You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan kuma Allah bai shafe ta ba, ya raya ta
fa?"
Takaicinsa ya k'ume Baba ya kasa ce masa komai domin bai ta'ba zaton Yaya J zai iya
fada masa hakan ba tunda mutum ne mai biyayya, mai kuma gudun zuciya.
A sanyaye ya ce "Kowa ya ki fahimtar halin da nake ciki, me yasa zaka biyesu wajen
yin watsi da zumunci Baba?
Annabi cewa ya yi mu yiwa wanda basu yi mana ba".
A matu'kar zafafe Baban Marina ya ce "To dai ni ne uban Yabi! Ni kuma shari'a ta
girmama ta mayar a hakku ya za'ba mata miji, idan kuwa hakane, ko mutuwa ce ta
riske ni gabannin na aurar da ita da kaina. To waliyyinta baza su baka ita ba, bare
kuma ina fatan a ara mini dama na aurar da ita da kaina. Ka je ka yiwa Mahaifinka
biyayya, na gode sosai da soyayyarka. Mu cigaba da addu'a da sannu komai zai dai-
daita mana. Amma Yabi kam ba matarka ba ce".
Tsawon lokaci bai amsa ba. Ni dai daga sama na ji muryarsa yana cewa "Sai da safe
Baba".
Ajiyar zuciya mai nauyi na ji Gwaggo ta yi tare da cewa "Alhamdulillah! Ubangiji ka
sake nisanta wannan al'amarin kamar yadda ka nisanta gabas da yamma."
Na kasa magana, amma dai zuciyata ta yi nauyi, na kuma gamsu da gaske Yaya J yana
sona da dukkan zuciyarsa.
Gefe guda kuma ina gasgata tsinkayen Nazira da ta ce Baban Marina ma ba zai bashi
aurena ba.
Na k'udire bazan sake bari mu hadu ba, bare zuciyata ta dinga karaya a dalilin ta
so mini da soyayyarsa da nake ta kokarin danne wa da dukkan iya wa ta.
Washagari na tashi sukuku ba wanda ya tayar da maganar.
Da yamma sai ga kwamshina ya zo, sai da ya fara zuwa wajen Baban Marina a wajen
sana'arsa, ya sanar masa nan da kwanaki biyar zai zuro a yi maganar aure da saka
rana gaba'daya.
Shi yake fa'da mini hakan.
A wannan ranar ma kayan da ya kawo mini ba k'aramin yawa ne da su ba.
Tunda ga kan sutura, ga provisions tamkar wacce nake rike da kaina.
Sai kuma dalleliyar waya da zoben gold wai a matsayin tukuicin amincewa da shi.
Tuni Baba ya sallama ya bar ni ina rike waya.
Wadanccan ma da ya rike tuni ya fito mini da abina.
Dama k'ananu ne sai kawai na ce ya bawa iyayenmu mata tunda uku ne dama.
Ni bansan me yake faruwa ba, ashe Yaya J bai fasa sintiri a wajen Mahaifinsa da
Dada ba.
Da ya kasa samun tallafinsu, sai kawai ya doshi Baban kasuwa mahaifin Maijidda.
Nan ma fatattakarsa ya yi tare da alwashin idan mummunar k'addara ta afko aurenmu
ya tabbata, to kuwa ya kwana da sanin sai dai ya sako masa Maijidda.
Hankali ya fara tashi domin gaba'daya Yaya J ya susuce ya rasa nutsuwa har ta kai
Maijidda ta dawo gida a dalilin zaman nasu babu da'di sam, ita kuma ta gaza ha'diye
damuwa ta taho, da k'yar Dada ta mayar da ita.
Baban Marina da kansa ya fa'da wa Dada da yan'uwansa cewar ranar asabar za'a zo
neman auren Yabi, kada su yi nisa.
Daga Baban Tsakiya har na Kasuwa suka gabatar da uzzirin suna da daurin aure
muhimmi a wannan ranar.
A wannan karon hankalin Baban Marina ba k'aramin tashi ya yi da wula'kancin da suke
yi masa ba.
Ya gabatar da korafinsa gaban Dada cikin kankan da kai ya ce
"Ba zai yiwu na dauko wasu daga waje su marabci masu neman auren y'ata ba. Alhalin
ga y'anuwana ban da ransu da lafiyarsu, har wanne daurin aure zasu je da yafi
al'amarina muhimmanci Dada?
Ki shiga cikin wannan maganar, ina jin tsoron kada na kasa jurewa fa."
Ita da kanta ta sani ba'a kyautata masa ko ka'dan amma da yake bata iya tsawatar wa
wadanccan shiyasa bata iya magana, har komai ya rincab'e.
Da rashin walwala ta ce "Zamu zauna da daddare dukkanmu".
Da daddare kuwa dukkansu uku suka hadu a gaban mahaifiyarsu, a sanyaye take gabatar
da k'orafin da yayansu ya zo da shi.
Babu kunya dukkansu suka ce suna kan matsayarsu ba yadda za'a yi suna cikin
hankalinsu su jagoranci bawa mai saka d'agaggen wando aure, kema da za'a fito
k'arara a fa'da miki ainihin yadda ak'idarsa take da kin k'yamace lamarin wannan
mutumin. Mun yi shiru ne kawai dan kada ace hassada muke yi. Ko bamu da kirki, amma
waye a jahar nan bai san yadda Mustapha Zaki ya yi k'aurin suna wajen yiwa masu
akidar yin maulidi kafar ungulu ba.
Duk wani masallaci indai ba na yan kungiyarsa bane sai ya durkushe shi, ke kan ki
da yasan yadda kike son shehu da ya d'aure ki saboda zuciyarsa babu alheri."
Dada ta kad'u kwarai da gaske. Domin babban b'acin ranta a nemi ta'ba mata mutuncin
ra'ayinta. Ita din mai mai zazzafar akida ce akan hakan.
Ta fara tafa hannu tana cewa "Ashe hakane? Allah na gode maka da ka kubutar da
jinina fa'da wa hannun wanda zai yi mata sanadin rashin samun rabo ranar gobe".
Sai ta hau kuka tana sake godiya ga Allah da Annabi.
Jikin Baban Marina ya yi matu'kar yin sanyi ta yadda yan'uwansa suka shammace shi,
suka gabatar da hujjar da ba mai kankareta a zuciyar Mahaifiyarsu.
Ya tabbatar sun dade da kitsa maganar dan sun tabbatar auren ya rushe gaba'daya,
kuma wannan hanya ita ce mafi sau'ki da zasu ja hankali gyatumarsu ta lalata komai.
A zuciyarsa ya dinga ayyana shin wanne irin zamani muke ciki wanda dan-uwanka ma
baya son ya ganka a inuwa?
Me ya tare musu ne?
Shi ka'dai ne yake fuskantar irin wannan tsananin ko kuwa a ko wacce zuria ce?
"Allah kai ne mai zamani, a kawo mana mafita, da sassauci" ya fa'da a ransa.
Ya sake kallonsu, yana ganin sun hade sun bar shi daban, sai dai a zahiri ne suke
shiri a bad'ini kuwa ba wani taimakon juna a tsakaninsu, tunda kowa iya y'ay'an da
ya haifa ne dolensa. Sannan kowannensu boye wa dan-uwansa wadatarsa yake yi.
Ya sauke gauron numfashi kafin ya yi magana ya ji Dada tana fa'din "matu'kar ina da
iko akan ka ba za'a bashi aure ba, idan kuwa ka kafe sai dai na barka da Ubangijin
gizagizai ya bi mini kadina a wajenka".
A ki'dime ya ce "Har abada maganar ta mutu, Allah ya yanke mata wahala ya fito mata
da wani mafi alheri wanda za'a yi alfahari da shi".
Dada ta goge idonta tana fa'din "Ameen".
Baban Tsakiya kuwa ya ce "ai y'ar fariya ce , ba zata tsaya a matsayinta ba, dama
ya ta kasance? bare yanzu da wannan tsohon banzan ya sake kambaba burinta.
Ai idan ba tashi aka yi akan ta ba, sai ta tsofe tana gabanmu tana zuba d'ibar
albarka, ko yanzu tana ganin sakamakon hatsabibanci, tunda duk kintsatsse ba zai zo
wajenta ba.
Har yau ta k'i barin Jabir ya fuskanci matarsa sosai, da sun fara zama lafiya idan
har ya yi tozali da Yabi zai gigice.
Gashi kuma Maijidda matarsa ce, tunda cikine da ita, idan ba'a bashi aurenta da ake
ta munafurci ba, ta ya ya ake so wannan rabon ya bayyana?"
Baban kasuwa ya ce " Ai ha'kuri Muna cikinsa, amma sai ace mune da laifi, ban da
sha'anin jini tasirinsa yawa ne da shi ai wata shari'a sai a lahira kawai."
Dada ta ce "To ni kam ba zaku bar gun nan ba sai an samo wanda za'a ba shi auren
Yabi. Domin na fuskanci matsalar gidan nan tana 'damfare da ita."
Baban Tsakiya ya sake cafe wa da cewa "Kinsan dai ni da Iliya bamu da mutuncin da
zamu yi irin wannan ikon da ita, wannan maganarki ce da ubanta."
Cikin rawar murya irin ta sare wa da lamari Baban Marina ya ce "Yau muna watan
Safar ko Dada? To matu'kar rayuwata ta kai, watan jibi na gaban maulidi ke nan, zan
aurar da ita.
Domin ina da wadanda zan basu aurenta su kar'ba, sannan ita ma Ubangiji ya hore
mini ita zata ta yi mini biyayya.
Ubangiji kuma zai duba manufar kowa a nan ya cusa wa wanda zan ba shi auren ya
kar'ba da dukkan zuciyarsa".
Dada ta ce "Allah ya tabbatar ya nuna mana lokacin, amma ba za'a tashi ba sai ka
fadi wanene, d'an wacce haular ce? Gudun kada a sake kitso da kwarkwata."
Baban Tsakiya ya ce "yarinyar nan fa ta riga ta rik'a, idan aka kai ta wani wajen
ma mutuncin gidanmu zata zubar, me zai hana a lallaba a bawa wannan yaron kawai,
tunda shima yana da tambarin da aure zai yi masa wuyar samu wa?"
Baban Kasuwa ya ce "Ni ma tuntuni nake son na fa'di hakan, to amma ina jin tsoron
sharrin zuciyar da take raina alheri, yanzun nan sai a juya magana a ce da mugun
nufi aka yi kaza".
Dada ta ce"Ku yi magana sosai mana, ni duk kun saka ni a duhu ban gane wa kuke nufi
ba?"

Tirk'ashi
Karshen littafi na d'aya.

*Gaba'daya wadannan shafuka shimfida ne dan ku fahimci labarin da kyau, asalin
labarin da turka turkarsa yana littafi na biyu da na uku*
*Bisa soyayyar da kuke yiwa rubutuna ya sanya zan yi muku tsarin VIP.
*In Sha Allah babu jira.
*Babu posting ranar Lahadi*
*Sau biyu za'a yi posting a rana*.
*Ku zo mu yi tafiyar da babu nadama*
*Zaku dara, zaku koka, jikinku zai tsumu, zuciyoyinku zasu motsu. Tunani kuma zai
tafi cancanken me zai faru a gaba*.


*Marubuciyar HALIN YAU da SABO DA KAZA*
*Yanzu kuma alk'alaminta yana tafe da BAK'AR TA'ADAH*

*500regular page*
*VIP 1k twice pages*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim Dahiru*
*Zenith Bank*.
*Ko*
*7061488065*
*Surayya Dahiru Ibrahim.*
*Opay Bank.*

*08032773332.*


*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA
KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*07039269802


*Surayya Dee*
*Yar mutanan Gwaram*

✍️

*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE, BIYA KUDIN KARATUNKI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA
BAKAR TA'ADA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.

*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered,
Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan
farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon
yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
Cikin kasala irin wacce b'acin zuciya ke sababa wa, Baban Marina ya ce "waye kuke
ganin ba zai auru ba, tamkar Yabina! Wane ne shi?"
Hatta Dada jikinta ya yi lubus da Baban Marina ya ce Yabinsa a akan idon ta da na
y'anuwansa. Wanda hakan na alamta ce wa ya kai makura wajen kawaicin da yake yi
amma ba'a yi masa kara.
Daga Baban Tsakiya har na Kasuwa ba wanda ya iya cewa kanzil domin sun shiga yanayi
na jin nauyi da borin kunya.
Sun fahimci fishin da yake shinfid'e a fuskar yayan nasu ya tunbatsa.
Sai suka yi dabarar kame wa daga jaye jayen maganar.
Bai sake jiran komai ba, ya mike tare da yiwa Dada sallama ya fice.
Yana fita Baban Tsakiya ya ce "Muna cikin wani irin kalubale a wannan duniyar.
Ace ba dama ku tattauna da dan-uwanka ya fahimce ka, shike nan sai ya zama sanadin
tabarbare war al'amura?"
Ya yi k'wafa mai nuna takaicinsa muraran.
Baban Kasuwa yana bu'de baki sai ce wa ya yi "To ai irin wannan al'amarin wuya ne
da shi. Tuni Ubangiji yasan al'ummar Manzonsa zamu riski wannan zamanin shi yasa ya
saukar mana suratul Yusuf dan ta zama izina ga masu hassada da k'yashi. Ta kuma
zama gargadi ga masu hankali.
Wani abin kaicon ma mu babu y'an uba a cikinmu, amma babu yadda za'a yi a ha'du a
yi hira da walwala cikin farin-ciki saboda kawai ka fi mutum haske?
Gaskiya zan fa'da miki Dada.
Tunda ke kin isa da shi, ba wanda ya cancanci Yabi sai Tijjani, su rufa wa junansu
asiri, shine kuma zai iya biyar da ita, ya yi maganin shak'iyancinta".
Baban Tsakiya ya numfasa ya ce "Tunaninmu d'aya Iliya, sai dai ba lallai ne ya
amince ba.
Tunda duk iyashegenta bai yarda ja'irar yarinya ba ce. Zai yi wahalar gaske ya ba
shi tunda shi lalacewarsa ta bayyana a gida da dawa.
Ita kuwa mu na kusa ne muka fahimta kawai".
Dada ta saki ajiyar zuciya ta ce "Idan haka ta faru kuwa ina da yakinin mai sunan
manya zai nutsu domin komin ginshirarsa ba zai kushe ta ba.
Ubangiji ya kyautata halittarta, gata yar shawalwala da zata da'de tana cin
zamaninta".
Suka gintse fuska suna fa'din "Kyaun hali da tarbiya ai sune kyaun mace Dada."
Kawai dai ki sanya baki a ba shi ko ma sarara, domin idan shine mijinta zai karya
dukkan lagonta."
Basu tashi ba, sai da suka tabbatar ta gamsu bawa Bulkachuwa auren Yabi fa'ida ne
mai yawa a garesu bakid'aya.
Baban Tsakiya ya fi kambaba lamarin, a zuciyarsa kuwa so yake a yi a yi a auren ta
tunda kusan kullum sai ya yi mafarkin Jabir ya bijire masa ya aure ta.
Sun ki kwamishina ne dan kada haske ya shiga k'ofar dan-uwansu, tunda sun tabbatar
nagartacce ne, basa son ya'yansa su yi k'arfi.
Sun fi son a ce su da y'ay'ensu sune masu fa'da aji.
Auren Bulkachuwa kuwa sun san ba wani fiffika da y'ar iskar yarinyar nan zata yi
musu.
Tunda a bayyane yake matu'kar mace bata samu miji na gari ba to rayuwarta ta
na'kasa.
Washagari da sassafe Baban Marina ya yi sallamah ya ce ya tafi Azare.
***
Na fito sanye cikin uniform, na isa mashigar zauren Dada dan gaisuwa da kuma biya
wa Nasiba. Sai na ji magana k'asa kasa daga dakin Bulkachuwa.
Na kasa kunne dan na ji me yake fa'da.
"Bazan sake turo kowa gidanku ba Bilki. Na yarda ki na sona, amma kuma ai ba zaki
iya aurar da kanki ba, dole sai da wakilcin iyayen ki. Kema kin san ina sonki, amma
tabbas bazan sake turo kowa da zummar a nema mini aurenki ba".
Na yi fakare, jikina ya yi laushi akan abin da na ji.
Waton ba karamin son Bulkachuwa y'anmata suke yi ba.
Bansan me yasa shi kuma yake da jarumtar juya wa soyayya baya ba, matu'kar aka nemi
muzanta shi.
Na tsinci kaina da fa'din "Ina ma irin zuciyar Tijjani nake da ita?" Da tuni na yi
watsi da tunanin Jabir da soyayyarsa.
Amma ina! Har yanzu ina jin sonsa, kawai na danne ne dan babu yadda na iya.
Na shiga cikin gidan na tarar da Nasiba ta shirya.
Na gaida Dada kamar yadda na saba.
Sai dai amsa mini da ta yi, ya banbanta da sauran watannin baya. Domin tunda
kwamshina ya bayyana mini, da karsashi take amsa mini gaisuwa ta.
Amma a yau cikin wani irin yanayi da na kasa tantace wa.
Sai kuma ta zarce da fa'din "Wanda duk ya yiwa mahaifinsa biyayya ba zai tab'e ba.
Ina da tabbacin ko wuta na rura na ce da tsohonku ya shiga zai fa'da ne kawai babu
tambihi.
Ina rokonku ku dinga yi masa biyayya, ku yarda ya isa da ku, mussaman ke Yabi da
tun shekarar da kika iso duniya ya shiga cikin tala jaurar duniya".
Ta fa'da kuka na subuce mata.
Jikina ya mutu murus a dalilin kalamanta, tunanina ya shiga canke canken akwai
al'amarin da zai biyo bayan wannan jirwayen na Dada.
Muna tafe da Nasiba duk uban maganar da take yi mini akan Bulkachuwa na kasa ce
mata uffan.
A dalilin zuciyata ta riga ta baci da yadda Dada ta ce wai tunda na iso duniya
ubana ya fa'da cikin ibtila'i.
Na sani ba yau ake fa'da ba, Mama ta sha fa'da mini ni din tauraruwa mai wutsiya
ce, haka ma ya'yanta su Yaya Indo.
Tun ina damuwa har na zo abin ya daina damuna, domin Baban Marina bai ta'ba yi mini
wannan izgilancin ba.
Amma a yau sai na tsinci kaina da jin ciwon furucin Dada kwarai da aniya.
Na dinga hasashen me ya janye mini alfarmar da na a samu y'an watannin nan a
idonta?
A daren ranar Babanmu ya zaunar da ni da matansa ya fa'da mana aurena da Alhaji ba
zai yiwu ba, bisa wani dalili da bai bayyana mana shi ba.
Ya je shi da Alhaji Tanimu sun bashi ha'kuri. Ya gamsu sun yi masalaha, duk da ya
shiga rud'ani sosai.
Ya kuma ce ya yafe duk hidimar da ya yi.
Jikina ya mutu, zuciyata ta tsinke.
Na kasa bu'de baki na yi magana.
Ya sallami matansa suka bar ni da shi.

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA
BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWIA SAIWOWIN SANYI*
AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU*
*AKWIA SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*

Ya tausasa harshe har ya bani tausayi.
Ya ce "Yabi kinsan Nura dan wajen Babanku Tanimu?"
Na daga kai tabbacin eh.
Ya numfasa ya ce "Madallah! To zai zo ku gaisa, shi na za'ba miki ya zame miki
miji. Ubansa tuni yake ro'kon na ba shi ke ya bawa Nura, tunda ya samu labarin abin
da y'anuwana suka yi mini, ina ta bagarar da maganar. Saboda ganin Alhaji ya shigo
da k'arfinsa.
Amma a yau din nan na amince masa.
Ina ro'kon arziki Yabi, kada ki kunyata ni. Kinga shi namiji ma ubansa yana fa'da
masa ya amince da farin-ciki da walwala. Ki kwantar da hankalinki irin k'alubalen
da kike fuskanta da kananun shekarunki na alamta cewa zaki samu kyakkawar rayuwa a
gaba".
Hawaye taf a idona na ce "Na amince Baba! Allah ya sa hakan shine mafi alheri".
Ya amsa da ameen ikin farin-ciki mai yawa, tare da sanya mini albarka.
Ya sallame ni bakinsa dauke da addu'a a kaina da lamarina.
Ina shiga d'akin Gwaggo na fashe da kuka.
Ta ru'ko ni sosai ta dinga bani ha'kuri.
Wannan rarrashi da Gwaggo ta yi mini ya sanyayya mini zugin da nake ji a zuciyata.
Da na nutsu sai na fahimci ba kukan rabuwa da Kwamshina nake yi ba. Domin ba wani
sonsa nake ba, dama na yarda zan aure shi ne, dan na gaji da zaman Gidanmu. Sannan
Bulkachuwa ya kitsa mini cewar da na yi kukan takaici a gidan babu, gara na yi a
gidan wadata.
Amma sam babu soyayyar da zan yi ba'kin ciki irin haka.
Kawai ina kukan yadda al'amarina ya banbanta da na kowacce y'a a gidanmu ne.
Maganganun Gwaggo sun sake fahimtar da ni ita dama ba son aurena da Alhaji take yi
ba, ta yi shiru ne dan gara aurensa akan na Jabir.
Amma ta ce bata fasa addu'a ba, bata fasa nema mini zabin Allah ba.
Dan hakan kuma ya kasance sai ta gamsu Ubangiji ne ya amsa mata.
Kwanki biyu na warware tamkar komai bai faru ba, na cigaba da harkokina.
A yammacin wannan rana ta litinin mun taso daga Islamiya sai ga aike wai ana
sallamah da Yabi in ji Nuru Tanim.
Na dan diririce na kasa magana a dalilin yadda ya zamanantar da sunan na shi.
Na dinga canki canki wane ne Nura a y'ay'an, Baba Tanimu? Domin y'ay'an gidan yawa
ne da su, matasa sun kai bakwai ko wanne ya isa aure.
Na kasa cankar wane ne shi a cikin jerin matasan gidan.
Inna da kanta ta cewa yaron ya je ya ce "ina zuwa".
Hijabina har kasa na sanya, bayan Gwaggo ta matsa mini na shafa hoda.
Na fita cikin zullumin yadda zan gan shi. Tunda bani da sauran za'bi akan lamarin.
A babban zauren na hango shi sanye cikin shudiyar shadda sosai, kansa sanye da
hular da ta dace da kwalliyarsa.
Ko ka'dan ba shi da makusa, ya fi Yaya J cika, tsayi ne dai zasu yi taya.
Batki ne sosai, amma ma'abocin tsabta ne daga ga ni.
Take na ji abin da ya d'aure mini kirji ya fa'da mini domin ban ganshi a cikin
mummunan yanayi ba.
Baya aikin gwamnati, amma yana koyar wa a wata firame mai zaman kanta, boobies a
sannan yana da shagon caji da turin wakoki ko finafinai a wayar hannu.
Muka gaisa cikin yanayi na babu yabo, babu fallasa.
Muka yi shiru.
Tsawon lokaci kafin ya katse shirun ya ce "Asiya! Zuciyata ta harba domin har cikin
raina nafi son a ha'da mini da Yabi.
Na amsa a hankali da "Na'am".
Ya tausasa murya ya ce "Na da'de ina son ki, na sha fa'da wa Babanmu ya taimake ni
ya nema mini auren ki, sai ya bada hanzarin dan-uwanki ne yake son ki, ba zai yiwu
ya gabatar da maganata ba, tunda akwai nauyi a tsakaninsa da Baban nan gidan. Dan
haka ko da kika gan ni anan ba turo ni aka yi akan dole ko biyayya ba, dama ina son
ki tun ina zuwa makarantarku".
Na yi kasa da kaina ina sake samun nutsuwa mai yawa.
Ya sake sassauta wa ya ce "Idan har kina da matsala ko kina ganin ban yi dai-dai da
ra'ayinki ba, zan san yadda zan yi na zulle wa maganar ba tare da an ga laifinki
ba, domin al'amarin aure ba k'aramar tafiya ba ce da za'a yi ha'kurin dole a
cikinsa."
Na tsinci kaina da cewa "Babu damuwa Allah ya tabbatar mana da alheri".
Dadi ya kama shi, ya ce" kenan Asiya ta aminta da ni?"
Murya babu amo na ce "Yabi bata da burin yin fatali da burin iyayenta ko da ya ci
karo da nata ra'ayin."
Farin ciki ya sake lullube shi. Ya dinga fa'din ma sha Allah! Madallah da Yabi".
Na taya shi murmushi.
Ya ce "da alama kina son Yabi, ni kuma sai nake ganin karamci ne na kira ki da
Asiya."
Na cuna baki na ce "Tunda na riga na sami wannan falalar ta zuwa gabas, kawai ka
kira ni Yabi domin ina son sunan da dukkan zuciyata".
Ya murmusa ya ce "An gama Yabin Nuru".
Zuciyata ta tsinke yau ga abin da Yaya J ya guda, na jingina wa Yabinsa sunan wani
ba nasa ba.
Mun jima muna dan tattauna wa duk da shine yafi yin hirar sosai.
Ya ciro ku'di ya bani, na ki karba.
A sanyaye ya ce "Matu'kar baki karba ba, to alama ce ta ban samu karbu wa ba".
Jin hakan ya sanya na mik'a hannuna duka biyu na karb'a.
Daidai lokacin Bulkachuwa ya shigo a hargitse rigarsa daban haka ma wando daban duk
a yamutse. Da alamu ba nisa ya yi ba. Inda a ce d'an wanka ne sosai bansan irin
rubibinsa da za'a yi ba, tunda a hakan ma ba'a fasa sonsa ba.
Nura ya mika masa hannu suka gaisa ya wuce babu walwala nasan kuma yana taya
kwamshina kishi ne.
A lokacin na sake tabbatar da tsayi da cikar Bulkachuwa ya kai k'ure wa domin sai
na ga Nuru bai kai kafadarsa ba.
Daga haka muka yi sallamah ya tafi.
Na shiga gida ana kiran magariba.
Bayan mun idar da salla na bawa Gwaggo ku'din da ya bani sababbin yan dari biyar
guda goma cif.
Ta yi shiru sai kuma ta ce "Allah ka sawa al'amarin albarka, ya sa karshen
wahalarmu kenan".
Na amsa da Amin a zuciyata domin ni kaina na gaji da yadda komai yake kwace mini.
Gaba'daya shekaruna sha shida ne da ka'dan amma na gaji tunda al'adar auren wuri ne
a gidanmu.
Wai duk yadda nake da k'arancin shekarun nan, da yadda nake y'ar tsurut habaicin
rashin aurena a ke yi mini, ko a jefi Gwaggo da bak'ar magana.
Har ta kai bani da kalubalen da ya wuce zaman gidanmu a rayuwata.
Rayuwar gidanmu da ta gidan Yaya Ummi ta sanya na k'yamaci zaman babban gida. Wani
zaman idan an yi sa'a sai ya zama tsintsiya dan ha'din kai. Wani kuwa sai ya zama
tamkar sansanin yaki dan fitina.
Ta sake kallona ta ce "Nasan yaron dan wajen Sahura ne, yana da zuciyar neman na
kansa ga shi mai jin maganar iyaye ne, duk cikin matan gidan dakinta yafi na ko
wacce fasali da kayan jere mai kyau, kuma duk shi ne yake yi mata, shi ka'dai ne
namiji a d'akinta, y'ay'anta duk mata ne, amma da ya ke mai zuciya ne sai tafi mai
y'ay'a maza biyar gata da kyan ga ni, ta bar uwar maza je da fankamar ita ce da
gida.
Shikenan rabuwarmu da Kwamshina. Ya mini waya washagarin da Baba ya ce ya je Azare.
Ya fa'da mini yadda Baba ya je ya ba shi hakuri.
Ya fahimci Baba suka rabu cikin girma da arziki, tare da ro'kon idan auren ya zo a
sanar masa zai halarci dauri aure.
Nima ya mini maganganun masu taushi da nuna muhimmancin yiwa mahaifi biyayya.
Duk da ba wani sonsa nake yi ba, sai da na yi kukan yadda kalamansa suka dagargaza
ni. Kewarsa ta taso mini ba ka'dan ba.
Ya dinga rarrashi tare da tambayar me zai siya mini na kayan aure dan na yarda ya
gode da karamcin da na yi masa.
Na kasa cewa komai sai shine ya ce "Zan aiko miki da sako zuwa satin sama in sha
Allah"
Ya k'are maganarsa da fa'din "Allah ya sa ki shiga gidan auren a sa'a, Allah ya
zaunar da ke lafiya".
Bulkachuwa a bakin kwamshina ya ji maganar aurenmu ta ruguje.
Rannan da hantsi ya aiko yana kirana.
Zuciyata d'aya na je na tarar da shi

Please Login or Register in order to submit comment