You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

to ku musanya wa
Yaya Jabir ni da Nazira domin dukkanku nan ba wanda zai zargeta da rashin tarbiya
ko sharholiyar da ni nake yi".
Nan da nan Baban kasuwa ya ce "Anki a bashi ita din dan uwarki, makira, algunguma,
Maijidda ce matarsa har a kiyama kuwa".
Ga mamakina sai na mike na tsinci kaina da cewa "Gaskiya Baban Marina ne ba a so,
shi kuma har yana kora ta saboda ku.
Ba komai Ubangiji ya sanya alheri".
Har na fice ba wanda ya iya bu'de baki ya ce mini kala tsabar kad'uwar da suka yi
da furucina.
Baban Tsakiya ne cikin fishi ya ce "Ba shakka dangin uwar yarinyar nan akwai
majununai".
Na so na tsaya na ce "ko wanne d'a yafi gadon dangin ubansa, dan ya gane sune
majununai ba mutanan Kangire ba. Sai dai kuma duk iyashegena ai wata fuskar tafi
gaban mari, kannen ubana ne, ta ko wacce fuska idan na yi musayar yawu da su ni ce
bani da gaskiya. Sai kawai na had'iye.
Ina fitowa na yi kicibus da Bulkachuwa yana tsaye da buta a hannunsa, tabbacin daga
bayi ya fito.
Na tabbatar kuma ya ji komai har maganganun da aka yi a kansa da Nasiba.
Domin gaba'daya manyan idanuwansa sun kad'a, sun yi jajur.
Na wuce shi ban sake kallonsa ba, kallonsa ka'dai ya sanya na ji tamkar na yi amai
tsabar yadda na washe shi.
Wannan abin da na yi ya sake ki'dima wadannan bayin Allah domin dukkansu ba wanda
maganar bata shige shi ba.
A ranar na koma gidan Yaya Salisu ban san wainar da ake toyawa a gidan Marina ba.
Zama nake yi irin na taka tsantsan a gidan, ba dan komai ba sai togaciyar da aka yi
ta yi mini a gida.
Da safe zan yi wanke wanke da shara, na yiwa dansu wanka shi kenan sai na shige
daki.
Idan ta gama abinci zata mini zubin auki.
Yadda nake gudun bata mata, hakan ita ma take kaffa kaffa dan kada na ga beken ta,
ko idan na koma gida na bada ba'kin labari a kanta.
Ranar da na yi kwanaki hudu sai ga Nazira da Iklima.
Muka yi hira, sun kusa tafiya Nazira ta ce da Iklima ta fita ta jira ta a waje.
Ba musu Iki ta fita.
Ta sassauta murya tabbacin bata son a ji maganar ta ce "Kinsan me yake faruwa kuwa
a gida?"
Na girgiza kai ina fa'din a ina zan sani Adda Nazi?"
Ta sake yin kasa da murya ta ce "wata yarinya ce ta yi cikin shege har ta kusa
haihuwa fa, to ana ta shari'a, da ta lissafo wadanda suke mua'amalantar ta har da
Yaya Bulkachuwa yanzu haka kullum sai sun je kotu".
Zuciyata ta harba da tsananin gaske, na ce "Tijjani gaskiya baya kyauta mana,
gaba'daya sai ya gama ruguza darajar gidanmu alhalin shi ba dan gidan ba ne".
Nazira ta ce "Hmm abin sai ha'kuri ba ki ga yadda ya zama ba, ya kuma kafe akan
ciki ba nasa ba ne ba zai kar'ba ba. Babah ta Bulkachuwa ita ma ta zama abin
tausayi sosai tsabar ba'kin ciki."
Hawaye ya balle mini wata irin damuwa ta shige ni, kishin zumunta ya murde ni, ko
yaya ba zaka so ganin jininka a cikin tozarci ba.
Mun jima a hakan kowa da k'wallarsa ta ce "Jiya Malam Yunus Econs ya aiko a bashi
izinin neman aurena kinsan tunda matarsa ta rasu a wajen haihuwa har yanzu bai sake
wani auren ba, ga yaron nan tuni ya shekara biyu."
Na ru'ko ta ina fa'din "Kai na yi murna sosai Allah ya tabbatar da alheri mutumin
kirki ne, na amince Adda Nazi ta so shi ta bashi dama, Allah sanya albarka a
tafiyar".
Muka fito ina musu rakiya tana ce wa "Abdul sau uku yana zuwa amma Baba bai bari an
fa'da masa inda kike ba."
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA
BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.

Na ce zai bari ne, domin ko Yaya Jabir ne autan maza na bar shi Nazira".
Ta ru'ko hannuna ta ce "Madallah da zuciyar Yabin Marina! Ni nasan zuciyarta ba
zata cigaba da son wanda zata yi kuka a hannun ahalinsa ba, ba zata so wanda ubansa
yake k'yamarmu ba, in sha Allah sai kin auri wanda ya fishi komai, aurensa da
Maijidda kuma bama adawa. Sai kuma kuka ya goce mata, nima hawaye ya sake zubo
mini, domin idan na ce bana sonsa ko abin bai dame ni ba na yi k'arya.
Amma zan nuna wa su Baban Tsakiya ni din yar halak ce ina kishin ubana, ina kuma
kishin kaina.
Babban rufin asirin da Allah ya yi mini shine dama ina da Abdulrashid. Su biyun duk
ina sonsu amma nafi son Yaya J.
Yafi daukar hankalina matu'ka da gaske sai dai zan iya rayuwa da Abdul ba tare da
na takura ba.
Sai da muka yi kukanmu son ranmu sannan muka je gidan Yaya Salamatu, muka bata
labarin halin da ake ciki.
A sanyaye ta ce "Babanmu ne basa so fa, gara miki ma hakan, Allah ya kawo miki mafi
alheri me za'a yi ma da auren dangi irin namu ne?"
Mun jima sosai sannan muka tafi, bayan na bata labarin Malam Yunus da yake son
Nazira.
Ta yi murna, ta yi farin-ciki, ta bamu dari biyar mu hau mashin. Bayan ta bawa
Nazira kaya a leda ta kaiwa Mamansu.
Na koma gidan Yaya Salisu, su kuma suka wuce gida.
Kwanana shida da barin gida sai ga Yaya J a gidan Yaya Salisu.
A matu'kar birkice na ganshi.
Ya kasa mini magana, tsawon lokaci kafin ya ce "Me yasa haka Yabi?"
Ba walwala na ce "me yasa, me ke nan?"
Ya ce "na dauka ko baki ha'da komai da su Baban Tsakiya ba zasu ci darajata bare
kuma iyayenki ne da zasu daura miki aure".
Na bata rai na ce "Bana ma bukatar su mini walittaka Jabir, domin komin kashin
Babanmu da ake ga ni, Ubangiji ya azurta shi da yara mazan da zasu maye mana gurbin
kowa.
Kai ko ba ni da yan'uwa maza a cikin gidan Wallahi Ammar da Bulkachuwa zasu iya
daura mini aure duk da kasancewarsu ya'yan mata ne, amma idan har ya kasance sai ku
to lah shakka zan iya saka hula na wakilci kaina ko kuma na samu alkali ko liman".
Jikinsa ya yi matu'kar yin laushi.
A sanyaye ya ce "Ni yanzu mene ne laifina a nan Yabi?'
Yana rufe baki na ce "Rashin biyayyar ka. Na tabbatar an fa'da maka ka kiyaye ni,
domin ban cancanci ka aure ni ba, saboda mahaifina ba shi da daudar duniya".
Ya yi kasa da kansa ya ce "Ni da ke muke magana ki daina sako mini manyanmu domin
wannan ba dabi'a ce mai kyau ba.
Na gallah masa harara na ce "Madallah"
Na tsuke bakina na yi gum.
Ya marairaice ya ce "Yabi kada ki bari a bada kofar da za'a yi mana farraku, ina
son ki, ina kaunar kasance wa da ke, jikina na bani kamar ma na kusa barin duniyar
nan, ki taushi zuciyarki kada ki zalunci wanda yake tsananin sonki Yabi. Ban miki
komai ba, kada ki hukunta ni da laifin da bani na yi miki shi ba".
Jikina ya yi sanyi. Na kasa magana domin gaba'daya ya d'aure ni da jijiyoyin
jikina. Zufar da take karyo masa ta sanya na sake jin sonsa na taso mini.
Kafin na yi magana sai kawai na tuno maganganun mahaifinsa a kaina, wai ni da nake
matsayin y'arsa, yar dan-uwansa amma ya jefe ni da mafi munin kalma wai ina bin
maza, ke nan karuwa ce?
Bayan ga hakan kuma ya ci mutuncin mahaifina wanda wansa ne.
Take na ji karshen jakanci ne na cigaba da mua'amalantar jininsa da sunan soyayya.
Mussaman da ya ce yana tausayin zuri'ar da d'ansu zai kwaso musu ni.
Na dago cikin karfin zuciya na ce "Jabir mu yi datse wannan soyayyar ka ji, na
rantse maka tun jiya na shak'e ta, na kwashe mata karama.
Babanka ya tabbatar mini Maijidda ya za'ba maka, domin ita ce arzikin ubanta yayi
daidai da shi, ban yi ba'kin ciki ba, domin kullum zabin Allah muke nema.
Alhamdulillah! Na karbi wannan kaddarar da hannu bibbyu, domin Ubangiji na bar wa
al'amarin, ya yi mana za'bi da kansa.
Amma zan roke ka Yaya Jabir ka yi iya kokarinka wajen taka burki a ta'ba mutuncin
Baban Marina da ahalinsa.
Ina jin tsoron kada wannan matsalar ta yi girman da ba zata gyaru ba.
Ina jin tsoron kada a wayi gari a ga gidan Marina ya zama sansanin yaki a tsakanin
jini guda".
A matu'kar birkice ya ce "Allah kada ya kaddara mini ganin hakan Yabi! Ina fatan
mutuwa ta riske ni kafin wannan lokacin"
Na girgiza kai na ce Shi kenan".
Ya marairaice ya ce "Na tsugunna miki Yabi Asiya?
Ki taimake ni, ki fahimce ni, idan kin kwantar da hankalinki ai za'a a samu sulhu
ta sanadin aurenmu.
Sai mu kawo dai-daito, an yi abin da yafi haka muni, kuma an dawo an shirya, kada
ki tsananta, ki yanke mini hukuncin da babu laifina. Allah da kansa baya kama mu da
laifin iyayenmu ko na y'ay'anmu. Daure ki ji tausayina, na rantse idan kin bani
ha'din kai ba abin da zai sa na bar ki komai za'a yi kuwa" .
Na girgiza kai na ce "Idan na yi hakan ba sonka nake da gaske ba.
A gaban iyayenmu Baban Tsakiya ya ce "Idan aka baka aurena Àllah ya isa.
Baya ga hakan kuma ya tsane ni, tsanar da ya danganta ni da karuwa ce ni, kuma ya
ce na zage su, hakan ya janyo ubana ya kore ni saboda shi kullum yana sonsu, yana
musu kyakkawan zato".
Daga haka kuma sai kuka ya subuce mini.
Bai hana ni yi ba, shima kuma idonsa ya ciko jijiyar kansa ta yi rud'u rud'u
tabbacin yana cikin rud'u mai girma.
Da murya kuka na ce "Maijidda ta fini kyau, ta fini gata tunda Babanta mai ku'di
ne, ta fini komai, ka karbi zabin iyayenka na tabbatar Ubangijin adalci zai juya
maka al'amarint fiye da al'amarina, tunda ka yi biyayya.
Zan fa'da maka gaskiya ko zan yaudari kowa bazan yaudare ka ba. Kana da muhimmanci
a rayuwata, da gaske ina ganin mutuncin ka.
Na roki arzikin ka rabu da ni, na riga na ha'kura da kai Wallahi, maganar soyayya
kam ta kau".
Ya numfasa ya ce "Oh! Haka kaddara ta za'ba mini? Na so ace kin saurare ni, na so
ace kin bani dama mun ha'da hannu da k'arfe mun yaki wannan *BAK'AR TA'ADAR* da
take neman zame wa alummarmu tamkar wutar jeji.
Ina cikin zullumin yadda zumuncin yau ya koma tsakanin masu kumbar susa.
Ina cikin takaicin yadda aka jahilci d'an-uba.
Ina matu'kar so a ce kin zama matata ta yadda zamu kawo cigaba ta fuskar zumunci a
cikin zuri'armu ta hanyar mua'amalantar kowa da girmama wa.
Amma babu komai, mu ci gaba da addu'a Allah baya juyar da addu'ar masu kyakkawar
manufa".
Ya saka hannu ya zaro hankicif ya fara goge zufar tashin hankali da take yanko
masa, kalaman sa ba k'aramin sukurkuta ni suka yi ba.
Amma na yi jarumtar waske wa domin har cikin zuciyata nake jin ban cancanci na zama
cikin ahalin Baban Tsakiya ba.

Ya kasa cewa tsawon lokaci sannan ya yi karfin halin cewa "Fatan alheri mai yawa
gare ki Yabin J".
Sai ya dawo da sauri cikin rawar murya ya ce "Yanzu kin mini adalci idan kika
jingina sunan ki da wani na?
Yanzu kin manta komai, bani da wata alfarma a wajen ki?"
Na yi kasa da kaina na ce "Alfarmomi masu yawa kuwa .
"Kai na fara so, kai kawai nake yiwa uzziri da sassauci bayan iyayena, sannan idan
akwai wanda na yarda da son da yake mini to kuwa kai ne.
Sai dai ko kusa bazan yaudari kaina ba.
Iyaye girmansu yawa ne da su, Annabi (S.A.W) ya yi ta jan hakankalinmu akan mubi
su.
Idan kuwa hakane zan gwada maka cikakkiyar soyayya ta hanyar dora ka akan turba
sahihiya, iyayenka duka biyu basa son almarinka da ni.
Dan haka ka bar son zuciyarka, ka musu biyayya, na yi imani Ubangiji ba zai barka
haka ba".
Daga haka na fashe da azababben kuka.
Jikinsa ya dinga kyarma ya ce "Na sani kina sona. Na roki arzikin, ki mini uzziri,
kar ki ce mu rabu, mu bar wa Allah ya yi mana za'bi, mu yi addu'a mu ga ni. Jikina
bai bani akwai namijin da zai aure mini ke alhalin ina numfashi a wannan duniyar
ba".


*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin
register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*.

*BAKAR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS M.I.NASHE)*

*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}```
✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


*ALBISHIRINKU*
*MASOYAN LITTAFAN MARUBUCIYA HAFSAT C SODANGI*!
*DUBA DA YADDA KUKE KEWAR RUBUTUNTA YA SANYA TA YI SHIRIN SAKE DAWOWA DAN TA SAKE
MUKU WANI RUBUTUN SABO DAL*
*AMMA KAFIN HAKAN TA DAWO MUKU DA TSOFAFFIN LITTAFAN TA ZUWA KAN WAYA, DAN KU SAKE
BITA TARE DA NAZARIN KYAWAWAN SAKON DA TAKE NUFIN ISARWA GAREMU*.

*A YANZU HAKA LITTAFAI HUDU NE RIGIS*

*WAYYO DUNIYA 1-3*
*KYAUTATA 1-3*
*DAGA K'IN GASKIYA 1-3*
*MATA MASU DUNIYA 1-3*
*KO WANNE 1K NE AMMA AKWAI DISCOUNT IDAN ZA'A SIYA SAMA DA GUDA DAYA*

*MISALI GUDA BIYU-1500*
*GUDA UKU 2500*
*GUDA HUDU 3500*

*ZA'A TURA KUDIN TA ASUSUN MARUBUCIYAR KAMAR HAKA*
*0082739293, ACCESS BANK HAFSAT YUNUS ABDULLAHI*

*SAI A TURO MINI SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*SAI NA BADA LITTAFIN DA AKE SO*

*MADALLAH DA KARFAFA GUIWARKU*
*MADALLAH DA SOYAYYARKU GA RUBUTUNMU*

*AKWAI LITTAFANTA SAMA DA GUDA GOMA DA A YANZU SUKE SOFT COPIES, KAWAI KI TAMBAYI
DUK WANDA KIKE NEMA A WAJENA CIKIN LITTAFANTA NA BAYA*.



*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin
register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*

13&14.
Da azama na shige cikin gidan na bar shi domin na samu sau'kin halin da nake ciki.
Kuka na dinga yi tamkar zuciyata zata fa'do k'asa, bansan son Yaya J ya tumbatsa a
zuciyata irin hakan ba sai yau, domin sai na tsinci kaina da addu'ar na zama gawa
kafin igiyar aure ta d'auresu da Maijidda.
A wannan daren barci rabi rabi na yi shi.
Washagari da hantsi sai ga shi ya dawo, kallo d'aya na yi masa na gane yana cikin
zullumi mai yawa domin gaba'daya ya zube ya sake fige wa.
Yaya Salisu da ba shi da matsala da kansa ya masa iso har cikin falon gidan da yake
dakuna uku ne a jere falle falle.
Na fito a sanyaye sanye da hijabi idanuwana a kumbure a dalilin kuka da rashin
barci.
Na zauna a kujerar da ta yi nesa da wacce yake zaune.
Tsawon lokaci muna zaune jigum jigum, tamkar masu makoki, daga karshe dai ya k'osa
cikin murya marar amo ya ce " Yabi babu gaisuwa ne?"
Kaina a kasa na ce akwai gaisuwar da tafi nema maka amincin da na yi?
Shin ka raina sallamar ne?"
Ya girgiza kai ya ce "Hakkun Yabi. Kin fini kusa da daidai, kin yi barci kuwa?".
Kaina a k'asa na ce "Me zai hana Yabin Marina barci a wannan duniyar? Sai mutuwa,
ko ciwo".
A matu'kar sanyaye ya ce "Idan kuwa hakane ki shirya kwanan zaune domin kullu
nafsin za'ikatul maut. A kowanne lokaci muna iya rasa mutane mafiya daraja a
rayuwarmu, ko kuma a jarrabemu da ciwo mai hana runtsawa. Fata dai Allah ya bamu
ikon cinye dukkan jarabawowin da suke dunfaromu.
Ban da dai dan-adam an jarrabe shi da tsoron mutuwa, mene ne abu mai da'di a cikin
wannan duniyar da a kullum tsanani da bacin rai suke sake yiwa mumini k'awanya?"
Ban tanka masa ba, domin kuwa gaba'daya zuciyata babu sukuni, kuma cike take da
ba'kin ciki mai nauyi.
Cikin alhini ya ce "Yabi ban yi zaton munin dambarwar da take faruwa ta kai
lalacewar da ta yi ba!
Na gamsu, na ha'kura da aurenki a yanzu, dan na tsaremu daga fa'dawa halaka.
Amma na rantse miki babu wata macen da zan sota irin son da nake yi miki, zan kuma
dauwama a cikinsa.
Tsoron hakkkm iyaye ne kawai zai sanya na yarda na yi aure kuma na mua'amalaci
matar cikin adalci. Amma ban ha'kura da ke ba, zan cigaba da kokarina har sai
Ubangiji ya mini taimakon tabbatar da aurenmu.
Hawaye ya balle masa tamkar ba namiji ba.
Da rawar murya ya ce "Akwai bukatar mu tsananta addu'a a cikin zumuncin Gidanmu
Yabi. Daga jiya zuwa yau na fahimci BAK'AR TA'ADAR wariyar launin fata, ta yi kane
kane a cikin gidan".
Na dago idona jage jage da hawaye na ce "Komai zai dai-daita idan arzikin Baban
Marina ya dawo, ko idan ya'yansa suka kawo k'arfi."
A kasalance ya ce "Ba wannan ce matsalar ba kawai.
Shin menene ribar hana ni auren ki?"
Na dago na ce "Saboda ana ganin zan samu cigaba, ana ganin ban cancanci na samu
irin wannan darajar ba, bai kuma kyautu ayi wa Baban Marina irin wannan zumuncin ba
tunda ba za'a amfana da shi ba, an kuma rufe ido an mance irin amfanar sa da aka yi
a shekarun baya".
Ya yi shiru ya ce "ban gamsu ba, idan kuma wannan ne hujjar da gaske?
Menene dalilin da zai sa ba za'a bawa Bulkachuwa auren Nasiba ba?
Ai duk lalacewarsa jininmu ne. Idan za'a hana shi mace a cikin danginsa to ina za'a
bashi? kawai halin da ya jefa kansa ne ya sanya baya iya tanadi. Amma idan aka
bashi mace na tabbatar indai yana samun nutsuwa da ita, zai nutsu ya zama mutum na
sosai, sannan zai daina zalama da tsilla tsillar da yake yi tunda yana da tasa ta
halal a dakinsa ."
Duk da matsananciyar damuwar da nake ciki sai da maganganunsa suka jefa ni cikin
kunya da takura.
Na kasa magana.
Ya sake cewa "To saboda Allah idan ba'a taimake shi a cikin danginsa an rufa masa
asiri, an tsaya kai da fata wajen ganin al'amarinsa ya kintsu ba, me za'a yi masa?
A wajene ake son ayi masa irin wannan sadaukarwar da kishin kai?
Babban tashin hankalin ita Nasiban sonsa take yi kamar ta kai kanta dakinsa. Da ace
bata sonsa na zan ga laifin kowa ba.
Shin wanne irin zamani muke ciki ne mai cike da son zuciya?"
Nan ma na kasa cewa uffan domin tunanina ya riga ya tsuke, ban sani ba ko dan har
yanzu ban gama fahimtar al'amuran da shi ya fahimta a tsakanin yammacin jiya zuwa
yau ba.
Ko dan ya fini shekaru, ya kuma fini ilimi da hangen nesa ne oho.
Gaba'daya a rikice yake, k'warai kwamacalar da take cikin gidanmu ta gigita shi.
Nasan bai san haka abin ya tsananta ba, tunda ba kasafai yake zaman garin ba.
Ya jima kafin ya sake cewa komai.
Ya mike ya zura hannunsa a aljihunsa.
Ya ce "Bansan me zan ce miki ba, amma nasan zan rayu da son ki a raina muddin rai.
Zan kuma rayu tamkar wanda ya rasa bangare guda a jikinsa. Ina fatan Ubangijinmu
Allahu ya sanya mu cikin masu soyayya dan Allah. Har kuma yanzu da nake miki wannan
jawabin ban cire alkalamina a cikin tawada ba. Ban cire rai cewar kaddara tana iya
bani damar mallakar ki a matsayin matata ba.
Ina neman alfarma, komin kankantar damar da zamu samu ta cikar burinmu kada laifin
da bani na yi ba, ya shafi hakan Yabi.
Ina da burin idan mun yi aure na mayar da ke makaranta ki zurfafa a ilimummuka
daban daban.
Amma ko yanzu ma ban fitar da rai ba, lokaci zai zo da zaki tsaya ki yi karatu
tuk'uru, ki cire shiriritar da kike yi.
Mu tsananta addu'a, mu barwa Allah ya yi mana zabin da ba zamu koka ba. Kin fini
gaskiya duk al'amarin da babu saka albarkar iyaye to tsinannen al'amari ne.
Fatan alheri gareki Yabin J".
Ya fice da sauri.
Jikina ya yi matu'kar sanyi, domin na tabbatar akwai abin da Yaya J ya ga ni a
cikin zumuncin Gidanmu da ya warware masa duk wani confidence dinsa.
Na kagu na samu labarin irin wainar da ake toyawa a gidan Marina.
Na rasa yadda zan yi, domin Yaya Salisu ba mai zama ya tattauna magana da mutane ba
ne.
Na matsu kwarai na ga Nazira domin a bakinta zan ji komai kuma babu k'arya ko karin
gishiri a cikin kalamunta.
Kwanaki suka yi ta shudewa, ban samu ganin Nazira ba, ban kuma ji labarin komai ba.
Abin da yake damuna daya ne takunkunmin hana ni zuwa gida da aka sanya mini.
A hakan har na shafe kwanaki ashirin da biyar a gidan Yaya Salisu.
Na riga na kai k'ololuwar gajiya da son jin makoma ta.
Gashi ba wanda ya zo daga gidanmu.
Dan ma ina samun y'an kitso da k'unshi, suna biyo ni, haka na unguwar ma suke yi
mini layi.
Rannan da na gaji, sai kawai na zari jiki na doshi gida a sayyadata duk da tazarar
gidan Yaya Salisu zuwa Gidanmu tafiya ce mai tsayi ainun.
Tunda na kusa k'arisa wa na fara jin jikina na kakkarwa, ga kuma luguden da
zuciyata take yi tamkar ta faso ta fito.
Bakina na ambaton sunan Allah, duk da idan ance na fa'di me nake fa'di ba zan iya
tantance wa ba.
Na fa'da zauren na yi kicibus da Baban Tsakiya, zai fita, da alamun rashin sukuni
a tare da shi.
A farko kamar ba zan gaishe shi ba.
Bansan ya aka yi ba, cikin rawar murya na ce "Baban Tsakiya ina yini?"
Ina daga tsaye ban rusuna ba.
Ya mini dak'uwar da ta zame masa dabi'a ya ce "Baban farko ba na Tsakiya ba. Wato
ke tabbataciyar yarinya ko? Sai kin ha'da da inkiya saboda ba kya mini kallon
arziki.l?
Zan ga mai daura miki aure, sai dai Ubanki ya waklice ki da kansa.
Kuma indai ina numfashi duk wanda ya zo neman auren ki sai na fa'da masa rashin
d'aarki da hatsabibanci irin na ki, domin fadar gaskiya a neman aure jihadi ne
kabiran".
Na yi k'asa da kaina ba tare da na ce komai ba.
Ya juya ya tafi yana ta yi mini sababi da kwashe albarka da fatan tsiya iri iri.
Na jingine a jinkin garun ina tambayar kaina "Wai haka kowa yake fuskantar bacin
rai da danginsa ko kuwa iya ni ce?

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA
BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH*.

Take na tuno Nazira bata fuskantar tsanani irin nawa a wajen Baffannin namu. Amma
kuma ko ka'dan bata samun sakin fuska da alherin da suke yiwa ya'yansu.
Na sake tafiya dogon tunanin yadda Baban Marina yake mua'amalantar nasu yaran.
Mua'amala ce ta sassauci da ja a jika.
Domin duk talaucinsa, yana k'ok'arin siyan albasa ko su mangwaro ya ce mu mika
kofofinsu.
Hakanan indai zai yi aski sai ya ha'da da ya'yansu an musu ya biya.
Bayan nan duk wani rikicin da ya'yansu zasu rakito shine zai yi ta zarya yana bada
ha'kuri har sai komai ya daidaita.
Amma su ba ruwansu damu, wani ikon Allah Yaya Musa da yake a lalace sun fi sonsa,
sun fi yinsa, sun fi tattalin farin-cikinsa.
Na jijjiga kai a fili kuma sai na ce "Allah haska kofar Baban Marina, Allah ka
jibanci al'amarinsa da na ya'yansa.
Na shige cikin gida ban doshi k'ofar Dada ba.
Yanayin da na tarar da Babanmu da ahalinsa ya sake sanyaya mini jiki.
Na shiga bakina da sallama na isa kan tabarmar da suke zaune na tsugunna ina gaishe
shi cikin girmama wa.
Ba walwala Baba ya ce "Asiya me kika zo yi?
Ba na ce sai na neme ki ba?"
Da rawar murya na ce "A mini afuwa Baba! Na kasa jure ji daga gareku ne."
A sanyaye ya ce "Na miki afuwa Yabi zo ki zauna.
Da rarrafe na karisa kusa da shi a dalilin rawar da jikina yake yi ya sake
ta'azzara.
"Na yi godiya Baba Allah ya k'ara maka lafiya, ya shirya maka zuri'a, Allah ya
mayar da ahalinka wasu masu fa'da aji".
Ya yi murmushin da babu nisha'di.
A sanyaye ya ce "Ameen Yabi! Duk yadda zan yi ba zan iya cire miki wannan BAK'AR
TA'ADAR k'ullaci da ta shiga ranki ba.
Amma abin da zan fa'da muku duk taku, duk wanda bai mutunta y'anuwana ba, to nima
kar ya mutunta ni".
Jikina ya yi sanyi, na yi kasa da kaina, na kasa cewa komai.
"Yabi".
Ya k'ira ni murya babu amo.
Na amsa a hanzarce "Na'am Babanmu".
Ya yi gyaran murya ya ce "Nan da kwanaki goma sha biyu auren y'anuwan ki.
A duk wanda kuka taso ke da Nasiba ne kawai babu ku a cikinsu.
Da gobe zan je na sanar da ke maganar a nutse cikin kwanciyar hankali.
Na tura wa iyayen Abdulrashid su turo ayi magana to bansan inda aka haihu a ragaya
ba, sai suka aiko mini da sun yi wa d'ansu mata tuntuni, ba

Please Login or Register in order to submit comment