You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yawunsu yake neman
auren y'ata ba."
Jikina ya sake daukar bari a dalilin idan na fahimci maganar Babanmu kenan zan rasa
Yaya J da kuma Abdul tashi guda, wannan shine biyu babu, kamun gafiyar b'aidu.
Na tattaro dukkan jarumta na yafa a dukkan sassan jikina da fuskata.
Na ce "Babu damuwa! Allah ya sanya alheri. Amma Baba har da Adda Nazi kenan?"
Na fa'da cike da karsashi irin na tsananin karfin hali.
Ya ce "Da ita Yabi, sai dai bana jin za'a yi tariya da ita, domin ban mallaki komai
na aurenta ba, tunda titsiye aka yi mini."
Na kalli dukkan yaran gidanmu masu hankalin suna wajen hatta Yaya Musa kuwa.
Hawaye ya b'alle mini na ce "A a Babanmu da ikon Ubangiji a ranar zata tare.
Na kalli Yaya Salamatu na ce "Yaya"
Sai kuma na fashe kuka sosai.
Dukkansu matan sai suka taya ni kukan in ban da Yaya Ummi da take Jin zafin yadda
nake damuwa da lamarinsu
alhalin ita ma ba sonta suke yi ba in aka dauke Naziran.
Da rauni Yaya Salamatu ta ce "su uku sun kawo dubu sha biyar biyar, yan dakinsu
kenan.
Sai ummi ta kawo dubu biyar, Ni kuma na bayar da ashirin maigidana kuma ya bada
buhun masara da na shinkafa ayi hidimar biki da su".
Su Salisu kuwa sun ha'da hamsin a tsakaninsu dan haka dari da ashirin ne a k'asa
kacal".
Nan da nan na zaro magana tamkar babbar mace na ce "Ai kuwa sun isa Yaya, kuje ku
siyo mata katifa da labule da ledar tsakar daki.
Na kunce hannun zanina na kunce na fito da kudi kimanin dubu sha bakwai da dari
takwas.
Na ce ga nawa a siya mata bargo da zanin gado. Su Mama ku fito da kwanuka da
tukunya.
A kai ta a hakan da ikon Ubangiji watarana sai ta yiwa wani kayan daki na alfarma,
ai duniya ce mai rawar y'an mata na gaba ya koma baya".
Hatta Mama a wannan ranar na ga kallon sassauci da adalci take yi mini, domin da ta
ga na sake dauko bankina na mik'a wa Nazira na ce "Ki fasa ki yi dinkin fitar biki
nasan zasu ishe ki tunda kinsan mu din masu k'aramin karfi ne, masu nema a wajen
Àllah."
A fili take fa'din "Yabi da Nazira sai Allah".
Baba kuwa zuba mini ido ya yi, tsawon lokaci kafin hawaye ya goce masa.
Duk muka ha'du aka yi ta kuka tamkar an ce ya mutu ne.
Domin ita kanta Mama da take ha'da kai da matan su Baban Tsakiya suna sake tsananta
mana, ta sha mamaki da ta ga suna yiwa ya'yansu hidimar aure basu yi kara sun saka
da Nazira ba.
Wata'kila a haukanta zasu yi ko saboda da ita.
Da rawar murya Baba ya ke fa'din "Allah ka sake jefa soyayya da tausayi a tsakanin
ya'yana, Ubangiji na gode maka".
Yaya Indo ta kira Malam Yunus ta fa'da masa ku'din lefe ya bayar yadda zai iya ba
sai ya yi ba , domin kuwa muma abin da zamu iya za'a yi.
Da yake ba yaro bane ainun, sai ya gamsu ya ce zai yi mata lefen yadda ya sauwaka,
sannan zai bawa Yaya Salisu ku'din da ya sauwaka shi mutunci ya gani dan haka komai
zai yi.
Ba wanda ya san me ake ciki domin kowa ya zuba ido yana jira aje ganin dakunan
amare
Yayin da ta bangarena nake ta danne damuwar auren da Yaya J zai yi da Maijidda.
Ita ka'dai ce amaryar da bata da kuzari a dalilin babu ha'din kai ko zumudin ango,
komai sai dai mahaifinta ko na angon su yi mata.
Gefe guda kuma Nasiba ta susuce domin ba karamin son Bulkachuwa take yi ba, wanda
aka ce ya fito kuma a dangin Babanta sun ce bai shirya ba sai bad'i.
Bulkachuwa kuwa yarinyar da suke takaddama ta haihu an yi gwajin halittar dan Adam
bashi da alaka da jaririn.
Sai dai an yi masa hukuncin bulala tamanin tunda ya amsa da bakinsa ya ta'ba
takarta.
Wannan lamarin, da bulalar ya yi matu'kar sururuta shi.
Ya zama abin tausayi, duk wani iyashegensa ya zubar da rabi.
Kowa ya ganshi sai ya tausaya masa.
Hatta ni da bama ga maciji sai da na yi masa jaje. cike da alhini, ya dinga fa'din
na gode "Asiya Toro, ki yafe mini, a duk sadda na tuna addu'ar da kika yi mini
cikin fishi da kika ce sai na hadu da sharrin mace, sai na ce ashe dai Asiya bayan
samun tallafin dan aljani yayin fa'da, har baki idan kika yiwa banu adam sai sun
taimake ki, ya zama wajabat. Shiyasa na k'udire zan roke ki, ki mini addu'a na zama
yadda mutane na gari suke".
Na girgiza kai na wuce shi "Ina cewa "Allah ya shirye ka Tijjani".
Ya d'aga murya ya ce "Da biyu kika yi wannan addu'a domin da zuciyarki fes take da
ni Yaya Tijjani zaki ce".
Ban tsaya ba, bare na tanka shi, a zuciyata kuwa ina fa'din mashiririci, ba sauya
wa zaka yi ba, borin kunya ne kawai, ka zubar da mutuncinka a idon kannenka da
iyayenka, Allah ya shirye ka kawai.
Shikenan sai na dawo gida, muna ta shirin bikin Nazira. Auren da ya zo tamkar dirar
mikiya, ya yi matu'kar rage mini tashin hankalin da nake ciki.
Kitso da lalle nake yi babu hutu, tun safe idan na zauna sai magariba, sallah kawai
take tayar da ni.
Haka nake mika ku'din ga Baba ina fa'din "A dinga siyan kayan cefanen biki Baba"
Da farin-ciki yake fa'din "Madallah da Yabi Asiya".
Kallo daya za'a mini a gane ina cikin tasku kawai boye wa nake yi, sannan son
Babanmu ya fita kunya da tozarta da ake son ya yi, ya danne wanccan damuwar.
Domin yadda nake kishin Babanmu da yan k'ofarmu bana jin anan kusa za'a samu mai
yin hakan.
Shiyasa na cire son jiki, da lalaci nake sana'a, Ubangiji kuma ya haska, ya saka
mini hannu, domin a rana ina hada dubu shida zuwa bakwai, mussamna idan kwanakin da
ake yin biki ne. Da ce a birnin Kano nake yarfa kunshin nan ai da ku'di masu nauyi
zan dinga ha'da wa, amma hakan ma na gode sosai, tunda mafi yawa manyan mata idan
sun zo basa bayar da iya ku'din sai sun mini k'ari.
Bana kuma jin k'yashin na bayar da komai dan mu yi hidimar mu cikin rufin asiri.
Duk yadda Yaya J yake son mu ha'du na rufe kofofin da zasu sa mu kebe.
Ranar litinin dukkanmu muna wajen Dada.
Ana ta hira, na yi lakwas a dalilin bani da kuzari, ba k'aramin cizona auren J da
Maijidda yake yi ba, har addu'a nake yi kada a wayi gari aga zuciyata ta buga a
dalilin ba'kin ciki.
Kwana nake yi ina kuka, ina kalubalantar wannan hukuncin da aka zartar mini tare da
tsanar Baban Tsakiya da Baban Kasuwa.
Tabbas a idona su din ba kowa bane face mutane masu son kai kuma y'an jari hujja.
Dada sai farin-ciki take zata aurar da jikokinta kusan goma.
Ta kalle ni ta ce ",Ke da Nasiba ne aurenku ya yi gardama, ga shi kune fitanannu."
Ban kula ta ba domin abin da yake zuciyata fadinsa da ciwonsa sai ni da
mahaliccina.
Balle Nasiba da ta bari halin da take ciki ya bayyana a komai na ta.
Ni mamakin da take bani wai akan Bulkachuwa take wannan ba'kin cikin, sannan abin
kaicon shi bai ce yana sonta ba, kawai ya lura da yadda take mararinsa sai yake
amfani da hakan yana sata tana yi masa bauta.
Misali komin dare zai kawo indomie ya ce ta dafa masa, ko kuma ya ce ta dafa masa
ruwan wanka, ko shayi.
Haka idan zai fita zai bata mukullin dakinsa ta je ta gyara masa.
Bai zame masa komai ba, ya kawo mata kayansa matu'kar zai ga tana wanki, yana
fa'din "Ga karo".
Bata damuwa hakan zata karba, ta wanke, ta goge.
Shi kenan sai yake sassauta mata ya daina yarfa ta.
Ita kuma ta dauki son duniya ta d'ora masa bata ko lura da rashin nagartarsa, duk
kuma wanda zai zo da nufin yana sonta bata sauararansa, sai Dada ta yi mata wuta
wuta. Matu'kar kuwa yana gida ba zata yarda ta fita ba, duk tijarar Dada kuwa.
Tunda mahaifiyarta ta ce bai cancanci a bashi aurenta ba, ya dauke mata wuta, ya
daina kula ta, ya koma muzurai ne a tsakaninsu shi kenan sai ta k'aratanwa kanta
walwala, tunda ba yadda bata yi ba, ya fahimce ta shi kuma ya taurare.
Saura kwanaki biyu aure domin tuni gidan ya fara cika da jama'a ana ta hidima tuni
an yi wa amare jere.
Da ni aka je jeren Adda Nazi, na dinga k'walla a dalilin irin rufin asirin da
Ubangiji ya yi mana.
Komai ya yi, ba wanda ya zaci za'a samu hakan.
Na dawo Yaya J ya rutsa ni a soro.
Murya a dushe ya ce "Yabi mene ne ya yi zafi ne, shin gaba zamu yi?"
Da sauri na ce "Eh mu yi gabar kawai, yafi mini sauki da na saurare ka."
Ya numfasa ya ce "Oh no! Kada ki yi mini hakan, ya miko mini leda mai dan dama.
Na dauke kai na ce "Bana bukatar komai na ka".
Ya rausayar da kai ya ce "saboda zumunci na baki fah".
Na ce "To kuwa bana so, domin na shafe alakar da ta ha'damu".
Ya fusata, sai kuma ya ha'diye dukkan fishin ya ce "To karbi dan Allah, dan
soyayyar da nake yi miki".
Na mika hannu na kar'ba ba tare da na ce uffan ba.
Ya sassauta ya ce "Wannan auren ba zabina ba ne Yabi, ba abin da zuciyata ta za'ba
mini ba ne. Dan haka zan yiwa kaina auren da zuciyata take so take kuma muradi.
Na rok'e ki, kada ki juya mini baya. Kada ki haramta mini farin ciki a zuciyata da
rayuwata."
Yana diga aya sai kawai na rushe masa da kuka mai tsananin gaske.
Fadi nake "Lallai kuwa wato zan yi ta zaman jiran ka ko?
To ko dai kallon Yabin mahaukata kake mini ba ta Marina ba?"
Ya ki'dima ya ce "me ya kawo wannan maganar?
To ai ni ko a turu nake kallon ki ra'ayil aini, zan cigaba da son ki babu gazawa,
cikin kowanne hali son ki nake yi, zan kuma cigaba da son ki YABIN J".
Na ha'diye kukan da nake yi.
Na zuba masa ido na ce "Na gode da soyayyar ka, Allah ya bada lada".
Kafin ya yi magana Bulkachuwa ya shigo, ya kalle mu kamar ba zai yi magana ba, sai
kuma ya kasa ha'diye maganar ya ce "Poor baby haka kawai kin zuba ido an k'wace
miki abin da yake na ki ne, ni fa akan abin da nake so sai dai ayi kare jini, biri
jini da ni."
Ya kalli J ya ce "Jabir ka daina tare yarinyar nan tunda dai an baka wata ka karba,
bar ta ta ji da suyar da kirijinta yake yi mata kawai".
Yaya J ya daure fuska ya ce "Menene hakan kuma Bulkachuwa?"
Ai kuwa ya ce "Gaskiya ce mana Jabir, ni yanzu da aka hana ni Nasiba ka ga na damu
ne?
Ai saboda dama soyayyar ba mai karfi ainun ba ce.
Da son ya zama so deep da komai zai faru, ba zan yarda na musanya ta da wata ba".

*Dukkan littafan Saliha Abubakar Abdullah Zaria akwai su in soft copies a hannuna.*

Takaicinsa ya shake Yaya J. Ya nuna shi da yatsa ya ce "Bana son irin haka
Bulkachuwa".
Ya make kafa'da alamun ko oho ya wuce yana sake fa'din "Ato ai gaskiyar magana
kenan, ku barta ta ji da bacin ran da take ciki mana, ai kowa yasan tana sonka,
akan idonta da na iyayenta aka dauki wata aka baka, ka karba da sunan biyayya, amma
ka kasa gwada kwanjin ayi maka alfarmar ka ha'de su biyun ka yi wuf da su.
Sai kuma ka dinga tare ta kana tayar mata da hankali a wofi. Ita ma k'uruciya ce ya
sanya take zubar da hawaye akan ka.
Ni yanzu da na fahimci inda aka ajiye ni, na sake yiwa Nasiba kallon soyayya ne?
Duk nacin ta bana sauraron ta".
Daga haka ya fice gaba'daya.
Yayin da Ba'kin ciki mai tsananin gaske ya dabaibaye Yaya J.
Ya ce "Ban da ma idon ka babu kunya Bulkachuwa har ka iya tsayawa ka ce zaka fa'da
wa wani dai-dai?
Ina ka santa, ai kanka zaka fara yiwa bitar gaskiyar kafin wani, wanda tsoron Allah
baya iya hana shi aikata kaba'ira, shine zai yi kishin ana bata wa wata lokaci, kai
kuma *BAK'AR TA'ADAR* lalata y'ay'an jama'ar da kake yi fa?
Ko an ce maka daga sama suka fad'o babu mai kishinsu?"


*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*


✍️
*BAKAR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS M.I.NASHE)*

*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}```
✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAYAN G.H.T.* *DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA*.
*HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*07039269802*

*Follow me @Arewa books*
https://arewabooks.com/chapter?id=6504c04660ef31f52af5ad6c

*VIP 1k*
*Regular 500 via*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*08032773332*.
*Free pages na daf da tsinke wa*
*Ku zo ku shiga tafiyar Yabi. Sa'adan Mk da Guduyon Gudale tuni suna cikin paid
group*.

15&16.
Bulkachuwa ya juyo ya ce "Tir da masu gori, Albarkar Annabi ba zaka samu Asiya Toro
ba, tunda kallon kitse nake yiwa rogo, marar mutunci kawai".
Ya juya ya yi tafiyarsa a tunzure.
Ya juyo da nufin yi mini magana sai kawai na d'aga masa hannu na ce "Kada ka ce
mini komai Yaya J.
Wannan maganar fa, gaskiya ce tsagwaro.
Na roki arzikin ka bar ni na ji da damuwata".
Na juya na tafi.
Na bar shi yana fa'din "Kaicon Bulkachuwa, ko har yaushe yasan mutuncin gaskiyar da
har yake wannan zugar?"
Ina shiga d'akin Gwaggo na zube na fashe da kukan da ya ja hankalinta k'warai da
gaske.
Ta jani jikinta ta ce "To mene ne kuma?
Kin yi k'ok'ari, kin yi ha'kuri, sake daure wa mana, komai zai wuce fa".
Na saka hannuna na rike ta sosai, baki na rawa na ce "Yi mini addu'a Gwaggo, ki
yafe mini bacin ran da na yi ta sanya ki.
Ina jin mutuwa zan yi."
"Ba zaki mutu ba Yabi.
In sha Allah! Ubangiji ba zai bar ki hakan ba, ai yasan an zalunce ki, amma daure
ki cigaba da nuna jarumta, ki cigaba da sha'aninki tamkar baki da wata damuwa."
Na ce "Abin ne yake neman fin k'arfina".
Na fa'da, kuka na sake kwace mini.
Ta dinga bubbuga bayana tana fa'din "yadda aka yi din ne akwai tozarci a ciki, amma
ni dama bana son wannan ha'din domin tsananin da zaki fuskanta mai girma ne. Allah
ya sa haka ne mafi alheri.
Share hawayenki ki d'oro alwallah ki yi ta nafila tunda hantsi ne yanzu."
Na kuwa mike ina share idon nawa, na fita da zummar yin alwallah.
Na dawo na tarar da ita, tana ganin kayan da suke cikin ledar.
Leshi mai kyau, da mayafin da ya dace da shi, da doguwar riga abaya, da takalmi da
jakarsa, sai tarkacen sark'a da abin hannu ga kayan kwalliya da turaruka.
Da envelope mai dauke da wasika da kudin dinki.
Gwaggo ta ce "Wannan kaya masu daraja haka? Ajiye wa za'a yi sai Babanku ya ga ni".
Na tayar da sallah ban ce komai ba.

Mama da zata dafawa Nazira kazar aure har da Maijidda ta hada ta dafawa.
Ina kallo yadda ta samo tattabaru ta hada da saiwowi ta sake dafa musu. Haka Gwaggo
ta maze kamar bata gane ba.
*Mai bukatar saiwowin dahuwar kaza ko na tattabaru da sauran kaya na mussaman ta
mini magana akan lambata 08032773332*.
Ina ji, ina ga ni aka daura auren Yaya J d'ina, da Maijidda.
A ranar kam buya na yi, a makwabta na yi kukan da ban ta'ba yin irinsa ba.
Na dinga jin wani irin abu tamkar zai fasa mini zuciya gaba'daya.
Fa'di nake "Ya Allah! Ya Allah".
Idan na tuna nagarta da sanyin halinsa sai na ga ba karamar asara na tafka ba,
wacce na saddakar ba zan mayar da irinta ba.
Har dare ba wanda yasan inda nake, sai da na ji dirin isowar motar daukan amare
sannan na fito.
Dan ba zai yiwu ace ban raka Nazira d'akinta ba.
Da na fahimci Nazira za'a fara kai wa domin motocin kai ta ne suka fara iso wa sai
kawai na fa'da daya daga cikin motocin.
Sai a dakinta muka ha'du.
Duk yadda ta ke lullube a cikin mayafi said da ta riko hannuna ta ri'ke gam tana
sake kankame shi tabbacin farin-cikin da take ciki bai sa ta manta tawa damuwar ba.
Sai da kowa ya watse aka bar ni da ita, domin dai bamu da wasu kawayen da zasu kai
mana dogon dare.
Ta kalle ni ta ce "Mu yi ha'kuri Yabi, kara daure wa, idan muna ganin ki a hakan ba
wanda zai samu sukuni. Kinga ma yunwa nake ji, tun jiya da muka ci abinci ban sake
saka komai a bakina ba, ba wanda hankalinsa ya kai a bawa amarya abinci, na sani da
kina kusa da ni da kin bani".
Na ce "Afuwan Adda Nazi, amma ai yanzun nan Malam Yunus zai shayar da ke nama da
madara".
Ta galla mini harara tare da fa'din aku sarkin magana".
Na mike domin na ji ana fa'din mai motar ya dawo.
Da k'yar ta bar ni na tafi, tana kuka, ina yi.
Kwanaki ukun da suka biyo bayan bikinsu Yaya J sun fi ko wanne tsauri a gare ni.
Sa'ar da na yi ma ba a gidan aka yi masa gini ba, a can bayan gari ne da kansa ya
gina abinsa sai dai da tallafin Baban Tsakiya.
K'aramin gida mai fasali na ban sha'awa, ba burin da banci akan wannan gidan ba. Ko
bandakin gidanmu da yake sani takaici, da zarar na tuno bandakina a cikin daki yake
a gidan Yaya J sai komai ya wanke mini, na yi ta zumudin zuwan lokacin da zamu yi
aure, ashe dai wasikar jaki nake tsara wa.
Tayals a ko ina, ga furanni har da fasadabir ya shuka mini, ga bishiyar mangawaro
da ni na bayar da kwallon ya shuka, ita ma ta kama sosai.
Amma tashi guda aka ruguza mini komai, Maijidda na cikinsa an kuma sake kawata mata
gidan da kayan alfarma domin takanas aka tafi Jos aka siyo mata furnitures, ko
yaran Baban Tsakiya su Firdausi basu samu gatan ta ba.
Haka na dinga rama tamkar ku'din guzuri.
Ban samu sassauci ba sai da aka doshi kwanaki ashirin da auren a dalilin na koma
zuwa makarantar boko mun shiga aji shida.
Da k'yar Dada ta bari muka koma.
Gaba'daya na zama shiru shiru, idan ba kure ni aka yi ba, na daina fa'da, ko yara
na gani sai dai na rabasu na yi musu sulhu. Amma na daina rama wa wani duka, bare
ni na doku da kaina.
Duk da yadda na canja ba yaron da yake kuka sabo da ni, ban tsira a wajen mutan
Gidanmu ba. Gaisuwata da kyar Baffanina suke amsa wa. Na rasa laifina, zamu gansu
tare da Nasiba mu gaishe su, su amsa ta ta gaisuwar cikin walwala har suna ambaton
sunan ta amma ban da ni.
Na fa'dawa Gwaggo ta ce "Na cigaba da gaishe su kada na gaji suna da hakkin na
mutuntatasu.
A sanyaye na ce "Gwaggo ni bani da hakkin su sakar mini fuska su mua'amalance ni da
mutunci tunda jininsu ce ba agola ba?
Nasiba fa ba yar gidan nan ba ce, amma ace ta fini a wajensu?"
A duk sadda na yi mata wannan k'orafin dauke kai take yi ta ce "To ai laifukan da
kika yi musu ne, da yawa, sannan ita Nasiba ko ba y'ar gidan ba ce amma tana da
wata alfarma tunda a ko ina ana son y'ay'an da yar'uwa mace ta haifa, ke ma ai har
da halin ki ya sanya suke yi miki hakan".
Idan ta fa'di hakan sai kawai na kalle ta na yi shiru, domin na sani ta fa'da ne
dan kawai na fahimci girmansu. Ba dan suna yi mini adalci ba.
Har sati uku sannan na warware na rungumi zuwa makaranta duk da karatun ma sai a
hankali saboda kewar Nazira na damuna.
Dada kuwa fa'di take na fito da miji domin wanda za'a bawa Nasiba ya ce "Kowanne
lokaci zai iya gama gidansa ba sai bad'i ba, ita kuwa ranar auren Nasiba ita ce
rana ta, ko na fito da miji, ko a bani Malam Nata'ala shine damo sarkin ha'kurin da
zai jure wa dukkan iya shegena.
Malam Nata'ala dattijo ne da yake zaune a unguwarmu mutumin kirki ne kwarai da
gaske matansa biyu da yara da dama, tsanagaya ce da shi ma'ana Malami ne mai
almajirai.
Ban wani dauki maganarsa da Dada ta ambata da muhimmanci ba, illah k'anzon kurege.
Kwanci tashi asarar mai rai har aka cinye kwanakin wata da auren su Nazira.
Har lokacin kuma ban yarda na je gidanta ba duk nacin aikar da take akan tana nema
na.
Ikilima ce take zuwa akai akai duk sadda ta je kuma akwai abin da zata bata ta kawo
mini na ci ko na sha.
Ga wasiku birjik tunda bani da waya duk da an kawo mini har uku amma Baban Marina
ya ce "Baya son mu ri'ke waya.
Duk yadda Yaya J yake nacin mu hadu gaba'daya na tsike zuciyata, domin yanzu
haushinsa nake ji ba ka'dan ba.
Kan dole ya koma makaranta tunda ya kammala sawes din da yake yi a Jos.
Ina cikin wannan yanayin da na cire komai a raina nake iyakacin bakin kokarina
wajen mayar da hankali a karatuna, sai dai ba wani fahimta nake sosai ba.
Na dai yi sa'a zan iya karatu da rubutu.
Na gama fahimtar ni din basirata a wajen kirkirar abin ado ne, misali idan na samu
kan mace mai gashi zan b'ata lokaci na yarfa mata kitson da kowa sai ya ce "wow".
Haka kuma duk gunjin gashi sai na kitse shi, zana adon lalle kuwa tamkar wanda aka
bu'de mini ido.
To yanzu da nake sake koyon kwalliyar da ake ya yi, ban jima da fara koyo ba amma
har hannuna ya fara fa'da wa.
Dan haka na daina takura wa kaina sai dai ina ta kokari dan na samu na ci jarabawar
kammala sakandire.
Ranar asabar tun safe nake ta murnar zan je gidan Nazira, tunda muka zo duniya bamu
ta'ba rabuwa na lokaci mai yawa haka ba.
Mutum uku kawai na yarda zan yi wa kitso, duk masu zuwa lalle kuwa ha'kuri nake
basu, sai d'aya da take unguwar Nazira, layinsu d'aya domin Naziran ce ta turo mini
ita.
Dan haka na saka mata lallen a gurguje na barta da nufin ta same ni gidan Naziran
na yi mata kitso a can.
Da murna nake komai domin Allah ya sani ina son Nazira, ina samun farin-ciki idan
ina tare da ita.
Har Malaminmu na tarar yana dakon iso wa ta, ga abinci an shirya mini tamkar wata
babbar bak'uwa ta mussaman.
Spaghetti ce da miyar kifi, saboda ita ce favorite dina.
Ga kuma zobo ya sha ha'di an fasa masa k'ank'ara, gefe kuma babbar kula ce shake da
pure water da aka jefa masa k'ank'ara yini guda aka yi mini tanadinsa.
Da farin-ciki yake taya amaryarsa marabta ta.
Ta rungume ni tana k'walla da mitar ashe zan iya yin watsi da ita na tsawon wannan
lokacin?
Da dariya na ce "Babanmu ne ya ce "Ba zan dinga yi miki sintiri a gida ba".
Malam Yunus ya ce "Ba wani sintiri idan kin so ma ki tattaro kayanki ni bazan gaza
ba".
Na yi dariya ina fa'din "Na gode da karamci, Allah ya sanya alheri".
Ya fice ya barmu tare da cewa "Ameen Asiya".
Tunda muka zauna hira muke yi, ba a gama wani zancen ba za'a sake, a kama wani.
Na bata labarin yadda muka yi da Dada akan Malam Nata'ala.
Ta dinga dariya tana tintsira wa tamkar ta samu tab'i.
K'wallar dariya a idonta ta ce "Lallai ma tsohuwar nan, ke ce za'a bawa wannan
tsohon?"
Na taya ta dariya tare da cewa "To ba namiji ba ne? Kuma ai ta ga ya dace da ni ne,
tunda ana kore mini duk wanda ya zo da niyyar aure na".
Ta yi shiru ta ce "Kawai lokacin yin auren ne da saura, amma ba dai Alaramma ba."
Muka shiga hirar duniya, muka ci abinci, muna santi a fili na ce "Na ji da'din
ganinki Addah Nazi, Allah ya kara miki kwanciyar hankali, ya kawo zuri'a dayyiba".
Ta ce "Ameen Yabi! Yanzu addu'ata mafi yawa taki ce Àllah ya kawo miki miji na
gari".
Na yi shiru.
Ta ce"Baki amsa ba?".
Idona ya cika dam da ruwa na ce "Baban Tsakiya ya lashi takobin duk wanda ya zo sai
ya b'ata ni, ya fa'di munanan dabi'una kin ga kuwa aure ai zai yi mini wuya tunda
kanin mahaifina ne yake fa'din munanan kalami a kaina."
Ta yi shiru sai kuma ta ce ",Ba abin da yafi k'arfin addu'a Yabi! Fa'da kawai yake
yi ba zai yi hakan ba".
Na hade fuska na ce "bana son haka, wanne irin zance kike yi?
Kema kin san gaskiya, zai yi abin da yafi haka in dai Alle Badamasi ne"
Dariya ta subuce wa Nazira ainun, tana yi tana nuna ni da yatsa tare da ce

Please Login or Register in order to submit comment