You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na yi dambe da mai daudar zunubi irin ka, kuma ni ba
ballagaza ba ce, kawai zan kare kaina ne daga cutarwar ka".
Ya jima bai ce komai sai ya kalle ni ya ce "shahsa da bata iya komai ba, sai fa'da
da rashin kunya a aji kuwa ita ce dalkiya".
Ba'kin ciki ya mamaye ni, idona ya ciko da hawayen takaici na ce "Na gode wa Allah
da na yarda ina zuwa makarantar, wani ma tsabar akuyanci korarsa aka yi daga
karatun nasa. Me za'a yi da mai halin bunsuru?"
Ya rasa yadda zai yi da ni sai kawai ya shammace ni ya dauke jakata yi wuf ya zaro
takardar sakamakon da take a farko farko.
Ya juya zuwa waje ya bu'de ya ga yadda jan biro suke mamaye sakamakon.
A karshe ya ga ta yadda na zo sannan ya mayar ya shigo ya kalli yadda na tumbatsa
ya ce "Anya Asiya ba dusa kike ci ba kuwa?
Ace har kin doshi hamsin?
Gaskiya ina taya Baba ba'kin cikin asarar ku'din taran da ya wanzu yana baki".
Cikin rawar murya na ce "Bulkachuwa Yadda ka tozarta ni a gaban wanda suke son na
tozarta in sha Allah sai an tozarta budurwarka fiye da yadda ka mini, da ikon
Ubangiji sai ka ha'du da sharrin mace, sai ka muzanta a idon duniya".
Ya make kafa'da alamun ko a jikinsa tare da cewa "Yabi yanga mai kwakwalwar kifi".
Ganin hakan ya sanya Maijidda ta mike tana jin karfi yana shigar ta tunda ta ji
abin da take son ji.
Ta mini gwalo tare da cewa "Na ji dai, dama nasan baki tsinana komai ba".
Ta shige wajen Dada da saurin ta.
Yayin da ragowar suke fa'din "Yi ha'kuri Yabi, ai kin nuna mata ruwa ba sa'an
kwando bane. Ba gashi ta tsere ba".
Na jijjiga kai na ce
"Ai dan ta ga Bulkachuwa ya tsaya mata ne".
Yayin da shi kuma ya ce "Ba dole na tsaya mata ba, tunda ke din karfinki na aljanu
ne, na tabbatar ba ke ka'dai kike fa'da ba, kina samun tallafin aljani mai kilabo
da gwaigwai".
Duk wajen aka fashe da dariya illah ni dana sake fusata na daga murya "Ina ce wa
"Allah ka dora wa matar Bulkachuwa aljanun da zata dinga daga shi sama tana danfara
shi da k'asa".
Ya wuce yana fa'din "Duk bala'in aljani ba zai shigo mini gida ba, domin hafiza zan
aura mai hazakar gaske a ilimin boko da na addini.
Safiya da marairaice ta yi ta tofe mini gidan da azkhar, idan kin ga aljanu sun yi
tasiri, sai a gidan wanda basa mayar da
kai a wajen bautar Allah irin ki".
Na wuce shi zuwa shashin Dada.
Na tarar da Maijidda tana ta kuka yayin da Dada take sakacen hakori da tsinken
zabori hankalinta a kwance.
Na bu'de baki na ce "Dada sannu da gida, mun dawo".
Ta amsa ba alamun damuwa a tare da ita.
Na juya na tafi sai na ji kukan Maijidda ya karu tana cewa "Kin bar ta tafi baki bi
mini kadina ba?"
Na yi tsam dan na jiyo amsar Dada.
Kamar ba zata tanka ba sai kuma na ji tana ce wa "Na k'i na yi mata maganar. Yar
kankanuwa a gabanki, sannan kin bata kwanaki arba'in cif amma kin kasa kwatar kanki
a hannunta sannan dan asaranci ki ce na tare miki fa'da?
Ai kinsan fa'dan ta baya mutuwa akan me zaki tsokano abin da yafi karfinki?"
Maijidda da bata yi zaton haka Dada zata ce ba, domin mun saba yin fa'da da yan
k'ofarsu ta basu gaskiya ko da kuwa ni ce mai gaskiya.
Dada ta ja tsaki ta ce "Sadda nake cikin shekarun kuruciyata haka nake nima duk
girman mace bata bani tsoro, haka nan duk wanda ya mini kan ice sai na yi masa na
kara.
Sai yanzu na fahimci wannan tijarar ta Yabi sawuna ta biyo domin komin sharrin mai
sharri ba zai ce ubanta mafadaci ba ne ko kuma uwarta.
Dukkan iyayenta sanyin kalau ne, dan kuwa inta sune kiyama ba zata tsaya ba."
Kukan Maijidda ya tsananta ta dinga yi tana ce wa "Ai dai kinsan bata isa ta kai ni
k'asa ba, dunbular mini kirji ta yi ta yakushe ni a wajen."
Salati Dada ta dauka tana cewa "Ikon Rabbani, tarihi na maimaita kansa ni Fadimatu.
Wallahi Maijidda sadda aka mini auren fari ina kankanuwa aka kai ni babban gida,
matar wan miji ta saka ni a gaba, duka, kyara zagi.
Har na fara girma a cikin fargabar wannan baiwar Allah na ke.
Ai kuwa da tura ta kai bango na fara rama abin da take yi mini.
Har muka kai jallin da muka fara dokuwa, sai dai kashi take bani da yake ta fini
sosai, ai sai kawai nake fakar ido idan muna damben ina mintsinin nonuwanta ko na
na cije su. Shi kenan na yi maganin gallazawarta, ta shiga kiyayata.
Yau ga Magajiyata na samu a haulata".
Ta fa'da tana tafa hannu tana sake jan salati.
Na wuce ina son yin dariya amma ba'kin cikin Bulkachuwa ya dabaibaye ni.
Na wuce shashinmu ina jaddada wa kaina ko a gaban Baban kasuwa ne Maijidda ta
tsokano ni sai mun sake cire raini, bare Dada.
Bamu jima da dawowa ba sai ga mahaifiyar Maijidda da kanta ta kawo togaciya.
Fadi take "Tura ta kai bango kullum Yabi sai ta yi mini sanadin bacin rai jiyan nan
ma sai da ta dakar mini Kaltume akan sun samu sabani da Ismail, akan me zata tisa
mini yara a gaba irin haka?"
Ha'kuri kawai Gwaggo take ta bata, Inna da ta rage tsananta gaba da ni a dalilin
ina yiwa yaranta hidima tamkar yan dakinmu, sannan ba mai tab'asu a waje matu'kar
ina wajen sai hakan yayi tasiri, ta rage daukar zugar Mama.
Dan haka sai ta ce "Ban da ke ma Abu da shiga shirgin yara ina ce Maijidda ta girmi
Yabi ne?
Sannan idan kinsa ha'kuri anjima ka'dan zaki iya ganinsu tare".
Nan da na ta harzuka ta ce "To Yabi ni kaina ai sai ta dake ni tunda fa'dan yan-
iska take yi, ban da dai ta riga ta rik'a ta yaya zata dinga dumbular kirjin
y'anmata, tabbas dayan biyu ne, ko dai niyyar kisa take yi ko kuma ta shiga sahun
masu *Bak'ar Ta'adar* neman mata."

*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko kuma kina sha'awar yin
register da su. Ki tuntubi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn mai kore dukkan kwadayi*.
*07036662633*.

Gwaggo ta ce "Dutse a tsakaninmu da duk masu wannan al'amarin, muna neman tsarin
Allah da su, muna kuma nema musu shiriyarsa."
Ta ce "ASMA'U Wallahi kin siffatu da agwagwa, ace wai baki isa ki sarrafa y'ar
cikinki ba, ta gallabi kowa a gidan amma ba k'ya yi mata fa'da, saboda tana samun
ku'di shiyasa ta gagareku?
Sai ayi ta fankamar ku'din kitso da na lalle ne, alhalin munsan samarin da suke
mata layi ne suke bata. Wallahi idan ba sa'a kika yi ba sai Yabi ta hana ki shan
ruwa kamar yadda ta fitine mu".
Na fito na ce "Umma ya isa haka nan, ba zai yiwu fa kizo k'ofarmu ki zagi Gwaggo
ba".
Ta mini dakuwa ta ce gidanku tabbataciyar yarinya marar albarka".
Tana rufe baki na ce "yarinya tana bayan uwarta Wallahi, albarka kuwa da ikon
Ubangiji sai na yi ta".
Gwaggo ta yo kaina na ki guduwa tasan kuma matu'kar ta kawo mini duka ban gudu ba,
na riga na shiga yanayin da nake bu'katar a kashe ni kawai na huta.
Inna ta yi maza ta karbe itacen hannun Gwaggo tana fa'din "Wannan ai sai ki sabauta
ta".
Yayin da Umma Abu ta juya tana fa'din "Zaman babban gida ko masifa, ba dama a ganka
da haske sai an tisa ka a gaba da ba'kin ciki da hassada tamkar dai kai ofne ka
tare wa mutum nasa arzikin".
Tana fita Gwaggo ta kalli inda nake a tsaye kik'am tana fa'din "Kin ji da'di ai da
wannan wula'kancin da kika janyo mana".
Ban ce komai ba, sannan kuma ban ji a raina cewar zan koyi ha'kurin dole idan an
ta'ba ni ba.
Wannan rikicin yana cikin al'amura masu tsananin gaske da ya faru.
Domin da daddare babu kunya bare kawaici Baban kasuwa ya gurfanar da mahaifina a
gaban Dada yana ta sababin ya gaji da yadda na takura wa ya'yansa amma ubana ya
kasa tsawatarwa.
Da yake Dada bata iya tsallake umarninsa sai kuwa tabi bayansa.
Ta dinga fa'din ai tsoron zuciyata yake yi.
Cikin rishin kuka Baban kasuwa ya ce "Ki gafarce ni Dada! Wani satin zan koma
gidana dana kammala gina wa tun bara, amma na kasa tashi saboda ke, to yanzu kam
zan tashi na gaji da wannan masifar Wallahi".
Dada ta ce "Wallahi ko ubanta ba zai tashe ka ba tunda matsayinku guda a cikin
gidan bare kuma ita.
Share hawayenka ita ce zata bar mini gidan".
Na sake kasa kunne domin tunda aka aiko cewar Babanmu ya zo in ji Dada nasan karata
za'a kai sai na bi bayansa ba tare da yasan ina binsa ba.
Na makale a soron Dada ina addu'ar kada Allah ya kawo Bulkachuwa tunda dakinsa a
cikin soron yake.
Ta ce "ka fa'dawa Yabi ta tsayar da miji da dukkan yaran ma.
Na umarce ku, ku aurar da su nan da watanni biyu".
Baban kasuwa ya ce "Shi kenan"
Ya fice ya barta da Babanmu."
Ganin zai fito ya gan ni sai na yi maza na fice daga soron na tsaya a bakin k'ofar
shashinmu.
Ya zo wuce wa ya dallaro mini ido da sabuwar tocilayit dinsa da alamu suka nuna yau
ya zuba mata sabbin batira saboda tsananin hasken ta.
Na dauke kai tare da saka hannunwana na rufe fuskata dan rage wa kaina kaifin
hasken da ya dauke mini ido.
Takaicin rashin gaishe shi ya sanya ya ce "Asiya ce?"
Na dauke kai a shak'e na ce "Yabi ce?"
Ya kuwa bu'de murya ya ce "Ja'irar yarinya mai mugun y'anci dama nasan ke ce zaki
gan ni ki mini irin wannan iyashegen. Na ce ba, zaki yiwa ubanki Sani hakan?"
Na dauke kai ina kunkunin fa'din "Ai kai ma ba zaka yiwa su Maijidda irin hakan
ba".
"Me kika ce? Bude Baki sosai ki fa'di abin da kike ce wa shedaniya."
Ganin Baban Tsakiya dawo ya nufo mu dan ya shiga wajensa ya sanya Baban kasuwa ya
d'auki k'arfaffan salati.
Ganinmu hakan ya sanya Baban Tsakiya ya dakata ya ce "ya ya ne Iliya?"
Ai kuwa ya hau rattab'a masa bayanin da aka yi masa na karya akan fad'anmu da
Maijidda.
Wani abin mamaki a gabana ya lauya zance yana fa'din a gabansa ma, na zage shi
yanzu nan. Da kunnensa ya ji ina zaginsa.
Baban Tsakiya yana bu'de baki sai ce wa ya yi "Tuni fa na d'iga alamar tambaya akan
yarinyar nan domin wacce ta saba cudanya da maza ne take irin wannan dibar
albarka."
Gabana ya yanke ya fa'di wacce irin magana ce mai muni ta fito a bakin kanin
mahaifina kuma uban wanda nake burin aure?"
Na yunkura da nufin mayar masa da zazzafar magana sai kuma na tuna girman aika
aikar da zan janyo wa kaina da uwata.
Na sani mahaifina ba zai d'auki al'amarin da sauki ba, domin kuwa zai ce tunda na
iya zagin dan-uwansa shima zan zage shi, hukuncin da zai biyo baya kuwa na tabbatar
zai zama mai tsananin gaske.
Na ha'diye maganar na juya na tafi na barsu dan kada na yi subutul kalam.
Sai na sake juyo muryar Baban kasuwa yana sake cewa "Na kagu a samu mai tsautsayin
daukar kara da kiyashi ya zo ya kwashe ta, ko zamu sarara da musibarta domin ta
riga ta zame mana tamkar annoba" .
Baban Tsakiya ya ce "Lallai kuwa kara da kiyashi daukar marar sani, na tausaya wa
ahalin gidan Sarkin gida q tunda ina ganin d'ansu a wajenta"
"To namu d'an fa? In ji Baban kasuwa.
Baban Tsakiya ya yi wata irin dariya ya ce "Ta yaro ai kyau take yi bata k'arko,
yaushe kana ganin kashi a jikin mutum, za kuma ka yi kuskuren bari naka ya dauki
abin nan?"
Kai-tsaye dakin Gwaggo na fa'da na zauna akan tabarmar da take shinfide, yayin da
take zaune gefe daya, yanayinta ya nuna a takure take ma'ana tana cikin zullumin
kiran da aka yiwa Babanmu me zai haifar mata.
Na sassauta murya na ce "Gwaggo ki yi ha'kuri dan Allah"
Ta muskuta ta ce "Idan ban yi ha'kuri ba ya ya zan yi ne Yabi?
Ai a gabanki aka tabbatar mini ni agwagwa ce akan ki.
Kinsan me hakan yake nufi kuwa?"
Manufa kina gaba ina bin ki a baya, saboda gudun zuciyarki da nake yi.
Ace yanzu kullum a cikin d'aukar wa kanki baki kike, sai ka ce ke kad'ai ce a
gidan?
Ga yar'uwarki nan ban ta'ba jin an kawo togaciyar Nazira ba.
Amma ke idan ba'a kawo k'ararki ba, sai idan baki fita ba, ko kuma kin ha'du da
masu alkunya, anya Yabi kina ganin kin hau turba mai b'ille wa?
Jikina ya yi sanyi sosai na ce "Duk fa'dan da nake yi kowanne takala ta ake yi, ba
wanda nake yin sa na rashin gaskiya, amma ki yi ha'kuri zan yi kokarin koyo ha'kuri
idan an nemi ganin rikicina".
Ta kafe ni da ido tana cewa "koya ma zaki yi Yabi?
To fa'da mini zuwa yaushe zaki fara bita?"
Na yi kasa da kaina na ce "Addu'a zaki tsananta yi mini a sanya ni cikin bayi masu
ha'kuri da kawaicin cutarwar mutane. Amma a zahiri saboda ke zan yarda na zama mai
kawaicin tunda abin da kike so ke nan.
Domin ni dai har yau ban ga ranar da ha'kurinki ya miki ba, ban ga kuma ranar da
kawaicin Babanmu yayi masa ba, tunda yau an kai dan-uwansa ne mai kirana da
lalatacciya mai bin maza".
Na fa'da hawaye na kwace mini ba tare da na shirya zubarsu ba.

*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*


*VIP 1k, regular 500.*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*Shaidar biya ta*
*08032773332.*
*BAK'AR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS M.I.NASHE)*.

*Marubuciyar*
*Halin Yau*
*Sabo da kaza*.


*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}```
✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*


11&12.

A ki'dime Gwaggo ta ce "Baban Kasuwa ne ya fada miki hakan Yabi?".
Na girgiza kai na ce " A a Baban Tsakiya ne".
"Tirk'ashi"
Gwaggo ta fa'da a hautsine.
Na sunkuyar da kaina k'asa ina jin wani irin al'amarin tashin hankali na ratsa ni.
Da kaina nake jin shekaruna sun yi k'aranci na dinga fuskantar irin wannan rikita
rikitar.
Na rasa dalilin da ya sanya nake da ba'kin jini a cikin gidanmu.
Hatta a k'ofarmu mak'iyan da nake da su sun wuce misali.
Domin kafatalin y'an d'akin Mama Nazira ce take sona fisabidillahi, sai ko Yaya
Salamatu ita ma kuma ba yadda za'a yi alheri ya samu ta doshe ni da shi, sai dai
Nazira, tana dai bani kuncen kayanta da suka sha ruwa ainun.
Ni kuma murna nake yi domin tafi sauran yi mini adalci da sassauci.
Mama kuwa da tana da ikon da zata kore ni a gidan da tuni ta yi hakan tsabar yadda
ta washi ta bude ido ta gan ni, mussaman yanzu da sana'ata take sake kafuwa.
Y'an dakinmu ne bana fuskantar adawarsu sai dai muna yawan haura wa sama da su a
dalilinsu na ce wa ina daga wa Gwaggo hankali tunda kusan kullum sai na janyo mata
bacin rai.
Inna kuwa tare wa yaranta fa'da da nake yi ne ya sanya na kubuta daga nata kaidin.
A hankali ta ce "Ai kuwa ribar ha'kurina gashi nan a bayyane tunda ban yarda na
tafi na barku kun yi rayuwar ni y'asu a dalilin rashin uwa ba.
Kina gani ina nan din ma ya ya kuka kare ne, bare kuma na zubar da ku na tafi?
Ashe yanzu yadda yayunki suke dawainyar rike gidan nan bai isa abin alfaharina ba?
A bayyane yake kafatalin ya'yan gidan nan ba wanda Babanku yake mora irin yaran
dakin nan. Ai kuwa ko iya hakan na ga ni ba abin da zan ce da Allah sai godiya.
Domin wasu da yawa yaran nasu basu amfani kansu ba bare waninsu ya amfanesu.
Ubangiji ba abin da bai yi mini ba, na gode masa, kema na hore ki ri'ke ha'kuri ba
abin da hakuri ba zai baki ba.
Ta ri'ke kaina ta ce "Àllah ya miki albarka, ya sassauta miki al'amuranki.
Ina fatan Ubangijin da yake sarrafa zuciya, ya sarrafa taki ta zama mai sassauci da
afuwa".
Kuka ya k'wace mini sosai ina cewa "Ameen Gwaggo".
Ba komai yake sanya ni d'imuwa ba irin maganar Baban Tsakiya.
Maganarsa ishara ce akan aurena da Yaya J ba zai yiwu ba.
Zuciyata ta yi nauyi ainun. Na shiga rud'ani mai yawa, na sani idan har zan yi aiki
da lura kamata ya yi na nisanci d'ansa tunda har yake neman maraba da ni a cikin
gidanmu, ina kuma ace na zama cikin ahalinsa?
Mutumin da bakinsa yake ambaton jaje da alhini ga ahalin wanda d'ansu zai kwashe
ni.
Bansan yadda aka yi ba na tsinci kaina da fashe wa da matsanancin kuka.
Saboda fishin Baban kasuwa ya sanya Baban Tsakiya tsayawa ya mini irin wannan
tozarcin da zai yi wahalar gaske na sake ganin girmansa.
Na samu kaina da tambayar anya kuwa Babanmu ba dan uba ba ne a tsakaninsu?
Sai nake ayyana ai ko y'ay'an Baffanni suke (cousins) bai kamata su dinga yi masa
irin wannan kaskancin ba, dan kawai sun fishi wadatar abin duniya. Balle kuma
girman nasaba irin ta uba guda, sai dai kuma babu haufi cikinsu daya ma'ana Dada ce
ta yi nakudarsa tun gabbannin a yi tasu.
Babban farin cikina d'aya, bai rasa wadatar zuciya ba, tunda duk tsananin wahala ba
zai bu'de baki ya ce su taimake shi ba.
Idan sun yi niyya akan kansu sun yi masa kyauta to zai kar'ba, amma idan zamu kwana
mu yini bamu ci ba, ba dai ya ce wane ga halin da nake ciki ba, sai dai idan ya'yan
cikinsa ne.
Har ya k'wammace ya fa'da wa aminisa Alhaji Tanimu tsananin da yake ciki, ya
tsananta.
Matu'kar kuma zai fa'da masa to kuwa zai sauke masa buhun masara, dawa, dana gero.
Sau tari kallon wadatar da ake yiwa su Baban Kasuwa yake hana masu k'arfi tallafa
wa Babanmu.
Sannan mutanan yau suna da dabi'ar k'in taimaka wa matu'kar ba ro'konsu ka yi ba,
yayin da mafi yawa aka fi taimako da azumi, shima fake wa ake yi da sunan neman
lada alhali a ku'din zakkar da Allah ya wajaba a fitar ne suke siyan kayan abinci
suna rarraba wa.
Oh mutanan yau mun rungumi *Bakaken Ta'adodi* daban daban.
Allah ya shirye mu kawai.
Muryar Inna na ji cikin sigar umarni ta ce "Ki cire Jabiru a ranki, nasan zai yi
matu'kar wahalar gaske wannan al'amarin bai zama sanadin yin shamaki a tsakaninki
da shi ba.
Ina son ki ninka jarumtar ki, tun kafin su miki 'kwalele da shi."
Kafin na bu'de baki sai ganin Baban Marina muka yi ya shigo a fusace yana fa'din
"Ina Asiya?"
Da rawar murya na ce "Ga ni Babanmu".
Ya ce "zo ki fice ki bar mini gida tunda har zaki iya tsaya wa gar da gar ki zagi
Badamasi da Iliya akan idonsu.
Ai bansan zaki iya irin wannan dib'ar albarkar ba. Na dauka abin naki akwai lissafi
a ciki amma tunda kina ganin idan kin yi karo tsakanin kwai da dutse zai miki
daidai sai ki je ki yi a wani gidan, amma ba a nan ba.
Ban haifi d'an da zai zagi dan-uwana akan idonsa na bar shi ba.
Na sha fa'da miki babu ruwan ki da shiga tsakanina da y'anuwana.
Amma sam kin k'i ji"
Cikin kuka na ce "Ka yi ha'kuri Babanmu!
Ba yadda aka fa'da maka al'amarin ya kasance ba. Ban zage su ba, har abada kuma ba
zan zage su ba, kada ka kore ni a gidanka, zai iya zama sanadin tabarbare war
al'amura masu yawa, ka mini dukkan hukuncin da zaka gamsu. Ka taimaki kanka, ka
kuma tserar da ni fa'da wa halaka akan wad'anda basa nufin ka da alheri".
Ya jijjiga kai ya ce "Yabi ki yawaita hamdala da baki zo a cikin mutanan farko ba,
lah shakka da irinku ne masu kafiya akan ra'ayinku ko da ya ci karo da gaskiya.
Na ji ba zan kore ki ba, amma dole ki yi nisa da gidan nan tun ban fusata na miki
baki ba, tunda ba'kin cikin da kika cusa mini a sanadin musayar yawun da kika yi da
iyayenki ba mai sau'ki ba ne, akan kannena mahaifiyata take mini mugun baki. Yabi
kibi a sannu fa."
Na sake tsorata na ce "Àllah ya huci zuciyarka Baba, Allah ya shiga cikin
al'muranka, ya iya maka da iyawarsa".
Nan da nan ya sauka ya hau fa'din "ameen".
Gobe ki shirya ki tafi gidan Salisu har sai na nemi ki, saura can din ma ki nemi
gigita masa zaman lafiya a gidansa, dan nasan zaki gano masa laifukan da iyalinsa
take yi wanda shi yake yin uzziri a cikinsu".
Na yi kasa da kaina na kasa cewa komai.
Washagari kuwa Gwaggo da kanta ta shirya mini kayana a ledar biba tana ta jaddada
mini idan na kuskura na yi rikici da matarsa to ba tantama da ita na yi.
A sanyaye na ce "Komai zan ga ni zan runtse idona babu ruwana, ko da kuwa zata
tsokane ni."
Wani irin salama ya shiga Gwaggo ta dinga fa'din "Yauwa Yabina Allah ya sassauta
miki".
Anas ne ya fara yi mini gaba da kayana.
Yayin da zamu tafi da Nazira da Iki idan anjima.
Nazira sai kuka take akan tafiyar da zan yi na barta.
Na yi shirin zuwa gaida Dada wanda rashin zuwa wannan gaisuwar ba k'aramin abu take
mayar da shi ba.
Babu kuzari na ce "Nazira mu je mu gaida Dada".
Ta girgiza kai tare da cewa "je ki kawai, bana jin dadi anjima na leka".
Na ce "Tom na tafi, ina jin da'di tare da k'arfafa wa kaina guiwar ko na rasa
soyayyar kowa a fuskar zumunci ina da yakinin ba zan rasa soyayyar Nazira ba.
Tana sona fiye da zatona, haka nima nake sonta tamkar yadda nake son shakikiyata
Yaya Ummi.
Tun daga bayan katangar Dada nake jin tashin muryoyinta da na Ya'yanta
Na karasa har cikin soron sosai na dinga jin kumfar bakin da Baba Maryo uwar Nasiba
take yi akan ba zata ta'ba yarda a dauki Nasiba a bawa Tijjani ba.
Kuka take yi wiwi. Tana cewa "sai dai a ga laifina a banza, amma wannan ha'din ba
mai yiwu wa ba ne."
Yayin da Babah ta Bulkachuwa take fa'din "Ai ban ga laifinki ba, gaskiyar magana
kika fa'da.
Kuma dama mutum shi yake mutunta kansa, da ya nutsu ya zama mutumin kirki ina ce a
ko ina zai nemi aure a ba shi?.
Yanzu kuwa da ya zama abin da ya zama a cikin danginsa ma gudunsa za'a yi bare a
waje".
Dada ta ce "Ya isa haka, ba cece-kuce zaku yi mini ba.
Na rufe wannan maganar, na yi zaton auren nasa da ita zai kawo masa dai-daito tunda
tana sonsa, idan aka yi sa'a sai ya shiryu, ruwan wankan aure ka'dai maganin wanda
ko wacce suka fand'are ne. Amma tunda abin zai zama tashin hankali a bar maganar
haka nan
Nasiba ba matarsa ba ce."
Kafin na yi wani motsi sai jin muryar Baban Tsakiya ya yi yana fa'din "Kazalika
wannan yar iskar yarinyar ba matar Jabir ba ce, ko bayan raina idan aka bari ya
aure ta Wallahi Allah ya isa, na fa'da a gabanku, kuma yanzu ma idan na tashi zan
je na sami Yaya Sani na tabbatar masa babu maganar aure, mun gama magana da Iliya,
Maijidda zai aura.
Domin ba zan yadda ya dauko mini majuniniyar yarinyar nan ta zo ta tarwatsa mini
zuri'a ba".
Daidai lokacin na yi sallama na gaida Dada sannan na gaishe su a jamma'u.
Babar Bulkachuwa ce ta amsa cikin karfin hali tana danne bacin ran da ya ke kutso
mata.
Nima na yi jarumtar cewa "Ashe kin zo Babah?"
Ta ce " Na zo dazun nan kin san sammakon zuwa nake yi saboda motar Jos muke
shigowa.
Na yi yake na ce "Sannu da zuwa".
Na mike da nufin tafiya sai kuwa Baban Tsakiya ya ce "Dawo ki zauna.
Na zauna ina kallonsa k'ir domin ya riga ya wanke mini a zuciyata.
Ya kausasa murya ya ce "ki hanzarta turo wanda kuka shirya domin kuwa watan jibi da
saba'a zaku bar gidan nan".
Cikin son nuna masa iyaka na ce "To ai Jabir naka muka daidaita da shi, wannan
satin zai iso garin, wajenka zan turo shi, ko wajen Baban Kasuwa?"
Ya zabura ya mini dakuwa ya ce "Marar kunya, marar mutunci ki zagi dan-uwana, ki
mini tsaki a gabana ki yi zaton kuma zaki zama surukuta, ko dai bayan sharholiyar
da kike yi har shayeshaye kike had'a wa da shi?
To saurara ki ji! Jabir ba zai auri wanda zata zagi ubansa ba."
Babu fargaba na ce "Na karbi wannan hukuncin da hannu biyu Baba, ban kuma saka ka
cikin masu son rai ba, domin na yi laifin da na cancancin hakan.
Alfarma d'aya nake ro'ko a wajenku tunda ni ce bani da tarbiya,

Please Login or Register in order to submit comment