You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered,
Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan
farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon
yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.


*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin
register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633


Ya juya ga Babah ya ce "To ga shi nan ta fada miki ta hak'ura".
Ta fita tana fad'in "Y'aya'nta dai sun raunana ta. Ni kam ban so hakan ba."
Gabadaya ya yi sanyi da kalamanta. Yana ganin zasu sa na sake botsare wa. Da sanyin
murya ya ce "Mu tafi yanzu ko sai anjima little?"
Na dauke kai ban amsa ba. Ya diririce. Ya ce "Mun gama magana fa Asiya".
"Sai na shirya kayana". Na fada ba tare da na juyo ba. Ya ce "To bari idan an yi
azahar sai mu tafi ko?"
Ya fada da sigar da tambaya. Ni kuma na yi bakam.
Ya yi shiru yana kallona. Ya saki gauron numfashi ya ce "Ina kayan na ki suke na
hada miki?"
Ban juyo ba na ce "Suna cikin wadirof din".
Ya bude ya fito da jakar kayan nawa. Ya gyara su. Ya ninke wanda Hamim ya dauko a
igiya ya saka, sannan ya zuge.
Ya zauna yana ta yin mini maganganu da nufin mu yi hira. Ni kuwa sai basarwa na ke
yi. Amma bai daina ba.
Ya dawo daga masallaci ya tarar yara sun tashi muna falo duka muna cin abinci.
Ya zauna shi ma ya zuba nasa.
Babah ta sake yi masa fada sosai. Sannan ta hadamu gabadaya ta ja kunnenmu akan mu
kara hak'uri da junanmu. Sannan ta gode mini da har yau ban canja mata matsayin da
na bata ba.
Ta rufe da ce wa "Dama idan kin ga kin gaji to wajena ne mafarki matukar ina raye".
Na amsa mata da ce wa "In sha Allah Babah".
Ya kasa hak'uri ya ce "Kin bata lasisin ta yiwa zaman aure tustu kawai Babah".
Ta girgiza kai ta ce "Matukar za'a tozarta ba. Amma idan akan son zuciya zata yi,
ai ba yarda zan yi ba. Kai ba abin kunya ba ne ace anji kanki?"
Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa. Ya ce *Tsautsayi ne. Zan kuma kiyaye.
Muka gama sannan muka yi haramar tafiya.
Har kofar gida ta rako mu tana sake ba ni hakuri.
A hanya kuwa shi da su Hanif suke ta hirarsu, yana ta amsa musu gwarmcin maganarsu.
Muka isa gidan. Kaca-kaca yake tabbacin bai samu nutsuwar da yake gyara shi ba.
Ya tafi masallaci sallar laasar. Ina idarwa na hau aikin gyara gidan. Ya dawo ya
shiga taya ni. Cikin lokaci k'ank'ani muka kammala.
Na yi wanka, na shiga kicin na fara hidimar had'a abincin dare.
Ya fito sanye da jallabiya sai kamshi yake yi tabbacin shi ma wankan ya yi . Sannan
ya yiwa yaran.
Ya shigo kicin din ya ja turmi ya zauna.
Ya zuba mini ido. Ya ce "Little ba ki huce ba ne?
Ban kalle shi ba. Na ce "Me ka ga ni?"
Murya babu amo ya ce "Ba ki dawo da walwalar ki ".
Na yi k'asa da kaina tare da ce wa "Na huce mana. Kawai zuciyata ce take ta yin
wasiwasi mai yawa".
Ya mik'e da azama ya rungume ni ta bayana.

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA
BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWIA SAIWOWIN SANYI*
AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU*
*AKWIA SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.

Ya rankwafo sosai in ya dora kansa a wuyana ya sassauta murya ya ce "Bai kamata ki
yi wasiwasi a kaina ba Little. Kuskure ne wanda ajizanci yake sababa shi. Ki manta
wannan al'amarin. Ina cikin matsanancin damuwa da fishin ki. Pls my little angel
double sorry ".
Na saki ajiyar zuciya tare da ce wa "Allah ya kiyaye na gaba"
Ya amsa da "Ameen dear. Allah ya yi miki albarka."
Ya dinga kissing d'in kunnena da wuyana da duk inda ya yi masa.
Tamkar ya jani daki. Amma kusantawor magariba ya sanya ya hakura a dole.
Da daddare yara na yin barci, ya fito da maitarsa a fili. Bai sarara mini ba sai da
ya samu nutsuwar da yake so. Kalaman soyayya da na rarrashi ya dinga amayarwa. Wasu
ma ni ban tab'a jinsi ba sai a ranar.
Ya jadda mini ce wa "Dukkan nasarar da ya samu tana d'amfare da irin gudunmawar da
na ba shi a zamanmu. Ya sani bai manta ba, ba kuma zai mance ba.
Ni kuma na yi lamo a jikinsa na shige ya rufe ni ruf. Ina jin kalamansa suna
warware dukkan damuwata.
Ina sake gasgata yana sona, so na hakika. Domin ya shayar da ni kalolin kauna masu
tsayawa a rai da gangar jiki gabadaya.
Ya kaurara murya ya ce "Ki mini alkawarin baza ki sake barin gidan nan babu izinina
ba. Ki mini alkawarin komin runtsi ba zaki juya mini baya, Asiya ki mini alkawarin
zaki gasgata ni ko da kowa bai yarda da ni ba. Idan har kin tsaya mini zan yi ta
samun cigaba a rayuwata. Amma idan kika juya mini baya ina tabbatar miki komai zai
lalace mini ya cakalkale watak'ila ma na shiga rayuwar da tafi wanda na yi a baya
muni!"
Ya karasa cikin matsanancin damuwa da karaya.
Tausayin sa ya baibaye ni. Na nisa na ce "Idan har ka mini alkawarin zaka kame daga
kule kulen mata, zaka kiyaye dukkan iyakokin shari'a to mene ne ba zan yi maka ba
Baban 2?"
Ya sake tsanta rungumar da ya yi mini.
Yana fad'in "Na gode sosai Asiyata".
Sai kawai na ji hawayensa na sauka a kan goshina.
Na shiga rudani mai yawa domin a tsawon lokacin da na shafe tare da shi ban tab'a
ganin kukansa ba hana rantsuwa lokacin rikicin Rafi'a. Na ga k'walla a idonsa amma
hawaye bai zuba ba . Murya na rawa na ce "mene ne?"
Shi ma da rawar murya ya ce "Haka kawai nake ganin kamar duniyata ta zo karshe.
Karbar filina da kamfani ya yi, yana neman zame mini fitina. To idan ke ma zaki
dinga yi mini irin wannan fishin akan sabanin ra'ayi, ki dinga zargina akan abin da
baki ga ni ba. Na tabbatar wata rana za'a wayi gari ne bakin cikin duniya ya mayar
da ni gawa".
Murya babu amo na ce "Da ikon Ubangiji hakan ba zata faru ba. Ba zan sake yi maka
irin haka ba. Ka yi hakuri ".
Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa, domin shi din mai son na ba shi hak'uri ne
ainun.
Ya sake ce wa "na sake rokon ki?"
Zuciyata na bugawa ainun na ce "Ina jin ka."
Ya ce "Dan Allah ki yi dukkan iyawar ki, kada ki bari yaran nan su tagayyara idan
har mutuwa ta yi gaggawa ta sure ni".
Ai bansan yadda aka yi ba, kuka ya goce mini mai tayar da hankali domin k'warai ya
gigita ni.
Maimakon ya kwantar mini da hankali sai ya sake ce wa "Na sani idan na mutu dole
zaki yi aure Asiya. Domin a yanzu ne ma kika yi shekaru ashirin. Amma dan Allah,
dan darajar ma'aiki ban da Jabir, ban da shi little!".
Ya fada da wani irin yanayi na tashin hankali sosai.
Kukan da na ke yi ya tsaya cak a dalilin tashin hankalin da ya jefa ni ya wuce
kukan hawaye ko na baki. Sai kukan zuci da na gangar jiki. Zufa ta dinga yanko mini
tamkar na yi tsere.
Na kasa ko da motsi. Tsawon lokaci muna ta fama da sake saken zuciya da fargaba.
Murya babu amo na ce "wannan ne tukuicin dawowar da na yi ko Baban 2? Haka kawai ka
tayar mini da hankali. Kana nufin mutuwa zaka yi ka bar ni da k'ananun y'aya'n ka
Tijjani?"
Ya ce "Jikina da zuciyata ke raya mini hakan, amma ai bani da tabbacin hakan domin
gaibu ne. Fatana dai ki cigaba da zama jajirtacciya ko bayan babu ni. Akwai mata da
yawa da suka sadaukar da kuruciyarsu da jin dadinsu dan inganta goben y'aya'nsu. Ki
kula da su, ki saka idon a kan tarbiyarsu, idan Ubangiji ya baki tsawon rai sai
suma su raine ki, su ji kan ki".
Na sake kece wa da kuka tare da ce wa "Kada ka mini haka Baban 2. Dan Allah ina son
na rayu da kai. Ina son twins su girma a tsakanin uwa da uba, bana son na rasa ka.
Kai nake fatan ya zame mini miji har a aljanna. Idan mutuwar zata dauke ni, to
kawai ta hada ta dauke mu tare."
Da sauri ya ce "A a In sha Allah ke zaki rayu, ki zame wa y'aya'nmu bangon jingina.
Me yasa ba ki gano girman kalubalen da zasu fuskanta a dalilin rashin uwa da uba
ba?."
Cikin kuka sosai na ce "Allah ka jinkirta mana rayuwarmu gabadaya".
Ganin hankalina ya tashi ainun, sai ya kawar da maganar ya shiga rarrashina da
tarairaya ta. Amma gabadaya hankalina bai kwanta ba. Na riga da na ankara matuka da
gaske.
Washagari haka na tashi sukuku babu kuzari bare walwala. Ya yi shirin tafiya
kasuwar Ilela. Zuciyata ta dinga ayyana mini na hana shi fita domin sai nake ganin
tamkar ba zai dawo ba.
Ai kuwa na fasa masa kukan ba zai fita ba. Duk yadda dinga rarrashina amma ban
yarda na amince zai fita ba. Kan dole ya zauna ya fasa fitar.
Ya sassauta murya ya ce "Idan Ubangiji ya so ikon sa sai na mutu a kan katifata
lafiya lau ba tare da ciwon komai ba."
Ina hawaye na ce "Masifa da jafa'in kake jawo mini Tijjani Allah ya yafe maka
kawai. Allah yasa kai ne zaka ga gawa ta. In kuwa ba haka ba tabbas sai ka yi mini
sababin hawan jinin da zai nannad'e ni na kasa moruwa".
Ya numfasa bai ce komai ba, fitar da bai yi ba ke nan. Yaranmu suna ta kai komon
farincikin ganina a tare da su. Mu kuma muna cikin wani irin yanayi mai wahalar wa.
Kwanaki biyu na rik'e Tijjani a gida. Masallaci kawai nake barinsa ya je. Mukullin
motar na boye na hana shi. Na kafe sai ya canja sana'a. Da wa'azi da nasiha da
lallashi ya shawo kaina ta hanyar cusa mini tauhidi tare da gasgata hukuncin
Ubangiji baya sauyawa. Kawai na dinga fahimtar maganganunsa tare da zama jaruma,
mai fuskantar dukkan kalubalen rayuwa da k'arfin zuciya, sai kuma na dage da
addu'ar duk runtsi Ubangiji ya tsare mini imani ya kuma shirya mini zuria.
Na yarda da nasiharsa. Na ba shi mukullin motar sa.
Ranar da ya fara fita, na k'ira wayarsa tafi sau goma, ina tambayar sa inda yake.
Kwanaki suka yi ta shud'e wa ba abin da ya samu Tijjani. Sai na fara warware wa.
Zullimin da nake ciki ya yi sauki. Yayin da shi kuma yake ta samun nasibi. Domin a
yanzu ya bar kasuwa. Amma yana sarar kayan miya ya kai kasuwannin k'auyuka. Idan
zai juyo sai ya saro abin da yake sauki a garin ya zo ya siyar a cikin gari. Kafin
azahar ya dawo gida. Sai ya sake fito da dabarar kai da karbo sako(Delivery). Sosai
yake samun alheri da harkar.
Ya fara tafiya Jos ya kai kayan miya da sakonnin jama'a, idan zai dawo ya sake
karbo sakonni ya kuma saro dankalin turawa da su atile. Nan da nan sai al'amarin ya
karbe shi. Muka canja mu da y'aya'nmu a dalilin wadatar da yake samu. Na fara murje
wa, ina haske, suturu suka yawaita mini. Mussaman material din Umm Nihla mazauniyar
Malaysia. Bana gajiya da siyan yadinka ta. Saboda rashin nauyinsu da kuma yadda
suke shan ruwa babu kode wa. Shi kansa Tijjani yana matukar son na yi masa kwalliya
da su....
Yawan fataucin da yake yi tsakanin Bauchi zuwa Jos ya sanya akai akai yake zuwa
Toro. Ganin wadatar da yake ciki sai aka fara yi mana sintiri da sunan ziyara ko
hutu. Wanda kafin ya shiga wannan rufin asirin ba'a cika tunawa da shi ba. Bare a
taimake shi.
Nasiba ce dai bai sake yarda ta zo ba, ya yanke dukkan hulda da ita.
A wannan tsukun na fahimci al'amarin da yake zuciyar Tijjani, domin yadda yake yiwa
Baban Marina hidima ko su Yaya Salisu basa yi masa hakan. Yanzu a gidanmu ana iya
soya dankali ko doya. Shi da su Yaya Salisu da Yaya Rabiu suka kwaskware kofar tamu
ta farfado. Baban Marina da kansa ya fada mini a waya ce wa Duk satin duniya sai
Tijjani ya tura masa kudi. Ban da kayan miya da su dankali da yake kai masa babu
gajiya.
Haka kuma yake yiwa mahaifiyarsa. Dada kuwa kayan shayi ne da sabulai da turare
baya rabata da su.
Maimakon a yaba masa sai gabadaya gidan aka hau cece kucen ni na hana shi ya
kyautata wa su Baban Tsakiyar da Baban kasuwa sosai. Tunda ai duk daya suke da
Baban Marina a wajen sa. Amma suna gani za'a yi ta shiga da kayayyaki kofarsa akai
akai. Amma su a leda ne kuma sai jifa jifa. Shin dan yana surukinsa ne, ko kuwa
akwai wata alak'a ce da tafi tasu?"
Nazira ke tsegunta mini. Tare da bani labarin yadda Baba Maryo take cusa masa
Nasiba da fad'in ai ba komai ba ne dan ya hadamu ya aura. Rabon y'aya'n da ta haifa
ne ya sanya ba a yi da shi ba. Haka kuma ga rabon y'an biyu a jikin Yabi.
Dada dai bata ce wa komai a dalilin tana gudun bacin ran autarta. Yayin da Nasiba
bata zafafa ba. Tabbas tana son Bulkachuwa. Idan ya nuna yana sonta a radin kansa
zata amince domin ba zata zalunci kanta saboda Yabi ba. Amma ta karaya a dalilin ta
fahimci shi kansa a hannun Yabin ya ke. Tunda ta dawo daga gidansa ta zauna ta yi
nazari da kyau ta fahimci Yabi ta bar masa gidan ne saboda ya kai ta. Tun daga
lokacin kuma bata sake ganin walwalarsa ba. Idan ta gaishe shi zai amsa. Amma ko
kallon inda take baya yi, bare ya fahimci me take ciki. Ta kuma tabbatar fishin
Yabi yake gudu na gaske. Ita da kanta mamakin yadda yake shiga nutsuwar sa yake
idan yana gabanta. Idan kuwa ya zo Toro ta bugo masa waya gabadaya nutsuwa wa yake
tamkar uwarsa ce ta masa waya. Ya dinga b'are b'are yana tambayar lafiyarta da ta
tagwaye. Sannan ya bawa Dada wayar dan ya tabbatar mata a inda yake.
A kasan ranta bata ganin aibun matsananciyar soyayya da gudun zuciyar Yabi da yake
yi. Domin ta tabbatar Yabi ta cancanci ya mata irin wannan soyayyar domin ta
sadaukar da abubuwa da yawa saboda shi. Ta jure a lokacin da kowa yake gudunsa duk
da tirsasata aka yi. Ta rufa masa asiri da sana'arta. Kenan a yanzu da ya fara
samun dama, dan ya kyautata mata ba abin birge wa ya yi ba. Abin da ya kamata yake
yi.
Ta sake yarda ko ya aure ta, ba zata iya da jidalin Yabi ba. Tunda a bayyane yake a
hannunta yake. Kawai zaman hak'uri zata yi.
Abin da ya dame ta daya ne. Yadda mahaifiyarta ta fantsama nemo mata maganin da
za'a karkato da hankalinsa kanta. Kullum a cikin bata rubutu take wanda ta tabbatar
sunansa ake rubuce wa.
Tana kwance ita kad'ai a daki tana ta nazari tare da alkalancin bai kamata ta aure
shi ba. Mafi muni ma ta hanyar asiri. Ta tabbatar mahaifiyarta ce ta yi sanadin
raba ta da shi a dalilin ba shi da komai, kuma ba a kintse yake ba. "Yanzu kuma da
ya zama mai daraja sai ki cusa masa ni a kan dole?"
Ta furta a fili ba tare da ta shirya yin hakan ba.
Kunya ta kama Nasiba. Ta ya ya mahaifiyarta zata runtse ido daga yin alkunya ga
d'iyar wanta uwa daya uba daya? Ta san zumuncin zamani ya shiga tasgado mai yawa,
mussaman na gidansu. Amma tana matukar kaduwa da son kai irin na gyatumarta. Har
kunya ta taya ta ji a sadda ta karbo mata taimakon da aka rubuce sunan Tijjani da
na uwarsa. Alhalin a sadda yake sonta akan idon uwar tasa ta wulakantasu ta hanyar
ce wa d'anta bai kai a ba shi aurenta ba. Amma yanzu wai ba wanda take so ya zama
surikinta sai Tijjani, mijin Yabin Baban Marina. Ta sake ce wa "wacce irin BAK'AR
TA'ADA ce wannan? Wanne irin son zuciya ne ya yiwa mutanan yau katutu a zuciya?"

✍️




*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Saiwowin maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki
da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*

83&84.
Zaune nake ina duba kayan gyara da na siya a wajen Surayya Halin yau. Domin lokacin
haihuwar twins a wajen ta Yaya Ummi ta siya mini kayan da suka gyara ni matuka da
gaske har Baban 2 ya dinga tambabar ni na haife su kuwa?.
Tsumin kwakwa ya tayar mini da kwadayinsa da na jima ina yi. Domin dad'i gare shi.
Na dauka na sha. Na tashi na je kicin na dauko gwangwanin Madara ta ruwa na fasa.
Domin tunda Tijjani ya fara samun sukuni kullum sai na sha gwangwanin Madara. Ban
da sauran abubuwan da suke inganta lafiyar jiki.
Na fasa na juye a kofi. Na dawo falo na bude robar koren maganin da na tabbatar da
kyaunsa. Na zuba na juya na shanye. Ina hasasho subadin da zan sha yau a wajensa.
Na tattara sauran na kulle dan kada na yi over dose.
Na dauki waya na k'ira shi. Ya amsa na ce "ka taho ne?"
"Eh kina son wani abu ne?"
"Ka taho mini da dabino ko kwakwa ".
Da azama ya ce "Done my little, ban ji hayaniyar 2 ba". Na ce "gasu nan barci suka
yi".
Ya ce "Da yammacin nan? Tashe su dan Allah. Bazan yarda da daddare su tisamu a gaba
su hana ni hutawa ba".
Na kyalkyale da dariya. Domin nasan nufinsa.
Na mayar da robar y'aya'n gadali domin sai gobe zan ci tunda bani da kwakwa ko
dabino a hannuna.

*Akwai kayan Chad masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin Saiwowin ne
da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku
kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*.
Sosai muke zamana lafiya da taka tsantsan kan abin da zai janyo mana rikici. Na
fahimci yajin da na yi, ya sake sawa Tijjani tsoron mu yi fada. Duk da hakan kuma
wani loakcin zai fitittke ya yi mini sababin na raina shi, ko akan abu kad'an sai
ya tsiri fishi yana fad'in "Tunda Babah ta bani lasisin na dinga yi masa yaji shi
ke nan nake yi masa abin da nake so. Dan na ga ba shi da yadda zai yi. Idan yana
irin wannan fishin, wani zubin ya bani dariya. Wani lokacin ya bani mamaki. Idan na
so sai na rarrashe shi tunda shi haka yake kamar su Hanif wajen son a ritata shi, a
tarairaye shi. Wanii lokacin kuwa na share shi, na fi shi fishi. Idan ya lura da
hakan sai ya yi maza ya hadiye nasa fishin ya hau lallaba ni.

*Shekara daya a gaba*

Kwanci tashi tagwaye suka yi shekaru uku. Haka muke gurgura rayuwa yadda ta zo.
Wataran fari, wataran baki. Zuwa lokacin sosai harkokokin Bulkachuwa suka sake mike
wa. Ni kaina ina siyar da dankalin turawa da su karas da atile a cikin gida. Ba
kuma k'aramin alheri nake samu ba. Tunda shine yake siyo mini babu maganar kudin
kawowa. Idan na siyar na cire riba na ba shi kudin sai ya sake siyo mini wasu. A
hakan har na tara jarina ba tare da na zuba wani kudin ba. Dan haka na ware kudinsa
na ba shi, tare da yi masa bayanin yadda kudaden suka haihu dan haka zan cigaba da
yi da nawa. Yana bude baki sai ce wa ya yi wadananan din ma naki ne. Kin tuna
bashin da kika yi ta ranta mini a lokacin da bani da shi?". Na girgiza lai na ce "
A a tsakanina da kai babu bashi Baban 2. Ba ka dauke ni yadda na dauke ba Wallahi."
Da azama ya ce "Na gode, na yarda babu bashi. To na ba ki kyauta.
Na murmusa na ce "Ka dai biya ni kawai. Shike nan na gode, Allah ya kara budi da
lafiya." Ya amsa da "Ameen maman 2."
Ya kanne mini ido tare da ce wa "Na kosa a yiwa su twins Gambo fa".
Na yi dariya na mike na bar shi dan yanzu sai ya fara tsokana ta akan abubuwan da
na yi ta yi masa a baya.
Muna cikin haka babu zato sai ga shi ya zo mini da takardar da take nuni na samu
gurbin karatu a kwalejin ilimi ta jihar Bauchi.
Ban yi murna ba, domin tun filazal na fi son na yi kasuwanci. Na kuma fahimci
Ubangiji ya sanya mini nasibi a cikin juya kudi. To akan me zan damu kaina sai na
yi karatun da babu garantin zan ci moriyarsa tunda kullum kasar sake lalace wa take
yi. Aikin gwamnati siyar da shi ake yi da makuden kudade, sai kana da hanya ma da
ka samu a siyar maka d'in.
Bai yi fishi ba, ya zauna ya dinga zayyano mini tasirin ilimi a wajen mace ba dan
ta yi aiki ta samu kudi ba ne kawai. Ilimin mace da gogewarta na taimaka mata
k'warai wajen bawa yara tarbiya da sanin yadda zata yi cudanya da mutane daban
daban. Ya sanyaya murya ya ce "Ki daure ki sawa zuciyar ki soyayyar karatun nan
Asiya dan sai kin yi shi. Fata na ke yi ko na mutu a ce ke din kina da wata
madagora da zaki rik'e mini y'aya'na. Duk duniya ke nake da tabbacin ba zaki gaza
da hidimarsu ba. Daure ki bani hadin kai mana".
Na dinga kuka domin idan yana irin wannan maganganun gabadaya kidime wa nake yi.
Shi kuma baya fasa fada mini lokaci zuwa lokaci, tamkar mai son na yi haddarsu.
Tare muka fara makaranta da su Hanif. Domin Nursery da take cikin college din ya
snaya su. Da kansa yake kai mu. Sai ya wuce garin da zai je. Bama koma wa gida sai
na gama daukar darussa.
Komawa ta makaranta sai ta jawo takaddama mai yawa a cikin gidan Marina. Domin a
tarihin gidan ni ce na kammala sakandire har na fara ta gaba da ita da kuma aurena.
Dada ta dinga sababin ya rungumi BAK'AR TA'ADAR arna masu barin matansu suna
cud'anya da mazaje kullum da sunan neman ilimi. Babu kishi babu komai. Alhalin
ma'aiki ya ce wanda baya kishin iyalin sa babu shi babu jin kamshin aljanna.
Yanzu gabadaya gidan Marina ni na tsole ido. Rufin asirin da muke ciki ya na
matukar mintsinin ahalin gidan.
Bana damuwa tunda ba a garin nake ba. Wani abin ma har a yi yamididinsa a gama bana
ji bare raina ya baci a banza.

Kwatsam sai ga Maijidda a gida, wai ta yi yaji. Al'amarin bai yiwa iyayenta dadi
ba. Domin ni da ake son ganina ina cikin tasku da jele da sunan bacin rai ba a
tab'a ganin na yi hakan ba. Kuma abin mamaki Jabir din ne ya kawota gidan da kansa.
Domin ta k'ure hak'urinsa a yadda ya fada.
Ya murje idonsa ya juya ya barta. Hakan ya kawo cece kuce da rashin jituwa a
tsakanin Baban Tsakiya da na Kasuwa. Duk yadda suka so boye maganar kada mu ji. Sai
da maganar ta fantsama domin aure zai k'ara ita kuwa ta ce bai isa ba, sai dai ya
zaba ko ita ko amaryar. Ya so su fahimci juna amma ta tada balli domin da ta ga
yarinyar da zai aura tunda dalibar kwalejin da yake koyarwa ce. Ai sai ta gigice
domin haka take yar tsurut fara kal tamkar dai abokiyar tagwaitakar Yabi ce.
Hankalinta ya rubanya tashi domin ta tabbatar ya sota ne a dalilin yadda suke
yanayi da ex love dinsa. Ta kuwa ce ba dai ita ba. Shi kuwa ya ce bata da hurumin
zaba masa wacce zai yi zaman aure da ita.
Watanni biyu basa cikin zaman lafiya, gabadaya ya murde mata fiye da yadda ta
murde. A karshe ya kawo ta gida ya ce ta zauna ta huta tukun.
Da ya tafi ya kashe wayarsa da dukkan hanyar da za'a same shi. Baban Kasuwa ya
dinga fad'a tare da fad'in tozarcin da Jabir ya yi, da shi yake. Kuma ubansa ya
kasa tsawatar masa.

Please Login or Register in order to submit comment