You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naka ne. To mene ne kuma dan ta fita ta bar muku
gidan ku tabbata a ciki?".
Ransa ya baci ainun. Ita ma bata fahimce shi ba. Su duk haka mata su ke da kishi
ne?. Basa fahimtar komai matu'kar akan kishi ne.
A hankali ya ce "Yanzu dan Nasiba ta zo shi kenan sai ya zama masifa? Ta ce sai ta
bar gidan? Duk zamanmu da ita bata gasgata ni ba ke nan? Ni ba kula ta nake yi ba,
bare ta ce ta fahimci wani abu a tsakaninmu. Wallahi saboda sababin Yabi ko kallon
inda ta ke bana yi. Amma hakan bai yi mata. Shin Nasiba ba zata zo gidana ba, ba
yar'uwa ta ba ce?".
Babah ta girgiza kai ta ce "K'warai yar'uwar ka ce ta gaske tunda har ka zabi
fishin matarka akan ta. Madallah da Yabi bata za'bi zaman muzanci ba. Ta daga
hannuwanta sama ta ce "Allah kasa yarinyar nan tana hannu na gari. Allah kasa tana
Kangire ko kaduna gidan Jabir".
Nan da nan ya muzanta. Ya kasa yin shiru ya ce "Kaduna! Ya fa'da cikin takaici mai
yawa.
Ya kasa yin shiru da rawar murya ya ce "Na rantse idan aka same ta a Kaduna duk
masifarta sai ta ga ne bata iya komai ba".
Ta galla masa harara ta ce "To me zaka yi ne? K'arshe dai ka sake ta. Ni kuwa
Wallahi tana gama idda zan bada aurenta ga saurayi ma, don bazan yarda ta fita daga
ahalina ba."
Idonsa ya kad'a ya yi jawur. Da rawar murya ya ce "Babah a gabana kike nuna zaki
bawa k'anina auren matata?"
Ta bu'de murya ta ce "Na fa'da na ji ruruf!".
A matu'kar ki'dime ya ce "Allah ya huci zuciyarki. Allah ya tsare ni aikata irin
wannan BAK'AR TA'ADA din".
Ya bata tausayi ainun. Amma ta cije ta ce "Akan idona uwar Nasiba ba abin da bata
fa'da akan ka ba. Ita ta hana a baka aurenta saboda suna ganin ka baka da mamora.
Amma Yaya Sani ya juyawa dukkan nak'asunka ya tursasawa Yabi auren ka sai kuma dan
ka fara samun dama, ka fara shiga sahun mutane sai a yi maka shunen ta har cikin
gidan Yabi! Ta yi shiru. Saboda yadda zuciyarta take jin tsananin zafin yadda aka
tado mata tsumin bacin rai na tsawon lokaci.
Ta zuba masa ido wanda rabon da ta yi masa haka ya manta.
A kaurare ta ce "Nasiba ba matarka ba ce, ko bayan raina ba zata zama matarka ba.
Shari'a ta halasta ka aure ta babu aibu a cikin hakan. Amma kuma shariar da kanta
ta ce "ku girmama ra'ayin iyayenku sama da naku. Matu'kar ina da hak'ki akan ka
Wallahi na haramta maka ita. Soko marar tunani. Har ka manta tozarcin da uwarta ta
yi mini akan maganarku?"
Hankalinsa a matu'kar tashe ya ce ", Wallahi Tallahi ba ni da manufar komai akan
ta. Dan Allah ku fahimce ni mana"
"An k'i a fahimce kan. Ban da sakarci me ya kai ka taho da ita tunda ga Toro har
Bauchi ku ka'dai ka kawo ta gidan ka. Ai sai a rasa gane wace ce matar gidan tunda
sai ta goyi Yabi da zani tsab. A kan wanne dalilin da ta ce ba zata zauna mata a
gida ba, ka kafe sai ta zauna d'in? Ban da munafunci irin na ku na maza. Na gode wa
Yabi da ta fahimci bata da daraja a wajen ka. Ta fice ta bar maka gidan".
Da rawar murya ya ce "Allah ya huci zuciyar ki. Na yi kuskure a yafe ni dan Allah.
Tun ranar kuma Nasiba ta tafi, da kaina na ce tafi din"
Ta ja tsaki mai tsananin gaske tare da fad'in "Ta baya ta rago".



Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki
da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA
BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES.*

*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.

*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered,
Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan
farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon
yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.


Ya yi shiru ya kasa ce wa komai. Haka ita ma. Yara ne kawai su ke ta wasa a
tsakaninsu. Sai iskar fanka da take kadawa da karfi sosai. Amma hakan bai sa zufa
ta daina yanko masa ba. Gaba daya ya shiga rudani mai yawa. Ya rasa inda Yabi ta
gudu. Ga magaganun Babah masu tsauri. Wanda hakan yake alamta masa yana cikin
fishinta.
A sanyaye ya sake bata hak'uri tare da matsar da jakar kayan yaran gabanta. Ya
mik'e ya faki kallon yaran da suke wasan tsere a tsakaninsu. Ya ce "Zuwa gobe zan
dawo".
Galala ta kalle shi ta ce "Dauki jaka da y'aya'nka. Ai ba zai yiwu ka kori uwarsu
da baki cikinka ba. Sannan ka saka rai zan maka wahalarsu. Wato na zama shasha ma!
Ya koma ya zauna ya sassauta murya ya ce "Haba mana, dan Allah ki ji tausayi na.
Gabadaya nutsuwa ta yi mini tutsu. Idan na barsu ma ba wai hutawa zan yi ba. Neman
ta zan cigaba da yi. Gobe Kaduna zan tafi".
Cikin rashin nutsuwa ta ce "To ka tafi da su, ko ka fara kai su Toro wajen Nasibar
sai ka wuce. Amma Wallahi ko gwaggonsu ka kai wa yaran nan, ni da kai ne".
Ya yi shiru, idon sa ya kad'a ainun, ya koma ya zauna. Murya babu amo ya ce "Ki yi
hakuri dan Allah Babah."
Ta jijjiga kai ta ce "A kan Yabi Bilhillazi zan yi matukar saba maka. Zan fita a
sha'anin ka gabad'aya."
Ya yi shiru. Amma ransa suya yake tamkar ya fad'o kasa.
Me ya yiwa Yabi da zata janyo masa irin wannan jidalin?
Ya dinga bata hak'uri. Da k'yar ta ce sai ya gano Yabi idan ta huce, sannan ita ma
zata hakura." Ya mik'e da sauri yana fad'in "Na gode sosai. Bari na tafi neman ta
da ikon Allah zan nemo ta".
Daidai lokacin Hamim ya fasa kuka yana nuna windo. Tare suka isa gare shi, suna
fad'in mene ne?"
Shi dai Hanif yana tsaye, yayin da Hamim yake kuka tare da nuni da saitin windo.
Nan da nan zuciyar Baba ta tsinke domin ta gano kayan Yabi yake nuna wa akan igiya.
Ma'ana ya gane kayan uwarsu, a ba shi ya rik'e mata.
Nan da nan ta dauke kai, ta shiritar da Tijjani da ce wa "Tofa masa addu'a mana,
watak'ila shaid'anu ke son bude masa ido. Allah ya tsaremu daga sharrin abin da
bama kallonsu".
A gigice ya hau tofa masa falaki da nasi. Yaro kuwa sai zabura yake akan zai je ya
dauko abin da yake ganin na uwarsa ne. Yayin da Babah take ta hirji tare da addu'ar
kada Yabi ta kasa jure kukan Hamim da yake d'ada canyarwa tamkar gyare ta fito. Ita
da kanta ta gane irin kukan da Yabin ta yi tana yarinya ya gado.
Ta ce "Dauke shi ku tafi. Idan ya ga kun shiga mota zai yi shiru."
A raunana ne ya ce "Yadda ya razana hakan zan tafi da shi? Ki yi hakuri na bar su a
nan, gobe ko jibi da ikon Allah zan dawo na dauke su. Ko ban ganta ba.
Ta ce "A a ba fa zan rike su ba. Ai idan kasan zan rik'e maka yara ka dinga
shagulatin bangaro da auren ka kenan. Ina ce lokacin da suke hannuna ka fi uwarsu
nuna zalamar na baku su? Yanzu kuwa ba zan karbe su ba."
Kamar zai rushe da kuka ya ce "Gobe Kaduna zan je Baba."
A gajar ce ta ce "Tafi da su ka kai wa Ihisan. Idan ka dawo ka je ka dauke su".
A kan dole ya sunkuya ya dauki Hamim. Ya rike hannun Hanif. Bayan ya saba jakar
kayansu. Yadda ya d'ebi yaran da jakarsu sai tausayinsu duka ya kama ta.
Suka fita, sai da suka jima da fita. Sannan ta bude dakin da Yabi ta ke. Ta tarar
da ita zaune akan gado tana faman goge idonta tabbaccin kuka take yi.
Ta k'arisa kusa da ita. Ta ce "Yabi kuka kike dan ina kokarin ya fahimci
muhimmancin ki a rayuwar sa da ta y'aya'nsa?"
Da wata irin tab'ara da kuka na ce "Ai da sai ki karbe su. Kukan Hamim kad'ai abin
dubawa ne".
Ta yi galala ta zuba mini ido ta kasa ce wa uffan.
Na kuwa matse na ce "To ni dai na huce tunda haka ne. Ai ya yi ta zuwa, na kuma san
yana cikin tasku, sai ki zaunar da mu, a mayar da zan ce, ki yi masa fada, mu
tafi."
Ta jijjiga kai tare da ce wa "Ban yi hakan ba Yabi. Ba kuma zan yi ba".
Na kuwa juya na kwanta ina kunkunin bazan sake yin yaji na zo nan ba, tunda ba
sulhu zata yi ba".
Ta dinga salati tana tafa hannu. Tare da ce wa "Ban ga laifinki ba. Amma zaki ga
karshen iyashege. Dauko hijabin ki, ki bisu. Na bata rai tare da daure fuska ainun.
Ta sassauta ta ce "Ba fishi na yi ba. Tunda laifin kaina zai juye to kawai ki bisu.
Duk tsamin ran da nake taya ki, baki yaba ba, bare ki bani hadin kai mu yi
maganinsa da kyau".
Murya na rawa na ce "To ai da sai ki karbi yaran Babah".
Ta bude murya ta ce "Na ki karbar tasu. Ina ce ke kika barsu a gidansu? Kuma ba a
hannun ubansu suke ba tabbatacciyar marar ta ido!"
Na yi shiru amma dai fuskata a daure.
Kafin ta yi magana sai kukan Hamim muka jiyo tabbacin sun dawo. Kafin Baba ta fita
har sun shigo falo.
Da azama ta fita tana mini kashedin kada na fito da hannu.
**
Turus ta yi ganin Hamim na rike da riga da hijabin Yabi a hannunsa, ya kuma
sassauta kukan da yake yi. Sai ajiyar zuciya yake faman saki.
Kafin ta ce komai Hanif ya ruga ya dauko takalman Yabi da suke gefen falon. Shi ma
ya rik'e.
Tijjani ya samu nutsuwa domin ya tabbatar tana gidan.
Yayin da Babah ta kasa ce wa komai.
Cikin nutsuwa Tijjani ya ce "Ashe ba shaid'anu ya ke nuna mana ba. Kayan ta ya ga
ni. Har mun fita ya tsananta kuka, ya kuma k'i yarda ya shiga motar. Sai hannuna
yake ja. Na yarda na biyo shi muka dawo, sai kawai ya kai ni baya wajen kayan. Anan
na fahimci kayan Yabi ya ga ni. Dan Allah Babah ki yi hakuri, ki ji tausayinsu ki
basu uwarsu."
Ta yi kicin kicin ta ce "Idan ka ganta ba sai ka daukar musu ita ba. Ai tunda har
zaka wulakanta Yabi irin haka, tabbas nima zaka wulakanta ni. Dan haka ba zan zuba
ido ka fara mata cin kashi bayan ta gama shanye wahalar ka ba".
Ta rik'e hannun yaran ta tura su cikin dakin. Domin sun bata tausayin yadda suka
rik'e kayanta gamgam. Kayan da shafa'a ne ya sanya aka barsu har yaran suka ankarar
da ubansu.

Suna shiga ta janyo k'ofar ta zauna akan kujera, ta tsare gida ainun.
Ya rasa ta yadda zai fara yi mata magana.
Tsawon lokaci kafin ya tausasa harshe. Ya ce "Ina sake baki hakuri. Tunda wannan ne
karon farko da ta kawo miki karata a zamanmu da ita. To ki yi mini uzziri a wannan
karon . Ni kuma na miki alkawarin ba zata sake kawo miki karata akan wannan
matsalar ba. Ki yi hakuri dan Allah".
Jikinta ya yi sanyi. Mussaman da ta zuba masa ido ta ga ya fada ya kuma birkice
gabadaya.
Ya dinga magiya. Da ban baki tamkar zai rushe da kuka tsabar tsananta rokon da ya
yi.
Rauni irin ma uwa ya shige ta. Ta furzar da iskar takaici. Ta ce "Ba dan ta yi
hankalin tahowa nan ba. Da an yi ta yamididi da murnar ka yi kudi ka fara wulakanta
ta. Da wanne idon zamu Kalli iyayenta da suka yi alkunya da kawaicin baka auren ta?
Ta dinga yi masa fada da togaciya tamkar zata bige shi. Yayin da shi kuma yake
fad'in "Ki yi hakuri zan Kiya ye da ikon Allah".
Ta tashi ta nufi daki. Ya yi maza ya mik'e ya bi bayan ta a d'arare tare da
fargabar kada ta dakatar da shi.
Tana tsakiyar gadon. Yayin da Hamim yake kwance kan cinyarta. Hanif kuwa sarkin
hakuri filo kawai ya yi da cinyar jikinsa na kan gadon. Daga ita har yaran kowa ya
yi shiru tabbacin suna cikin alhini.
Baba ta sassauta murya ta ce "Yabi ga shi nan ku sasanta. Idan kin ga zaki yi
hakuri ki bisu to, idan kuwa kin ga ba zaki bisu ba. Ba zan matsa miki ba. Ban san
me kike hadiye wa ba".
Ya rasa inda zai tsoma ransa. Murya babu amo ya ce "Amma na baki hakuri fa".
"Dan ka bani hakuri sai na tirsasa ta?"
Ta jijjiga kai tabbacin ba zata mini dole ba.
Ya sassauta murya ya kalle ni ya ce "Asiya ki yi hakuri da abin ya faru. Na yi
kuskure duk da dai fahimta ta ne baki yi ba".
Yana rufe baki na ce "Ba zan fahimta ba."
Babah ta yi shiru tana kallonmu. Watak'ila kuma mamakina ta yi na yadda na kame
kamar ban gan shi ba tamkar ba yanzu na gama yin tijarar na huce ba ".
Ya munfasa ya ce "shi kenan ki yi hakuri." Ya furta a hankali.
Babah ta zame ta fice.
Yana ganin hakan ya matso kusa da ni ya zauna. Ya rage murya ainun ya ce "Saboda
Allah little ya kamata ki bar dakin ki babu iznina?"
Na galla masa harara na dauke kai ban ce komai ba.
Ya sake tausasa harshe ya ce "Tashi mu tafi, idan mun je gida sai ki yi mini ko
wanne irin darun ni kuma zan yi ta rarrashin ki, da kalolin soyayya masu tsayawa a
rai."
Na ja tsaki tare da fad'in "Na bi soyayya da gudu. Ni yanzu bana son ka, kai ko
ganin ka bana kaunar na bude ido na yi".
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Tom shi kenan, ki dawo dakinki dan yaran ki, ko ban ci
arzikin komai ba ki dawo dan y'aya'n ki".
Na dauke kai na ce "Idan na mutu zasu fasa rayuwa ne?".
Ya rik'e kafata da tafi kusa da shi. Na goce da sauri. A tunzure na ce "Kada ka
kuma tab'a ni. Ka je ka cigaba da damukar wadanda suke da daraja a wajen ka".
A zafafe ya ce "Na cigaba Asiya?".
Na dauke kai na ce "Eh".
Murya na rawa ya ce "Kin ga na damuk'e ta ne? Me yasa kike son jifa na da wannan
mummunar maganar ne?"
Ba ja in ja na kalle shi na ce "Saboda ina da hujjoji na gaskiya. Sannan idan ba
hakan ba, me yasa zaka kawo mini wannan suntumemiyar cikin gida? Har kuma kana
kumfar bakin ba zaka ce ta tafi ba, saboda ta yi maka alkhairai. Fada mini
alherorin da ta yi maka dan kuwa ban sansu ba".
Ya kafe ni da ido. Cikin matsanancin bacin rai ya ce "saboda kin fahimce ni a
baibai shi yasa kika taho babu izinina, sannan kike kallon idona kike jifana da
alamarin da kika san na tsani a jingina mini. Me yasa kike son ki dinga tayar mini
da hankali ne Asiya?"
A tunzure na ce "Saboda ba ni da alheri a wajen ka sai sharri. Yanzu ba sai ka
sakawa Nasiba da kalar naka alherin ba. Ni kuma ka bini da irin nawa sharrin ba".

*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Saiwowin maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki
da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*

Ya jima bai iya ce wa komai ba. Da alamu kokawa yake da zuciyarsa. Domin fishin da
ya ke shimfide a fuskarsa ya kai intaha.
Tsawon lokaci mun yi shiru. Yaran kuwa duk sun yi barci.
Ya munfasa ya ce "Ki yi hakuri. Na baki hakuri. Tashi mu tafi, na yafe miki".
Na sake hade rai na ce "Ba na son ka yafe mini, domin ban maka komai ba. Ban
zalunce ka ba. Kai ne ka ke shirin zalunta ta. Shi yasa na saukaka maka hanyar
rabuwa da ni. Kawai ka sallame ni, ba zan iya zaman zullimi da fargaba ba. Tunda ka
fara samun kudi ka ke canjawa. Nan gaba bansan yadda zamu kwashe ba. Gara tun wuri
na barka tun baka gama barina ba ".
Murya babu amo ya ce "me nake yi miki Asiya?"
Baka yi mini komai. Son ka ne ba na yi! Ko dole ne?"
Ya mik'e tsaye ya ce "Babu dole, to ba ni yarana".
Na rungume Hamim da yake ta barci yana sakin ajiyar zuciya. Na ce "Ba zan bayar ba,
dauki Hanif shi kenan an raba."
Nan da nan ya hau rantsuwar ba zai bar shi ba. Ba zai raba su ba. Na dage tamkar
har cikin zuciyata da gaske nake yi. Sosai muke yin takaddama.
Sai da na gama famfa shi. Ya sakankan ce bazan iya yarda ya tafi da su ba.
Sai kawai na ce "Dauke su ku tafi, Allah ya shiga al-amarinsu."
Nan da nan ya yi turus. Jikinsa ya yi sanyi ainun. Ya zuba mini ido tsawon lokaci,
ni kuma na yi kamar ban ga ni ba.
Ya koma ya zauna a maimakon mikewar da ya yi, yana kumfar bakin sai na ba shi
y'aya'nsa.
Ya sassauta murya ya ce "Na baki hak'uri fa little. Ki mini uzziri mana".
Murya na rawa na ce "Sau nawa ka ke yi mini laifi ina share wa?"
Da sauri ya ce "Da yawa. Ina kuma gode miki. Na kuma dha fad'a miki kina da
alfarmomi masu yawa a waje na. Yanzu ki mini hakuri dan Allah. Bazan sake yin hakan
ba."
Na hirgiza kai tabbacin ban karbi ban bakinsa ba.
Ya marairaice ya ce "Haba mana my little angel. Ki huce, kin san fishin ki kassara
ni yake yi".
Sai lokacin na ji kuka ya zo mini. Na dinga yinsa bilhakki. Tsawon lokaci sannan na
daina. Ya saki gauron numfashi ya ce "very sorry little. Nasan kin huce, tashi mu
tafi dan Allah".
Na girgiza kai na ce "Ni kam bazan koma ba fa. Ai tunda har waya ka ke yi da ita,
nasan akwai abin da zai biyo baya. Dan haka ka je na bar mata kawai."
Ya diririce ainun. Ya fara musun basa waya.
Na zuba masa ido na ce "Waye ya ce mini Nasiba ta ce da Dada za'a zo ganin gida?"
Ya ce "Ni ne".
"Me yasa ni bata fada mini a wayar ba? Me yasa kullum sai ta kira ka? Me yasa sai
kai Tijjani? Tunda bata kirana, bata kiran Yaya Salisu da ragowar. Na tsani rashin
kame wa".
Ya kasa magana tsawon lokaci. A sanyaye ya ce "Ba ni da bakin magana , am
speechless. Abin da zan iya ce wa biyu ne. Ki mini uzziri, ki yi hakuri."
Na yi shiru. Cikin rarrashin ya ce "Wallahi duk hasashen da kuke yi ni ban tab'a
d'arsa shi a raina ba. Amma na gamsu kin fini gaskiya. Idan kika yarda muka tafi
yanzu kuma. Na miki alkawarin har kasa ta rufe idona babu magana mai tsayi a
tsakanina da ita bare soyayya ko aure, In sha Allah ".
Na yi k'asa da kaina, ban ce komai ba, amma kuma k'ullin zuciyata ya hau warware
wa".
Ganin rarrashin ya fara tasiri. Ya sake tausasa harshe ya ce "Ai ni na dauka babu
abin da zan yi miki, ki yi mini yaji. Tunda baki kai hakan ba ma, na miki babban
laifi, kika rufa mini asiri kika yafe mini. Amma yanzu kuma a kan zato da zargi
kika tozarta ni. Me yasa zaki munana zato a kaina? Me yasa kika zabi ki janyo mini
fishin Babah?"
Yana rufe baki na ce "saboda ka fahimci ban dauki alamarin da wasa ba, ka kuma gane
yanzu hankali ya fara ratsa ni. Ba komai zan lamunta ba".
"A karo na ba adadi ina sake baki hakuri. Allah ya huci zuciyar ki. Dan Allah mu
rufe wannan matsalar. Wallahi bazan sake yi miki hakan ba, babu ruwana da ita, ko
kallon inda take bazan sake yi ba. Ko na ganta a wajen Dada idan ta gaishe ni, zan
amsa ne ba tare da na kalle ta ba, bare na gane me take ciki".
Na yi shiru. Ban tanka ba. Ya ce "Haba mana Little"!
Na cuna baki na ce "To kuma wayar da kuke yi fa?"
Da hanzari ya miko mini wayar yana fad'in duba ki ga ni. Na share lambarta. Na kuma
jefe lambar a black list ta yadda ita ma ba zata same ni ba".
Na yi shiru ya ce "please mana Little ki ce kin huce, ki ce komai ya wuce".
Na dauke kai na ce "To kuma iyakar da ka nuna mini fa? Da ka ce gidan ka ne ba nawa
ba?"
Da rawar murya ya ce "Kinsan An nadamu ala ma fata? To hakan maganar ta ke. To ni
me ma zan yi da gidan da babu ke a cikinsa? Idan wannan maganar ne ta sake b'ata
miki rai to ki huce. Na baki gidan ma gabadaya. Ki yi yadda ki ke so a cikinsa. Shi
kenan?"
Na ce shi kenan, amma bazan koma yau ba".
Da hanzari ya ce "A a kada mu yi hakan, yanzu zamu tafi idan ba so kike hankalina
yafi hakan tashi ba."
A hankali na ce "To kawai sai Babah ta ga zamu tafi? Ka bari idan na fada mata jibi
sai ka dawo mu tafi".
Da azama ya ce "Wallahi bazan iya ba, kada ki zalunce ni, kin sani bazan iya ba.
Tunda mun shirya ina ruwanta da mu?"
Ya mik'e yana ce wa "bari na je na fada mata zamu tafi".
Na bi bayan sa da kallo. Ina jin fishin da na yi da shi yana warware wa.
Na zuba wa yaran ido. Ina rasa ga ne wa nafi so a cikinsu. Dukkansu Abu guda nake
ji a kansu. Amma na fi jin tausayin Hamim haka siddan duk da shine fitinanne kuma
marar hak'uri.
A fili na furta "Allah ka rayamu tare da yaranmu, ka tsare mana su, ka yiwa
rayuwarsu albarka".
Ina kallon Hanif da yake barcinsa akan gado illah kansa da yake jikina. Ina ayyana
mutane masu karamci da sadaukarwa tun suna kananu ake fahimtarsu. Yana wahalar
gaske ya ture d'an-uwansa a jikina. Ko abu ya dauka da Hamim ya fara kuka zai ba
shi. Haka nan baya damuwa idan na goyi Hamim shi na rik'e hannunsa.
A raina sai nake ganin shine yafi dace wa ya amsa sunan Baban Marina. Ko da yake
bansan ko Baban Bulkachuwan shi ma haka yake mai hak'urin gaske ne.
Na shafa kansa ina ce wa "Allah yasa ka zarce da hak'uri da yakanar ka. Allah ya
saukaka muku rayuwarku gabadaya".
Na yi shiru ina jin wani irin abu na tsirga mini da bansan ko mene ne ba.
A hakan Babah ta shigo, Tijjani na biye da ita a baya.
Ta kalle ni ta ce "Wai har kin hakura kin ce zaki bi shi Yabi?"
Yadda ta yi maganar sai na kasa amsawa.
Nan da nan ya ce "Ta hakura mana Babah. Dan Allah kada ki sauya mata shawara. Na
bata hak'uri, ke ma ina sake baki hak'uri."
Ta ce "Idan ta ce zata koma ai shike nan. Amma idan ta ni ne ko zata koma sai na
kira maza sun taya ni kafa maka hujja".
Ya marairaice ya ce "Harshe da hakori ma ana samun sab'ani. Mun fahimci juna yanzu.
Na yi alkawarin bazan kuma yi mata hakan ba. Mu rufe wannan matsalar a tsakaninmu
dan Allah".
Ta kalle ni ta ce "Zaki koma, ko sai mun zauna da iyayensa na nan na fada musu
BAK'AR TA'ADAR da yake neman tsiro da ita, kada nan gaba su ce na kashe masa aure".
Na kasa magana. Shi kuma fadi yake "Babah mun fa shirya ta fahimce ni, na bata
hak'uri."
Ta ce "Kasan Allah sai na ji da kunnena sannan zan bari ku tafi. Ai kai yanzu
maganar ka ba abin dubawa ce ba".
Ya rasa inda zai sa ransa. A kidime ya ce "Asiya taimake ni ki fada mata, kin huce,
daure ki ce komai ya wuce. Kalli yadda yaran nan suke barcin nutsuwa a jikin ki. Ko
baki hakura dan ni ba, huce saboda su".
Dakin ya dauki shiru. Kallon Tijjani kawai za'a yi a gane yana cikin zullimi sosai.
Ta sassauta ta ce "me kika ce, zaki koma, ko kuwa?"
Na yi k'asa da kaina na ce "Tunda ya gane kurensa, ya janye kalamansa, ya kuma bada
hakuri, to ba sai an tara masa jama'a ba. Ai mun ba shi assignment ".
Ya yi maza ya ce "Wallahi exam ma kuka ba ni."

*Anti Rabi how far?*

✍️
*UMM

Please Login or Register in order to submit comment