You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya goce mata, jikina ya sake yin sanyi, domin ita din
wata irin mace ce mai k'arfin zuciya k'warai da gaske, abin da zai saka ta yi kuka
to kuwa ya girgiza ta ba ka'dan ba, duk tsananin da take fuskanta a rayuwar gidanmu
ban ta'ba ganin ta yi kuka ba.
Na yi kasa da kaina cikin rauni mai yawa na ce "Ameen Baba! Allah ya kara maka
lafiya da nisan kwana mai albarka. Na gode sosai".
Duk muka yi shiru kowa na cikin alhini. A hakan Nazira ta fito rai a bace da gani
Mama sababin yadda ta like mini ta yi mata.
Kusa da ni ta zauna, cikin sanyin murya ta ce "Sannu Baba".
Murya ba amo ya ce "Sannu kadai Nazira, Allah ya kara miki ha'kuri kin ji. Ki
cigaba da jajirce wa a kan gaskiya ko da hakan ya ci karo da ra'ayin kowa, ku so
junanku, ku binne a tsakaninku, kin fi Yabi ha'kuri, a duk sadda kika ga zata yi
aikin nadama yi amfani da fikon da kika yi mata ki dakatar da ita, komin runtsi
kada ki bari ta dauki hukunci cikin fishi. Ke kuma Yabi kul kika ki jin shawararta,
idan ta ce yi ha'kuri, to na roki ki bar abin nan komin girmansa.
Ina jaddada muku ne dan ku ri'ke su da kyau, ko babu ni idan kuka ri'ke maganganuna
ba zaku ta'be ba. Allah ya yi muku albarka ya ha'da ku da maza na gari, ya raba ku
da sharrin shaidan a cikin zumunta".
Muka amsa da Ameen amen cikin sanyin jiki.
Nazira ta mika hannu ta karb'i Maficin hannun Gwaggo ta cigaba da yi masa fifita,
duk da gumin ya yi sau'ki.
Har lokacin kuma bai saki hannuna ba.
Ya jima kafin ya saki hannuna yana sake cewa "Na hore ki da ha'kuri Yabi! Ku zauna
da yan'uwana lafiya, ku mutunta su, ku gaishe su da girmama wa".
Na gyada kai yayin da Nazira ta ce "Duk yadda kake so hakan zamu yi, amma ka
taimake mu ka daina sanya damuwa a ranka Baba! Fatanamu mu ganka a tsaye akan
kafafuwanka, idan muna ganinka cikin walwala ba abin da zai dame mu sosai."
Haka muka kwanta ni da Nazira tana ta jan kunnena na kiyayi Dada, tunda zata iya
yin ha'din kitifo har ya zama sanadin da za'a samu damar cin zarafin Babanmu akan
idonmu.
Tun daga wannan ranar na kame bakina a gaban Dada, duk karatun da zata yi bana
tankawa, haka nan ban cika zama na yi doguwar magana da ita ba.
Zanje gaishe ta babu fashi, kuma sai na tabbatar mun ha'da ido sannan zan kama
sunanta na gaishe ta.
Na daina jan magana a tsakaninmu ne kawai.
Sannan na soke zuwa hirar dare, amma matu'kar zata d'ora karatu sai ta sa an kira
ni.
Janye war da na yi da ita kuma sai ya dame ta, amma ta kasa bu'de baki ta yi
magana.
Tunda Nazira ma ba wani sake wa take yi ba, balle ta yi mata korafi.
***
Karshen wata Yaya J ya dawo. Mun taso daga Islamiya muka ganshi zaune akan
dandamalin kofar gidanmu.
Sanye yake cikin kananun Kaya da suka yi matu'kar kar'barsa, sai kamshin turaren
Dagmar yake tashi sannu a hankali.
Dukkan y'anmatan suka hau rige-rigen gaishe shi, yayin da ni na sunkuyar da kai
kasa alamun kunya.
Na zo wucewa ta gefensa na saci kallonsa ai kuwa karaf muka hada ido, wani irin abu
ya tsikare ni, kwalliya da tsabtar Yaya J ko mace ce ta kai a sata a masu tsabta,
sannan kankantarsa tana sawa na ji mun dace da juna.
Domin da ka'dan ya zarta ni cika ido da tsayi.
Babban abin burgewa mai nutsuwa ne, sannan mai ha'kuri ne, bashi da hayaniya ko
ka'dan.
Da sauri na janye idon nawa, murmushi yana subuce mini wanda ban shirya yinsa ba,
na tsananin shauki ne.
Na wuce ba tare da na yi gaisuwar ba.
Cikin raha ya ce "Nasiba ki koya wa Asiyan Toro gaisuwa tunda ta zama bak'auya".
Da dariya ta ce "Yaya Jabir kaine da fa'din Asiyan Toro yau? Babu ruwana a
shirginka da Yabi".
Ya k'yal-k'yale da dariya ya ce "Tsoron ta kike ji ne Nasiba? Kin fita tirinya fa,
to kuma ya za'a yi ne tunda ku biyu zan ha'da na aure rana guda?".
Ta yi maza ta ce "Lallai kuwa ka shiryawa darun Yabi domin har ka tafi ba zata
saurare ka ba, ni kuma ba zan taya ka rarrashi ba".
Ta wuce ni da sauri ta shige shashin Dada.
Ni kuma na wuce shashinmu a dalilin yau Nazira ba ta samu damar zuwa ba, saboda
tana fama da ciwon mara.
Zuciyata har wani tukiki take yi na tsananin bacin ran kalaman Yaya J.
Wai zai ha'da ni da Nasiba ya aura.
Na yi tsuka na ce "Sai dai ya aureta ita ka'dai. Dama na san dunbula dunbulan
kirjinta na iya tafiya da shi, ba'kin ciki ya sake turnike ni a dalilin ni ba mai
cikar k'irji ba ce. Har yanzu bana saka breziya sai dai half best, domin a manne
suke a kirjina yan kananu da kadan suka fi tsakuwa.
Amma Nazira da Nasiba kam kirjinsu a cike yake sosai.
Wataran har rayawa nake yi ko dai na fara shan ruwan baru ne ko zan yi sa'a su fito
su cika mini kirji ni ma.
Amma sai na kasa, mussaman da sai na ro'ko ruwan kuma sai nake ganin kamar za'a
gane dalilin shan da zan yi.
Da daddare ya dinga aiken na zo amma na yi mirsisi na ki fita.
Washagari a zauren Dada na tarar da shi.
Na sani sammakon tashi ya yi dan ya hadu da ni. Domin shi ba ma'abocin tashi
sassafe bane, da zarar ya dawo daga sallar asubahi idan ya kwanta sai tara yake
tashi.
Nazira ta gaishe shi ta shige, yayin da na dauke kai fuska murtuk zan wuce shi.
Ya yi maza ya sha gabana yana fa'din "Haba Yabin J baki san wasa ba ne?
Na yi bakam tamkar dai ban fahimci da ni yake magana ba.
Na yi kasa da kaina.
Ya sassauta murya ya ce "Yanzu Ashe zaki iya mini irin wannan fishin Yabi?"
Na dago na kalla shi na ce "Oh wai ka yi zaton ba zan iya ba?
To kuwa ka dauka zan yi maka fiye da hakan domin zan iya shafe babinka gaba'daya."
Ya jima yana kallona cikin ki'dima.
Ya yi k'arfin halin cewa "Me ya yi zafi haka, daga wasa?"
Na sake d'aure fuska na ce "Bansan wasa ba, ban iya shi ba, ban kuma ta'ba daukan
al'amarinka a matsayin wasa ba, bare har na yi maka tsokanar da zaka ji ka
tozarta".
"Hakane, na kuma gasgata ki, yanzu ki yi ha'kuri ba zan sake miki irin hakan ba kin
ji".
Na jijjiga kaina tare da yin wata irin shakiyar dariya na ce "Ha'kurin ma ban iya
shi ba. Ba kuma zan koyo shi a dalilin cin fuskar da aka yi mini ba. Na riga na
barwa Nasiba kai, dan haka ka manta da wata Yabin Marina".
Ya yi tsam cikin kaduwa wata'kila yana mamakin yadda kishi yake kutsowa tunda ga
kasan zuciyata ne, kallon yarinya k'arama yake yi mini, sai dai bai san yar shekaru
goma ma zata yi kishin abin da take so ba, bare ni da nake da shekaru sha sha
biyar, na ke harun sha shida.
Ya lankwashe murya cikin rarrashi ya ce "Ai na yi zaton ina da wata alfarma ta
daban a wajen ki, ban ta'ba zaton zan yi miki laifin da zaki shafe ni a zuciyar ki
ba.
Yau dai daya tak da na sab'a miki, ki daure ki mini uzziri, ni kuma na yi
al'kawarin ba zaki sake kama ni da laifi irin wannan ba".
Na dauke kai na ce "To idan na yi ha'kuri na ce maka komai ya wuce, ya zan yi da
tafasar da zuciyata take yi idan na ga Nasiba?
Ya zan yi na goge amincin da zuciyata ta yi akan ita kake so bani ba, tunda ita din
ta fini zama y'anmata?"
Tsananin mamakin da na ba shi ya sanya ya kasa magana na tsawon lokaci.
Sai da ya jima kafin ya numfasa ya ce "Ni fa ba wacce take burgeni nan duniya idan
ba Yabin Marina ba.
Kinsan dai ina tsokanar Nasiba tun fil'azal tunda abokiyar wasanmu ce, yar mace da
dan namiji muke.
A kaikaice na ce "Oh oh, ashe dama ana wasa har irin haka?
To kuma wai ya matsayin wannan *Bak'ar Ta'adar* a shari'a tunda ba'a wasa da
maganar aure?"
Ya dan tunzura ka'dan ya ce "Ke Yabi".
Nima na ce "Ke Yabi ko kuma ke gaskiyar magana?"
Ya girgiza kai ya ce "Shi kenan na gode, na gode sosai da yadda kika ajiye ni".
Ya fice ya bar ni, kafin na shiga wajen Dada Bulkachuwa ya fito daga dakinsa.
Ya yi fitoh irin na tantiran yan-iska ya kalle ni ya ce "Asiya Toro rikakkiyar
budurwa".
Ya kwashe da dariyar iyashege ko me ya tuna kuma sai ya gintse dariyar tasa.
A fili ya ce "Ban da ma shan koko d'aukar rai ne, ta yaya kamar Jabir da yake ganin
Bigger babes zai tsaya wajen kwailaye irin Asiya Toro? Ya wuce yana sake fa'din "
Soyayya da kananun yara menene a cikinsa ban da raini da ba'kinciki, yar yarinyar
da bata gama iya wanka ba ma sai ta caccaba maka magana son ranta, abin ba'kinciki
kuma dole ka rarrasheta ko ka hadu da gallazawar zuciya."

*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin
register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*

Na yi kwafa a dalilin yadda furucinsa suka sake sawa na washe shi.
A dole na shiga ciki na gaida Dada. Ina kallon yadda Nasiba take rawar jikin zuba
masa ruwa a buta, dan ya yi brush.
A raina na ce wannan fa shine shan kokon.
Sai da ta gama barebaren yi masa hidima sannan muka fito muka wuce makaranta.
Gaba'daya wannan zuwan na Yaya J ban yarda mun shirya ba, haka ya koma Jos.
Ni kuma ina k'arfafawa kaina gwara mini Abdulrashid kamar yadda Gwaggo take so,
domin ni da kaina ban san waya fi sona a tsakaninsu ba.
Sai dai me?
Juma'a da maghariba muna tsakar gidanmu sai jin ihun yara muka yi suna "Oyoyo Yaya
Jabir, oyoyo".
Nazira ta ce "wannan dawowar taki ce Yabi. Na ro'ke ki huce hakanan ai ya garu".
Na tabe baki na ce "Rabu da shi, nifa dama ina ta neman hanyar da zan yakice shi a
raina, ki ga fa irin yadda Baban Tsakiya ya yi wa Baban Marina, akan idonmu".
Ta fesar da iskar takaici ta ce "Amma Baban ya ce ba ruwanmu da kasafinsa da
yan'uwansa, a gabanki ya tabbatar bamu fi yan'uwansa a gunsa ba.
Aure ai kaddara da rabo ne Yabi.
Ban da haka da wani namijin bai isa auren wacce yake aure ba, sai kaddara ta ba
shi, haka nan wata macen bata isa mijinta ya kalle ta da nufin soyayya ba, amma
saboda karfin kaddara da rabo sai kiga ta zame masa mata kuma uwar ya'yansa.
Matu'kar Yaya Jabir mijinki ne, sai kaddara ta sanya aurenku ya yiwu komin k'in da
iyayensa zasu yiwa al'amarin. Mu da muka yi sa'a ma dukkan iyayenmu suna da ransu,
kullum kuma suna roka mana mu dace da maza na gari, na yi imanin Ubangiji ba zai
juyar da addu'arsu ba, hakan kuma ba zai hana mu ga kalubale a cikin ko wanne zabi
ba, domin sunnar rayuwa ce komai na da irin nasa cikas din, sai dai albarkacin
addu'ar iyaye sai ki ga komai ya saukaka.
Jikina ya yi sanyi, na kasa bu'de baki na ce komai.
Ta ru'ko hannuna sosai ta ce "Ki yi ha'kuri kin ji Uktina".
Na nisa na ce "Na yi ha'kuri saboda ke, amma ki fa'da masa bana son irin wannan
wasan, bana so".
Cikin jin da'din na yarda da maganarta ta ce "Madallah da K'anwata kuma kawata
YABIN J".
Na murmusa a raina kuma sai addu'a nake yi mata ita ma Ubangiji ya kawo mata
saurayin da zan taya ta sonsa, domin hatta Abdulrashid da ba wani sonsa take yi ba,
bata ta'ba kushe shi ba, illah iyaka tafi son Yaya J.
Idan ina yi mata d'an bikin ita bakin ganga ce, domin a gabansa bata ta'ba nuna
masa akwai wanda take supporting sama da shi.
Sai ta murmusa ta ce "Tunda har zuciyar Yabina tana dan sonsa ai kuwa yafi karfin
na wula'kanta shi, baya ga haka son ki yake yi, dan haka nake girmama shi. Amma ai
bazan so shi na bar Yaya J ba domin yafi shi cancantar ya same ki".
Bata ta'ba nuna k'yashi ko takaicin ina da samari ita bata da su ba, duk da ta fini
zama cikakkiyar budurwa.
Ni da kaina na sani Nazira tana cikin Yan ka'dan da Ubangiji ya wanke musu zuciya
akan k'yashi.
Allah kenan! Sarkin hikima sai ya bawa bak'ar uwa karimi ko karimar yarinyar da
za'a yi ta yi mata alfarma saboda kunyarsu. Hakan ce ta kasance domin sau tari sai
na yi yun'kurin yiwa Mama iyashege irin ta dan yau dan ta fahimci dan Babanmu da
Gwaggo suna shayinta, tunda laya ce ita, ni kuma mai zamani ce dole kuwa ta kiyaye
ni.
Nauyin Nazira ka'dai yake sawa nake hadiyar dukkan matsatsin da take sanyamu. Domin
na riga na ajiye alakar matar Babana ce tunda bata ta'ba yi mini karar ni din
y'arta ce ko ta mijinta ba.
Ana idar da sallar isha ya aiko na je.
Yana jingine jikin katanga hannuwansa biyu a kirjinsa, sanye cikin shadda shud'iya
kalar sararin samaniya.
Sai kamshi yake yi.
Na rakube gefe guda ba tare da na ce kanzil ba.
Ya matso kusa da inda nake ya ce "Assalamu alaikum Yabi".
Murya babu amo na ce "Wa'alaika Salam".
Ya ce "ki yi ha'kuri, na yi kuskure, tunda na gane da gaske ba kya son irin wannan
wasan bazan sake yi miki ba shi kenan?".
Na yi kasa da kaina, ba tare da na ce komai ba.
Ya numfasa ya ce "Kin yi shiru".
Cikin yauki domin da k'yar na ce "Ya wuce".
Ya murmusa ya ce "Yabina sarkin ginshira, da rikici".
Na kawar da fuskata gefe ban ce uffan ba.
Ya dan damu ya fara fa'din "Kin ce "Ya wuce amma kin k'i sakar mini fuska, saboda
ke fa na dawo".
Fuska ba walwala na ce "Ya wuce mana, mantawa ai sai a hankali, yo ban da ma dai
ina ganin mutuncin ka ai da an rabu ke nan, ina ruwana da duk wanda zai nuna mini
yana son wata dan ta fini tirinya".
Ya kame baki alamun mamakina.
Tsawon shudewar mintina sannan ya iya ce wa "Yabin Marina ho".
Na sake tsuke fuska.
Murya ba amo ya ce "Ba tone tone zamu yi ba, ai kin gama magana tunda na yi sa'a
kina ganin mutuncina. Na gode miki da wannan karamcin, ina son ki fiye da komai".
Ya lankwashe murya ya ce "Mutunci da soyayya idan suka hadu fa'din irin al'amuran
da zasu haifar na nutsuwa ma bata lokaci ne Yabin J".



*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
✍️
*BAK'AR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS M.I.NASHE)*.

*Marubuciyar*
*Halin Yau*
*Sabo da kaza*.

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA
BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*MASU SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S ONLY*.

*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko kuma kina sha'awar yin
register da su. Ki tuntubi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn mai kore dukkan kwadayi*.
*07036662633*

https://arewabooks.com/chapter?id=64ff47e14ba2e11c69ef3f2f

9&10.
Na sunkuyar da kaina k'asa alamun kunya, gane hakan da ya yi, sai ya mayar da
hankalinsa wajen kwarzanta ni, tare da maganganun masu taushi da nuna kurewar
matsayin mutum. A hakan har ya samu na dawo masa Yabin J bata Marina marar ragayya
idan an tabo ta ba.
Domin sai da kunyarsa da nake ji ta dawo, walwalar da fuskata take yi idan ina
gabansa ta dawo.
Hakanan shaukin da zuciyata take yi ya bayyana.
Sai goma saura ya tafi bayan ya bani ledar atile da kuma turare, wannan karon har
da takalmi mai kyau.
Ina shiga gidan na ci burki a dalilin maganganun da suka ja hankalina.
Muryar Mama nake ji daga dakinta tana cewa "Da gangan kake zuba mata ido take yin
yadda ta ga dama.
Jiyan nan yarinyar nan ta muzanta gyatumarka, amma tana shigowa ka bita da addu'ar
da ban ta'ba jin ka yiwa wata cikin manyan ya'yanka ba.
Ba wacce ta samu lasisin tara samari a gidan nan sai Yabi, nan Indo ta yi farinjii
fiye da nata, sai ka fititke akan sai dai ta zabi guda daya, amma wannan da yake
y'ar tijara ce ka barta ta zamo wa uwarta haja, dan kuwa nasan baka samun abin da
take roro musu. Saboda ba'kin cikin kada wasu su ci.
Yau Jabir ya kawo musu, jibi Audurashid, gata malamin makarantarsu".
A hankali na ji muryar Baba yana ce wa "D'a ai mallakin uwarsa ne Habiba, duk abin
da uwa ta ci ko ta samu a sanadin y'ay'anta bai zama abin a yi magana a kansa ba
domin ta cancanci dukkan sadaukarwa daga wajensu. Ban da Dada da take da ra'ayin
auren wuri wai duka nawa ma suke ne?
Inda za'a bar ni da ra'ayina kamar yadda ake barina da hidimarsu da ba wacce zan
aurar sai ta kammala sakandire bare Yabi mai karamin jiki ce".
Ta harzuka ta ce "Waton ba zaka dai dakatar da su, ka bar guda daya ba ko?
Wai yaushe ka zama mai son zuciya ne haka?
Jikina ya yi sanyi da irin amsar da ya bata.
Ya ce "Kinsan talauci ba abin da baya sawa, bana haufin shine ya mayar da ni mai
son zuciyar, kamar yadda kika mayar da ni banza ko wacce magana zaki fada mini babu
fargaba.
Kin ta'ba jin na yi magana akan yadda yaranki ke ka'dai suke nufa da tallafinsu, ai
saboda nasan uwa mafi uba ce ko da kuwa uban sarki ne".
Ban sake jin harshenta ba, na wuce a raina ina ta murnar Babanmu ya fara gwada
k'arfin halin taka mata burki, duk da a yanzu ma babu garantin ba zai lallabata ba.
Domin ta riga ta jarraba shi ainun.
Washagari asabar da wuri na tashi na ha'da kayan wankin dakinmu gaba'daya.
Na aiki Anas ya siyo mini sabulu da omo tun daren jiya dama.
Na fara wanki, yayin da shi kuma yake janyo mini ruwa a rijiyar bayan shashinmu.
Kafin karfe takwas din safe na kammala na shanya su reras.
Tuni kuma Inna ta kammala abin karin kumallo.
Na karbo mana namu dumamen tuwon da Nazira, ga kuma kokon a jug da kullum Gwaggo
sai ta bawa duk wanda yake son sha a gidan.
Kusan kullum sai na tambayi ko ribar nawa take samu?
Yadda bana gajiya da tambayar itama bata gajiyawa wajen cemin "Wanda ake sha ne
ribata".
A duk sadda ta fa'di hakan ban cika fahimtar rufin asiri ba ne sai kawai na kalli
ita din mace ce mai yin hidima a inda ba'a ganin darajarta.
Kafin Nazira ta gama wanke baki na k'osa domin indai na yi wanki to bani da
jarumtar ri'ke yunwa sai na ji tamkar an mini yasa a cikina.
Ta tarar tuni na fara cin tuwon.
Ta zauna tana fa'din "Yabi sark'a, yanzu da ni ce na fara ci ban jira ki ba, sai
kowa ya ji kwakwazon ki"
Na rausayar da kai tare da fa'din Ayyah Addah Nazi kinsan bana shiri da yunwa ko
kadan.
Muna karyawa ina bata labarin yadda ta kaya a tsakaninmu da Yaya J.
Ta murmusa ta ce "Yabi duniya! Yanzu Yaya Jabir din ma ba zaki dinga raga masa ba?
Na dan daure fuska na ce "Ai matu'kar zai tsokano ni tabbas zan ajiye komai na
yamutsa shi inta kama a rabu ma shi kenan.
Ba zan dauki wula'kanci ba ko ka'dan.
Ta girgiza kai tare da cewa"Allah ka shirya mini Yabina".
Dai dai lokacin Baba ya fito da nufin fita.
Muka gaishe shi ya amsa yana cewa Nazira da Asiya albarka ta kewaye mini ku".
Cikin farin-ciki mai yawa muke fa'din ameen Babanmu".
Amma sai na sake cewa "Babanmu Asiya fah?"
Ya murmusa ya ce " Ho Yabi! Da ikon Allah sai kun sauke farali daga ke har y'ar-
uwarki. Sai kin zama Hajiyar ta sosai".
Cikin karadi na ce "Ai kuwa dai Babanmu "Dawafi na mussaman zamu yi maka!"
Ya fice yana dariya.
Babanmu wani irin uba ne da yake wasa da raha a tsakaninsa da y'a'yansa, babbar
matsalarsa kawai Mama ce, domin yanzun nan sai ta saka ya ci mutuncinka ko na
uwarka akan idonka dan ma an yi sa'a abin ya dan fara sau'ki, na sani kuma karfin
addu'ar da muke yi ne mu da Gwaggo".
Kwanaki suna ta shude wa har muka yi jarabawar zangon karatu na uku.
Muna tafe kowa da sakamakonsa a hannunsa, Nasiba da su Firdausi sai murna suke yi a
dalilin sakamakonsu ya yi kyau.
Nazira ma babu laifi domin ta sha biyu ta zo.
Amma ni kam sakamakona ba zai nunu ba domin kuwa ta arba'in da takwas na zo a cikin
mu hamsin da bakwai.
Kowa ya nuna sakamakonsa a tsakaninmu. Amma ni na boye nawa kamar yadda na saba.
Muna tafe Maijidda sai fa'di take "Akan me za ki dinga ganin results dinmu amma ke
ba zaki yarda a ga na ki ba?"
Na gallah mata harara na ce "Saboda mahaifina bai fara gani ba, ba kuwa wanda yafi
cancantar ya fara gani sai shi".
Ta tunzura ta ce "Kins an Allah yau sai na ga ni, ai na sani ta karshen aji kike
yi.
Ban da class master din ajin naku saurayinki ne ai demotion ne ya kamace ki Asiya".
Na fusata kwarai da gaske na ce "Tabdi jam! Yabi kika je fa wa wannan maganar?"
Ba shakka ta ce "An fa'da miki Asiya. Kin dauka ina jin tsoron ki ne? Idan ba jakar
aji kika dauka ba to miko mini sakamakon ki kamar yadda na baki nawa kika ga ni".
Na girgiza kai da tare da yin k'wafa mai tsananin gaske.
Nazira kuwa sai fa'di take "ba ruwanki da al'amarin Yabi fa Maijidda".
Ta ce "Na shiga komai zata yi, ta yi ina daidai da ita".
Ban ce komai ba sai da muka isa zauren Gidanmu ba zato na shake Maijidda da dukkan
k'arfina, ina kai mata duka ko ta ina.
Kafin ta yi yun'kurin ramawa na jibge ta sosai, sannan kuma muka ci gaba da gwabza
wa.
Aka rasa mai rabamu domin duk wacce ta ta'ba ni kanta fa'dan zai koma sun san haka
dabi'ata take.
Nazira sau fa'di take Yabi sake ta, amma bata ri'ke ni ba, domin ta san ce wa zan
yi bata taya ni fa'da, ta taimake ni ba tunda bata kishina, akan me zata ri'ke ni?
Na turmushe ta ke nan na debo k'asa ina shirin cika mata bakin da ya yi mini
izgilanci sai ga Bulkachuwa ya shigo.
Ya hau fa'din ke Asiya Toro wanne irin abu kike yi haka ne?"
Ganin na fara kokarin danna mata a baki ya sanya shi iso wa garemu, bai jira komai
ba ya saka hannunwan sa ya cira ni cak kamar y'ar tsana ya yi wurgi da ni.
Na yi sa'a na dire akan sayyadata.
Da yake a hassale nake sai na durfafe shi ina cewa "To kai ma din ai ba tsoronka
nake ji ba, ka zo ka zaune mana a gida ka uzzira mana haba.?"
Na kalli yadda ya harzuka amma ko gezau ban yi ba, duk da ban fi iya cikinsa ba.
Ya kalli Nazira ya ce "Me ya ha'da su?"
Ta tsara masa yadda aka yi ba ragi babu kari.
Ya juya ga Maijidda da take hawaye ga jini a hancinta tabbacin habo ne ya goce.
Ya ce "Dube ki gansamemiya da ke amma wannan y'ar tsakon ta lallasaki haka, wanne
irin mutuwar zuciya ce ta same ki?"
Na galla masa harara tare da murguda baki na ce "To ni komin girman gardi ma ba zai
hana na zubar masa da jini ba, bare kuma mace yar-uwata".
Ya nuna kansa ya ce "Asiya Toro ni kike tunanin zaki buga?".
Na ce "Ba dan ha'da jiki da kai sai ballagazaye ba, ba abin da zai hana na zage mu
gwabza y'ar k'ashi Wallahi".
Ya nuna ni da yatsa ya ce "Asiya Billahillazi zan sumar da ke, yar iska marar
mutunci kawai.".
Yana rufe baki na ce "Ga ka nan babban dan-iska mai shiga fa'dan mata, yabi bayan
wacce take da abin da zai lallaba ya cuce ta."
Ya yo kaina yana fa'din ashe "Izgilancinki mai girma ne haka?"
Ga mamakinsa sai kawai na yi shirin kai masa naushi tamkar bacaniya.
Wannan dunukule hannu da saitin da na yi, ya yi matu'kar bashi dariya da tu'ajjibin
k'arfi halina.
Ya tsaya ya ce dambe zaki yi da ni?
Na ce "Allah suturu bu'kui

Please Login or Register in order to submit comment