You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunda ba balance yake kai wa ba. Ni ce ma na koya masa dabarar ya dinga ajiye
wani abu a banki saboda ko watarana motar zata bukaci gyara. Ko wata lalurar zata
gitto bakatatan. Ba ja in ja ya yarda da shawara ta. Akai akai yake yiwa
mahaifiyarsa da Baban Marina sako. Dada ma bai barta a baya ba. Wani lokacin idan
ya je Jos sai ya tsaya ya musu alheri, sannan ya taho. Hatta su Baban Tsakiya yakan
yi musu alheri kai musu kayan miya ko doya.
Ku'di ne dai baya basu.
Wannan rufin asirin da ya samu ya sanya masu yi masa kallon banza suka shiga nan
nan da shi. Akai akai ake bugo masa waya, sabanin lokacin baya da ba'a saka shi
cikin mutane bare a tuna da shi.
Rannan kwatsam sai ga shi ya dawo da Nasiba tare da akwatinta shake da kayan da
suke nuni zata jima tare da mu.
Na gama nazarinta. Gaba'daya ta goge ta yi fes da ita. Ta cika ko ina dam tabbacin
yanzu tafi samun nutsuwa.
Ni ce shaida muka akan son da take yiwa Baban 2.
Na ha'diye komai na yi mata uzziri tunda shi so Ubangiji ne yake kitsa shi a
zukatan bayinsa. Sannan a lokacin da aka zartar da aurena da shi bata yi mini
koamai ba, sai fatan alheri duk da kuwa yadda al'amarin ya buge ta. Dan haka nima a
yanzu zan mata kawaici ka'dan. Amma ban da aurensa. Wannan kam bazan iya ba. Na
kuma tabbatar da niyyar hakan aka turo ta. Uwarta zata yi komai dan ganin Tijjani
ya aure ta ba tare da ta jin kunyar ubana ba. Ta manta yadda ta ture komai ta yi
sanadin datse soyayyarsu. A yanzu kuma da ake ganin ya samu mamora shine za'a lika
masa ita. Ko kunyar ha'damu kishi bata yi. Kiri-kiri take nuna mini tsana tamkar
wadda agola ce ni a gidan haka take yi mini.
Da daddare muna kwance gaba'daya na kasa sakin raina. Har shi ma na ji haushinsa ya
turnik'e ni, akan wanne dalilin zai dauko ta tunda ga Toro su taho Bauchi?
Ya kasa ha'kuri ya ce "Little wai mene ne?"
Na yi masa banza. Ya tunzura ya ce "Amma dai kin san na tsani na miki magana ki
share ni ko?"
Na kasa bu'de baki na ce mass komai a dalilin kuka nake yi irin na sharbe.
Jin shesshekar kukana ya sanya ya shiga rud'u.
Ya dinga tambayar ba'asin kukan nawa. Sai da na tabbatar na rikita shi matu'ka da
gaske sannan na ce masa "A kan me za'a sa ya kawo mini Nasiba gida ba tare da yarda
ta ba?"
A hankali ya ce "Dada ta ce na taho da ita ta mana kwana biyu. Ita ma kuma ta da'de
tana fa'da mini tana son zuwa ta ga sabon gidanmu. Shine yau da ta ce zata biyo ni
na ce to".
Na tashi na zauna na ce "Hakan ya yi. Wato har waya kuke yi ko Tijjani?"
Ya zuba mini ido sosai domin yasan tunda na gatsa sunasa gatsal to zan iya yin
komai na rikici a tsakaninmu.
Ya sassauta ya ce "Dan ta zo mana bakunta mene ne a ciki?"
A tunzure na ce "akwai komai ma. Bana son bakuntar ta, ba kuma zata zauna mini a
gida ba".
Ga mamakina sai ce mini ya yi "Wai gidan na ki ne?"
Na kad'u matu'ka da gaske. A matu'kar sanyaye na ce "A a naka ne mantawa na yi,
amma ka tabbatar ba zan yarda da kai alhalin ina ganinku a gida daya ba." Na koma
na kwanta, shi ma ya kwanta bayan ya juya mini baya da alamu ya yi matu'kar fusata
da na ce Ban yarda da shi ba. Ya sani kuma ina da hujjar da zan guji zamansu a gida
daya, mussaman karamin gida irin namu.
Washagari muka tashi kowa na ganin laifin d'anuwan sa. Na yi matu'kar boye wa
Nasiba halin da muke ciki. Tare da ita muka karya a kwano daya. Tunda shi ya fice
bai saurari abincin ba.
Da daddare ma hakan muka sake kwana babu jituwa. Domin nasan jira yake na ba shi
hakuri, na kuma rarrashe shi. Ni kuwa al'amarin da yake cina ba k'arami ba ne.
Ko magana bama yi ni da shi.
Ba dan bana son ta fahimci akwai matsala a tsakaninmu ba da ko dakinsa ba zan je
ba.
Amma ina zuwa bayan mun sha hira ni da ita.
Ranar da ta yi kwanaki biyu da daddare mun kwanta. Na bu'de baki na ce "Tijjani
gobe bakuwarka zata yi kwanaki uku a gidanka. A ka'idar shari'a kuma bakunta ta
kwanaki uku ce. To kasan yadda zaka yi ta bar maka gidan a gobe, ko kuma ka ga abin
da baka so".
A tunzure ya ce ",Tun yaushe na ga abin da bana so Asiya? Ai tunda babu yarda a
tsakaninmu magana ta k'are. Ba kuma zan kore ta a gidana ba. Ni da kika gan ni bana
manta alheri komin tarin kalubale da rashin kirkin mutane. Dan haka komai zaki yi
Bismillah".
Na ce "Hakane. Madallah da Tijjani".
Kasan zuciyata kuwa tamkar na tashi na cinnawa gidan wuta haka nake ji.
Washa gari ya saka kai ya fice bayan ya amsa gaisuwar ta a tsaitsaye ba tare ma da
ya kalle ta ba. Haka kuma yake yi mata tunda ta zo.
Mun gama karyawa na kalle ta na ce "Nasiba zan je Kangire dubiya. Wata'kila na
kwana, wata'kila kuma na dawo. Na tafi da yaran nan ko na bar miki su?"
Zucyarta daya ta ce "Ki barsu mana indai baza su yi rikici ba. Idan suna ganin
Babansu baza su yi kuka ba ai babu damuwa".
Na ce "Hakane.
Na shirya kayana set uku a dan k'aramin akwatina, na yi sallama bayan na yi dabarar
tura tagwaye kwaso shanya a baya. Na fice a hankali, bayan na ce mata na bar ki da
wahalarsu kuma".
Ina jin ta tana fa'din 'yayanki ba nawa ba nawa ba ne ke nan Yabi?"
Ban tsaya bata amsa ba gudun kada su fito, su ga tafiya ta.
Da azahar ya koma gidan a dalilin ya dawo daga Dass.
Ya tarar da yara na kukan neman Amminsu. Ya fahimci Yabi ta fice ta bar gidan babu
izininsa. Hankalinsa ya kai k'ololuwar tashi, ransa ya baci ainun.
Cikin hikima ya ce "Da nasan da wuri zan dawo ai bazan bari ta fita ba.".
Nasiba da take kicin ta ce "Nima da ta ce mini zata iya kwana a can na shiga
zullumi."
Ya mik'e ya ri'ke hannun yaran suka fita, ya rasa inda zai tsoma ransa da wannan
tashin hankalin da ya kewaye shi.
"Sha'anin mata yana da gigitarwa. Mene ne abin tafiya ki bar dakinki idan ba kalen
masifa ba little?" Ya furta a fili a kuma ki'dime.


*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*


✍️
*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin
register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*


*JAN HANKALI*
*BAN YARDA A HADA MINI DOCUMENT BA! BAN AMINCE BA.*
*DUK WACCE TA YI HAKAN YANZU, KO BAYAN NA KAMMALA LABARIN NAN, WALLAHI NA KAI TA
K'ARA WAJEN UBANGIJI.*

*FATAN ALHERI GA*
*Aunty Umma Kulsum Muhd Kumo*
*Aunty Maryam Saminu Sulaimanu*
*Gaisuwa da fatan alheri, na gode sosai da alherinku a gare ni*.

*Yabo da godiya ga*
*Mamana*
*Hajiya Zahra Shehu*
*Fatan alheri mai yawa a gare ki da ahalin ki*



Tsawon lokaci yana tunanin abin yi. Ya rasa inda zai dosa meman ta. Ya tabbatar ba
zata nufi Toro ba.
Ya tambayi kansa to ina zata tafi har tana fa'din idan dare ya yi zata kwana?.
Kukan Hamim na sake rib'anya tashin hankalin da yake ciki.
Ga haushinta, ga zullumin fishinta gaba'daya sun ha'du sun yi masa rubdugu.
Ya mike ya shiga gidan, ya tarar ta kammala abincin da take yi. Ransa ya sake b'aci
da abin da Yabi ta yi, wato manufarta ta bar musu gidan su yi komai ma.
Cikin rashin sukuni ya ce "Ha'da kayan ki zan kai ki tasha ki koma gida. Tafiya ta
same ni zuwa gadar mewa. Ba zai yiwu kuma na bar ki ke ka'dai a gidan ba."
Cikin nutsuwa ta ce "To". Amma yaran fa?"
Cikin rashin sukuni ya ce "Zan kai su wajenta daga can, tunda hanya ce".
A hankali ta ce "To ko zamu tafi gaba'daya ina ajiye mu a wajenta sai mu dawo gobe
da ita".
Da rawar ya ce "A a, mu je dai na kai ki tashar, ba zai yiwu na yi ta yawon kasuwa
da ke ba."
Tunda ya ajiye ta a tasha yake gararanba a titunan Bauchi. Gaba'daya ya rasa ta
inda zai fara nemanta.

Nasiba kuwa da ta Isa Toro a gidan Marina ta tarar da gyatumarta tare da Dada.
Cikin mamaki Dada ta ce "Ke da kika ce sai an gan ki kuma sai ki dawo, duka duka
yaushe kika tafi ne?"
Cikin nutsuwa ta ce "Yabin ce ta tafi Kangire dubiya. Shi kuma ya ce na taho tunda
kwana zata yi".
Dada ta ce "Ikon Allah. Ga kuma uwatata bata fadi wani abu ya samu ba, bare mu yi
mata ja je".
Sai lokacin Baba Maryo ta ce "Hmm Wallahi ba abin da ya faru, kawai zamanta ne bata
so a gidan. Shi kuma da yake salallamamme ne shine ya ce ki taho. Yarinya
k'ank'anuwa sai azabar iya barikanci. To duk shure shuren kaza baya hana a dirza
mata wuka. Yabi akwai tuggu Wallahi shi yasa na washe ta, bata da kunya ko kad'an
bare mutunci".

***
Da azahar na dira a Bulkachuwa. Babah sai ganina ta yi kwatsam. A sanyaye ta shiga
yi mini barka da zuwa. Sai da na yi sallah ta bani abinci da ruwa, na ta'ba ka'dan
na rufe. Ta zuba mini ido ainun. Ta ce "Wai mene ne damuwar ki ne Yabi? Maimakon
tunda yanzu ba shayarwa kike yi ba, ki murje ki cike, amma kullum sai fige wa kike
yi tamkar wacce ake tsakurarki?."
Na yi k'asa da kaina, ba tare da na ce komai ba. A tausashe ta ce "Yanzu me yasa
kika taho ba shiri ba komài?"
Na fara hawaye, ba tare da na bu'de baki na ce komai ba.
Ta ri'ke hannuna ta ce "Da ke da Ihisan daya nake jinku. Dan haka zan fa'da miki
gaskiya. Gaba'daya aure hakuri ne. Ba yadda ake so ake ga ni ba. Idan Ubangiji yasa
farin yafi ba'kin yawa a cikin zamantakewar sai a yi ta gode wa Allah. A kuma yi
hakuri da inda aka kuskure. Idan kuwa ba hakan ba sai ki ga gidan aure ya zama
tamkar kurku dan tsanani. Adadin mutuwar aure ya yi ta tunbatsa. Yin sassauci da
kawaici babban jigo ne da yake rike da gidajen aure.
Cikin kuka na ce "Wallahi ina yi."
Ta ce "Na sani. Yanzu fa'da mini abin da ya yi miki har kika kasa hadiye wa"
Cikin kuka na tsara mata yadda muka yi da shi, ban yiwa al'amarin kwaskwarima ba.
Da kuma kafewar da ya yi sai ta zauna da mu saboda tana da alkairai masu yawa a
idonsa. Cikin kuka na ce "Ni kuma Wallahi bazan yarda na zauna da ita ba".
Ta yi shiru, na tsawon lokaci kafin ta ce "Tashi ki je d'aki ki yi kwanciyar ki.
Kar kisa wannan maganar a ranki. Kina da gaskiya dan hakan zan tsaya miki, da kuwa
baki da gaskiya da a yau zan mayar da ke dakinki".
Dad'i ya kama ni. Babah ta fahimci irin rad'ad'in da nake ji. Ina kwance ta shigo
ta ce "Kuma sai kika bar mata yaran?"
Fuska ba walwala na ce "Eh". Ta ce "Da kin taho mini da su, ina cikin kewarsu
ainun. Amma bar masa din da kika yi akwai hikima mai yawa tunda ba sha suke yi ba.
Kukan Hamim kadai ya ishe su ai. Ki yi zamanki ba wanda zai san kina nan tunda
Umman gidan nan tana garinsu tafi wata a can. Ko Nasiru ma baya gari. Aliyu ne ya
ce zai zo yau, to kuma ya fasa sai satin sama, saboda zasu je Ibadan".
Ta dauki abin da zata dauka ta fice. Tana fa'din "Da ni yake zancen".
Sai da dare ya fara ja sannan ya koma gida. Bayan Nasiba ta masa text din ta sauka
lafiya. Tunda ta kira shi ya fi sau biyar yana gani amma bai dauka ba.
Da asuba ya kira wayar Yaya Ummi.
A d'an tsorace ta ce "Yaya Bulkachuwa barka da asuba"
Murya na amo ya ce "Ummilolo taimake ni ki bani lambar mijinki na nemi izinin
aikenki yanzu zuwa gidan Marina".
Ta ce yana jinka ma yanzu haka, na saka ta a sifika ka tambaye shi."
Ya bu'de murya cikin ladabi ya gaishe shi. Ya kuma roki alfarmar zai aiki Ummi zuwa
gidan akan wani al'amari da tayar masa da hankali.
Nan da nan ya ce "Babu komai na amince ta je. Ya mika wayar ga Ummi.
Ta ce "Ya ya ne Yaya Bulkachuwa?".
Cikin zullumi ya ce "Asiya ce ta yi mini yaji Ummi! Tun jiya ta fice ta bar mini
gidan da yara."
A zabure ta ce "Subhanallah a kan me Yaya Bulkachuwa?"
A sanyaye ya ce "Hmm! Kawai mu bar maganar tattauna wa ki tashi yanzu ki je gidan,
ki duba ko ina. Idan kin ganta kada ki nuna komai kawai ki dawo gidanki. Ki fa'da
mini sai na taho".
Yana rufe baki Ummi ta ce "Gaskiyar magana ban jin Yabi zata iya zuwa gidanmu da
sunan yaji. Ta tsani yamididi, tana kuma matu'kar tsoron bacin ran Baban Marina".
Ya fesar da iskar damuwa ya ce "To saboda Allah ba kisan inda take ba Ummilolo?"
"Wallahi ban sani ba, ko waya bamu yi da ita ba. Amma bari na je sumame gidan
Nazira".
Da sauri ya ce ",Yauwa Ummilolo, na gode, hanzarta dan Allah".
Ta ce "Zan sallami mutanan gidan da abin karyawa tukun".
Akan dole ya ce "To."
A hanzarce ta gama dumame ta sallami kowa.
Kusan da sanda ta shiga gidan Nazira domin ta tabbatar mijinta baya nan. Amma bata
ga wata alama mai kama da rashin gaskiya ba. Suka gaisa ta tambayi yara.
Ta ce "Daga ina Yaya Ummi?"
Ta ce "Mafarkin ki na yi Nazira shi ne na taho dan na ganki, na ga lafiyarki".
Da'di ya kama Nazira. Ta ce "Madallah da Yaya Ummi. Kin kuma tarar da ni lafiya,
har na karya na yi hidimar gida".
Ta mike tana fa'din "Alhamdulillah! Tunda na ganki lafiya bari na tafi".
Ta hanzari Nazira ta yi kicin dinta ta juyo mata dafadukan macaroni mai dan dama a
madaidaicin filas. Ta ce ga shi ki kaiwa yaran nawa. Na maigidan ne bai tsaya
karyawa ba. Ana ta jiransa zasu je Lame. Ya dai sha kunu a tsaitsaye."
Ta karba da godiya ta tafi. Maimakon ta zarce gidan ta, gidan Marina ta yiwa
tsinke. Duk wani bin kwakkwafinta bata ga ko ganin wata alama da take nuna sun san
Yabi bata gidanta ba. Dan haka suma ta yi musu sallama ta tafi ba tare da ta bu'de
musu komai ba.
Sai da ta isa gidanta sannan ta kira Bulkachuwa ta tabbatar masa Yabi bata zo Toro
ba. Ya lalube ta anan Bauchin.
A rikice ya ce "Yanzu Ummi abin da Asiya ta yi mini dai-dai ne?"
Kai tsaye ta ce "To ai bansan me ya faru ba Yaya Bulkachuwa".
Ya ce tsaya ki ji, ki fa'da mini inda nake da laifi, ki kuma fa'di shin ta kyauta
mini kenan?"
Ta ce "To zan fa'di gaskiya tsakanina da Allah kuwa".
Ya numfasa ya shiga koro mata bayani tiryan tiryan na gaskiya.
Bata katse shi ba sai da ya gama tsaf ya ce "kin ji abin da ya faru".
Ta numfasa ta ce "Ka yarda gaskiyar magana zan fa'da?"
Da sauri ya ce na gasgata ki Ummi. Komin tasirin jini na sani zaki yi adalci domin
ke din mai kauna ta ce na shaida."
Ta ce "Na gode sosai. Amma gaskiyar magana kai ne baka kyauta ba. Kasan Yabi tasan
akwai tsohuwar soyayya tsakaninka da Nasiba. Yanzu Kuma bata da aure. Akan wanne
dalilin zaka dauke ta da kanka ka kai ta gidanka da sunan ta zauna, ba zama irin na
bakunta ba.? Me yasa da Yabi ta ce bakuntar kwanaki uku ta amince ta yi muku baka
yarda kun fahimci juna ba? Me yasa ka ankarata ta hanyar ce wa Nasiba tana da
darajar da ba zaka kore ta a gidan ka ba?. Tsakanina da Allah wannan maganar ta yi
nauyi a zuciya. Ai da sai ka ce mata ita ta kore ta, shi kenan magana ta k'are."
A sanyaye ya ce "Na gode na kuma yarda na yi kuskure. Amma me yasa ta zarge ni?"
Kai-tsaye Ummi ta ce "Kai ka bada k'ofar. Me yasa dan Nasiba zata zo gidanka sai ta
hannunka zata biyo? Ba Yabi ce matar gidan ba? Me yasa sai da kanka zaka kai ta? Me
yasa ka kausasa harshen ka akan zamanta?"
Ya ce "Yanzu dai Ummilolo Yabi ta yi dai-dai da ta fice ta bar gidan babu izinina?"
Ta numfasa sannan ta ce "A fuskar shari'a bata kyauta ba. Amma tunda ni mace ce
nasan yadda take jin zafi a zuciyarta bata yi laifi ba, tunda ka nuna wacce bata
zama dolen ka ba sai ta zauna mata a gidan ko tana so, ko bata so, ba tare da
rarrashi ba".
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Na gode sosai Ummi. Na kuma gamsu da wannan gaskiyar
ta ki babu son kai a cikinta. Kuma yanzu hakan tun jiya na saka Nasiba a mota ta
dawo Toro. Na sallame ta a kurarerren lokaci ko?"
Nan ma Ummi ta ce "Eh, baka girmama ra'ayin matarka ba, sai da ka bari ta yi maka
tutsu, hakan kuma zai haifar muku da tazara da tsatsar zuciya mai yawa".
Cikin karaya ya ce "Na gode bari na shirya yaran nan, mu fita nemanta, ki taya ni
addu'a, gaba'daya yarinyar nan ta gigita ni. Wato Yabi jidalinta mai girma ne."
Ummi ta kwashe da dariya ta ce ni fa ban ga laifinta ba Yaya Bulkachuwa. Haka kawai
za'a lallaba a yi mata kutse mai dafa zuciya, da saka jinya a gangar jiki".
Ya numfasa ya ce "Allah ya sauwake, ni Wallahi babu tunanin komai a zuciyata akan
hakan".
Ta ce "Kai kasan hakan, mu ina muka san zuciyar ka?"
Ya ce "Shi kenan bari na saka d'ambar neman ta."
Suka yi sallama, ya kashe wayar tare da zurfafa a tunanin ta inda zai fara nemanta.
A daddafe ya yi wanka saboda azabar kukan Hamim. Domin a bakin band'akin ya zauna
yake kuka na tashin hankali. Hanif kuma sai ri'ke shi yake alamun wai ya yi shiru.
Dan haka ko da ya fito a rikice ya shirya, ya dauki yaran da yake ta gunjin kuka.
Yasan kukan neman Amminsu yake yi. Allah ya zuba masa k'ulafacin uwa. Ya gama shawo
kan Hamim ya yi shiru, sai kawai Hanif ya fa'di ya dan bugu a goshinsa. Ya fara
kuka shi ma.
Hamim da dama kukan ba daina shi ya yi gaba'daya ba, sai kawai ya bu'de baki yana
taya Hanif. Suka rikice masa ainun.
Ya jima kafin ya samu su tsagaita. Shi da kansa ya fahimci d'a sai uwarsa. Duk da
yadda ya iya raino. Amma rashin Yabi a tare da su sai komai ya k'wace musu daga shi
har y'ay'an sa.
Har suka bar gidan bai yanke shawarar inda zai dosa ba.
Amma yana hawa titi zuciyarsa ta fi rinjayar masa ya je Bulkachuwa.
Dan haka gidan mai ya shiga ya sha mai. Ya siya wa yaran yoghurt da cake. Sannan
suka dau hanya. Yana yi yana daukar fasinja dan ya samu sau'kin tsadar mai.
Da walwala Babah ta karb'e su. Tana ta tambayar ya aka yi suka baro Yabi a gida ita
kad'ai?
Ya dan diririce, bayan ya ga rashin wasa a fuskarta. Murya babu karsashi ya ce
"Bata jin da'di ne shi yasa bamu taho tare ba, nima kayan miya na kawo nan Dambam".
Ta ce "Ayyah me ya same ta? Ko zazzabin damina ne da ko ina yinsa ake yi".
A sanyaye ya ce "zazzabin cizon sauro ne, amma da sau'ki rashin k'warin jiki ne
kawai."
"To Ubangiji ya bata lafiya". Ya amsa da Amin cikin damuwar to ina Yabi ta fantsama
kenan?
Ya kasa ko da shan ruwan da yake gabansa bare kuma abinci. Yara dai suna ta cin
abincinsu.
Ta zauna tana fa'da masa sati mai zuwa Aliyu zai je Ibadan yin jarabawar zama
likita, tunda karatun likitanci yake yi a jami'ar Jos.
A gajarce ya yi murna da fatan alheri. Ta fahimci rudun da ya shiga amma ta matse
ta yi kamar bata gane ba.
Ya sassauta murya ya ce "Tafiya zan yi, zan bar yaran a nan, zuwa jibi zan dawo".
Cikin nutsuwa ta ce "Haka kawai ka dauko su babu shirin zasu zauna ka bar mini su?
Uwarsu ba zata ji dadi ba".
Ya basar ya ce "Ko ba wajen ki na kawo su ba, har ta yi mini inkarin inda na kai su
bare kuma wajen ki ne".
Da azama ta ce "Wallahi ba zaka bar su ba, tunda kai ma ba da nufin su kwana ka
taho da su ba. Kaya kala daya ka sako musu a leda. Nasan kuma idan sun bata na
jikinsu a sauya musu ne iya yau. Ka bari idan ka shiryo su da kayansu sai su zo
mini, amma ba haka kawai a shiga hakkin uwa da y'ay'an ta ba".
Ya rasa yadda zai yi, a kan dole ya kwashe su suka juya.
Ni da nake mak'ale a daki, zuciyata sai tsalle take yi a kan na ga yarana. Da k'yar
na daure ban fito ba.
Da suka tafi kuwa sai na ji tamkar na ruga a guje na ce "Ga ni nan".

Na kwanta lamo. Ina kallon silin. Babah ta shigo yanayin da ta ganni a ciki sai ta
yi turus. Ta iso ta zauna a gefen k'afafuwana. Ta sassauta murya ta ce "Nasan zaki
so yaranki a tare da ke. Amma ki daure ba jimawa zaki yi ba. So nake ya rikice
gaba'daya, ta yadda da kansa zai zo da bakinsa ya fa'da mini ba kya tare da su.
Har da ce mini wai kina gida zazzabi kike yi".
A hankali na ce "Idon Hamim ya yi ja?"
Ta galla mini harara ta mik'e ta na ce wa "Ban sani ba. Idan kuwa haka zaki mini,
ki kuntata kanki sai ki zo ki bi bayansu kawai".
Ta fice tana ta sababin masifar son y'ay'a da iyayen yau suka mak'alawa zukatansu.
Da gaske dai mace tana saurin yin afuwa ga namiji a dalilin yaranta. Domin tun
yanzu na fara kewarsu. So nake na bu'de ido na ga suna wasan hawa da sauka a
jikina.
Na fesar da iskar damuwa. Na sani daga shi har yaran suna cikin kewata mai yawa.
Barin ma sarkin kuka da k'ulafaci Hamim.
Haka na zauna, ina jin wani irin abu na bina.
**
Bulkachuwa kuwa da k'yar ya isa Bauchi domin ya shiga rudun inda zai ga Yabi. Ya
kira wayarta yafi sau goma ana fa'da masa a kashe take. Amma ya kasa dainawa.
Suna isa gida, dakinta ya dire. Yaran da suka waiwaya basu ganta ba, suka dinga
kuka a tare. Shi kansa ji yake tamkar ya bare baki ya tayasu. Gaba'daya azanjinsa
ya k'are. Da k'yar ya shawo kansu suka yi shiru. Kwanaki biyu yana tiritiri da su.
Sa'ar da ya yi ma ya riga ya saba da hidimarsu. Jiya a Toro suka yini, yana bulayin
yiwa gidajen mutane dirar mikiya ko zai ga Yabi. Amma shiru tamkar Malam ya ci
shirwa.
Komai ya tsaya masa cak. Kan dole ya sake komawa Bulkachuwa da su.
Ya rasa ta yadda zai fa'dawa Babah Yabi ta gudu ta barsu.
Ya gama kame kamensa ya fa'da mata gaskiya sun samu sabanin fahimta da Yabi ta yi
yaji, ya kuma neme ta ya rasa tsawon kwanaki uku kenan.
Ta dauki salati mai tsananin gaske. Ta dake ta ce "Yarinyar da ubanta ya damka mini
amanarta a hannuna ka yiwa sanadin da ta gudu ta fantsama duniya?"
Ya yi tsumu ya rasa me zai ce. Ta ce "Sai ka fa'da mini abin da ka shuka mata har
ta kasa ha'diye wa ta bar maka wadannan yaran da suka shiga ranta. Ta tafa hannu
tana skae kambaba girman lamarin. Fadi take yi "Duk uwar da tafi ta bar k'ananun
y'ay'anta ai ba'kin cikin da take ha'diye wa ba ka'dan ba ne. Tura ce ta kai
bango".
Ya kasa ce wa komai. Illah zufa da take yanko masa tamkar mai hadiyar kunama.
Cikin bacin rai ta ce "Ya ya ina magana ka mini shiru sai zare ido ka ke yi irin na
rashin gaskiya".
Murya babu amo ya ce "Wallahi ba komai na yi mata ba. Nasiba ce ta zo shike nan ta
kwarzabi kanta."
"Ta kwarzabi kanta kamar ya ya?"
Ta tambaya cikin wani irin yanayi na bacin rai mai yawa.
Ya numfasa ya ce "Ce wa ta yi sai na kore ta. Ni kuma na ce bazan kore ta ba. Shi
kenan na dawo na tarar ta bar gidan".
Ta rausayar da kai ta ce "To ai Yabi
ta yi adalci. Sai da ta fa'da maka bata son zamanta. Kai kuma ka nuna kana da
bu'katar ta zauna a gidan tunda

Please Login or Register in order to submit comment