You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sai dai na lura da rud'anin da
Gwaggo take ciki, gaba'daya ta zama wata iri, ta yi zuruzuru.
Na tambaye ta ta ce mini gudawa take yi. Take na gasgata na tura Anas ya siyo mata
filagil.
Da daddare bayan dare ya d'an fara tura wa Baba ya kiramu ni da Ubaida.
Na cika da mamakin ha'damu da ya yi.
Muna durkushe a gabansa, shi kuma yana kan kujerar ba'kin karfe irin ta da, da take
dakinsa.
Ya kalle ni ya ce "ku zauna sosai. Ina bu'katar hankalinku da nutsuwarku".
"Muka nutsu kuwa, amma gaba'daya zuciyata ta shiga rud'ani sosai.
"Shi da kansa ya jima bai iya yin maganar ba. Ya jima yana juya maganar yana
tunanin ta yadda zai iya fa'dawa Yabi a karo na biyu za'a bawa wata saurayinta.
Babban damuwarsa irin yadda ya ga ta sanya Nura a ranta.
Ransa ya baci fiye da jiya. Ba'kin cikin y'anuwansa ya mamaye shi. Wai me ya tsare
musu a wannan duniyar ne?
Da k'yar ya yi k'arfin halin cewa "Yabi kinsan ce wa a duniya ba wanda zai so ki,
ya so cigaban ki irin ni da gyatumarki ko?"
Ba haufi na ce " "Eh Baba".
Ya ce "Madallah! Sannan kuma ba wani abin kaico da zai dunfaro d'a mahaifi ya zuba
ido ya cimmasa, sai idan abin ya gagare shi.
Ina son ki fahimce ni, ki mini adalci, ki kuma ninka biyayyar da zaki mini a wannan
karon.".
Jikina ya fara tsuma, zuciyata ta shiga zullumi, idanuwa suka cika da ruwa.
Na kasa bu'de baki na ce komai dan tsananin bugun da zuciyata take yi.
Ya numfasa sosai ya ce "Ina son na fa'da miki auren ki da Nura ba zai yiwu ba, ba
kuma na son ki kalli hakan a matsayin shirina ko shirin wani, ki yarda shirin Allah
ne, shi kuwa idan Ubangiji ya jarrabe ka, ka yi ha'kuri a farkon al'amarin kana da
lada da sakamako mai girma".
Take ruwan da ya cika a gurbin idona ya tumbatsa ya fara zuba.
Ina jin nauyin da zuciyata ta yi ba zai kwatantu ba.
Wacce irin Bak'ar kaddara ce nake gudu take bina da gudu shigen na fanfalaki?
Na kasa bu'de baki na ce uffan domin sai na fara hasashen mafarkin da nake yawan yi
ne akan aurena da Nura zai iya ruguje wa.
Jin shiruna ya sanya ya ce "Na sani kina sona, son da yake sanya ki son duk abin
dana haifa, ko nake so.
Ina ro'ko ki taimake ni, na yiwa mahaifiyata biyayya, ni kuma zan dauwama ina miki
addu'ar wanye wa lafiya da kuma rufin asirin duniya."
Cikin rishin kuka na ce "To Babanmu".
Ganin irin rudin data shiga sai wata dabara ta zo masa.
Sai ya ce "Babanku Iliya ya bu'kaci na bawa Nura Kaltume a madadinki".
Na d'ago a matu'kar birkice na ce "Wai me na yi muku ne Baba?
Yan'uwanka suna azabtar da ni, kai kuma ka zuba ido kana kallo, ka kasa kare mini
darajata! Ko dai da gaske karayar arzikinka tana damfare da zuwana duniyar nan mai
cike da ba'kin ciki mai tsanani?"
Na fa'da ina kuka sosai.
*Auzubillahi! Na yafe miki Yabi! Na sani kina cikin ki'dima ne, ni kaina da na
haife ki kiris ya rage ban zautu ba a dalilin wannan al'amarin.
Allah ka sassauta, Allah ka kawo mafita. Allah kada ka jarribi Yabi da jarrabawar
da zata bijire mini. Bare ta haifi wanda zai bijire mata."
Na yi kasa da kaina ina kuka kasa kasa.

*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered,
Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan
farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon
yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.

Tsawon lokaci kafin na ce "Na ha'kura da shi Baba. Amma Wallahi indai aka ba shi
Kaltume to zan roki Ubangiji ya matso mini da ajalina kusa, domin na sani bazan
sake farin ciki ba.
Indai kunyar Babansa kake ji, to ka bashi Ubaida tunda dama saboda kai ya turo
d'ansa ya neme ni, ka bashi ita, zai fi mini sauki a maimakon ka rasa suruki nagari
irinsa".
Ina rufe baki kawai Babanmu ya fara hawayen da ya daskarar damu.
Wanda na tabbatar na zallar ba'kin ciki da kuma farin cikin yadda nake tsananin son
y'anuwana.
Ai ko murya na rawa ya ce "Irin yadda kike son yan'uwanki haka nake son nawa, amma
shaidan da son zuciya sun shiga cikin al'amarinmu sun yi kane kane."
Ya daga kai ya ce "Allah kada ka jarrabi ya'yana da rugujewar zumunta".
Jikinmu ya sake yin mugun sanyi ya ce "Ubaida kin ji me yayarki ta ce shin zaki bi
bayanta wajen sadaukar da burinki, ki mini biyayyar da ke ma zan dauwama ina yi
miki farar addu'a?"
A sanyaye ta ce "Zan yi Baba! Na amince, da ikon Ubangiji ba zan kunyataku ba,
komai zan zama kuma a duniya a sanadin auren nan, na sani arzikin Adda Yabi na ci,
ba kuma zan juya wa al'amarinta baya ba".
Zan yi zumunci da ita a cikin ko wanne hali da rayuwa zata wullamu".
Daga hakan kuma ta fashe da kuka sosai.
Wanda ita kanta bata san dalilinsa ba, amma dai tana jin na tausayin Yabi ne.
Da ya rasa yadda zai fadi Tijjani ne mijin da aka zaba mata sai ya ce "Yabi ki
tsananta addu'ar shiriya ga Tijjani! Ki kuma rage tsananta al'amarinsa ta yadda
zaki fahimce shi da kyau, Annabi ya ce "Addu'ar miji akan matarsa karbabbiya ce,
haka addu'ar mata akan mijinta karbabbiya ce.
Dan haka ki tsananta yi masa addu'ar shiriya, da kuma a cika kirjjnsa da soyayyar
ki da tausayin ki, sannan a buda masa kofofin arziki"
A ki'dime na ce "Baba dan Allah warware mini wannan curarren bayanin, d'an yi mini
gwari gwari".
Da matu'kar rauni ya ce "Tijjani zan aura wa ke".
Ai kuwa na dage na zunduma ihu ina birgima, ina fa'din "Wayyo Allah mutuwar tsaye
ta samu Yabi! Wayyo Allah nakasa ta zo mini. Yabi zata zama iyalin mai *BAK'AR
TA'ADAH*

*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin *Saiwowin ne
da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku
kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*


*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR
TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*

*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.
*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta
sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar
taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi
muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun
san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa,
mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai
soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan
littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan
numbers*
*08089965176*
*07084653262*


*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*



Ina alwallah ina kuka. Ba abin da ya sake karya mini zuciya irin yadda na jiyo
Baban Marina yana cewa Baba "Ni fa ki daina ro'ko na Hauwa! Tuni na yafe mata, amma
walwalata ce ba zata ga ni ba, har sai ta kwantar da hankalinta an yi hidimar nan
lafiya lafiya. Sannan kuma ta zauna lafiya da mijinta kamar yadda y'anuwanta suke
zaune lafiya.
Ina ce Ummi gidan mai iyali aka kai ta? Ga kuma mijin ya d'orawa ransa masifar son
abin duniya. Ba ya sauke hakkin da shari'a ta wajabta masa.
Duk k'uncin da take ciki yau shekaru kusan takwas da aurenta, bata ta'ba zuwa
gabana da nufin wata matsala ko da zummar na taimake ta ba.
Na sani kuma tana bu'katar a taimake ta, amma da yake ta dauko ha'kurin uwarsu ta
shanye komai tana zaune da y'ay'anta, sai kuma ta yi tabarar koyon sana'a cikin
cire girman kai da buri.
Shiyasa ni kuma ban ta'ba yin sallah ban roka mata sassauci a wajen Ubangiji ba.
Duk kuma wanda Allah ya ba shi nisan kwana zai ga yadda Allah zai albarka ci
zuri'arta. Allah sai ya yi mata tukuicin hakuri da biyayyar da ta yi da ikon
Allah".
Da k'yar na tokara na tashi zuwa daki na tarar da Gwaggo tana share hawaye.
A sanyaye na ce "Gwaggo baki huce da ni ba ne?"
Ta girgiza kai sai kuma ta ce "Ina mamakin duk alherin da mace zata yiwa namiji na
ha'kuri da juriya akan al'amarinsa ko na ahalinsa. Amma idan d'anta ya yi laifin da
ita kanta bata sani ba sai ya shafeta.
Ko sai yaushe uwa zata kubuta daga irin wannan kalubalen a k'asar hausa?
Duk lalacewar uwa ba zata so d'anta ya zama marar tarbiya ba. Na sani akwai uwayen
da basa son laifin ya'yansu, amma me yasa aka fi yiwa masu hakuri da kawaici raddi?
Yanzu duk laifinki a kaina ya k'are. Yana wahalar gaske Babanku ya yaba ha'kurin da
nake yi a gabana sai dai a bayan idona. Shikenan ita mace ba za'a yabe ta a
kurzanta ta ba?
Ba za'a yayata alherinta ba, amma kuskuren da ba ita ta yi shi ba ma sai an yi mata
tuya a kai".
Ta fa'da hawaye na sake k'wace mata.
Na taya ta kukan da take yi domin na sani sanadin tafiyar da na yi ne.
Da rawar murya na ce "Ki k'ara hakuri Gwaggo! Idan kika yi sa'a Ubangiji ya yabi
ha'kurinki shikenan kin gama dace wa."
Ta zuba mini ido sosai ta ce "Kema na hore ki, ki yi hakuri, ki yi juriya, ko bana
raye shine tsanin da zaki ri'ke, ki tsallake dukkan k'alubale a wannan duniyar".
Jikina ya sake sanyi. Domin kalmar ko bata raye ta yi matu'kar dukana.
Na ha'diye kukan na tayar da sallah.
Sai dai hawaye bai yanke mini ba, na idar da sallar ina zaune ina lazimin Ya ladifu
da fatan na samu sau'kin halin da nake ciki.
Washagari sassafe Babah ta koma Bulkachuwa.
Ala dole na ha'kura na zuba ido aka cigaba da shirin aure, wanda yake sake
k'arantowa.
Duk da na ha'kura amma wata irin rama nake yi mai tayar da hakankalin masu kallona.
Na sake zama wata yar sumoli da ni.
Ba annuri a fuskata.
Na kasa yiwa jama'a kitso bare kuma lalle.
Idan ba k'ure wa ta yi ba yana wahalar gaske na yi magana. Na zama very silent.
Makarantar boko ma na daina zuwa duk da a shekarar k'arshe muke.
Kwatsam sai ga Yaya J ya dawo daga Bauchi.
Bai samu labarin aurena da Bulkachuwa ba sai a jiya.

A ki'dime ya iso gidan Marina. Ya gurfana gabana Dada yana fa'din "Dada wanne irin
abu ne haka?
Ta ya ya za'a dauki Yabi a bawa Bulkachuwa! Saboda Allah Dada wannan daidai ne?
Me yasa aka hana shi Nasiba baki tsawatar ba?
Me yasa aka tirsasa ni na auri Maijidda?
Akan me ita kuma za'a yi mata hakan? Ciwon abin ba shi ya yana sonta ba.
Idan saboda kada na sameta ne kuka k'ulla wannan al'amarin, na sadaukar da soyayyar
da nake yi mata, na janye, bazan sake furta sonta, ko a bani aurenta ba. Amma ki
yiwa Àllah Dada kada ki kassara mata rayuwarta.
Waye bai san BAK'AK'EN TA'ADODIN da yake yi ba?
Ta ko ina basu dace da juna ba.
Yabi mai son sana'a ce, yayin da Tijjani bai damu da ya gina kansa ba, irin mazan
da suke barwa mace hidimar da shari'a bata dora musu ba ne.
Tijjani manemin mata ne, yayin da Yabi ta kasance mai tsananin kishin gaske.
Tijjani fari ne, Yabi bak'i take so.
Tijjani mai zafi ne. Yabi mai tsiwa ce.
Ta ina zasu ji da'din zama?
Ta ina suka dace?"
Kafin Dada ta ce wani abu Bulkachuwa da yake tsaye a bakin k'ofar Dada ya ce "Bamu
dace da juna ba Jabir. Sai dai ka sani Ubangiji ne yake jujjuya al'amura, yake kuma
k'addara afkuwar komai ko da bamu tsara faruwarsa ba.
Maganganunka sun yi matu'kar ta'ba zuciyata. Tabbas gaskiya ka fa'da, duk da na ji
na muzanta. Da a ce son Yabi bai yi mini kamun kazar kuku ba.
Dana tirje wa aurenta. Sai dai an jarrabe ni akan ta cikin kankanin lokaci."
Ya numfasa ya sake fa'din " Na gode da ka ankarar da ni, duk inda sana'ar da zan
gina kaina take zan nemota zan kuma yi duk wahalar ta.
Laifin da ka jingina mini kuma na neman mata wannan kai da Allah! Domin baka ta'ba
ganina na yi ba.
Allah ne shaidar na yi tuba, Allah ne shaidar tunda na yarda aka zartar da hukuncin
da ya yi a kaina ban sake yi ba.
Amma kun rike abu kuna ta faman jifana da shi."
*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered,
Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan
farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon
yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
Ya fa'da cikin wani irin yanayi na bacin rai mai tsananin gaske.
Dada ta zuba masa ido cikin son ta nazarce shi.
Ta k'asa ha'diye abin da ta fahimta akan sa cikin dak'ik'a.
Ta nisa ta ce "Mai sunan manya, shin ka fa'da komar Yabi ne har haka?"
Takaicin ta ya k'ume shi.
Bata ce da Jabir komai ba, da yake faman sakin maganganun da suke nufin tozarci a
gare shi.
Amma tana neman shiriritar da maganar. Bai ce mata k'ala ba ya juya tamkar ya tafi,
sai kuma ya toge a jikin bishiyar zogalen da take gefen dakunan ka'dan. Cikin bacin
rai na sosai.
Yayin da jikin Jabir ya yi sanyi domin ya fahimci ba k'aramin son Yabi Tijjani ya
afka ba. Sannan ya ji kunyar maganganun da ya ji yana yi a kansa.
Dada ta kalli Jabiru ta ce "gara ma da baka auri Yabi ba Jabir. Na fahimci irinsu
ne matan jaraba. A kansu ba abin da namiji ba zai yi ba. Mafi yawa haka zaka gansu
yan firit amma suna murza mazaje ingarmai. Yadda kake sanyi k'alau din nan ba zaka
sarrafa ta ba. Ko mai sunan manyan da yake a tsaye, tun komai bai gitta a
tsakaninsu ba, ga shi nan yanayinsa ya nuna ta riga da ta shiga ransa ta yi kane
kane".
Cikin jin nauyin maganarta Jabir ya ce "wacce irin magana ce haka Dada da girman
ki?"
Ta nisa ta ce "Gaskiya ne mana! Kawai murnar da nake yi masa d'aya ce. Ta iya
sana'ar samun ku'di, dolenta ta fito da ku'di su ci abinci. Idan ku'din da suke
saka ta yiwa iyayenta raini basa zama mata ai ta nutsu ta girmama manya".
Tana rufe baki Jabir ya ce "Haka su Baban suka fa'da miki shiyasa kika tirsasa aka
yi wannan bahagon hadin?"
Ta yi dan tari kafin ta ce "Gaskiyarsu ne ai! Sannan shi mai sunan manya tunda ba
shi da sana'a asirinsa zai rufu".
Jabir ya ce "Gaskiya kun kassara rayuwarta, amma akwai Allah. Ina fatan alheri ya
biyo baya, sai dai har yau din nan ban hakura ba. Na sani *Hannu daya* baya daukar
jinga. Bazan ha'kura da ita ba har sai na ga ranar da aka shafa fatiharta da
wanina. Daga ranar na zubar da makaman nemanta. Amma matu'kar ban mutu ba idan an
kaddara mini cikar burina zai zama gaskiya. Idan da rabona zata dawo mini, ni kuwa
zan aureta komin tsufanta, domin ita nake so ba wani abu a tare da ita ba".
Dada ta kyabe baki ta ce "Idan k'asa ta rufe mini ido komai ma sai ku yi tunda ban
ga ni ba".
Tijjani da yake jinsu zuciyarsa ta dinga bugawa da k'arfin da ya zarce ka'ida.

Yana son ya je ya fa'da wa Dada duk lalacewarsa bata kai mace ta ciyar da shi ba,
bai yi mutuwar zuciyar da macen aurensa zata dauki nauyin kanta da nasa ba. Sannan
ta fahimtar da y'ay'anta hakan.
Amma sai ya daure ya ha'diye. Ya ja jikinsa ya fa'da dakinsa ya fa'da kan
katifarsa.
Wani irin yanayi na shigar sa na tsananin bacin rai da ya sababa masa k'arfin
zuciya.
Domin gaba'daya ji ya yi hatta dako na daukar buhun gero da na su wake zai iya yi,
dan ya ciyar da Yabi da guminsa ba wai ta ciyar da su ba.
Idonsa ya ciko da hawayen tausayinta domin ya gane k'iyayyar da ake yi mata ne ya
sanya aka bashi aurenta.
Ya yi shiru yana nazari wato saboda ana ganin shi din lalatacce ne. Ana ganin shi
ba zai amfana wa kansa komai ba, bare ita ta amfana da shi. Ana kuma fatan ya
dauwama cikin lalace wa da mutuwar zuciya.
Sai ya tsinci kansa da tambayar shi da Yabi wa aka fi tsana ne a gidan Marina?"
Take ya muskuta ya janyo wani kwali.


*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin
register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*
*Lame fa garin su Yabi ne*

Ya dauko memo da biro, ya yi rubutun magananun Jabir, da wanda su Baban Tsakiya
suka yi da ya ji a harshen Dada.
Da irin manufar ba shi Yabi. Da yadda ake fatan ta tabbata cikin halin ni 'ya su.
Sai kuma ya je shafi na gaba sosai ya rubuta "Zan yi komai na halal dan na sauke
nauyin da yake kaina.!
Allah ka sani ban sake aikata zina ba! Allah ka taimake ni ka cigaba da tsare ni.
Allah ka fahimtar da ni sarrafa mace ta yadda Yabi zata rayu cikin farin-ciki a
hannuna.
Allah ka hore mini kofofin arziki ta yadda zan sauke nauyinta ba tare da tallafinta
ba.
Na sani al'kawarin ka baya tashi, da kanka ka yi al'kawarin taimakon wanda ya
k'udire niyyar aure saboda kai. Ga ni bawanka, Ibnu bawanka cikin kankan da kai, ka
taimake ni, ka kubutar da ni kunyata a idonta da na dangimu. Allah ka hore mini
lafiya, ka sanya mini hakuri akan sha'anin ta, sannan a mallaka mini zuciyarta da
tunaninta." Sannan ya rubuta kwanan wata.
Ya rufe yana jin girman k'alubalen da yake gabansa.
Wani irin son ta da tausayinta yana sake bin dukkan jikinsa yana kutsawa.
Har yake jin anya akwai wanda ya so mace kamar yadda yake jin son Yabi ya sake
shak'e shi a yanzu?
Domin shi son ta yake yi babu wani dalili na sha'awa ko na burge wa.
Na farko yafi son manyan mata masu manyan halittu. Yabi kuma yar mitsil mai
k'ananun halittu, maimakon ya ga ba hakan yake so ta zo ba. Sai yake jin ko bata da
komai na cikar mace yana sonta a hakan.
Na biyu yafi son mace mai sanyin hali, mai kawaici.
Amma daga ranar da aka jefa masa sonta shikenan ya ji da tsiwarta zai yi amfani
wajen kutsawa dan ya sami kusanci a zuciyarta.
Ya sani ba zai yarda da rashin kunyar da ta wuce ka'ida ba.
Amma yana fatan a cikin rashin kunyarta ya dinga isar mata da sakwanni masu girma.
Na uku akan abin da aka yi mata na tirsasa Jabir auren Maijidda, da kuma yadda uwar
Nasiba ta ture komai na zumunci ta fadi maganganu marasa dad'i a gaban
mahaifiyarsa! Shike nan ya k'yamaci auren zumunci.
Amma a yanzu yadda yake jin Yabi zai iya yin komai dan ya same ta.
Ya gamsu tausayi da sonta sun masa rubdugu.
Ya rufe littafin ya mayar da shi ma'adaninsa.
Ya jima a zaune yana ta tunanin sana'ar da zai fara.
Ya saki gauron numfashi! A fili kuma sai ya ce "Allah ka hana Tijjani sanya Yabi
kuka! Allah ka hana ni zaluntar ta. A hore mini ita ya Ubangiji".
Ya zabura ya mik'e yana ganin lokaci ya yi da zai daina buga buga ya samu
tartibiyar sana'ar da zai dogara da ita tunda nauyi mai yawa ne zai hau kansa,
wata'kila ma badi war hakan yana shirin zama Abba.
Murmushi da kunya suka subuce masa ya dinga sosa k'eyarsa tamkar yana gaban manya
ne.
A fili ya furta wa ya ga "Yabi as uwa?"
Sai dariya ta sosai ta kama shi, har bacin ran da Jabir da Dada suka cusa masa ya
yi sauki.
Ya fito ya nufi wajen Alh Tsoho magini dan ya ji ko zai masa hanyar samun aikin
ginin.
Yana tafe sanye da yadi na wando da riga bata kai guiwar sa ba.
Kamar kullum a wanke suke amma fa babu guga.
Sannan ya saka hular sanyi ya rufe gashin kansa.
Domin tunda aka furta za'a bashi auren Yabi. Bai sake yarda an ganshi da gashin
kansa ba, duk da ya ki aske wa.
Ba wanda yake jin kunyar ya ganshi da sumar irin Baban Marina. Domin ya sani baya
so, ya sha tisa shi a gaba ya saka a masa askin akan dole.
A yanzu kuwa wata irin kunyarsa yake ji ta sosai domin bayan kawunsa ne da yake yi
masa adalci, yanzu shirin zama surukinsa yake yi.
Bulkachuwa da kansa ya yi amannar ba dan zuciyar Baban Marina irin ta daddako ba ce
da ba za'a yi masa wannan k'arfin akan diyarsa ba. Ba dan alherinsa mai yawa ba ne,
da ba zai ba shi aure ba, komai za'a yi kuwa.
Amma ya yi shahadar ba shi, babu dogon turanci. Yana tafe yana fa'din "Allah ka
fitar da Tijjani kunyar Baban Marina".
Ya sha kwanar shiga cikin wani kwararo sai kawai ya fara jin k'amshin turaren da
yake ji a jikin Yabi da kuma wanda yake shaka a jikin Jabir.
Ya shiga sai kuwa ya hangosu kowannensu jingine a garu.
Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi.
Kishi mai tsananin gaske ya dabaibaye shi.
Tamkar ya juya sai kuma ya tsinci kansa da tunkararsu.
Ya zuba musu ido. Yabi na kuka sosai yayin da Jabir idonsa ya kad'a ainun.
Sau d'aya za'a kallesu a gane suna cikin tsananin soyayya da kuma halin
cankacakare.
Ya kalli Jabir da yake tsab da shi cikin shadda ruwan toka ta sha guga. Farin
gilass ya mak'ala.
Ga k'amshi mai da'di na tashi a jikinsa domin komin hassada baka isa ka ga wani abu
na rashin tsabta ko gayu a tare da Jabir ba.
Yayin da Yabi take sanye da hijabanta har k'asa sai dai duk ya b'aci da hawaye har
da ba'kin kwalli.
Kishi sosai ya turnike Bulkachuwa.
Har ji ya yi zukar numfashi na neman yi masa turjiya.
Amma a hakan ya motsa k'wanjinsa ta hanyar cewa "Jabir na tabbatar babu jahilci a
tare da kai tunda ka yi zurfi a ilimummuka daban daban. Sai dai abin mamaki sanin
naka bai amfana maka komai ba, tunda zaka iya tsayawa da wacce kwanaki kadan ya
rage a daura mata aure a cikin lungu inda babu sawu.
Ni ba zan yi maka rashin adalci na yi maka kazafi irin yadda ka yi mini ba.
Sai dai na sha fa'da kai din azzalumi ne, ba masoyi ba. Ta ya ya an baka aure ka
karba, dan kwadayin albarkar iyaye ita kuma ka dinga hure mata kunne da ga yiwa
nata tsohon biyayya? Ban da ita din sakara ce har wanne kalami ne a bakinka da zaka
tsara mata da yafi na ubanta da kannensa tasiri?".
Jabir ya sandare ya zuba wa Bulkachuwa ido, yana jin wata irin fargaba from no
where tana shigarsa.
Yayin da ni kuma na dago ido jage jage da hawaye na watsa masa kallon kiyayya da
raini na ce "Ba ruwan ka da ni Tijjani! Na saurare shi din, domin shi nake so, nake
fatan kasance wa da shi".
Ga mamakina sai kawai ya ja kakkuran tsaki tare da ce wa "Ai ke din shasha ce! Kuma
kin ji na saka maganata da ke?
Da shi na ke wanda na gamsu da hankalinsa da iliminsa, kawai adalcinsa ne bai
gamshe ni ba. Amma ke da baki da hankali ina ruwana da ke?
Jiyan nan na gan shi da matarsa a asibiti yana ri'ke da ita. Yana faman tattalinta.
Wai matar da ya aure ta ba dan yana so ba yake yiwa irin wannan son da adalcin,
amma ke kullum yana cikin dama miki lissafi. Da yake ya mayar da ke shargalle marar
tunani."
Ai kuwa yana rufe baki kuka ya k'wace mini sosai.
Jabir ya kasa magana domin ya tabbatar Bulkachuwa ya gansu a asibiti ba k'arya ya
yi masa ba.
Bulkachuwa ya sake yin k'uta tare da nuna Jabir da yatsa ya ce "Neman aure cikin
aure haram ne in ji ma'aiki (S.A.W).
Da ku'din aurena akan ta, ko ba zaka yi mini kawaici irin na zumunci ba, to ka yiwa
ka'idojin shari'a biyayya. Ka fita mini a harkar Asiya! Ubangiji ya baka Maijidda
wacce ita ce mafi alheri a gare ka. Amma bar mini Asiya Toro domin ina da yakinin
akwai babban al'amari a tsakanina da ita. Daga ranar da aka tabbatar mini an ba ni
ita, na fara addu'ar na yi nisan kwana mai yawa dan na tabbatar ni kad'ai na
mallake ta".
Still Jabir ya kasa magana domin gaba'daya almarin ba k'aramin bugunsa

Please Login or Register in order to submit comment