You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Saboda yana jin tsoron sa. Rikici ya kaure a tsakaninsu Dada ta
kasa shawo kan matsalar domin Baban kasuwa ya dauka da zafi, kuma dama tafi gudun
zuciyarsa. Baban marinar da ba'a saka shi ba, shine ya tuntunbesu bayan Dada ta
fad'a masa a dunkule ba a bude ba.
Abin mamaki kowa ya ce masa babu komai, duk da Dada ta fad'a masa. Shi kuwa sai ya
hak'ura ya zuba musu ido.
Bai gane kan al'amarin ba sai da ta yi sati biyu. Da kanta ta je ta durkusa tana
kuka ta fad'a masa yadda abubuwan suka kasance, sannan ta roki Baban Marina akan ya
bawa Jabir hak'uri. Gabadaya ta shiga damuwa da tunani domin dukkan y'aya'nta uku
suna can tare da shi. Mai shan nono kawai ya bar mata. Bata tab'a zaton zai yi mata
hakan ba.
Duk kokarin Baban Marina ya amsa samun Jabir. Washagari ya tisa ta a gaba ya nufi
Kaduna da ita. A ransa ya tabbatar dan tana son komawa dakinta ne. Ba dan hakan ba
da bai isa ya yi irin wannan ikon ba.
Jabir na ganin sa ya ware fuska ya marce shi da girmamawa. Baban ya dinga yi masa
fada tare da tabbatar masa ya yi tsaurin ido.
Cikin jin nauyi ya ce "Ka yi hak'uri Baba! Ta kai ni bango ne da yawa. Ni fa dama
hak'uri nake yi domin ba hakan nake so ba, amma tunda kaddara da rabo ya ba ni ita,
ban zalunce ta ba. Ga ta nan ta fada maka inda na kuskure domin nasan iyakar adalci
ina yi mata. Aure kuwa bata isa hana ni yi ba, bata kuma da hurumin zaba mini wacce
zan aura domin ni din ba makaho ba ba ne, bare ta ce zata zaba mini wacce zan
aura".
Baba dai ya yi masa fada tare ce wa "Ka dauke ta ka kai mana ita, ka yi tafiyar ka
ai rainamu ka yi Jabiru. Duk cikinmu ka rasa wanda zai maka maganin matsalar sai ta
hanyar mayar mana da ita? Ko a lahira wani na cin arzkin wani. Kada ka sake irin
haka. Kishi kuma ai dole ta yi, ka rarrashe ta, ka kwantar mata da hankali ba wai
ka ankara ta ba."
Ya juya ga Maijidda take kuka sosai ya ce "Ke kuma ba ruwan ki da auren sa, matukar
yana yi miki adalci, kawai ki yi hakuri ki yi addu'a. Ai kishiya yar uwa ce, ina
ruwan ki da ita. Ban da ma sakarci me ya ka ki yin fitina akan wacce ma bata zo
hannunsa ba? Kina ahalin gidan Marina ki ce ba kya son kishiya? To ko da kika ga
gyatumar ki ita kad'ai ai mu kina ganin kofofinmu mata ne da yawa ba kuma wacce ta
kori wata, ko ta hana ta samun arzikin ta."
A ranar ya juyo ya dawo.
Ba jimawa kuwa Jabir ya yi aurensa. Hakan ba k'aramin tasgado ya janyo a taskanin
Baban kasuwa da na Tsakiya ba. Da k'yar aka samu suka fara gaisawa. Kunyar mutane
da yadda aka san kansu a hade yake ya sanya suke gaisawa. Da kuma yadda Dada ta yi
kuka sosai akan gabar da suke yi da juna.
A zahiri sun shirya amma kasan zuciyoyi babu dad'i. Ba yadda zasu yi ne kowa yana
ganin shine akan dai dai.
Baban Marina dai bai ce kala ba. Domin yanzu da abubuwa suka fara warware masa a
dalilin mafi yawa y'aya'nsa muna cikin rufin asiri. Muna had'a abin da za'a ci a
k'ofarmu. Tijjani kuwa ya dauke masa cefanen kayan miya da kudin k'ananun bukatu.
Hakan ya sake janyo masa bakin jinin da babu yadda za'a yi sai zunde a bayan ido.

***
A hakan na cinye shekara d'aya da fara karatun. Na fara nisa a cikin ta biyu. Tun
bai shiga jikina ba, har na sanya shi a raina na mayar da hankali, hakan ya faranta
ran Tijjani tunda ban sami carry over a shekarar farko ba.
A hankali sai nake ganin Tijjani na d'an sauyawa. Sauyin bai shafi mu'amalata da
shi ba. Amma yana yawan zuwa Toro. Kusan kullum sai ya je ko da ba zai je Jos ba.
Ina ta jin rade radin yadda yanzu yake zama ya yi hira da Nasiba da har yanzu bata
yi aure ba. Sai ma kasuwanci da take yi sosai. Kayan gwanjo take siyowa a Jos masu
kyau. Har ce mini aka yi yana karbo mata sakon kayan.
Tun ina daure wa ina dauke kai daga abubuwan da nake ji har na fara sike wa.
A dalilin kullum dare sai ya fita k'ofar gida ya shafe lokaci mai yawa yana waya.
Haka nan kaffa kaffa yake da wayarsa abin da baya yi a da. Da na yi masa magana sai
ya balbale ni da fad'an na saka masa ido ne. Ban da hakan me yake yi mini? Dan ya
yi wayar da bata shafe ni ba a waje shine laifi?
Na kasa bude baki na ce komai domin ba ni da hujja.
A hankali muka fara samun tazara a tsakaninmu. Na sani bai canja daga kawo mini
abubuwan abincin ko na bukata ba. Bai canja a hidimar makaranta ta ko hidimar
y'aya'nsa ba. Sannan bai canja mini a mu'amalarmu ta auratayya ba. Har yau din nan
a cikin mararina ya ke. Duk da ni din ma kullum a cikin gyara kaina nake da
ingantattun kayan Surayya da basu da illah ga lafiya. Sannan ina amfani da kayan
g.h.t na FASEELAT.
Amma yawan wayar da yake yi da sintirin zuwa Toro, da sabunta mu'amalarsa da
Nasiba da nake ta jin rade radinta, tana matukar ci mini tuwo a k'warya. Na rasa wa
zan fad'awa ya fahimce ni. Domin da na fadawa Gwaggo ce wa ta yi "Ina ruwan ki da
jita jita? Sannan ai bai zai yi aure bai fada ba. Ki rage kishi mussaman kan abin
da baki gani ba, zato ne da shati fadi kawai.
Haka na hak'ura na cigaba da zuba ido tare da hak'uri. Amma sai nake ta d'ad'are wa
da shi. Ko a shimfida bana wani katabus shi zai yi kidansa da rawar sa. Wani
lokacin ya tambayi dalilin sauyin nawa cikin kwanciyar hankali. Bana iya ce masa
komai sai dai na ce "Ban canja ba, babu komai".
Wani lokacin ya ce "Allah ya sauwake. Wani lokacin ya yi tsuka ya juya mini baya
tare da fad'in "Zan yi maganin wulakanta ni da kike haka siddan Asiya."
Gabadaya mun koma muna ganin laifin junanmu a dalilin kowa bai gamsu da kokarin
d'an-uwansa ba.
A haka na kammala aji biyu. Twins sun yi wayo sosai tunda sun shiga shekaru biyar.
Wani irin wayo da fikira a cikinsu tamkar wanda suke siyo dabara a kasuwa. Gabadaya
sun juye ubansu sak. Ga shi suna girma suna sake zama iri d'aya. Ni da kaina ina
gane su ne ta halayyarsu. Domin har yau din nan Hanif mai hakuri ne, magana bata
dame shi ba. Sabanin Hamim d'an hayaniya kuma mafadaci irina. Har yanzu bai bar
kuka ba.
Sau biyu ina yin bari. A yanzu haka ina zuwa ganin likita a dalilin hakan. Na
karshen nan da na yi Bulkachuwa ce mini ya yi "Ina sane nake bararwa tunda na saka
masifa a raina. Ya rasa me yake mini da nake gana masa azaba haka.
Kallon sa na yi kawai. Ba tare da na tanka masa ba. Domin na riga da na saka a
raina ce wa hakurin da aka yi ta jaddada mini na yi a lokacin aurena. Yanzu ne zan
fara shi. Dan haka na rungumi addu'a, y'aya'na da karatuna hadi da sana'ata. Na
tattara shi na zuba masa ido yana yin almuransa yadda yake so.
Muna cikin wannan zaman na fallasa tafi yabon yawa. Kamfani suka sake biyansa kudin
hayar filinsa tunda shekaru uku ta cika. A wannan karon har da kari akan wanccan.
Duk yadda muke jin haushin juna sai da ya zauna ya mini bayanin komai. Ya kwashe mu
ni da yara zuwa Kano. Ya yi mana siyayya. Muka kwana biyu, muka juyo da kaya niki-
niki.
Yara na baya duk barci ya sure su. Ya sassauta murya ya ce "Zan canja motar nan.
Zan siyo wacce ta fita."
A takaice na ce "Allah ya kara budi".
Ya zarce da fad'in "Ana mini cinikin wani gida mai kyau a Toro zan siya".
Nan ma a gajarce na ce "Allah ya sanya alheri."
Daga haka bamu sake magana ba har muka iso Bauchi. A dalilin ya fusata duk yadda ya
kwashe ni ya mini hidima bai sa na saki raina ba. Ni kuma ina masa kallon a yanzu
yana ganin yafi karfina tunda yana samun duk abin da yake so. Kasuwa tana gara masa
ainun. Shi yasa gabadaya yake neman bijire mini. Duk abin da yasan bana so a yanzu
baya jin komai ya yi a gabana. Jiya da daddare ina jin sa a waya yana ce wa "Ga ni
kike ba zan iya bata wayar ba? Wai me kika dauke ni ne? Bari ki ga na sayi gidan da
zan saka.ki a ciki, ki ga yadda zan fito da maganar gabadaya. Namiji dan zai k'ara
aure sai a ce ba zai iya ba? Mata nawa ne a gidansu? Nima kuma mahaifina biyu gare
shi. Da ba'a karin aure da ba'a haife ni ba, tunda tawa gyatumar ce amarya a
gidanmu ".
Dai dai nan na fito a bandakin. Nan da nan ya katse wayar tare da ce wa "Zamu
cigaba da tattauna wa da safe". Ya katse wayar tare da kashe ta gabadaya.
Tun lokacin na sake karaya da shi. Tabbas aure yake nema kuma a Toro tunda har zai
sayi gidan da zai saka ta a can.
Sannan tun yanzu na dame ta tunda har tana masa shaguben tsorona yake ji ba zai
iya aure ba. A raina na shiga yiwa mutanan da suke ganin Bulkachuwa tsorona yake ji
Allah ya isa ta fi goma. Domin a yanzu da kowa yake mini kallon ina cikin rufin
asiri da jin dad'i a gidansa. Ni kad'ai nasan me nake fuskanta. Nafi samun nutsuwa
a lokacin da ba shi da ko sisi. A yanzu ba abin da bani da shi a gidan na cima,
tunda ga kan nama, kifi, madara, dankali, doya, bare kuma kayan miya, da duk nau'in
kayan abincin. Ruwa da lemo basa yanke wa. Komai baja baja yake ajiye mana. Haka
sutura ta wadace ni ainun. Amma kuma bani da nutsuwar da nake da ita a da. Ba ya
shiririce mini kamar lokacin baya. Dan haka sai na fi son waccar rayuwar da kowa
yake mini kallon tausayi.
Babah ta kawo mana ziyara. Ta dinga rarrashi tare da shan cikina akan matsalar da
ta sanya bana girma, da na fara murmure wa zan sake tsomare wa. Ban yarda na ce
komai ba, saboda nasan ba zata yi masa ta dad'i ba, idan ta tafi kuma ya hau
sababin ina had'a shi da uwarsa duk da ba komai yake mini ba, ni ce nake
zaluntarsa.
Da kanta ta fahimci a yanzu ni da shi kowa harkar gabansa yake yi. Gamu nan ne dai,
babu warkajabi irin na da, babu nishadi a tare da mu duk da ba gaba muke yi ba.
Da daddare bayan yara sun yi barci ta zaunar da mu tana bincikar matsalarmu a
kokarin ta na son ta sulhunta mu ta dinke barakar da kullum take sake bunk'asa a
zukatanmu ba tare da mun ankara ba.
Tsawon lokaci ban iya bude baki na ce uffan ba. Ta hakura ta koma kansa. Cikin
kwanciyar hankali ta tambaye shi me yake faruwa. Ai tamkar gudawa haka ya b'arke da
zano laifukana. Ya kaurara murya ya ce "Gata nan gabadaya ta ki sarrafuwa mini. Ko
dariya take yi da y'aya'nta idan na zauna a cikinsu ta gintse dariyar ke nan. Idan
tana zaune a falo na zauna sai ta san abin da zata kirkiro da zai sa ta tashi ta
bar mini wajen. Ba zan mata abu ta nuna ta ji dad'i ba, zata dai ta ce ta gode a
takaice. Gabadaya ta fitini kanta ta kuma fitine ni. Gara ma da Allah yasa kika
fahimci masifar da d'orawa ranta. Gata nan ta fada miki mene ne bana yi a gidan nan
da zata kwarzabe mu irin haka. Yanzu idan na fita har fargabar dawo wa nake yi
tsabar yadda take shagulatin bangaro da ni, da dukkan al'amarina. Ban sani ba ko
miyagun kawaye suke hure mata kunne. Na tabbatar cikin da baya zama idan ta samu ma
akwai dalili, idan an tsananta bincike, tunda ta riga ta taurare mini, ita tasan me
take nufi da zaman".
Na yi k'asa da kaina ina hawaye mai cin rai. Zuciyata tamkar ta fad'o k'asa idan
yana danganta b'arin da nake yi ni ce da alhakin hakan.
Babah ta dawo kaina cikin tausasa harshe ta ce "Haba Yabi me zai sa ki abin da baki
yi a da ba, sai yanzu da kike girma, kuma Ubangiji yake ta yi muku Alam nasharaha.
Me zai sa ki yi haka?"
Na fashe da kuka mai ciwo na kasa ce wa koma a dalilin yadda nake gunji da
shessheka mai nauyi.
Baba ta yi zuru tana kallon yadda nake kukan.
Ta koma kansa ta ce "Kai ne kake musguna mata, kai ne ka janye dukkan rarrashi da
tarairaiya a tsakaninku saboda kana ganin kana ajiye mata komai na bukata."
Ya yi shiru. Ta sake juyo wa gare ni ta ja ni zuwa jikinta tana bubbuga bayana
cikin rarrashi. Tsawon lokaci ina kuka su kuma ba wanda ya iya ce wa komai. Sai da
na yi kuka sosai, domin tsawon lokaci ina ta son na yi ban samu inda zan yi ba. Shi
yasa yanzu na yi shi son raina. Sai da na nutsu sannan ta d'ago ni ta ce ",Fada
mini damuwowinki Yabi". Na ce "Babu komai Babah". Na saci kallonsa na ga ya kidime
sosai domin ya sani idan har na ce babu komai to kuwa abin da yake raina mai nauyi
ne. Irin kukan da na yi kuma ya saka shi zullimi.
Babah ta hau fad'in "Wato ban isa ba ko Yabi? Na zaunar da ku dan na ji
matsalalolinku amma kin ce babu komai alhalin ko makaho idan ya ji irin kukan da
kike yi yasan kina cikin bacin rai."
Idona ya sake cika da hawaye na ce "Wallahi Babah ba isa ne baki yi ba, ke ma kin
san yadda na dauke ki. Kawai ban san me zan ce ba ne. Abin da na fahimta kawai
yanzu ya fi k'arfina ne. A yanzu ya samu damar da zai auro daidai da ra'ayinsa,
irin wacce ta dace da shi. Ai dole na ga komai! Dole komai zan yi masa ya zama
laifi, dole ya janye dukkan tausayi da sassauci a tsakaninmu, Tunda bana birge shi.
Yana zaune da ni ne a kan dole, gane hakan da na yi ya sanya na koma gefe dan na ba
shi dama ya yi komai tunda Allah ya ara masa damar."
Na goge hawayen da ya zubo mini da hijabin jikina.
Babah ta yi shiru tana kallonmu tare da nazari sosai.
Ta kasa gane waye yafi gaskiya a tsakaninmu. Amma kalamaina sun yi matukar dukansu
gabadaya, shi kansa kallona yake yi ya kasa ce wa uffan.
Karshe dai Babah ta rinjayar da gaskiya a tare da ni.
A sanyaye ta ce "Ban yi mamaki ba. Domin mafi yawa maza haka suke yi. Da sun samu
wadata kuma sai wulakanci ya biyo kan wacce aka sha gwagwarmaya da ita. Ba ko wanne
namiji yake yin hakan ba, amma dai masu yin sun zarta marasa yin yawa. Sannu Yabi!"
Ta fada cikin wani irin yanayi, mai wuyar fasaltawa.
Kalaman Babah suka sake fadada zullimiin da yake ciki.
Murya babu amo ya ce "Babah kada kalamanta su rude ki, ki bata lasisin cigaba da
gasa ni da ruwan sanyi da take yi. Ubangiji ya bata iya sarrafa harshe. Wallahi ita
take k'warata. Satin da ya wuce muka dawo daga Kano. Na kuma shirya mana tafiyar ne
dan mu samu sauyin muhalli watak'ila hakan zai sa ta huce daga murdewar da ta yi.
Jikina na rawa na dinga siya mata komai na ga ni. Amma Wallahi yadda kika san mugun
abu na yi mata haka ta sake botsare wa. Tunda muka dawo ta sake taurare wa. Wai a
ce yarinyar mace kankanuwa kamar wannan ta iya BAK'AR TA'ADAR gaba da miji haka
siddan?"
Na kalle shi na ce "TA'ADAR da baka yi ta sharri a baya, yanzu so kake ka k'ware a
kanta. Bana gaishe ka? Masharranci kawai!
Babah ta ce ",Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ashe kina iya zagin miji Yabi? A
gabana kika ce masa masharranci? Ta jijjiga kai tare da ce wa "Tun baku je ko ina
da zaman auren ba kun fara zaman da babu mutunci a ciki?"
Ta dinga sababi ta inda ta shiga bata nan take fita ba. Gabadaya ta hadamu ta ki
yarda da gaskiyar kowa.
Ta kalle ni ta ce "Da kam ni kad'ai nasan wulakancin da zan yi masa a kan abubuwan
da yake yi miki. Amma tunda na gane ba ki d'auki tarbiyar gidanmu ta barranta daga
zagin mijin aure ba. To ai bani da ta ce wa. Domin na gane dukkanku ne baku da
mutunci, dukkanku ne kuke son yiwa auren tawili".
Ni da danuwana kuke son ku tozartawa, ku kunyata, ku jefamu cikin bak'in ciki da
zunden jama'a ".
✍️

*Y'ar uwa, ya mukaji da bubukuwa?* *Daga nan fa har january kusan ko wanne sati
akwai biki, in ba na kusa ba akwai na nesa, ban da tunanin gudunmuwa da ma kudin
man da zakaje bikin ga tunanin abunda zaka saka.*
*Balle ace maaikaciya ce ko CEO ce kina business din ki, kinsan all eyes on you🧐,
ke ba sayen atamfa ba komi tsadanta anyo copynta, shima lace haka, cabdi! To
albishirinki yar uwa!*
*UMM NIHLA malaysianfabrics ta dauke miki damuwa, tana da fabrics kala kala masu
sauki da inganci kuma babu inda zaki samesu in ba wurinta ba, kije taro ki haska
kowa sai ya tambaye ki me kika saka ina kika samu💃 maza garzaya gurinta kusa
labule.* https://wa.me/message/F3EWRSHQPQAAH1
Ta fashe da kuka tana fad'in ai bata san haka zamu yi mata ba. Da bata zo gidanmu
ba. So muke mu kunyata ta ita da Baban Marina.
Dukkanmu kowa ya shiga tashin hankalin kukan da take yi. Domin kuka ne wanda yake
bayyana tsananin bakin cikin da me yinsa yake ciki.
Da k'yar na bude baki na ce "Dan Allah ki yi hakuri Babah".
Bata kula ni ba, ba kuma ta fasa kukan ba.
Da k'yar ta yi shiru. Amma duk juyin da muka yi akan ta yi hak'uri ta tashi ta
shiga daki bata ko yi motsi ba bare ta tanka.
A wannan ranar na gane ita ma kafaffiya ce ta gaske. Domin kuwa dukkanmu a falon
muka kwana a zaune, don bata yarda ko kishingida ta yi ba.
Tashin hankalin da muke ciki tamkar idan an tsaga jikinmu ba za a ga jini a ciki
ba.
Ana idar da sallar asuba kuwa ta fice ko sallama bata yi mini ba. Haka nan Tijjani
bai kai ga dawowa ba. Na bita ina fad'in "Dan Allah Babah ki rufa mana asiri ki yi
hakuri, ki dawo ki gafarce mu."
Tafiya kawai take yi. Muka yi kicibus da shi ya dawo daga masallaci. Duk kokarinmu
akan ta dawo bata yarda ba. Duk rokon da Tijjani ya yi akan ya mayar da ita bata
tanka ba, bare ta amince.
Akan dole na dawo gida a dalilin ya ce na taho saboda mun bar yara.
Na zauna ina hawaye domin ban tab'a ganin Babah ta yi fishi irin haka ba tunda na
ke.
A sururuce na shirya yara, na basu abinci . Amma ko makaranta na kasa tafiya. Kan
dole suma suka zauna. Har azahar babu Tijjani babu labarin sa. Na tabbatar bin ta
ya yi dan ya bata hak'uri. Tun fil-azal yana gudun bacin ran ta. Bare kuma yau da
ta yi matsanancin fishi.
Sai la'asar ya dawo gabad'aya ya yi zuru zuru, ya hargitse. Kallon sa kawai na yi
na gane bai ci komai ba. A sanyaye na masa sannu. Ya zauna a falon ya amsa mini shi
ma a raunane. Kaina a kasa na ce "Ya ya Babah?"
Ya ce "Bata huce ba. Ya zuba mini ido ya ce "Asiya taimake ni ki fada mini laifukan
da nake yi miki."
Na yi shiru na k'i ce wa komai. Ya numfasa ya ce "Wallahi sai kin fada mini, na
gaji da wannan jidalin na ki. Komai na yi miki babu gwangwaninta, kin tada
hankalina kin tashi na ki. Mene ne haka. Kowa ya gan ki sai ya ce kina cikin damuwa
ko jinya mai tsanani. Me nake yi miki hakan?"
Na dauke kai daga kallonsa. Ya taso daga inda yake a zaune ya gurfana a gabana. Ya
ce "Tun ban miki duka ba, ki bude baki ki fada mini musgunawar da nake yi miki"
Na ce "Doke ni kawai, ai ka fi ga hakan ranka ya dade Alhaji".
Ya damke ni ya ce "Tunda kika yi mini sanadin da uwata ta yi mini tofin Allah tsine
Bilhillazi komai zai iya faruwa a tsakaninmu ".
Ganin ya rikice da gaske idonsa ya kad'a tamkar wanda ya sha kayan maye.
Yasa na bude baki na ce "Son ka ne bana yi, na gaji, kawai ka sallame ni".
Jikinsa ya saki, damkar da ya yi mini ta yi sanyi a dalilin ya rasa karfinsa.
Ya zuba mini ido tamkar mai son ya fahimci hakikanin abin da yake cikin zuciyata.
Murya babu amo ya ce "mene ne dalilin janye soyayyar da kika yaudare ni da ita, har
na yi zaton babu abin da zan yi ki janye ta Asiya?".
Ban amsa masa ba. Ya kasa hak'uri ya ce"Mene ne bana yi miki? Duk abin da na gani
burina na siyo na kawo miki, ko na siyo wa y'aya'n ki. Wanne nau'in abinci ne bana
ajiye miki duk tsadarsa?
Wanccan watan kina ce mini kayan Oriflame kike son amfani da shi, haka na daure na
ce ki fadawa yar lame din da take siyarwa ta aiko miki, kuma tuni na biya. Da me na
rage ki da kika janye samar mini da nutsuwa?
Tunda muka dawo gidannan bamu jitu sosai ba, bamu samu nutsuwar da ta dace da mu
ba. Na dauka bandakin da na samar miki a cikin daki zai sa ki yi farincikin ki gane
komai kike so sannu a hankali zan yi miki shi "
Ido cikin ido na kalle shi duk da bai sake ni ba, na ce "Duk wadananan abubuwan da
ka lissafa hakkina ne da ya zama wajibi ka yi mini su, ba wai taimakona ka yi ba.
Idan kuma yinsu alfarma ce to ka daina bana so. Daki mai bandaki kuma bana sonsa,
nafi son wanccan gidan da yake fallen falle mai bandaki a tsakar gida, domin nafi
samun gamsuwa da mutuntawa a cikin sa. Ya sake ni yana fad'in "Innalillahi wa inna
ilaihir rajiun. Asiya sai yaushe mata zaku gane hidimar da take kan namiji ba zata
bar shi kullum ya mu'amalance ku yadda kuke so ba? Da din da kike marari ba ni da
abin yi ne, ina rayuwa ne a takure saboda bana iya samar miki abubuwan da suka dace
da ke. Yanzu kuma da na samu hanyar daukan nuyinmu sai ya zama tashin hankalin? Shi
kenan sai ya zama laifin da zaki janye soyayyar da kike yi mini?"
Na ce ",Eh dama ai ba son ka nake yi ba. Kirki da ririta ni da kake yi ne ya janyo
maka soyayyata. Amma tunda ka janye su, nima na fasa son naka sai ya ya kuma? Har
kana kumfar bakin ka kai ni Kano ka mini siyayya to ga kayan can bana so. Tunda har
zaka yi waya a cikin dakin da kasan ina ciki kana fad'in baka tsorona, zaka bayar
da mamaki akan lamarina. To ina ce sai na damu da kai ko kuma idan na zauna da kai?
Sannan zaka tozarta ta ni ta hanyar nunawa duniya ni din ba komai ba ce a wajen
ka. Ni kuwa me zaka yi mini na ga farin ka Tijjani?"
Ya sake ni a matukar sanyaye. Domin ya gane da dukkan zuciyata na shirya wa ko
wacce irin fitina. Ya zauna kawai ya jingina da bango sama da awa bai iya ce wa
komai ba.
Sallah ta fitar da shi. Ya dawo ya zauna a inda ya tashi, gabadaya ya zube tamkar
mai amai da gudawa. A sanyaye ya kalle ni ya ce "Ba ni shayi na sha. Yau ko ruwa
ban kai bakina ba. Ban yi masa musu ba na hado na kawo masa. Yaran namu su kansu
sai suka zama babu walwala a dalilin sun ganmu a birkice.
Yana dawowa daga sallar isha ya rufe gida. Da yake da yaran ya je. Suna dawowa
Hamim ya yi barci. Hanif ne ya dan jima yana kallon cartoon kafin shi ma barcin ya
sure shi bai sani ba.
Har lokacin muna zaune jigum jigum tamkar masu zaman makoki. Ya numfasa ya ce
"Asiya mu fahimci juna mana. Ko motsi ban yi ba. Bare na tanka masa. Ya ce "Na rasa
gane halin da nake ciki. Gabadaya jina nake yi a juye. Amma mu fahimci juna. Kin ga
Babah ta yi fishi da mu mai tsanani. Mu shirya kanmu, gobe sai mu je mu bata
hak'uri."
Na ce "To".
Ya ce "Ban gane to ba Asiya".
"Allah wahidun! Me zan ce maka to?
Na ce a,a?"
Ya kalle ni kawai.
Ya mik'e ya sure ni tamkar yar tsana ya yi dakinsa da ni. Yana fad'in "Mu je kan
katifa na rarrashe ki, domin na gane rarrashi akan katifa yafi na kan gado ratsa
jiki".
Na dinga mutsu mutsu tare da son na kwace

Please Login or Register in order to submit comment