You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanta
Adda Nasibar ai dan ba yadda zata yi ne, akan dole ta bi ra'ayin ki domin tana da
darhamin imani a zuciyarta. Ya fara hawaye ya ce "Duk duniya ki rasa wanda zaki
yiwa kulunboto ya so diyar ki sai mijin d'iyar Baban Marina! Kaico da
Bakar hassada, kaico da mutanan da suke da son zuciya, wacce irin BAK'AR TA'ADA ce
haka? Asiri kika yi wa Yaya Bulkachuwa! Innalillahi wa inna ilaihir rajiun " Sai
kawai ya fito daga bayin a gigice ya zunduma ihu da dukkan muryarsa tamkar mace ba
jarumin namiji ba. Domin ya riga ya gigita da abin da ya ga ni k'warai da gaske.
Ta hau tafa hannu tana ce wa "Ashe a maza ma akwai makirai majununai? Zaka ga tsiya
da tuggu kuwa! Zan nuna maka uban ka ma ya wuce ya tozarta ni, ya kwaye mini
asirina. Zaka gasgata makircin mace aziman ne yau din nan".
Sai kawai ta takarkare ta zunduma ihu mai tsananin gaske. Da yake Dada barci take,
a firgice ta farka tana fad'in "Waye ya mutu Maryamu? Jin shiru sai kukan Anas da
na autarta ya cika mata kunnawan, ita ma sai kawai ta fashe da kukan daga dakinta.
Tana fad'in "Allah kasa basu harbe mini "Mai sunan manya ba. Lah ha ilah ha
ilallahu!
Mintina kalilan jama'a suka taru a k'ofar ta da Dada.
Baban Kasuwa da na Tsakiya suna gidan yayin da Baban Marina baya nan. Dan haka a
sukwane suka bu sahun ahalin gidan da suke ta shigowa a gigice.
Kowa sai tambayar ba'asin kukansu yake yi. Anas sai hadiyar zuciya yake yi ya kasa
bude baki ya yi magana.
Jikin kowa ya yi sanyi tare da sake shiga rudani mai yawa. Domin kowa yasan Anas ba
mai hayaniya ba ne sannan yaro ne mai juriya da hak'uri na gaske. Sun tabbatar ba
zai yi kuka irin haka ba tare da ya ga wata masifar, domin a lokacin da yake yaro
ma ba mai fitina ko koke koken banza ba ne, bare kuma yanzu da yake da shekara
ashirin da biyu, ya zama saurayi na sosai.
Baban Kasuwa ya ce "Maryo mene ne haka? Me ya faru ya tambaya zuciyarsa na rawa
irin ta zullimi.
Ta kuwa karkace ta kara k'arfin kukanta ta ce "Ban san yana makewayi ba. Sai na
afka bayin ba tare da na tambaya ko akwai mutum a ciki ba. Babu zato na ga Anas ya
gogawa al'aurarsa sabulu yana wasa da ita! Na zauce na fito a sukwane ina hirji.
Kunya tasa ya kasa fitowa. Sai yanzu ya yi jihadi ya fito, wai dan na yi masa
matashiya akan haramcin hakan shine ya fasa mini ihu yana neman k'ulla mini sharri
tunda dama dukkansu y'aya'n Alhaji sun tsananta mini akan Tijjani, mussaman y'aya'n
Asma'u da ko gaisuwa sun yanke yi mini dan su nuna mini Yabi ta fini a wajensu.
Amma ni ban ga laifinsu ba. Ubansu ne ya yarda
ta ni irin haka." Sai ta zarce da sabo n kuka.
Su Baban Kasuwa suka d'auki salati tare da ce wa "Muminin kare ne ashe kai. Kullum
da kai ake kwatance a gidan nan da ma unguwar baki daya saboda nutsuwar ka da
hamlnkalin ka ashe BAK'AR TA'ADAR da kake tafi ta yaranmu da ake yi musu kallon
fitinannu ne! Duk yadda aka yi kai ne ka yiwa y'ar wajen Malam Kabiru fyade satin
da ya wuce. Yarinya karama da ko magana bata iya ba, aka kasa gano mugun da ya
aikata mata aika aikar ashe kai ne".
Kuka ya tsayawa Anas cak. Ya Kalli Baba Maryo ya kalli Baban Kasuwa. Yana ta
kissima sune k'ananu a cikin iyayensu amma sune suke kan gaba wajen ruguza gidan
Marina. Bai gama nazarinsu ba sai ya jiyo Baban Tsakiya ya ce "A a tunda ba mu ga
ya haike mata ba, bai kamata mu jingina masa ba, shaidar zina babban al'amari ne.
Sannan idan aka ji maganar a bakinmu ai muma mun kunyata domin baza mu ce ba daga
gidan nan ya fito ba. Kawai shata masa layi zamu yi da y'aya'nmu kada ya dinga
b'ata manaa su bamu ankare ba tunda ya jefa kansa a wannan BAK'AR TA'ADAR ta
istimina'i".
Yara da manya kowa yabi Anas da kallon tsana da tuhuma. Duk Mama da kanta ta ce
"Anas ba lallatacce ba ne. Na tabbatar bai aikata hakan ba Maryo".
Sai lokacin ya samu kuzarin Budeibaki ya ce "A a Mama kada ki ce mata komai. Na
riga na kai alkalanci gaban Ubangiji. Idan ya tabbata na yi abin d at fada to ku
nema mini gafarar Allah. Na kuma yafe mata tozarta ni da ta yi, tunda ai ba hakan
ya kamata ta yi mini ba.
Idan kuwa ban aikata ba ta mini hakan to da ikon Allah ba zaki mutu da ido ba Baba
Maryo ".
Ta zunduma ihu tana d'ura masa ashariya.
Bai rufe baki ba ya ce "Ganinta na yi ta tono mugun k'ullin da ta yiwa Yaya
Bulkachuwa akan ya rikice akan Adda Nasiba. Tana fad'in ta fasa auren tunda dan
k'waya ne kuma mazinaci. Ganin na ganta ta k'ona layar shine ta mini hakan. Ba zan
zage ki ba, ko a lahira wani kan ci arzikin wani. Ban ci arzikin ubana a wajenki
ba. Nima ba zaki ci nasa ba. Kin ci arzikin kasancewar ki uwar Yaya Ammar. Ba dan
shi ba, ina rantse miki da girman Ubangiji sai na miki dukan da ko Dada sai ta yi
gaske da ta shaida ki. Amma babu komai na barwa Allah komai."
Ya mik'e yana tangadi yayin da kowa ya yi tsit. Ya kalli Baban Kasuwa ya ce "D'a na
kowa ne Baba".
Baban Kasuwa ya ce "Ni kad'ai zaka fad'awa hakan, shima Baban Tsakiya ai ya tofa
nasa"
Anas ya ce "Ko ya tofa dai bai mini k'azafi ba, gaskiyar fahimtarsa ya fad'a.
Dada tana bakin k'ofarta tana kurshegen kuka tana fad'in "Dambarwa ta tsananta a
cikin ahalina. Ubangiji na ci albarkacin sallah da salati, ka sassauta, yafe mini,
ka shirya mini zuria gabadaya".
Har aka gama wannan cecekucen Baban Marina da Gwaggo basu tofa ba. Mama ce ta shiga
lamarin ta yi kane kane tunda yanzu yar tsama ce mai tsananin gaske a tsakaninta da
Maryo.
Baya ga hakan kowa yasan Anas ba zai yi abin da ta fad'a ba. An kuma gasgata
shi,asirin da yaga ta tone.ne ya ya sanya ta yi wannan dibar albarkar.
Nasiba kuka ba wanda bata yi shi ba. Ammar da yake BAUCHI da ya ji labarin bai
dauke shi da muhimmanci ba. Murnar yadda ta kunce k'ullin da ta yi yake yi. Domin
yana matukar tausayin yadda Bulkachuwa yake damunsa ya kawo masa Nasiba ya ganta.
Yanzu kuwa tunda an warware zai daina, zai samu nutsuwa, tunda wani lokacin har
susuce wa yake zufa na karyo masa.
Da labari ya zo mana Babah ta ce mini "Tare ta hada ta mana ai, ni tun kwanaki na
kubuta. Nawa a kasan randa aka yi mini ta yadda zan zama mai sanyi akan sha'anin.
Sannan aka danne mini zuciyata.
Shi kuwa a k'asan murhun. Matukar aka hura wuta a murhun ba shi ba sukuni idan bai
ganta ba. Kai wacce irin BAK'AR TA'ADA ce haka?
Ta fara hawaye. Na taya ta muka yi kukanmu sosai domin ta ba ni tausayi. Da ciwo
kwarai ace d'an-uwanka ne zai musguna maka irin haka.
A raina kuwa na yafe dukkan musgunawar da Tijjani ya yi mini akan Nasiba. Na sake
gasgata ba yin kansa ba ne. Na kuma sake kudire a raina matukar ba Babah ba, wani
mahaluki ba zai ji halin da nake ciki da shi ba.
Zan jira shi har ya kammala WA'ADIN da zai yi, zan kuma yi gwagwarmaya har komai ya
daidaita mana.
Karshe na yi jarumtar ce wa "Mu yi hak'uri Babah ai ba kuka zamu yi ba.
Alhamdulillah zamu tsananta fad'a, mu kuma sake dage wa da addu'a."
Murya babu amo ta ce "Allh ya yi miki albarka, ya kara miki hak'uri, da ikon Allah
Ubangiji zai miki sakamakklon alheri na gode sosai"
Nafi wata biyu ban warware na fara sabgogina ba. Duk karshen wata zamu je mu gano
shi. Aliyu kuwa daidai gwargwado idan karshen wata ya zo zai siyo mana kayan
abinci, ya kawo da kansa ya kuma damkawa Babah kudin da zamu rik'e. Ya tisa yara a
gaba su fita, ya yo musu siyayya sai ya dawo da su. Shirin aurensa ake yi wannan
al'amarin ne ya dakatar da komai.
Haka su Yaya Salisu akai akai suke mana aika. Yaya Ammar kuwa duk sadda muka je
prison sai ya bawa Yara kudi masu auki, kuma babu jami'in da yake tsaya mana a kai
saboda Yaya Ammar.
Ba laifi kuma yana leko mu jifa, jifa shi da iyalinsa.
Yaya J ma duk watan duniya yana aikowa yara kudi amma bata hannuna ba, ta hannun
Yaya Rabiu. Shi kuwa yana turo mini ta asusuna. Idan na yi masa text din godiya sai
ya ce ba sai an ji ba. Bamu da wata matsala gagaruma. Amma da tafiya ta fara nisa
sai na fahimci dukkan masu tallafa mini kama daga kan mahaifana, Aliyu kanin
Tijjani, su Yaya Salisu da J hadi da tsirarrarun dangi masu bamu sabulai kowa yana
da nauyi a kansa baza su tabbata suna mana hidima ba . Mussaman da kullum rayuwar
take sake tsefe wa. Ina kwnace ni kad'ai a daki yara sun tafi makaranta yayin da
Baba take dakinta tana lazimi. Tunani nake yi tare da nazarin kaalaman da Tijjani
ya yi ta yi mini a lokacin da nake bacin ran shiga makaranta. Ba abin da yafi tsaya
mini a rai fiye da yadda yake ta nanata ni kad'ai ce yake da tabbacin bazan gaza da
hidimar y'aya'nsa ba.
A lissafi watanninsa tara a tsare. Har lokacin kuma bana aikin komai, ban dogara da
komai ba sai wanda dangi suke mana. Tunda na riga na gajiya na kasa yin kitso bare
lalle.
Na numfasa a fili na furta "Ya kamata na yi hobbasa na taimaki kaina.
Na hakurkurtar da zuciyata na fita na siyo kayan kunshi. Na fara posting na fara
lalle.
Ba'a dauki lokaci ba mutane suka fara dawo mini.
Da yake bamu da wasu matsalar sosia, sai na ninka aiken da nake yiwa Babanmu. Tunda
aka rufe Tijjani ahalin Baban Marina suka gane Tijjani ke hidimar k'ofar da kaso
bakwai cikin goma. Wanda ko ni ban gane hakan ba sai yanzu.
Dan haka na dage nake tallafawa Yaya Salisu da Yaya Rabiu rik'e gidan.
Gefe ina ajiye dan ajiye wani abu a banki, dan tsaron lalurar da zata zo mini
b'akatatan. Na shafe tunanin siyan gidan da nake burin yi. Domin tunda muka yi
fad'an da Baban 2 ya ce mini gidansa ne ba nawa ba nake tunanin ya kamata na siyi
gidan kaina. Idan na had'a zobuna na da dankunne na na sani ciko zan yi tunda manya
ne sosai kowa yasan yadda gold ya tsefe. Zan siya zuwa gaba idan na warware
matsalar Tijjani.
Sannu a hankali nake samun k'arfin zuciyar rungumar kaddarar da afko mana
bakatatan. Mussaman da Baban 2 ya kwantar da hankalinsa ya yi imani da kaddarar da
ta same shi.

*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Saiwowin maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki
da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*


95&96.


*HAJIYA HANNE ADO ABDULLAHI?*
*MARUBUCIYAR WANKA DA GARI DA KUMA WACE CE UWA?*
*KUN TUNA IRIN BAJINTAR TA AKAN RUBUTUN ADABI DA TARBIYA?*
*TO ITA MA TAKANAS NA SAMO MUKU LITTAFANTA DOMIN KUN SANI TA YI RUBUTU MASU
MA'ANA*.
*LITTAFAN DA YAWA, AMMA AKWAI DISCOUNT DOMIN SO NAKE KU YI TA SIYAWA Y'AYA'NKU DA
KANNENKU LITTAFAI MASU DARASI DA MA'ANA*.


*INA MUKU ALBISHIR AKWAI DUKKAN TSOFAFFIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA SALIHA
ABUBAKAR ZARIA*
*ZAKU SAME SU SOFT COPIES, A HANNUNA*
*SANNAN SABO DAL NA KAN HANYA*

*HAKA NAN AKWAI WASU DAGA CIKIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA HAFSAT C SODANGI, SUMA
SOFT COPIES KAZALIKA ITAMA SABON LITTAFIN TA MA KAN HANYA*

*BA DA JIMAWA BA ZAN ZO MUKU DA SU*.
*08032773332*


*INA MATUKAR GODIYA BISA ADDU'ARKU DA KUMA KAUNARKU GA RUBUTUNA*
*WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE TARE DA GODIYA GA DUKKAN WADANDA SUKA SAKA KUDINSU
SUKA SIYI WANNAN LABARIN DON JADDADA MINI SOYAYYA DA KUMA KARFAFA GUIWA*
*NA GODE, NA GODE*.


Auren Aliyu ya samu tasgado. Ba akan komai ba sai akan an kai suka gidansu amaryar
cewar d'an-uwansa dan safarar kwaya me gwamnati ta rufe shi Shima ana kyautara
zaton yana da BAK'AR TA'ADA. Muna ji muna ga ni aka hana Yaya Aliyu aure ba a akan
laifinsa ba. Dama Kuma Babaiba son inda ya dauko auren ba, yar babban attajirice. A
raina na Jin ciwon yadda mutanan yau suke yiwa mutane hukunci da laifin yan'uwansu
ko na dangunsu alhalin Allah da kansa baya bawa da laifin mahaifansa bare kuma
laifin d'an-uwansa. A zuciyata tamkar na ce masa ya nemi Iklima da a yanzu take
kwalejin koyon aikin jinya da ke Azare, tana shekarar karshe. A kansu a aka zurfafa
karatu ba tare da aure ba a gidanmu. Sun kammala sakandire babu samarin aure. Hakan
ya sanya Jabir samowa kannensa gurbin karatu a inda yake koyarwa. Gabadaya mun tafi
a cewa iyayensa suka hana ya had'a da ita. Hakan da muka gani ya sanya ni da su
Yaya Salisu muka yi kundubalar saka Iklima a Health Technology Azare.
A tsaye take cak, doguwa mai cukar halitta kuma fara tas. Na tabbatar ba zai
tankwabe ta ba, amma ina jin tsoron na furta.
Dan haka sai na tsiri gayyato ta hutu a karshen watan da na tabbatar yana yi mana
jele. Akai akai suke haduwa kuwa. Su yi ta cakar juna tunda shi ma mai zolaya ne.
Ni kuwa na dinga fad'in "um um fa Yaya Aliyu kada fa reshe ya juye da mujiya."
Wani lokacin ya yi dariya ya waske, wani lokacin kuma ya ce "Ba Wani reshe da zai
juye, yarinya kankanuwa, raini dai nake son jawo masa.
Baba kuwa idan ta ji ya ce haka sai ta ce "Saboda ka kallafawa ranka son ka auri
sa'aninka. Ban da haka ai itacw daidai da kai ".
A duk sadda Babah ta fad'i hakan dad'i ne yake matukar kama ni. Ina ganin nasara a
kudirina.
Matukar yana gidan ita zan saka ta yi masa girki, ta dafa masa zobo. Wani lokacin
ya yi godiya ya kwashi girki. Wani lokacin ya ce "Tunda na zama matar yayansa na
ture girme mini da ya yi, nake mu'amalantarsa a matsayin k'anina. Ban da haka me
yake hana ni na yi masa hidima da kaina sai na saka yarinya ta yi masa."
Na yi dariya na ce "Yaya Aliyu ko a lahira wani na cin arzkin wani ai"
Ba'a d'auki lokaci mai yawa ba ya fara fad'awa tarkonmu. Domin idan ya zo bai ganta
ba, ya dinga tambayar me ya hana ta zuwa. Ko ba hutu suke yi ba, da sauran
tambayoyi. Da na fahimci hakan kuwa sai na dakatar da zuwan nata. Domin so nake ya
taka ya neme ta a inda take ba wai sai ya ganta dan ya zo ba.
Ilai kuwa wanne tudu wanne gangare ya silala yake zuwa daga haka har suka had'a
kansu.
Tunda aka garkame Tijjani ban yi farin ciki har zuciyata ba sai akan wannan
al'amarin. Domin dai Na tabbatar Aliyu mutumin kirki ne. Sannan Babah uwace ta gari
bayan haka Ikilima zata auri mai rufin asiri. Zamu sake zargowa k'ofarmu wani
hasken.
Bugu da kari y'aya'nmu zasu kasance cikinsu guda. Tunda shi da Tijjani daya ne,
haka ni da ita.
Da maganar ta fasu a gidan Marina a lokacin da iyayensa suka je nema amsa aurenta.
Ba abin da ba'a ce ba. Bak'in ciki muraran har ce wa aka yi ai k'aramin likita ne,
wasu kuwa cewa suka yi ba ma likita ba ne. Malamin tsafta ne. Shi dai Baban Marina
ya ce ya basu. Mu kuma dukkanin y'aya'n sa muka goyi bayan al'amarin. Aka saka aure
idan ta kammala makaratan da wata daya, watanni biyar masu zuwa.
**
Alhaji Auta yana zaune al'amarin duniya ya sake damalmale masa. Gabadaya kasuwa ta
juya masa baya fiye da bara. Fatan da yake yi akan kamfani ya kyamaci filin Tijjani
saboda an kama shi da laifi bai ci ba. Har asiri yake nema akan su saki filin amma
shiru. Su kuwa kamfani sunce riba suke nema. A wajen suke samun gamsuwa, babu
ruwansu da laifin Tijjani. Idna lokacin da zasu biya ya yi, zasu tuntubi iyalinsa.
Ya rasa inda zai saka ransa. Jiya aoa kama babban dansa a cikin sahun y'an
kidnaffing.
Dazu kuma k'aramin dansa aka kama shi da yana yuwa yarinya yar shekaru uku lalata a
cikin gidansa. Gabadaya kwanciyar hankali da nutsuwa ta yi masa tutsu. Ya rame, ya
zama tamkar mai ciwon sida, tsufa ya keto masa na ban mamaki.
Yana kishingide amma damuwa ta yi masa k'awanya. Wai shine naira dubu take yi masa
wahalar rik'e wa?. Zullimi ya kama shi, idan akwai Bakar Taadar da ya yi ta dame
shi bata wuce had'a kai da aka yi da shi wajen yiwa dan amininsa kazafin da yake
kulle tsawon shekara guda ba. Ya yi shiru yana tuna irin yadda Tijjani yake zuwa
yana gaishe shi cikin girmamawa. Akai akai yake yi masa alheri a matsayinsa na
aminin ubansa kuma ubangidansa a kasuwa. Amma shaid'an da hassada suka saka ya
jagoranci zaluncin da aka yi masa.
Kuka shabe shabe da hawaye. Ya rasa ta inda zai warware wannan k'ullin da suka yi.
Kan dole ya kira diaya abokin sharrin nasa, wanda yaro ne a kansa dan ba zai girme
wa Bulkachuwa ba. Ya dauka murya a shak'e ya ce "Alhaji kana mini waya da ta wuce
kaidar hankali gaskiyar magana na ke fad'a maka. Nima nema nake idan zan samu, ka
fitine ni da bani bani gaskiya".
Da zullimi ya ce "Ba rokon zan yi ba Haladu! Maganar Tijjani zan yi maka. Gaskiya
na yi abin da ya sha mini kai. A harzuke ya ce "To ni me zan yi maka? Ina ce Kai ka
kawo shawarar, Kai ka kitsa yadda za'a yi? Ni kawai na karba a hannunsa tare da
bawa haro ya ba shi. Hatta lambar wayar da aka kira shi, kai ka siya tun kuma a
ranar ka taune shi. Kai ka yiwa Yan sandar hanya shunensa tare da bada lambar
motarsa. Kaine zaka yi dakon zunubin ka. Idan ka yi kuskuren saka ni a ciki kuwa
Wallahi sai na bata maka suna a idon duniya. Sannan sai na lahanta ka."
Kuka wiwi ta k'wace wa Alhaji Auta tamkar mace.
Ta ya ya zai kubutar da Tijjani?

***
Yini na yi ina yiwa wata hamshakiyar Hajiya kunshi ita da mukarrabanta. Da zata
tafi ta ajiye mini kudi a envelope. Ga mamakina da na bude dubu hamsin na gani a
ciki. Duk da sunzo da yawa sosai. Amma tabbas kudina bai kai haka ba. Rub'anya mini
ta yi. Ban sani ba ko dan na yi jarumtar yi musu jollof din taliya mai dad'i ne. Na
kuma baibaye su da pure water mai sayi tunda Ina siyarwa.
Na lura ta ji dad'in yadda na yi musu, sannan ta yaba da kunshin da na yarfawa
kakkaurar k'afarta fara tas.
Cikin hira nake fad'a mata na iya kwalliya ma sai dai nafi bada k'arfi a lalle da
kitso.
Kwanaki biyu da tafiyar ta sai ga waya ta k'ira ni akan wani satin zan je gidan
gwamnati na yiwa mai dakin gwamna kunshi zata je bikin d'iyar gwamnan Jigawa.
Jikina ya sab'e da rawa. Ni Yabi zan je government house a sanadin sana'a ta?
A fili na ce "Alhamdulillah! Ubangiji ka bani damar da zan yi amafani da ita na
fito da Baban 2. Allah ka yi alkawarin taimakon wanda aka zalunce shi. Ubangiji ka
shiga lamarin Tijjani."
Na zauna kusa da Babah ina fad'a mata. Ta yi farinciki sosai.
Na ce "Idan mun je ganinsa zan fad'a masa, idan bai amince ba zan hak'ura, tunda
nasan baya son na dinga zuwa gidajen mutane".
Ta zuba mini ido ta ce "Allah ya yi miki albarka, Ubangiji ya kawo mana karshen
ibtilain nan. Allah ya dawo da mijin ki, zaman zai yi miki yawa babu miji a tare da
ke."
Sai kawai ta fashe da kuka sosai. Da rawar murya nake bata hak'uri. Ina ce wa "Zan
iya Babah! Zan jira shi, da ikon Allah zai dawo a kusa ma".
**
Muna ta shirin tafiya dubo Baban 2 a dalilin a irin wannan ranar ta asabar din
k'arshen ko wanne wata muke zuwa duba shi, tare da kai masa kayan shopping tamkar
na dan makarantar kwana.
Ni nake had'a masa wannan kayan. Kudin lallena da kitso suna tafiya ne a hidimarsa
da ta gidanmu domin Yaya Aliyu ne yake rik'e da mu. Daidai da pencir ban san na
siyawa su Hanif ba. A yadda na taso a irin gidanmu da babu tausayi da tallafawa na
k'asa ban yi zaton Aliyu zai yiwa Bulkachuwa irin wannan zumuncin ba. Na sani
hidimar kayan abincinmu da baya mantawa akwai alfarmar mahaifiyarsu a tare da mu.
Amma yadda baya mance wa da y'aya'n Tijjani na gamsu ko Babah bata tare da mu zai
yi iyakacin kokarinsa.
Da na fahimci basu mayar da hankali wajen kai wa Tijjani kayan ciye ciye ba. Ni
kuwa sai na mayar da hankali, domin shopping nake yi masa mai sunan shopping. Hatta
kifin gwangwani ina siya masa fiye da dozin guda duk wata. Kayan shayi da su
conflakes kam ba'a maganarsu. Babah har fad'i take wai kayan suna yin yawa. Biskit
irin masu dadin nan kullum na yi lalle sai na siya, kafin lokacin da zamu je, sai
na yara masu yawan gaske. Sannan bana raba shi da cincin da cake. Kullum fes muke
ganinsa. Illa duhu da ya yi. Amma da dukkan zuciyarsa ya karbi kaddarar da ta fad'o
masa. Da wuri muke tafiya, da k'atuwar tabarmarmu. Tunda Yaya Ammar yana cikin
manyan gandorurobobin kurkun bamu da matsalar komai. Domin yini muke sai yamma lis
muke dawowa.
Muna zaune mun gama cin abinci. Ya kalle ni ya ce "Baba lafiya bata zo ba yau?"
Na yi murmushi na ce "Ta ce wai takuramu take yi, ba zata zo ba sai wani zuwan".
Murya babu amo ya ce "Da ta zo abin ta."
"Ni ma hakan na ce mata Wallahi".
Ya kalli yaran suna can nesa damu suna kallon bishiyar mangwaro da y'aya'n suka
sauko kasa kasa ana iya mika hannu a tsinko.
Ya kankance murya ya ce "Little kina kewata ko?"
Na yi k'asa da kai, idona ya cicciko domin babu yadda za'a yi mu zo bai mini wannan
tambayar ba. Na fahimci ita ce tafi damunsa. Na kalle shi na ce "Ina kewar ka sosai
Baban 2. Kullum dare idan na kalli inda kake kwanciya sai na jika filo da hawaye!
Amma ina karfafa kaina guiwar cewa tunda muna shakar numfashi daya a wannan duniyar
akwai lokacin da zai zo da zaka dawo cikinmu mu cigaba da rayuwa. Ina kuma da
tabbacin rayuwar da zamu yi zata Fi wacce muka yi a baya nutsuwa da kwanciyar
hankali. Yaya Aliyu yana matukar kokari akan gidanka. Su Yaya Salisu da su Ammar
suna taimaka, bamu da matsalar komai sai rashin ka."
Ya ce "Ke Baki fad'o naki k'ok'arin ba little ".
Na ce "Ka sha fad'a mini, ni kake da tabbacin ba zan gaji da hidimar y'aya'nka ba.
So nake ka gane ba y'aya'nka ba kawai kai kanka da mahaifiyarka ba zan gaji da
hidimar ku ba, muddin ina numfashi."
Ya kasa magana. Sai can ya nisa ya ce "Ina son ki sosai little. Ina rok'on Ubangiji
ya taya ni son ki, ya k'ara miki hak'uri da jarumta".
Cikin rauni na ce "Ameen" domin ya yi matukar ba ni tausayi.
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "jiya shekara ta d'aya a nan. Tunanin ki kad'ai yasa
nake ganin na dade. Amma ban da hakan ba k'aramin gata aka yi mini ba. Domin tunda
nake ban tab'a samun damar da nake yin ibada nake ambaton Ubangiji irin a wannan
lokacin ba. Na gamsu akwia hikimar Ubangiji ta sakaye ni a nan. Ba ni kaina ba, ko
ke addu'ar da nake yi miki little ta ishe ki, bare kuma y'aya'n ki. Shi yasa ban
damu sosai ba, da aka kasa fitar da ni".
Na ce "Allah ya karba. Ina kuma ganin tasirin addu'ar ka garemu domin bamu tozarta
ba Baban 2."
Ya ce "Ki tsananta addu'ar nan ta*RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN
FAQIRUN.* Kullum ina fad'a miki tasirinta mai yawa ne".
Na zuba masa ido, shi ma ya zuba mini tsawon lokaci muna kallon juna, idanuwanmu
cike da k'walla.
Ya yi k'arfin halin danne nasa hawayen ya hadiye. Ya ce "So nake na gan ki da ciki
Little"
Nasan yadda kike son haihuwa. Na kuma tabbatar renon ciki da hidimar bebi zaisa ba
zaki ga nisan zaman da zan yi ba".
Na ce "Ta ya ya hakan zata kasance Baban 2?"
Domin ni kaina idan har zan samu cikin zan yi matukar farinciki mai yawa.
Ya ce "Kina so?"
Na daga kaina da sauri amma ban yarda na d'ago kaina ba. Domin haka kawai na ji
kunya ta rufe ni.
Ya ce "Shike nan zan roki arzikin Ammar ko zai mini alfarma".
Na ce "Me zaka ce masa?"
Ya ce "Zaki ji daga baya."
Na d'ago na ce "Amma Baban 2 idan na samu ya bare kada ka ce na zubar maka fa,
nasan halin ka".
Ya dan murmusa ya ce "Ai ina fad'a miki ne dan na rama rikici da tashin hankalin da
kika dinga yi mini kafin ki samu cikin twins".
Na rufe idanuwana ina dariya sosai".
Na ce "wanccan

Please Login or Register in order to submit comment