You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai bayan ta zata bi. Sannan fishi zata yi
da ni! Yanzun ma ya nake fama ne a rayuwar nan bare kuma ace ina cikin fishin uwa.
Rabu da ita kawai Dada. Idan na fa'di na mutu ba shi kenan ba. Sai ta je ta auri
wanda take so."

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA
BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWIA SAIWOWIN SANYI*
AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU*
*AKWIA SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.


Yadda ya yi maganr ya yi matu'kar dukanmu. Ko ni da ba sonsa nake yi ba. Ya bani
tausayi kwarai da gaske. Bare Dada da kowa yasan bata jure ganinsa cikin damuwa.
Ta rasa inda zata tsoma ran ta. Ta kasa cewa komai.
Can ta ce "Tashi ki kawo masa abinci".
Na zum'bura baki ainun na ce "Ba fa ya ci Dada. Akan me zaki ce sai na ba shi,
salon ki sa zuciyata tafi hakan b'aci tunda barinsa zai yi".
Da sauri ya ce "Wallahi bazan bar shi ba Asiya. Ci zan yi, yunwa nake ji rabona da
abinci tun daren jiya. Na gaji da abincin siyarwa, ban saba ba, tun fil'azal."
Jikina ya mutu murus.
Cikin murya marar amo ta ce "Kin ji ya rantse zai ci".
Na sake d'aure fuska ban tanka ba.
Ta kalle shi ta ce "Kai me yasa idan ta dafa kake k'in ci?"
A hankali ya ce "Zubin wula'kanci ta yi mini. A bu'de kuma a farantin roba".
Dada ta fara ce wa "Eh dole ranka ya b'aci, duk namiji sarki ne a gidansa komin
kashinsa kuwa. Lalle Yabi wula'kanci da tozarcin ki kabiran ne".
Nan da nan ya ce "A a Dada ya kuma zaki sake ankara ta. Ai ban ce ki tayar mata da
hankali ba. Ke dai kawai ki rarrashe ta, ai dazu ma kin ce yarinya ce zata daina
ne".
Ta yi sukuri tana kallonsa cikin tu'ajjibi mai yawa.
Jin ya fa'di hakan, na k'ara kukana na ce "Bar ta ta yi son kan da ta saba yi a
tsakaninmu.
Kuma kai ma dan me baka fa'da mata ka kira budurwarka har falona kun yi hira ba. Me
yasa baka fa'da mata bayan hakan da ka yi, bai ishe ka ba. Har umarnin ta yi maka
girki a kicin d'ina ka bata?"
Na fada cikin kuka sosai.
Dada ta dauki salati tana ce wa "A cikin gidan auren ki, ya yi irin wannan ba'kin
zunubin? Eh lallai ba laifin ki ba ne, nasa ne. Wato ni a lokacin da nake kamar ki
yaushe za'a mini hakan na bar al'amarin salin alin ba tare da na fitarwa da ja'irar
jini ba. Na goge hawaye na ce "Ban yi komai ba na kai k'ara wajen Ubangiji. Sannan
kuma har abada bazan sake ba shi abincina ba. Ba kuma zan huce ba, daga nan har na
tsufa".
Dada ta yi maza ta ce "Eh to ba dan ina jin tsoron kada kwanaki arba'in din ta cika
auren ya samu karaya ba. Dana goyi bayan wannan tutsun na ki. Amma yanzu ki yi
ha'kuri, ki yafe, ki huce! Ubangiji yana son masu afuwa da sassauci. Idan ya kuma
ni da kaina ne zan sanar da iyayenku. Ai bazan yarda ki yi irin wannan zaman na
kuttu ba".
Na girgiza kai na ce "Ai Dada babu maganar huce wa. Babu ni babu sake shiga
shirginsa tunda juninsa wula'kanci da nema mini raini ne".
Kafin Dada ta yi magana ya yi fit ya ce "Ban san zaki ji haushi ba Asiya. Na rantse
ban yi da gayya ba. Amma tunda ban kyauta ba. Allah ya baki hakuri. Ba zan sake
ba."
Na dauke kai ina harara tamkar idona zasu fa'do k'asa.
Ya ce "Dada ki ce ta yi hakuri mana."
Ta nisa ta ce "ki yi ha'kuri kin ji. Ta shi ki ba shi abincin ba dan halinsa ba.
Dubi Allah, ki duba Manzonsa."
Ban sake ce wa komai ba. Na mik'e din.
Ban san ya aka yi ba, da na isa kicin din na samu kaina da d'auko plastic plates
masu fadi guda biyu.
Na zuba masa na rufe na dora cokali a kai. Na dauka na nufi falon. Ina jin Dada na
fa'din "kada ka sake kuskuren saka wata ta yi maka girki. Ban da sakarci ma ina kai
ina doguwar magana da ita, bare har kasa a yi maka girki akan idon matar ka. Ai
gwara da ta murd'e maka. Kasan halin fa'dan ta ai, bare kuma an tsokano ta".
Murya ba amo ya ce "ki bar maganar nan, sai na zo dakin ki. Yanzu dai lallaba mini
ita Dada kawai".
Na shiga na ajiye a gabansa. Ya saki murmushi ya ce "
"Madallah da Asiya". Na cuna baki na dauko ruwa na ajiye masa a gabansa na koma
gefe na zauna.
Ya dauki abincin ya dinga ci tamkar bai ta'ba cin abinci irin hakan ba. Cikin
kankanin lokaci ya tashi da uban abincin da na danne farantin da shi.
Fanka na kad'awa amma zufa sai yanko masa take yi.
Ya ta'ba ruwan ya ji sanyi sosai.
A hankali cikin kwantar da murya ya ce "Asiya idan kina da ruwan Lipton taimake ni
da shi mana please" .
Na dauke kai, kamar bazan amsa ba, sai kuma na tashi na fita ba tare da na ce komai
ba.
Dada ta bini da ido tana fa'din "Kasaitacciyar mace. K'aramar halitta mai babban
al'amari".
Sai da na isa kicin na yarda na yi dariya.
Na dauko kofi da cokali. Sannan na dauki filas din ruwan zafin.
Na sake ajiye wa a gabansa ba tare da na ce komai ba.
Na zauna na dauki waya ta ina danne danne.
Dada ta ce "Ba ki kawo masa sigari ba."
Kafin na yi magana ya ce "Idan zata dafa take zubawa, dan rage masa tasiri."
Ta murmusa ta ce "Yabi mutanan turai".
Shi ma ya taya ta murmushin. Ni kuwa ban ce komai ba.
Ya kammala, ya yi gyatsa tare da hamdala.
Ya ce "Har na ji ni a duniya. Na gode sosai Asiya. Allah ya yi miki albarka."
Ban amsa ba. Dada ta amsa da sauri tare da fa'din "Barka da arziki Yabi! Kin
rabauta tunda kika samu farar addu'a daga mijin ki".
Na yi shiru ban tanka ba. Yayin da shi kuma ya mik'e yana cewa "Bari na canja riga
na zo na mayar da ke."
Yana fita Dada ta ce "Yabi maganar nan ta wuce. Ku zauna lafiya. Ko makaho ya zo
gidan nan sai ya gane mijin ki na son ki".
Cikin fishi na ce "Baya sona Dada. "
Ta murmusa ta ce "Yana son ki. Ke ma da gangan kike inkarin hakan. Yanzu bazan
fa'dawa kowa ce wa ba k'alau kuke zaune ba.
Amma fa idan na dawo gidan nan, na fahimci baku shirya kanku ba. Ku tabbatar sai na
ha'da muku iyayenku da Malamai. Dan bazan yarda da zaman kafirci ba."
Na dinga k'unk'unin babu ruwanta da shiga al'amarin da bai shafe ta ba.
Ta gyada kai ta ce "komai zaki ce Yabi ki fa'da. Amma ki sani, ni bazan ha'inci
shari'ar musulunci ba. Tilas ne ku bi ka'idojin shari'a a kan aurenku."
Ya lek'o daga bakin k'ofa ya ce "kin gama Dada, ko na je na dawo bayan maghariba
sai na kai ki?"
Ta yun'kura tana fa'din "Na gama, yinin ya isa, ba sai na kai almuru a waje ba."
Nima na bi bayan ta muka fito. Na kalle shi ya sanya jallabiya. Ko mai bai shafa
ba, bare tuarare. Àllah ya sani ina son na dinga jin k'amshin na tashi a jikin
mutum.
Na shiga daki, na d'auko ledar kayan da ya siyo. Na dauki dubu guda a cikin ku'din
da na tara na lalle. Na saka mata a ciki. Na k'ulle. Na sake k'ara wata ledar.
Na tarar har sun kusa fita.
Na bu'de baki na ce "Dada mun yi sallama ne?"
Suka dakata na isa garesu. Na mika mata tare da ce wa "Ga shi Dadarmu na gode da
ziyarar ki. Amma Wallahi bakin ki k'anin kafar ki akan sha'aninmu Dada. Idan kuwa
kika fa'di wani abu, sai dai a neme ni a rasa."
Ta sassauta ta ce "Ayyah Asiya me na ga ni ma ban da alheri? Ai ko da na ce zan
fa'di baku zauna lafiya ba. Dan ban fahimta ba ne. Yanzu da na fahimci shine da
laifi, ai na fa'di gaskiya. Kawai da ke da shi ku yi kokarin d'abbaka sunna, kada
auren naku ya b'aci ba'a ankara ba.
Kunya ta yi matu'kar kama ni. Na rasa yadda zan yi, sai kawai na juya da sauri na
yi ciki na barsu.
Shi kuma ganin hakan ya sanya ya ce "Allah yasa dai ba sai yanzu kika yi mata
wannan bitar ba Dada?
Domin a zaune zaki yi mata ba a kurarerren lokaci irin haka ba. Idan kuma zaki fasa
tafiyar sai bayan Isha da na fi haka gode wa Dada".
Ta nuna shi da yatsa ta ce "Tabataccen marar ta ido. Oh ni Binta ina kallon
shak'iyanci. Ai gara ma da Asiyan ce matar ka, ita ce maganin ka. Haba kana da
fitina Wallahi".
Ya yi gum. Ta d'aga murya ta ce "Na tafi Yabi, na gode Allah ya yi albarka.
A ci gaba da hakuri."
Ina zaune ina kallonsu ta windo har suka fice.
Suna tafe a hankali yake jan mashin d'in gudun kada ta subuto tunda ba iya hawa ta
yi ba.
A hankali take fa'din "Ashe haka zaka yi mana? Akan me zaka kawo wata har gidan
auren ka?"
Ya ce ba ni na kawo ta ba. Wajenta take zuwa fa.
Kuma kunshi take yi, wai ni rage mata aiki nasa aka yi"
Ta hassala ta ce kaniyarka da rage mata aikin. To bata so. Kada ka kuma wannan
d'anyen aikin."
Ya ce "To bazan sake ba, da gaske."
Suna isa ana kiran magariba. Dan haka da ya kafe mashin din a zaure bai shiga gidan
ba, ya nufi masallaci.
Da nutsuwa ya isa kofar Baban Marina ya gaisa da su Gwaggo cikin kunya da girmama
wa.
Kansa a k'asa ya ce "Gwaggo idan uniform din Asiya na nan wai a bata zata fara
koyon dinki"
Da sauri ta shiga daki tana ce wa "Sabon yana nan. Tsohon dai Ikilima tana amfani
da shi."
Jimawa ka'dan ta kawo masa a bak'ar leda.
Hannu biyu ya sanya yayin karba.
Ya yi godiya, ya yi musu sallama ya tafi.
A gurguje ya yiwa Dada sallama ya wuce gidansa. Yana Jin zumudi da d'okin zama kusa
da Yabi.
Yana son yi mata ba zata. Yana son ya shawo kanta, ya d'ora mata girma ko zata rage
tsiwa da zafin kai.

*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta
sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar
taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi
muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun
san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa,
mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai
soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan
littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan
numbers*
*08089965176*
*07084653262*
✍️.

*BAKAR TA'ADA*

*45&46*


*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA
BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES.*

*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.

*Tallah Tallah Tallah*

Shaharriryar marubuciyar nan wacce tanishaɗantar ku a littafin ta mai sunan
SAMHA```!

```Ta sake sabon shirin ta, wajan ƙara faranta maku rai' tazo maku da sabon book
ɗin ta Wato KECE SANADIN [rayuwa]```

```Masoyana kufito ku nunamin ƙaunar da kuke cewa, kuna min```
```farashin KECE SANADIN ₦500 0nly```
```wacce bata shirya ba kada tamin magana```
```masu san fara pyarment da wuri gashi, 810353370 kimin screen shot ki turo ta
wannan no 08138012334```
```masu kati kuturo ta wannan layin 08108353370```

*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered,
Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan
farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon
yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.

45&46.
Ya shiga da kuzari. A falo ya tarar da ita tana kallon tashar Bollywood.
Yana wahalar gaske ya ga tana kallon tashoshinmu. Har gara tana kai wa Sunna TV
sa'i zuwa sa'i.
Ya manta da uniform a cikin but din mashin din.
Ya zauna kusa da ita.
Ya sassauta ya ce "Asiya Toro babu magana, babu yi mini barka da zuwa?"
Na galla masa harara na ce "To ni ina ruwana da kai da zan yi maka magana? Ba gaba
mu ke yi ba?"
Ya ce "mun shirya ai. Na baki hakuri, kakarmu ta baki, mene ne kuma ya yi saura?"
Na ja tsaki mai tsananin gaske na ce "Da wa din ka shirya? Ai ni duk mutumin da zai
tozarta ni, ya kuma ta'ba lafiyata da sunan duka to babu ni, babu shi har gaban
abada".
Na fa'da cikin matsanancin fishi.
Jikinsa ya fara mutuwa. Ya numfasa ya ce "Ashe duk maganganun Dada basu shige ki
ba? Daga tafiyar ta Asiya zaki fara d'aga mini hankali, mene ne nak'asuna ne da
kika washe ni har hakan?"
Yana rufe baki na ce"nak'asunka ai birjik ne. Mafi muni baka da kamun kai.".
Ya zuba mini ido ya ce "sai me kuma Asiya?"
Kai tsaye na ce "Baka burge ni ko kadan. Domin bana jin k'amshi a tare da kai. Baka
iya kwalliya ba. Kullum kayan ka babu guga. Kalli faratan hannun ka.
Kullum na kalle ka ba'kin ciki ne yake kama ni maimakon farin-ciki."
Jikinsa ya yi sanyi kwarai da gaske. Idanuwansa suka canja launi sosai.
Murya a dashe ya ce "Sai me kuma?"
Na ce "Idan na tuna, na fa'da maka".
Ya numfasa ya ce "Duk zan gyara indai sune cikas dina a wajen ki. Idan na sauya din
shi ke nan zaki daina tsananta mini?"
Na sake shan kunu ban tanka ba.
Ya ce "To nima ina da damar da zan fa'di abubuwan da kike yi mini da bana sonsu?".
Kamar bazan kula ba.
Sai kuma na ce "Baka da damar domin ni ba so nake sai na burge ka ba. Ba kuma so
nake ka zauna da ni akan dole ba.
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Shike nan! Amma ina ro'kon ki kada ki sake shiga mini
da mata dakina".
Na tunzura! Na tashi zaune sosai na galla masa harara na ce "Sannu mai d'aki. Komai
dakinka, dakinka. To sai na shiga d'in.
Shima ya hassala ainun ya nuna ni da yatsa ya ce "Kada ki fasa Asiya. Ai tunda na
gane ba kya son sulhu da sassauci, to mu zuba tsiyatakun mu ga wa zai janye wa
wani".
Na ja tsaki na ce "Ai ka k'oshi shi yasa ka samu kuzarin yin musayar yawu da ni".
Ya juyo a tunzure, ni kuma na zabura na yi shirin kai masa naushi.
Dariya ta kama shi ya ce "Wai dambe zaki yi da ni? Ko da yake ai mai hali baya fasa
wa."
Na ce "oho dai."
Ya fita ban sake jin sa ba, sai da asuba ya tashe ni.
Da safe ba yadda bai yi ba akan na tafasa masa wani abu, duk da ya shigo da burodi
a safiyar, kawai bai dame shi ba ne. Na yi tsallen bad'ake na ce bansan zancen
girki ba, gara mu cigaba da zaman doya da manja kawai.
Ya shiga ya tafasa farar taliya ya zuba yajin *Annur food* da manja. Ya ci ya fice
bai bi ta kaina ba.
Sai da na gama komai sannan na d'ora shayi.
Na karya na yi wanka. Ina zaune babu wuta, kuma babu kowa.
Sai da azahar sai ga y'anmata uku sun zo k'unshi.
Muka shiga d'akin da ake ta mini kashedin kada na shiga na fara yi musu.
Na gama wa mutum d'aya sai ga Hajiya babbar mace sosai. Dan zata haife ni. Mun saba
tuntuni, wani lokacin har gidanta ina zuwa na yi mata, sanadin haka suka saba da
Gwaggona.
Na marabce ta da murna.
Na kammala saka musu. Na kammala yiwa Hajiya a hannu.
Sai ga shi ya dawo. Ban san me yasa ba, na ji faduwar gaba ainun. Wata'kila ko dan
ya yi ta jaddada mini kada na shigar masa d'akin da nufin yin kunshi ne?
Ya lek'o ya tabbatar ban ji maganar sa ba.
Ya juya ko gaisuwarsu bai amsa ba.
Ya dauko bokiti ya janyo ruwa.
Hajiyar ta ce "tashi ki je ki masa sannu".
Na ce To" ba dan ina so ba, na yun'kura na fita. Na gan shi ya gama cika bokitin,
ya dauko na tsaya ban ce masa kanzil ba.
Zuciyata ta tsinke a dalilin yanayinsa ya koma na Bulkachuwa na asali, ba na yanzu
da ya koyi sassauci ba. Ya shige ni bai ko kalli inda nake ba. Ya kai ruwansa
band'aki. Nima na koma na cigaba da lallena.
Mintina biyar sai ga shi ya shigo d'akin babu sallamah. Y'anmatan suka fara gyare
gyaren jikinsu yayin da Hajiyar ta rasa yadda zata yi a dalilin duk na yiwa
hannuwanta k'unshin.
Ba zato ya cire rigarsa ya mak'ale. Zuciyata ta tsinke. Wani irin abu ya tokare ni.
Kafin na wartsake sai kawai ya zame dogon wandonsa, ya yi saura daga shi sai
singileti da gajeran wando. Hankalina ya kai k'ololuwar tashi lokacin da ya cire
singletin.
Ya dauki tawul din da yake rataye ya daura a kugunsa. Ban san me ya hana shi zame
gajeran wando ba. Yasa kai ya fice zuwa band'aki.
Na yi kasa da kaina hawaye ya b'alle mini.

*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA
KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBE TA DAN KUWA DA
KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*

Gaba'daya y'anmatan suka bi shi da kallo. Wani irin mak'aki ya tokare ni. Na sani
zai burgesu tunda Ubangiji ya masa kyakkawar sifa kwarai da gaske. Motsa jikinsa da
yake yi, ya sanya jikinsa ya ginu sosai.
Wanne irin wula'kanci Tijjani ya yi mini yau? Na fa'da a zuciyata.
Matar ta ce "Cire mini lallen nan. Ai bansan maigidan baya so ba. Na tabbatar ba da
izininsa kike wannan sana'ar ba. Shiyasa ya dauki wannan k'azamin matakin.
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Yau na ga lukutar tsiya ni Hadiza."
Ta fa'da cikin kad'uwa.
Na fara kuka sosai, ina yi, ina cire mata. Ai kuwa ina gamawa ta ja ni jikinta ta
mak'ure ta rufe ni da duka tana cewa "wanne irin shak'iyanci kike yi masa da ya
janyo miki wannan d'anyen hukuncin. Shin baki da makusanta da suke fa'da miki
gaskiya ne? Kowa ya kalle shi yasan yana tsananin son ki. Me kike yi masa?"
Dama so nake na yi kukan sosai, ko na samu sau'kin zugin da kirjina yake yi mini.
Dan hakan na bu'de baki na dinga canyara ihu. Ita kuwa sai dukana take tamkar ita
din Gwaggo ce.
Sai kuma ya fito a bazame. Dan ya ga me ya sani irin wannan kukan. Ganina a hannun
Hajiyar ta matse ni tana ta mintsini na ya sanya shi ce wa "Na ha'da ki da Allah ki
bar ta haka nan Hajiya, k'yale ta"
Ai kuwa ta k'yale ni. Ya tsaya daga ba'kin k'ofar ya mika hannu ya d'auko
jallabiyarsa da take rataye. Ya yi baya, ya sanya.
Ya dawo ba'kin kofar ya ce "Darajar wannan baiwar Allah kika ci, tana gidan. Na
rantse miki da yau kin ga k'arshe taurin kai da tsiya."
Ya kalli Hajiya ya ce "Na gode sosai, amma dan Allah kada ki sake ta'ba ta. Ki yi
ha'kuri".
Yasa kai ya bar gidan gaba'daya.
Y'anmatan nan suka kasa ce wa komai amma dai gaba'daya sun shiga rud'anin al'amarin
da ya faru.
Ta tashi, ta fita tana fa'din "Zan je har gidanku na sanar wa Gwaggonki baki shirya
zaman aure ba. Gara ta sani kada rana daya ta gan ki kamar jifa kin koma gabanta.
Ke ko tunanin halin da take ciki ba kya yi? Tare da kanwar ki aka aurar da ku. Tana
zaune k'alau, amma ke kin fitini kanki kin fitine shi."
Na dinga kuka ina bata hakuri akan kada ta fa'da wa Gwaggo fishi zata yi da ni.
Da k'yar ta yarda ba zata fa'da ba.
Bayan ta ce na kira mata shi a waya.
Akan dole na kira shi. Na danna speaker.
Yana dauka sai ce wa ya yi "Bebina kin daina kukan? Ki yi ha'kuri kin ji. Ai da
nasan mutumiyar kirki ce irin haka da bazan yi hakan a gabanta ba".
Ba'kin cikinsa ya nemi kassara ni. Na mika mata wayar cikin b'acin rai.
Jin muryarta ya sanya ya shiga cikin nutsuwa sosai.
Bai bari ta ce komai ya fara bata ha'kurin abin da ya yi.
Ta ce "Tambayar ka zan yi. Baka son ta yi k'unshin ne?"
Da sauri ya ce "Ina so. Ai bazan hana ta sana'ar da ta kafu da ita ba. Amma dai
dole ta bar abin da na ce mata. Na ce kada ta kuma yi mini lalle a d'akina, ta je
ta yi a nata d'akin. Shine kawai rikicina da ita".
Ta ce "To shike nan. Magana ta k'are."
Ta kashe wayar ta murd'e mini kunne tare da ce wa "Dama can dakinsa ne, amma kike
masa k'unshi a ciki?
Saboda ke tabbataciyar marar kunya ce?
Amma yanzu ai kin ga 'karshen tsageranci."
Ta saki kunnena ta tashi ta bud'e wadrof d'ina ta ga dukka kayana ne babu nasa ko
daya. Ta sake kai kallo ga d'akin ta ga babu alamun hula ko wani abu na miji a
ciki.
Ta daure fuska ta ce "kwanta na duba ki, wato har yanzu ke budurwa ce ko?"
Na rushe da kuka wiwi. Ina fa'din Dan Allah ki yi ha'kuri sanin da na yi ita din
mai zafi ce. Sannan ba mai wargi ba ce, y'ay'anta ma shakkarta suke yi ainun.
Ta cije ta ce "Kin san Allah sai na ga ni. Ko kuma yanzu na saka Salisu ya dauko
mini Gwaggonki tunda ni ba ni da mutunci a wajen ki."
Na sake tsananta kukana ina fa'din "Dan Allah Hajiya ki rufa mini asiri. Dama fushi
suke yi da ni. Mussaman Babanmu, ki yi hakuri. Kuma ni akan wannan ba laifina ba
ne. Na yarda na yi kuskure akan maganar d'akinsa, ba kuma zan sake maimaita wa
ba.".
Ta saki ajiyar zuciya ta ce "Shikenan na hakura. Amma na baki daga nan zuwa kwanaki
uku ki kwaso kayansa ki dawo masa da su nan.
Sannan ki kwantar da kai, ki roke shi ya baki iznin zama a d'akin tunda gidan naku
babu bishiya ko rumfa.
Ba sai na fa'da miki muhimmanci sana'ar ki ba. Komin wadatar miji neman na kai
da'di ne da shi. Zaka yi harkokinka kai-tsaye ba sai ka jira an yi maka ba. Bare ke
da kika saba yiwa iyayenki hidima a cikin sana'arki".
Ina kuka na ce"To. Domin dai na gamsu da maganganunta.
Ta sake ce wa "Ki ajiye komai ki rungumi auren ki, kowa da kaddararsa Yabi. Ke taki
ma da kyua. Tunda mijin na ki yana son ki da alama kuma yasan me yake yi tunda
soyayyar bata rufe masa ido ya sarayar da yancinsa na miji ba. Ki shiga taitayinki.
Wadanccan y'anmatan zarata kallon so da fatan ace nasu ne suke binsa da shi. Ki
ribaci damarki. Ki rike darajarki tun baki tankwabar da ita ba. Idan a yanzu da
yake neman zaman lafiya da ke, kika yarda kuka zauna, to har tsufanku ya dinga
kaffa kaffa da ke. Ban ce ba zai bata miki ba, ban ce ba zai kuntata miki ba. Amma
dai zaki samu sau'ki, zai kuma din ga shakkar ki botsare masa. Kada ki yarda ki
koya masa jure wa fishin ki Yabi".
Cikin kuka na sake ce wa "To" Wanda ban san dalilin da ya sanya na kasa daina wa
ba.
Ta nisa ta sake ce wa "Ban da ma ke din sakarya ce ai cikin hikima zaki gaje can
din. Da kin nuna masa nan ne dakinsa ai shike nan. Yanzu kuwa can din da kika raina
sai ki ga ya samu wacce zata yarda ta zauna a cikinsa. Sai dai ki ji an kawo masa
amarya."
Ba k'aramin dukana wannan maganar ta yi ba. Na k'ara sautin kukan da nake yi. Ta ce
"Sha sha a haka kamar wayayyiya amma bagidajiya ce. Baki iya komai ba sai kishi. To
wai wannan kishin na mene ne tunda ba sonsa kike yi ba? Ya auro uku mana me zai
dame ki? Na so bana gidan yau, ya tub'e ya zauna cikin mata na ga yadda zaki yi.
Kin san kuma duk masu hankali baza su sake zuwa miki ba. Marasa tunani kuwa sun
dinga zuwa, dan su k'ulla alaka da shi".
Bata bar gidan ba sai yamma lis, bayan y'an matan sun cire nasu sun tafi.
Sai bayan Isha ya dawo. Ya same ni a dakina ina kan abin sallah duk na

Please Login or Register in order to submit comment