You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na fahimci ba a daina zuwa ana katse mana jin da'dinmu ba sai nake yawan
rubutawa a status d'ina cewar babu lalle ranar lahadi haka ma kitso.
Mun yi kyau, mun shak'u da juna, komai yana tafiya dai-dai mussaman da na daina yi
masa rikicin bai yi mini ciki ba.
Da kansa ya dauke ni muka je asibiti da muka cika shekara guda da aure. Dukkanmu
aka auna mu aka tabbatar mana lafiyarmu k'alau cikin ko wanne lokaci zamu iya
haihuwa. Shike nan sai na daina damuwa illah iyaka ban daina addu'ar ma samu ciki
na haihu ba.
Muna cikin wannan yanayin mai da'di Rafi'a ta kammala karatunta na jamaia ta dawo
gida gaba'daya.
Kusan kullum sai ta shigo mini. A zuciyata bana so amma tunda uwarta ba k'aramin
kirki take yi mini ba. Sai nake share wa mussaman ita din ma mai kirki ce.
Amma haka kawai nake jin fargabar zakewarta a wajena domin na riga da na sani
mijina yana son yan lukataye irin ta. Ni kuma yar firit ce. Sannan bazan yaudari
kaina ba, zai iya sha'awarta tunda jikinta rugu rugu ne, kuma bayltw damu ta saka
mayafi ba. Tunda tana ganin ba sai ta fita waje da ta shigo ba. Bugu da kari ba
Hausawa ba ne. Wasu abubuwan nasu da namu akwai banbanci.
Haka dai nake ta daure wa ina ta k'ok'arin ban bar shi da kewa ba. Komai yake so
sai na yi masa. Ba kuma na tab'a k'osawa da al'amarinsa duk da nima ina son harkar.
Amma bana ja masa rai saboda kada ya ga ni a waje ya yi sha'awa. Ba kuma na nunawa
ya gundure ni.
Ana cikin haka aka tashi bikin. Ihsan k'anwarsa. Tun saura sati biki na tafi,
saboda a fara komai da ni, sannan ni ce zan mata k'unshi da kitso.
Babah sai ina ka saka take yi da ni. Yadda ta ga na murje na yi kyau ba karamin
da'di ta ji ba. Na sani kuma da a ce da goyo na je mata da tafi haka murna.
Shi da kansa ya kai ni. Washagari ya tafi akan sai nan da kwanaki ka'dan zai juyo.
Komai sai da na bar masa, hatta miya sai da na soya masa, na yi masa cincin. Kawai
tafasa farar taliya ko shinkafa zai yi sai kuwa shayi.
Ana gobe biki y'an Toro suka iso. Aka yi hidima cikin rufin asiri taro ya tashi
lafiya.
Kwanaki biyu a tsakani ya zo muka tafi shake da kayan biki masu yawa.
Tunda muka yi aure bamu ta'ba nisa da juna ba sai wannan karon.
Duk da dai a Bulkachuwan ma ranar biki sai da ya faki ido ya jani muka je wani waje
ya yi abin da zai yi sannan ya dawo da ni.
Amma muna isa gida ko hutawa bamu yi ba. Daki ya ja ni bamu fito ba sai da ya samu
nutsuwa.
Da daddare ina zaune a cinyarsa sai ce mini ya yi "Little baki da nauyi, shafal ban
ji kin danne ni ba".
Na zabura na kalle shi, gabana ya fa'di sosai. Da rawar murya na ce "Sai yau ka
fahimci haka? Wa ka d'ora a cinyar da yanzu baka ji yadda kake so ba?"

*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA
KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA
KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*

Ya daburce ya ce "Wallahi babu kowa Yabi".
Fa'din Yabi da rudun da ya shiga sai yasa na kasa gasgata shi amma kuma na danne na
ha'diye saboda babu kyau zargi.
Duk yadda na so na bar maganar amma a zuciyata sai wasi-wasi nake yi. Na kasa samun
nutsuwa. Hakan ya fara shafar walwalata. Ban sauya masa ba, ba kuma na bijire masa
amma kuma babu shiriritar da nake yi masa a baya.
Rannan na ce masa ina son na je gida na yini. Da rawar baki ya ce "To, yaushe zaki
je?"
Domin ya takura da rashin walwalata.
Na ce "Duk ranar da ka ce".
Ya ce "To gobe sai na kai ki"
Haka kuwa da kansa ya kai ni, muka fara isa k'ofar Dada muka gaisa. Tana ta
barkwancinta da karatunta. Ban wani jima ba na tashi na nufi k'ofarmu."
Ya shigo suka gaisa ya ce mini zai tafi da yaushe zai zo ya d'auke ni?
Na ce "ko yaushe ma".
A k'ok"arinsa na son ya kyautata mini sai ya ce "Tom idan an idar da Isha zan zo".
Na ce "Allah ya kai mu".
Ya tafi. Na yini cikin iyayena cikin nutsuwa da walwala.
Da yamma lis Gwaggo da Inna zasu je duba yar kanwar Mama da ta haihu kusa da
unguwarmu ne.
Dan haka Baban Marina ya ce "Asiya sai ku je tare ki rakasu idan kin dawo sai ki
shige gidanki".
Na amsa da ce wa "To Babanmu, domin idam Gwaggo ta fita ba jin da'din zaman zan yi
a dakin ni ka'dai ba, tunda Ikilima ta tafi Islamiya, shima kuma Baban fita zai yi.
Mama kuwa babu wata ma'amala mai yawa a tsakaninmu.
Dan haka muka tafi tare. Da muka dawo na yi lungun da zai sada ni da gidana, su
kuwa suka mik'e suka koma nasu gidan.
Haka kawai nake jin nauyin jiki na saukar mini. Wani irin b'acin rai ya ziyar ce ni
da na karyo kwanar da na fara hangen gidanmu. Haka nake tafe ina ta jin fargaba.
Ina kuma ayyana abubuwa marasa da'di a zuciyata.
Nan da nan na fara ta'awizi ina kore shaid'anin da yake son yin wasan kura da
zuciyata. Har cikin zuciyata ina son Tijjani, ina son na rayu da shi. Domin a zaman
da muka yi na shekara daya da kusan rabi na tabbatar yana da kyawawan dabi'u. Na
farko shi mutum ne mai mutunta sallar farillah. Sannan mai yawan tsayuwar dare ne
na shaida hakan. Domin duk lokacin da zai shafe yana tiritiri da ni da daddare, to
da zarar k'arfe uku ta yi kuma zai tashi ya yi wanka. Ya yi ta yin munajati da
Ubangijinsa, wani lokacin ya matsa mini na tashi, wani zubin kuma ya k'yale ni na
yi barcina. Sau tari kuma idan ban tashi ba, da asuba idan ya tashe ni sai ya ce
"Tashi ki yi sallar farillah akan lokaci, na raba dare ina roka miki alherin duniya
da lahira my little".
Bayan hakan na karance shi yana da matu'kar son ya kiyaye ka'idojin da shari'a ta
d'ora masa mussaman na ri'ke gida da kula da tarbiyata. Sannan ba shi da mugunta ko
ka'dan har yau din nan Tijjani bai ta'ba saka mini ido akan ku'dina ba. Asalima
kullum cikin k'ara k'auwame kansa yake yi da abin hannuna.
Sannan ya iya Soyayyar da duk taurin zuciyar mace sai ya dargaza ta. Ga kuma
girmama iyaye, yana mutuntata manya kwarai da gaske. Wadannan dabi'un da ya
siffantu da su ya sanya nake hakuri da inda yake kuskure mini, hakan ne kuma
dalilin da yasa na k'i yarda na k'arfafa wa kaina zargin ko ya koma Bak'ar Ta'adar
sa ta baya.
Na shiga zauren na ga kofar tamu a rufe ruf. Na fara tunanin ai ban fito da mukulli
ba, tunda mun yi shi zai zo ya dauke ni.
Na zaro waya da nufin na k'ira shi ya zo ya bu'de mini, sannan na wuce k'ofar Maman
Safiyanu na jira shi. Sai na jingina da k'yauren k'ofar ga mamakina sai na ga ta
bud'u.
Na tura a hankali na ga sakata a ture tabbacin an saka bata shiga ba ne.
Na shigo a hankali. Amma sai na ci birki na tsaya cikin tsananin tu'ajjibi da
mastanancin mamaki mai yawa.
Jikina ya d'auki b'ari, zuciyata ta yi nauyi ainun. Amma idona ya bushe k'amas.
Na saka hannuna na murtsike idanuwana da tunanin gizo yake yi mini, tare da fatan
ace sak'e sak'en zuciyata ne da wasi-wasi irin na shaid'an.
Amma ina zahiri nake ganinsu. Tijjani zaune akan baranda yayin da Rafi'a take kan
cinyoyinsa da manyan mazaunanta. Ta kwanta luf a kirjinsa, shi kuma idonsa na kan
k'irjinta yana kallonsu. A zahiri iya abin da na gani ke nan amma zuciyata sai ta
shiga wassafo mini cewar yanzu ma suka sanya tufafinsu.
Na ki'dima ainun, amma na kasa yin kwakkwaran motsi, na tsaya cak ina kallonsu
tamkar mutum mutumi
K'arar faduwar wayata ne ya ankarar da shi.
Ya d'ago da fuskarsa ai yana ganina ya yi wani irin zabura ya wancakalar da ita, ta
hantsilo ta fa'do kan guiwowinta.
A matu'kar rude ya k'araso gare ni.
Ya rasa mai zai ce, sai kawai ya zube a gabana guiwa bibbiyu. Ya ru'ko hannuna na
kalle shi na ce "Tijjani gizo idona yake yi, ko mafarki nake yi?".
A ki'dime ya ce "Zan so a ce mafarkin kike yi Asiya".
Daidai lokacin Rafi'a ta zo ta shige sum sum tamkar k'wai ya fashe mata a ciki.
Na dinga jin tukukin ba'kin ciki da tashin hankali. Amma kuma idona a soye duk
yadda nake son hawaye ya zubo mini abu ya ci tura.
Na sunkuya na d'auki waya ta na k'wace hannuna na yi d'akina ina jin jiri na
katantanwa da ni.
Kai tsaye na hau cire rigar cikina domin zafin da nake ji a zuciyata har jikina
yake kutso wa. Zufa sai yanko mini take yi.
Na cire komai na d'aura zani. Na zauna amma ban daina jin zafin jiki ba.
Na fita har lokacin yana durk'ushe a inda na bar shi.
Na dauki botiki na nufi rijiya. Da azama ya tare ni, ya ce " Bana hana ki jan ruwa
da kan ki ba?".
Ban ce komai ba na matsa gefe ya janyo mini ruwan. Ya kinkima ya kai mini
band'akin.
Na shiga na yi wanka. Amma dana fito ina goge jikina da tawul, zufar na sake keto
mini.
Na dauki rigar barci marar nauyi na saka, bayan na saka gajeran wando ta ciki. Na
d'aure kaina da dan kwali mai taushi.
Kicin na fa'da na hau girki, ina yi ina hailala. Gaba'daya jina nake yi tamkar ba
ni ba. Na yi matu'kar kad'uwa da abin da na ga ni a cikin gidan aurena.
Ban san falalar kuka ba sai a yau, domin gaba'daya hawayen ya k'i zuba.
Shi kuma ya takure, a gefe tamkar ka ce k'yat ya zura a guje. Cikin lokaci k'alilan
nadama mai tsananin gaske ta bayyana a dukkan jikinsa. Ya kasa sukuni, da alamu
kunya ce ta hana shi sukuni. Tunda ni dai ban bu'de baki na ce masa komai ba.
*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*



✍️
*Dandano*
*DAGA Littafin BAK'AR TA'ADA*
*NA SURAYYA DEE*
*MARUBUCIYAR HALIN YAU DA SABO DA KAZA*

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/GICSrs9TfxG1Q6FUXiu1Qg

*Ina tallata muku make up artist din Guduyo*
*Aisha Lame mai kayan kwalliyar yan gayu*.
*Jakadiyar oriflame, duk wani nauyin kayan oriflame tana kawo su cikin farashi mai
sau'ki*.
*Ba iya kayan kwalliya masu daraja ba, ita din GWANAR sarrafa pop corn ce(gugguru),
ni shaida ce ta hakika*.
*Sannan tana da spices kasaitatu. Masu mayar da girki ya zama na alfarma*
*07036662633*.


*INA SANAR MUKU ZAMU BUGA LITTAFIN KANA NAKA ZUWA HARD COPY*.
*MASU BU'KATAR MALLAKAR NASU SU TUNTU'BE NI, KO SU TUNTU'BI MARUBUCIYA JANAFTY*.

*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*.

Na gama komai na kai falo kamar yadda na saba. Shi kuma ya zama mutum mutumi.
Na fito na ce "Ga abinci ko sai ka dawo daga masallaci?"
Ya zuba mini ido ya rasa abin fa'da.
Ya tashi ya ce "Da sauran lokaci ai."
Na zuba mana kamar yadda na I'm. Amma gaba'daya mun kasa ci sai faman juya shi muke
yi.
Gara ni na ci loma biyu na ji mak'oshina ya cushe na ajiye. Shi kuwa yama kasa kai
wa ba'kin nasa.
Ya gaji ya kalle ni ya ce Dan Allah Yabi ki yi ha'kuri, ki yafe mini".
Ba ja in ja na ce "To".
Daga haka kuma ban sake ce wa komai ba. Ya yi maganganu na ban ha'kuri da nuna
nadama masu yawa amma ban ko kalle shi ba. Aka kira sallah ban yarda na bu'de baki
mun yi magana kamar yadda yake fata. Ya yi alwala ya tafi masallaci.
Har muka haramar kwanciya ban bu'de baki na ce k'ala ba. Duk jaye-jayen maganarsa
kuwa. Da muka kwanta ya fara lalubata ban hana shi ba, amma ko kwakkwaran motsi ban
yi ba. Ya yi duk abin da zai yi dan na motsa ko na mayar masa martani amma tamkar
an shuka dusa.
Ya gaji ya koma ya kwanta yana fa'din "Innalillahi wa ilaihir rajiun" .
Ya ru'ko ni da rawar murya ya ce "Yabi ki yiwa Allah, ki bu'de baki mu yi magana".
Yana rufe baki na ce"To".
"Asiya ki yi ha'kuri, ki yafe mini, dan Allah, dan Annabi, ki yafe mini".
Na yi shiru. Ya sake ce wa Bansan me ya same ni ba Yabi. Dan Allah ki mini uzziri
ki yi ha'kuri ki gafar ce ni".
Nan ma na ce "To".
Ya yi iya ban hakuri, amma ban yarda na ce komai ba.
Da gari ya waye da wuri ya dawo daga masallaci ya hau hidimar gyaran gida.
Ya yi abin karya wa. Har d'aki ya kawo mini amma ina ci sau daya ban sake kai wa na
biyu ba, na ce na koshi. Ya yi shiru ya rasa yadda zai yi.
Bai fita ko ina ba. Yini aka yi ana zuwa lalle amma ban iya yiwa ko mutum daya ba.
Sai ha'kuri nake basu tare da uzzirin cewa bani da lafiya ne.
Hakan da ya ga ni ya sake rib'anya tashin hankalinsa. Domin yasan yadda nake
matu'kar son sana'ata. Bana son abin da zai hana ni yin lalle ko kitso.
Amma da bakina nake sallamar mutane yasan al'amarin da yake zuciyata ba k'ank'ani
ba ne.
Kwanaki uku muna cikin wannan halin. Daga ni har shi, mun yi matu'kar rame wa tunda
bama iya cin abinci ga rashin nutsuwar zuciya.
Ya yi juyin duniya mu yi magana na ki, domin har yau ban yarda na yi masa korafi
ba. Komai kuma zai ce sai na amsa da "To". Kullum safiya zan gaishe shi, zan kuma
amsa sallamar sa idan ya shigo. Daga hakan kuma bazan sake yarda na ce komai ba.
Rashin yin lallen har zuwa lokacin ya fara ta'bamu tunda shi ma baya iya fita, ko
ya fitan ma baya nisan kiwo zai dawo.
Ranar da aka yi kwanaki biyar da faruwar al'amarin, ya zauna ya bani hakuri tamkar
yawun bakinsa zai k'afe. Har da k'wallarsa. Amma ban ce komai ba, sai ma murmushi
mai ciwo da na yi na ce masa "To me ka yi ne?"
Duk da k'arancin shekaruna amma na fahimci shirun da na yi masa ba k'aramin dafa
shi take yi ba. Ba abin da yake so irin na yarda mun yi magana ko da rashin kunya
ne na yi masa. Amma ban yi hakan ba. Ni a karan kaina so nake na yi kuka, na
caccaba masa maganganun da zasu gasa masa zuciya tamkar yadda ya yi dalilin da tawa
zuciyar take gasuwa, amma na kasa.
Tsawon sati guda muna cikin wannan matsanancin halin, daga ni har shi mun zama wasu
iri. Gidanmu ya koma tamkar na zaman makokin mutuwar uwa mahaifiya.
Sannan na k'i yin k'unshi har lokacin. Al'amarin da ya sake damalmala mana komai.
Shi kam kawai k'arfin halin da aka san maza da shi ne. Amma kana kallonsa kasan
yana dandanar kudarsa da shiruna. Yadda bana cin abinci haka shi ma baya ci. Gara
ma ni da daddare na kan yi barci, amma shi duk juyin da zan yi zan gan shi kan
sallaya ko yana zaune ko kuma yana sallah.
Da asuba ya dawo ya tarar har na koma na kwanta.
Ya zauna a bakin gadon. A sanyaye ya ce "Yabi wai a haka zamu rayu ne? Bazan iya
wannan rayuwar ba. Ki yiwa Allah da ma'aiki ki bu'de baki ki fa'di duk abin da kike
so. Na ro'ke ki ba dan ni ba, da Allah nake ha'da ki."
Ko motsi ban yi ba. Bare na tanka masa.
Ya tsananta da magiya. Sai kawai ji na yi cak ya dauke ni ya yi nufin d'ora ni kan
cinyoyinsa. Ai gaba'daya wani irin k'arfi mai tattare da matsanancin fishi ya taso
mini. Da dukkan zuciyata na fisge na ingiza shi ya fadi k'asa warwas.
Na dinga huci mai zafi, amma na kasa bu'de baki na yi magana.
K'irjina sai harbawa yake yi da tsananin gaske.
Ya mik'e ya kafe ni da ido, cikin kad'uwa da tashin hankali. Ya ce "Dan Allah bu'de
baki ki yi magana. Fadi me zaki ce, idan kuma na zauna ki mini duka zai fi mini
akan irin halin da nake ganin ki, ki yafe wa mijinki, ki yafe wa masoyinki, ki yafe
mini, kaddara ce ta hau kaina Asiya".
Na juya na kwanta ba tare da na ce uffan ba.
Kukan kuma bai zo ba.
Ya kasa hakuri ya sake biyo ni inda nake kwance ya hau lalubata, ban hana shi ba,
ban kuma yi wani yun'kurin da zan tankwabar da shi ba. Ya yi abin da zai yi. Yana
gamawa na lalubi zanina na daura na fice.
Wanka na yi, sannan na dawo na kwanta. Bayan na mulke jina da hadadden man
oriflame. Wanda jakadiyar kamfani ce ta za'ba mini shi fa kanta, q cewarta shi zai
fi dace wa ta tarar fatata.

*Kunsan dai Aisha Lame make up artist din Guduyo ce. Yanzu ma bata bata bar fatar
Yabi babu gyara ba*.
*Kun tandadi fame wash din nan kuwa da na yi ta jaddada muku muhimmancinsa a
wajenku?*
*Ku tuntu'be ta a wannan lambar dan samun sabbin kayanta masu kyau da farashi mai
sau'ki da ya zarta na saura*.
*07036662633*.

Shi kuma yana kwance sai fa'din "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" ya ke yi da
k'arfi.
Yau duk jarumtar sa kasa yin ayyukan gidan ya yi. Dan haka na yi abuna. Na yi abin
karyawa har na gama yana kwance. Na d'aga labule na ce "Ka zo mu karya."
Yana daga kwancen ya ce "Ko na zo d'in ma ai ba ci muke yi ba. Ki yafici abin da
zaki ya fita ki rufe".
Wasa wasa yana kwance har azahar, ko wanka bai fito ya yi ba. Abin da ban ta'ba
ganin ya yi ba, zama da janaba. Komin dare baya kwanciya sai ya yi wanka. Ko da
kuwa zai yi second round. Amma yau safiyar Allah kuma ba barci ba, amma yana nad'e
ya kasa tashi bare ko ruwan shayi ya kurb'a. Na sani fishin nawa ne ya fara k'ure
malejin jarumtar sa.
Ina zaune ina tunanin al'amurar rayuwa sai na ga fitowar sa, d'aure da tawul da
k'yar yake daga k'afafuwansa rauni gaba'daya ya bayyana a jikinsa.
Da ya tashi dawo wa daga masallaci sai ga shi da Malam liman da Malam mai Tafsiri.
Ganin dattawa kuma manyan Malamai na shiga marabatarsu da girmama wa. Shi da kansa
ya yi musu jagoranci zuwa falonmu.
Na zuba ruwa a k'aramin tray na ajye a gabansu. Na gaishe su cikin ladabi. Suka
amsa suna saka mini albarka. Na yun'kura zan tashi na basu waje dan a tunanina
wajensa suka zo.
Sai kawai na ji sun ce "Ina zaki kuma, ai zuwan na ki ne".
Gabana ya yanke ya fa'di to me ya kawosu waje na ni kuwa?"
Malam liman ya yi gyaran murya ya yi addu'ar bude taro, ya nemi tsari daga sharrin
shaidan da rundunarsa. Sannan ya ro'ki Ubangiji ya sanya albarka a abin da za'a
tattauna.
Aka amsa da ameen.
Ya zarce da cewa "Asiya mijinki ya same mu, ya kawo k'arar kansa da kansa gabanmu.
Da bakinsa ya ce ya yi miki laifi da ya amsa sunan laifi. Amma yana ro'kon mu zo mu
baki ha'kuri a madadinsa".
Na yi k'asa da kaina, ban ce komai ba.
Domin ba k'aramin nauyi na ji ya kama ni ba. Akan me zai dauko mini manyan mutane
irin haka?
Malam liman ya zarce da cewa "falalar hakuri yawa ne da shi Asiya. Mijinki ya yi
nadama, irin wacce ake so mumini ya yi. A wannan zamanin idan mutum ya yi kuskure
ya yarda ya yin ma, har yake bada ha'kuri ba k'aramin mutumin kirki ba ne. Abin da
yasa na yarda na zo kenan da bakinsa ya ce ya yi miki k'aton laifi. Sannan na ga
rauni mai yawa a tare da shi, wanda idan ba'a ba shi dauki ba zai iya kwantar da
shi. Ki gode wa Allah da ya baki miji mai kiyaye sallah. Sama da shekara da zuwansa
unguwar nan ban ta'ba fashin ganinsa a sahun gaba na sallar isha da asubahi ba.
Annabin Rahma ya ce wadannan sallolin munafukai basa kiyaye ta. Ki yi hakuri da
inda ya gaza mutumin kirki ne, na shaida hakan".
Sai lokacin kuka mai tsananin gaske ya k'wace mini, irin kukan da yake ki'dima duk
mai sauraronsa, kuka mai dafa zuciya mai sawa a shid'e.
Kowa ya yi shiru, illah Tijjani da yake fa'din "Alhamdulillah! Alhamdulillah cikin
wani irin yanayi. Domin ya sani rashin kukan da ban samu na yi ba. Da rashin furzar
da maganganu. Ya sanya na taurare nake dafa shi ta hanyar zuru.
Malam mai Tafsiri da yafi kusa da ni, kuma yafi tsufa, domin ya tsufa ainun, na
tabbatar ya haifi kamar Babanmu.
Ya d'ora hannunsa a kaina yana shafa mini, cikin muryarsa ta girma ya ce "Yi hakuri
jikata. Kara hakuri, Innallaha ma-assabirin. Ki daina irin wannan kukan zai janyo
miki ciwo. Yi salati ki samu nutsuwa. Tsawon lokaci yana shafar kaina tare da
maganganu masu taushi har na samu nutsuwar.
Hannunsa na kaina ya ce "Shin Asiya ta huce ta ha'kura, ta yafe wa mijinta?"
Da rawar murya na ce "Akan me zai dauko mini ku? Ni bai mini komai ba, kuma nima
ban ce masa ya yi mini wani abu ba."
Da azama kuma da cikin rawar murya ya ce "Na yi miki Asiya! Ni nasan ban kyauta ba.
Amma ki dubi Allah ki yi ha'kuri. Ki bani dama mu tattauna, mu rufe maganar nan ta
wuce".
Na kalle shi hawaye na zuba mini na ce "Tunda ka kafe ka yi mini laifi, fadi laifin
da bakinka. Fa'da musu su ji".
Ya yi k'asa da kansa ya kasa ce wa komai.
Na juyar da fuskata na ce "Kun ga ni ba. Ai bai mini laifi ba. In ma ya yi Allah ya
yiwa, na tabbatar kuma ya nemi gafarsa tunda kwana yake yi yana ibada. Ni kuwa bai
mini komai ba."
Malam liman ya ce "Ga shi da bakinki kike shaidar yana kwana sallah anya bai
cancanci ki yafe masa ba. Kinsan darajar wanda yake munajati da Allah fil lail
kuwa?"
Kamar na ce "Amma ibadar tasa bata hana shi ya yi barna ba, bata hana shi ya
tozarta ni ta hanyar yin bak'ar TA'ADAR a gidan aurena ba.
Amma na kasa bu'de baki na fa'da musu hakan.
Ban san da gaske ina son sa ba sai yanzu. Domin bayan matsanancin kishinsa da yake
cina, sai na ji bazan iya tona masa asiri ba.
Bazan iya fa'dawa wani mahaluki abin da na ga ya aika ta ba.
Malam liman ya sake cewa "Ki yi ha'kuri kin ji Asiya. Ki yi koyi da mai sunan ki
Nana Asiya. Annabi ya fa'da mana falalar ta. Abin da kuma ya janyo mata babban rabo
a wajen Ubangiji imaninta da hakurinta akan mijinta ne. Ki yi hakuri, da sannu
Ubangiji zai daidaita muku al'amuranku."
Jikina ya mutu tubus. Na ce "To".
Suka dinga saka mini albarka da godiya. Malama liman ya mike ya ce "Tunda ta amsa
ta huce ai shikenan, kai kuma ka kiyaye, kada ka sake aikata laifinka."
Da sauri Tijjani ya ce "In sha Allah! Na gode amma Wallahi bata ha'kura ba, kuna
tafiya zata cigaba da fishinta. Nima ta ce mini to yafi a k'irga."
Jin haka Malam mai Tafsiri ya sake d'ora hannunsa a kaina ya ce "Asiya na yafe wa
mijinki a madadinki, na rufe wannan maganar har abada, shin zaki yi mini wannan
lamini, zaki mini wannan mutuntawar?"
Yam jikina ya amsa. Wani irin abu ya tsriga mini a zuciyata wadda tun ranar da abin
ya faru ya tokare ni.
A sanyaye na ce "Shike nan Malam na yarda, na kuma yafe masa". Yana jin hakan.
Da k'arfi ya ce "Alhamdulillah! Allah na gode, Allah ka taimake ni, ka tsare ni."
Ya matso yana fa'din "na gode Yabi".
Na galla masa harara na ce "Wallahi ba dan Malam ne ya yafe maka a madadina ba, da
har ka tsufa kamar sa baza ka sake ganin walwala a fuskata bare dariyata. Ba kuma
zan sake aminta da kai ba. Amma yanzu ka ci darajar masu daraja".
Ya matsa kusa da Malam din ya ce "Na gode sosai Malam. A kuma taya ni da addu'a
Allah yasa k'arshen al'amarin kenan. Na gode muku, Allah yasa ku gama lafiya".
Suka tafi suna mini godiyar yarda da na yi sun isa da ni. Sai addu'ar mu samu
haihuwa mai albarka suke yi mana.
Shi kuwa jan kunne da tunasar da shi girman hakkina da yake kansa suke yi.
Suna ta jaddada masa idan ya musguna mini da gangan ba zai ga haske a al'amuran sa
ba.
Ya jima bai dawo ba, da alamun dai har gidajensu ya musu rakiya.
Ya dawo ya tarar da ni a falo. Na amsa sallamar sa na d'auke kaina.
Ya shigo da d'an kuzarinsa. Ya kalle ni ya ce "little me kike

Please Login or Register in order to submit comment