You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake yi ba.
Kishin Bulkachuwa ya shak'e shi k'warai da gaske. Domin idan gaskiya zai fa'da ya
ga son Yabi a idonsa irin wanda bai yi zaton Tijjani zai yi mata ba. Mussaman yadda
bai dauki soyayya da muhimmanci ba. Mace tana bata masa rai zai juya mata baya duk
yarda yake da ita kuwa.
Ina kuka, ina kallon Yaya J. Na sani dan na yi ba'kin ciki ya sanya Bulkachuwa sako
maganar Maijidda. Ban da haka mene ne dan ya nuna kulawa akan matarsa ta aure?
Nan da nan zuciyata ta hassala cikin rawar murya na ce "Mene ne dan ya kula da
lafiyar Iyalinsa? Tabbacin nima zai kula da ni ke nan tunda har ya yiwa wacce baya
so adalci to ina kuma a ce ni ce da yake so? Kai sau nawa ana ganinka da
tambadaddun matan banza?"
Take jikin Yaya J ya yi k'wari domin yasan yadda nake da kishi na gaske, maganar
Bulkachuwa na iya tunzura ni na yi masa fishi. Dan haka ya dan murmusa. Sannan ya
ce "Ko yanzu na mutu a sanadin rashinki ba ni da kaico tunda kin mini kyakkawar
shaida Yabin J".
Da rawar murya na ce "Idan ka mutu, kuma ka bar ni da wa? Wanne irin ba'kin fata
ne, akan me zaka mini fatan irin wannan asarar haka?"
Tijjani ya harzuka ya ce "Ba zaka mutu ba ka ga yadda Asiya Toro zata manta da
al'amarinka ba Jabiru.
Ya sake sakin tsaki sannan ya ce "Idan kuwa har ka mutu ba wanda ya yi asara irin
abin da yake cikin Maijidda, sai kuwa ita Maijiddan, da zata shiga takabar mijin da
yake sonta yake gudun bacin ranta".
Na sake fasa kuka ina fa'din "Allah ga Tijjani nan ya takura ni, ya fitine ni haka
siddan, ka sani bana sonsa, ka gaggauta cire mini shi a duniya ta".
Sai lokacin Yaya J ya ce "Yi hakuri kin ji Yabi! Ko zan mutu ba yanzu ba, da saura
In sha Allah".
Na wuce na fara tafiya a hankali.
Bulkachuwa ya ja tsaki ya ce "k'aryar banza! Dan Allah ka mutu yanzu Jabir. Da an
ga tsiya domin kuwa ana dawowa daga rufe ka zan lallaba na koma. Tamkar wanda zan
yi maka addu'a. Nan kuwa fitsari zan tsula maka a kabarinka ta yadda sai ka shekara
a kwance kafin addu'ar jama'a ta riskeka, mussaman ta Asiya Toro. Kai da addu'a ta
riske ka sai damina ta zo. Idan na so k'eta ma, daminar na dauke wa na sake tsula
maka wani. Kuma idan juninka tsiya ne Maijidda na haihuwa zan aure ta. Na ha'da su
da Asiya Toro su yi ta faman buga competition a kaina".
Na juya da nufin na yi masa raddi ya nuna mini yatsa ya ce "Idan kika kuma tozarta
ni sai na fasa miki bakin ki domin ban yi da ke ba, marar kishin kai".
Jabir ya yi hanzarin ce wa "Kar ki ce komai Yabi cikin yanayi na kad'uwa sosai.
Ya kalli Bulkachuwa ya ce "Har zaka iya yi mini fitsari a kabarina Bulkachuwa?
Sannan ka ce "zaka auri matata akan idona?"
Wani irin murmushi Bulkachuwa ya yi mai dauke da nisha'di da ma'anoni.
Ya ce "In dai son Asiya ya zama ajalinka zan tabbatar na hana adduarta riskar ka.
Sannan dan na auri Maijidda ai rufa maka asiri na yi tunda tare da abin da ta haifa
zan ha'da na rikesu. Idan kuwa kana kishinta kamar yadda yanayinka ya nuna har ka
kasa ha'diye hakan a gaban wacce kake kirarin kana so. To kawai ka k'yale mini
Asiyata.."


*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.


*Zuma ta mussaman*
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku
kayan cikin sauki da mututantawa*.
*08032773332*


✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR
TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*

*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.

*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered,
Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan
farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon
yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.


"Shikenan idan ka yi haka ba zan maka fitsari idan ka riga ni mutuwa ba. Ba kuma
zan aurar maka bebinka ba, tunda wani irin so kake yi mata wanda baka iya b'oye
kishinta a gaban kowa"
Ba'kin ciki mai tsanani ya lullub'e ni.
Na kasa bu'de baki na ce komai domin na tabbatar yana iya fasa mini baki kamar
yadda ya fa'da din tunda baya fa'dar magana da zummar wak'e.
Na juya na tafi, ina tafe ina hawaye, ina kuma ha'da hanya. Domin idan akwai abin
da yake ci mini zuciya bai wuce a mini zancen Maijidda ba.
Na kuma fahimci Bulkachuwa yana son bani labarin irin tarairayar da J yake yi mata.
Na tuna tun kafin zancen aurena da shi ya b'ullo, ya sha fa'da mini yana ganin Yaya
J goye da Maijidda a mashin dinsa.
Har na isa gida kukan sharbe nake yi.
Na shiga dakinmu na zauna bakin gado ina kuka sosai.
Domin abin ya ha'de mini, ga bacin ran auren dole da mutumin dana tsana ga kishin
Maijidda da yake azalzalata tamkar zuciyata ta fa'do kasa.
Gwaggo ta kalle ni ta yi k'wafa tare da fa'din "ki yi ta kuka har hawayen idonki
su k'afe, aure kuwa kinsan babu fashi".
Ta fice ta bar ni.

*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*

*Dada*
Bulkachuwa zaune a kusa da ita kan baranda sai faman bacin rai ya ke yi.
A hankali ta ce "To menene zaka tisa ni a gaba kana ta faman k'unci kaki fa'da mini
damuwar ka?"
A hankali ya ce "Jabir ne mana ba dama Yabi ta fita sai yasan yadda ya yi ya tare
ta. Gaskiya abin ya fara tayar mini da hankali, ki fa'da masa ya bari".
"A sanyaye ta ce "zan fa'da masa kaima ka kara hakuri duka kwana nawa ya rage ne?
Ai da zarar am shafa mata fatiharka dole kuma su kiyayi juna."
Bai kai ga amsa mata ba, ya ga masu aikin gini da fenti sun shigo da kayan aiki sun
shige k'ofar ciki".
Ya kalli Dada ya ce "me suke yi a ciki ne?"
Da walwala ta ce "Tun dazu suke fama, sallah suka je yi. Kawunanka suka saka a
gyara maka wajen sun ce bai kyautu su barka da neman muhalli ba".
Ransa ya baci ya ce "Shi Baban Tsakiya ne zai ce haka?
Me yasa bai mini gini irin na Jabir ba?
Idan kuwa Baban Kasuwa ne me yasa ya hana Salisu zama a lokacin da ya roki a bashi
ya zauna kafin ya samu sararin yin nasa?"
To bana so, na sani kuma Yabi ba zata so wajen ba, ya yi tsufa da yawa".
Daga haka ya tashi ya barta tana faman buga salati tare da fa'din "Ni Binta ina
kallon wuyar zama irin ta y'ay'an yau. Komai aka yi musu babu mutunci bare su yi
godiya.
Wannan zamani da wuyar sha'ani yake".
Ta yi k'wafa sannan ta sake cewa "Allah na yi tuba, kai ne mamallakin zamani. Allah
ka shirya".
Har washagari bani da sukuni, a kuma wannan ranar aka kawo mini lefe daga
Bulkachuwa.
Sosai aka zuba kaya a lefen tamkar na masu wadata. Na sani kuma y'anuwan ubansa da
Babah ta Bulkachuwa suka hada kayan, sisinsa bai yi ciwon kai ba.
Maza ne suka kawo kayan dan haka ba ayi gayya ba.
A k'ofar Dada aka taru aka ga ni, masu fatan alheri na yi, masu shagube na yi.
Sai da ya kwana ya yini a wajen Dada sannan ta saka aka kawo kofarmu.
Hatta Babanmu sai da Inna ta bu'de masa kayan ya ga ni, ya yi addu'ar alheri tare
da fa'din "Oh haka suka yi wahala mai yawa?"
Ni kuwa ko kallon kayan ban yi ba, bare na ga mene ne a ciki.
Da yamma ina zaune ina k'ulla wa Gwaggo siga.
Sai ga Anas ya shigo ya kalle ni ya ce "Dada ta ce ki je yanzu".
Na bata rai na kasa amsawa domin na tsani na je kofarta saboda dalilai masu dama.
Na farko haushinta nake ji.
Sannan bana son ganin mawuyacin halin da nake ganin Nasiba a ciki. Domin sosai ta
mak'ala wa zuciyarta son Bulkachuwa. Kishina sai ya galgalata yake yi, duk da bata
bu'de baki ta mini maganar ba, sai ma murnar da ta yi mini na samun miji irinsa
wacce na ji tamkar ta caka mini wuk'a ne. Wannan shine daidan wani, karkataccen
wani.
Sannan kuma ina sake k'in shiga wajen Dada ne saboda kada na ga Tijjani. Shi yasa
ma bana zuwa gaishe ta sai hantsi ya yi sosai.
Gwaggo ta ce "Je ka ce tana zuwa".
Ya ce "To" ya tafi.
Akan dole na dauki mayafi na nufi shashin Dada.
Ina hasashen menene dalilin kiran?
A zauren Dada na tarar da shi a tsaye. Zuciyata ta tsinke sosai. Na yi kamar ban
gan shi ba. Na wuce da nufin shiga cikin gidan.
Ya bu'de baki ya ce "Ni ne mai kiran na ki ai".
Na tsaya cak. Ba tare da na iya ce wa kanzil ba.
Ya saki gauron numfashi kafin ya ce "Ga ni na yi abu ya matso kusa sosai amma babu
fahimta a tsakaninmu bare nasan abubuwan da kike bu'kata".
Na ja tsaki na ce "auren so ake yiwa irin wannan tagomashin".
Fuskarsa ta yamutse kadan. Ya ce "To na biyayya fa?"
Nan da nan idona ya ciko da hawayen takaici. Na yi k'asa da kaina na kasa ce wa
komai.
Murya babu amo ya ce "Abokina da muka yi karatu a Gad'au gobe zai zo.
Ya dame ni akan na ba shi lambar amarya ko na kawarta dan ya ji irin yadda ake
sallamar amarya da kwayenta a nan, da kuma abubuwan da kike bu'kata".
Na ja tsaki tare da ce wa "Komai zai fito ta hannun ka ko ta sanadin ka bana sonsa
ba kuma zan kalle shi ba."
Ya zuba mini ido sosai cikin damuwa mai yawa.
Cikin wani irin yanayi ya ce "Asiya Toro alfarma d'aya nake so ki mini, ko da kuwa
ita ka'dai ce alherin da zaki yi mini. Ki taimake ni kada ki tsinka ni, ki yi mini
wannan arzikin dan Allah".
Ban san ya aka yi ba, jikina ya yi sanyi, mussaman yadda na ga ya yi kalar tausayi
tamkar ba Bulkachuwa ba.
Na yi shiru amma fuskata a cukune sosai.
Ya sake ce wa "ki bani lambar wacce zai yi magana da ita Asiya. Sannan idan sun zo
mini ranar daurin aure kada ki wula'kanta ni a gabansu. Na yarda bayan sun tafi ko
menene ki yi mini, zan jure".
Na sake gallah masa harara tamkar idona zasu fa'do k'asa. Tare da ce wa ban iya
Yaudara ba, ba kuma zan fara yanzu ba. Ai na sha jin kana fa'dawa abokan naka ba
macen da zaka aureta alhalin kasan bata sonka. Ba ayi macen da zata ce baka yi mata
ba, sannan ka nace sai ka aure ta, duk wanda ya sanka yasan wannan alwashin na ka.
To me yasa yanzu ka yarda zaka aure ni alhalin kasan bana son ka, bana farin-ciki
da al'amarinka gaba'daya?"
Kuka ya k'wace mini sosai.
Murya babu amo ya ce"Kaddara ta ce a hakan Asiya! Ni kaina na kasa gane kaina.
Wata'kila cika bakin da na yi ta yi ne, ya sanya aka jarrabe ni da son auren wacce
ta washe ni, wata'kila kuma Ubangiji ne zai mini wani alherin ta sanadin ki shiyasa
ya jingina mini sonki mai yawa."
Na sake jan tsaki na ce "Ba wani alheri domin da zan ga sadda zai tunkare ka zan
karkatar da shi na bawa wanda suka fika mutunci da so na".
Ya girgiza kai ya kasa magana domin ransa ya baci idanuwansa har canja wa suka yi.
Tsawon sakwanni bai iya ce wa uffan ba.
Ni kuma sai fama nake da kuncin zuciya. Sannan sai yanayinsa ya sanya na ji babu
da'di, domin duk yadda na tsane shi. Sai na ji ya d'an ba ni tausayi ka'dan.
Muna haka Baban Marina ya dawo, ya zo wuce wa ta babban zaure ya hango mu a zauren
Dada.
Ina kallon yadda yake murmushi yana amsa gaisuwar Bulkachuwa da walwala.
Ni kaina a wannan lokacin ya sace da fishin da yake yi mini. Domin da murmushi a
fuskarsa ya amsa barka da zuwan da na yi masa.
Har yana fa'din "Sannunku Yabi"
Kunya ta saka na yi nufin shige wa wajen Dada. Sai ce wa ya yi "Dawo ku cigaba da
tattaunawarku. Allah ya yi muku albarka. Allah ya sa ku zamo abin alfahari, Allah
ya shiga al'amarinku".
A hankali Tijjani yake amsa wa yayin da ni kuma ban amsa ba ko da a zuci ne.
Yana shige wa ya kalle ni a sanyaye ya ce "Asiya Toro Baban Marina bai dauki auren
nan namu da wasa ba fa. Mu ha'da kanmu, kada mu ba shi kunya dan Allah".
Na ja tsaki tare da ce wa "Ni Malam na gaji tafiya zan yi".
A sanyaye ya mik'o mini wayarsa ya ce "Saka mini lambar"
A tunzure na ce "Ba ni da k'awa".
Da sigar lallashi ya ce "Yanzu duk ro'kon da na yi miki?
Farin cikin da Baban Marina ya yi a dalilin ganinmu bai sa zuciyarki ta rusuna ba?"
Na murguda baki na ce "To ai dai kasan ba ni da k'awaye, Adda Nazira ce kuma ta yi
aure, sai kuwa Nasiba ita ma kuma ai auren ta za'a yi ko?"
Ya girgiza kai ya ce "Hakane! To Ina wannan fara mai dan jikin nan da yanzu kuke
dawowa daga boko tare? Sannan tare nake ganinku a wajen koyon kwalliya".
Na zuba masa harara na ce "Tsabar sawa mata ido har ka gane halittar ta?
Har abada ba zaka burge ni ba Tijjani. Ba kuma zan baka lambar ba, domin dai da
bakin ka ka tabbatar mini nema cikin nema haramun ne. Bari na shaida maka tuni an
kai ku'din aurenta. Dan nasan kana iya lallabawa wajen ta".
Ya yi sororo sai kuma b'acin ran fuskarsa ya ragu.
Ya ce "Bana ma son lambar, na fasa, zan ba shi lambarki sai ki fa'da masa ta yadda
zai turo miki ku'din kunshi da na kitso, ya damu akan a sallame ki ke da kawayen ki
ne".
Na yi shiru ban ce komai ba.
A hankali ya ce "ya yi miki hakan?"
Na sake yi masa banza.
Ya sassauta ya ce "please mana Asiya Toro".
Na harzuka na ce "Gaskiyar magana baka yi mini adalci, idan ina kaunar yadda kake
gatsa sunana ha'de da na garina Allah ya tsine mini!.
Ya dan murmusa ya ce "Da sannnu idan kin kwantar da hankalinki zan daina fa'da, na
samo miki sunaye masu da'di da tsuma zuciya".
Ba'kin ciki ya sake turknike ni. Na ce zuciyar waye din zata tsumu?"
Ya make kafa'da ya ce ta "Asiya Toro".
Na yi kwafa na ce "Ai na gane zuciyarka babu alheri ne shi yasa kake k'yashin ce
mini Yabi. Da'din abin ma dubun ka suna fa'da mini cikin girma da arziki".
Ya ce"Nan da lokaci ka'dan komai zai zama tarihi. Kin ga dai na nemi arzikin ki,
ban kuma mayar miki da martanin bakaken maganganun da kika yi ta yab'a mini ba. Ina
sake ro'kon ki idan abokina ya kira ki, ki taimake ni kada ki bayar da ni."
Ban amsa ba. Ya sake cewa dan Allah Asiya Toro".
Cikin fishi na ce "Na ji".
Da'di ya kama shi ya dinga fa'din "Na gode sosai. Ina fatan na ga ranar da zaki
fahimci irin tarin alkhairorin da suke zuciyata mussaman akan lamarin ki".
A hanzarce na ce "Ai kuwa dai ba zaka ga ranar ba".
Ya girgiza kai tare da ce wa "Babu damuwa time will tell".
Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ina son na tambaye ki, zaki iya zama a wanccan daya
bangaren na Dada?"
Maimakon na yi masa magana da baki, ai sai kawai na d'ora hannu aka na fashe da
wani irin kuka na tashin hankali.
Murya na rawa na ce "wato dai a cikin masifar gidan nan zan tabbata? Idan kuwa har
a cikin gidan nan ake nufin na zauna da sunan zaman aure Allah ya dauki raina kafin
hakan ya tabbata. Na shiga uku ni Yabi".
Ya rikice ya hau fa'din yi shirun ki dama na fa'da mata wajen ya miki local da
yawa, sannan baki samu sauyin muhalli ba. Yau din nan duk inda gida yake zan nemo
kafin dare. Da ku'di a hannuna.
Yi hakuri ki daina irin wannan kukan. Kin ga yadda kika koma kuwa Asiya?"
Da k'yar ya lallaba ni, na yi shiru.
Ya zura hannunsa a aljihu ya ciro cakulet manya masu da'di da tsada k'waya biyu ya
mik'o mini.
Bansan ya aka yi ba na fashe da dariya ga kuma hawayen ba'kin ciki na ziraro mini.
Da yake d'an duniya ne sai kawai shima ya fashe da dariyar yana cewa "Ni nasan
Ubangiji zai cusa miki soyayyata dan yasan yadda ya gina ki a tawa zuciyar. "
Da k'yar na samu dariyar ta tsaya.
Da hawaye a idona na ce "me zan yi da wannan abar?"
Ya zuba mini ido yana wani lumshe su ya ce "Wai fa dan kada na zo hannu na dukan
cinya ya sanya na taho miki da su"
Na rasa me zance masa tsabar takaicinsa da ya d'ada makure ni.
Na ce "To ajiye idan ka ga Yarinya k'arama ka bata amma ba ni ba".
Ya waske ya ce "Asiya Toro maraina ka'dan fa barawo ne. Kowa ba iya karfinsa zai yi
kyauta ba?
Kin san wahalar da na sha kafin na samo miki wannan cakulet din a garin nan? Saboda
nasan kina son ta ne. Amma ban burge ki ba? Idan kin yi hakuri wataran katon zan
siyo na ajiye miki."
Da sauri na ce "da dai ace ba hannun jinjirai ne da kai ba tsabar rowa."
Ya nuna kansa da yatsansa ya ce "Ni ne mai hannun jarirai? Lallai kuwa zan baki
mamaki Asiya Toro local government. Bauchi state of Nigeria".
Ko kula shi ban yi ba na wuce shi na tafi na bar shi a tsaye. Tsabar takaicinsa da
ya sake kular da ni.
Ya d'aga murya ya ce "Sai gobe zan dawo, ko da anjima ma na dawo?"
Da kansa ya bawa kansa amsa da ce wa "To zan dawo da daddaren ran ki ya da'de."
Har na isa k'ofarmu mamakin Bulkachuwa kawai nake yi. Ban da dai ya riga ya same ni
a araha ya rasa me zai kawo mini sai cakulet k'waya biyu. Shi ko kunya bai ji ba?
Amma da na tuna halin rowarsa sai kawai na janye mamakinsa. Na shiga tambayar kaina
wanne irin zama zamu yi ne da shi?
Na tabbatar sassaucin da ya yi dan baya son na yarfa shi ne.
Amma da tuni ya baje mini kalolin rashin mutuncinsa.
Na zauna na fara kokarin cigaba da k'ullin sigan.
Zuciyata ta shiga hakaito mini kayan jikinsa.
Shadda ce a jikin sa kalar ganye wato kore sosai. Ya d'ora hular sanyi mai tambarin
kungiyar Manchester United. Na sani kuma d'an ya boye wa Baba curarriyar sumarsa ne
tunda zafi ake yi ba sanyi ba.
Daga ni tun farar safiya ya sanya kayan a hakan kuma shi ya k'ure malejin kwalliya
ne.
Na ja tsaki tare da ce wa "Idona ya saba ganin samari ma'abota wanka da gayu.
Irinsu Yaya J da Nuru Tanim. Ta ya ya Bulkachuwa zai burge ni?."
Gwaggo ta shigo ta ce "me ya faru da kika je?"
Na yi kasa da kai na ce "Ba Dada ba ce ashe".
Ta ce "To waye?"
Na bata rai duk da kan nawa yana kasa na ce "Tijjani ne".
Daga hakan bata kara ce wa komai ba ta dauki abin da zata dauka ta fice tsakar
gida.
Washa gari da azahar ina kwance a tsakar daki sai ga Nazira ta zo. Karon farko da
ta zo gida tunda aka yi mata aure. Duk rud'anin da nake ciki sai da na tashi da
azama na rungume ta.
Muka haye k'aramin gadon Gwaggo da muke kwana a kansa ni da ita tun fil'azal.
Da murmushi a fukskata na ce "Yau Adda Nazira ce a gidanmu?"
Ta d'aka mini duka tare da cewa"oh har kin cire ni a cikinsa, to kema kwana nawa ya
rage miki mu yi kunnen doki?"
Na bata fuska sosai. Ta ce "daga wajen Dada nake suna can, suna artabu da Yaya
Bulkachuwa akan inda zaku zauna.
Wai akan me zai je ya kama haya tamkar ba shi da kowa a Toro?
Shi kuma ya kafe ba zai zauna a cikin gidan nan ba.".
Na bata rai na ce "Ai Wallahi na fa'da masa indai ya yarda da tsarinsu to kuwa sai
dai a tsine mini dan bazan zauna a gidan nan ba'kin ciki ya karasa ni tun ajalina
bai zo ba"
Adda Nazira ta ce "Haba ashe tirjiya ya samu daga gare ki, kin ga yadda ya
fitittike akan ba zai zauna a wajen ba?
Dada har da kukanta wai sai da ya bari su Baban Tsakiya sun gama gyara masa wajen
sannan ya ce zai fita ya kama haya tamkar wanda bashi da galihu a Toro? Shi kuma
kinsan shi ya ce "Salisu da yake hayar rashin galihu ne ke nan?
Ashe ashe Gimbiya Yabi ce ta saka ya rikice ya turje.
Ya kama miki gida mai kyau a bayan sakatariya. Ba ki ga gidan ba. Yanzu muka dawo a
mashin dinsa ya goye ni muka je ya nuna mini gidan. Ni Wlh har na ji na daina
k'insa. Kin ga rawar jikin da yake yi. Sai fa'di yake ya kika ga wajen Nazira?
Nasan idan ya burge ki to zai burge kanwar ta ki ma.
Gaskiya Yabi ke d'in mai sa'a ce. Gaba'daya kin rikita namiji irin Yaya Bulkachuwa.
Murna nake yi, da dukkan zuciyata nake jin addu'armu ta karbu. Da ikon Ubangiji sai
kowa ya yi mamakin alherin da zai biyo bayan wannan auren."
Na tab'e baki na ce "Hmm ai ni dai an cuce ni kawai. D'azu muna maganar k'awayen
amarya. Na ce masa ba ni da k'awaye, ke ce to kuma kin yi aure.
Yana bu'de baki da yake shi d'in bunsuru ne sai ce wa ya yi wai ina k'awata fara
mai dan jiki. Kin san wa yake nufi?"
Kafin ta ce komai na zarce da ce wa "Shafa'atu yake nufi fa. Har ya k'yalla ya ga
halittu a tare da ita shine zai silala me za'a yi da Tijjani ne. Na fa'da cikin
kunan rai.
Ga mamakina sai ganin Nazira na yi ta k'yal-k'yale da dariya sosai. Sannan ta ce da
wuri haka Yabi?"
Na bata rai na ce 'ban gane ba?"
Ai kuwa cikin ido ta ce" tun yanzu kin fara kishin Yaya Bulkachuwa ina kuma idan
kin shiga hannunsa?"
Hawaye ya b'alle mini ina ce wa "Allah ya sauwake, ashe ba ki fahimce ni ba Adda
Nazira?"

*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA
KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA
KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*

*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR
TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*

*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.


*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA
KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBE TA DAN KUWA DA
KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*

"Tunda Kika kasa gane abin da yake zuciyata ba wanda zai fahimce ni dai-dai".
Na fa'da cikin kuka sosai.
Ta maze ta ce "Ai kuwa dai kinsan na sanki tamkar yunwar cikina. Wata'kila kuma
y'an watannin da muka yi ba tare ba ya sanya na soma mance ki. Amma tunda kin ji
bacin rai a dalilin maganar ki yi hakuri da wasa nake yi shikenan?"
Da haka na fara goge hawayen idona.
Sai yamma lis ta tafi. Na rakata hanya ta hau abin hawa.
Ina kan hanyar dawowa sai ganin mutum na yi tamkar daga sama yana biye da ni.
Bai yi magana ba, bare ni kuma. Har muka iso gida sannan ya ce "Asiya Toro manyan
mata. Na wuce shi na yi shigewa ta. Ina ayyana shi bai san ya kintsa kansa idan za
shi wajen budurwa ba.
Ina shiga na tarar da Babanmu a zaune.
Ko hijabi ban cire ba, sai ga yarinya cikin yaran Baban kasuwa ta shigo ta ce "Adda
Yabi

Please Login or Register in order to submit comment