You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma ina.
Ya mini kamun kazar kuku. Duk fizge fizgen da nake yi bai kula ba. Sai da ya
dangana ni da katifar. Ya bini ya mini rumfa da jikinsa. Karshe ma ya sakar mini
nauyinsa ta hanyar danne ni. Na daure na ki na nuna na kosa.
Ya bini da kisses da sauran al-amura masu nauyi.
Tun ina dauriyar kin karbar rarrashin nasa har na kasa jure wa na fara karba ta
hanyar sakar masa jiki da daina ture shi. Sai da ya gama jagwalgwala ni, sannan ya
kankance murya ya ce "Da gaske ba kya sona Asiyaty?"
Na dauke kai ina jin kunya na kama ni. Domin ni kad'ai nasan yadda nake jin sa a
zuciyata. Kawai wulakancinsa ne yake neman kwantar da ni.
Sai da yasan yadda ya yi muka shirya, ya zangwanyar da fishin da na yi.
Bayan ya jaddada mini, ba abin da yake so nan duniya sama da ni.
Cikin saa'a bai mini zancen mutuwa ba.
Bamu yi barci ba, a wannan dare, domin ko da muka samu nutsuwa. Maganganu muka
cigaba da tattauna wa. Haka ya dinga bani hak'uri tare da rokon na daina yi masa
irin wannan fishin mai tsanani. Na daina damun kaina ta hanyar kaurace wa abinci da
kuma walwala.
Sai da muka karya, muka shirya sannan muka dauki hanyar Bulkachuwa.
Da k'yar Babah ta sauraremu. Mun shafe fiye da awa ban da sallamarmu bata sake
kallon inda muke ba. Harkokokin ta take yi ita da su Hanif. Su kawai ta bawa ruwa
da abinci, mu kuwa ko kallon inda muke bata sake yi ba.
Ni na fara yin kundubalar bin ta daki. Yayin da ya biyo bayana, amma ya toge a
bakin k'ofar tabbacin jiya bai ji da dad'i a hannunta ba. Na zauna a gefenta. Na
lankwasa harshe na ce ",Dan Allah Babah ki yafe mana. Idan ba ki huce ba, ba zamu
ga haske ba. Kuma tun jiyan ma mun sasanta kanmu."
Sai lokacin ta bude baki ta ce "To ni kuma ina ruwana da al'amarinku? Ni da kika
ganni bana shiga kasafin da babu mutunci a cikinsa. A gabana ki zagi mijin ki
Yabi?" A sanyaye na ce "Ban zage shi ba Babah". Ta ce "Kalmar da kika fada masa ai
zagi ne
Na yi shiru. Ta dinga yi mini fad'a
tamkar zata doke ni. Ganin ta tsananta ya sanya na ce ",Babah Wallahi ni kad'ai
nasan kuttun da yake cusa mini. Yanzu ba dama ya dawo ya zauna mu yi hira, sai dai
ya yi da wayarsa, na sani kuma da y'anmata yake yin hirar ni ya bar ni gaho. A Kano
kuwa da kunnena na ji yana zancen zai tura gidansu".
Ta ce "Akan me ba zai yi aure ba? Akan ki zata zauna, me ce a cikin kishiya ne da
kika tsananta wa kanki k'in ta. Allah ya ce su yi mataye sama da d'aya idan zasu
iya adalci. An janye ayar ne, ko kuwa rushe ta zaki yi, ki kafirta?"
Tana rufe baki na rushe da kuka ina fad'in "Kin bi bayansa ya yi mini kishiya ko
Babah?"
Ta janyo mafici ta shiga kwada mini tana fad'in "Na bi bayan nasa sakarya. To hakan
da kike yi masa ne zai hana shi k'ara auren. Tun yanzu kin tattara kin bar shi,
idan ta zo ba sai ta karbe shi gabad'aya ba."
Cikin kuka sosai na ce "Babah na rantse da Nasiba yake soyayya. Ya auro kowa amma
ban da ita. Ni Wallahi bazan yi kishi da ita ba. Mutuwa zan yi, idan kuwa ban mutu
ba, daga ranar da ya aure ta. Billahi a ranar na haramta gare shi!"
Na fada cikin matsanancin kuka.
Ta saki maficin hannunta ta ruko hannuna ta ce "Ni ma matukar bai nisance ta ba
Wallahi sai dai ya nemi wata uwar. Na yafe shi. Share hawayen ki har abada ba zaki
yi kishi da ita ba. Na miki wannan alk:awarin".
Ya shigo a sanyaye ya durkusa a gabanta ya ce "Ki tsananta yi mini addu'a. Ban san
me yasa nake jin ina zakuwa akan lamarinta ba. Idan na je wajenta kwata kwata bana
jin sukuni dan tsananin takurar da nake shiga. Ko ganin ta bana son yi. Amma da
zarar na taho kuma sai na ji zuciyata tana azalzalar na koma Toro dan na ganta. Ku
mini addu'a, ku mini uzziri dan girman Allah. Wallahi addu'ar da nake yi ne ma take
saisaita mini al-amurana, amma abubuwan da suka sha kaina masu tsanani ne. Ku
taimake ni, kune mafi kusa da ni a yanzu."
"Tirkashi"
Babah ta furta a fili domin ta fahimci ba haka aka bar shi ba tabbas.
Ta nisa ta ce "Allah mun tuba, Allah kada kasa shaid'an ya yi galabar tsinka
siriryar igiyar zumucin gidan marina da ta yi saura."
Kukana ya tsaya cak a dalilin yadda na ga Babah ta tsorata da furucinsa ainun.
Yayin da zuciyata ta shiga zullimi sosai. Ke nan Tijjani da gaske yana burin auren
Nasiba.
Wani irin k'ullutu mai ciwo ya tokare ni.
A matukar sanyaye take fad'in "Zan dage da addu'a, kai ma ka dage da addu'ar da
kuma danne yadda kake ji akan lamarinta. Sannan ka saka a ranka ba matar ka ba ce,
domin matukar ina raye ba zaka had'a su ba, kai gabadaya ne ma ba zaka aure ta ba.
Dalilin da ya hana a baka ita a farko, shine dalilin da yasa ba zaka zama mijinta
ba a yanzu"
Ta juyo gare ni ta tausasa harshe ta ce "ki yi hakuri kin ji Yabi. Yana cikin canka
cakare. Ki tallafe shi har ya tsallake wannan siradin. Mutanan yau da yawansu
mugaye ne, zuciyarsu cike take da gilli mai yawa."
Na kasa ce wa komai domin na kidime, idan har Tijjani da yake kawaici a gaban Babah
zai bude baki ya ce yana zakuwa akan lamarinta a gabanta to lah shakka abin da yake
ji babba ne.
Hawaye ya dinga tsere a fuskata. Tabbas ina cikin tashin hankali. Bana jin tsoron
karawa kishi da ko wacce mace, domin na yi imani namiji baya zama da wacce baya so.
Idan kishiya ta kere ka a wani fanni to kai ma da ikon Ubangiji sai ka samu fannin
da zaka kere ta. Abu biyu ya dame ni. Nasiba suntumemiyar halitta ce irin matan da
suke birge Bulkachuwa. Sannan mahaifiyarta kowa yasan bata barin mazanta haka, a
hannunta suke, ko marigayi mijin Nasiba kullum a yunkurin mallake mata shi ta ke.
Na tabbatar Tijjani ma za'a yi komai dan ta sha gabana, tunda a yanzu ma da bai
aure ta ba idan ta gan ni kamar ta doke ni haka take ji. Da k'yar Babah ta shawo
kaina na samu nutsuwa, na daina kuka.
Sai yamma muka baro Bulkachuwa. Dan haka sai dare muka iso.
Na daure na yi k'arfin zuciya ban cigaba da share shi ba. Na rungume shi da hannu
biyu muka cigaba da zama lafiya. Duk dare kuma sai ya fita waje ya yi waya. Idan
kuma yana gida baya amsa waya matukar bata shafi kasuwancinsa ba. Asalima kamar ya
dakatar da a a kira shi idan yana gida ne. Da kaina na fahimci da gaske ya canja,
wulakancin yin waya idan yana gida yanzu ya daina, asalima kaffa kaffa yake kada na
tuntsire masa.

*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin
register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*.

Yayin da ni kuma na tsananta addu'ar Ubangiji ya tsaremu akan duk abin da ake nufi
da mu na sharri. Sa'a d'aya har yau Tijjani bai bar sallar dare ba. Yana wahalar
gaske ya kwanta bai tashi ya yi nafila ba. Kullum kuma a cikin addu'ar duk kaddarar
da zata hau kansa ta zama mai sassauci daga Ubangiji.
Na sani asiri zai kama shi, amma na yi imani zai zo da sauki tunda wadatar da ya
samu bata sanya ya bar Allah ko ya koma BAK'AR TA'ADAR neman matan da ya yi a baya
ba.
Na kira gwaggo na fada mata komai na roki ta tsananta yi mini addu'a.
Cikin rarrashi ta ce "Ina yi miki Yabi. Zan kuma ninka addu'ar da ne yi miki. Abin
da zan fad'a miki shine ki barwa Allah ya yi miki zabi, ba wai ke ki yanke hukuncin
idan ya aure ta kin bar shi ba. Allah ne ya halasta dan haka akwai bukatar ki
nutsu, kada ki bari Ubangiji ya bar ki da dabarar ki."
Da kuka na ce ",To Gwaggo".
Cikin rauni ta ce "Allah ya yi miki albarka ya shiga tsakanin ki da duk abin da zai
birkita miki auren ki. Da ikon Allah ba za'a kai ki k'asa ba. Kin yi sa'a kina
cikin albarkar uwa da uba. Dan haka ki yi ibada tuk'uru ki kuma yi barci da
minshari ba abin da zai same ki sai alheri da ke da dukkan zuriar ki Yabi".
"Na gode Gwaggo". Na furta cikin rawar murya irin ta kuka.
Sannu a hankali na samu sassauci na cire hankalina kan maganar Nasiba da Tijjani.
Iyaka dai ban daina addu'a ba, ban daina tofawa Tijjani addu'ar tsari a cikin duk
abin da zai ci ko ya sha ba.
Na rungumi zaman lafiya a tsakanina da shi. Na rungumi karatuna da y'aya'na.
Mussaman a yanzu da nake gaf da kammala N.C.E.
Twins sun girma domin suna shirin shiga shekaru shida da haihuwa. A lokacin suna
aji daya na firamari. Hanif yafi Hamim kokari domin kullum na daya yake zuwa. Amma
kuma ba shi da magana. Yayin da Hamim yake zuwa tsakanin bakwai zuwa goma. Amma
kuma ba wanda bai san shi ba, saboda suruntunsa, ya kuma yi sa'a ya iya turanci.
Kamar wanda ya girma a cikin masu yi. Surtunsa da fadansa ya sanya a ke fafatawa da
shi. Sau tari sai ya yi tsokana ko laifi a hukunta Hanif a madadinsa tunda ba'a
gane su. Shi kuma Hanif ba zai ce ba shi ba ne. Ko ni ma yana mini wannan iya
shegen. Dan haka na daina binsu a guje. Sai ya manta yana ta surtunsa kamar aku
sannan zan rik'e shi.
Duk sadda na je Toro bin mu kawai ake yi da ido ni da y'aya'na a dalilin yadda muke
fita daban muke daukar ido.
Wadanda kuma basa iya boye wa hassadarsu a fili sai da kawai na ji suna fad'in
iyalin babban direba shugaban masu kayan gwari na Bauchi gabad'aya. Ko yaushe aka
nada masa wannan mukamin?
Ni da Nasiba kuwa muna gaisawa, bama gaba sai dai babu doguwar hira. Domin idan ta
gan ni sai na ga tana d'ad'are wa bata da katabus duk da bata yi mini kallon raini
ko na izgili. Shi yasa nima nake jarumtar mu'amalantar ta da sakakkiyar fuska.
Ina kammala rubuta jarabawar karshe. Na fara hutun zirga zirgar da na shafe shekaru
uku ina yi. Hatta lalle sai da na tafi hutun wata guda a kokarina na son na dinga
yin barci yana isa ta. Da zarar na sallami twins da babansu sun fita da yake shi
yake kai su makaranta, sadda zasu tashi idan ya dawo yana gari sai ya dauko su.
Idan kuwa baya gari sai su taho da yaran bayan layinmu.
Suna fita nake rufe gida na gama abin da zan yi na karya na kwanta na yi barci,
bana tashi sai azahar.
Daidai wannan lokacin Tijjani ya k'osa na samu ciki. Har ta kai ya fara zargin ni
nake yin wani abu dan kada na sake haihuwa.
Haka kawai rannan ya tuntsire akan ba zai yadda ba. Daga haihuwa d'aya zan kulle
bakin mahaifa, to shi ba yahudu ba ne, ba kuma ba Caine ba ne da za'a kiddidge masa
yawan y'aya'n da zai haifa. Ya riga da ya gano hak'uri kawai yake yi, to yanzu kuma
ya gaji.
Na kalle shi a tausashe na ce "Ashe ba Allah ne ke kawo ciki da haihuwa ba Baban
2?"
Da kumfar baki ya ce ",Tun kafin ki zo duniya nasan da hakan Asiya. Akan me duk
abokan aurenmu haihuwarsu uku amma ke sau daya tak. Ba dan Allah ya so ya bani biyu
tashi guda, da yanzu d'aya ne jallin jal. Gaskiya ni yara da yawa nake so malama."
Na sake daure wa na ce "Allah bana shan komai ka yarda da ni".
"To akan me ina bakin kokarina ba zaki karbi cikin ba?"
Na zuba masa ido cike da fargabar ko dai ya fara afa wani abu ne. Tas
na gan shi babu alamun maye ko rashin lafiya.
Ido cikin ido na ce "Wato ma ni ce na ki karba ko?"
Fuska a daure ya ce "Eh mana. Nima ba haka kika yi ta yi mini sadda baki samu ciki
ba, ce wa kike ni ne ban yi miki ba. To nima yanzu kawai ki karba Asiya na gaji, ki
yi ciki abin da na sani, na ke kuma son ga ni ke nan".
Na yi dariya na daga hannu sama na ce "Allah kasa na samu ciki ya zauna kada ya
zube ".
Ya saki ransa ya ce "Yanzu kika nemi zaman lafiya tunda kin roki mai bayar wa. Kuma
na saka miki doka kullum ki dinga wannan addu'ar idan kin yi sallah."
Na gintse dariyar na ce "To mai sunan shehu".
Ya harare ni tare da ce wa "Kin dauki umarnina wasa ko?"
Na girgiza kai da sauri tare da ce wa "Wace ni da wasa da lamarin ka, indai ba so
kake Babah ta ce na raina miji ba".
Da haka na lallaba na shiritar da maganar, dan kuwa da na dauka da zafi rikici zamu
yi mai yawa. Tunda da gaske ya kosa na haihu kamar bamu da yara kwata kwata. Tun
wannan lokacin na tsananta addu'ar na samu ciki ya zauna. Na cigaba da zuwa ganin
likitan da na daina zuwa.
Na kuma yiwa Aisha lame maganar ta siyo mini Saiwowin maganin sanyi a wajen Surayya
08032773332.*

***
Baba Maryo ta isa gidan yar'uwarta a Bulkachuwa da la'asar lis. Babah ta karbe ta
da karamci da walwala. Har dare suna hirarsu da ta shafe su. Sai da daddare sun
kwanta. Babah a kasa ta yi shimfida yayin da kanwarta yake kan gadon.
Cikjn hirarsu ta kutso da maganar Nasiba da Tijjani.
Ta ce "Na rasa ga ne inda matsalar take, sai sun shirya ya ce zai tura gidan
iyayenta sai kuma magana ta kwanta. Sama da shekara guda yana mata yawo da hankali.
Shi bai fito ba, shi kuma ya fantsama mata mane ma".
Da madaukakin mamaki ta ce"Ban fahimce ki ba Maryo!"
Ta kuwa ce "Maganar y'ar ki da Tijjani mana. Ai gara ki yi magana da waliyyinsa a
yi komai a gama na gaji da wannan hirar tasu ba tare da an yiwa lamarin kai ba".
Babah ta sandare a zaune, ta cika k'warai da rashin kunyar kanwarta.
Amma sai ta ce "To shi ban da ma rashin tunani me zai sa ya nemi Nasiba da sunan
soyayya. Ai ita matar manya ce. Sannan ta ya ya zai hada yan'uwan jini kishi?"
A ladabce Baba Maryo ta ce "Wa ce ce Nasiba da za'a ce tafi k'arfin Tijjani? Bayan
haka zumuntar ta da Yabi ba zai hana su zama kishiyoyi ba, tunda Allah bai hana
ba."
Ba ja in ja Babah ta ce "Gaskiya ba zai yiwu ya had'a Yabi da Nasiba a matsayin
matansa ba".
Haka kawai ta fad'a Baba Maryo ta fashe da kuka tare da ce wa "Ta fifita bare akan
Nasiba".
Babah ta ka'du da furucin yar'uwarta. Ta kasa daure wa ta ce "Wacce baren na
fifta?" Ta yi tambayar da dukkan zuciyarta.
Da kuka ta ce "Yabi mana. Dama sai da na yi zargin ke ce baki d'aure gindin ya aure
ta ba, saboda kina gudun zuciyarta da ta uwatata. To komin abin dai ni ce taki ba
Asama'u ba".
A sanyaye Babah ta ce "Ni Yabi d'iyar Asama'u ce da ta zo da ita daga wani gidan ko
kuwa tare da Yaya Sani ta same ta?"
Cikin ko in kula ta ce "Shine ubanta amma ai wata ce ta haife ta. Ni kuwa fa?
Jikina Nasiba ta tsaga ta fito. Kuma tun lokacin Annabta zumuncin dangin uwa yafi
na uba sahihiyar soyayya da tausayi".

*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA
KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA
KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*

✍️

*Y'ar uwa, ya mukaji da bubukuwa?* *Daga nan fa har january kusan ko wanne sati
akwai biki, in ba na kusa ba akwai na nesa, ban da tunanin gudunmuwa da ma kudin
man da zakaje bikin ga tunanin abunda zaka saka.*
*Balle ace maaikaciya ce ko CEO ce kina business din ki, kinsan all eyes on you🧐,
ke ba sayen atamfa ba komi tsadanta anyo copynta, shima lace haka, cabdi! To
albishirinki yar uwa!*
*UMM NIHLA malaysianfabrics ta dauke miki damuwa, tana da fabrics kala kala masu
sauki da inganci kuma babu inda zaki samesu in ba wurinta ba, kije taro ki haska
kowa sai ya tambaye ki me kika saka ina kika samu💃 maza garzaya gurinta kusa
labule.* https://wa.me/message/F3EWRSHQPQAAH1


*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA
KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA
KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*



Babah ta kasa ce wa komai domin ita gabad'aya ma alamarin tsoro ya shiga bata. Tana
kuma mamakin rashin kunya da son kai irin na Maryo.
Bata yi zaton son zuciyarta ya kai hakan ba.
Ta kasa ce wa uffan saboda tsananin kaduwa da ta yi.
Ita kuwa ta dinga kuka tana face majina tamkar Dada ce ta kwanta dama.
Washagari ko karyawa bata yi ba ta ce zata juya. Da k'yar Babah ta roke ta akan ta
bari ta karya.
Rai a bace suka rabu a dalilin Babah ta tabbatar aure kam babu a tsakanin Nasiba da
Tijjani.
Rai a matukar bace ta isa Toro. Ta gurfana gaban Dada tana kuka tana fad'a mata
karya da gaskiyar cin mutuncin da Hauwa ta yi mata.
Dada ta taya ta bacin rai tare da rarrashinta tamkar yarinya karama. Tana cin
alwashin sai ta ci mutumcinta tunda bata san yakamata ba.
Bijirewar da Babah ta yi akan auren tare da fitowa baro baro da ta yi ta ce
alamarin ba zai yiwu ba. Sai ya zama d'an zani. Domin hakan ya fusata Baba Maryo
tare da cin alwashin sai Tijjani ya auri Nasiba ko zata yi yawo tsirara, ta ga
karshen rashin kara da nuna banbanci.
Takanas ta tafi cikin jeji can kudu da Jos. Ta samo asiri da surkullen da muradinta
zai cika.

*Bayan waatanni biyu*

A hankali Tijjani ya fara rikice mini fiye da bara. Sai mu kwana gari ya waye bai
ce mini uffan ba. Zan masa magana goma bai fi ya amsa ni sau biyu ba a gajarce.
Ya daina shayin yin waya a gabana. Yanzu har an kai jallin da zai bawa twins waya
su gaishe ta. Duk da dai bai tab'a kama suna ba.
Sai ya ga dama yake cin abincina. Jiya ma da na zauna kusa da shi ce mini ya na
tashi yana bukatar kad'aici. Murjewar da na yi, nan da nan na fara tsomare wa.
Sosai ya murde irin yadda ban taba zaton zai yi ba. Na hakurkurtar da zuciyata na
dinga ba shi hak'uri tare da rokon ya fad'a mini laifin da na yi masa.
Yana bude baki sai ce wa ya yi "Haihuwa yake so. Tunda ba zan haihu ba, shi aure
zai yi, idan zan zauna na zauna idan kuma bazan zauna ba, to bai rik'e ni ba."
Na zuba masa idona da suka soye. Na ce "Tsakanin ka da Allah kana mini adalci
Tijjani?"
Ya hassalo ainun tare da ce wa "Ta ya ya zan yi miki adalci Asiya? To ko kawai zaki
yi gaba ko zaki samu adalin?"
Na sake daskare wa. Na yi maza na kame bakina domin na gane komai na iya faruwa a
tsakaninmu.
Amma hawaye ke tsere babu jinkiri kuncina.
Ya ja tsaki ya fice ya bar ni. Yana fad'in "Me za'a yi da mace mai rainuwa da
azababben kishi. A ce mace ba zata taimake ka ta rufa maka asiri, ta taya ka son
abin da kake so ba. Sai sarhutu da mance alheri kawai ta iya ".
Na yini cikin bacin rai. Yayin da shi kuma ya yi tafiyarsa Toro da yara bai damu da
halin da ya bar ni a ciki ba.
Ina kuka na d'auki waya na bugawa Baban Marina karon farko da na yi hakan tunda ya
aurar da ni. Na kasa magana sai kuka nake yi masa mai tsuma zuciya.
Bai katse ni ba. Sai da na gaji dan kaina na katse wayar.
Baban Marina ya dawo gida cikin sanyin jiki a dalilin yadda kukan Yabi ya buge shi.
Ya leka kofar Dada dan ya bata man zafin da ya siyo mata sai kawai ya ga Tijjani da
Nasiba a gefen bisihiyar zogale suna zance. Dada na daki abin ta. Duk da ba yau ya
saba ganinsu ba, amma yau din sai da zuciyarsa ta buga da tsananin gaske.
Ya amsa gaisuwarsu cikin k'arfin hali. Ya shiga wajen Dada ya fito, ya fita.
Ya zauna kan tabarma amma zufa ta rufe shi. Ya dinga jin wani iri. Duk yadda ya so
jurewa kasa wa ya yi. Yana tambayar kansa yanzu Tijjani yana da rigar da za'a bashi
aure ke nan?.
Ya tuna irin kukan da Yabi ta kira ta yi masa dazu, ya san kuka ne na neman agaji,
kuka ne mai harshen damo. Daren ranar ya yi masa tsawo ainun.
Washagari ana idar da sallar asuba ya ce Salisu ya raka shi Bauchi.
Tamkar jifa haka Yabi ta gansu. Zuciyarta ta karye. Domin ta hango rauni da wata
irin soyayyar ta a kan fuskar mahaifinta.
Tare da Tijjani suka musu iso zuwa falo.
Yana amsa gaisuwarsu ya yi gyaran murya ya ce "Zuwa na yi takanas dan na fad'a miki
ce wa ki yi hakuri ki zauna a dakin ki. Ki kuma sauke dukkan hakkina da kika san
Ubangiji ya dora miki. Daga nan har zuwa lokacin da Allah ya kaddara muku zaman
kada ki yarda ki zalunce shi. Kada kuma ki fito babu izininsa. Aure da kike ga ni
darajar sa ta wuce duk zaton mai zato. Sai dai bisa adalcin Ubangiji ya kewaye shi
da dokoki da kuma sharudda daban daban. Bai barmu kara zube ba. Ina rokon ki, ki
k'ara hak'uri a cikin wannan tsukun da ake son kaimu k'asa da bak'inciki mai
tsanani. Idan har kika yarda kika yi hak'uri, ni kuma na miki alkawarin zan jaddada
damar da shari'a ta baki na zabin cigaba da zaman ko akasin hakan matukar zalunci
da cin fuska ya shigo gidan auren ki".
Cikin kuka da rawar murya na ce "To Babanmu".
Ina fad'in haka ya mik'e tare da ce wa "Allah ya yi miki albarka. Ya fice bai ko bi
takan tagwaye da suke ta rige rigen gaishe shi ba. Yaya Salisu ne kawai ya amsa
musu tare da ciro ledar alawowi a aljihunsa ya damka kowa tasa ledar.
K'warai Tijjani ya muzanta da yadda suka fice basu bi takansa ba. Ya bi bayansu. Ba
jimawa ya shigo ya zauna. Ya ce "Baban Marina ya canja, ya yi bangaranci. To wai a
kaina aka fara k'arin aure ne da za'a mini wulakanci irin haka?"

*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin
register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633

Ban kalle shi bare na ba shi amsa. Maimakon shi ma ya sawa bakinsa linzami tamkar
yadda na yi sai ya zarce da ce wa "Baban kasuwa ne kawai mai mace daya, shi ma
nasan a dole yake zaune bai k'ara ba. Shi Baban Marina din da yake tunzuri irin
haka ai uku ne da shi, shine ni zai nemi hana ni jin yadda a ke ji?"
Na kalle shi da fishi sosai na ce "Ya isa haka! Ina rantse maka da Allah Tijjani
zamu kwashi y'an kallo. Komai kake ji da shi na wulakanci ya tsaya iya kaina. Amma
ka yi kad'an ka tabo alfarmar ubana. Ya wuce hakan Wallahi".
Bansan ya aka yi ba jikinsa ya mutu. Ya kasa ce wa uffan.
Na ja tsaki mai tsananin gaske na tashi na bar masa wajen.
Muka k'ulla gaba sosai. Domin ya kullaci zuwan Baban Marina da kalamansa, dazu har
da shaguben laifinsa ya shafi twins a wajen Baban Marina bai kula su ba. Yana
wankin kayansu yana mini azanci. Ya kuma zabe iya nasu ya bar mini nawa. Ko kallo
bai ishe ni ba. Domin sosai nake jin zafinsa.
Ranar da aka tabbatar mini su Baban Tsakiya sun kai masa kudin aure gidan iyayen
Nasiba kwana na yi ina kuka. Sassafe na yi Bulkachuwa. Ina zuwa na sake

Please Login or Register in order to submit comment