You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da cewa gaba'daya ma auren naku wata shad'aya ne fa
Yabi. Sannan shekarunki shabakwai. Ban da an miki auren wuri ai har yanzu baki isa
auren ba, bare aje ga zancen haihuwa. Wadanda suka zarce shekaru goma babu haihuwa
fa sai su ce da Ubangiji me? Ki shiga a hankalin ki fa".
Sai da ta shawo kaina sannan muka fita cikin jama'a.
Watanni uku bayan haihuwar Ubaida mai gidan burodi da Tijjani yake zuwa ya rasu.
Magada sun yi yawa a kai dan hakan suka siyar da shi. Wanda ya siya kuwa kabila ne
dan haka ya sallami galibin ma'aikatan ya debo nasa y'anuwan ya zuba.
Cikin wadanda aka sallama kuwa har da Tijjani. Ban gane aikin da burodin da yake yi
rufin asiri ne mai yawa ba, sai bayan an rasa shi. Domin ba'a dauki kwanankin sati
ba sai da muka ga gurbinsa. A da bamu da matsalar abin karya wa tunda burodi har
yawa yake yi mana. Ga kuma donougt da ita ma bata yanke mana. Ko baki na yi zan
basu. Sannan da daddare ba kasafai muke cin abinci ba, sai kawai muci da shayi mu
yi kwanciyarmu.
Sannu a hankali rashin samun ku'di ya dabaibaye shi k'warai da gaske. Tunda aikin
saka tiles sai an samu. Haka na satellite shima hab'o ne.
Tsawon wata biyu muna cikin wannan yanayin. Ga shi ya k'i yarda na taimake shi,
tunda ni kullum kasuwancina tamkar ba iya mutane ne suke zuwa mini kitso da lalle
ba. Saboda yadda Ubangiji ya ba ni jama'a.
Tunda kayan abincinmu suka k'are kullum cikin dirka mana garin rogo ko wainar
fulawa yake.
Tausayi yake ba ni saboda gaba'daya ya zama desperate kullum cikin yawon neman abin
da zai yi yake. Wani lokacin na ga ya fita da takardunsa, wani lokacin idan ya fita
tun safe sai azahar zai dawo, haka kuma yake dawowa sai dai na gan shi da garin
rogo da siga a leda. Ni kuwa sai ya bani filawa a farar leda ya ce ki yi abin da
zai samu da ita, ki mini hakuri dan Allah"
Rannan na gaji da bin ra'ayinsa muna kwana da yini cikin yunwa.
Na ha'da kan ku'din da na samu na kwanaki biyu na rubuta koamai da nake bu'kata a
takarda na bawa almaajirina na ce ya je ya ce nawa ne kudinsu. Jimawa ka'dan ya
dawo ya ce "Wai dubu sha bakwai da dari shida".
Na kirga na ga har da canjn dubu uku ya rage mini.
Dan haka na cire canjin na ba shi ya tafi ya karbo mini.
Na duba na ga komai ya cika. Na kinkima na kai kicin na shiryasu.
Na ba shi gudar dubu akan ya siyo mini gawayi rabin buhu, da kuma danyar kubewa.
Domin na tsani siyan abu dan tsurut a leda kullum. Ina da gas amma na bar shi sai
iya da safe zamu dinga amfani da shi.
Ya siyo mini bushasshe kuma manya dan jos haka ma kubewar. Na ce "To je ka dawo
anjima ka'dan."
A lokacin kuwa yammaci ne sosai. Dan haka na ha'da wuta na dora tuwon garin masara
wanda yana cikin siyayyar da na yi d'azun.
Na gama na kwashe na mayar da miya. Magariba tana yi ina kammala wa.
Sai da na yi sallah, na yi wanka sannan almajirin ya dawo. Na zuba masa ya tafi.
Sai ga Tijjani ya dawo. Ya kalle ni na ci kwalliya ko'ina kamshi ke tashi. Ya kalle
ni da alamun tausayi ya ce "Sannu da gida. Ya mik'o mini ledar hannunsa wacce awara
ce. Na kar'ba tare da godiya.
Na tashi na gabatar mana da abinci, na zuba mana a plate guda.
Na ce "Bismillah".
Ya girgiza kai ya ce "Na gode".
Na zuba masa ido murya na rawa na ce "Ba zaka ci ba, bayan na tabbatar da yunwa a
tare da kai!
Da rauni sosai ya ce "Ni ni ne mai ciyar da ke, ba wai na zauna ki ciyar da mu ba".
Na tashi na koma kusa da shi na ru'ko dukkan hannuwansa na sassauta murya na ce "Ba
ciyar da mu zan yi ba. Ubangiji zai buda maka k'ofofin da zaka samu ka sauke nauyin
rik'on iyali tunda shi ya wajaba maka. Kana kuma da niyyar yi d'in. Abin da nake so
ka fahimta ko aure bai ha'da mu ba, ai jini ya ha'damu. Ko ina wani gidan idan ina
da ikon kula wa da iyalinka ai zan yi, bare kuma ni ce iyalin naka, to mene ne
amfanin sana'ar da ka bar ni nake yi alhalin ba zata yi maka rana ba?"
Ya yi shiru bai ce komai ba, na sake sassauta murya na ce "Dan Allah ka yarje mini
na yi iya abin da zan iya yi".
Ya saki gauron numfashi ya ce "Idan na amince ya tabbata dai da aka ce ke ce zaki
ciyar da mu Asiya. Shike nan zan rasa yancina na mai gida, shike nan zan zama mata,
ke ki zama mijin".
Ya fa'da murya na rawa ainun.
Na durk'ushe a gabansa na ce "Wallahi ba zaka zama ba. Yadda muke hakan zamu cigaba
da tafiya kai ne miji. Ni ce mata, zan dinga karban umarni daga gare ka, abin da
kake so hakan za'a yi.".
Ya yi shiru yana nazari bai ce komai ba.
Na matse hannunsa na ce "Pls mana" cikin sigar shagwaba.
Ya zuba mini idonsa da ya kad'a sosai ya ce "Asiya zuciyata ba zata nutsu ace kina
siya mini abinci a gidan nan ba. Gara dai ki bari na dinga baki abin da aka yassare
mini, idan ma zaki kara da abin da kike so to bazan hana ki ba, tunda ban wadatar
da ke ba. Amma ni kada ki yi da ni. In sha Allah ko da bashi ne dai bazan kasa baki
abin da zaki saka wa ba'kin salatinki ba. Sai idan kin raina".
Na kalle shi na gane da gaske yake yi.
Na yi k'asa da murya na ce "Anya kasan kalubalen da yake tare da cin bashi kuwa
mussaman a waje? Kawai ka yi hakuri tunda dai Ubangiji ya baka matar da ya bata
sana'ar hannu mai k'arfi. Ina fatan Ubangiji ya kawo maka aiki ko sana'ar da zaka
dogara da ita."
Ya girgiza kai tabbacin bai gamsu ba.
Na ce "To shike nan ka dinga karban bashin a wajena."
Ya gyara zama ya ce "Nawa kika kashe a hidimar tuwon?"
Na ce "mu je kicin a lissafa.
Ya mike muka je. Na nuna masa komai da aka siyo wanda a k'alla zamu kai wata muna
ci a talau ce.
"Nawa kika kashe a wannan siyayyar?
Na ce dubu sha bakwai da dari shida na. Sai gawayi na dubu daya."
Ya ce "To kub'ewar fa?"
Na ce "A bar wannan".
Ya girgiza kai.
Da sauri na ce "Ta naira dari ce."
Ya ce "Sha takwas da dari bakwai ke nan ko?"
Na ce "Eh" ya ce "In sha Allah zan biya ki, matu'kar ina shakar numfashi."
Muka koma falon muka ci abinci ina ta yi masa hira dan ya ware sosai.
Wannan kayan abincin da muke da shi sai ya rage masa damuwa mai yawa. Duk da hakan
kuma bai yarda ya zauna a gida ba. Kullum sai ya fita. Rannan ya yi sa'a ya samu
hada saltelite har gida uku. Da k'arfinsa ya dawo ya mik'o mini dubu biyar ya ce
"Ga shi, na rage miki bashin ki. Ya fita ya dawo da leda mai d'auke da soyayyen
kifi.
Na kar'ba tare da addu'ar Allah ya kara budi.
A wannan tsukun gaba'daya a takure nake domin maimakon na samu ninkin tattalin da
yake yi mini kafin mu shiga tsananin da muke ciki. Sai ya zamana ni ce nafi rawar
kai a kansa domin dai na samar masa nutsuwar shine mijin. Tunda na lura yana kame
wa ne dan kada na samu dama a kansa. Na dinga mamakinsa domin gaba'daya ban yi
zaton zai mini kallon zan raina shi dan ya shiga halin babu ba.
Ya takura kansa sosai, komai kaffa kaffa yake yi.
Idan na yi kamar zan yi masa magana sai na ha'diye.
Na dinga hakuri ina lallabawa ina binsa a hankali.
Hidimar da ta karu a kaina sai ya zama ina ta kokarin fa'dada kasuwancina. A
dalilin an kawo wa Tijjani takardar biyan ku'din gida tun kwanakin baya.
Na fara tunanin yin Home service domin na samu na tara masa ku'din kafin lokacin da
suka diba mana ya cika.
Na kalli yatsun hannuna guda biyu gold ne. Daya na wajen kwamishina ne, dayan kuwa
da sana'ar tawa na siya.
Jiya na bashi daya na ce ya siyar ya biya ku'din ya ce "Ba ya so, kada na sake na
siyar da kadarata akan al'amarin da ba hakkina ba ne. Idan kuma na siyar to ba zai
karba ba.
Da zai fita na tambaye shi zan fita, zan je bayan layinmu. Bai hana ba.
Tunda na fita da hantsi ban dawo ba sai yamma lis tunda asabar ce ban cika samun
k'unshi a ranar ba sai kitso.
Na dawo na tarar da shi a gida. Ya gyara ko ina.
A falo na tarar da shi yana kallo. Na yi masa murmushi ya mayar mini a gajarce. Ya
kalle ni ya ce "Daga ina kike na ji sai k'amshin muhallibiya kike yi"
Zuciyata daya na ce "Wallahi lalle na yiwa wata babbar mace da ahalinta zasu je
biki Abuja.
Na fito da kudina dubu sha biyar na ajiye masa na ce "Idan Allah ya yarda a satin
nan zamu ha'da ku'din da zaka biya gidan".
Ya zuba mini ido galala sai kuma ya kad'a kansa ya ce "Babu laifi".
Ni ban kawo komai ba. Na tashi na yi kicin da nufin dora girki. Sai na tarar da ya
girka ya juye a flask. Ga shi ya mayar da ruwan wanka kan gawayin. Na bu'de na ga
ya yi zafi ainun. Na dauko babban flask din da nake zuba ruwan zafi na cika shi. Na
ajiye sannan na juye ragowar na shiga wankan.
Sai da na shirya na ha'da Mana abincin na kai ina cewa "Yau dai ka zama Yabi, na
dawo na tarar ka yi komai sannu da kokari".
Ya sake yi mini wani irin kallon da ban gane ma'anarsa ba.
Duk da dai yanzu ya canja amma ba musguna mini yake ba, kawai walwala da sukuninsa
ne suka ragu, sannan yana yawan yi mini abubuwan da suke kona mini rai ta hanyar
shata layi da abin hannuna.
Na kalle shi na ce "Sauko mu ci to".
Ya girgiza kai ya ce"ci, ni ba yanzu zan ci ba".
Na marairaice na ce"To zo ka dinga bani a baki na gaji sosai Wallahi".
Ya sake kafe ni da kallon da yafi wadanda ya yi mini. Bai kuma ce komai ba. Na rasa
gane manufar hakan sai kawai na fashe masa da kuka mai tsananin gaske.
Ya taso ya zauna kusa da ni ya ce "Me na yi miki zaki yi mini irin wannan kukan?"
Da kuka sosai na ce "To akan me zaka dinga yi mini kallon tuhuma? Akan me ba zaka
zo mu ci abinci tare ba? Na riga da na gane ka tunda ka fahimci na fara sonka
shikenan ka nade kafar wando fara yi mini wula'kanci kala kala".
Ya matso jikina sosai ya kwantar da ni a kirjinsa ya ce "Da gaske kina sona Asiya?"
Na ture shi na zum'bura baki na juyar da fuska gefe.
Na kasa bu'de baki na ce uffan.
Ya saki gauron numfashi ya ce "Shikenan na daina yi miki wula'kanci, duk da nasan
ba na yi din".
Da kansa ya zuba mana abincin. Lokaci zuwa lokaci kuma zai debo ya bani a baki. Ko
ruwa da ya bula ledar bai sha ba, bakina ya nufa da shi. Na zuke tas na bar masa
leda a hannu. Sai wani ya bu'de.
Da yake ina siyar da pure water, saboda masu zuwa lalle kawia na tsiri siyar wa
kuma sai nake yin ciniki sosai.
Na yi gyatsa "Na yi hamdala. Gaba'daya sai jikina ya mutu murus gajiya ta taso
mini, ba abin da nake so irin na kwanta na yi barci. Ga shi maghariba ta kawo kai.
Na kalli agogo na ga za'a kai minitina arba'in da biyar kafin a kira sallah.
Na mik'e na kwashe kwanukan, na hau zaga tsakar gida dan abincin da na ci ya dai-
daita. Na koma falon na kwanta a kujera na yi daidai iskar fanka na kad'a ni. Ya
taso ya fara bin gabbobina yana dannawa sannu a hankali nake jin da'di a jikina.
Ban ankara ba sai kawai ya sure ni yana cewa "mu je daki na wartsake miki gajiyar
gaba'daya. Na fara shure shure shi kuma ya ri'ke ni gam. Fadi nake yi "No bazan
yarda ka dora mini wata gajiyar ba gaskiya".
A kunne ya ce "Amma kinsan na ce idan kina yin gardama komin kankantar ta cikin ba
shiga zai yi ba".
Nan da nan kuwa na yi muk'us domin har zuciyata so nake na ganni da ciki, so nake
na ganni da baby a hannuna kamar yadda nake ganin su Ubaida.
Har aka fara kiran sallar Bai samu nutsuwa ba. Kan dole ya tsallake ya bar ni. A
gurguje ya yi wanka ya nufi masallaci.
Ni kaina a dole na sake wanka na sauke farali.
Yau da wuri muka kwanta domin ana idar da sallar isha da ya shigo ya rufe gidan, ni
dama a kwance ya tarar da ni. Sai da ya karasa abin da bai ida ba sannan muka yi
wanka, muka kwanta wajen tara da rabi. Washagari lafiya muka rabu, da zai fita na
ce "Idan fita ta kama ni zan fita. Bai ce komai ba, ni kuma ban yi zaton bai amince
ba.
Da yake na dora cewar na fara Home service akan status dina. Sai kuwa na dinga
samun k'ira akan ana bu'kata ta a wuri kaza.
Na za'bi gida biyu, na bawa guda biyu hakuri akan wasu sun rigasu.
Na kammala gyaran gidan tsab.
Na fice. Wannan ranar har dare sannan na koma gida. A k'ofar gidan na tarar da shi,
cikin wani irin yanayi. Yana ganina ya zabura ya mik'e.
Ni kuma ganin a waje muke yasa na zarta shi na shige. Sai kawai na tarar da k'ofar
tamu da sabon kwad'o.
Na jinkirta amma bai shigo ba. Na gaji da tsayuwar jiransa. Na fara hassala ya gan
ni amma ya kasa shigowa, yasan kuma ya canja kwad'o.
Na gaji na fita na tarar da shi yana zaune tamkar dutse ko motsi ba ya yi.
Na ce "K'ofar a rufe take fa".
Ko kala bai ce ba.
Na sake fusata. Na ce "Ka zo ka bu'de mini".
Nan ma tamkar da Dutse nake magana.
Allah yasa ma babu kowa a wajen. Zuciyata ta hauro matu'ka da gaske. Duk fa'din
tashin da nake yi dan asirinsa ya rufu shi bai ga hakan ba. Murya na rawa na ce "Ni
kake yiwa wula'kanci haka?"
A fusace ya ce "Wace ce ke? Gida ne bana bu'katar ki a cikinsa ba, ba sai ki koma
inda kika fito ba, kin ga kin yi maganin wula'kancina, nima na huta da rainin da
kike yi mini".
Jikina ya yi matu'kar sanyi, hawaye ya b'alle mini. Murya na rawa na ce yanzu a
daren kake so na tafi gida?"
Shima murya na rawa ya ce "Ai ni a daren kika dawo mini gida. Dan haka ki koma inda
kika fito ko ki je inda zaki, ai dai babu sisin ki wajen kama gidan har yanzu, bare
ki yi mini sabon isgilanci".
Na fara kuka na ce "Na rantse da Allah Tijjani kai bahago ne na k'arshe. Duk
tunanina mu ha'du mu rufawa kanmu asiri wani bai ji ko ba'a gane halin da muke ciki
ba, amma gaba'daya ka murde ka canja, ka ki da'din azanci. Dan Allah ka fahimce ni,
nifa ba jin da'din yadda kake yi nake ji ba".
A tunzure ya ce "Yo dama ni ina da abin da zan jiyar da ke da'di ne?"
Na yi sakare ina kallonsa gaba'daya ya juye ya koma wani azababben mutum.
A hankali na ce "To zo ka bu'de mini, tunda dare ya yi."
Ya girgiza kai ya ce "bana son ganin ki a cikinsa."
Na juya na ce "Shike nan na gode".
Na fara tafiya ni kad'ai ga shi wajen ba kowa, tsoro ya kama ni, da na ji kamar ana
bina. Sai da muka iso wajen hasken solar na juya sai na ga shi ne yake bin bayana.
Na tsaya na ce "To mene ne kuma, ba dai ka kore ni ba?"
Da sanyin murya ya ce "Bakin titi zan raka ki, kada karnu ka su biki".
A tunzure na ce "Allah yasa ma kuraye su kama ni, su cinye ni!
Bai ce komai ba, har muka isa inda zan bi na yi gida. Na kalle shi na ce "Yanzu me
kake so na fa'dawa Baban Marina?"
Kai tsaye ya ce "ki fa'da masa gaskiyar abin da ya faru kawai".
Na marairaice na ce "Tunda har ka rako ni nan, nasan ka huce, mu koma gida ka fa'da
mini abin da na yi, ba sai ka ce na baka hakuri ba, zan nemi afuwarka".
Ya girgiza kai ya ce "A a bana bu'katar ki a gidan ne, ki je gida, ko ki je ki
kwana a wajen neman ku'din ki".
Ganin zai sake tunzura da yawa yasa na tafi din. Amma tafiya kawai nake yi, bana ko
sanin inda zan jefa k'afata. Tashin hankalina ace na je gidan Marina da sunan bacin
rai. Na sani masu murnar ganina sai sun fi masu yin jajjabi yawa. Kuka nake yi
sosai. Me zan cewa Baba da Gwaggo ni Yabi? Ko Ubaida k'aramarmu ba'a taba tura ta
gida da sunan ta yi laifi ba sai ni? Ni kuwa dama akuyata ta yi shura.
Ina ganin hanyar da zan bi na isa gidan, amma sai na bi wanda zata kai ni gidan
Yaya Ummi.
K'arfe tara da rabi na shiga d'akinta tamkar jifa. Cikin sa'a mijinta ya je Jos
d'aurin auren yar kaninsa sai gobe litinin zai dawo.
Ganina a wannan daren ga kuka ina yi, duk sai ta diriri ce ta dinga fa'din mene ne,
daga ina kike?"
Ina kuka, na fa'da mata Tijjani ne ya ce "Bazan shigar masa gida ba."
Ta dauki salati ta ce "To ke da ina kika je?"
Na fa'da mata gaskiya.
Ta yi shiru ta ce "Tsakani da Àllah laifinki ne Yabi. Tunda bai amsa miki ba, ai
kinsan ba wai yana so ba ne. Sannan me yasa kika yi dare har wajen tara?"
Na yi shiru sai kuka kawai nake yi. Domin tskani da Allah ban san ina son Tijjani
sosai ba sai yanzu da ya yi min irin wannan hukuncin. Ji nake kamar na yi ta
zunduma ihu har kowa ya fahimci rad'ad'in da nake ji. Baya ga haka kuma fishin da
na ga ni shinfide a kan fuskarsa ya sake dagula mini lissafi.
Cikin kuka na ce "Ni bana son na je gida Yaya Ummi. Baba fishi zai yi da ni, haka
ma Gwaggo. Ga magauta su tasa mu gaba da dariya da zunde".
Ta nisa ta dauki k'aramar wayarta ta ce "ku'din ciki babu yawa, amma bari na gwada
na ga ni.
Bugun farko ya dauka tamkar me jira a k'ira shi.
Ta gaishe shi da walwala.
Sai kuma ta ce "Yaya Bulkachuwa sai ga Yabi ta zo mini a wannan daren, kuma abin
mamaki ta ce wai kai ne da kanka ka koreta, ai da sai ka yi hakuri da safe ka tura
ta gidan."
Dake a sifika ta saka sai na ji ya ce "Na kasa yin wannan tsinkayen Ummilolo. Amma
yanzu taimake ni ta kwana a gidan ki, gobe sai ta wuce gida".
Da sauri ta ce "A a kasan ni dakina daya ne. Zan dai rako ta, ko mene ne da safe
zan dawo mu tattauna tunda dare ya fara yi".
Ya yi shiru tabbacin bai gamsu ba.
"Ka yi shiru Yaya Bulkachuwa".
Ya ja gauron numfashi ya ce "Kunyar ki nake ji ne Ummilolo. Kada ki shiga wannan
maganar. Ba ke ce zaki yi alkalancin nan ba. Domin ban dauki al'amarin da sau'ki
ba".
Ta sassauta ta ce "Ai tunda na gan ta na sani baka dauke shi da wasa ba. Amma tunda
na yi maka waya ai sai ka mini lamini tunda ni da kai ai kasan tun fil'azal bata
b'aci."
Ya ce "To shike nan".
Da walwala ta ce"Yauwa Yaya Bulkachuwa rabin raina na gode".
Daidai lokacin kuma ku'din wayarta ya k'are. Ta ce "Ai bu'kata ta biya."
Kafin ta yi mini magana, sai ga shi ya biyo bayanta. Tana dauka ya ce "Yi zaman ki
Ummi ai ba zai yiwu ki fito b'akatatan a wannan lokacin ba. Bari na wakilce ki, na
zo da kaina. Amma ki fa'da wa mijinki gobe, ki zo mu zauna".
Ta ce "Na kuwa gode! Gobe da ikon Ubangiji da wuri zan zo".
Ya ce "Na gode, ki gaida yaran namu".
Ba a wani dauki lokaci mai yawa ba, sai ga shi ya k'ira ya ce ya zo.
Ta raka ni har soron gidan sannan ta juya tunda k'ofar gidan nasu tamkar kasuwa
yake shaguna ne reras gefe kuma teburan masu sayar da nama na gaba kuma masu kayan
miya.
A mashin dinsa ya zo. Na haye ba tare da na ce komai ba.

*End of part 2.*

*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta
sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar
taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi
muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun
san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa,
mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai
soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan
littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan
numbers*
*08089965176*
*07084653262*

*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA
BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES.*

*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.

*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta
sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar
taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi
muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun
san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa,
mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai
soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan
littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan
numbers*
*08089965176*
*07084653262*


Har muka isa gidan ba wanda ya yi magana.
Kai tsaye daki ya shige ya yi kwanciyarsa. Ni kuma na shiga kicin na sama wa kaina
abin da zan ci. Sannan na yi wanka. Na gyara jikina sosai, na isa dakin na tsaya
gaban madubi na bi ko ina na goga turare.
Na tarar da shi idon sa biyu. Na zauna na tausasa murya na ce "Fa'da mini abin da
na yi, mu shirya kafin Yaya Ummi ta zo".
Ko motsi bai yi ba, bare ya yi magana.
Na zuba masa ido ina tuna yadda yake rawar jiki da tsoron fishina. Amma tunda ya
fahimci na fa'da komar sa shikenan abu ka'dan zai fitittike ya yi mini fishi.
Na kai hannu na fara shafa sumar kansa da nufin lallashi tunda na gane shi mutum ne
mai son a rarrashe shi tamkar mace.
Da kakkausar murya ya ce "Bari Asiya Toro".
Nan da nan kuwa na cire hannun nawa domin gargadi ya yi mini mai kauri.
Haka muka kwana duk rai babu da'di.
K'arfe takwas sai ga Yaya Ummi da alamu tare suka fito da yaranta yan makaranta su
suka wuce ita ta taho nan.
A falo muka zauna.
Ita ta fara ce wa Yaya Bulkachuwa ka ga yadda ka koma kuwa me yake faruwa ne?"
Ga mamakina yana bu'de baki sai ce wa ya yi "Ba'kin cikin Asiya ne yake neman
kassara ni".
Gabana ya takarkare ya fadi. Me nake yi masa ni Yabi?"
Yaya Ummi ta ce "me ya faru haka Yaya Bulkachuwa?"
Na kasa kunne sosai dan na fahimci abin da zai ce da kyau.
Sai ji na yi ya fara rattabo laifukan da nake yi.
Cikin nutsuwa ya ce "Ummi tunda aka rufe gidan burodi da nake zuwa na shiga yanayin
rashin ku'di. Har ta kai bana iya yin abin da ya kamata. A farko rimi rimi Asiya ta
ke ha'kuri da duk abin da zan kawo. Tare zata sarrafa mu ci, ko da garin kwakai ne.
Amma tafiyar bata yi nisa ba sai ta fara gazawa. Ta fara raina kokarina saboda an
riga an cusa mata akidar watarana ita ce zata rike mini gidan. Komai zan siyo na
bata ba zata yi amfani da shi ba. Kwanaki na siyo sabulun wanka Gif har yau bata
ta'ba ba, ta bayar an siyo mata wanda ya dace da ita.
Duk ban ce komai ba. Sai shekaranjiya kuma ta ce mini zata fita, ban zaci wai gida
gida zata dinga bi tamkar dilalliya ba. Tun safe da ta fita sai yamma lis ta dawo
wai ashe gida je ta dinga bi tana yin k'unshi ana biyanta saboda kawai ta fahimtar
da kowa ita ce take ri'ke da ni!
Ya nisa ya zarce da fa'din tana shigo wa ta tarar na yi komai Kamar yadda ta sani
tun farko ni aikin gida bai zame mini komai ba, amma kinsan me ta ce mini?"
Yaya Ummi ta girgiza kai cikin sanyin

Please Login or Register in order to submit comment