You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k'are wa.
Ya zaunar da ni ya sassauta murya ya ce "Asiya yanzu a ce abincin da zamu ci ba
zaki dinga girka wa ba?
Kina kallon kayan miyan can da yawa sun lalace. Ya kike so na dinga yi ne? Idan na
fita tun safe na dinga bulayin abin da zan yi na samu taro da sisi dan asirinmu ya
rufu amma bazan dawo na tarar da kwanciyar hankali ba? Yini nake cikin zullumi da
fargabar halin da kike ciki, da abin da zan dawo na tarar.
Me yasa bani da wata alfarma ne a wajen ki?"
Na zum'bura baki ainun.
Tsawon lokaci ban ce komai ba.
Ya numfasa ya ce "Pls Asiya na roke ki, mu zauna lafiya ki kwantar da hankalinki
dan Allah".
Tsawon lokaci ya dauka yana rarrashi, akan na ce masa na yarda zan dinga yin girki.
Amma ban yarda na ce masa komai ba.
Ya harzuka ya ce "Allah kai ne shaida ta."
Ya tashi ya bar ni.
A hakan na cike sati biyu.
A wannan lokacin kuma aka fara zuwa mini lalle da kitso. Na rasa a inda zamu dinga
zama. Domin tsakr gidan babu bishiya kuma babu rumfa.
Baranda kuma idan rana ta bude babu dadin zama.
Dakin da kayansa suke nan ne yafi dace wa ya zama dakin da zan dinga yin sana'a ta.
Dan haka na shiga na tattara masa kayansa gefe d'aya, na kunna turaren wuta a
dalilin kayansa masu datti na zube a k'asan. Na ha'da na d'aure su waje guda.
Yini na yi ina lalle. Sai yamma ya dawo gidan da ledar abincin da ya siyo mini.
Kallonsa kawai na yi, na gane ya ji haushin cika masa daki da na yi da mata.
Ya ajiye abincin ya juya.
Sai dare ya dawo lokacin babu kowa. Tuni kuma na share dakin na kintsa shi tamkar
ba'a ciki muka yi ba.
Fuskarsa a daure ya tarar da ni ya ce "Asiya Toro kada ki kuma shigar mini daki da
nufin yin kitso ko lalle".
Na cuna baki na ce "Idan na kuma fa?"
Ya girgiza kai ya ce "To ki kuma din".
Washagari da hantsi sai ga Rafi'a ta shigo mini.
Da walwala na karbe ta.
Ta dinga fa'din "Amarya ashe haka kika iya kunshi da lalle?"
Da murmushi na ce "Ina koya dai, idan kina so sai ki zo na yi miki".
Da babbar muryarta ta ce "Ai kuwa na gode sosai".
Tijjani na fita na shiga d'akin muka fara yin kunshin.
Kafin na gama mata har mutum ukun sun zo.
Da azahar ya dawo gidan, ko d'ar ban ji ba, balle na yi fargabar na karya dokar sa.
Ga mamakina bai shigo ba, bare ya dauki matakin da nake son ya dauka.
Amma sai na ji ya bu'de murya yana kiran Rafi'a daga falon.
Ita kuma ta shiga da saurin ta.
Wani irin abu ya d'an mintsini zuciyata.
Amma na sanya jarumta na boye abin dana ji din.
Ina dan jiyo maganganunsu, har na fahimci sun saba dama tunda yayanta abokinsa ne.
Bansan me ya ce mata ba, na ga ta fito ta shiga kicin.
Abin ya sake buguna.
Ban ankara ba na ji ta fara jajjage.
Wata babbar mace da na gama sanya wa lallen.
Ta kalle ni babu alamun wargi ta ce "Je ki karbi hidimar mijinki a hannun waccar
yarinyar tun baki janyo wa kanki sanadin bacin rai ba".
Na yi yak'e na ce "Ai tare muke da ita, k'anwarsa ce."
Ta saki gauron numfashi ta ce "Tau ya yi babu laifi, na dauka babu sidi bare sadada
a tsananinku. Amma dai kada ki fara saka wani lallen, tashi ki je ki marabce shi,
ki bashi ruwa sai ki dawo.
Ki kula da auren ki da kyau kin ji".
Ganin ta haife ni, dan na tabbatar tana da yaran da suka zarta ni.
Hakan ya sanya na tashi na yi tamkar na je wajensa, nan kuwa dakina na shiga na
zauna bakin gado.
Tamkar mai jirana sai gashi ya shigo mini.
Ya kaurara murya ya ce "Asiya Toro ba ki ji kashedin da na yi miki ba akan shigar
mini daki da mata ba ko?"
Na murguda baki na ce "Ban ji ba Tijjani! Ba kuma zan ji ba".
Ya ce "Shike nan"
Na riga shi barin dakin.
Ina kallon yadda ta shirya masa abincin a tray, cikin flask mafi kyau a kicin din.
Plate din na tangaran ta saka. Maimakon da ta kai ta fito, sai ta yi zamanta suna
hirarsu.
A daddafe na kammala lallen. Dan da wata ta zo ma ha'kuri na bata, na ce ina da
ayyuka mai yawa ga kuma maigidan na nan.
Wani irin makakin ba'kin ciki nake ji har cikin mak'oshina.
Duk da bana son Tijjani amma na ji zafin kiran Rafi'a da ya yi. Mussaman umarnin yi
masa girki da ya bata.
Ina da eani irin kishi tun ina karama ta. Har ta kai Gwaggo kullum cikin yi mini
addu'ar samun sassauci take yi.
K'asan zuciyata kuma ban yarda kishinsa nake yi ba. Tunda ba wai ina sonsa ba ne.
Kawai wula'kanta ni da ya yi ne ya mini ciwo.🤣
Sai da ya gama ta fito da kwanukan abincin.
Da murmushi ta ce mini "Na gode sosai Amarya. Sai na sake shigo wa".
Ga mamakina na kasa yi mata ko da yak'e ne.
Murya a dakushe na ce "Madallah".
Da daddare ina falo, ina kallo ya dawo. Sai da ya yi wanka, sannan ya shigo ya
zauna.
Cikin nutsuwa sosai ya ce "Asiya na ce kada ki kuma shiga mini daki da nufin yin
lalle ko kitso amma baki ji ba ko?"
Yana rufe baki na ce "Tijjani ban ji ba, ba kuma zan ji ba, ka yi abin da zaka yi
marar tsoron Allah kawai".
Ya yi mini k'uri ya ce "Me na yi miki na rashin tsoron Allah? Ni ban fa'di hakan
akan ki ba, sai ke zaki fa'da mini hakan?"
Babu fargaba na ce "Ina da tabbacin bana aikata kaba'ira, kai kuwa kaba'irori nawa
kake aikata wa? Tsabar shaharar da ka yi a BAKAKEN TA'ADODI har gidan auren ka ma
bai tsira da sharholiyar ka ba".
Ransa ya baci. Amma da ya fahimci kishin Rafi'a ne ya k'ume ta, sai farin-ciki ya
maye gurbin bakaken kalamanta. Da alamun da Rafi'a zai yi amfani ya dinga rama
wula'kanta shi da take yi.
Ya girgiza kai ya ce "Sharri dai dan aike ne. Mussaman wanda aka ginasu akan zato
da jita jita."
A kufule ainun na ce "Ba batun sharri a lamarinka. Iya karshen cuta an yi mini.
Amma na barwa Allah al'amurana"
Na fa'da hawaye na subuce mini".
Ya kasa cevwa komai.
Tsawon lokaci mun yi jigum jigum! Sai hawaye da suke tsere a kan fuskata. Babu
kuzari ya taso ya dawo kusa da ni sosai ya sassauta murya ya ce "Kinsan bana son
kukan ki Asiya!
Na tari numfashin sa a zafafe na ce "A gidan uban waye baka son kukan nawa?
Makaryaci, mugu, bunsuru..!
Ai ban karasa ba, na ji wani irin gigitaccen mari a fuskata. Wanda ya sanya na
zunduma ihu a matu'kar ki'dime.
Cikin fishi mai yawa ya ce "Kin ci uwar karya kin kwana da yunwa Asiya. Kin yi
ka'dan ki zagi ubana, ki wanye lafiya. Ashe togaciyar da na yi miki kwanaki a
zauren gida baki ji ba?
Wallahi ki mutunta ta kan ki, ki kame bakinki daga zagina. Ni zaki ce wa a gidan
uban wa? Ubana zaki zaga? Baki isa ba, rashin kunyar ki ya tsaya a kaina. Ni da
kike ganina nasan mutuncin iyayena da gaske, ba wai yaudarar ina sonsu a baki ba,
amma na kasa kare musu martabarsu a bayan idonsu ba."
Ya mike tsaye ya ri'ke kunnensa alamun gargadi.
Da kumfar baki ya ce "Billahillazi kika kuma yi mini lalle a daki sai na wula'kanta
ki, ke da gayyar ta ki.
Sannan yau ne rana ta karshe da zaki yi gigin zagin iyayena. Ki bari, bana so! Idan
kuma kin ki ji, lah shakka ba zaki k'i ga ni ba".
Ya tafi ya bar ni ina kuka mai tsananin gaske, domin ba k'aramin shigata marin ya
yi ba.
Tunda ga wannan lokacin gaba ta k'ullu a tsakaninmu mai tsananin gaske.
Ya fita daga al'amarina gaba'daya. Baya bin ta kaina, yana dawowa daga sallar
asuba zai fice tun gari bai yi haske ba. Ba zai dawo ba sai wajen Tara. Nan ma
yana gama uzzirinsa zai sa kai ya fice. Ba zai dawo ba sai dare.
A hakan na fuskanci wajen gini yake zuwa. Fitar asubar ne bansan me yake yi ba.
Zuciyata har kissima mini take yi lalata yake fita yi. Dan haka na sake wasarsa, na
sake jin haushinsa.
Bana girki sai dai na saka almajiri ya siyo mini, abincin siyar wa tunda ana yi a
makwabta.
Ina samun lalle da kitso. Ban kuma fasa yi a dakin nasa ba. Sai dai kafin ya dawo
sun tafi, ni kuma zan gyara masa dakin, sai dai k'amshin muhallabiya ya kama dakin.
Bai ta'ba magana ba. Ban sani ba, ko dan bai dawo ya tarar da mu a ciki ba. Ko kuwa
ya hakura ne?.
Cikin wannan yanayin da muke ciki na yi matu'kar rame wa. Na yi baki. Kullum cikin
kuka da b'acin rai na ke.
A ranar da na cika wata guda a ranar Dada ta zo ganin dakina.
Bulkachuwa da kansa ya dauko ta a mashin ya kawo ta.
Ta dinga yaba tsarin dakunan.
Amma ta kasa gamsuwa da yanayinmu. A sanyaye ta ce "Mai sunan manya Yabi ta sake
kankace wa, ta yi duhu, duk da ita fara ce kal.
Kai ma dube ka, babu wani annurin angwanci tare da kai."
Ga mamakina sai ya sassauta murya ya ce "Kowa da yadda yake fuskantar kalubalen
duniyar nan ai.
Me nake da shi da zan jiyar da Asiya da'di bare na samu nutsuwa da ita. Na barwa
Allah komai. Idan na mutu Dada na yafe miki wannan ha'din da kika jagoranci aka yi.
Cike nake da fargabar kada auren namu ya sake d'aid'aita zumuncin gidan Marina."
Dada ta dauki salati tana fa'din "Ashe har yau baku shirya ba? Ashe ba kalau kuke
zaune ba, shi yasa ka dinga zille wa idan na ce ka kawo ni gidan ka?".
A hankali ya ce "k'alau muke Dada."
Ta kalle shi ta ce "Tashi ka bamu wuri."
Bai yi musu ba, ya fita din.
Ta kalle ni ta ce "Haba Hajja Yabi. Me yasa ba zaki kwantar da hankalin ki ba? Mai
sunan manya son ki yake irin son nan mai tsananin gaske. Ban ta'ba ganin abin da ya
sanyaya shi irin lamarin ki ba.
Tun wanccan satin na je gidan Ubaida tana zaune k'alau da mijinta. Sai ke ce zaki
kunyatamu?"
Na rushe da kuka sosai na ce "Ita mijinta ai baya wula'kanta ta, baya yi mata
sanadin da zata kwana ta yini da yunwa. Mijinta mai kamun kai ne. Amma ni kuwa fa?"
Kuka ya ci k'arfina sosai.
Duk son kan da Dada ta wanzu tana yi a tsakaninmu da su Bulkachuwa a wannan ranar
na ga damuwa mai yawa akan fuskarta. Na ga alhinin halin da ta gan ni a ciki a
jikinta
Ta bu'de baki ta kira shi. Ya amsa ya shigo.
Ta ce "Me ka ke yiwa yarinyar nan haka? Ai farkon zaman bata birkice ba, tunda kowa
ya zo sai ya ce Yabi tana zaune cikin walwala kamar ba ita ba. Me ya jefa ta cikin
wannan tashin hankalin?"
Da rashin kuzari ya ce "Zagi irin na tsamar nama ta yi mini. Hakurina ya k'wace na
mare ta. Shike nan fa! kuma yau zancen nan an kai sati biyu. Amma ta taurare ta k'i
barin abin ya wuce."
Ya fa'da cikin damuwa mai yawa.
Dada ta ce "Ai baka rarrashe ta ba. Baka ha'diye fishin ka dan ka kawo masalaha
ba."
Da sauri ya ce "To na yarda, na yi kuskure, taya ni bata hakuri. Bazan sake dukan
ta ba, amma ita ma kada ta sake zagi na".
Tausayinsa ya cika Dada domin ta sake fahimtar ya fa'da matsanancin soyayyar Yabi.
Ta nisa ta ce "kin ji abin da ya ce Yabi. Ki yi ha'kuri, komai ya wuce ba zai sake
ba.
Na cigaba da kuka sosai. Ina son na fa'da mata ni girkin da ya sanya aka aka yi
masa ne, yafi nukurkusa ta fiye da marin. Amma bansan dalilin da ya sanya na kasa
fadar wannan maganar ba.
Ta dinga rarrashina tamkar ba Dada da bata yi mini sassauci ba.
Sai da na yi shiru. Sannan ta kalle shi a zafafe take yi masa magana.
"Idan har ka kuma dukanta, to ka tabbatar zan aikawa uwarka ta zo, tunda ka nuna
ban isa ba. Ai ba'a baka ita dan ka dinga gwada mata k'arfi ba. Duka duka ma nawa
take ne Yabin? Ba zaka yi hakuri da kuruciyar ta ba?"
Ya yi shiru ya kasa bu'de baki ya fa'di abubuwan da nake yi masa.
Karshe ya buge da bata hakuri da al'kawarin zai canja.



Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki
da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*.
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA
BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES.*

*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.

*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered,
Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan
farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon
yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.

Tsawon lokaci kafin su samu na yi shiru.
A kokarin Dada na son na warware sosai, sai ta fasa tafiyar ta ce ya yi tafiyarsa
sai yamma ya dawo ya mayar da ita gida.
Ya fita, sai kuma ya bu'de baki ya ce"Asiya".
Na yi shiru kamar ban ji ba.
Dada ta sassauta ta ce "Kiran ki yake yi fa Yabi.
Ki na son ki k'one ne? Girman sa yawa ne da shi a wajen ki fa".
Na tashi bayan na cuna baki tamkar na buta.
Da fishi sosai na tsaya a gabansa.
A sanyaye kuma murya k'asa ya ce "Zan je na samo ko kifi ne, ki yi girki dan
Allah".
Nan da nan na ce "Wallahi bazan dafa da kai ba".
Ya ce "Shike nan ki yi muku. Hakan ma na gode sosai".
Ya fita na bishi da harara. Ba'kin cikin yadda na takarkare na yi masa doya da
k'wai ya k'i ci, ba k'aramin cizo na yake yi ba har yanzu.
Sannan girikin da ya sanya aka shigar mini kicin aka yi masa, sai ya gane ni ba
irin matan da za'a yi musu hakan ba ne.
Bai wani jima ba, ya dawo. Sai da ya shiga kicin din sannan ya fito ya yi dakina.
Dada ta zuba mini ido alamun na tashi na bi shi.
Akan dole na je din.
Ya mik'o mini leda mai d'auke da sink'in sabulun wanka da kwalin TURAREN
Ismiyaki.
Na kar'ba galala.
Ya ce "Idan zata tafi sai ki bata".
Na gatsina baki na ajiye a bakin gadon ban ce komai ba, na fita na bar shi a tsaye,
ya yi wani iri abin tausayi!.
Ya fito ya dan tsokani Dada sannan ya fice.
Zafi ya sanya na yiwa Dada shimfida a baranda.
Ta fito, muna hirarmu ina gyaran kayan miya.
Ina tunanin artabun da zan yi da attaruhu yayin greting. Don kuwa indai na murtsika
attaruhu sai na kwana na yini hannuna na yin mini zugi.
Kwatsam aka kawo wuta. Cikin karambani da giggiwa na ha'da bilandar na fara
markade.
Sai da na zuba shinkafa a dalilin ruwa ya tafaso.
Sannan na koma wajen Dada.
Da murmushi ta ce "Oh ashe dai da rabon za'a samu mai tu'amalli da injin markade na
zamani a jikokina".
Na yi dariya tare da cewa "Dada kenan.
Bari na zauna ki d'ora mini karatu, ina kewar karatun ki."
Ta gyatta, na zauna kusa da ita.
Ta ce "Tunda Ubangiji ya sanya na ga auren ki har ga ni a gidan ki.
To zan 'dora miki karatun da har abada kin wuce yin boranci a idon namiji. Ban
ta'ba koya wa kowa wannan addu'ar ba, saboda jarraba namiji ake yi da ita k'warai
da gaske. Kema dan ina son ki tsare mijin ki, daga sharholiya ne!".
Ban ce komai ba.
Ta yi waiwaye dan ta sake samun tabbacin babu me jin abin da zata furta.
Ta matso kusa da ni ainun.
Murya k'asa kasa ta ce "A yayin da kuka shiga mayafin aure sai ki yi Bismillah ki
ce "Allah daraja, MA'AIKIN Allah daraja a taimake ni akan aure. Zan jarraba y'an
maza wane.. Ibnu wance.
Ki kamo ainihin sunan sa da sunan babar taku, sai ki tofo yawun bakinki akan yatsan
sai ki yi matsi da wannan yawun addu'ar. Amma a zuci, zaki yi fa". Ta fa'da da
dukkan zuciyar ta.
Duk da na saba jin karatun Dada wannan ya yi matu'kar sanya ni mamaki da dariya.
Amma na sanya jarumta na maze, na yi k'asa da kaina a zuwan kunya ce ta hana ni
sukuni.
Ta kuwa dage ta ce "Ba kunya zaki ji ba Yabi! Na baki wannan fahamin ne dan na
taimake ki, ku zauna lafiya. Amma fa kada ki yarda ki dinga jansa a k'asa. Domin
k'arfin addu'ar yawa ne da shi tamkar yankar wuka take".
Na k'yal-k'yale da dariya saboda bilhakki take maganar zan jarabta shi da wannan
karatun surkullen.
Sai da dariya ta tsagaita mini na ce "Allah ya bada lada Dada. Amma ni bazan yi a
kansa ba. Baya sona, bana sonsa. Kowa harkar gabansa yake yi."
Ta dauki salati tana fa'din"Ashe har yau baku zama d'aya ba? Tisa ki yayi a gaba
yake kallon ki kawai?
To idan na tafi zan fara tsayawa wajen Malam Nata'ala na ji ya ya matsayin aurenku.
Domin nasan duk ma'auratan da suka shafe kwanaki arba'in basu hadu ba, tabbas aure
ya haranta. To ku kwanaki talatin da biyu da aurenku. Zan je na sake jin fatawar
kada aje ko auren ya b'aci ba'a sani ba".
Na yi shiru domin na kasa gane bayanin na ta. Ban ce komai ba, domin kuwa ban ta'ba
jin makancin hakan ba.
Ta numfasa ta ce "Yabi kin san duk macen da ta ki d'agawa mijin auren ta k'afa.
Zata zama makamashi ne a cikin wutar jahimu?"
Na yi shiru tare da b'ata fuska. Ta sake ce wa "Wannan hukuncin lahira ne. A
duniya kuwa babu ita babu ganin hasken rayuwa tunda malaiku dubu maitan ne zasu yi
ta kabarbari suna d'ebe mata albarka. Kin san kuwa ko limamin unguwarku ne ya tsine
miki, kin yi hannun riga ke da walwalar rayuwa bare kuma ma'asumai irin malaikun
Allahu".
Jikina ya yi sanyi da wannan karatun na karshe. Wanda babu kuskure ko shaci fa'da a
cikinsa.
Amma da na tuna ai bai ta'ba nema na hana ba, ke nan bana cikin tsinuwar malaiku,
sai na samu sau'kin tsoratar da na yi.
Kafin ta sake magana na zabura na tashi ina ce wa "Bari na duba girikina".
Na tace shinkafa, na yi k'asa da wutar na mayar.
Na duba ledar da ya ajiye na ga salak da kuma ledar soyayyen kifi.
A gurguje na yanka na wanke da gishiri na bar shi a kwandon tsane wa bayan na rufe.
Daidai lokacin na sauke sanwar, na d'ora ta miya.
Na juye a flask na fito da tukunyar na jika ta da ruwa.
Na ce "Dada mu shiga ki yi kallo. Rana ta fara kusantomu.
Ta ce "Zan tashi dai saboda rana, amma ba dan na yi kallon shagala ba.
Na kunna na kamo mata wa'azin Malam Guruntun tana saurare can ta nisa ta ce "ya iya
karatu kuwa. Amma dai wannan ba namu ba ne ko Yabi?"
Cikin k'arfin hali na ce "Musulmi ai d'anuwan musulmi ne Dada. Bare wannan bijimin
Malami ne. Ke dai ba ki ji abin da Allah da ma'aiki suka ce ba ne na ki?"
"Ta kyabe baki ta ce"Masu daddagen wando ai tsakaninmu da su sai a lahira. Tunda
suna raina karamar shehu".
Dariya ta kwace mini. Na dinga yi sosai.
Na canja tashar cikin sa'a kuwa sai ga sheikh Mak'ari yana bayani irin wanda ta
gamsu da shi.
Na gama abinci tsaf. Bamu ci ba sai da muka yi salla sannan na kawo mana. Tare ta
ce na zuba mana. Muna ci tana yaba girkin nawa.
Tana kuma ta yi mini maganganun da suke nuna girman da miji yake da shi.
Ban ce uffan ba, sai da ta ce "Ki kwantar da hankalinki ki zauna lafiya. Nan da
kwanaki ka'dan zan sake kewayo ku. Idan har kika bari kwanakin auren ki ya kai
arba'in baki bari ya ri'ke hannun ki ba. Tabbas zan fa'dawa mahaifin ki. A san
halin da kuke ciki. Kada ku fara zaman haranci".
Na fara kuka tare da ce wa "Ba ruwan ki Dada! Kada ki ha'da ni da ubana, kada ki
janyo mini fishin sa."
Ga mamakina sai ta sassauta ta ce "Idan kuwa har irin haka kike gudun fishin uban
ki. Kamata ya yi ki guji fishin Allah fiye da hakan. Ai ba Babanku ba ne ya hukunta
faruwar al'amarin ba. Allah ne da kansa. Fishin Ubangiji akan bawansa kuwa yana
nufin tabarbarewar dukkan al'amuran rayuwa".
Na kasa bu'de baki na ce "Bai ta'ba nuna wa yana da bu'katar hakan daga gare ni ba.
Saboda yana samu a waje. Sai kawai na sake tsananta kukan da nake yi. Domin har
ciki mak'oshina nake jin ba'kin cikin halin da nake ciki.
Har la'asar ta kawo kai, bata fasa sakin maganganu ba. Wasu na gaskiya, wasu na
barkwanci wasu kuwa masu nauyi ne. Ita kuwa ko a jikinta.
Ina kuka sosai amma bata damu ba sai ce wa ta yi "Da kin san kanki ai da tuni kin
mayar da shi bita zaizai. Mata irinmu masu k'aramin ruwa ai mafi yawa murza maza
muke yi. Kin ga duk haiba da siffar mijin ki. Da kin kwantar da hankalinki, kina
masa biyayya, kina ba shi kanki ai wataran ma sai ya shirya zai fita, idan kika ce
kada ka fita ce wa zai yi to."
Na cuna baki na ce "Da dai ba dan-iskan duniya ba ne".
Ta kuwa zabura ta jefe ni da kofin kusa da ita.
A ki'dime ta ce "Mijin ki kika zaga kai tsaye babu nadama bare shakka?
Tabbas kin kafurta, kin halaka Yabi. Dole sai kin sake karban shahadar shiga
musulunci.
Na kasa kunshe dariya ta. Na k'yal-k'yale da dariya sosai.
Ranta ya baci k'warai da gaske. Ta shiga share hawayen takaici.
Murya na rawa ta ce "Ki aikata kaba'ira sannan ki yi dariya? Saboda ku yaran yau
babu darhamin imani a zuciyarku?"
Na ha'diye dariyar a dalilin kukan gaske take yi.
Da sanyin murya na ce "Ki yi hakuri Dada."
Ta ce "Na ha'kura amma, ai dole ki sabunta musuluncinki Yabi. In kuwa ba hakan ba,
tabbas kin zama arniya.
Cikin k'arfin hali na ce "Ba ni kalmar shahadar na sabunta din."
Ta rike baki ta ce "Wace ni na shiga sahun Malamai. Ni almajira ce me neman sani.
Gaban babban malami za'a kai ki ya baki shahada ki kar'ba. Ko kuma ki yi tuba a
gaban mijinki ki nemi afuwa sannan ya baki kalmar ki kar'ba".
Na bata rai na ce "Haba Dada tunda ba'a gabansa aka yi ba, ina dalilin sai ya ji.
Tunda kin ce na sabawa Allah. Ki bari na ce Astagafirillah! Amma kada ki fa'da
masa. Dukana zai yi, son girmansa yawa ne da shi".
"To shikenan bazan fa'da masa ba.
Amma ki tsananta intigifari Yabi".
Daga haka muka yi haramar sallar la'asar.
Na tattare kwanukan na share wajen kafin ta fito daga bayi.
Mun jima da idar da salla sannan ya dawo.
Kallonsa kawai na yi na gane bai ci abinci ba.
Dada ta dinga yi masa barka da dawowa. Ya amsa yana murmushi wanda na tabbatar na
yak'e ne.
Ta zuba masa ido ta ce "Ya na ganka haka ne?"
Ya ce "Babu komai. Sauri nake yi kada ki ce ban zo da wuri ba."
Bata ba shi amsa ba ta kalle ni.
A dole na ce "Sannu da dawo wa".
Ya amsa da walwala sosai".
Ya ce "Na kai ki yanzu, ko na watsa ruwa?"
A tausashe ta ce "Yunwa kake ji, ka fara cin abinci, nasan baka shiri da yunwa".
Ya yi k'asa da kansa. Bai ce komai ba.
Ta ce "Yabi ki kawo masa ruwa da abinci mana".
Na daure fuska matu'ka da gaske sannan na ce "Baya cin abincina ai".
Ta fara fa'din "Allahu Akbar kabiran, wa subhanallahi bukuratan wa asila. Wanne
irin zama kuke yi ne na kafirci ni Binta?
Baya cin abincin ki sai na wa to?"
Da yake abin na yi mini ciwo sosai. Cikin rawar murya na ce "Sai na y'ar iska
mana."
Dada ta kalle ni da kyau tamkar me yin nazari. Sannan ta mayar da kallonsa kansa.
Gaba'daya ya yi laushi tabbacin ya buga bai samu abin da ya sanya a bakinsa ba.
Tsawon lokaci ta ce "Kira mini lambar Alhaji. Da alamun al'amarin naku ya yi munin
da ba zan iya gyara shi ba."
Tana rufe baki na fashe da kuka Ina cewa "Saboda son kai sai ki kira mahaifina ki
bata ni a wajensa, ki tayar masa da hankali. Alhalin tunda na zo gidan nan ba abin
da nake ga ni sai wula'kanci da tozarci. Ai ni an cuce ni karshen cuta kuwa".
Na fa'di hakan cikin kuka mai tsananin gaske.
Ta saki ajiyar zuciya ta ce "To kira mini Hauwa tunda ita din kin yarda uwar ki
ce".
Shima cikin sauri ya ce "A a Dada kinsan

Please Login or Register in order to submit comment