You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a tsakar gidan Dada yana zaune kan kujerar
tsuguno. Na zauna akan turmin da yake fuskantarsa.
Ya kalle ni da tarin kulawa ya ce "Asiya Toro me yake faruwa ne? Jiya na shiga
Bauchi sai nake jin labarin da ya ki'dima ni a bakin Honarable.
Nasan ba zai mini karya ba, me yasa kika canja?
Me yasa dan Allah?"
Na yi k'asa da kaina haka kawai na ji hawaye ya k'wace mini. Domin idan aka cire
yan kofarmu ba wanda ya nuna damuwarsa ko alhini akan shiririce wa da maganar
Kwamshina ta yi sai Tijjani.
Na tabbatar bayan soyayyar da yake yiwa lamarin, to akwai kishin wula'kanta ni da
aka yi a gidan, shi yasa yake son na yi auren ke ce raini.
Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi ya ce "Ba kuka zaki yi ba, ya ce mini Baba ya
gabatar masa da hujja mai k'arfi shi yasa ya ha'kura.
Wacce irin hujja ce wannan dan Nabiyur Rahmati?"
Ya fa'da a matu'kar zafafe.
Kafin na ce komai sai Dada ta rarrafo ta ce "Ni ce nan! Na barranta lamarin, na
kwashe masa albarka, ba zai yiwu na ha'da jini da mai kafirtamu ba. Ba zai yiwu ta
auri wanda iyayenta suka tabbatar ba mutumin arziki ne ba".
Da kakkausar murya ya ce "Dada me kika yi hakan?
Su waye iyayenta?"
Yana rufe baki ta ce "Su Badamasi mana".
Maimakon na ga ya sake fusata sai kawai na ga ya kwashe da dariyar iyashege ya na
fa'din "wannan shine abin dariya kunama ta ciji danwanke. Shi Baban Tsakiya idonsa
da kwalli har ya ce wani bai cancanci Yabi ba?
Sanin kowa ne Jabir da Yabi masoya ne tun suna yara k'ananu, amma shi da kansa ya
datse soyayyar kuma yanzu Allah ya turo mata wani sai ya ce bai cancanci a ba shi
aurenta ba. Wanne irin lamari ne mai kama da k'yashi da kuma hassada?"
Dada ta rabka salati tana fa'din "Kawunka kake fa'din wannan kalaman a kansa?
Mai sunan manya anya zaka yi hankali kuwa?
Kusan ma fa saboda kai ya yi wannan al'amarin amma ka ke sakin maganganun da suka
yi daidai da zaginsa kake yi."
Ya sake fashe wa da dariya ya ce "a kaina, ni kuma?
Lallai kuwa, zan ga ta yadda za'a yi, wannan bawan Allan ya nufo ni da wani alheri.
Rannan ba abin da bai fa'da mini ba, akan sun je kai mini ku'din aure gidan kananun
mutane ba'a karba ba.
Ya dinga cin alwashin ba zai sake shige mini gaba a harkar aure ba. Ni kuma abin da
bai sani ba, ai kawu ba uba ba ne, dama dangin uba ne a hakku su nemo mini aure,
bare ya ce zan wani damu."
Dada ta sake rangada salati tare da cewa "Mai sunan manya wanne irin dibar albarka
kake yi ne haka tamkar ka sha k'waya?"
A tunzure ya ce "Ras nake! Na gaji da fitinar mutanan ne, duk wata fitina su suke
kitsa ta.
A gabansu uwar Nasiba ta dinga sakin maganganu a kaina ta barranta y'arta da ni, ba
wanda ya ce kala a cikinsu. Haka nan shima har yau ba wanda ya kalubalan ce shi
akan hukuncin da ya yiwa Jabir na auren Maijidda saboda yana da cikakken iko a
kansa. Akan me zai yiwa lamarin Asiya katsalandan alhalin ba kallon y'a yake yi
mata ba?
Akan me zai nemi ya dinga nuna ya isa da ni alhalin akan idon uwata suka kasa yi
mini alfarma da kawaici."
Ta ce "Allah ya shirye ka, albarkar mai sunanka shiriya zata sauko maka."
Ya bata fuska ya ce "Tare zaki roka ta zo mana da ke, tunda akan idonki ake yin
abubuwa na kura kurai amma ba kya iya tsawatar wa. Rannan na ji wani malami yana
fa'din ainihin manufar ma'anar kuyanga ta haifi uwargijiyarta. Sak fatawar da ya
bayar tamkar ke ya siffanta haka na dinga ji".
Na zuba ido. Ina jiran ta rushe da kukan da zata tara masa jama'a tamkar yadda take
yi mana. Amma sai ta share ta yi mirsisi ta fanshe da cewa "Shi ubanta ai ya yarda
na isa da shi, shi yasa ya katse al'amarin babu tashin hankali.
Allah ya shirye ka mai sunan Shehu.".
Ya shareta ya kalle ni ya ce "Yanzu kina son wannan ba'kin yaron ko kuwa dole aka
yi miki?"
A hankali na ce "ko bana sonsa tunda Baban Marina ya amince ai maganar ta kare".
Ya girgiza kai ya ce "Baban Marina mutum ne Wlh amma ban son ha'kurinsa, any way
Allah ya sanya albarka all the best Asiya Toro".
Daga haka ya mike ya fice yana fa'din da kin ce ba kya so. Wallahi da tsaya miki
zan yi, komin sharrin mai sharri ba za'a baki wanda ba kya so ba, domin kema y'a ce
ba baiwa ba. Kina da hakkin ki so a kuma so ki".
Wannan abin da ya yi mini sai ya rage tsanar sa a raina.
Dada ta dinga fa'din "Sha sha kamar ba saboda shi aka yi komai ba."
Na rasa gane manufar wannan maganar ta Dada.
Tsawon sati da kulla alakarmu da Nura wanda ya yi zuwa uku kenan.
Mamakin kaina nake ta yadda ya shiga raina sosai.
Ko dan sau'kin kansa da yadda ya iya kwalliya da shirya zan ce ne?
Ga shi ma'abocin kyauta duk zuwa sai yasan me ya ru'ko mini wala na ci, ko na
amfani, gwargwadon k'arfinsa.
Mahaifiyarsa da ake kira Yaya itama ba karamin son al'amarin take yi ba. Domin da
kanta ta zo da kuma ledarta mai shak'e da kayan kwalliya.
Kusan yini ta yi lamarin da ya takura ni, kunyarta sosai na ji. Wanda ko kusan ban
ta'ba jin irin hakan akan mahaifiyar Yaya J ba.
Karba ta samu daga ahalin gidanmu, dan kuwa ko Mama bata yi abin kaico ba, har ta
tafi.
Dada ce dai bata wani karbe ta da fuska mai yakanah ba, hatta shi da kansa da ya je
gaisheta bai ji da'din karbar da ta yi masa ba.
Hankalina ya fara tashi domin kuwa ba hannu Rabbana ya je mata ba, sai da ya siyo
mata lafiyyayun lemo da kankana da ayaba tika tika.
Na dinga fargaba da tunanin wata'kila wannan d'in ma, ta yi mini sanadinsa tunda su
Baban Tsakiya kullum cikin fadin Alh Tanimu munafiki ne wai yana nuna wa ya fisu
kusanci a wajen Dan-uwansu".
Kuma gaskiyar magana a yanzu da muka shafe satika kusan uku ba k'aramar shakuwa
muka yi da shi ba.
Ina matu'kar kad'uwa a duk sadda zuciyata ta ayyana mini muna iya rabuwa. Ban ta'ba
kuma shiga irin wannan yanayin a baya ba.
Duk kishin Yaya J a kaina ya ha'kura ya bar ni da Nuru domin da kansa ya ce ba zai
hana ni kula shi ba, amma shima kada na ce na sallama shi, ya yarda ni din allura
ce cikin ruwa mai rabo ka dauka.
Dan haka zai cigaba da lalube cikin ruwa har Ubangiji ya taimake shi ya damk'e abin
da yake nasa ne


KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA
KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA
KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*


✍️

*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA
BAKAR TA'ADA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.



*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta
sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar
taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi
muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun
san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa,
mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai
soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan
littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan
numbers*
*08089965176*
*07084653262*

*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA
KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA
KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*MASU BUKATAR YON RIGISTA DA G.H.T. KAKARKU TA YANKUE SAKA DOMIN KUWA FASEELAT ZATA
MUKU JAGORA HAR KU FAHIMCI KOMAI CIKIN KYAKKWAR MU'AMALA DA KYAUTATAWA*.
*07039269802*


Haka rayuwar ta cigaba da tafiya, kusancina da Nuru yana sake shahara. Har ta kai
ya goge mini rad'ad'in rashin kwamshina a zuciyata.
Rashin Yaya J ne bai bar ni gaba'daya ba, amma ya yi rauni matu'ka da gaske.
Yayin da Bulkachuwa ya d'ora masa karan tsana haka siddan.
Sau biyu yana ganinmu idan Nuru ya ba shi hannu sai kawai ya d'aga masa, amma ba
zai yarda ya ba shi nasa ba.
Na cigaba da zuwa makaranta hankalina ya fara kwanciya. A lissafi saura kwanaki
talatin da tara na bar gidan.
Tare za'a ha'da da na Nasiba domin tuni wanda za'a bata ya ce ya kammala gininsa
dan haka ba za'a kai bad'in da suka ambata da farko ba.
Lafiya lafiya yan uwan Alh Tanimu suka kawo komai na al'adar aure aka karba, cikin
mutuntunta juna.
Saboda Baban Marina ya gayyato yan'uwansu na Lame da Kano kan dole su Baban Tsakiya
suka zauna aka karbi bak'i da su.
Gidan Nuru da yake bayan gari k'arami mai kyau shigen na Yaya J.
Irin murnar da nake ciki na barin gidanmu tamkar wacce na girma ba'a gaban uwa da
uba ba.
Domin na riga na kai makura wajen son na kauce na bar wa su Baban Tsakiya gidan su
tabbata a cikinsa.
Ubaida ce farkon wacce aka kai makaranta kwana a gidanmu.
Idan mai karatun bai manta ba diyar Baban Marina ce itama diyar Inna ta biyu.
Yau an yi hutun zangon karatu na biyu.
Bulkachuwa ne ya taho da ita tunda shi kusan akai akai yake zuwa Bauchi.
Tana GGC Bauchi ne ajinta uku, mutumiyar Ikilima ce haka suke tamkar ni da Nazira
sai dai banbanci akwai tazara mai yawa tunda shekaru kusan uku ta bawa Iki. Amma
amincin da yake tsakaninsu sai Allah.
Saboda Ubaida, Iki ta nace boarding ita ma zata tafi, duk da dai ta fara day ajin
ta d'aya a sakandire su d'in kamar karatunsu ba zai yi sauri irin namu ba.
Tunda a yanzu haka har Dada ta fara maganar auren Ubaida, a dalilin tana da garin
jiki, kuma tana shirin shiga shekaru sha biyar ne.
Cikin farin-ciki muke hutunmu, na saje a tsakanin Ikilima da Ubaida tunda ni din ba
ni da auki.
Ba abin da yake damuna sai bibiya da nacin yaya J.
Matu'kar kuma na yi saken da muka ha'du yini nake yi babu sukunin a dalilin fama da
tsallen badake da zuciyata take yi.
Da yake aurena ba kwatsam ya zo kamar na Nazira ba, Baba ya samu damar siyan
dimemiyar katifa mai nagarta.
Ya tanadi labulaye da kafet, da ledar tsakar daki da kuma bargo.
Irin dai kayan da aka yiwa Nazira.
Ya ce idan ya samu dama ko a ranar da za'a kai ni ne idan ku'din gado da kujeru sun
samu sai a siya tunda gasu nan a bakin titi ko ina, idan kuma bai samu ba to a
hakan zai kai ni arzikin gidan miji yafi na uba.
Ban damu da rashin kayan katako ba, na sani in sha Allah yan'uwana zasu yi mini
irin na Nazira.
Sai dai bani da garanti akan manyanmu yan dakin Mama. Domin sun yi nisa a cikin
*BAK'AR TA'ADAR* Y'an ubanci.
Su Yaya Salisu ne kawai zasu tsaya mini tunda sun fara daukar albashi duk da dai ba
mai wani nauyi ba ne amma dai sunfi da .
Ranar asabar mun dawo daga Islamiya.
Yammaci ne sosai muna tafe da yan ajinmu.
Mun zo daidai wani gida da bai kammala ba, muka ga Bulkachuwa da wata yarinya wacce
nafi zaton ita ce Bilkin da na ji yana fa'da a waya kwanaki, sun fito daga cikinsa.
Gajeriya ce, amma fara ce sai dai ko kusa bata kai ni ba.
Sannan ita din yar duma duma ce tamkar su Nasiba.
Kirjinta a cike yake, jikinta irin rugu-rugu ne.
Nan da nan shaidan ya kawo wa zuciyata caffa domin take sai na yi aiki da zato, na
zarge su da al'amarin da shaidarsa yana da tsananin tsauri.
Na kalli Nasiba na ga hankalinta na kansu, tausayinta ya kama ni, domin sai yanzu
na gane ba son Nasiba yake yi ba, domin ko ka'dan bai yi mata uzziri irin wanda ya
yiwa Bilki ba. Ko da yake maganganun da mahaifiyarta ta yi wa uwarsa ne suka yi
masa ciwo ba ka'dan ba.
A zuciyata na ce shi kuma Bulkachuwa yana son lukataye masu manyan nonuwa.
Na sake kallonsu na gan shi kamar kullum ba wani wadatatcen wanka, yana cikin
yanayin babu yabo babu fallasa.
Amma ni kam duk saurayin da ya zo mini a haka ina da tabbacin ba zan saurare shi
ba.
Domin an sanya mini son namijin d'an wanka, haka nan na k'yamaci marar gyara irin
Tijjani.
Amma a hakan yake murza zuciyoyin yan mata kintsatssu da watsatssu.
Na sani kuma kyaunsa da zubin k'arfin da yake da shi yake rudarsu.
Gaba'daya a murde yake dukkan physiques dinsa sun bayyana alamun yana motsa jiki
yadda ya kamata.
Na ja tsaki muka wuce, yayin da ya yi kamar bai hango mu ba.
Ba zato na ji Nasiba ta barke da kuka mai sauti.
Wani har tsayar da mu ya yi yana tambayar ba'asin kukanta, domin dai ya dauka ta
samu labarin rasuwar uwa ko ubanta ne.
Kukan nan na Nasiba ya yi matu'kar dukan zuciyata, domin na san pain din da ake ji
na kubuce war masoyi domim ni din katuwar victim ce.
Muna tafe, tana kukan bata fasa ba, duk yadda nake bata ha'kuri da kalamai masu
nutsar da zuciya.
Kukan nata sai ya zama sanadin tabarbare war sassaucin da na yi akan al'amarin
Bulkachuwa.
Domin na dauke shi a mai son kansa, mai fifita bare akan jininsa.
Sannan fitowar da suka yi daga kongon gidan da babu kowa a ciki ya sanya na sake
k'yamarsa da dukkan zuciyata, domin kowa ya shaida shi din mai BAK'AR TA'ADAH ne.
Da k'yar na shawo kanta ta yi shiru.
Amma a k'asan raina haushin makauniyar soyayyar da take yi masa nake yi.
Gaba'daya ta lalace, ta zube bata farin-ciki ko ka'dan da auren da za'a yi mata.
Uwarta kuwa ta ja ta dake akan sai dai ta canja uwa matu'kar ta ce ba zata yi wa
mahaifinta biyayya ta so d'an-uwanta da ya za'ba mata ba.
Duk da k'arancin shekaruna na fahimci Tijjani ne kawai mahaifiyarta bata so, domin
kuwa mahaifin su Nasiba bai cancanci ya yi irin wannan ikon ba, tunda gaba'daya
fita ya yi daga hidimarsu, ba wanda ya taba ganin an kawo musu wani abu daga
mahaifinsu, ko danginsa, duk wahalarsu uwarsu ce da danginta.
Amma an zo batun aure ya nuna ikonsa na uba, ita kuma duk ba'kin cikin da ya k'unsa
musu daga ita har Dada sun manta.
Abin da nake tambayar kaina shine shi wanda Baba Maryon ta fifita akan dan
yar'uwarta tana da tabbacin nagari ne?
Ko dan kawai ma'aikacine, ya kuma gina gidansa?
Na yi imani da ace Bulkachuwa yana da ku'di to ko yafi haka lalace wa za'a ba shi,
duk wani na'kasunsa sai an yi masa kwaskwarima ya zama abin uzziri.
Amma da yake bashi da ko sisi, sai take ta akilon y'arta ta nisan ce shi, ta so
d'an-uwanta na dangin ubanta, na d'an yar'uwarta kuma ya tabbata a lalace.
Muna isa gida Dada ta hau tambayar makusidin kukanta.
Kai tsaye na shiga rattaba mata dalilin.
Ta yi tsaki ta ce "Kare ya cinye miki zuciya Nasiba. Ina ce jiya a gabana ya tsaya
yana miki kashedi akan ki sakar masa kurwarsa?
Bakaken maganganun da ya cusa miki, ai masu cizo ne da kina da hankali.
Domin bai ji kunyar idona ba ya ce miki komin k'wadayin ki shi yafi k'arfin ko
dandana shi ki yi, bare kuma ki mallake shi a matsayin miji.
Amma dan lalace wa har ki zauna kina kuka dan kin gan shi da wata? Bayan Allah ya
baki mai son ki, nutsatssatse ba irinsa ba. Bayan hakan kuma mai abun hannune ta ko
ina ya yiwa mai sunan manya fintikau. Ban da ma darajar jini me zai sa ki so shi
haka?
Ko an yi auren ma wahala zaki sha tunda ba sonki yake ba, ga kuma talauci da
takaicinsa."
Jikina ya sake mutuwa ina ayyana duk soyayyar da take tsakanin Dada da Bulkachuwa
amma take iya fa'din hakan a kansa saboda Nasiba?
To wai wa take so ke nan a tsakaninsu?
Take na yanke hukuncin Nasiba take so.
Na tsinci kaina da jin haushin yadda bai san ciwon kansa ba.
Kullum a fa'din ya daina mugayen dabi'aunsa yake, ashe ba hakan ba ne.
Ina tsaye tamkar gun ki aka fara kiraye kiraye sallar maghariba.
Murya a dashe na ce "sai anjima Dada".
Na tafi na barta tana ta kumfar baki da dan mulmulallen bakinta.
Muna idar da sallar na kalli Gwaggo na hau rattaba mata bayani.
Ina fa'din "Gwaggo ashe har yau Bulkachuwa yana yin iskanci?
Dazun na gan shi da wata sun fito daga kongo".
Ba zato na ji ta gwabe mini baki. Tare da cewa "A ina kika san iskancin?
A ina kika ga yana iskancin?
Kinsan girman al'amarin da kike fadi kuwa?.
Dan sun fito daga kongo shike nan sai ki yi shaidar zurr?
Annabi ya tsananta jan kunnenmu akan shaidar zurr.
Kinsan matakan da sharia ta gindaya kafin a zartar da ce wa mutum ya yi zina?
Sai an ga mutum turmi da tabarya, kuma daga bakin muminai da aka gasgatasu har guda
hudu.
Ba dan komai ba saboda kiyaye nasaba da mutunci.
Amma mutanan yau sun manta wasiyyar ma'aiki a kan kazafi da shaidar zurr. Ki kiyayi
yada sharri Yabi."
Na kasa ce wa komai a dalilin ba k'aramin azaba na ji ba, domin da k'arfi ta bugi
bakin nawa.
Ta zarce da fa'din " Àllah ka shiryi duk wanda ya kauce hanya, Allah ka shirya
zuri'ar al'ummar Annabinka. Allah ka shirya Tijjani, ka bashi sana'a, ka tsare shi,
ka mayar da shi nagartacce".
Na amsa ameen a zuciyata, ina alkalancin maganganun Dada da na Gwaggo akan
Bulkachuwa.
Shike nan sai na kame bakina ban yarda na sake fa'din wannan maganar ga wani ba.
A hakan har aka shafe sati dai-dai lokacin saura sati biyu aurenmu.
An kawo lefen Nasiba.
Lefe kuwa mai kyau, komai sai son barka, domin komin kushen mai kushe na zai kushe
kayan ba.
Amma gare ta babu wata murna. Dan ko dazun nan sai da na ga tana wanke wa
Bulkachuwa kayansa.
Ba kuma sata ya yi ba. Ajiye wa ya yi a inda ake wankin ita kuma ta jika ta wanke
tare da na Dada.
Kwanaki biyu a tsakani aka kawo lefena.
Sun yi kokari kwarai da gaske domin duk ha'duwar kayan Nasiba, nawa sun zarta nata
da ka'dan.
Amma abin mamaki ahalin gidanmu basu zuzuta kayana kamar yadda aka yi ta kuranta na
Nasiba ba.
A lokacin kuma Dada da y'ay'anta kullum sai sun zauna, Babanmu ne kawai ba'a sa shi
a cikin zaman sai Baba ta Bulkachuwa ita kuwa ba a garin take ba.
Saura kwanaki goma sha biyar auren Dada ta zaunar da Babanmu.
Bamu san me ta ce masa ba, amma dai mun ga ya shiga cikin rashin sukuni har
washagari.
Ashe ce wa ta yi auren Yabi da Nuru ba zai yiwu ba matu'kar tana da iko akansa.
Ya nemi sanin ba'asi ta ce ya saurare ta zuwa jibi.
Bai sanar da kowa ba, har sai ranar da ta ambata.
Dukkansu suna zaune a dakinta.
Cikin rashin damuwar komai ta ce "Alhaji! Yanzu ya kyautu ace an bar mai sunan
manya yana gararanbar neman aure ana hana shi, alhalin akwai yara a gabanku?
Kullum da abin nake kwana, nake tashi, tare da zullumin kar'bar da zaka yiwa
al'amarin.
Sai kuma na tuna ikon da shari'a ta bawa uwa ".
A sanyaye ya ce "Hakane".
To maganar auren Yabi da wannan ba'kin yaron ba shirayayya ba ce daga Allah.
Domin mai sunan manya za'a bawa ita."
Wani irin zullumi ya shige shi.
Murya a raunane ya ce "Dada ina ce Nasiba yake so?"
Nan da nan ta ce "Nasiba ai ubanta ne ya yi iko a kanta ya ce dan k'aninsa zai
bawa."
Ya ce "Dada ina ro'kon arziki a ba shi wata cikin yaran Badamasi ko na Iliya tunda
an riga an karbi komai na aurent a, akwai nauyi mai yawa a tsakaninmu da uban yaron
nan ke ma shaida ce".
Ta kai kallon ta ga Baban Tsakiya ta ga ya murtuke fuska.
Nan da nan ta ce "Duk abin da yake tsakaninku da Tanimu ya kai da yar'uwar ka ne?"
Da sauri ya ce "Ba kai ba Dada! Sai dai haramun ne neman aure a cikin aure."
Baban kasuwa ya ce " Ai ba bisa son zuciya ba ne, biyayya ka yi, Allah kuma zai
karrramaka tunda ka bi uwa. Idan ya so sai a bawa Nura Kaltume ba shike nan ba."
Baban Marina ya kalli kaninsa da wani irin duba.
Yana mamakin son zuciya irin tasa. Ya dauki y'arsa ya bawa Jabir yasan kuma
saurayin Yabi ne. Yanzu kuma a kan idonsa yake fadin zai sake bawa Nura y'arsa
tunda yasan akwai mamora a tare da yaron.
A hankali ya ce "To ko zaka lamince na bawa Tijjani Kaltumen kawai?"
Nan da nan ya ce "Ina! Ai ba ita Dada ta umarta ba, so ka ke na shiga fishin uwa?"
"Shike nan Allah ya amsa addu'ar ka, Allah ya sanya albarka a cikin wannan ha'din ,
ya amintar da lamarin. Na bawa Tijjani Yabi, da dukkan zuciyata"!
Baban Marina ya fa'da cikin wani irin yanayi mai ban tausayi.
Dada ta ce "Allah ya yi albarka".
Har ya yunkura zai tashi sai ya ce "Zan bawa shi Nuran kanwarta. Komai da suka kawo
da sunan Yabi ya koma kan Ubaida".
Ya fita yana ha'da hanya.
A zaure suka yi kicibus da Bulkachuwa.
Baban Marina ya kalle shi cikin wani irin yanayi.
Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Dubi gashin kanka, kamar ba bahaushe ba,
ka dubi wando jikinka, tamkar babu iyayenka a gidan, yaushe zaka zama cikakken mai
kamala ne?"
Ya sunkuyar da kai ya ce "Za'a gyara Baba"
Domin kuwa da dukkan zuciyarsa yake ganin kimar Baban Marina fiye da su Baban
Tsakiya.
A dakin Dada kuwa Baban Kasuwa ya dinga fa'din"Dada ai da kin ce a ba shi Kaltume
kawai, ina ce ta fi Ubaidan a haife?"
A dan tsorace ta ce "Ga ni na yi zan takura da yawa, sannan dole hankalin mutane
zai dawo kanmu".
Ba shakka ya ce "To ya dawo mana! Idan ka daka ta mutane ai ko sallah ba zaka yi
ba, domin kana yi suna kallon ka, ba dan su gyara maka ba, sai dan su gano
na'kasunka su yi zundenka
Bare kuma akan wani al'amarin duniya da bai zame komai a juya maka manufarka
kyakkawa zuwa mummuna ba."
A sanyaye Dada ta ce "Hakane".
Suka tashi ba tare da sun so a bawa Nura Ubaida ba.
Washagari sassafe Baban Marina ya zaunar da matansa ya shaida musu juyin da aka
sake yi, da kuma hukuncin da ya yanke akan yin madadi da Ubaida.
Daga Inna har Gwaggo abin bai musu da'di ba. Mussaman Gwaggo da take gani ita ce
zata fi shiga cikin tashin hankali, domin matu'kar Yabi bata samu dacen aure ba, to
komai ma zai kwace mata ne. Ga Ummi ita ma fama take a nata gidan.
Shike nan a hakan zasu kare ita da y'ay'anta?.
Shirun da suka yi gaba'daya shi ya sake sanyaya masa guiwa.
Ya ce "Kun yi mini zuru?"
Mama cikin walwala ta ce "To me zasu ce Alhaji? Y'ay'anka ne fa ka yi iko da su,
sannan ba shawara ka nema ba, tunda an riga da an zartar to wace ce zata yi inkarin
hukuncin Dada matu'kar tana son ka rabauta?".
Maganar Mama ita ta sanya wa Gwaggo k'warin guiwa domin ta sani so take ta ganta
cikin rashin sukuni da tashin hankali.
Nan da nan ta ha'diye damuwarta, ta murmusa tare da ce wa"Allah ya sanya alheri da
albarka, ina fatan Allah ya sa ace gara da aka yi".
Wata irin nutsuwa ta zo wa Baba domin dama uwar Yabi yake ji. Ya sani borin da Yabi
zata yi ba zai yi tasiri ba tunda an yi sa'a ita din mai jin maganarsu ce mai kuma
kishin kada su kunyata ne.
Ya dinga yaba mata tare da sanya mata albarka.
Ya juya ga amaryarsa Inna uwar Ubaida.
Ya ce "Ke kuma fa?"
Murya babu amo ta ce ", Allah ya sanya albarka".
Ya sake numfasa wa tare da cewa"Yadda kuka kwantar mini da hankali a lokacin da aka
jefa ni cikin matsanancin hali, ina rokon Ubangiji ya kewaye y'ay'anku da farin
ciki da kwanciyar hankali a wannan aure.
Allah ya sanya alheri mai yawa ya biyo baya. Allah ina rokon a azurtasu ta inda
muka zata da
ta inda bamu zata ba".
Suka amsa da ameen cikin juriya. Amma Mama bata ce uffan ba.
Ha'din kai da ya samu daga wajen matansa ya taimaka kwarai wajen kwantar da
hankalinsa.
Har dare muna namu yi, ban samu labarin komai ba.

Please Login or Register in order to submit comment