You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsarki ba ne.
Har ta kai bana k'aunar na fita. Amma idan ban je ba sai ta aiko wai na je, a
wannan lokacin k'warai Dada take tausayina ni da yara. Kullum a cikin sadaka da
addu'a take yiwa Tijjani. Kuka kam bansan wa yafi yi a tsakaninmu ba. Ta damu
k'warai har jininta ya hau.
Ban sake samun damar gano Tijjani ba har aka yi sati da zuwanmu. A lokacin kuma na
fara gazawa.
Tashin hankalina na sake hauhawa.
Baban Kasuwa da na Tsakiya babu wanda ya tako kafarsa da nufin yi mini jaje.
Ashe wai na yi laifi da ban bisu kofofinsu na gaishe su tare da yi musu jaje tunda
ai su d'ansu ne tun kafin ya zama mijina.
Ni luma damuwata ta girmi tunanin zuwa gaishe gaishe. Sannan mafi yawa a wajen Dada
nake ganinsu na kuma gaishe su a mutunce.
A lokacin na sake fahimta tare da gasgata idan Baban Marina ya kauce bamu da wanda
zai tsaya kai da fata ya tallafemu idan mun shiga cikin kalubalen rayuwa. Tausayin
k'ananun y'aya'n Baban Marina ya sake rub'anya tashin hankalina. Gabadaya na zama
tamkar wata zararriya, na k'are na fige tamkar kudin guzuri. Bayan addu'ar da nake
yi wa Tijjani da y'aya'na, sai na sake tsananta addu'ar Ubangiji ya sanya soyayya
da tausayi mai yawa a tsakanin y'aya'n Baban Marina.
Domin kam al'amarin Baffaninmu sai shukuran. Kullum mutuwa na daukarmu daya bayan
d'aya amma bata zame musu izna ba.
Abin da na sake fahimta kawai shaidan da son zuciya gami da hassada ne suka yiwa
zumuncin yau k'awanya.
Sassaucin rayuwar da Baban Marina ya samu a dalilin y'aya'n sa ya zama wani abin
tattaunawa. Kullum a cikin fad'in ai yanzu ya farfado suke.
Na tabbatar ba za'a bar ni na ji da ibtilain da ya fad'o mana ba, sai an tusa ni
gaba da muzanci kala kala. Dan haka na kudire da na yi sati biyu zan fad'awa Baban
Marina zan koma dakina tunda dai Tijjani bai mutu ba.
Washagari muka tafi Kano da ni da Nazira da Yaya Salisu.
Gabadaya Tijjani ya fita a hayyacinsa. Ina kuka nake fad'in "Basa baka abinci ko?"
Ya girgiza kai ya ce "Abin nan da nake fad'a miki. Da zarar hantsi ko yamma, ta yi
sai gabad'aya na rikice, zuciyata kamar ta yi bindiga wajen son na tafi Toro na ga
Nasiba. Masifar zafin da nake ji a zuciyata da kirjina ya wuce misali ina fatan na
mutu kawai Asiya".
Na kasa ce wa komai. Yaya Salisu ya ce "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun! Allah
mun tuba."
Nazira kuwa kuka take yi tana fad'in "Dama nasan ba haka siddan ka runtse ido ka
kafe sai ka aure ta ba."
Ni kuwa na zama tamkar mutum mutumi. Domin a yanzu na yarda Tijjani na bukatar na
samar masa da nutsuwa. Tunda duk yadda yake cikin wannan tashin hankalin amma yana
fad'in yadda yake ji game da al'amarin ta. Na tabbatar ba son zuciya ko tozarci ba
ne ya sanya yake fad'a mini yadda yake ji akan Nasiba ba.
Cikin tausayi nake kallon sa gabad'aya ya zube, ya yi duhu. Tausayi, so, kauna suka
sake yi mini rubdugu a dukkan zuciyata da gangar jikina.
Murya a tausashe na ce "Ka tsananta addu'a ka kuma yi hak'uri. Da kaina zan kawo ta
ka ganta".
Ya zuba mini ya ce "Yaushe?"
Na ce "Gobe ko jibi".
Ya yi k'asa da kansa ya ce "Goben dai."
Da k'arfin hali na ce "To".
Ya kidime ya ce "Wanne irin to kike nufi Asiya?"
Na ce na gaskiya da gaskiyar magana ".
Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa ya ce "Ina twins, me ya hana ki zo da su na
gansu?"
Idona cike da k'walla na ce "makaranta suka bi yaran gidan."
Haka muka ba shi abin da zamu ba shi. Aka tafi da shi.
Tuni kuma an saka ranar da za'a gurfanar da shi gaban kotu.
Sai dai Yaya Ammar ya tabbatar mana BAUCHI za'a dawo da shi. Tunda a cikin jahar
Bauchi aka kama shi. Ba'a san dalilinsu na kawo shi Kano ba tare da sun sanarwa da
kowa nasa ba har tsayin kwanaki biyu.
Da yammaci sosai muka isa Toro. Muka tarar da Nasiba a k'ofar Dada domin mijin
babarta aka kwantar a asibitin koyarwa na jamiar Jos. Lokacin da abin ya faru tana
can bata dawo ba, sai yau aka sallame su. Babar tata ta wuce gidanta da marar
lafiya.
Ni da Nazira muna kallon yadda gabadaya ta takure ta kasa sakat tunda muka shiga.
Akwai alamun tasku a tare da ita.
Na yi jarumtar ce wa "Nasiba Bulkachuwa na ta jajen ki. Ya damu da rashin ganinki
cikin masu zuwa duba shi tare da jajanta masa. Gobe zan koma, sai mu tafi tare ko
ya samu nutsuwa".
Ta kasa amsawa. Hatta Dada ma na kashe ta da kunya gabad'aya sun rasa me zasu ce.
Yanayinsu ya sa na gane suma tamkar an tursasu ne akan sha'anin Tijjani.
Washagari kuwa na shirya yara na ce mun tafi Kano. Baba bai so ba, amma saboda
lallaba farincikina yake yi bai hana ba. Sai ma ya ce "Ubaidun Inna ya raka ni.
K'ofar Dada na dire. Na tisa Nasiba a gaba muka tafi a kan dole ba yadda zata yi.
Domin na lura tsoro nake bata.
Har muka isa Kano ba wata hira a tsakaninmu.
Sai kuma muka hadi da tasgadon y'an sanda. Wai ba zamu gan shi ba, ana yawan yi
musu zarya da sunan ganin Tijjani bayan shi mai babban laifi ne.
Hanif ya fashe da kuka yana ce wa "Zamu ga Baban 2 dan Allah ".
Hamim ma ya fara kuka sosai.
Watak'ila tausayi suka bawa wannan babban dansandan sai kawai ya bada umarnin a
fito da shi.
Ga mamakina sama da mintina goma da isowar Tijjani bai kalli inda Nasiba take zaune
ba. Tunda ta gaishe shi ya amsa hankalinsa na kan su Hanif da suke kan cinyarsa bai
sake bi ta kanta ba.
Ni da yara kawai ya ke kulawa.
Na mike na ce "Bari na baku waje tunda idona yasa ka kasa yin hirar".
A zabure ya ce "Zan ci mutuncin ki little! Jiya da yau ban ji azabar da nake ji ba.
Akwai abin da ake yi mini wanda zalunci ne da k'eta. Alfarmar Annabi kuma Allah zai
kawo mini k'arshen al'amarin tunda kwana nake ina fad'awa Ubangijin al'arshi ya
warware mini wannan masifar. Ni ko wannan k'azafin da aka yi mini baya gigita ni,
kamar yadda al'amarin ta yake gigita ni. Amma akwai Allah."
Ba Nasiba ba, ni kaina sai da na ji babu dad'i ainun. Na yi tsuru tsuru na kasa ce
wa komai. Domin na tabbatar k'arshen muzanci Tijjani ya yi shi. Amma na sake
gasgata surkulle ake yi masa. Ban da haka jiya k'iri k'iri ya fad'a mini yau na
kawo masa ita. Ko tunanin rikicin da zan yi masa bai yi ba, saboda an ringa an
kidima shi a kanta. Na daure na rakito ta, amma bai ko kalli inda take ba, sai ya
b'uge da cin mutunci. Jikina ya mutu domin nasan zata zargi na kwaso ta ne dan na
saka mijina ya wulakanta ta a gabana. Tunda a hakan kafatalin gidan Marina sun tafi
akan na gama da Bulkachuwa tsorona yake ji. Sai abin da na shimfi'da zai bi. Har
fad'i suke idan bana son mutum to ko kallon arziki Tijjani baya masa saboda gudun
zuciyata.
Ta mike a kasalance ta ce "Bari na jira ku a mota Yabi".
Murya babu amo na ce "To".
Tana tafiya ya saki dogon tsaki mai karfi da na tabbatar zai je kunnuwanta.
Na zuba masa ido ba tare da na iya ce wa komai ba.
Da k'yar na ce "To da sun san zasu mayar da kai Bauchin me yasa suka kawo nan?"
Ya kalle ni ya ce "Akasi aka samu. Sun tsayar da ni a farko ban tsaya ba. Shine
suka harbi tayar motar ikon Allah ne yasa motar bata yi bari da ni ba".
Zuciyata ta buga da tsananin gaske na ce "mene ne dalilin ka na k'in tsayawa Baban
2? Ta ya ya kana dan k'asa amma ka ce ba zaka girmama dokar k'asar ba? Ko dai kasan
dama baka da gaskiya ne?"
Nan da nan ya kidime ya ce "Wallahi Tallahi ina da gaskiya, bansan an saka mini
wannan abin ba. Ban sani ba, ki yarda da ni Asiya!.
Na saki karfaffan numfashi tare da ce wa "Rashin tsayawar ka ba k'aramin hujja zasu
kafa da ita ba. Na yarda da kai".
Ya nutsu ya ce "Idan har kin yarda da ni to kowa ma kada ya gasgata ni Asiya! Nasan
mahaifuyata zata shaide ni, duk fitina ta bana harkar maye bare kuma a yanzu da na
girma. Ba zan shiga safarar abin da nasan illah ce ga al'umma ba. Ina miki ranstuwa
da girman Allah ban san mugun abu aka bani ba. Waya kawai aka mini akwai sakon kaya
da zan karba a Dutsen tanshi, idan na kai Kano za'a karba a biya ni. Kinsan kuwa
ina harkar sakonni(Delivery). Ban tab'a zaton za'a mini kutse a cikin sana'a ta ba.
Ni yanzu babban tashin hankalina ke ce. Ban san hukuncin da za'a yanke mini ba
little. Kinsan k'asar nan waka sani ne waya sanka."
Idona taf da hawaye na ce "Nasan baka aika ta wannan BAK'AR TA'ADAR ba. Da ikon
Allah ina tare da kai, komin tsanani".
Ya murmusa ya ce "Alhamdulillah! Na samu amincin firgicin da nake ciki. Dan Allah
Asiya kada ki canja, kada ki juya mini baya a cikin wannan halin canka cakare da
nake ciki." Idonsa ya kad'a sosai ya kasa cigaba da magana alamun ya shiga rudani.
Hanif ya ce "Baban 2 kada yi kuka zamu zauna mu taya ka zama. Ammo ta tafi ta barmu
tare da kai".
Hamim ya ce "No zamu je mu koyo yadda zamu kwace shi daga hannun yan sandan kawai".
Na yi k'asa da kaina kawai ina hawaye domin tausayin da suka ba ni ba kad'an ba ne.
Ban iya ce musu komai ba. Shine ya yi jarumtar sake rungume su tunda a akan
cinyoyinsa suke. Murya na rawa ya ce "Baban 2 baya karya domin wanda ya yi karya ya
zagi Allah, Wanda ya zagi Allah kuwa dan wuta ne. Dan haka am innocent, ban yi
laifi ba. Sharri aka yi mini. Kowa ya yi sallah ya yi wa Baban 2 addu'ar ya zama
free".
Suka had'a baki wurin ce wa zamu yi sosai ".
A sanyaye muka rabu domin gobe za'a dawo da shi BAUCHI dan shiga kotu.
A hanya Nasiba ta sake rasa kuzarin ta, dama kuwa bata iya sake wa a gabana na dade
da fahimtar a takure take da ni. Abin da Bulkachuwa ya yi mata kuwa ya sake sanyaya
mata jiki. Ina hankalce da ita, ina ganin yadda take son yi mini magana amma ta
kasa.
Cikin kundubala ta ce "Yabi!.
Na amsa da "Na'am" murya babu amo.
Ta kalli twins da suke barci a jikina. Ta ce "Idan na ce miki bana son Yaya
Bulkachuwa na yi karya domin na girma da son sa, ke ma kin sani. Idan na ce miki a
yanzu dole aka mini a kan aurensa zaki yarda?"
Ban ce komai ba. Illah ido da na zuba mata.
Ta numfasa ta zarce da ce wa "Ni da kaina bani da yadda zan yi ne. Domin kuwa
mutane da yawa suna haduwa da kalubalen a hadasu da iyaye karkatattu. Sai dai duk
da hakan ba zamu ki sonsu ko janye wa daga gare su ba. Na sani tun farko soyayyar
sa gare ni ba mai yawa ba ce, bare yanzu da yake auren ki. Dan Allah ki yi hakuri
kada ki datse mu'amala da ni Yabi. Al'amarin zumuncin yau ya shiga rudani mai yawa,
amma idan aka yi hak'uri aka danne, aka yi sassauci sai a samu masalaha a duniya, a
kuma samu rabauta a duniya.
Zan yi iyakar kokarina na fita a harkar mijinki, na yarda Yaya Bulkachuwa ba mijina
ba ne, ba kuma zai zama ba. Kada ki ce maganganun da ya yi cin fuska ya yi mini,
zahirin gaskiya ya amayar".
Na rik'e hannunta murya na rawa na ce "Ban kullece ki ba. Amma idan na ce ban ji
ciwon abin da ya faru ba na yi karya. Har abada ba zan iya auren mijin ki ba
Nasiba. Amma na hak'ura na barwa Allah ya yi mini zabi akan lamarinku. Tunda ai ba
haramun ba ne. Shi yasa na hak'ura na barwa Allah komai".
Dukkanmu kowa zuciya ta narke, muka dinga kuka.
Ubaid da yake gaban motar ya yi tsaki ya ce "Sai ku yi ai. Amma ai mu kam mun
kudire matukar ya aure ta sai ya sako mana ke ko da kuwa a gaban alkali ne".
Na daskare da maganar sa. Na tuna na ba shi watanni shida. Gabadaya ma shekarunsa
ashirin da uku ne. Amma ya yi magana kamar wani babban wanmu. Sai kuma hawayena ya
sake zuba a dalilin yadda maganar auren Nasiba da Bulkachuwa ta zama silar samar da
soyayya a tsakanin ahalin Baban Marina. Yan ubancin da manyanmu suke gwada mana ya
yi matukar zangwanye wa.
Na yarda mafi yawan kalubale ya kan zo da wata nasarar komin kankatarta sai dai
idan ba a kula ba, ko an bari hankali ya kwace an yi fishin da ya shallake hankali.


✍️
*Y'ar uwa, ya mukaji da bubukuwa?* *Daga nan fa har january kusan ko wanne sati
akwai biki, in ba na kusa ba akwai na nesa, ban da tunanin gudunmuwa da ma kudin
man da zakaje bikin ga tunanin abunda zaka saka.*
*Balle ace maaikaciya ce ko CEO ce kina business din ki, kinsan all eyes on you🧐,
ke ba sayen atamfa ba komi tsadanta anyo copynta, shima lace haka, cabdi! To
albishirinki yar uwa!*
*UMM NIHLA malaysianfabrics ta dauke miki damuwa, tana da fabrics kala kala masu
sauki da inganci kuma babu inda zaki samesu in ba wurinta ba, kije taro ki haska
kowa sai ya tambaye ki me kika saka ina kika samu💃 maza garzaya gurinta kusa
labule.* https://wa.me/message/F3EWRSHQPQAAH1

Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*


Washagari duku duku Baba Maryo ta zo.
Domin na je gaida Dada na juyo muryarta tana ce wa "Ai ko baki bijire mini ba
gabad'aya ba zai aure ki ba, wane shi. Ashe dama arzikin da ake ga ni a tare da shi
kazami ne? To ba zata sabu ba. Aure kam tabbas ya fasu fas. Dama ai ba so kike ba,
tunda kin ringa kin tsorata da iblishiyar mata tasa. To ta je ta samu sai ta
tabbata a matar d'an safarar kwaya ita kad'ai. Mutane babu Allah a ransu. Ka dinga
neman arziki yaki haram yaki halal. Dama so na yi na nuna wa uwarta da ita Yaya
Hauwa iyakarsu. To tunda bai shiryu ba, huta toro an bar musu shi. Watak'ila ma
daurin rai da rai za'a yi masa. Ai da a sau'udiyya aka kama shi fille wa d'an banza
mai yiwa iyayensa kallon raini za'a yi".
A sanyaye Dada ta ce "Ai kuwa mai sunan manya ya yi hankali da girmamawa yake gaida
kowa kamar ba shi ba. Kawai dai yana nuna son kai ne, ya fi nan nan da k'ofar
Alhaji. To wannan kuma dariyar matarsa yake so, ya za'a yi tunda ya jarabtu akan
ta.!"
Baba Maryo ta ce "Ban da ni din, ni ce ai ko gaishe ni ba zai yi ba, ya kullace ni
ainun. Tunda ake fad'in labarin wadatar da yake ciki, ashana bata tab'a had'a mu
ba. Kai ya taka ya je gidana bai san wannan ba. Idan ya gan ni tamkar zai doke ni.
Amma yanzu da yake ba shi da kunya har zarya yake yi mini. To na fasa ba shi
Nasibar. Ba zai yiwu ba, ya je dai ya k'arata da afiruwar matarsa mai izgili. Kai
ahalin Tijjani da Yabi za'a yi majununai, biyu ta had'u y'aya'n iska marasa
albarka".
Na sake jin cikin rauni Dada ta ce "Yanzu fa sun yi hankali suna girmama kowa. Yabi
da kanta jiya ta zo har nan ta tafi da Nasiba wajen mai sunan manya. Kin san idan
Yabin da ce ba za'a yi hakan da ita ba".
Ta saki tsaki ta ce "Yo tunda ya rikice mata ai dole ta kai ta. Amma daga yau zan
yanke komai."
Dada ta kame bakin ta. Ita kuwa ta ci gaba da sakin maganganu masu nuni da dama ba
Tijjanin take so ya zama surikinta ba. Wadatar da ake kallon ya samu ne ake son su
lasa. A yanzu da ya hadu da ibtila'i kuma an janye saboda dama ba da zuciya d'aya
aka yi abin da aka yi ba.
Na shiga daga bakin kofa na gaida Dada, duk da tana ce wa "iso mana, ina tagwaye ko
basu farka ba?"
"Eh suna barci Dada".
Na gaida Baba Maryo a gajarce. Ta amsa fuska babu walwala. Har na juya sai ce wa ta
yi "Yabi ashe haka ya faru da Tijjani?"
Na ce "Eh!
Sai ji na yi ta ce "To wadannan kadarorin da suke yatsun ki da kunnawan ki sai ki
hanzarta kad'ar da su dan ki dauka masa lauya domin dai a gindinki da na iyayen ki
ya k'are. Gyatumar sa ma yar amshin shata aka mayar da ita. Watak'ila hakkin ta ne
ya sanya yake gani a k'waryarsa.
Na juya da nufin bata amsa sai na tuna kanwar mahaifina ce. Ba zai yiwu na yi fad'a
da ita a yanzu da hankali ya ratsa ni ba. Nasan kuma dole ni ce a ciki tunda shi da
kansa Baban Marina zai ce ai kanwarsa ce ta shiga rigarsa mana.
Dan haka sai na hadiye na ce "To Baba Maryo zan yi hakan".
Ta tunbatsa domin ta washi mu fad'i sunan ta.

***
*BAUCHI*

Kotun ta cika makil domin sharioi za'a yi masu daukar hankali.
A kuma wannan ranar za'a yanke wa Tijjani hukunci.
Da wuri muka iso. Da ni, da Yaya Salisu da Baban Marina da kuma Yaya Salamatu.
Sai ko Yaya Ammar da yake Bauchi.
Karfe shadaya aka fara shari'arsa. Babu wata hujja da zata wanke Tijjani. Domin
lambar da ya ce an k'ira shi da ita kwata kwata bata shiga. Sannan an tambaye shi
me yasa da aka ba shi kaya bai bude ya duba ba? Tunda ya dauki delivery a matsayin
sana'a. Me yasa ba ya nazarin kauce wa dukkan wata matsala da zata taso. Wajibi ne
idan zaka karbi sako, ka duba ka ga mene ne a ciki tunda idan aka kama ka ai kai ne
a ciki.
Sannan me yasa bai binciki ainihin inda mutumin yake ba?"
Lauyan da k'aninsa Aliyu ya daukar masa, ya kasa inkarin hujjojin lauyoyin gwamnati
tunda tabbas Tijjani bai yi bincike ba ya karbi kaya. Bai kuma bude ya duba ba. An
ba shi abu a d'aure cikin buhu kawai ya danna a mota. Sannan bai san mutum ba.
Kawai ance idan ya je Kano za'a karba a biya shi.
Sannan lauyan gwamnati ya k'ara kafa hujja da ce wa "saboda Tijjani yasan ba shi da
gaskiya ya dauko wiwi da koken mai nauyin tam goma shi yasa ya ki tsayawa da
jami'an tsaro suka tsayar da shi wanda hakan rashin da'a ne da raina jami'an tsaron
da k'asa ta wakilta su duba shige da ficen al'umma."
Na zuba wa Tijjani ido da yana tsaye jikin kantar da ake tsayar da wadanda ake
tuhuma. Ya zube aiun, ya sake yin duhu.
Zuciyata ta karaya, na hangi rashin sassauci a shari'ar. Ta zo fiye da yadda muka
tsammace ta.
Domin maganarsa d'aya ce ba shi kayan aka yi, bai san kuma san mutanan ba. Lambar
wayar da ya gabatar a matsayin wacce aka kira shi da ita bata yi.
Jikin kowa ya yi sanyi. Bayan dogon rubutu da alkalin ya yi.
Ya yi gyaran murya ya ce "Duba da hujjojin da lauyan gwamnati da kuna jami'an tsaro
suka gabatar kotu ta yanke wa Tijjani hukuncin shekaru biyar a gidan yari babu
tara. Bisa kama shi da safarar kwaya wanda hakan ya saba kashi na goma sha takwas
b cikin baka. Bayan haka kotu ta sake d'aure shi shekara d'aya bisa cin zarafim
jami'an tsaro da ya yi ta hanyar yi musu gaddama. Har ila yau kotu ta daure Tijjani
na watanni uku ko tarar dubu ashirin saboda rashin kiyaye kaidojin kasuwanci. Ba
zai yiwu mutum yana hulda da jama'a ba amma babu taka tsantsan da sanin me mutum ya
dauko ko mai zai kai. Yana cikin dab'iun d'an kasa na gari ya zama yana duba komai
yana kuma kiyaye dukkan doka."
Ya rattaba hannu akan takardun tare da buga stamfi.
Gabadaya ahalinmu hankaliinmu ya yi mummunan tashi. Ni kam kuka na ke yi mai gunza.
An daure shi shekaru bakwai babu tara?
Wacce irin bak'ar kaddara ce wannan?
A harabar kotun muka tsaya da shi tunda Yaya Ammar na cikin ma'aikatam gidan yarin.
Na kalle shi sai kawai na fashe da kuka a dalilin raunin da na ga ni ya bayyana
masa a dukkan jikinsa da zuciyarsa.
Muka zubawa juna ido ba tare da mun tuna daruruwan mutanen da suke wajen ba .
A sanyaye ya ce "Asiya shekaru bakwai da yawa. Tashin hankalina bai wuce ke ba. Ba
zaki iya ba. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun "
Sai kawai hawaye ya ya k'wace masa shabe shabe".
Na rik'e hannunsa na ce "Ko shekaru sha bakwai ne zan jira ka Baban 2. Idan har
rayuwarmu ta kai zaka fito ka tarar da ni a dakin ka. Zan kiyaye maka amana, zan yi
aiki tuk'uru na kular maka da y'aya'n ka. Jarumtar nan da ka ke fad'in na dinga yi,
zan nin ka ta daga yau".
Baban Marina ya dauke idonsa amma bai iya tsayar da hawayensa ba. Tijjani ya matsa
kusa da shi ya ce "Wallahi ban aikata laifin da aka jingina mini ba, rami aka haka
mini na fad'a. Ka taimake ni, ba zullimin hukuncin ne ya zautar da ni ba. Fargabar
yadda zan iya rasa Asiya ne. Shekaru hudu ne gejin da shari'a ta dibawa mace akan
dakon mijinta. Ni kuwa shekaru bakwai aka zarge ni".
Hawaye ya cigaba da tsere babu kakkautawa.
Baba ya kasa ce wa komai. Su Yaya Salisu kowa hawaye. Cikin k'arfin zuciya na ce
"Idan ni ce matsalar ka, to ka kaddara baka da damuwa. Zan jira ka. Ba ka ce ko ka
mutu na zama jaruma dan na tallafi y'aya'n ka ba? Zan kiyaye mutuncin ka, zan kuma
maye wa y'aya'n ka gurbin ka har zuwa lokacin da zaka dawo ka cigaba da kulawa da
mu gabadaya. Ka sa a ranka ban yi kokwanto akan ka ba Tijjani. Na gasgata ka, na
yarda da kai."
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Allah ya k'ara lafiya Baba. A sanya ni cikin addu'a.
Ni kuma ya mini murmushi kad'an ya ce "Na gode".
Daga haka suka tafi da shi.
Fir na k'i yarda na koma Toro. Domin idan ina gida tashin hankalina yafi yawa a
dalilin ina ganin tamkar Tijjani ya rasu ko mun rabu. Bayan haka karatun yara ya
dakata.
Baban Marina bai matsa mini ba, jikinsa ya yi laushi ya kamu da mugun tausayinmu.
Yaya Indo ta zauna da ni na kwanaki biyu. Komai ita take yi, ta ji da hidimar yara
ta kuma yi girki da kwantar mini da hankali. Tun sanadin auren Nasiba muka hade da
su. Gabadaya yan k'ofarmu muka dinke, muka dunkule, duk wani tsegmi ya yi s'auki
tunda dama manyan namu ne karkatattu.
Sai da Babah ta Bulkachuwa ta zo sannan ta tafi. Dada ce ta zartar da umarnin Babah
ta zo ta zauna da ni. Cikin alhinin rashin Tijjani da kuma tausayi da kyautatawa
muke zaune. Nasirun ta wanda shi Ihisan take bi a kai a kai yake zuwa mana domin
dalibi ne a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da take cikjn Bauchi.

*Toro*.
Anas da yake bin Yabi. Yana bandakin k'ofar Dada yana simince shi a dalilin wanda
aka yi mata da ta rubza ya farfashe, ba'a yi aikin aminci ba.
Gabadaya Baba Maryo ta shafa'a shaf yana k'ofar, kuma kusa da kicin din da take
zaune ne.
Ta hau tonon murhun tana ce wa "Allah suturi buk'i da auren mazinaci kuma mai dilar
k'waya. Wane mutum na had'a iri da shi cikin sanina?"
Kalaman ta suka ja hankalinsa ya ajiye abin aikin ya leko tunda bayin ba me k'yaure
ne ba.
Ganin da ya yi tana tono ya sake jan hankalinsa k'warai da gaske, ya matso sosai.
Yana kallonta k'yar. Ya jima yana zargin Yaya Bulkachuwa ba a bar shi haka siddan
akan al'amarin Nasiba ba. Ashe kuwa hakane. Ya sandare cikin tu'aajjibi a lokacin
da ya ga ta fito da laya a k'asan murhun ta kyasta mata ashana ta k'one.
Ta ja tsaki mai tsananin gaske tare da ce wa "Allah na gode da baka k'addara mini
ganin auren ta da mai arzikin bogi ba. Ban da ma dai batan basira me za'a yi ne da
wanda aka yiwa bulalar zina a bainar nasi? Lallai na yi mantuwa mai yawa. To na
tone ramin da na hak'a tun ban rufta ba. Dama Yabi ce ta dace da shi a wannan
duniyar."
Daidai lokacin Anas ya kasa jure wa ya yi gyaran murya. Ta waiwaya a ankare.
Idanuwansu suka hadu, ta yi wura wura. Ta rasa inda zata tsoma ranta. Shi kuwa sai
ya ce "A dinga yin sara ana duban bakin gatari Baba! Da Yaya Bulkachuwa, da Adda
Yabi, da kuma Adda Nasiba kamata ya yi ki dauke su abu guda. Ba wai ki nemi
rugurguza zaman lafiyarsu dan bukatar kan ki ba. Kin cutar da su duka. Ita

Please Login or Register in order to submit comment