You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akan kunnenmu
mu ke jiyo yadda ake fadin "y'an Marina ne, kasan yawa ne dasu tamkar tsaki."
Ko muji an ce "kai wato gidan Marina akwai zuka zukan zaratan y'anmata fa."
Muna tafe ina tambayar Basira da Nazira jiya Dada ta d'ora musu karatun kuwa bayan
na tafi?.
Nasiba ta ce "Bayan kin bata mata rai yaushe zata iya yin karatu? Kin san kullum
sai ta ce haramun ne yin karatun addini a cikin fishi ko a cikin rashin tsarki".
Muka k'yal-k'yalale da dariya gaba'daya.
Muka isa makaranta hatta Malamai kwarjini muke yi musu saboda yawanmu da kuma yadda
muke kama da juna baya ga hakan tare ake ganinmu tamkar kashin awaki alhalin a
gidajenmu babu wannan soyayyar da jin kai da ake gani a tare da mu.
Lokacin tashi yayi muka dawo a jiga ce a dalilin rana ake yi duk da zafin ranarmu
da sau'ki akan ta Bauchi da Jigawa.
Wajibi ne idan zamu tafi sai mun shiga mun gaida Dada, haka nan idan mun dawo.
Tsabar saka ido da kwakkafin baiwar Allan nan duk wacce bata je ba sai ta ga ne,
hakan kuma na iya zama sanadin rikici a gidan, domin bai zame mata komai ba, ta
kira uwar yarinya ta yi mata tass, ta ce da sa hannunta y'arta ta raina ta.
Kuma abin mamakin idan baka kama sunanta ba, to da kai da wacce bata je ba daidai
kuke.
Ina tsaye suka dinga shiga suna fitobwa ba abin da ake ji sai "Dada mun dawo, sannu
da gida" .
Yayin da ita kuma take kama sunan kowa tana cewa "Sannunku da dawowa, lale da
y'anmata Dada".
Sanin da na yi garina da tsakuwa da ita, ya sanya nake jingirta wa sai na je
gabanta sosai ta yadda zata shaida ni da kyau.
Tunda kullum sai na je, amma idan ta so ci mana mutunci ni da Gwaggo sai ta ce ban
je ba, ko kuma na yi mata gaisuwar gadara da wulakanci daga bakin k'ofa
Dan haka da na k'ara wayo sai nake isa gabanta mu hada ido sosai sannan na yi
gaisuwar.
A gajiye na k'arisa k'ofarmu na tarar da bacin rai domin tsagwaya na tarar an yi a
matsayin abincin rana, wani irin nau'in abinci ne da ake sirfa dawa sai a dafa a ci
da manja.
Na tsani abincin ba dan babu da'di ba, sai dan kawai bana so.
Na zauna a tsakar d'akin Gwaggo ina kunci sosai.
Ta shigo ta kalle ni ta ce "ban ga kin cire inifom din naki, kin yi sallah kin zuba
abinci ba?"
Na tumbatsa da fishi ban tanka ba.
Ta kafe ni da ido ta ce "Yabi kullum aka yi tsagwaya sai kin tayar mini da hankali?
Sanin kan ki ne mahaifinku ya saka takunkunmin siyo abinci a waje ko a ro'ko a wani
waje. Me yasa ba zaki rufe ido ki ci dan ta yi miki maganin yunwa ba?
Idan kin yi ha'kuri ai wataran barin gidan zaki yi, ranar da Allah ya kai ki
dakinki komai kike so sai ki yi wanda bai wuce wadatar mijinki ba".
Cikin bacin rai na ce "Ki taimake ni ki bar ni na jika gari na sha, Allah ya sani
yunwa nake ji kamar na mutu".
A sanyaye ta ce "To ki jika amma nafi son ki dinga ci tunda idan kin ci din ba
illah take miki ba."
Haka na jika gari na bu'de jakar makaranta na dauko gyada maro na bushe na zuba,
ina sha, ina fa'din "ba dan na k'osa ba, da Iklima ta siyo mini madara, to aikenta
bana me sauri bane ko wanda yake a matse irina, domin shad'arta ta yi yawa".
Gwaggo ta girgiza kai ta ce "Ke dai duk salon k'wadayi kin san shi, ki dinga bin
duniya a sannu sannu Yabi".
Na yi dariya na ce "Gwaggo tuni aka daina bin duniya a sannu. Saboda gaggawar
mutanen cikinta ba zasu bar mai binta a sannu ya kai ga gaci ba, yanzu da nake yin
kitso na ha'da da lalle ba gashi muna d'an samun taro da k'wabo ba, da sannu nake
bi iya kitson kawai zan yi Gwaggo. Yanzun ma so nake na koyi wata sana'ar na sake
ha'da wa domin ina da burin na samu ku'di masu nauyi na jiyar da ke da'di, na jiyar
da su Iklima".
Ta girgiza kai ta murmusa ta ce "Na gode sosai Yabina! Allah ya ida nufi, amma dai
ki bi a sannu da ikon Ubangiji komai zai saukaka a gareki, kullum sai na rokar muku
kada a jarrabe ku da rashin abincin a gidan aurenku kamar yadda aka jarrabi
Yayarku, ita ma ina fatan da'di ya biyo bayan wannan wahalar da take ciki".
A sanyaye na ce "Allah ya amsa bakinki Gwaggo".
Ina kammala wa na yi haramar sallar azahar, sannan na shiga wanka dan shirin tafiya
Islamiya.
Dai-dai lokacin Babanmu ya dawo daga wajen sana'arsa.
Gwaggo ce mai girki ta hau hidimar kai masa abinci, a raina sai kiyastawa nake yi
ina ma ina da hali na dinga soya masa miya mai d'auke da naman kaji ko na shanu
zuk'u zuk'u a ciki. Din ya dinga ci da abinci.
Na fito na gan shi zaune a rumfa akan tabarma jikinsa duk ya yi futu futu, ga
alamun gajiya mai yawa a tare da shi.
Tausayinsa ya tsirga mini, cikin rauni na ce "Sannu Baba, sannu da kokari".
Ya dan sassauta ya ce "Sannun ka dai Yabi Asiya".
Na dan murmusa domin shi ka'dai ne yake ha'da mini sunan guda biyu. Tunda ya
fahimci ina bacin rai idan ba'a ce mini Yabi ba, sai ya kankare kirana da gayan
Asiya.
Na wuce shi na fa'da d'akin Mama wajen Nazira.
Na tarar itama shirya wa take yi.
Tare muka fito muka risina muna cewa "mun tafi Baba".
Ya amsa da cewa "A dawo lafiya, ku kula da kanku".
Muka shiga sashin Baban Tsakiya muka fito da su Firdausi da Saratu.
Amma wani irin abu ya tsirga mini mai nauyin gaske, ba dan komai ba illah ganin da
na yi Baban Tsakiya yana cin dafadukan shinkafa gefe kuma kunshin balangu ne, ga
pure water mai sanyi a gefensa cikin yar bak'ar leda da alamu shi ya shigo da su.
A banzan ce ya amsa gaisuwarmu tamkar ma bai ganemu ba.
Na tuna gabzar da muka baro Baban Marina yana ci zufa tana yanko masa.
A hankali na ce "Àllah ga Yabi! Ka buda mata hanyoyin arziki ta jiyar da iyayenta
da'din duniya".
Kafin muje k'ofar Baban kasuwa muka yi kicibus da Maijidda, ta fito.
Na ji da'din hakan domin shi kam ma tsiyatakunsa sun fi na Baban Tsakiya yawa.
Gaba'daya muka d'unguma k'ofar Dada dan yi mata sallama da kuma biya wa Nasiba.
D'aya bayan d'aya muke gaisuwar tamkar masu neman tabarraki, kuma dole sai an kama
sunanta idan ba hakan ba sai ta dauke kai tabbacin bata karbi gaisuwar ba. Abin da
zai biyo baya kuwa ba mai sau'ki ba ne.
****
An idar da sallar isha dukkan mun hallara a k'ofar Dada.
Sai jiranta muke ta kammala nafilfilinta ta d'ora mana karatu, domin karatun nata
ba k'aramin nisha'di yake sanya mu ba.
Ta idar ta dinga jan dogon carbinta wanda kafin ka kammala jan k'afa d'aya ma
lokaci ne mai yawa.
Amma haka muka jira ta kammala. A fili ta cika addu'arta da salatil fatih.
Dada tsohuwa ce da bata samu ilimi sosai ba, amma Ubangiji ya cika zuciyarta da son
addini, ta rabauta da yawan yin istigifari, matsalarta guda tana da son zuciya,
matu'kar zaka bata abin duniya to zata juya gaskiya ta koma karya.
Hakan kuma ya yi tasiri a zukatan ahalinta, domin kuwa a tsakaninmu ma mun k'ullaci
yadda take fifita Nasiba akanmu, ta yadda ta fimu gata da iko a gidanmu. Kowa yasan
Dada tafi son jikokinta da y'ay'anta mata suka haifa, mussaman su Nasiba sannan
Bulkachuwa.
Saratu ta ce "Dada muna dakon karatun ne, jiya kin ce addu'ar tsari da makarai da
miyagu zaki d'ora mana."
Ta dan yi tari ka'dan ta ce "Hakkun Saratu".
Ta numfasa ta ce zan biya sau uku daga nan sai ku dinga fa'da bayan na fa'da."
Muka amsa da cewa "To".
Ta yi Basmalah, ta yi salati ga Annabi, sannan ta nemi tabarrakin SHEHU.
Na yunkura zan yi magana sai kawai na yi maza na saka hannu na kame bakina.
Da karsashi ta ce *"Wa makaru, wa makaru, Wallahu kairan makirina".*
Na amsa karatun nata ina ganin kuskuren ciki ka'dan ne.
Muna saurare har ta biya sau uku kamar yadda ta fa'da.
Sannan muka koma tana yi, muna amsawa har kuma ta ce mu yi da kanmu.
Muka dinga yi har muka rike dama kuma mun biya ayar a islamiyya.
Ina son na yi mata gyara amma ina jin tsoron abin da zai biyo baya.
Ganin mun ri'ke sai ta ce "To zan baku addu'ar farin jinin samari, ku yawaita yinta
atafe kuke, ko a zaune ko kuma a kwance".
Muka yi shiru dan nuna kunya.
Ta numfasa ta ce *"Ya tifa risubuha ragadan".*
Muka k'yal-k'yalale da dariya, na kasa daurewa na ce *"Min kulli.."* kafin na
karasa ta ce "Lah! Ai iya inda na tsaya, zaku dakata, duk wacce ta yi karambanin
cika ayar to ta kuka da kanta. Domin maza kala kala zasu yi ta bin ta har mazan
dabbobi sai sun bi'de ta da sunan soyayya saboda karfin addu'ar, kunsan Annabi
Isibu aka saukar wa ayar."
Muka kasa cewa uffan domin kowa dariya ce a bakinsa yake gimtse wa".
Ta kalli Nazira, Saratu, da Nasiba ta ce ku dimance ta babu kakkautawa kune masu
nauyin jini, ke Yabi ba sai kin yi ba, ku kuma ragowan saffa saffa zaku dinga yi
tunda kuna samun mane ma."
Nasiba ta bata rai ta ce "wanne irin nauyin jini kike magana Dada?
Duka duka fa shekarunmu sha shida ne wasu ma basu cika ba, ban da dai ana auren
wuri a gidan nan ina ma muka isa a samu a sahun y'anmata a wannan zamanin?".
Dada ta ce "A wajena kun wuce y'anmata ma kun zama iyayen mata, tunda ba wacce bata
yin wanki duk watan duniya, ni kam kullum sai na yi tuba sama da sau dari uku, tare
da addu'ar Allah ya cika mini burina wajen sallar layya ace ko wacce maneminta ya
tsaya duk sai mu tattara mu rabu da ku salin alin.
Amma a duk sadda na hango zugar ku gabana faduwa yake yi, inta shiga firgicin yadda
sallolimmu suke goriya a madakata basa isa gaban Zati".
Cikin dariya na ce "Wai a ina kike koyon wadannan karatun naki irin na makafi ne?".
Haka kawai na fa'da ta rusa ihun da ya janyo hankalin ahalin gidanmu, mu kuwa
gaba'daya muka zuba mata ido muna mamakinta, yayin da jikina ya yi mugun sanyi,
zuciyata ta shiga kaiwa da komowa cikin fargaba mai yawa.
Cikin kankanin lokaci dukkan iyayenmu maza sun bayyana, wasu daga cikin matan gidan
suma sai iso wa suke yi cikin zullumi duk da dai ta kan yi irin haka sa'i, sa'i.
Tana kukan tana fa'din "Yabi ce, Yabi ta zage ni, ta mini gorin mijina makaho ne".
Mamaki ya sake kama mu, domin sai a ranar muka san kakanmu Alh Garba wai ashe ya
makance a karshe karshen rayuwarsa, duk cikinmu ma ba wadda ta san shi bare har a
yi mata gori, sannan dama ana gorin ciwo ne?"
Haka Baban kasuwa da yake jin shine a saman kowa, ya hau cin mutuncina yana fa'din
ba zai yiwu kullum sai na tozarta uwarsu ba.
Zai dauki mummuna mataki a kaina ya ga take takena so nake na gagari kowa, to shi
ba zai zame masa komai ba akan mahaifiyarsa ya kore ni daga gidan, ko kuma ya dauke
Dada su bar mini gidan, idan ya so iyayena su shata jan layi da shi.
Baban Marina kuwa cikin sanyi yake fa'din "Haba Iliya yaushe zan haifi y'ar da zata
shiga tsakaninmu, komai zaka yi mata ai ka isa ne".
Baban Tsakiya ya ce "A a ai yaran yanzu basu da kunya balle mutunci baka ganin
yadda ta saka uwarmu kuka to mu kuma idan muka ce zamu shiga shirgin ya'yanka ai
sai dai su rufe mu da duka tunda a cikin idonsu muke ganin bakincikin da suke yi da
mu, tamkar dai mune muka hanaka ka sake tara arziki, ko muka hanasu yin zuciyar
tallafa maka. Ban da lalace wa Musa ka'dai bai isa ya ri'ke kofarka ba? Ya'yanka
wajen hudu ko biyar ne a daki amma duk wula'kantattu ne, basa taimaka maka da
komai, amma abin kaico sun raina kokarinmu akan ka."
Baban Marina ya sunkuyar da kai kasa gwanin tausayi yana fa'din sai ha'kuri da
yaran yau, ni kuma har yau din nan basu fiye mini ku ba".
Na kalli Nazira na ga hawaye na tsere akan fuskarta, na sake kallon ragowar, su
Firdausi kowa idonta a bushe tabbacin basu da kaico akan cin mutuncin da iyayensu
suke yiwa ubanmu.
Na kasa hawaye a dalilin ba'kin cikin da yake cina yafi gaban hawaye.
Ba abu mai ciwo irin wanda ba za'a barka ka keta shi ba, ya tisa iyayenka a gabanka
da cin mutunci akan idonka.
Na sake kai idona kan Dada da take matsar hawaye, na dinga mamakin yadda ta tara
mini jama'a haka.
Na gama yarda kafatalin jikokinta ba wacce take jiran kiris akanta iri na.
Duk yadda Nasiba take zage wa suna yin sa in sa, hakanan kowa a cikinmu tana mayar
mata da magana amma ba wanda take mayar da laifinta garma sai ni.
Tausayin mahaifina ya yi matu'kar kama ni ta yadda kannensa suka tsaya a gabansa
suke fa'da masa maganganun da komin sanyin halinsa sai sun mintsine shi.
Kirjina ya sake nauyi akan wanda ya yi dazu da naga Baban Tsakiya yana cin da'di a
kofarsu amma mu muna cin abinci irin na yan fursuna, kuma suna da halin tallafa wa.
Amma sun runtse idonsu.
Haka Baban Marina ya dinga bawa Dada da sauran y'ay'anta ha'kurin katobarar da na
yi tamkar dai shi din ba uwarsa ba ce.
Sai lokacin hawaye mai ciwo ya goce mini, ina jin tsanar mutanan da a baki
Baffanina ne.
Maganar gaskiya kuma na fi jin ciwon Baban kasuwa.
Haka suka fice suna kumfar bakin na fitine su, na fitini y'ay'ensu, tunda ba'a
sati ba a doku da ni ba a cikin gidan.
Rainin da aka yi mana ne ya sanya dukkan mutanan gidan suke ganin zasu mayar da mu
gidadawa, shiyasa ni kuma na lashi takobin duk wanda ya nemi ta'ba ni, ko taba wani
cikin yan k'ofarmu la shakka ni ya ta'ba domin zan siyi fa'dan ne ya dawo kaina,
duk yadda nake yar shafal amma Ubangiji ya hore mini wani irin karfi tamkar
shari'a, ko dan da dukkan zuciyata nake yin fa'dan ne oho.
Yadda nake tare wa kannena fa'da da muke daki d'aya haka nake tarewa na yaran Inna
amaryar Babanmu babu banbanci.
Hatta Nazira da take yayata ni nake tare mata fa'da domin duk wanda ya fa'da mata
maganar banza zan yi ruwa na yi tsaki na shiga na dinga yarfa bak'ar magana har sai
abin ya juye kaina.
Duk yadda nake jin haushin Mama bai shafi son da nake yiwa Nazira ba.
Domin yar-uwata ce da uba ya ha'damu, idan da abin da na tsana ban kuma yarda da
shi ba shine yan'ubanci.
Ina matu'kar takaicin yadda wai gidanku daya da mutum, cikinku daya, gadonku daya
amma babu yarda da amana a tsakaninku.
Duk wani alherinka baka son dan-uba ya ji, zaka iya fa'dawa bare matsalarka amma
ban da dan-uwanka da uba daya ya hada ku.
Kuma mafi yawa iyaye mata ne suke bari yaransu su shiga cikin rikicin da ba nasu
ba.
Da ace Nazira tana biye hudubar Mama da tuni ta gurbata mana zumunci da soyayyarmu,
mun koma muna adawa da junanmu.
Wai uwa ce zaka ji tana zayyane wa y'ay'anta laifin kishiyarta, ko kuma laifin y'a
ko d'an da ba nata ba.
Da ace iyaye mata zasu dinga ha'diye rikicin kishi a tsakaninsu, suna boye rashin
jituwarsu a gaban yaransu, sannan idan matsala ta faru suna barinta a tsakaninsu da
an samu sassauci wajen yan ubancin da ake yi a yau.
Idan d'an kishiya ya yi miki laifi ko ta yi miki, daure ki ha'diye ba sai kin baza
wa yaranki da basu sani ba, gudun haddasa gabar da baki san iyakacinta ba.
Ko wanne d'a a duniya gaibu ne, ba wanda yasan me gobe zata zo da shi, ba lallai
d'an da kika haifa ya samu daukaka ba, wata'kila sai d'an miji ya samu daukaka fiye
da yaranki, adalcin ki ne zai sa Ubangiji ya sarrafa zuciyarsa ya ji k'anki, haka
nan ke ma babu jin kunya ko nauyin kin yi abubuwa a baya marasa da'di.
Na sani mutanan yau bamu cika gode wa da yaba kokarin abokan zamanmu ba, muhimmi
dai mu yi adalci a tsakanin zaman kishi da yaranmu, ko ba a shiri ya zama akwai
sassauci da ha'diye bacin rai, shi adalci yana haifar da farin-ciki da yalwar
arziki da hadin kai a cikin gida.
Addinin musulunci cewa ya yi ko wanne musulmi dan-uwan musulmi ne, bare kuma wanda
jini mai k'arfi ya ratsa a tsakaninku.
Daga shakiki sai li-Abbi a duniyar musulunci da zumunci amma mutanan yau mun dauki
wata irin *Bak'ar Ta'ada* ta mayar da dan-uba abokin gaba kuma makiyi.
Da kaina na jinjina wa kaina da duk wacce bata da wannan mummunar manufar a ranta.
Madallah da mutanan da suka yarda Ubangiji ne yake zaba mana mutanan da zasu zama
iyayenmu da yan'uwanmu.
Alhamdulillah, Allah ka bamu ha'kuri da juriya wajen mua'amalantar mutanan da ka
d'ora mana hakk'in zumunta da su.


*Kafin lokacin zaku iya fara payment ta yadda idan an kammala free pages babu dogon
jinkiri.*
*Madallah da masoyan RUBUTUNMU*.
*Madallah masu sauke hakki komin kankantar sa, madallah da masu k'arfafa guiwarmu*.
*Fatan alheri ga masu kiyaye hakkin sana'ar y'anuwansu*.
*500 for regular*
*1k for VIP*

*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*ZENITH BANK*
✍️




*BAK'AR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS M.I.NASHE)*.

*Marubuciyar*
*Halin Yau*
*Sabo da kaza*.

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KO DIYAR DA ZAKI AURAR. TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA
BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*MASU SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S ONLY*

*Ina makaranta labaran Books ɗin Ayshat Ɗansabo lemu, marubuciyar TAIMIYYAH DA
NUFIN ALLAH kai har ma da sauran daɗaɗan littafanta? Marubuciyar na muku albishir
da cewa sabon littafinta mai suna ƘADDARAR ZOYA ya fara sauka da zafinsa,labarin
ƘADDARAR ZOYA labari ne da ya faru a gaske ba ƙageggen labari bane.Don haka kar ku
bari ayi wannan tafiyar babu ku a cikinta,labarin zai zo muku akan 500 Whatsapp
group sai VIP group on Telegram 1k.Ku tuntuɓi marubuciyar akan lambarta 08167768704
domin samun free pages na labarin kai tsaye, kafin ku kai ga yin payment.Kar ku
manta it's a true life story,don haka ku hanzarta shiga cikin tafiyar da babu
✍🏻
danasanin bin alƙaminsa.... *



*Shafin nan kyauta ne sukutum ga mamana*
*Hajiya Hadiza Sodangi*
*Na gode sosai Ubangiji ya shirya zuria*

7&8.
Maganar Baban Marina ta dawo da ni tunanin da nake yi.
Kamar a sama na ji ya ce "Na gode miki Asiya! Duk yadda nake jan kunnenki akan
b'atawa Dada rai, da kuma dukan yaran gidan nan ba kya ji, saboda kin riga kin zama
y'ar kuka.
Uwarki kullum cikin yi miki kashedi akan shiga fa'dan yara da kuma tsokanar Dada,
amma duk a iska ko? Na gode sosai da wannan bacin rai da kika sanya ni, Allah ya
shirye ki".
Ya tsugunna gaban Dada ya ce "Ki yi ha'kuri! Halin Asiya ni kaina ha'kuri nake yi
da ita, amma zan dauki mataki akan ta'ba ki da take yi".
Ta kyabe baki ta ce "To ka fara dan takidin aurensu. Jiya mun tattauna da kannenka
sun ce su babu matsala ko yaushe auren ya zo a shirye suke, kai dai za'a fa'dawa ka
fara tanadin tunda yaran ka har biyu ne".
Ya yi gyara murya cikin k'arfin hali ya ce "Babu damuwa Dada ina saka rai Ubangiji
zai kawo mini hanyar da zan samu na yi musu iya abin da zan iya."
Ta murmusa tamkar ba ita ce mai kuka tana face majina ba. Ta ce "To babu laifi
Allah ya basu na gari, masu kuma ha'kuri, domin mai yakana ne zai iya zama da Yabi
dan wuyar zamanta ya kai inda ya kai, ba inda ta baro uwarta".
Cikin sanyin jiki Baba ya mike yana cewa"Dada sai da safe mu kwana lafiya".
Ta amsa masa da fa'din "Allah ya tashe mu lafiya".
Na mike, Nazira ma ta biyo ni muka fice, ba tare da mun ce uffan ba.
Domin na sake fusata da ta ce sun tattauna da kannensa amma shi ba'a saka shi cikin
zaman ba.
Muna jin ta tana fa'din "Wanda Allah ya bashi tsawon rai zai yi kallon tak'ama a
wajen ki Yabi. Yarinya da ke amma kusan ke kike juya shashinku gaba'daya. Kina
tashi Yayarki ta biki zungui zungui ko sallama ta kasa yi mini saboda tana
rarrashin zuciyarki?".
Ban juya ba, bare na tanka mata, balle kuma Nazira da take da sau'kin hali.
Muna shiga shashinmu muka yi turus a dalilin halin da muka ga mahaifinmu a ciki,
zaune yake akan tabarma a tsakargida. Sai fifita Gwaggo take yi masa, gumi na yanko
masa babu kakkautawa.
Muka isa gabansa, muka tsugunna, baki na rawa na ce "Sannu Babanmu!
Abin mamaki sai ya daga mini hannu tabbacin ya amsa gaisuwar tawa.
Nazira ma ta yi masa sannu ya amsa ta hanyar gyada mata kai.
Mama ta fito daga bandaki ta kalle ni ta ce "Wannan ja'irar yarinyar sai kin zama
sanadin mayar da kananun ya'yansa marayu, fitananniya tabtacciya.
Ai duk gwanin na iya a rana ya ke"
Ta ja tsaki mai tsanani ta wuce d'akinta.
Bata jima da shiga ba
ta k'walawa Nazira kira, ta mike a hanzarce ta nufi dakin nasu.
Daidai lokacin Baba ya dan samu sau'kin zufar da take karyo masa.
Ya yafito ni, jiki na rawa na isa gabansa.
Ga mamakina sai ya mik'o mini hannunsa na dama.
Hannu bibbiyu na ri'ke hannun nasa, cikin barin jiki gaba'daya.
A sanyaye ya ce "Ina alfahari da ke Yabi! Kafatalin ya'yana ke nake da tabbaci akan
ba zaki cigaba da yin mini *Bak'ar Ta'ada* ta y'an ubanci ba, na tabbatar da hakan.
Ina saka rai ta dalilinki yarana zasu dawo tsintsiya. Na so ace da wuri na haife ki
Yabi. Da al'amuran da suka dame ni basu yi mini tsananin da nake ciki ba. Amma
Alhamdulillah! Ubangijinmu baya kuskure na gode masa, ina kuma tuba a gare shi."
Hawaye tuni ya goce mini dukkan zuciyata a jagule take da tsananin tausayin
Mahaifina da a yau nake ganin wani irin tashin hankali da raunin da ban ta'ba
ganinsa a ciki ba.
Gwaggo tana fifita, tana kuma share k'walla.y
Ya numfasa ya ce "Idan na mutu Yabi, duk runtsi ku gaisa da yan'uwana, ko ba zasu
taimakeku ba, to lallai ku dinga saka su a cikin al'muranku, idan kina yi, sannu a
hankali zaki samu wanda zasu yi koyi da ke, tunda tun yanzu al'amura sun haska ke
ce mai tsayayyen ra'ayi wanda yafi kusa da kyau da kuma dace wa."
Murya na rawa na ce "Mu sasu a alamuranmu ko da ba zasu taimakemu ba, ko da idan
mun fa'da musun ba zasu dauki al'amarin namu da girma ba?"
Ya sake damk'e hannuna ya ce "Haka nake so Yabi".
Da karfin zuciya na ce "Da Ikon Ubangiji zan yi yak'i da dukkan zuciyata na yi
hakan.
Amma ina ro'kon arziki ka mini afuwa, ka yafe mini muzancin da na janyo maka dazu".
Ya girgiza kai ya ce "Baki yi laifi ba, na sani. Sannan su d'in ma bana son ki
d'auki abin da suka yi mini a matsayin muzanci ko tozarci, na sani baki da sauki,
kina da ru'ko, dan haka na umarce ki, ki manta komai".
Na murmusa hawaye na kwaranyo wa na ce "Shi kenan Babanmu! Allah ya kara maka
lafiya da nisan kwana, yadda a ke mini habaicin tunda aka haife ni ka tsiyace, ina
ro'kon Ubangiji kullum, ya saka idan na girma na samu sanadin da arzikinka zai dawo
ta dalilina fiye da wadda ka rasa a shekarar da na iso duniya".
Ya ce "Rabu da maganar jahilai, ko iya hakan na ga ni ai na gode, sanadin
sana'arki na daina fargabar a tambaye ni ku'din sabulu a gidana.
Alherin da kika janyo mini mai yawa ne, mafi farin-ciki a ciki shine wanda kike
yarda ya'yan da na haifa duka daya ne a wajenki ta fuskantar mua'amala ta zahiri."
Da'di ya tsirga mini ban ta'ba zaton Baba ya fahimci yadda nake da ra'ayin rikau
akan kannena ba, bansan ya fahimci ina tare musu fa'da ba, hakanan ban san hakan
yana yi masa da'di ba, tunda kullum a cikin kirarin bani da hakuri yake.
Sannan kuma baya ta'ba nuna mini ina abin a yaba, sai dai ya ce ai duka yan'uwane
tunda ragowar ma y'ay'ansa ne da yan'uwansa suka haifa masa.
Cikin son na sake k'arfafa nasa guiwa na ce "Duk d'an da ka haifa ina jin sonsa har
cikin zuciyata Baba".
Idonsa ya ciko da k'wallah cikin k'arfin hali ya ce "Allah ka shirya mini yarana,
ka saukaka musu, ka basu lafiya, ka cika zuciyarsu da tsoronka, ka jefa soyayya da
tausayin juna a tsakaninsu. Allah ya yi miki albarka Yabi".
Daga ni har Gwaggo muka hau fa'din "Ameen ameen".
Na kalli Gwaggo na ga hawaye

Please Login or Register in order to submit comment