You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rufe baki Dada ta zabge da kuka tare da ce wa "Ashe zan koma gabar ni
Binta? Hauwa kin iya haihuwa! Shehu ya haifu. Allah ka yiwa Shehu abin da mai zato
bai yi zatonsa ba ". Sai kuma ta rushe da kuka wurjajan.
Aliyu ya ce "Ganin hakan ya sanya na biyawa tawa uwar sai ku tafi tare"
Nan ma Dada ce ta yi fit ta ce "Wayyo Ali Allah ya yi albarka, yasa kai ma ayi maka
tagwaye."
Ya ce "Ai tuni ya bani Dada. Wadannan da suke gittawa ta gabanki ba nawa ba ne? Ko
kuwa dan a gidan Marina kowa d'an da ya haifa ne nasa shiyasa kike ganin sai na
haifi wasu tagwayen?"
Da yake babu wata shak'uwa a tsakaninsu, asalima tsoro tsoronsa take ji. A sanyaye
ta ce "A a kuskure ne, da mantuwa Ali. Yanzu dai ba zamu yi fad'a ba, bayan ka zo
mana da babban albishirin da babu irinsa. Allah ya saka da alheri, ya yi muku
albarka gabad'aya".
Ya ce "Ameen".
Babah itama ta yi masa godiya da fatan alheri da bunk'asar arziki. Yabi tana bude
baki ta ce "Na dad'e ina son na tura Baban Marina Umrah. Na dad'e ina fatan na yi
masa ba zata. Ta ce zan tattara abin da nake da shi a yi tafiyar nan da shi".
Idon ta ya ciko da k'walla tana ayyana yadda Baban 2 yake fatan ya kai ta Makkah.
Ashe abin na ransa, ashe itace zata riga shi zuwa Sau'udiyya?
Hawaye ya tsinke mata. Babah ma ta shiga taya ta. Aliyu ya ce "Maimakon ku yi masa
addu'a sai kuma ku yi masa tukuicin kuka?".
Cikin kuka sosai Dada ta ce "Kai ku yi kukanku da kyau kun ji ai! Ali ai dole mu yi
kuka. Yau sama da shekara Shehu na garkame a haka aka samu rabon Asma'u. Kai rabon
haihuwa zazzafa ne".
Aliyu ya ce "Kai Dada da fitina kike. Me ya kawo wannan maganar a yanzu kuma?
Sannan kuma Yaya Tijjani ne ya koma shehun ko kuwa?"
Ta ce "Eh shi fa. Tunda ga y'aya'nsa na girma ai gara na tsayar masa da suna d'aya.
To na zabi Alhaji Shehu kawai domin sha Allahu wataran zai zama Alhaji da ikon
Ubangiji kuwa".
Ya gintse dariyasa ya ce "Ni na tafi, tunda Yabi ta had'a ni da aikin dauko Baban
Marina gobe".
Sai lokacin na ce "Tare zamu je, zan duba yaron Adda Nazira da ya yi targade."
Ya ce "Tom in sha Allah".
Babah ta ce "To kuma ya zaka yi da wannan kilifar ne tunda bata isa yaye ba.
Watanta uku kacal" Ya ce da ita zaku tafi mana".
Dada ta ce "Allahu akabar! Yabi ta haifo Yabi."
Ya kwashe da dariya ya ce "A a Dada. Ai Yabi wadda aka haifa a hanyar sau'udiyya
dan aikin Hajj ne ko aka je da cikinta. Ita kuwa wannan ai an riga an haife ta,
sannan Umrah zaku je ba tawwali ba".
Ta ce Hakane, sai ace mata Ummara Husna. Domin na tabbatar sai ta yi jidalin Asiya
idan ba'a ce mata Ummarah ba. Oh ashe dai da rabon burin Yabi na zama Hajiya a kusa
zai tabbata. Nasan Shehu ya biya mini ne dan na kula da ita, na jagorance ta a
wajen sa'ayi da safa da Marwa".
Ta bawa Aliyu dariya ainun ya ce "A Ina zaki jagorance ta din? Ai ko ke yanzu kika
je d'aya zaku zama, ko wanda ya je bara idan ya koma bana sai ya ga abubuwan da bai
san da su ba. Saboda yadda gwamnatin Sau'udiyya ta mayar da hankalinta akan Makkah
da Madina gabad'aya. Bare ke mai shekaru ashirin da biyar da zuwa, ina ce da kika
je ma ba'a haifi Anas ba?"
Ta rausayar da kai ta ce"Ko Yabi yayarsa ma ba'a haife ta ba. Kasan ana daf da
aihuwata ta Alhaji ya hadu da sharrin masu zamba cikin aminci, aihuwarta ta zo
cikin wani irin yanayi mai tsananin gaske ".
Na hauro na ce "Dada kina son fad'an wannan labarin. Nasan idan tafiya ta mika zaki
k'arasa abin da kuke fad'a cewar ni na kore masa arzikinsa".
Ta kama baki da azama ta ce "Yabi ki yiwa darajar Alhaji da Asma'u kada ki birkice
mini. Ko mahaukaci ya ji labarin ki da irin bajintar da kike yiwa uwa da uba ai
yasan ke din arzika ce ba wai Yabi ba. Yo duk gidan Marina akwai wanda bai ci
arzikinki ba ne? Babu shi Wallahi. Allahu ya huci zuciyar ki. Bazan sake ba. Kai
Ali tashi ka yi tafiyar ka, nima alwallah zan yi na yi munajiti da Ubangiji. Kai ma
ka yawaita zikirrn ambaton Ubangiji ko na istigifari, ko da kuwa tukin mota kake yi
".
Ya yi dariya ya ce "Wato da Yaya Tijjani da Nasiba da Yabi sune maganin Dada."
Na dauke kai na ce "Kada ka sani Yaya Aliyu! Baban 2 da Nasiba dai. Tun fil-azal
sune zasu yi sa insa da ita ta yi mukus. Amma ni kam menene bata yi mini ba?"
Ta yi shiru ya kasa ce wa komai. Sai Babah ce ta fanshe ta da ce wa "To marasa
kunya ta yi din. Suma wadancan din waye su da zasu yi maganin uwarmu? Ai tunda aka
yi sa'a tana tsananta ibada komai zai daidaita mata."
Da haka aka bar maganar domin jikin Dada ya yi sanyi.


*INA MUKU ALBISHIR AKWAI DUKKAN TSOFAFFIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA SALIHA
ABUBAKAR ZARIA*
*ZAKU SAME SU SOFT COPIES A HANNUNA*

*HAKA NAN AKWAI WASU DAGA CIKIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA HAFSAT C SODANGI, SUMA
SOFT COPIES*

*HAJIYA HANNE ADO ABDULLAHI?*
*MARUBUCIYAR WANKA DA GARI DA KUMA WACECE UWA?*
*TO ITA MA TAKANAS NA SAMO MUKU LITTAFANTA DOMIN KUN SANI TA YI RUBUTUN MASU
MA'ANA*.
*LITTAFAN DA YAWA, AMMA AKWAI DISCOUNT DOMIN SO NAKE KU YI TA SIYAWA Y'AYA'NKU DA
KANNENKU LITTAFAI MASU DARASI DA MA'ANA*.

*BA DA JIMAWA BA ZAN ZO MUKU DA SU*.

*0803277333*.


Da kaina na je Toro na sanar da Baban Marina cewar Tijjani ya biya mana Umrah ni da
Dada Aliyu kuwa ya biyawa Babah. Ni kuma na biya masa.
Ya yi k'asa kansa tsawon lokaci bai yi ko da motsi ba bare ya yi magana. Ya jima
kafin ya d'ago. Na ga hawaye jagejage a fuskar sa.
Nima nawa hawayen ya kwace mini amma ni kam na farincikin yadda Ubangiji ya yiwa
fafutukar sana'ata albarka nake yi. Domin bani da burin da ya wuce na sanya Baban
Marina farinciki tun ina mitsitsiya ta. Gorin da ake mini, haihuwa ta ce ta tsiyata
shi. Da kuma bak'in cikin yadda ya zama koma baya a cikin gidanmu na matuka
mintsinin zuciyata.
Da k'yar ya yi jarumtar ce wa "Na sha fad'a miki ke kad'ai gayya ce Asiya. Na fad'a
miki zaki yi albarka. Na dad'e ina fad'a miki akwai lokacin da zai zo da kowa sai
ya so ki har makiyan na ki. Ga shi na fara ganin sakamakon alherin da Ubangiji zai
yiwa hak'uri da juriyar da kika yi a rayuwar ki. Allah ya yi miki albarka. Daga nan
har kasa ta rufe mini ido na yafe miki, kina cikin farar addu'a ta. Allah yasa
y'aya'n ki su yi fiye da ke. Allah ya miki tukuici da alheri. Kin yi hak'urin aure,
kin yi juriya. Da ikon Allah ba zaki sake fuskantar tsanani a gaba ba."
Ina kuka na ce "Allah ya amsa Babanmu! Na gode Allah ya k'ara lafiya.
Ya ce "Ku tafi da gyatumar ki Yabi. Kin ga dukkanku mata ne. Da ikon Allah zaki kai
ni."
Na girgiza kai na ce "Zata je Baba! Amma wannan kudin na tara kaso uku cikin hudu
da sana'ar da na rayu ina yin ta. Kai nake son ka je, dan ka ji dad'i ka kuma
godewa Ubangiji da ya jarrabe ka da fitinar yan'uwa. Sai kuma ya baka y'aya'n da
zasu sadaukar da komai dan ka yi murmushi. Ka je ka yi mana addu'a. Ka kuma tayamu
addu'ar Ubangiji ya kubuto mana da Tijjani ".
Sai kuka na sosai ya k'wace mini. Abin mamaki sai shima ya taya ni kukan muka dinga
yinsa a hankali.
Da yake a dakin Gwaggo yake. Ta shigo da Husna a hannunta da ta fara kukan neman
nono. Ta tsaya cak bata miko mini ita ba. Ta sassauta murya ta ce "Ayyah Yabi baki
ga kullum girma sake kama shi yake ba? Me yasa kike kasa hak'uri a idan kina
gabansa? Kin san yadda kukan ki yake rikita shi kuwa? Kalli irin kukan da yake yi
mana. Me yasa kike rasa dukkan jarumtar ki a gabansa?"
Na kasa magana. Sai shine ya ce "Ni ne nake rasa dukkan jarumtata akan lamarin
Yabi. Tana matukar bani tausayi, kuma dama ita ce raunina a cikin dukkan y'aya'na.
Shiyasa Ubangiji yake ta jarabtata akan sha'anin ta. Tafi kowa shiga garari da
kalubalen rayuwa. Asma'u ki ji tausayin ta?. Ki sake ninka addu'ar da kike yi mata.
Zauna a zaune ki ji al'amarin da ta zo da shi."
Yana hawaye ya fad'a mata zuwn nawa albishir na yi masa zai tafi gabas. Yana rufe
baki itama ta fara hawaye tana fad'in Allah mun gode. Ina taya Yabi godiyar yadda
ka cika mata burin ta, na mayar da Alhaji dakin ka. Allah ka k'ara yaukaka mata
arziki, ka shirya mata zuria. Ka mata tsari da dukkan abin da zai cutar da ita ko
iyalinta".
Ya k'ira Mama da Inna ya fad'a musu alherin da ya same su ya rufe da ce wa kada su
fad'awa kowa sai abu ya kankama. Domin tafiya gabar kiran Allah ne.
A gurgurje na je gidan Nazira na dubo yaronmu.
Da yamma muka juyo da Yaya Aliyu akan gobe Baban zai zo BAUCHI don ayi masa
passport.
Ba a fito da maganar tafiyarmu ba sai da komai ya kammala ya rage saura kwanaki
hudu.
Baban Marina da kansa ya fad'awa y'an uwansa cewar zasu tafi Saudiya. Da Yabi da
diyarta da Dada Tijjani ya biya musu. Aliyu ya biyawa Hauwa. Shi kuwa Yabi ce ta
biya masa. Suka ka'du k'warai. Amma da yake dangantarsu ta yi tsami ainun kowa ya
hadiye a ransa tunda yanzu so suke ace kowa yafi kusa da Baban Marina a tsakaninsu.
Sannan basu gamsu Yabi ce ta biya ba. Duk da dai sun yi matukar sikewa da lamarinta
tun auren Iklima. Zuwan tawagar matar gwamna Toro gidan Marina ba k'aramin cece
kuce da girmama lamarin Yabi ya janyo ba.
Ranar talata da asuba muka nufi Kano tunda an ce shabiyun rana zamu tashi.
Karfe tara a airport din ta yi mana. Aliyu bai tafi ba sai da ya ga tashinmu.
Sannan ya juya da twins da Ikilima da suka yo mana rakiya. Hamim sai kukan sharbe
yake yi. Hanif sai hak'uri yake ba shi yana ce wa "Mun girma fa Hamim. Ammi ba
dadewa zasu yi ba. Ba ta ce addu'a zasu je su yiwa Baban 2 ba? Husna zata raina ka
fa". Suka bawa Aliyu tausayi. Haka kawai yaran suke ba shi tausayi ainun.
Bai bar Kano ba sai da ya siya musu kayayyakin wasa da na ciye ciye dan su warware
gabadaya.
Kai tsaye a Madina muka sauka. Mun gaji likis. Dole muka kwanta. Dada sai addu'a
take yi tana fad'in "Allah k'amshi ya cika hancina, haske ya cika idona, k'arfi ya
yiwa gangar jikina k'awanya, farinciki da imani sun cika zuciyata. Allah ka karawa
Annabi daraja. Allah ka karbi addu'ar da zamu yi, ka bamu k'arfin da zamu yi ibada
ta gaskiya."
Sai ta zauna. Sai ta zabura ta je jikin windo tana leken asumayar masallaci
ma'aiki. Tana kuka tana fad'in "Rabbani yadda ka sake yi mini gatan ganin koriyar
gubba ta d'an Amina mai wuyar ga ni. Allah kasa zan gan shi da idona. Allah ka bani
ikon rokon gafararka idan na shiga rauda. Allah ka shirya mini zuria, ka jefa
soyayyya a tsakanin ahalina. Allah na yi tuba. Allah mai babban suna aiko ni ya yi
takanas, Ubangiji a karba a sassauta a kubuto da shi albarkacin masoyinka Baban
Nana".
Duk juyin da zan yi zan ga idonta biyu. Babah kuwa barci ta yi sosai domin bata
runtsa ba a jirgi, ita take ta fama da Husna.
Daf da asuba muka tashi, muka yi alwallah muka nufi masallaci. A harabar hotel din
muka had'u da Baban Marina shima ya fito zai tafi. Na kalle shi cikin sabuwar
jallabiyar da na siya masa guda uku a Kano. Ya yi fes da shi. Garin Madina rahama
ne.
Gabadaya zukatanmu cike suke da shauki da rauni. Duk juyin da muka yi da Dada ta
saka silifas din ta. Ce wa ta yi "Wane mutum ta taka k'asar Madina da takalmi? Mu
dai da muka ga zamu taka ba zata ce komai ba. Allah ya yafe mu kawai"
Kan dole muka k'yale ta. Domin har muka yi kwanaki biyar a a Madina bata yarda ta
saka ba. Duk ranar da aka yi ranar juma'a ma haka ta tako. Sai da muka shiga motar
tafiya Makkah sannan ta saka takalmi, tana hawaye tana fad'in "Allah ina son na
sake dawowa. Idna ban samu damar ba, na yi godiya. Allah karbi addu'ar da muka yi."
A Makkah kuwa har tausayi suke bani tunda muka je dukkanmu a masallaci muke kwana.
Mu yi sallah, mu yi dawafi. Duk shekarun Dada bata zama. Ko dan yar firit ce irina?
Ban sake gasgata komai na Dada na kwaso a halitta ba. Sai a tafiyar nan da muka yi.
Kamar da muke yi ta baci. Na tsinci kaina da addu'ar kada Allah yasa na yi halinta
idan shekarun girma suka cimma ni. Tunda ta sha fad'ar hatta fad'an da na yi ina
karama itama haka ta yi a lokacin kuruciyarta.
Baban Marina kullum sai ya ce "Dada yau ki kwanta ki huta, Hauwa ke ma ki huta,
Ubangiji ya ji addu'ar mu da ikon Allah Tijjani zai fito. Idan kuwa har muka ga bai
fito ba, to tabbas zamansa a can yafi alheri. Ku duba shekarun da Annabin Allah
Yusuf. Da'n Annabin Allah Yakub, d'an Annabin Allah Ishaq, d'an Annabin Allah
Ibrahim A.s. ya yi a kurkuku. An tambayi Annabin Rahma wanne mutum ne yafi
kololuwar daraja da nasaba, sai ya ce D'an uwana Yusuf A.s. Amma ya yi shekaru masu
nauyi a sijin. Hakan bai zame masa tawaya ba, sai ma k'ara masa kusanci da Ubangiji
ya yi. Bayan ya fito kuma Ubangiji ya karrama shi daga bawa ya koma shugaban kasa,
kuma babban d'an majalisar sarki."
Dada tana kuka ta ce "Hakane Alhaji amma tunda zan iya bari kawai na yi ibada
tuk'uru. Na nemi gafarar Allah, na nemi soyayya da tausayi da afuwa ta wanzu a
gidan Marina. Bar ni na yiwa Shehu addu'ar ya fito ya cigaba da walwala cikin
iyalinsa. Yabi kad'ai idan na kalla sai na ji kuka, bare y'aya'nsa. Ni dai na yafe
maka Alhaji. Kaima ka yafe mini". Sai ta kece da kuka. Ya rik'e ta a jikinsa ya ce
"Sha'anin uwa ai mai girma ne Dada. Hakkin haihuwa kad'ai ya isa ayi mata biyayya,
a girmama sha'anin ta. A kuma dauwama ana rokar mata alherin duniya da na kiyama.
Ban kullaci kowa ba bare ke da aljannata take damafare da sawunki."
Cikin kuka ta ce "Albarkar d'aki ka rabauta duniya da lahira Alhaji".
**
Kwanakinmu goma a Saudiya. Saura kwanaki biyar mu koma gida. Addu'a kam mun yi ta
sai fatan alheri ya biyo baya.
Imani ya sake cika mini zuciyata. Na ji sassauci mai yawa akan kullatar da na yiwa
mutanan da suke gwada mana rashin kirki. Sai na fahimci afuwa da yafiya suna warkar
da zuciya, suna sake girmama mutum a wajen jama'a da wajen Ubangiji.
Kwatsam na kunna wayata sai ganin status din danginmu nake babu kakkautawa dauke da
hotunan Baban 2 babu kakkautawa
Jikina ya sab'e da rawa na kasa gane me suke rubutawa domin gabad'aya na rikice!




*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Saiwowin maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki
da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*

*Y'ar uwa, ya mukaji da bubukuwa?* *Daga nan fa har january kusan ko wanne sati
akwai biki, in ba na kusa ba akwai na nesa, ban da tunanin gudunmuwa da ma kudin
man da zakaje bikin ga tunanin abunda zaka saka.*
*Balle ace maaikaciya ce ko CEO ce kina business din ki, kinsan all eyes on you🧐,
ke ba sayen atamfa ba komi tsadanta anyo copynta, shima lace haka, cabdi! To
albishirinki yar uwa!*
*UMM NIHLA malaysianfabrics ta dauke miki damuwa, tana da fabrics kala kala masu
sauki da inganci kuma babu inda zaki samesu in ba wurinta ba, kije taro ki haska
kowa sai ya tambaye ki me kika saka ina kika samu💃 maza garzaya gurinta kusa
labule.* https://wa.me/message/F3EWRSHQPQAAH1

*Kawata Janafty zata yi muku reposting din littafin Zaman Gidanmu*.
*Kada a manta da littafan marubutan Dab'i*
*Hajiya SALIHA ABUBAKAR ZARIA*
*Hajiya Hafsat C SODANGI*
*Hajiya Maryam Kabir Mashi*
*Hajiya HANNE ADO ABDULLAHI*

*INA KAWO MAGANIN GYARA MASU KYAU DAGA CHAD DA SUDAN*
*MAGANIN SANYI SADIDAN*
*INA AIKAWA KO INA A K'ASAR NAN*
*BA ZAI YIWU NA TALLATA MUKU ABIN DA BA SHI DA KYAU KO INGANCI BA. DOMIN SOYAYYA DA
AMINCI NE A TSAKANINA DA KU MASOYA RUBUTUNA*
*KU JARRABA SAIWOWIN DAHUWAR KAZA DA TATTABARU KU GA NI*

*KAZALIKA MAGANIN SANYI DA TSUMIN GORAN TULA BABU NA BIYUNSU*
*GA Y'AYA'N GADALI DA YAKE SHA YANZU MAGANI YANZU*
*ASALIN DAKA NA EMERGENCY*
*DA GUMBA DA KUMA TSUMIN KWAKWA DA ZUMA NA SHARHOLIYA*
*TUNTUBE NI KAWAI TA WHAT'S APP.DAN SAMUN BAYANI NA SOSAI*
*KU GYARA KANKU, KU GYARA Y'AYA'LNKU*
*MASU SHIRIN AURAR DA YARANSU KO KANNENSU A ZO A SAMA MASU KAYA MASU NAGARTA*
*08032773332*
*NA GODE*

*Alhamdulillah! Alhamdulillah!*
*Nasararorin da na samu a wannan labarin tabbas daga Allah ne*
*Na gode masa da ya bani lafiya da azanci*.
*Na gode masa da ya bani ikon sauke nauyinku, na gode da ban ja muku rai ba*.
*Idan rayuwa da lafiya sun cigaba da wanzuwa mini zamu sake haduwa a wani sabon
littafina*.
*Idan kuwa ba'a samu damar hakan ba, to na gode muku gabad'aya da soyayyarku ga
rubutuna*
*Allah ya shiryemu ya shirya zuria.*
*Wallahi ina matukar alfahari da duk wacce ta saka kudinta ta siyi wannan labari*.
*Ubangiji ya fini yabawa, ya rufa muku asiri duniya da lahira*.

*Lokaci ba zai bani na kama sunan kowa ba*.
*Domin shafin ya yi kad'an na zayyano sunayen mutanen da suka yi mini karamci ta
sanadin rubutu*.
*Labarin Bakar Taada ya janyo mini mutanen da basu san komai ba sai alheri*.
*Mahaifina a lokacin da yake raye yana yawan ce mini ke y'ar gata ce Surayya*
*Na gasgata shi, domin kullum Ubangiji cikin kewaye ni yake da rufin asiri mai
yawa, yana ta had'a ni da mutanan arziki da suke ta mayar da ni gayya a cikin
jama'a*
*Na gode sosai Allah ya kewaye y'aya'nku da rufin asiri mai yawa*.

*Zan yi KEWARKU Wallahi!*.

Na nutsu na lalubo na Aliyu sai na ga hoton Bulkachuwa sannan ya rubuta Barka da
samun yanci Yaya. Allah yasa wannan al'amarin ya zame maka tsanin shahararka a
duniya."
Na bude murya sosai na ce "jama'a Tijjani ya fito, an sake shi. Gabadaya na rikice,
na rikita su. Da k'yar na nutsu na musu bayani. Dada aka fad'i aka yi sujjuda. Ni
da Baba muka yi maza muka but bayanta muma muka yagi sukjadar. Ta zabura ta ce
"Haramin zan koma. Duk da dare ne bamu hanata ba, muma muka bi bayan ta. Bayan mun
je dakin Baba baya nan tabbacin yana masallaci a can zai kwana.
Duk son mun gan shi bamu samu zarafin hakan ba. Sai da gari ya waye muka dawo
masauki. Ai kuwa gabadaya muka kutsa dakin da yake ciki. Muka hau rigen yi masa
albishir. Muna tare a dakin Aliyu ya kira ni vedio call. Aka gaisa aka yi murna, ya
nuno mana fuskar Tijjani da ya kare da hannu. Da k'yar ya ce "Ina gaishe ku
gabadaya. Na gode sosai. A kuma sake yiwa Ubangiji godiya.
Duk yadda nake jin dad'i a Makkah amma sai na ji kwnanaki hudun da suka rage
gabad'aya sun mini tsauri. Ji nake tamkar na bude ido na gan ni a BAUCHI.
**
*Yadda al'amarin ya kasance*

Rundunar ta gurfanar da Alhaji Auta a gaban kotu domin da kansa ya kai karar kansa
ofishin y'an sanda ya tabbatar musu laifinsa akan abin da ya yiwa Tijjani. Cikin
kuka ya ce "Na aikata BAK'AR TA'ADA, na bari sharrin zuciya da shaidan sun janyo
mini wahala. Tunda aka rufe yaron nan. Al'amarina ya sake kacame mini, kullum
masifu sake yi mini k'awanya suke yi. Dan haka na zabi na kubuta daga azabar
lahira. Tiryan tiryan ya yiwa y'an sanda bayani yadda ya shirya komai.
Take aka k'ira yan jaridu na radio da talabijin ya maimata a gabansu.
Nan da nan abu ya watsu a
BAUCHI da kewaye ko ina maganar ake yi. Sai Allah wadai ake yi da halin Alh Auta.
Wasu kuwa su ce ya yi sa'a ma da ya zabi ya fadi gaskiya ya samu sassaucin
kwanciyar kabari. Wasu kuwa su ce Yasin aka yi ta buga masa da alkunut shiyasa ya
kasa gaba ya kasa baya har sai da ya fito ya lashe amansa.
Mai dakin gwamna na zaune a katafaren falonta tare da mai girma gwamana suna kallon
N.T.A BAUCHI. Suna kallon yadda kae nuna Alh Auta kai tsaye (live) yana bayanin
tuggun da ya had'a. Take ta tuna labarin da Yabi mai lalle ta yi mata. Nan da nan
ta ce "Yallabai ka yi magana a gaggauta sako yaron d aka yiwa kaAmzfin nan babu
dogon turanci. Ina sake rokon gwamyta bashi Wani abu na diyya bisa samaye shi da
aka yi babu laifinsa. Sannan a gaggauta gurfanar da wannan tsohon banzan a gaban
kuliya. Idan ka gaggauta sakinsa tare da yi masa wani alheri jama'a zasu sake son
ka su tabbatar adali ne. Tunda a yanzu babu abin da zai dauki hankalin al'ummar
BAUCHI irin wannan al'amarin ".
Take kuwa ya dauki waya ya yi magana da mahukunta. Kasa da awa daya aka.gata ganin
Tijjani a talabijin, tare da jajanta masa. Gwamnati kuma ya bashi kyautar milyan
ashirin bisa bata masa lokaci da suna da aka yi. Bayan haka take gwamna ya bashi
S.A. wato mai bashi shawara akan gidajen gyaran hali.
Ba a jima ba sai ga hukumar kare hakkin dan Adam sun dauke shi aiki. Haka ta costom
da kuma hukumar kula da kiyaye safarar k'waya da tu'ammali da ita. N.D.LA.
Cikin yini daya tak sai da aka yiwa Tijjani aiki tayin aiki a ma'aikatu biyar.
*KAWATA JANAFTY ZATA SAKE REPOSTING DIN ZAMAN GIDANMU, za Kuma ta kai shi AREWA*.
Ganin hakan gwamna ya sake ce wa ya bashi aiki a a ma'aikaar aikin Hajj. Da albashi
mai tsoka. Wajen da aka bawa Tijjani duk shekara sai ya samu gurbin kujerar aikin
hajji d'aya ko biyu. Ga shi babban mai bawa gwamna shawara.
Ga milyoyin kudi. An sha wahala, an yi bak'in ciki, amma a karshe sai alheri da
daukaka ya biyo ba.
Yanzu da aka gurfanar da Alhaji Auta a gaban shari'a sai aka yanke masa
kwantankwacin shekarun da Tijjani zai yi. Bisa kama shi da zambo cikin aminci, da
kuma yiwa k'asa da jihar BAUCHI zagon kasa. Ga mamakin alkali sai Tijjani ya mike
ya ce "Ni dai laifin ya yi mini na yafe masa. Allah shine shaida na yafe masa,
ubana ne, sharrin zuciya ne d azal ya hau kansa. Tare suka yi gwagwarmaya da
mahaifunay. A saddna naje gabansa da nufin ya taimake ni ya bani sana'a bai ki, ba
asalima ya daukake ni a cikin yaransa. Maganar filina d aka karaba ba nasa ba ,
shaidan ne ya shafi kirijinsa. Da yawa mutane basa iya tsallake tarkon kyashi da
hassada. Dan haka na yafe masa. Allah ne shaidar hakan".
Mafi yawan mutanan sai da suka yi kuka. Suna ayyana da ace mutane irin su Tijjani
ne suka fi yawa a duniyar da ba a shiga tsananin da ake ciki ba. Abin da ya yi ya
sake zaburar da jama'a girman afuwa da sassauci. Take kotu ta zabtare shekaru biyar
a cikin bakwai aka mayar masa shekaru biyu, wanda wannan hakkin cin amanar gwamnati
ne bata yafe ba. Sannan ya zama gargadi ga masu son k'ulla sharri haka siddan.
Gabadaya kafafen sadarwa labarin da ake tattunawa akai.
Cikin rakiyar jami'an tsaro aka ki shi gidansa.
Aliyu ne da su Yaya Salisu da Yaya Ammar suka tarbe shi. A ransa kuwa so ya yi ace
ya tarar da Babah da Yabi da kuma Dada. Ya tabbatar ukun nan suna gaba da komai a
rayuwarsa. Domin ya sani Dada ta so shi hakikanin soyayya.

A daddafe kwanakin suka cika muka tattaro muka dawo cikin tsananin farinciki da
murna.
Aliyu bai samu sukunin zuwa daukarmu ba. Muna dira ya kira Baban Marina tamkar mai
auna lokaci. Ya ce mu dauko shatar mota ta kawomu. Da yake karfe takwas muka sauka
a Kano na safiya. Hakan kuwa muka yi. Ban tab'a ganin nisan tazarar Kano zuwa
BAUCHI na sai yaiy. Jin na yi gabad'aya na kosa.
Haka muka isa Lafiya muka tarar da gida cike da mutanan Toro da na Bulkachuwa. Ana
murna tare da dawowa lafiya. Na kalle shi yana kan kujera ya yi wanka yana sanye da
k'ananun kayansa. Ya rame kam. Amma ya yi kyau. Ya yi aski saisaye. Ya yi fes,
twins suna gefen hagu da damansa ma'ana sum sanya shi a tsakiya. Sai satar kallon
juna muke muna murmusshi. Gabadaya mutanan da suka cika gidan sun gundure ni. So
nake kawai su kauce su bamu waje.
Sai la'asar suka dunguma

Please Login or Register in order to submit comment