
Yanzun nan Dada zata hau ihu matu'kar aka ta'ba guda a cikinsu.
Sai yaran Baban kasuwa, sai na Baban tsakiya.
Hakan dai hawa hawa abin yake.
Canjin da nake samu a kitso ba k'aramin taimakona yake yi ba.
Haka Gwaggo tana yin kokon safe, muna samu mu sha a ciki, har watarana a aikawa
Yaya Ummi.
Asusu na siya nake tura dan wani abu, domin ina matu'kar jin haushin yadda mu da
gwaggonmu muke koma baya a gidan.
Yaranta maza an d'ora musu nauyi mai yawa.
Yaya Salisu ne kawai ya yi aure, shima ba wai wadatar ne da shi ba, aikin gini yake
yi duk da ya yi karatu amma aiki ya yi wuyar samuwa tunda babu hanya.
Su Yaya Rabi'u kuwa koami na gidan sune, Mama fa'di take ai sune maza, sune zasu
taimaki ubansu, ga karatunsu su suke daukar nauyin kansu.
Dan haka Gwaggonmu bata samun komai, amma idan an nutsu za'a fahimci kowa a kofarmu
yana cin arzikin yaranta.
Duk yan dakinmu ni ce mai tsiwa, ban dauko sanyin halin uwarmu ba.
A tsaye nake kan kafafuna cak, haka zuciyata bata daukar raini. Sai dai kuma bani
da kullaci, ina da saurin afuwa.
A duk sadda na kalli Gwaggonmu da Yaya Ummi sai na tsinci kaina da yiwa kaina da
Iklima addu'a samun miji na gari mai wadata, ko muma ma shiga sahun masu mutunci.
Tun kafin hakan kuma sai Ubangiji ya hore mini iya yarfa kitso.
Duk wata matashiya yar kwalisa a yankin nan ni ce mai yi mata kitso.
A hankali sai na fara gwada lalle.
Nan da nan sai Ubangiji ya sake haska mini.
Layi ake yi mini na kunshi da kitso duk satin duniya.
Muka fara dan warware wa, domin muna samun yan kuda'den yin bu'katar yau da kullum.
Hatta Yaya Ummi ta d'an samu sau'kin matsatsacin da take ciki.
Domin duk sati sai na cire mata wani abu.
Da ku'din asusuna ya yi auki na fasa na siya mana kayan kwalliya masu sau'kin ku'di
ni da Ikilima da Nazira, har ma da Ubaidan Innah. Sai kuma na sake siyan wani na
k'udire niyyar dinki zan yi mana idan kudi ya taru.
Tsawon dauki lokaci ina zubi, kafin na samu na yi mana y'an suturu ni da Iki.
Ai Mama tana ankara da y'ar nutsuwar da muka fara samun kanmu a ciki, sai ta tayar
da ballin sai na bar kitso, domin gashi yana yawa a gidan, ba dama ta zubo abinci,
zata yi ta ganin gashi.
Ko ina gashi ne, ta gaji da wannan k'azantar.
A wannan karon Babanmu ya yi jarumtar cewar ba zai hana ni yin sana'a ba, tunda shi
da kansa ya sani ba k'aramin rufa masa asiri sana'ar take yi ba.
Kusan kullum sai na ba shi naira dari hud'u.
Maganar maganina kuwa idan ba ni da lafiya, na dauke wa kowa.
Dan haka sai muka fara saje wa da su Maijida.
Tunda muma yanzu muna samun yan suturu babu laifi, duk da bai kai nasu daraja ba.
Idan akwai abin da ya yiwa Mama tarnaki rashin kintsuwar Yaya Musa ne.
Gashi dai shi ne babba, amma gaba'daya ya lalace, ya zama d'an iska, hakan kuma
yak'i ya zame mata izna, a kullum cikin aibata yaran da ba nata ba take.
Ta kuma gasgata hannu aka sawa d'anta, da kuma bakin mahassada.
Ta kasa fahimtar rayuwa har yanzu.
Tsabar kyashinta ta hana ya'yanta mata su tallafawa Babanmu da d'an abin da zasu
iya .
Kullum fa'di take ai hidima ta y'ay'a maza ce. Dan haka komai yaranta mata zasu
kawo gidan to nata ne, sai ko idan dafaffe ne sai ta samma wadanda take so, wadanda
bata so kuwa ko ta yi babu.
Sai nake mamakin idan tana habaicin ku'din kitson da nake kar'ba, wai Gwaggo ta
kasa bari a mori haihuwarta, ko ita wa ta bari ya mori tata haihuwar?
Ko Babanmu da ya yi mata hidimar yaran ba dai tasa su kawo masa wani abu na
tallafin gida ba tunda yana da k'ananun yara. Idan ma sun yi hankalin kawo wa to fa
ita ce a hakku a kan kayan, ta dinga gadara kenan duk ba wasu kaya masu yawa ba ne,
tunda dai ba wai ku'din ne da su ba, rufin asiri ne kawai.
Sai nake mamakin wai mene ne manufarta ne?
Da na kasa gane wa sai na ha'kura, amma hakan ya ja hankalina har nake sha'awar yin
bincike da nazari akan gidan yawa mai dauke da mabanbanta iyalai.
*GIDANMU ne kawai kwamacala ta dabaibaye shi?*
*A GIDANMU ne kawai ake yin kasafi irin na kashin dankali ma'ana na sama ya danne
na kasa?*
*A GIDANMU ne kawai ake mayar da babba k'arami saboda ba shi da wadata ko kuwa?*
*A GIDANMU ne kawai ake ta'ba yan ubanci ko kuwa?*
*Ba k'aramin caji kwakwalwata take yi ba dan neman sahihohin amsoshi wadannan
tambayoyin*.

*Ayi bitar da nutsuwa domin wannan karon gidan yawa zamu kutsa sosai*


VIP 1K.
REGULAR 500.
2384876855
SURAYYA IBRAHIM
ZENITH BANK.


*ASSALAMU ALAIKUM*
*Masoyan rubutun Surayya Dee na gaishe ku, na kuma yaba muku*
*Dafatan zaku yi hakuri, ku bi labarin sannu a hankali, har ku fahimci sakon da
nake nufin isar wa.*
*Ba zan ce muku komai ba. Abu d'aya nake da tabbaci ba zaku yi nadamar bibiyarsa
ba.*
*Kawai fatana kada ku kosa da yanayin rubutuna.*
*Allah ya taimakemu, Allah ya zaunar mu lafiya da y'anuwanmu da abokan zamanmu*.
*Allah ya bamu lafiya, ya bamu hakuri da k'addarar da muke fuskanta a rayuwar nan*.



*Surayya Dee*
✍️.

*BAK'AR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*MARUBUCIYAR HALIN YAU DA SABO DA KAZA*


•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


*GODIYA*
*INA MATUKAR GODIYA BISA ADDU'AR DA KUKA YI WA MAMA*!
*ALLAH YA KARBA, YA BADA LADA*.
*HAKA NAN INA NEMAN UZZIRINKU BISA RASHIN AMSAWA. DOMIN NA KARBI SAKON MUTANE SAMA
DA DARI BIYAR, TUN INA AMSAWA HAR AL'AMARIN YA GAGARI KUNDILA*.
*DUK WACCE BAN AMSA BA, INA AMFANI DA WANNAN SHAFIN WAJEN GODIYA TARE DA YABAWA A
GAREKU GABADAYA*
*ALLAH YA JIK'AN DUKKAN MAGABATANMU*.


*KUNSAN DAI YADDA AISHA LAME MAKEUP ARTIST DIN GUDUYO, TA KWARE WAJEN SANIN
HAKIKANIN MAN DA ZAI DACE DA KOWACCE FATA, WALA DRY KO OILY*.
*BABBAN ABIN BIRGE WA DA KAYANTA FARASHI MAI SAUKI NE DA YA ZARTA NA SAURA SALAMA*
*HANZARTA KI TUNTUBE TA DAN KI GA JERIN KAYAYYAKIN ORIFLAME KALA DABAN DABAN*
*SANNAN TANA DA HADADDEN GANYEN SHAYIN DA AKA YI SHI DA GANYAYYAKI MASU SAISAITA
JINI DA KITSE A JIKIN DAN ADAM.*
*LAME TEA YAFI SHAYI MAE MADARA*.
*IDAN KUWA KIKA CI LAME POPCORN INA TABBATAR MIKI KIN YI ADABO DA SAKE CIN WANI
GUGGURU MATUKAR BA LAME POPCORN BA NE*.
*07036662633*.

*3&4*
K'aramar hukumar Toro tana cikin k'ananun hukumomin jahar Bauchi. Duk wani mai
nazari yasan yadda Ubangiji ya wadata Toro da girman k'asa.
Ita ce k'aramar hukuma mafi girma a dukkan fa'din tarayyar Nigeria dama Africa ta
yamma gaba'daya.
Garin Toro an kasa shi zuwa Gundumomi uku.
Gundumar Toro, gundumar Jama'a da gundumar Lame.
Sannan akwai kabilu daban daban bayan Hausawa da Fulani.
A karkashin jahar Bauchi ta ke amma tafi makwbataka da jihar Filato.
Shi yasa garin kewaye yake da ni'imomin kayan itatuwa da rashin zafin rana sosai.
Ba dan ina y'ar garin ba, Ubangiji ya dabaibaye garin Toro da tarin faloli
Alhamdulillah.
Dare ne amma ba ainun ba, mafi yawa mun ha'du a kofar Kakarmu Dada ana ta hira da
tatsuniya. Kannenmu kuma sai wasan d'an dunmi suke yi.
Dukkanmu y'anmata mu bakwai da muke kai d'aya muna zaune akan tabarma, idan aka
dauke shalele Nasiba da take kishingi'de a jikin Dada.
Sannu a hankali Dada take taunar goron bakinta tana mulmulawa.
Kyakkawar dattijuwa mai kyakkawan jiki. Asalin Bafulatanar Lame ce, kowa kuma yasan
asalin mutanan wannan garin fulanin Mali ne da kiwo ya saka suka tsallako Nigeria
suka yi sansani a yankin na Lame.
Wani ikon Allah mafi yawa na ahalinta sun samu kyawun halittar fulanin Lame.
Haka muke y'an gidanmu son kowa k'in wanda ya rasa.
Wani irin kallo take mana na kurillah.
Ta kasa ha'kuri ta ce "Na fa'da muku dukkanku ku zauna cikin shirin ko ta kwana.
Domin kuwa ba zaku fi haka gandare wa a gabanmu ba.
Dukkanku abubuwa sun cika muku k'irji. Ko wacce a cikin ku wanki take yi a gabanmu,
ina kallon zamani ni Binta! Muna cikin alhini. Allah yasa intingifarin da muke
nacin yi mun samu rabauta ana karban sallarmu".
Dariya ta kama mafi yawanmu.
Ni da nake da kaud'i na ce "Dada Ashe ba'a karban sallarku ne?"
Ta rausayar da kai gwanin tausayi ta ce "Ai matu'kar kana da yarinyar da ka yi
saken da ta fa'di a gabanka, to kuwa babu makawa sallarka bata isa gaban zati, daga
bakin k'ofa ake dakatar da ita!"
Nasiba ta ce "Allah ya kawo mafita. Yanzu biya mana karatun na yau".
Nan da nan ta furzar da goron bakinta dan girmama karatun da zata d'ora mana.
Ta tsume ta ce "Mu karanto na jiya".
Muka ha'da baki wurin rera karatu cikin sigar wake muka ce "Idan attishawa ta sauko
mana, idan

Please Login or Register in order to submit comment