You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yaya Bulkachuwa ya ce "sauri yake yi ki je yanzu sakon zai fa'da miki".
Ba'kin ciki ya tokare ni, wai shi nan masharranci.
Na fito babu b'ata lokaci na fita ba dan komai ba sai dan Baban Marina yana zaune
ba dan haka ba sai dai ya bushe a wajen.
Da fishi shinfide a fuskata na isa.
Ya kalle ni ya ce "Me kuma ya faru dan Allah. Dazun nan fa na ganki kina ta
murmushi har na yi zaton ko labarin gidanki da Nazira ta gano miki take baki ya
saukar miki da farin ciki mai yawa."
Na d'ago na kalle shi ina rasa ma ajin da zan ajiye Tijjani. Na lura kusan halin
mahaifina ne da shi. Zaka yi musu abin takaici sai su waske su nuna basu gane ma me
kake nufi ba, bare su nuna sun damu a karshe kuma sai su yi maka abin da kai ne
zaka shaki takaici cikin salama.
Na wuce shi na yi tafiyata.
A hakan har kwanakin suka zo ya rage saura kwanaki biyu daurin aure.
A wannan ranar kuma aka yi mini jere.
Da yake Yaya Salisu ya na aiki bansan yadda aka yi ba an ce dai an yi mana gado da
kujeru ni da Ubaida.
Na tuna irin yanayin damuwa da Nura ya shiga a dalilin rashina. Da hawaye a idonsa
yake fa'din "Na tafka asara Yabi! Tijjani ya zama mai sa'a. Na yarda da kaddara. Na
kuma karbi auren kanwarki da hannu biyu in sha Allah kuma zan yi mata adalci.
Allah ya sanya alheri. Allah ya sanyamu cikin masu biyayyar iyaye da ha'kuri saboda
shi".
Da alhini mai yawa muka rabu.
Kimanin kwanakin sati kenan.
Na nisa ina sake hakaito wa ban da y'an kofarmu ba wanda ya yaba lefe ko kyaun
gidana na rasa irin wannan masifar.
Har gara ma an dan yaba gidan Ubaida kadan duk da gidanta gida ne mai kyau sosai.
Amma da yake da ahalinmu aka fi adawa ba a wani yaba an zuzuta kamar yadda aka
kurzanta na su Maijida da Firdausi ba.
Haka gidan Nasiba aka yaba aka kod'a lefenta tamkar me? Amma namu mukus kake ji.
A hakan har asabar din da ta yi daidai da 20 ga watan 5 ta zo aka daura aurena da
Bulkachuwa, sannan aka daura na Ubaida da Nura.
Daga nan aka d'unguma gidansu Nasiba aka daura nata.
Fa'din halin da nake ciki na damuwa ba sai na fa'da ba.
Amma dai ji na yi tamkar na sheka barzaku.
Ina takure a dakin Gwaggo Nazira sai kai komo take yi cikin kwalliya. Ga cikin
jikinta da ya fara tasawa ya kara mata kyau sosai.
Ihisan k'anwarsu Bulkachuwa ta shigo wai na je abokan ango na jirana.
Akan dole na yarda na bita bayan na ce sai dai ta tsaya ni idan mun je.
Haka na dinga yak'e ina gaisawa da su. Ala tilas na yarda aka yi hotuna. Shi kuma
ganin ya samu dama har da sawa ayi mana daga ni sai shi.
Cikin rufin asiri aka yi hidimar bikinmu.
Ubaida aka fara rakawa da yake bamu da nisa.
Ni kuwa Baban Marina hannuna ya kama ya damkawa Babah ta Bulkachuwa.
Ya ce "Rakata dakinta Hauwa! Allah ya kawar da dukkan abin da muke tsoron faruwarsa
a cikin aurensu. Ki kula da ita, ko bani ne na haifa miki ita ba, ta zama y'arki
tunda surukuta ta mayar da ke uwa a gareta. Bare kuma ni din cikinmu guda. Ina
ro'kon ki duk kuskuren da zata miki a zamantakewarku kada ki mata hukunci cikin
zato. Kada kuma ki bari shaidan ya rinjayar da aibunta a zuciyarki. Yarinya ce ita
din a gaban ki koda kuwa ta kai shekaru hamsin a duniya. Na damk'a miki ita, cikin
gasgata cewar na bayar da ita a amintaccen hannun da ko bana raye za'a yi adalci da
sassauci. Ina fatan wannan ya zama sanadin karin zumuncinmu ba wai sanadin
tabarbarewarsa gaba'daya ba".
Duk da fuskata a rufe take amma na lura da yadda jikin Babah ya yi lakwas. Domin ta
kasa bu'de baki ta ce uffan. Na dai ga tana goge fuskarta da na tabbatar hawaye ne.
Tsawon lokaci ba wanda ya yi magana a tsakaninsu.
Sai Baban ne ya katse shirun ta hanyar fa'din "Ki saurare ni da kyau Yabi.
Aurenki ya banbanta da na dukkan y'ay'an gidan nan. Ina fatan kuma ya zama mafi
da'din misali a cikinku.
Ki dauka ibada zaki yi. Kinsan kuwa ibada wajibi ce ba wai ra'ayi ba. Ina ro'kon ki
zauna lafiya da mijinki.
Ina alfahari da ke tabbas Asiya. Amma zan sake alfahari da ke ne idan har kika taka
muhimmiyar rawa wajen mayar da Tijjani yadda muke son ganinsa. Na sani babban aiki
ne mai nauyi. Amma tunda an yi sa'a yana sonki to matu'kar kin kwantar da
hankalinki za'a samu dai-daito.
Ina fatan na ganku da iyali masu yawa kuna cikin rufin asiri. Tashi ki je, Allah ya
bada sa'a ya maki albarka".
Ina kallo yadda Babah ta tashi da k'yar amma bata yarda ta saki hannuna ba tunda
Baban Marina ya damka mata.
Ta tayar da ni ta fita da ni har lokacin kuma bata iya cewa komai ba.
Har muka shiga mota, muka isa gidan tana rike da ni.
Da kanta ta shigar da ni dakina bayan ta jira ni na karanta falaki da nasi da
attahiyatu har zuwa inda ake yin sallamah a bakin kofa. Ita ce ta bani umarnin yin
hakan wanda sai lokacin na ji ta yi magana, rawar da muryarta take yi ya sanya na
gane kuka take yi sosai.
Duk yadda jama'a suke shiga da fita na ganin dakin amarya bai sanya Babah ta tafi
ko ta saki hannuna ba.
Matan gidanmu duk wacce ta shigo ta ga Babah sai ta yi turus.

Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin Saiwowin ne
da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku
kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*
Hatta mamah da matan Baban Tsakiya da suka rakoni tare da ita sai da suka tsokane
ta suna cewa "To ko dai ba zaki bar ta a dakinta bane kamar yadda aka yiwa kowa?"
Duk da hakan kuma bai sa ta bar ni ba. Har sai da Aliyu ya dauko mata Bulkachuwa
cikin abokansa da suke dakon a gama watsewa su rako shi.
Yadda mahaifina ya damka mata ni a hannunta, bata saki hannuna ba duk tsawon
lokacin nan.
Ta kamo hannunsa ta ha'da da nawa ta damk'e cikin nata.
Ta ce "gata nan ubanta ya bani amanarta na kawo maka ita da kaina saboda ya nuna
mini ita ce tawa ba kai ba.
Na karbi amanarta, ni kuma na baka amanarta. Ka dinga tuna dalilin ha'da wannan
auren. Ka zama cikin mutane masu halarci da kuma sakanta alheri da alheri.
Ban ta'ba farin ciki irin na yau ba. Ka sani na ha'diyi takaici da wahalolinka
daban daban. Zan mance komai na yi alfahari da kai har ma na daga maka sawuna ka
shiga aljannah idan Yabi ta kubuta daga tozarcinka da gangan.
Ko bana raye idan ka kyautata mata tamkar ni ka yiwa.
Albarka da farin-ciki zasu kewaye ka.
Ka kula da tarbiyarta, kada ka bari ta bijire wa ka'idojin shari'a. Amma ka zama
mai sasauci da kawaici domin dai yarinya ce y'ar k'arama.
Ina fatan auren nan ya bud'a maka k'ofofin arziki da kuma fahimtar rayuwa daidai.
Àllah ya shirye ka ya shirya maka iyali.
Allah ya albarkaceku gaba'daya".
Ta mik'e ta bar shi a durk'ushe yayin da nake kan gado, hannunmu kuma suna sark'e.
Sai da na tabbatar ta yi nisa na fincike hannuna, na ja tsaki na koma gefe.
Murya a dushe ya ce "Na yafe miki Asiyata! A gabanki Babah ta ce amanarki ta bani,
na tausaya miki, na kuma yi miki sassauci."
Na sake jan tsaki fiye da na farko.
Ya mike ya fita bayan yan tsirarrun kawayena sun fara hayaniyar ba'a sayi baki ba
dare na yi.
D'aya ce ma k'awata a ciki ragowar hudun duk wanda suka zo daga Kangire ne wato
cousin dina na dangin Gwaggo. Sai kuwa Ihisan k'anwarsa. Ita kuma a takure take a
dalilin yayanta ne angon.
Ba jima wa suka zo. Suka taba barkwancinsu, sannan aka yi nasiha da addu'a.
Suka gwangwaje k'awaye da ku'din sallama mai auki. Sannan suka tafi da su.
Ina ganin sun fita, shi kuma ya bisu da niyyar rakiya.
Na tashi na rufe kofar dakina.
Da ya dawo ba yadda bai yi dan na bu'de kofar ba na ki.
Ta windo ya leko ya ce "Ga leda nan ki dauka ki ci nasan da yunwa a tare da ke".
Washagari ina jin ya fita sallah na yi maza na fita na doro alwallah a bandaki,
takaicina daya bandaki a tsakar gida yake ba a cikin daki kamar yadda na ci buri
ba.
A gurguje na kammala uzziri na koma na rufe dakina. Ina idar da sallah na yi
kwanciya ta. Sai tara da kadan na bu'de k'ofar dakin, domin barci na yi mai nauyi.
Ina bu'de wa kuwa ya shigo da sauri.
Ya ce "Kin tashi? Sannu ya kwanan bakunta?"
Uffan ban ce ba.
Amma wani irin bakin ciki ne ya turnike ni. A dalilin rashin bandaki a cikin daki.
Na hakaito kusan duk wadanda muka taso tare ko wacce band'akinta a dakinta ne.
Na tuna gidan J da na Nura, hatta Nasiba band'akinta a dakinta ne sai ni ce na samu
dakuna tamkar na Islamiya tunda na ga falon ma daban ne ba'a hade suke ba".
Sai kawai na fashe da kuka mai sauti sosai.
Ya diririce ya ce "Daga tashi sai kuka Asiya?
Tun dazu fa nake zaman jiran ki tashi ki karya.
Ina son na fita muyi sallama da abokaina zasu koma garuruwansu".
Ban ce masa komai ba. Illah kukan da nake yi mai tsananin cin rai da nuna
k'ololuwar ba'kin cikin da mai yinsa yake ciki.
Ya dinga rarrashi yana Fa'din "Ki yi ha'kuri Asiya komai zai dai-daita, daure ki
tashi ki yi wanka anjima ka'dan zaki fara yin baki, duk wadanda zasu tafi yau sai
sun biyo sun gan ki. Ina ganin kafin Babah ta wuce Bulkachuwa ma sai ta zo, idan ta
ganki a hakan kinsan ba zata ji da'di ba."
Gaba'daya ya rikice ya ce wannan ya saki, ya ce wancan.
Da kuka na ce "Ni ban ta'ba hasko zan shiga gida mai bandaki a waje ba. Gaskiya an
cuce ni, an gama da ni. Na saka fashewa da kukan da yafi na farko tsanani.
Hankalinsa ya tashi domin a ki'dime ya tattaro ni.
Na zabura na k'wace ina sake jin taikacinsa tamkar na rufe shi da duka. Jikina har
bari ya dauka domin lokacin ne karon na farko da jikin namiji ya rab'i jikina irin
haka.
Da muryar kuka na ce "kada ka kuma ta'ba ni. Bana son ka, bana ko son ganin ka".
Ya rasa yadda zai yi da ni. Ya zauna a gefena cikin rashin abin yi.
Tsawon lokaci ina shesshekar kuka.
A hankali ya ce "Ko na samo miki katon baho sai ki yi wankan anan idan kin gama sai
na dauke na gyara wajen".
Yadda ya yi maganar sai na ji wani irin abu mai kama da tausayinsa yana neman kama
ni.
Na sassauta kukan nawa. Amma ban kula shi ba, bare na tanka masa.
Ya sake lank'awasa harshe ya ce "Ki yi ha'kuri Asiya! A yanzu bani da halin irin
gidan da kike mafarkin samu. Ban ta'ba jin takaicin ta'adin dukiyata da na dinga yi
ba irin yau. Amma ina ro'kon arziki ki yi mini ha'kuri . Da ikon Allah zan yi aiki
tukuru dan na cika miki burin ki. Na miki al'kawarin matu'kar rayuwata da taki ta
kai lokacin da zan yi miki ginin da zai dace da ke, to ke zan bawa zabin yadda za'a
fasalta ginin".
Na ja tsaki na ce "Duk kana nufin ina nan tare da kai, ina kuma dakon ganin wasikar
jaki irin taka?"
Idonsa ya kad'a ya ce "Ni na sani Allah zai taimake ni, dan haka ba wasikar jaki
nake yi ba".
Na ja bakina na tsuke. Ya dinga magiya tamkar zai fashe da kuka akan na je na yi
wanka.
Da k'yar na yarda na tashi sai dai ban yarda na tube kayana akan idonsa ba.
Sai da ya fita. Sannan na cire. Na dauko sabon zanina gyauto guda. Na daura na saka
hijabi. Na bu'de akwatin da na shirya kayana a ciki.
Na ciro soson wanka da sabulu da burush, hadi da makilin. Na ajiye tawul akan
gadon.
Na fito na tarar da shi zaune akan baranda duk jikinsa ya saki babu kuzari a tare
da shi tamkar ba Bulkachuwa wanda baya barin ta kwana ba.
Yana ganin na fito ya mik'e ya dauki botikin da yake gabansa cike da ruwa.
Ya nufi band'akin.
Na dakata ya fito, ya kalle ni ya ce "yanzu na janyo miki a rijiya da dumi tunda
garin da zafi."
Ta tafasa ban ce ba.
Na shiga na turo kofar na sanya sakata.
Ina wanka ina ayyana, ina ma a cikin daki bayin yake?
Dan karami amma ko ina tayals ne.
Na fahimci sabon gini ne mune muka fara zama a ciki.
Sosai na yi wanka.
Sai da na alwala da kuma brush sannan na fito. Na shiga daki na tarar da tsintsiya
a hannunsa tabbacin shara ya yi mini. Ga gadon ya gyara tamkar gyaran mace.
Daga kasa kuma kwanukan abinci ne.
Ko kallonsa ban yi ba, bare na yaba masa ta hanyar cewa sannu ko na gode.
Ya kalle ni ya ce "Bari na baki wuri ki shirya".
Ya juya ya fice.
A hankali nake shafa mai tamkar mai ciwo sannan na goga powder. Na shirya cikin
sabuwar atamfa ta Buyers Batik. Doguwar riga ce amma dinkin ya yi kyau domin a Jos
aka dinko mini.
Gata shudiya ce sosai aka yi mata yarfen ja.
Tsaya fa'din yadda farar fata ta haska atamfar bata lokaci ne.
Na goga rol on din Nivea a raina sai tsaki nake yi ina fa'din da an bar ni da
kwamishina ko Yaya Jabir da tuni roll on din oriflame zan dinga tu'amalli da shi
dama sauran product dinsu gaba'daya.
Tunda su zance a zubo mini a lefena.
Na fesa turaren Far-away, na shafawa lebena jan baki mai jan duhu.
Gefe na ajiye jan mayafi Wanda ya dace da atamafar.
Da yake yanzu a hutar da mata bata lokaci wajen daura dankwali ana ta yin huluna.
Nima hular aka yi mini.
Ai kuwa na kafata a kaina na isa gaban madubi ina daidita zamanta.
Ni da kaina na dinga fa'din "Fatabarakallahu ahsanul khalik'in.
Sosai na yiwa kaina kyau.
Maimakon na zauna sai na tsinci kaina da son yin walaha tunda na yi alwallah kafin
na fito a band'akin.
Na idar na tsaya ina kallon dakin.
Madaidaici ne sannan kayan gadona suma matsakaita ne masu sau'kin ku'di. Amma sun
yi kyau babu laifi.
Labulayen sun fi komai dqukar hankalina, ledar tsakar dakin ma mai kyaun aka saka
mini wacce za'a kwana biyu bata fatattake ba.
Na bude akwatin na dauko wayata na kunna. Na koma bakin gadon na kishingida ina
dakon ta gama daidaita.
Ina cikin dube dube ya shigo shima tamkar alamara ya sanya shudiyar shadda irin
shud'in atamfar jikina.
Zuciyata ta harba da tsananin gaske. Domin komin k'in da nake yi masa tun fil'azal
nasan yana cikin yan ka'dan da Ubangiji ya yi masa kyaun fuska da kuma ciakken
zati.
Da walwala ya ce "Amarya kin sha kyau. Nan gaba fa idan zuciyoyinmu suka zama
aminai ba karamin gidan farin ciki zamu gina ba.
Tun yanzu zabin zuciyoyinmu ya zo d:aya.
Mun sanya kaya iri daya ba tare da mun shawarci juna ba".
Na zabura na cire hular na bu'de akwati ina laluben wasu kayan.
Da sauri ya karaso kusa da ni.
Ya ce "Dan Allah! Ba dan ni ba. Dan alfarmar Annabi ki bar kayan ki, sun miki kyau
ainun. Ina ta fa'da miki baki zaki ta yi yau. Ni fita ma zan yi".
Magiyar da ya yi ta sace mini guiwa na fasa canjawar.
Ya bu'de flask din abinci ya ce "Wannan doya ce da kwai Salisu ne ya aiko mana.
Ya bu'de d'ayan kuma masa ce itin tamu ta mutanan Bauchi da kuli kuli.
Ya ce wannan kuma daga gida aka kawo ga kuma kunu".
Yana nuna mini jug din.
Ya sake cewa "Na tafasa miki shayi na dauko miki?"
Ina kallonsa amma ko motsi ban yi ba bare na tanka shi.
Bai yi fishi ba, ya mike ya dauko flask din shayi wanda nawa ne a cikin kaya ya
dauko.
Ya koma ya dauko kofina da kayan hada shayin a leda wanda alamu suka nuna siyowa ya
yi.
Ya zauna ya ce "Sauko to mu karya".
Na sake sharewa.
A hankali ya ce "Da ace kin ji nasihar da aka yi ta yi Miki, iya ta jiya kacal da
kin raga mini, domin dai ko ya ya nake ni din Ubangiji ya za'ba miki ya zame miki
miji. Shi kuwa miji komin kashinsa ai daraja ne da shi."
Na yi kamar ban ji ba, na cigaba da danne danne wayata.
Ya karya, ya kwashe kwanukan da ya yi amfani da su.
Ya dawo ya ce "Zan fita Asiya. Zamu je yiwa iyayenmu ban gajiya. Nasan ba zaki yini
da kewa ba yau".
Ya sake cewa sai "Na dawo".
Daga hakan ya juya ko uffan bai sake cewa ba.
Sai tashin mashin dinsa na jiyo.
Yana fita na sauko na karya.
Na kai ragowar kicin.
Na tsinci kaina da son karewa gidan kallo.
D'akuna biyu ne a jere akan baranda.
Sai kuwa guda daya daga can gefe kusa da bandaki.
Sai kicin a dayan gefen.
Gini ne ba laifi gashi ya sha fenti. Kan barandar ma tayals ne. Haka kicin dinma.
A fili na ce "ko me ya hana a saka tayal a dakin?
Na kalli yadda aka k'awata
mini kicin din da kayayyaki. Na sani kuma mafi yawa dangin mahaifiyata ne suka zo
da kayan.
Da sauri na nufi d'akin da yake mak'wabtaka da dakina wanda na tabbatar shine
falon.
Ina shiga na ji sau'kin takaicin da nake ciki.
Domin dai falon ya yi kyau daidai na masu karamin buri.
Kujera ce irin mai L din nan. An saka ta a bango guda, da yake falon ma an saka
tayals sai aka saka madaidaicim kafet a tsakiyar falon.
Ga kuma TV an mak'ala a bango, sai fridges daga can gefe.
Shikenan sai labulaye kalar kujeru da kafet din wanda suka kasance royal blue ne.
Ga katon agogo mai kyau shima an kafa shi.
Na zauna ina jin da'din yadda na ga wajen. Na sani da ace Yaya J ne mijin tabbas da
na kasance cikin farin-ciki mai yawa.
Na kunna fanka ganin da akwai wuta.
Na fita na nufi daya dakin da ya fi kusa da band'aki.
Na leka na ga bashi da girman wanda aka saka mini gado a ciki.
Ba komai sai labule. Gefe kuma akwatin kayansa ne da tarkacensa sai takalmansa.
Na janyo kofar kamar yadda na ganta a sakaye na fito.
Na koma falo ina jin dau'kin tv na kama ni.
Duk kokarina na kasa ha'da ta.
Dole na hakura na kashe na jona wayata a caji.
Na zauna iska.lr fanka tana kad'a ni.
Ina haka sallamar babbar mace ta saka na zabura ina amsa wa.
Na marabce ta da sakin fuska duk da dai ban gane fuskarta ba. Sannan a kallon farko
na fahimci ba bahaushiya ba ce, tunda ga siffarta har tsagun da suka cika faffadar
fuskarta
Na gaishe ta da girmama wa tunda na ga zata haife wacce ta fini ma.
Ta ce "Ni ce a waccar kofar. Suna na Gadatu. Ana kirana Maman Safiyanu. Mijina
bara ya rasu, ina da yara maza da mata. Allah ya sanya alheri.
Allah kuma ya zaunar da mu lafiya.
Na yi k'asa da kaina. Na tashi na kawo mata cin cin da dubulan.
Bata ci ba. Na juye mata a leda ta tafi da shi.
Bata Jima da tafiya ba sai ga y'arta da alamu suka nuna zata girme mini. Gata da
garin jiki. Doguwa ce sannan a koshe take ainun. Ta ce "wai Mamansu ta ce na bada
kasko a kawo mini garwashi ko zan yi turare.
Na dauko na bata, fuskata a sake.
Ta kawo mini kuwa. Na tambayi sunanta ta amsa mini da cewa "Rafi'a" Na ce "To na
gode miki".
Na zuba turare nan da nan gida ya kaure, ya zama na amaryar sosai.
Ba jima wa kuwa jama'ar Kangire suka zo motarsu guda, suka dinga addu'a da jan
kunnena akan bawa marar d'a kunya na zauna lafiya da mijin da Allah ya za'ba mini.
Daga haka suka tafi wanda kai tsaye Kangiren suka wuce.
Haka kuwa aka dinga shigi da fice.
Hatta Babah ma ta zo kafin ta tafi Bulkachuwa ta dinga yaba yadda ta gan ni.
Tare da su Nasiru da Ihisan ta zo.
Da kulawa mai yawa ta ce "Duk abin da zai miki kada ki biye shi waya kawai zaki
dauka ki sanar da ni, ni kuwa zan miki maganin matsalar. Ki yi hakuri, ki yi
biyayya, ki yawaita addu'a. Sannan ban da rashin kunya.
Allah ya yi miki albarka."
Kuka kawai nake yi. Kukan da bansan dalili ba, ban saniba ko dan na ga ita ma
hawaye take yi. Bansan kukan da take ta faman yi ba, na farin-ciki ne ko na
tausayina ko kuwa na yadda aka juya al'amarin ne oho.
Ashe tare suke da shi ya coge a tsakar gida.
Sai da suka fito sannan ya bi bayansu ya rakasu.



*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta
sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar
taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi
muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun
san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa,
mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai
soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan
littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan
numbers*
*08089965176*
*07084653262*

✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR
TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*

*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.


*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin
register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*.

37&38.
Da yamma lis sai ga Yaya Ummi da tarkacen su tsintsiya da sauran kayayyaki har da
su kuloli masu kyau da zannuwan gado na sani wanda aka samu na gudunmawa ne aka
karo zabo mini masu kyaun cikinsu.
Ta sake gyara mini kicin din. Na bata tarkacen robobi da wani flask din roba irin
mai biyun nan.
Kayan lefena kuwa turamen atamfofi biyu na bata da hijabi hadi da kayayyakin
kwalliya.
Ta dinga yi mini addu'ar Allah ya zaunar da ni lafiya.
Ta bu'de jakar hannunta ta dauko wata yar roba mai dauke da garin magani kore. Ta
sassauta murya ta ce ko zaki dinga shan wannan a cikin madara ko yoghurt?"
Na kar'ba na ce "Na menene?"
Ta yi k'asa da kai ta ce "farin ciki da dokin juna zai sanya muku"
Na yi maza na mayar mata cikin jakarta. Tare da cewa "Da dai ba irin wannan mutumin
aka aura mini ba."
Ta ce "shikenan da har da INGANTATUN SAIWOWIN DAHUWAR GIMBIYAR KAZA. Amma zan ajiye
miki. Na sani wataran zaki nema da kan ki.
Idan kuma na yi amfani da su, sai a kawo miki wani ta hannun kanwar kawata Aisha
Lame mai siyar da kayan kwalliya masu daraja (oriflame).
Tasan Surayya Dee da take kawo su daga chadi.
Baki na tab'e baki, ina kallonta kawai, domin har abada ni Yabi bazan yi wani abu
dan na sanya Tijjani farin ciki ba.
Muna haka ya shigo, suka gaisa sosai cikin walwala da tsokanar juna.
Bai jima da dawowa ba, ta yi haramar tafiya nata gidan.
Da yake mutumiyarsa ce.
Ya ce "Ta jira ya kai ta a mashin".
Ta galla masa harara da cewa "Ni zaka goya Yaya Bulkachuwa?Wallahi ba zan sake biye
wa tsokanar da kake yi mini ba, dan ka riga ka zama k'anina".
Ya kwashe da dariya ya ce wannan kuwa shine tatsuniyar gizo da k'oki. Ke yanzun
nuna mini kika yi Asiya Toro ta fini a wajen ki?"
Ta mak'e kafa'da ta ce "Ato Wallahi ka kama k'afata dai".
Ya tsugunna a gaban ta ya ce "Dai-dai ina zan kama Ummi?"
Ta yi gaba ta bar shi tana fa'din "Hmm sai ka yi kai ka'dai".
Ta goyi y'arta shi kuma ya d'aukar mata ledar kayanta.
Ya yi gaba ya na jiranta.
Da k'yar muka rabu. Cikin lallashi take ta nanata "Ki zauna lafiya, ki kwantar da
hankalinki da na iyayenmu dan Allah. Kin ga dai an riga an yi auren nan. Allah ya
taimake ki, ya hore miki shi. Nan da wata daya ki cigaba da sana'ar ki, domin mace
mai neman na kanta ta huce takaicin babu".
Ta bata rai ta ce "kinsan dai ba'kin cikin da na kwankwada a dalilin bani da
yar'uwar da aka aurar da muke daki daya. Yanzu murna nake yi kema an aurar da ke na
samu abokiyar ha'di. Komai ya taso miki ni ce a hakku saura ki ce zaki bayar da ni
a wajensu ta hanyar nunawa duk daya muke ni da su a wajen ki.
Gasu nan su hudu ne dakinsu daya."
Nima na bata rai na ce "To idan hakane ita kuma Ubaida dawa zata hada kai kenan?
Ko so kike

Please Login or Register in order to submit comment