You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin na Bulkachuwa baya yin tasiri
akan sha'anina.
Na hakaito yadda yake ta ha'da zufa wanda na tabbatar dan ni yake yi.
Abin da nake ji mai kama da tausayinsa ya sake tsananta a tare da ni.
Bansan me yasa idan yana kusa da ni nake jin zafinsa ba. Amma ga dukkan alamu
rashin iya wanka da gayunsa na cikin cikas dinsa a wajena.
Na gama uzzirin na yi wanka sosai.
Sadda na fito a falo na hango shi ya kunna talabijin yana ta kokarin saita
tashoshi.
Na shirya tsaf. Kamshina ya cika dakin.
Na hau kakkade dakin.
Haka kawai sai na ji tamkar ana kallona. Na juyo ai kuwa sai ganinsa na yi yana
jingine da bango ya yi mini zuru.
Na b'ata fuska na juya na cigaba da aikina.
Ya shigo ya ce "Asiya me zan miki ki daina mua'amalanta ta irin haka?
Ko arzikin gaisuwa bani da shi a wajen ki? Me ya yi zafi ne?"
Na share shi.
Ya tausasa harshe ya ce "Burodi na siyo. Na dafa shayi, na kawo nan, ko zaki fito
falo?
Da kin daure ma, sai ki zo falon kina karyawa kina kallon tashar da kike so".
Ban d'ago ba, na ce "Kallo bai dame ni ba."
Ya yi shiru na sakwanni sannan ya saki ajiyar zuciya ya ce "Bari na kawo miki nan
to".
Ya fita ba tare da ya jira amsa ta ba.
Bai jima ba, ya shigo da da biredi da robar butter. Ya ajiye, ya sake juya wa.
Ya dawo da kofi yana turiri.
Ya ajiye a gabana. Na kalli shayin na ga hadin kauri ya yi masa na sosai.
Amma wani sashe na zuciyata ya k'alubalanci had'awar da ya yi. Akan me ba zai kawo
mini na ha'da da kaina ba kamar yadda ya mini jiya da shekaranjiya ba?
Take na yarda wani k'ullin ya shirya mini.
Ya zauna daga k'asa da rarrashi ya ce "sauko ki sha kada ya huce nasan ba kya son
shayi idan ya huce."
Na zo na zauna kamar da gaske shan zan yi, na dinga juya cokalin cikin shayin.
Ya zuba mini ido yana kallon yadda gown din material din Umm Nihla kalar k'wanduwar
k'wai ta karbi farar fata ta, dinkin kuma ya yi kyau sosai ya zauna mini.
*Umm Nihla mazauniyar Malaysia ce, daga can take turo kayanta masu aminci da
rahusa zuwa Kano*
*Tana bada daya tana bada sari yadda ke ma zaki sami alheri*
*Tuntube ta manhajar Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko
jeme wa*
*07020695644*
Ba zato kawai na tuntsurar da shayin.
Nan da nan kuwa shayin ya fara gangarawa inda yake zaune.
Ya zabura ya tashi. Ko ban kalle shi ba na sani ya kai k'ololuwar fusata tunda ya
ga ba cikin kuskure ya zube ba.
Murya na rawa irin ta tsananin b'acin rai ya ce "Wanne irin wula'kanci ne haka?
Idan ba zaki sha ba, ki bar mini mana. Almabozaranci babu kyau. Kin yi dan ki b'ata
mini rai, ki saka ni ba'kin ciki! Tabbas hak'kar ki ta cimma ruwa. Raina ya baci
k'warai da gaske. Sai dai ki sani, bazan sake yi miki irin wannan kyautatawar ba.
Yau kwanan ki uku a gidan nan. Daga yau kin fita daga bakunci a ka'idar shari'a.
Dan haka ki fito ki dora abincin rana yunwa nake ji, ko kuma na bar ki da
Ubangijin da ya wajaba miki yi mini biyayya".
Na fashe da kuka sosai domin ban zaci abin da zai biyo baya ba kenan.
Tun fil'azal na tsani ace za'a bar ni da Allah.
Cikin kukan na ce "Akan me zaka ha'da mini ba a gabana ba? Na sani ko ka jefa mini
wani
abu a ciki".
Ya ja tsaki mai tsananin gaske. Ya ce "oh ina ganin tala jaurar duniya. Wai ke nan
kina zaton zan miki wani abu a dole?
Ya girgiza kai ya ce "Babu macen da zan mata hakan. Sai kuma ya fashe da dariya mai
sauti sosai.
Da murmushi ya ce "Asiya Toro manyan mata. Ki yi ta abu tamkar wata babbar mace.
Dan Allah duka shekarun ki nawa ne?
Kin wuce sha biyar?
Ni kallon kwaila nake yi miki wacce bata gama fitar da halittun ta ba. Wacce bata
kai wankan girma ya hau kanta ba. To me kike zaton zan miki da har zan baki wani
abu na rashin gaskiya a cikin abin sha?"
Ba'kin cikinsa ya sake makure ni. Na sake fashe wa da kuka mai tsananin gaske.
Ya sa kai ya fice yana jaddada idan ban zo na dafa masa abin da zai ci ba, ya bar
ni da Allan da ya kallafa mini yi masa biyayya.
Na jima ina zaune ina kukan ba'kin cikin takaicin da ya cusa mini.
Ga cikina sai kiran ciroma yake yi.
Ala tilas na tashi na fita bayan na goge fuskata da tissue.
Har lokacin yana ta faman hade wayar satellite din a jigin bango.
Na wuce shi fuu na fa'da kicin din.
Na tsaya ina nazarin me zan dafa ne?
A yadda nake jin yunwa zan fi son jalaf din taliya mai dan ruwa ruwa.
Dan haka na zabi kayan miyan da suka fara yin laushi na wanke na fara jajjege dan
na rasa inda gireta take, duk da akwai wuta zan iya blanding dinsu. Sai dai na fi
son na gansu a jajjegen.
Na yanka albasa mai yawa.
Na bare maggi duk na ajiye a kusa da ni.
Na tashi na daurayo tukunya, ya kalle ni, na galla masa harara.
Ya yi murmushi tare cewa "The great Asiya a kicin dinta".
Na share shi, na shiga falo na dauko naman da ban ci ba a fridge.
Na duba na ga ya cire albasar ciki.
Na nufi kicin din. Na zuba mai a tukunya. Na zuba albasa. Na jere komai na bu'kata
a gabana.
Na kalli gas din da yake tsaye sabo dal da shi. Na fara tunanin yadda zan kunna
tunda zancen gaskiya ban ta'ba kunnawa ba. Bamu taba amfani da shi a gidanmu ba.
Na yi shahadar murda wa sannan na fara kokarin kyasta ashana.
Sau biyu ashanar tana karyewa saboda rashin k'warinta.
A karo na uku ta k'yastu, na nufi bakin gas din da ita. Ai kuwa gas ya yi wani irin
but da karfin gaske! Na furgita, na tsora ainun, na mike na dinga karo da fatali
da kayan da na jere a gabana na yi waje a guje cikin ki'dima mai yawa.
Ya fito a band'aki ke nan, ya gan ni a guje na yi dakina.
Ya biyo ni da sauri. Fa'di yake "mene ne, mene ne?"
Ya zuba mini ido yana kallon yadda jikina yake kyarma irin na tsoro sosai.
Da sigar salama ya ce "Asiya! Nutsu ki fa'da mini. Mene ne ya ki'dima ki haka?"
Ganin na kasa magana ya tashi ya nufi kicin din.
Ya tsaya a bakin k'ofar yaga yadda ruwa ya jiqa kasan kicin din. Komai a wancakale
tabbacin ta kansu ta bi.
Ga gas kuma yana ta yi fahh.
Ya rage karfinsa. Sannan ya dora sanwar. Domin ya saba girki tun yana makaranta.
Ya gyra wajen. Bai bar kicin din ba sai da ya tsaida ruwan girkin tunda ya ga
taliya ta yi niyyar dafawa.
Ya koma ya zauna kusa da ita a bakin gadon. Zuwa lokacin ta dan shiga nutsuwar ta.
Ya sassauta ya ce"Asiya wai mene ne? Kadangare kika ga ni ko tsaka?"
Na zum'bura baki na ce "Wutar abin nan ne ta yo kaina gaba'daya".
Ya kwashe da dariya sosai. Hakan kuma ba karamin kular da ni ya yi ba.
Cikin bacin rai na ce "Yi dariyar ka son ran ka Tijjani, ai ko k'onewa na yi baka
da asara tunda ba sanin darajata ka yi ba".
Na fara hawaye. Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi. Nan da nan ya gintse dariyar
da yake yi.
Ya ce "Very sorry Asiya Toro. Abin ne ya bani dariya yadda kike yar gayu kuma
wayayyiya amma gas ya yi miki wula'kanci irin haka?".
Sai kawai ya sake tintsire wa da dariyar da ta fi ta farko k'arfi.
Ba'kin ciki har mak'oshina nake jinsa. Na rasa me zan yi na sanya takaici akan
zuciya da fuskarsa.
Kafin na yi magana ya yunkura ya tashi a dalilin kamshin da ya fara cika hancinmu
wanda alamu ne na ya tafaso.
Bai dawo dakin ba, sai da girkin ya kammala.
Ya dawo da plate biyu a hannunsa. Ya dire a k'asa, ya sake fita. Kaamshin girkin ya
cika d'akin, hakan ya sake sabunta mini yunwar da nake ji.
Ya dawo dauke da pure water da lemo akan tire.
Hannunsa kuma da fork guda biyu.
Ya zauna ya ja plate daya gabansa ya bu'de murya ya ce "Bismillah Amarya".
Na bata rai na ce " Asiya Toro dai. Ina na kai darajar amarya bayan ni din yarinya
ce kwaila kuma kankanuwa".
Ya murmusa ya ce "Oh wai maganar ciwo ta yi miki ne?
Tsakani da Allah ba gaskiya na fa'da ba? "
Na girgiza kai ba tare da na kula shi ba.
Na sauko na ja abincin da yake jirana.
Na kai bakina duk kushena ban isa na ce ga inda girkin yake da tasgado ba.
Na dinga zura loma.
Sai da ya ga na kusa cinyewa ya kaikaice ya ce "Asiya Toro iyashegen ki yawa gare
shi. Jibi yadda kike zabga loma kina zare ido. Me ya janye tunanin zan zuba miki
wani abu a ciki Kuma?
Kunya ta kamani ka'dan. Amma na daure na yi kamar ban ji komai ba.
Na share shi. Sai da na gama na yi gyatsa, na kalle shi na ce "Na tabbatar da Yaya
J ne ya dafa abincin nan, zubowa zai yi a waje daya. Sannan ya manta cikinsa har
sai ya tabbatar nawa cikin ya cika."
Na saci kallonsa na ga har wata zufa ce ta karyo masa.
Zuciyata ta fara harbawa da tunanin hukuncin da zai yi a dalilin yadda yanayinsa ya
nuna maganar ta buge shi.
Ga mamakina sai kawai ya yi yak'e ya ce "Ba ki yi karya ba Asiya! Domin jiya mun je
gidansa ni da Salisu a dalilin an sace mashin dinsa.
A gabanmu ni da Salisu yake tarairayar Maijidda akan ta daure ta ci ayaba. Kinsan
cikinta ya tsufa ba komai take iya ci ba.
Ai Jabir kam yana mutuntunta maganar tsohonsa akan Maijidda. Sosai yake sonta yake
tattalinta. Har mamaki na dinga yi tare da shakkun idan har ya taba son wata mace
kafin ita.
Ita ma bata jin kunyar mu din yayunta ba ne sai tabara take yi masa son ranta.
Take na gano mata irinsu ba zasu ta'ba barin mijinsu ya yi tunanin wata macen ba.
Wanda duk ya samu irinsu ya gama morewa, ga cikar halitta ga shagaba ga kuma
biyayyar iyaye da aure. Wanda bai samu irinsu ba ai zai dauwama cikin cizon yatsa
ne.
Sannan tagomashin biyayyar da suka yiwa iyayensu ya sanya gidansu ya zama gidan
farin ciki."
Maimakon na b'ata masa rai, sai ya zamana nawa ran ne yafi b'aci. Bayan kod'a
Maijidda da ya dinga yi, tare da kwarzanta ta, sai na fahimci yarfe yake yi mini
akan ban yiwa nawa tsohon biyayya na mutuntata aurena ba.
Na yi shiru na kasa cewa uffan. Ya gaji da jiran kalamina, ya tokara ya tashi. Bai
dauke kwanon da ya ci ba, bare ya ha'da da nawa. Ya bar gidan ba tare da ya yi mini
sallama kamar yadda ya saba ba.
Tun da ya fita bai dawo ba, sai bayan sallar isha. Ga mamakina sai na ji haushin
hakan. Rashin dawowar tasa ta mintsinin zuciyata sai dai ban bari ta bayyana akan
fuskata ba.
Ya leko ni, ina zaune a daki. Bai shigo sosai ba. Ya ajiye mini leda ya juya bayan
ya ce "Sai da safe".
Bansan ya aka yi ba kuka ya k'wace mini.
Ni da kaina ban san dalilin kukan ba.
Amma so na yi ya shigo yana lallaba ni, da ro'kon na ci abin da ya siyo, ina
botsare masa.
Ko duba ledar ban yi ba, na yi kwanciyata bayan na rufe k'ofar dakin.
Cikin dare na tashi da wata azababbiyar yunwa.
A gigice na janyo ledar na hau cin awara irin manyan nan ga kabeji. Da k'yar na iya
janyo leda a lungun gado. Maman kawata Shafa'atu ce ta je Kano ta siyo yajin Annur
food mai dan karen dad'i. Shine ta ba ni roba d'aya.
*Annur food Delicious*
*Ba iya yaji ba har da garin danwake da man Shani, da yajin daddawa*
*Tuntube su a wannan lambar dan k'arin bayani 08039183880*.
Na sani sadda ya kawo da zafinta.
Sai da na cinye tas, sannan jikina ya daina rawar yunwa. Take na tuno ashe jiya iya
taliyar nan kawai na sanya a bakina.
Na jima barci bai dauke ni ba. Sai kawai na yanke shawarar na doro alwallah na yi
nafilah. Na mike ina da tabbacin Gwaggo na kan sallayarta a irin wannan lokacin da
bayi suke barci.
A hankali na zare sakatar na fita. Abin mamaki sai na ga Tijjani akan barandar yana
sallah. Yana sujjada. Na dakata ya idar tunda ba zai yiwu na wuce ta gabansa ba.
Na jingina da kyauren kofar dakin nawa. Ina kallon yadda ya kyautata sujjadar.
Tsawon lokaci bai dago ba.
Wani abu ya sake tsirga mini a kansa. Na tuna a duk sadda Gwaggo ta tashe ni cikin
dare dan mu yi nafila. Cewa take yi daure ki tashi ki nemi yardar Ubangiji Yabi.
Irin wanna lokacin sai zababbun bayi ne suke rabauta da yin ibada. Duk kuma abin da
mai yin ibadar dare yasa a gaba sai ya ga sau'kinsa.
Allah da kansa yake saukowa sararin subhana yana shelar ina mai bu'kata na biya
masa?"
Zuciyata ta sake harbawa domin ni kaina da bana son Tijjani. Kallonsa yana sujjadar
nan sai da na ji wani irin abu, to ina kuma Ubangijin da ya kyautata sujjadar
saboda shi.
Har lokacin kuma bai dago ba.
Na sake tuna jawabin Gwaggo da take fadin kada ki ce sai kina cikin damuwa ko
bu'kata zaki yi sallar dare. Domin idan ta zame miki dabi'a, to lah shakka duk wata
bak'ar k'addara da zata zo miki, sai ta zo da sau'ki, sannan komai kika roka zaki
ga biyan bu'kata duk nisan jinkiri. Ban da ma dai dan adam mai shagala ne, ai ya
kamata ace yana yawan yin godiya ga Ubangiji bisa dinbin niimomin da ya masa.
An yika musulmi, an baka lafiya, an kuma hore maka abin da zaka ci komin kankantar
sa.
Ashe kuwa ba sai da damuwa za'a yi ibada ba.
Na nisa ina jin na fara gajiya da dakonsa.
Har zan koma daki sai kuma ya d'ago.
Na dinka fatan ace sujjadar karshe ce ba zai koma wata ba.
Ai kuwa sai na ga ya zauna, alamun attahiyatu yake yi.
Ina ganin ya sallame na yi maza na wuce a dalilin fitsari ya kama ni ba ka'dan ba.
Yana zaune har na fito na shige shi. Sai dai Ina wuce wa ya sake mikewa tabbacin
dama ya jinkirta mini ne na wuce.
Raka'a biyu na yi mai dauke da gajerun surori.
Na yi yan adduoina. Ban san me yasa na kasa addu'ar da nake nacin yi ba.
Na Ubangiji ya tarwatsa aurenmu. Na tsinci bakina da fa'din Àllah ka mini zabin da
zai fi mini alheri. Karon farko da na yi addu'ar da dukkan zuciyata.
Na yi addu'oi, na yiwa mahaifana addu'a, na ha'da da al'ummar ma'aiki.
Na koma na kwanta ina fa'din "da wanda yayi doguwar sujjada, da wacce ta yi
gajeriya, Allah dai ake yiwa, to Ubangiji ka karba mana gaba'daya".



*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA
KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA
KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
✍️

*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA
BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES.*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.


*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*


Ina kwance ina jin dukkan k'uncin da yake raina yana zagwanye wa da kaso mai yawa.
Ban makara sallar asuba ba, a dalilin ya buga mini k'ofa na tashi.
Wajen k'arfe takwas da rabi na ji ana kwankwasa k'ofar dakin.
Na tashi na bu'de.
Na gan shi a tsaye. Ya kalle ni ya ce "Ki zo ki d'ora mini abin karyawa na fara jin
yunwa."
Na yun'kura da nufin na yab'a masa bak'ar magana. Amma ina ganin yadda ya d'aure
fuskar . Sai ya yi mini kwarjini sosai.
A sanyaye na kawar da fuskata na ce "Ni bazan sake kunna shi ba".
Ga mamakina sai ya sassauta ya ce "Wanko fuskar ki zo na kunna miki. Ai jiyan ma
shi kika fara kunnawa kafin ki kyasta ashana. Sa'a ma kika yi ai da gaba'daya
jkinki zai bi.
Na sake tsorata na ce "gaskiya ka siyo mini gawayi. Idan baka nan wa zai kunna
mini?"
Ya murmusa ya ce "Zaki iya a hankali."
Ya dakata na yi brush, na wanke fuskata, sannan muka nufin kicin din.
Cikin nutsuwa ya ce "Sai kin gama hada komai na girkin ki, sai ki kyasta ashana
sannan ki murd'a gas din ki.
Amma a fara kunna gas da sakwanni kafin a k'yasta ashana hatsarinsa yafi na
had'arin mota muni."
Ina tsaye ya kunna. Sannan ya fita yana cewa "Sai ki dora abin da zaki yi".
Na yi jim ina nazarin abin da zan yi. Sai kuma na yi azamar daukan tukunya na
dauraye na d'ora bayan na zuba citta da kaninfari.
Na sake nutsawa cikin nazarin me zan yi ne.
Idona ya sauka akan doyar da ya zo da ita.
Na dauko wuka na yanki ka'dan tunda manyan ne sosai.
Ina gama ferewa shayin ya tafasa.
Na juye, na mayar da doyar.
Ina zaune ina fatan na soya doyar nan ta yi kyau.
Zancen gaskiya ba saba soya doya da kwai muka yi ba.
Amma kwanaki mun kalla a wata tashar girke girke a YouTube mun gwada a gidan Nazira
kuma ta yi kyau.
Na dudduba na ga babu k'wai a kicin din.
Na fita na gan shi yana ta faman janyo ruwa a rijiya.
Na cuna baki na ce "Kwai za'a ba ni".
Da walwala ya ce baki kula da shi a fridge ba?"
Ban ce komai ba. Na koma kicin na dauko bowl, na nufi falon da shi.
Na debo guda hud'u.
Cikin ikon Ubangiji na kammala aikin lafiya, kuma ta yi dadi da kyau, k'amshi ya
cika gida.
Na zuba masa a plate mai zurfi irin na dafaffiyar roba, na dauko robar yaji na zuba
masa a gefe. Na dauki flask din shayi na kai masa falon.
Na dawo na dauki kofin shayi da cokali da kuma cokali mai yatsu, na kai, sannan na
rufe nawa a kicin din da zummar sai na yi wanka.
Na fito, na ga ya yi wanka ya shirya yadda ya saba.
Ma'ana kaya babu guga.
Takaici ya mak'ure ni. Nan da nan idona ya kad'a a dalilin tausayin kaina da ya
kama ni.
Ni d'an gayu nake so wanda ya iya wanka da soyayya ba marar kintsi irin Tijjani ba.
A shak'e na ce masa "Na ajiye maka a falo".
Ya share tamkar bai ji ba. Na shige band'akin na rufo kofa da k'arfin gaske.
Ya yi sakare domin ba karamin haushi ya ji na wannan tumbatsar da take yi ba.
Sannan ta yi magana tamkar da yaronta, bugu da kari ta buga masa kofa tabbacin
raini na gaske ta yi masa.
Ya ha'diye bacin ran da ya taso masa.
Ya isa falon, ya tarar da wani sabon bacin rai.
An ajiye masa abinci a bude babu sayawa. Sannan duk farantan tangaran din da ya ga
ni ta kasa zuba masa a ciki ta rufe sai a wnanan?
Duk yadda doyar ta yi masa kyau a ido, ga kamshin da ya cika hancinsa. Duk irin
yunwar da yake ji sai ya ji ba zai iya cin doyar ba.
Ya mik'e ya fice ya bar gidan gaba'daya.
Na fito na shirya tsaf. Sannan na shiga falon da nufin kwashe kayan sannan na zubo
nawa.
Sai ganin abincin na yi yadda na bar shi.
B'acin rai ya sake baibaye ni. Wato dama ba yunwa yake ji ba? Tsabar k'yashi da
adawa da barcina yake yi kawai?
Na ja k'wafa.
Har zan zauna na cinye, sai kuma na yi tunanin ko sallamah aka yi da shi, ko kuma
wani uzziri ya fita, zai dawo ya ci.
Na zuba nawa abincin, har na gama bai shigo ba.
Dan hakan na dauke, na kai kicin na rufe. Amma zuciyata tamkar ta fa'do k'asa.
Na hau shara, ina yi, ina hawaye tare da tir da auren dole.
Ina cikin mopping barandar ya shigo da leda a hannunsa. Kai-tsaye dakinsa ya fa'da
jim ka'dan na ji yana fa'din"Asiya Toro".
Kamar bazan amsa ba, sai kuma na amsa d'in tare da ajiye aikin na nufi inda ya ke.
Daga ba'kin k'ofa na ci burki a dalilin yadda kuka yake neman k'wace mini.
Ganinsa na yi yana cin masa da k'uli k'uli ga kunun gyad'a a leda yana zuk'a.
A tausashe ya ce "Samo abu ki diba idan zaki ci".
Na rasa inda zan saka raina, da ba'kin cikinsa.
Murya na rawa na ce "Dama ka katse mini barci dan kawai ka saka ni aikin da ba ci
zaka yi ba?"
Cikin rashin damuwar komai ya ce "Ci zan yi mana".
Na kasa bu'de baki na ce uffan, na juya ina jin tamkar na yi ta rusa ihu da
kururuwa.
Kirjina ya yi nauyi ainun. Na dinga hawaye ina share wa. Tsawon lokaci ina zaune
akan barandar nan, na kasa cigaba da aikin.
Ya fito da ledar ya kai shara. Ya wanke hannunsa, ya kalle ni ya ce "Sai na dawo
Asiya Toro".
Ko kallonsa ban yi ba, bare na tanka masa.
Shima bai tsaya ba, yasa kai ya fice.
Na dinga kuka tamkar dukana ya yi.
Yini na yi akan barandar nan. Ina kaico da auren Bulkachuwa.
Sallah kawai nake tashi na yi.
Sai da na yi sallar la'asar yunwa ta uzzira mini.
Na ha'da shayi mai kauri na kwankwada.
Ina kallon doyar da ya bar mini bai ko taba ba, amma ban ci ba.
Sai bayan isha sosai ya shigo. Hakan ba karamin sake fusata ni ya yi ba.
Ina zaune a dakina ido ya yi jawur, ya kumbure saboda kukan dana yini ina yi.
Da azama ya iso gare ni yana fa'din "Asiya Toro me ya same ki, kin ga yadda kika
zabge kuwa? Ga idon ki tamkar mai fama da matsanancin ciwon apolo. Mene ne yake
damun ki?"
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA
KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA
KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
Da zafin rai na ce "Kai ne ka fitine ni, irin fitinar da ko maki'yata bana fatan a
fitine ta irin haka."
Na sake rushe wa da kuka tamkar an fa'da mini mutuwar mahaifina.
Ya ki'dima ya ce "Me na yi miki? Fa'da mini dan Allah".
Takaicinsa ya nemi sark'e mini numfashi. Na kasa magana illah hawaye da yake zuba
tamkar famfo.
Tsawon lokaci ya yi shiru yana sauraron shesshekar kukana.
A sanyaye ya mike, murya babu amo ya ce "ki k'arantawa kan ki k'iyayya ta Asiya!
Bai kamata ki kuntata wa zuciyoyinmu irin haka ba.
Ki cigaba da addu'a da sannu komai zai wuce."
Har ya kai bakin kofa ya ce "kin ci abinci kuwa?"
Cikin fishi na ce "Bazan sake cin abinci ba, sai yunwa ta mayar da ni gawa In sha
Allah!
Ya girgiza kai ya ce "Babu laifi".
Maimakon ya yi kwanciyarsa sai na ji yana ta buruntu a kicin.
Shude war mintina talatin sai ga shi da bowl yana fa'din "Ki dubi Allah da ma'aiki
ki tashi ki ci, ba dan ni Tijjani ba. Dan Allah".
Na sassauta kukan domin Gwaggo ta cusa mana yin uzziri matu'kar aka ce saboda
Allah.
Ya zauna kusa da ni sosai ya miko mini.
Cikin rarrashi ya ce "Allah ka yarda da Asiya, ka sata cikin bayin da ka yarda da
su".
Jikina ya yi sanyi.
Na kar'ba, na fara cin indomien da ta yi da'di tamkar ba girkin namiji ba.
Ni da nake fa'din bazan ci ba, sai gashi na share ta tas. Da hanzari ya karbi
kwanon ya mik'o mini ruwan hannunsa mai rangwamen sanyi.
Take na nemi jirin da nake ji na rasa.
Na yi gyatsa. Sai kawai na gayra na kwanta. A hankali ya ce "da kin daure kin dan
yi tattaki kafin ki kwanta".
Ban kula shi ba, a haka barci ya sure ni.
Bansan sadda ya tafi nasa makwancin ba.
Washagari mirsisi na k'i yin abin kari.
Bai matsa mini ba. Ya siyo kosai da kunu ya kawo mini.
Kwanaki suka yi ta shud'e wa, har na samu sati a gidan aurena.
Har lokacin kuma ban yarda na sake d'ora tukunya ba.
Shi kuma ko ya yi fishi, ba ya jure ganina ban ci abinci ba. Kan dole sai ya nemo
mini.
Ranar da na cika kwanaki goma ya fara gazawa da al'amarina. Ga shi ku'din hannunsa
sun tasar ma

Please Login or Register in order to submit comment