You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ubangiji ya sa ya dace da kyakkawan rabo a lahira".
Shi da Yaya Ummi suna ta fa'din "ameen".
Ya sake kusantowa gare ni. Ya ha'demu gaba'daya ya rungume. A fili ya ce "Allah ga
ahalina, ka so su, ka taya ni kula da al'amarinsu, ka tsarkake mini su. Ubangiji ka
basu kariyar da ni ba zan iya basu ba. Ka zame mini jagoran wajen sauke nauyinsu da
ka d'ora mini. Allah ka bawa uwarsu lafiya da juriyar raino da tarbiya. Ina ro'kon
ka saukar da albarka a cikin gidanmu da rayuwarmu gaba'daya".
Ya dinga kaiwa kuncina da goshina sumba.
Jaririn da yake hannuna ya fara mutsu mutsu da k'ananun kuka tabbacin an takure
shi. Da azama Tijjani ya janye daga gare ni.
Yaya Ummi ta matso da nufin d'aukar yaron. Ya ce "Ashe ba ki fita rarashin Dada ba
Ummilolo? Da kika ga sun fice ai sai ke ma ki bi bayansu ki bamu waje".
Ta ce "ka gama borin kunyar ka dai".
Ya matse ya ce "To ba daukarsa zaki yi ba. Taimaka wa zaki yi ya sha. Da alamu
yunwa yake ji sai tsotson hannu yake yi".
A hankali ya na ce "A a ai ya d'an sha d'azu. Zafi Wallahi!.
Cikin tausayi ya ce "Ki yi ha'kuri, zafin na d'an lokaci ne k'alilan".
Kan dole na yarda na ba shi. Shi kuwa yaro sai zuka yake yi babu jinkiri da alamu
sai yafi d'an uwansa tsotso.
Ana hakan na hannunsa shi ma ya fara nasa sukur sukur din.
Ya mike ya saba shi a kafa'da, yana dan juyawa.
Daidai nan su Babah suka shigo. Ta kalle shi ta ce "Bawa Ummi shi, ka zo ka tafi.
Ka zo ka yi kane kane ko kunyar iyayen pka baka ji".
Ya bada yaron ya fice ba tare da ya sake ce wa komai ba.
Kwana na yi da yini sannan aka sallame mu. Yara lafiyarsu k'alau.
Kai tsaye gida aka zarce da mu. A dakin Gwaggo muke yin jego. Hidima kan hidima
Tijjani da mahaifiyarsa suke yi. Har sai da Baban Marina ya ce "Ka bi a sannu
Tijjani kada ka yi bashi". Tun kafin ranar suna aka lankayawa Yusuf(Hanif).
Muhammad Sani kuma (Hamim)
Har ranar suna ta zo aka yi taron sunan tagwaye cikin rufin asiri. Na yi kwalliya
da leshi, da kuma kyawawan sabbin material din Umm Nihla....
Har kala biyu. Kyaunsu da sau'kinsu ya sanya Tijjani ya siya mini kala biyu. Leshi
kuwa a cikin na lefena na dauka na dinka.
Fayyace irin kayan da muka samu ni da yan biyu bata lokaci ne. Domin gadajen Gwaggo
duka biyu sai da suka cika da kayayyakin barka.
Babbar matsalar da ta fara damuna rashin warke wa ta. Tafiya ta a bubbude. Na je
asibiti sun ware d'inkin. Suka ce na dinga kama ruwa da ruwan dumi da dan gishiri a
ciki zan warke.
Sosai Gwaggo take kula da ni. mun warware mun ciko ni da yara. Na murje tamkar ba
yara biyu nake shayarwa ba.
Matsala biyu ke damuna ta farko kukan yara. Domin idan dare ya fara nisa suka fara
kuka, babu me yin barci a k'ofarmu. Da daya ya fara, d'ayan ma zai dauka, su taru
su kidamamu. Basa dainawa sai an yi assalatu.
Dada kuwa sai fadi take yi "Ai kuka ma basu fara ba, tunda an riga an yi musu
sanadin wahala. Waye zai sha mataccen nono ya share k'alau?"
Matsalar ta gaba kuma nake jin na bu'de. Ina jin yadda iska ke shigata. Nasan na
karu amma ban yi zaton dinkin ba zai ha'de ni ba.
Ga shi ban fasa kama ruwa da ruwan zafi ba. Na kasa jin da'din kaina. Na kasa
fa'dawa Gwaggo. Yaya Ummi na zuwa na fa'da mata. Ta ce "na sa a kawo sassake da
saiwowi kalakala da ake kawo wa daga chadi."
A kunya ce na ce "Na gode.
Kwana biyu a tskani sai ga ta dawo da kayan. Da kanta ta dafa mini, ta ware mini
butar da zan dinga zuba maganin.
Dan kama ruwan da na yi da ruwan maganin har na fara jin da'din jikina. Da zata
tafi ta hada kan kayanta ta tafi da su. Ina son na ce ta bani koren maganin da na
dafa kazar, amma na kasa a dalilin kunya ta yi mini k'awanya.
Na tuna ranar sunan Ubaida yadda su Nasiba da su Maijida suke koda kyaun kayan da
suke siya daga Kano ta hannun Yaya Ummi. Na tuna sadda ta bani ina amarya na ki
kar'ba.

*Masu bu'katar kayan gyara na chadi gangariya, su yi mini magana. 08032773332*
Amma da yake Yaya Ummi yar'uwa ce ta gaske sai da ta bani kayan nan duka. Kazar ma
ta ce zata daho mini idan na kusa arba'in. Cikin dabara na kirgi ku'din da na samu
a barka na sawa y'arta mai d'an dama a aljihunta.
A haka na kwashe sati hud'u da haihuwa. Tijjani ya fara rawar kai da son na koma
gidanmu haka nan. Tunda na warware.
Idan ya fara wannan maganar shiriritar da ita nake yi.
Da safe an yiwa yara wanka suna ta barci tamkar basu ne masu kwana ido biyu suna
kuka mai tsananin gaske ba. Amma da gari ya waye ba za'a sake jin motsinsu ba. Yini
suke suna barci.
Ranar da muka yi kwanaki talatin ya iso daga Bauchi. Ya zaune kan sallaya a tsakar
d'akin Gwaggo. Ya ci abincin da aka kawo masa. Ya kalle ni ya ce "Little ki girmama
al'kawari. Ba irin cika bakin da baki yi mini ba akan idan kin haifi namiji suna na
mussaman zaki saka mini. Cikin ikon Ubangiji kin haifo har biyu amma har yau ban ji
sunan nawa ba. Anya kin yi daidai kuwa?"
Na dauke kai ina murmushin kunya. Tare da ce wa "gaggawa ne da kai. Ka bari sai mun
koma gidanmu zan fara fa'da maka."
Ya yi murmushi ya ce "Gaskiya na matsu fa'da mini na ji kawai".
Na yi dariya na yi shiru.
Ya zuba mini ido sosai ya ce "So nake ku koma, mu yi kwanaki ka'dan kafin mu fara
ha'da kayanmu. Kin san mun kusa cika wa'adin kudinmu. Bazan sake biya ba. Idan na
samu dama a Bauchi nake son na samu k'aramin gida mu koma can. Zirga zirgar zata
mini yawa ga tsadar ku'din mota. Zan fa'da wa su Baba zamu k'aura zuwa Bauchi."
A sanyaye na ce "Allah ya k'ara budi."
Domin na shiga zullumin yadda zan rasa jama'ar da nake da ita, tunda bazan samu
jama'a a Bauchi kamar yadda na yi shura a Toro ba.
Ya ce "Ameen Asiyata! Amma fa ban bar waccar maganar ba.
Dai-dai lokacin Haneef ya fara kuka da alamun razana ya yi. Da azama ya dauko shi,
ya shiga tofa masa addu'a. Sai kuwa ya yi shiru. Ya bu'de idonsa kirr yana kallon
Babansa. Da murmushi Tijjani ya ce "Halo Babana, how you doing today?"
Na murmusa na ce "Kana jiran amsa ne?"
Ya ce "ko bai amsa ba, ya ji ni. Yasan yana tare da Babansa ba ki ga ya yi shiru
ba?"
Na ce "Hakane".
Daga hakan ya tsoma hannu a baki ya fara tsotso.
Tijjani ya ce "shima shan hannu ya fara?"
Na ce "Eh! Shi ne ma yake yi kawai. Hamim din da ya fara, yanzu ya gane nono, baya
yarda ya sha hannu, wannan yafi shi hakuri".
Ya d'aga shi ya ce "To ba shi ya sha kada a dinga amfani da hakurinsa ana barinsa
da yunwa."
Na karb'e shi na gyara na fara shayar da shi. Tijjani ya tsura mini ido yana kallon
yadda k'irjina suka cika, suna tsaye tunda k'ananu ne.
Ya kasa hakuri ya dauko Hamim da yake barcinsa ya ce "Ka ji Momi ta ce "Ba ka da
hakuri. Baban Marina da ka ci sunansa kuwa hakurinsa mai yawa ne".
Shi bai bu'de ido ba. Barcinsa kawai yake yi.
Ya ce "Ta shi kai ma ka sha".
Na ce "kana shigowa, ina kwantar da shi. A koshe yake."
Ya kankace ido ya ce "Ba kya kewata ko little?"
Na ji kunya irin sosai. Na kawar da fuskata ba tare da na ce kanzil ba.
Ya yi kasa da murya ya ce "Na yi matu'kar gajiya. Na matsu sosai".
Na kasa amsa masa.
Ya sake ce wa "Yaushe Baba ya ce zaki koma?".
Murya babu amo na ce "idan mun yi arba'in mana. Ai yanzu ma saboda kukan yaran nan
ne ya barmu da ana yin sati uku zai tattaramu."
Ya nisa ya ce "Idan ta kukansu ne ai zan iya da su Asiyata."
Na yi dariya na ce "baka san kalar kukan da suke yi ba ne."
Ya ce "Da gaske nake yi miki, zan bar komai na ji da su. Kinsan yadda nake jinsu a
raina kuwa?"
Na girgiza kai na ce "Ina zan sani? Amma ni da su waye a gaba?"
Ya tillike da dariya sosai ya ce "Yanzu kishin ki har da y'ay'an ki Asiya?".
Na cuna baki na ce "Yo daga tambaya sai ka hau sarhutu".
Ya murmusa ya ce "Yaushe zasu fiki, to wa ya haifa mini su?"
Na murmusa ka'dan.
Ya ce then fa'da mini sunan da kika ce".
"Oh Allah! Bari na fa'da maka tunda kai gajen hakuri gare ka. Baban 2. Shike nan?"
Da'di ya kama shi, ya washe baki dukkan hak'oransa suka bayyana ya ce "Na gamsu da
suna na mussaman ne. Ke kuma Maman 2?".
Na juyar da fuska ina murmushi na ce "A a ni ba Mama ba ce."
Ya ce to me ce ce?"
"Yaya".
Ya sake cewa wanne irin Yaya kuma?. Ko da yake tare zaku taso tunda kin yi haihuwar
wuri. Amma dai su ce miki Ammi tunda ba kya son Mama".
Na ce "To."
Su Hanif basu bar kuka ba sai da muka kusan arba'in. Kafin lokacin kuwa sun yi
girma na ban mamaki tamkar sun yi watanni biyu. Amma tunda ana fa'din da Bulkachuwa
suke kama dole su yi girma.
Ana jibi zamu yi arba'in Baba ya ce a shirya ni, domin ranar da na cika arba'in zan
koma dakina.
Haka Gwaggo ta hau shirya mini kayanmu, tana ha'de su waje guda. Sannan k'anwar
mahaifiyarta ce zata zo ta zauna ta taya ni rainon tagwaye har su dan yi k'wari.
Ranar da muka yi arba'in tun da sassafe Tijjani ya zo daukarmu, ko kunyar su Baba
baya ji.
Baban kuwa bai yarda ya tafi da ni ba. Kayanmu dai ya yi ta diba yana kaiwa. Mama
Baba ya ce ta rakamu, bayan ya dauko shatar mota ta fara kaimu asibiti a yiwa yara
allurar rigakafi. A cewarsa baza mu hau mashin da jinjirai a kwasar musu sanyi ba.
Mamah ta tab'e baki ta ce "Alhaji da alamu dai y'ay'an Yabi sun zarta na kowa
daraja a wajen ka".
Kai tsaye ya ce "To ai su tudu biyu suka ci, kin san Tijjani ne ubansu. Jikokin
Hauwa ne fa".
Takaici ya kume ta ainun.
Ni kuma na dinga mata kallon ko sai yaushe zata daina Bak'ar Ta'adar rashin ri'ke
girmanta. A shekarun ta ai ta wuce ta dinga irin k'ananun maganganu marasa kan
gado. Wanda babu azanci a cikinsu sai tarin k'yashi da hassada.
Akan dole ta raka ni, a asibitin duk inda muka wulga sai an yi sha'awar tagwaye
tare da yi musu addu'a. Wajen goma da rabi na safiya muka gama da asibitin sannan
muka zarce gidan.
Muka tarar da gidan a gyare tamkar ina ciki. Ban yi mamaki ba domin ya riga ya saba
da gyaran gida.
Jimawa ka'dan ta yi mini sallama tabi motar ta tafi abin ta.
Tijjani ya tisa ni gaba da rawar jiki. A sanyaye na ce "Duk gajiyar asibitin da na
sha. Ka bari mana dare ya yi".
Ya hau jijjiga kai yana fa'din "Ba zan iya ba. Na yi hakuri Asiya! Ke ma kin sani.
Kawai ki bani hadin kai. Da daddare rainon twins zan yi, ke kuma ki yi barcinki son
ran ki".
A hankali na ce "Dama dai ba Baban 2 ba ne".
Ya yi dariya ya ce "me kika ce?"
Na girgiza kai tare da cewa "Ban ce komai ba".
Ya mikar da ni, ya ja ni zuwa d'akin. Na yi turus ganin su Hamim kwance akan
sabuwar katifa madaidaiciya daga gefe. Hakan ya saka dakin ya cike. Na zuba ido ina
kallon yadda ya shimfida zanen gado sosia, su kuma ya jere su, duk da akwai tazara
a tsakaninsu. Na ce "wannan katifar fa?"
Ya ce "Tasu ce. Tunda ba ni da halin siya musu gado, shine na siya musu katifa.
Kinsan ba yarda zan yi su dinga shiga tsakiyarmu ba. Can ne makwancinsu. Idan sun
yi kuka zan koma na kwanta a cikinsu".
Na yi k'aramar dariya ban ce komai ba.
Ya ja ni jikinsa ya rungume tsam tsam yana shakar kamshin jikina. Al'amarin da ya
biyo baya ba mai sau'ki ba ne. Na gamsu ya yi kewata, na kuma gasgata shi da ya ce
a matse ya ke. Duk yadda na takura a dalilin yadda kayan chadi suka saka na matse,
na daure na bar shi ya samu nutsuwa.
Shi kuma sai fa'din "anya ba cs aka miki ba little? Ni ban ji alamun tana nan twins
suka fito ba".
Ni dai ban bude baki na ce masa uffan ba, amma ni da kaina na gasgata kyaun
saiwowin da na yi amfani da su. Na ji dadin maganin sanyin da na sha ba ka'dan ba.


*Domin samun naku kayan gyara na mussaman, ko maganin sanyi sadidan.*
*SAIWOWINE da ake kawo su daga Chad da Sudan gangariya. Ku tuntu'be ni a kai-tsaye
ta manhajar WhatsApp*
08032773332.

*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA
KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA
KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*


*Annur food Delicious Nig*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*


*Wannan page din tukuici ne ga masu comments akan littafin BAK'AR TA'ADA*

Kwana biyu da komawa ta Muna ta barzar amarci. Yaran kuwa tamkar almara basa kuka.
Da sun yi ka'dan suka sha nono sai su yi kwanciyarsu sai an idar da sallar asuba
zasu farka.
Yana dawowa kuwa zai d'ora mana ruwan wanka. Da aka sa zai juyo, ya taya ni mu yi
musu wanka.
Ni da kaina na tabbatar zai yi wahalar gaske a samu miji irin Bulkachuwa. Domin duk
aiyukan gida ba zai zame masa komai ya yi ba.
Ina jin dadin Supplement din FASEELAT. Sun taimake ni wajen gyara mini ruwan nono
da sake hade ni. .G H.T duniya ne na yarda *07039269802*.

Rainon yaran nan kuwa ba abin da ba ya yi. Kafin na yi musu hidima d'aya ya yi musu
biyar. Ko pampars suka bata, ba ya jin komai zai cire ya wanke musu ya saka musu
wani. Idan sun yi barci, sai kuma ya dawo yana tiritiri da ni.
Tun tafiyar tamu bata yi nisa ba na fara fa'din madallah da aurensa a zuciyata. Ban
dai furta a fili ba ne.
Kwana duk da kuwa yana da na'kasu, sai dai alherinsa yafi tsiyatakum yawa.
Kwana biyar da komawa. Baba Lami ta zo daga kangire. Wacce matsayin kaka ce a
wajena. Tunda k'anwar mahaifiyar Gwaggo ce uwa daya uba daya.
Ranar da ta zo, a ranar ya koma Bauchi.
Cikin sau'ki da rangwame nake rainon yan biyu. Basu da fitina. Sannan Baba lami
mace ce mai kazar kazar ainun. Abin da nake yi ka'dan ne. Watana biyu da haihuwa na
koma kan sana'a ta.
A hankali kuma Tijjani yana samun rufin asiri a zamansa a baucy. Tunda abinci dai
baya yanke mana. Iyakar kokarin jarfinsa yana yi. Duk sati zai taho musu da
Pampers. Ni kuwa kayan shayi duk sati ne. Idan na ce "Basu kare ba".
Ya dinga fa'da akan me bazan dinga shan shayi mai kauri ba, alhalin ina shayar da
yara har biyu. Ga su nan su sun yi girma ni kuma na sake zuke wa.
Watarana Baba lami ta ce masa ba rashin cin abinci ba ne, wasu matan idan suna
shayarwa hakan suke yi. Sai sun ya ye sannan su yi kumari.
Baba Lami bata tafi ba sai da muka kwashe watanni kusan biyar a tare. Lokacin su
Hanif na da watanni shida.
Muka ha'da mata alheri sosai. Sannan suka tafi da Gwaggo da Yaya Ummi bikin da za'a
yi a can Kangire. Na so zuwa, amma ya yi mirsisi ya hana.
Sannu a hankali muke rayuwa, bamu cika samun matsala ba, tunda kwanakin da yake yi
a Bauchi sun fi wanda yake yi a Toro.
Kullum idan ya dawo sai ya ce "ki tsananta yimini addu'a little. Mahassada sun
kewaye ni a kasuwar nan. Ga shi an rasa gane inda matsalar take kullum Alhajin da
muke wajensa sai karayar arziki ya ke samu.
Ina jin tsoro k'warai da gaske.
Cikin tausayi na ke kwantar masa da hankali da kalamai masu taushi.
Wani zuwa da ya yi, ya ce "mu
shirya zai kai mu Bulkachuwa mu yi sati.
Na dinga murna domin rabona da zuwa tun kafin na haihu. Ga shi yazu watannin su
tara har sun fara tsayawa. A yanzu kam na gasgata kama suke yi da Bulkachuwa. Domin
suma haka suke dogaye, masu gaba manya. Ba wanda zai ce ni ce uwarsu. Domin manya
ne sosai, sannan ni yar tsurut ce sosai. Kawai faratuna suka diba, da kuma yan
k'ananun kamanni. Amma kammanin ubansu yafi yawa a tare da su. Tun yanzun kuma
halayyarsu ta banbanta. Haneef mai sanyi da hakuri ne. Sai ya yini baka ji kukansa
ba. Kafin ya nemi nono sau daya Hamim ya nema sau uku.
Zai yi wahalar gaske ya damuki d'anuwansa yasa shi kuka. Amma Hamim kullum cikin
nukurkusrsa yake.
Ga shi da shegiyar kiwa. Ko wajen Babansu sai ya akan dole yake zuwa. Ko idan ya ga
ya dauki Hanif zasu fita.
Shi dai kullum yana jikina. Ko k'unshi zan yi, sai dai na ha'da masa kayan wasa a
kusa da ni.
Ko ya ce ",sai na goye shi.
Sabanin Hanif da ba ya yin kiwa. Kowa ya mika masa hannu zuwa yake yi.
Shiyasa ma na fi kai shi gidan Yaya Ummi ya yini tunda yanzu ba ni da nisa da ita.
Kullum Bulkachuwa sai ya ce halina ya kwaso. Domin mafad'aci ne na gaske, ga kuka.
Idan ina mita akan halinsa Gwaggo ma ce wa take yi hakan na yi mata. Haka ta sha
fama a goyona. Bana yarda a dauke ni. Ko band'aki zata shiga sai an yi artabu da
ni.
Da yammaci muka isa Bulkachuwa. Babah sai ina ka saka take yi da ni da yara. Komai
ta mika hannu a kai sai ta dauko ta ajiye a gabana. Yara kuwa kayan wasa sabbi sun
fi kala uku tamkar dama a wajenta suke. Na kasa ha'kuri na ce "Babah wadanda kayan
wasan fa?". Domin ihisan ba a garin take ba. A cikin Bauchi take bari na yi zaton
na yaranta ne.
Da walwala ta ce "Tunda ya ce zaku zo na siya musu, tunda na ga mai sunan yayan
nawa rigimamme ne. Shi dai bai kwaso halin mai sunansa ba. Hanif ne ya kwaso halin
mai sunansa."
Nasir da yake gefe ya ce "Su Babah ana yabon sunan masoyi".
Ya bani dariya na rufe fuskata na dinga yinta. Ta mike sabe da Hanif tana fa'din
ja'iran yara bari na baku waje.
Shi dai Tijjani bai ce komai ba. Asalima matse wa ya yi ko dariyar bai yi ba.
Kwana biyu ya yi, ya barmu ya wuce Bauchi.
Bayan dakina da na Gwaggo ba inda nake samun natsuwa irin a dakin Babah. Domin wata
irin mua'amala take yi da ni mai dadi da tattali. Bata taba nuna surukunta a
tsakaninmu ba. Sai ni ce ma nake jin kunyar yin wasu abubuwan a gabanta. Ita kuwa
da taga hakan zata balbale ni da fa'da tana fa'din bata son rashin kunya. Har
yaushe na zama matar tasa da zan ture ta a uwa na mata kallon suruka. Na sake na yi
komai yadda nake so kamar yadda nake yi tuntuni.
Da kanta ta dafa mini kazar da na tabbatar ta mata ce. Kunya ta kama ni. Ita kuwa
fadi take ci ki sha romon. Tun lokacin haihuwar na siya na dauka zaku zo yawon
arba'in. Tunda baku zo ba. Na ajiye nasan a can ma za'a gyara ki."
Na rasa yadda zan yi, ita kuwa ko a jikinta.
Ranar da Bulkachuwa ya dawo. Da daddare an hadu a falonta ana ta hira cikin walwala
ya kutso da maganar yana son mu koma Bauchi gaba'daya.
Ta ce "ka dai kafe. Yanzu kam tunda yaranta sun yi k'wari ba zan hana ba. Allah ya
bada sa'a.
Dama har da tunanin yadda sana'ar ta zata durk'ushe ne. Amma In sha Allah a can din
ma sannu a hankali za'a santa."
Ni kuma sai kawo masa abinci abubuwa nake yi. Gaba'daya na kasa sukuni. Babah da
kanta ta gane yanzu kam sonsa nake yi da dukkan zuciyata.
Washagari ana zaune bayan mun karya. Sai kawai ya kalle ni ya ce "A irin wannan
ranar ta shekaru uku baya kika zo har nan kika ce ba kya sona Asiya".
Nan da nan na ji tamkar k'asa ta tsage na shige. Kunya ta rufar mini. Na rasa yadda
zan yi. Sai kawai na fara kuka ina ce wa "Idan juninka tashin tashina ne, da son
sai ka kunyata ni, to ni ba damuwa zan yi ba, kai ne zaka ji kunya Wallahi".
Nasiru ma cikin dariya ya ce "Ai kuwa nima na tuna yawun da kika kwalbana masa a
fuskarsa. Yau kuwa sai faman girmama lamarinsa kike yi".
Na sake rushe wa da kuka ina ce wa "Ai kai dama baka fa'din gaskiya".
Babah ta ce "Yo ni ke kika fi ba ni haushi, to kukan na mene ne? Ware wa zaki yi ai
ku yaga, suma ki nutsu ki fadi irin nasu al'amarin da baza su so a taso musu shi
ba."
"Nasiru ya ce "Ni dai babu abin da zata fa'da a kaina, sai dai ko akan mijinta".
Tijjani dai tunda ya kunyata ni bai sake ce wa ba.
Jimawa ka'dan Babah ta mike ta shiga cikin gida.
Nasiru ma ya mike yana ce wa "Hajiya Yabi bari na fece tun Babah bata zo ta fa'da
miki wani abu a kaina ba."
Ko kula shi ban yi ba.
Yana fita na kalli Tijjani na ce "Na gode sosai Baban 2"
Ya yi murmushi ya ce "wannan godiyar fa! Ta mece ce?"
Na matso hawaye na ce ",Na gode da kunyata ni da ka yi, na gode da wannan
sakayyar".
Ya dara ka'dan ya ce ",Kin san na fa'da miki lokaci zai zo da zaki ji kunyar abin
da kika yi".
A hassale na ce ",To mene ne zaka tayar a gabanta? Gaskiya kada ka sake yi mini
irin haka. Idan kuwa ba hakan ba kasan kai ma ka mini laifin da ban ta'ba bude wa
an ji ba".
Nan da nan ya shiga nutsuwarsa ya ce "Ai ni ba da bacin rai na fa'di hakan ba. Amma
ba zan sake ba, mu rufe maganar haka nan.
Na girgiza kai na juyar da fuskata gefe. Ya shiga kiran sunana a hankali, na ki
juyowa. Ya diririce. Ya ce "Asiya wasa fa nake yi miki. Me zai sa
mu yi fa'da a gaban Babah".
Na ce "Ai so kake ka bakanta ni a wajen ta, shi yasa ka dauko wannan maganar".
Ya marairaice ya ce "Billahillazi ba hakan ba ne. Gaba'daya ya rikice jin na lauya
magana zan tado da tashin hankali.
Ya dinga lallaba ni da son sai na dawo da walwala ta.
Ni kuma ina sane na yi masa hakan.
Bamu bar garin Bulkachuwa ba sai da muka shafe sati biyu.
Da zamu tafi, tamkar wanda muka je fatauci saboda kayan da muka samu.
Lafiya k'alau muka isa Toro. Kwana biyu a tsakani ya koma Bauchi.
Kwatsam aka tashi da mutuwar mijin Nasiba. Wannan mutuwa ta bigemu, domin babu
jinya sai mutuwa. Ashe kasurgumin dan shaye shaye ne. Can wajen sharholiyarsu
rikici ya kaure tsakaninsa da abokinsa ai kuwa ya daba masa kwalbar a kahon zuci ya
mutu a wajen nan take.
Gaba'daya maganar ta cika Toro da kewaye.
Na tausayawa Nasiba kwarai da gaske, duk da dama ba zaman dadi take yi da shi ba.
Duk cikinmu ita ce bata samu sukuni a gidan aurenta ba. Yaranta biyu Muhsin, da
kuma Maryam da bata fi watanni shida da haihuwa ba.

*Watanni bakwai a gaba*

Zuwa wannan lokacin mun koma Bauchi da zama. A satin nan kuma na yaye yara.
Bulkachuwa aka kaiwa Babah su. Kwance nake ina fama da zazzabin da ciwon nono ya
zuba mini. Ga kewar yara, abin sai ya hadu ya kwantar da ni. Nasan Hanif ba shi da
matsala, amma Hamim kam sai Allah. Rashinsa ya fi takura ni.
Tijjani kuwa sai tsokana ta yake da fa'din Hanif ne kawai zai dawo, Hamim ya zama
dan Bulkachuwa.
Bana ce wa komai amma na sani zolaya ta yake yi.
Sai da na sha allurai sannan na warware.
Sannu a hankali na shiga saboggina tunda anan Bauchi ma na fara sanuwa a wajen
k'unshi da kitso, sai dai ba kaman Toro ba.
Matsakaicin gida ya kama, cikin madaidaiciyar unguwa.
Cikin nutsuwa da rufin asiri mukr rayuwarmu. Har yau din nan Bulkachuwa tattala ni
yake yi. Baya kaunar abin da zai ha'damu rikici sai dole. Baya

Please Login or Register in order to submit comment