You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani bawa a kusa da mu ya ce mana "Rai ya hadu da Gafarar Allah!"
Sai mai attishawa ya ce "Ya-hadi kumalle.
Idan kuwa zamu ci adda'ami.
Zamu fara da ambaton Allah. Idan koshi ya zo mana sai mu ce "Sawaba ta sauka akan
me nemo wa da mai dafa wa".
Dada ta murmusa tabbacin ta gamsu mun ri'ke karatun nata da kyau.
Ta ce "Madallah!". Cikin alfaharin muna da fikirar fahimtar karatun da take yi
mana.
Ta muskuta ta ce "yau karatun yiwa kai rigakafi daga shaidanu da makarai zan dora
muku".
Muka ha'da baki wajen fa'din "Mun gode Dadarmu, Allah ya kara miki nasibi.
Annabi yasan da ke".
Ta numfasa ta ce "Ameen, a kuma tsananta yi mini rokon dacewa da shiga cikin
masoyan SHEHU".
Na kasa jure wa na ce "Ashe Dada ba zaki bar zancen Shehu ba?
Kowa ya bar Allah da ma'aiki ai ya bar hanyar tsira."
Nan da Nan ta fusata ta ce "kaico da Yabi! Yabi ba zaki tsira ba, waya yake inkari
da jikan Manzo? Tabbas sai gafalalle".
Na ci je na sake ce wa, Annabi dai aka ce mu ri'ke ba waninsa ba Dada, iyalan
gidansa suna da girma da hakkin mu so su mu kare mutuncinsu.
Amma ba'a ce a kai su wani bigire da zai iya zama halaka ba.
Da kansa ya ce "Zan bar muku kura'ani da sunnata wato (Hadisansa) idan kuka bisu
kun tsira.
Amma ku kun shure komai, kun dauko shehu kuna neman mayar da shi abin bauta?".
Ai kuwa ta sake harzuka ta ce "Wahalar rayuwa akan ki Yabi! Mai gadon taurin rai da
kafiya, kaicon ki, kaicon ki! Da yi mini izgilanci Asiya".
Jikina ya sabe da rawa a dalilin ba irin jan kunnena da Gwaggo bata yi mini ba,
akan kada na sake na janyo abin da Dada zata dinga yi mini mugun fata. Ga shi ban
ji ba, na yi sanadin da take fatan na dauwama cikin wahalar rayuwa.
Kafin na ce komai sai ga Tijjani wanda mafi yawa an fi k'iransa da sunan garinsu
Bulkachuwa.
Wani irin zabgegen saurayi.
Dogon gaske har d'an rankwafa wa ya yi ka'dan.
Fari ne tas, irin fulanin Bulkachuwa, a murde yake, shi ba siriri ba, kuma ko
ka'dan baya cikin masu kiba.
Ga dogon hanci da ya k'awata doguwar fuskarsa.
Baya ga hakan manyan idanuwansa ka'dai sun isa abin burge wa.
Ban ta'ba ganin namiji mai jajayen lebe ba sai Tijjani kyakkawan gaske.
Wani irin mutum mai saurin fishi, da k'arfin zuciya.
Amma mai saurin saukowa da mantuwa.
Illarsa d'aya manemin mata ne, a yadda a ke fa'da. Na shaida kuma duk wata budurwa
ballagaza a Toro to kuwa budurwarsa ce ko kuma suna d'asa wa, shiyasa kowa yake jan
kunnen y'arsa a kansa, barin ma ni, kullum ne sai Gwaggo ta ce kada na sake na
bashi fuskar da zamu dinga doguwar magana.
Gaba'daya dabi'unsa na tantiran yan-iska ne, sannan k'azami ne, baya damuwa da yin
wanki sai kayansa sun k'are.
A hakan kuma shashan y'anmata suke sonsa, ko da yake baya yarda ya fita da dattin
sosai, yana wanke wa ya jira su bushe, guga ce sai ya samu ku'di, sai ya bayar da
kayan ma a wanko a gogo masa, amma da wahalar gaske ya yi guga da kansa.
Duk yadda Dada take kulafacinsa, matu'kar ya shigo muna nan sai sun haura da shi,
domin yafi kowa takalarmu da magana, yana yi yana lumshe ido ta yadda zai sure
zuciyoyinmu.
A hakan ya yi nasarar yin wuf da zuciyar Nasiba.
Idan Dada ta ga yana sakin maganganu ko lumshe ido a gabanmu ta dinga bagarar da
shi, ko ta tsiri aiken sa, ko kuma ta ce mu je ta sallame mu, duk yadda take sonsa
to bata son doguwar magana a tsakaninmu, kazalika kuma bata son a k'i gaishe shi.
Burgar da yake yiwa mata ya sanya har yanzu bai bar dauke dauke ba, komai ya gani
zai dauka ya siyar ya kashe wa budurwa ku'di. Amma iya kayan Dada yake dauka.
A duk sadda take yi masa fa'da kuma zai waske ya ce bashi ba ne, ko kuma sharri ta
yi masa, haka kuma sai ya d'auke mata wuta, har sai ta nemo shi ta bashi ha'kuri.
Bayan soyayyar da take yi masa, yana sake samun alfarma a wajenta saboda sunan
SHEHU ne da shi.
Kullum bakin ta akan ya nutsu ne, ya bar shiririta ya kawo matar aure, tunda ga
Yaya Salisu nan da yake sa'an sa tuni ya yi aurensa har matar ta haihu, amma shi ko
maganar aure baya yi saboda sharholiya da mutuwar zuciya.
Duk da k'arancin shekaruna ina tambayar kaina ko waye zai iya d'aukar y'arsa ya
bawa Bulkachuwa aurenta?
Tabbas sai idan yarinyar ta kasance shasha ce irinsa.
Na tabbatar mahaifiyar Nasiba ba zata ta'ba bari a bashi ita ba, domin kuwa kowa
nasa yake so, bare idan maganar gaskiya za'a yi bai cancanci a bashi ba, domin
bashi da sana'a, gashi manemin mata, shiyasa kowa yake masa kallon shasha.
A duk sadda Dada take yi masa fa'dan shigar da yake yi ta gajerun wanduna yana yawo
a gari babu kunya, ko tara suma ya gegareta daga gefe, ko kuma wani zubin ya sauya
launinta bayan ya mayar da ita cibiri cibiri.
"Akan kunnena na sha jin tana ce wa "Saboda bamu da mutunci a idonka shiyasa kake
iya zuwa gabana a hakan ko kuma gaban kawunanka".
Ba jin nauyi yake ce wa "Tunda nake yin sallah a hakan, ai kin ga bai zama aibu dan
kun gan ni a hakan ba. Domin Ubangijina ma a hakan yake gani na, kin takura mini fa
Tsohuwa"
Nan da nan ta zabura ta ce
"Imaninika ai a makogaro yake shi yasa kake hakan, amma da za'a jarrabe ka da son
wata yarinyar ba zaka yarda ka je mata a hakan ba. Alfarmar Shehu sai ka samu wacce
sonta zai hanaka yin wannan shakiyancin. Tunda ka ki daina wa saboda Allah da
Ma'aikinsa."
Dariyar iyashege yake yi ya ce "Ni da nake da y'anmata kamar jamfa a Jos suna bina
dan na so su, shine har son wata zai canja ni?
Lah! Ba dai Bulkachuwa ba".
Da wani kuma a Cikinmu ko a cikin samarin gidan matu'kar ba Yaya Anwar ba ne zai
saka musu baki, a take Dada zata nuna wa mutum shine bare a tsakaninsu.
Tana kuma sake kambaba shi da kawar masa da kai saboda alfarmar mai sunansa ne,
domin ko ta yi masa sababi, sai ta yi ta tuba tana kamun kafa da mai asalin sunan
akan a saka mata jikanta cikin shirayayyu. Hatta shi kansa dariya take bashi akan
yadda take tuba idan ta saki harshe a kansa.
Amma wani ikon Allah jarumi ne na gaske.
Idan na ce jarumi ina nufin zai tsaya ya fafata da kowa akan hakkinsa, matu'kar
kuma ya sanya kansa zai yi abu, to duk tsananin wahalar abin sai ya ga abin da ya
turewa buzu nad'i.
Baya ga hakan kuma tausayi ne da shi, duk zafinsa inda zai ga kana kuka to zaka ga
ya bar yi maka tijara.
Sai dai kallon marowa ci nake yi masa na gaske, ni dai ban ta'ba ganin ya yi kyauta
ba.
Ko garinsu ya je ya dawo, duk abin da zai samo ba dai ya kawo gidanmu ba. Amma
kullum a cikin karbe wa jama'a nasu yake, mussaman Dada da ko ta hana shi a k'arshe
take kasa juriyar ganinsa cikin rashin sukuni, sai kawai ta bashi.
Mazan gidan kuwa basa bashi duk irin yadda zai karyar da kai yana fa'din bashi da
lafiya, tunda suka gane matu'kar ku'di ya shiga hannunsa y'anmata banza yake kashe
wa, sai kowa ya kulle bakin aljihunsa dama kuma masu k'aramar niyya ne. Sai dai
gara shi ma suna bashi, amma da a ce wani ne cikin y'an k'ofarmu baza su bayar ba,
daman kuma bamu isa mu ce a bamu ba.
Haziki ne na sosai, kwarai da gaske yake ja, amma lalacewar da ya yi ya sanya da
k'yar ya iya kammala Diploma a kwalejin Tatari Ali data ke cikin Bauchi.
Ya riga su Yaya Salisu samun gurbin karatu a jami'ar amma yak'i mayar da hankalinsa
akan karatun har sai da aka kore shi. Hankalin mahaifinsa ya yi tashin gauron zabi,
domin zaryar da ya dinga yi tsakanin Bulkachuwa zuwa Toro ba ka'dan ba ce.
Haka ya sake samo masa yin diploma akan shaanin tsaro da tafiyar da gwamnati wanda
da k'yar ya kammala dan ma shekaru biyu ne.
A hakan kuma sakamakon ya yi kyau, domin ya wuce fallasa. Duk da hakan Babansu bai
bar shi ba, sai da ya sake samo masa gurbin karatun digiri a jamiar jahar Bauchi ta
garin Itas-gad'au. Inda zai karanci ilimin halayyar dan Adam. Wannan kam da taimkon
Ubangiji ya kammala domin ba ya zuwa sai an kusa fara jarrabawa, sannan bai fasa
al'amari da y'an mata ba.
Shekaru biyu da rasuwar mahaifinsa kenan. A kuma wannan shekarar ya tafi bautar
k'asa, da shekara ta dawo ya kammala. Yanzu zaman kashe wando kawai yake yi. Sai
dai yana yar buga bugarsa domin kusan kullum sai ya je Bauchi.
Haka ya dinga satar jiki yana siyar da kadarorin da ya mallaka. Abin kaico kuma ba
komai ya yi da kudin ba sai sharholiya da burga a mata.
Wani k'aton fili a Bauchi kawai ya tsira da shi, shima dan an zuba masa matakan
tsaro ne.
Yau da wata sana'a yake da ku'din ko kuma wani gini yake fa'da'da wa da an samu
sau'kin bacin ran da ake ciki.
Ya zauna kusa da Nazira da take kusa da karshen tabarmar.
Murya ba amo ya ce "Madallah da Dada da y'anmatantanta".
Duk suka hau rige rigen gaishe shi Amma ban da ni.
Ya amsa hankalinsa na kaina.
Ya kasa ha'kuri ya ce "Asiya Toro how far?".
Na yi banza da shi.
Domin dai na tsani yadda yake gatsa ainihin sunana, dan kuturun wula'kanci har sai
ya ha'da da Toro.
Kusan kowa Yaya Bulkachuwa yake ce masa, ni da bama shiri bana ce masa Yaya
Bulkachuwa.
Amma sai nake mutuntunta shi wajen kiransa da Yaya Tijjani amma bai yaba ba, bare
ya gode. Yabin da zai ce ne yake ganin asara saboda an cika zuciyarsa da k'yashi.
Shi yasa nima na janye yayan tuntuni nake gatsa Tijjani gatsal wanda na lura shi ko
oho.
Ina nan, ina kallon wadanda basa ce mini Yabi, duk ranar da Ubangiji ya sanya na je
Saudi akan girma da hankalina ko tsarabar abin da ba'a so ba zan basu ba.
Tijjani na cikin sahun farko.
Yaya Ummi ce mutumiyarsa, baya zuwa gidan kowa amma yana zuwa gidanta, har idan da
ku'di a tare da shi ya yi wa ya'yanta alheri. Sosai suke d'asawa, mutimiyarsa ce ta
sosai.
Dada ta fusata ta ce "Mugun nufi ya k'are miki Yabi! Ko wacce ta gaishe da dan-
uwanku amma ban da ke, bai yi fishin wula'kanta shi da kika yi ba, ya sake bu'de
baki ya yi miki magana amma kina ji sarai kin k'yale shi, saboda ke din kina gaji
nunkufurci da ba'kin hali ko?"
Raina ya baci domin a kullum kalaman Dada a kaina kenan, bansan me Goggo ta tsare
mata da a kullum sai ta jingina mata munafurci da ba'kin hali ba, ko da yake na
taba jin labarin cewar tun haihuwar Yaya Ummi da dangin Goggo suka zo suna daga
garinsu na Kangire cikin k'aramar hukumar Birin Kudu suka fuskanci wulakanci daga
wajen Mama. Shikenan duk haihuwar da take yi basu sake yin gayya sun zo ba.
Sai dai a samu mutum biyu su zo su ganta washagari su juya sassafe.
Wannan matakin da suka dauka shine ya zama laifin da yak'i wuce wa a wajen Dada da
take ta musguna mata da gorin ba y'ar babbar haula ba ce, sannan yan'uwanta masu
k'ullaci ne, duk kuma cikin matan gidan mahaifiyarmu ce kawai bata da kowa a garin
Toro shi yasa ma wani abin ake yi mata da gan gan.
Duk da ba jin dadin zaman take yi ba, ta jure dukkan kalubale dan kawai ta zauna da
mu yaranta, amma bata tsira ba tunda Babanmu ma haka siddan sai ya dauke mata wuta
na tsawon lokaci mai yawa. Mama kuwa bata fasa yi mata yankan baya a duk inda ta
zauna ko ta samu damar yin hakan ba.
Ko yaushe Gwaggo a cikin mutuntunta Dada take hatta wankin kayanta har yau bata
daina yi mata ba, amma babu gwaninta bare yabawa.
Nan da nan na tunzura na ce "Da yake shi kina jin tsoron kada ya keta ki shiyasa
kike fa'din hakan. Amma ni kin bu'de baki kina niyyar tozarta ni.
Tunda ban gaishe shi ba, ya yi mini magana ban amsa ba, ba sai ya rabu da ni ba?
Bana son harka da shi ne, a duniya na tsani sunan da yake kirana da shi. Sannan
idan zai mini magana sai ya lanjare murya, kuma kinsan dai ba sosai nake ji ba,
bare na ji shi da kyau".
K'wafa ta yi tare da cewa "Kowa ya yi na gari ai dan kansa Yabi".
Basira ta ce "Yi ha'kuri Dada d'ora mana karatun kawai".
Ta rausayar da kai gwanin tausayi ta ce "Kayya Basira zuciyata ta jagula ainun
karatun nan sai gobe kuma".
Firdausi ta ce "Yaya Bulkachuwa saka baki Dada ta d'ora mana karatun, bata ha'kuri
mana".
Ya kalle ta ya ce "Dadarmu share kawai, nima na ha'kura ai. Kinsan hankalin Asiyan
Toro a k'auri yake".
Na sake hauro wa na ce "Tijjani ka bari, ka ga dai bana shiga harkarka akan me zaka
nemi takure ni ne? Gaskiya bana son haka".
Dada ta sake yin k'wafa tare da cewa "Yabi kin janyo muku, domin na lura tashen
balaga kike ji, zan kuwa yi maganinki."
Kafin wani ya yi magana sai ga Ikilima k'anwata da a yanzu take shekaru tara.
Ta shigo cikin nutsuwa ta kalle ni ta ce "Adda Yabi ki zo".
Da azama na mike domin nasan Yaya Jabir ne.
Saurayin da yake gigita zuciyata da ruhina.
Ban ce komai ba, na mike ina cewa "Sai da safenku".
Dada ta bimu da ido tana cewa "Jabiru ne ko kuwa wani ne?"
Ban kula ba, ba kuma wacce ta tanka.
Domin dai na fi su farin jinin mane ma duk kuwa da ba finsu kyau na yi ba, asalima
wasu sun fini kyau, sun kuma fini cikar mace.
A bakin kofar Shashenmu ya jingina.
Matashin saurayi mai cike da nutsuwa da kamala.
Wankan tarwada ne, siriri mai matsakaicin tsayi, mai sanyi a halayya da kuma
dabi'a.
Bashi da kwaramniya tun tashinmu, mai hakuri ne na gaske, da wahalar gaske ka ga
fa'dan Yaya Jabir.
Sosai muke shiri da shi, duk kuwa da ni din mai tsiwa ce, mai kuma hayaniya ce.
Amma jininmu ya ha'du sosai.
Kusan tun soyayyar kuruciya ce ta rikide ta zama ta gaske.
Dalibi ne a jami'ar tarayya ta Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
Ajinsa uku sawess yake yi a cikin Jos.
Sannan ya yi sa'a ma'aikaci ne a karamar hukuma da aka dauke shi aiki da sakandire
a lokacin kawunsa kanin mahaifiyarsa kansila ne a yankin gundumar Toro.
Na isa gare shi, yana sanye cikin farin yadi fari k'al.
Wato duk samarin gidanmu babu mai tsabtar Yaya J.
Ina jin da'din k'iransa da Yaya J. Na lura shima ba karamin son sunan yake yi ba.
Ni ka'dai ce nake fa'da masa hakan kuma.
Kusan halayyarmu daya ni da shi, domin nima tsabta ce da ni, har fa'di ake yi
aljanun tsabta ne da ni. Baya ga haka muna da son y'anuwanmu, bama jin k'yashi
wajen salwantar da duk abi da yake namu ne akan d'an-uwanmu, har rashin girman
jikinmu iri d'aya ne.
Shine d'a na farko a bangaren Baban Tsakiya.
Mutane da yawa suna fa'din kama muke yi ni da shi, ni kuma bana ganin kamar kawia
dai yanayinmu ne daya tunda shi din ba wani girma ne da shi ba, haka yake dan
madaidaici avarage height ne.
Haka nima duk cikin y'anmatan da muka taso ko wacce ta fini tsayi, bani da tsayi,
nafi kusa da gajerta.
Ina da gashi sosai, sannan ina da manyan idanuwa baya ga hakan fara ce sosai.
Yadda nake yar cif cif sai nake matu'kar daukar hankalin mutane.
Kullum idan zan fita sai Gwaggo ta ce ban da wulakanci Yabi, domin al'adar gidanmu
ne yarinya bata kammala karatun sakandire.
Shekaru sha biyar ake aurar wa, amma mu da alamu za'a bari mu kammala duk da dai
Dada ta fara fa'din mu shirya dama kuma ita ce take matsa lambar sai an yi aure.
Ya zuba mini ido babu walwala jikina ya yi sanyi na yi kasa da kaina ina fa'din
"wannan kallon tuhumar fa Yaya J?"
Ya saki gauron numfashi ya ce "kin kama kanki da kanki Yabi. Jiya ma fa sai da kuka
tsaya da yaron nan dan gidan Sarkin k'ofa ko?".
Na yi murmushi na ce "Ai dai baka ji me na ce masa ba".
Na fa'da cikin shagwaba shagwaba.
Ya sake yin kasa da murya ya ce "Ban ji ba, amma yanzu fa'da mini na ji".
Na yi k'asa da kaina na ce "Na fa'da masa cewar ni bana sonsa akwai wani bawan
Allan da ya riga shi yin wuf da zuciyar Yabin Marina".
Ina kallonsa ya dan murmusa ya ce "Waye wannan bawan Allan?"
Na dago amma ban kalle shi ba a dalilin hasken kwai na kanmu.
Na juyar da fuska na ce "Yaya J mana".
A wannan karon murmushi mai sauti ya yi.
Ya nisa ya ce "Yauwa Yabin J, kin biya ni.
Amma idan kina son ki burge ni, ki daina ma sauraronsa ba shi kawai ba, kowanne
namiji ma.
Sannan ki daina fa'da dazu ma sai da kika yi dambe da Saratu.
Kin ta'ba gani na ina dambe?"
Na girgiza kai tare da cewa "Ha'kuri ne ya yi maka yawa, ni kuwa bani da shi, domin
duk wacce ta ta'ba ni ba zan k'yale ba"
Ya girgiza kai ya ce "Ha'kuri fa falala ne da shi Yabi".
Na girgiza kai na ce "To ka dinga yi mini addu'a na shiga sahun masu ha'kurin domin
kuwa ni duk wanda ya ta'ba ni idan ban rama ba sai nake ganin na zama sullutu".
Ya murmusa sosai domin ba mai dabi'ar k'yal-k'yala dariya ba ne.
Ya zuba mini ido ya ce "Wai Goggo ce ta haife ki, al'amarin Ubangiji da girma yake.
Waton idan kika rama baki zama sullutu ba?".
Da hanzari na ce "Ras Yaya J domin dai kai din shaida ne na yadda ake kaffa kaffa
da ni, da duk kayana".
Ya zuba mini ido ya ce "Allah ka sanyawa Yabi ha'kuri da juriya, a mayar mini ita
ta zama mai shanye dukkan kalubale da ha'kuri da kuma kawaici".
Na ce "Gaskiya Yaya J kada mu yi haka da kai, roka mini na zama yar gwagwarmaya
mana, sai kawai ka roka mini na zama mai ha'kuri komai aka yi mini sai dai na yi
kuka, ko ya yi ta cina a zuciyata, watarana sai dai kawai a budi ido aga Yabi ta
ha'du da jinya ko ta mace ma gaba'daya. To ni ba zan zama hakan ba".
Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Kinsan darajar ha'kuri kuwa Asiya?"
Na kalle shi domin bai cika fa'din zahirin sunana ba, tunda ya fahimci ina son
inkiyata ta Yabi shi kenan ya wajabta ma kansa fa'da mini duk da dai yafi son
Asiya.
Domin an sha dakuwa da ni akan ce mini Asiya, ina ganin duk wanda ba zai ce mini
Yabi ba, to hassada yake yi mini, tunda an yi dawafi da ni a ciki, an yi tsayuwar
arfa da ni, an yi jifan shaidan da ni, an yi sa'ayi da ni to mene ne na tauye mini
Hajjin?"
Ban bashi amsa ba ya ce "W
anda Ubangiji ya masa baiwar ha'kuri to ina tabbatar miki an ba shi arzikin duniya
da lahira, ba kuma abin da ba zai cimma ba a rayuwarsa, daure ki zama jaruma amma
ba jarumtar rashin ha'kuri ba".
Na girgiza kai ina murmushi domin dai ban gamsu ba.
Har yau da na fara mallakar hankalina ban ga ribar ha'kurin da mahaifiyata take yi
ba.
Ban ga ribar kawaici da ha'kurin da mahaifinmu yake yiwa zumunci ba.
Ban ga ribar ha'kurin da Yaya Ummi take da mijinta da uwargidanta ba.
Tunda har yau ita ce a wahale, kuskure ka'dan zata yi ya mata tijara a tsakar gida
a gaban kowa tamkar ba ita ce mai k'uruciya ba.
Dan haka na k'udire a raina ba wanda zai nemi ta'ba ni, na k'yale shi, zan yi komai
dan na tabbatar ban bari na zama gajeriyar katanga mai da'din k'etara ba.
Yanayina ya tabbatar masa ban yarda zan iya yin hakan ba.
Ya girgiza kai ya ce "Ai shikenan sai dai zan cigaba da yi miki addu'ar dace wa da
babban arzikin duniya wato Ha'kuri".
Na yi dariya na ce "Dama addu'ar na zama hamshakiyar y'ar kasuwa kake yi mini, ta
yadda kasuwacina zai d'auke mini hankali daga dukkan wani rashin ha'kurina da kake
ga ni".
Da sauri ya ce "Ina yi miki Yabina! Da ikon Ubangiji komai kika kasa sai kin sayar,
kullum sai na roka miki Ubangiji ya baki dauwamammiyar sana'a da zaki tsufa kina
cin gajiyarta".
Da'di ya kama ni, domin Yaya J ne kawai ya fahimci irin yadda nake son na zama
shahararrriyar y'ar kasuwa.
Ya miko mini tsarabar Jos leda biyu da ya ajiye a bayan k'yauren shiga shashinmu.
Na karb'a ina godiya sosai.
Na tabbatar Atile ce da kuma turare, tunda sune abu mafi soyuwa a mini kyautarsu.
Fahimtar hakan da ya yi, sai ya dimanci yi mini tsarabarsu.
Shine ya fara koya mini amfani da turaren Far-away.
Daga haka muka yi sallamah.
Kai tsaye dakin uwata na nufa ban koma wajen Dada ba.


*Akwai kayayyakin gyara mace sosai irin na kasar Chad.*
*Akwai maganin sanyi sadidan*
*Ku tuntube ni a wannan lambar*
*08032773332.*
✍️


*BAK'AR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS M.I.NASHE)*.

*Marubuciyar*
*Halin Yau*
*Sabo da kaza*

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA
CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA
BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*MASU SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYERS*
https://www.wattpad.com/1381521145?
utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp.w4b&utm_content=share_published&wp_page=
create_on_publish&wp_uname=SurayyaIbrahim1&wp_originator=2c15XL0D2bIzHhiZQM1Ufz9MWP
lKieRkWxJuGH2P9gX0b9XHQk5Jym8fxiz%2BPI0TAhOUhwh2GWl2lunKDNI2ObmS%2B%2FfL1BUVY3%2Ft
%2BNKg%2B0D0iEZNLOPdWH9AZxOaGd51


https://arewabooks.com/book?id=64e93a53984f91b3605ae432


*Ina makaranta labaran Books ɗin Ayshat Ɗansabo lemu, marubuciyar TAIMIYYAH DA
NUFIN ALLAH kai har ma da sauran daɗaɗan littafanta? Marubuciyar na muku albishir
da cewa sabon littafinta mai suna ƘADDARAR ZOYA ya fara sauka da zafinsa,labarin
ƘADDARAR ZOYA labari ne da ya faru a gaske ba ƙageggen labari bane.Don haka kar ku
bari ayi wannan tafiyar babu ku a cikinta,labarin zai zo muku akan 500 Whatsapp
group sai VIP group on Telegram 1k.Ku tuntuɓi marubuciyar akan lambarta 08167768704
domin samun free pages na labarin kai tsaye, kafin ku kai ga yin payment.Kar ku
manta it's a true life story,don haka ku hanzarta shiga cikin tafiyar da babu
✍🏻
danasanin bin alƙaminsa.... *

5&6.

A zaune na tarar da ita tana kullin siga, da yake tana auno rabin kwano tana
k'ullawa, idan an zo siyan koko ana siya.
Ikilima tana gefenta tana faman barci.
Na ajiye ledar a gabanta.
Ta kalle ni ta ce "Yabi na sha fa'da miki, jikina na bani sha'aninku da Jabiru ba
mai yiwuwa ba ne, ba sa'an auren ki ba ne, gara ki tsaya akan Abdulrashid zai fi
mana sau'ki da kwanciyar hankali".
Na yi shiru, amma zuciyata sai tsalle take yi.
Babban tashin hankalina a duniya shine Gwaggo ta ce mini aurena da Yaya J ba zai
yiwu ba.
Na yi k'asa da kaina a hankali na ce "Gwaggo fa'da mini dame ya fini da kike ganin
yafi k'arfina?"
Ta murmusa ka'dan ta ce "Saboda Babanki ba shi da arziki, sun tsere mana, sannan
uwarsa tana da buri a kansa, bayan haka ga Mama k'ut take da uwarsa, dan haka zata
yi dukkan mai yiwuwa ta sake b'ata lamarin tunda akwai haske a tare da shi, ba zata
so wannan hasken a tare da ke ba.
Sanin kanki ne kuma mutanen gidan nan baza su dauke ki su ba shi ba, tunda kuna da
yawa, zasu yi kwarya tabi kwarya ne a tsakani.
Da ace ke din diyar Baban kasuwa ce to, da ba fargabar da zan yi".
Na numfasa k'irjina ya daure ainun.
Na dinga tambayar kaina shin zan iya rabuwa da Yaya J?
Da gaske har lalacewar zumunci ya kai za a iya hanamu aure ba tare da wani dalili
gamshasshe ba?
Ashe har za'a iya ture karfin jini saboda kawai dan-uwanka ba shi da wadatar abin
duniya?
Na sauke nannauyan numfashi na ce "Ki daina damuwa Gwaggo! Ban tsananta ba, ban
kuma dage sai shi ba.
Ki cigaba da yi mini addu'a".
Ta sake kafe ni da ido ta ce " Ina yi miki addu'a sosai Yabi, amma zata yi tasiri
ka'dai idan kin barwa Allah ya yi miki zabi, kin kuma yak'i zuciyarki akan Jabiru.
Ina nufin ki rage zurfafa a al'amariinsa."
A sanyaye na ce "To Gwaggo".
Sai kuma na zauna ina taya ta k'ulla sigan ina bata labarin yadda ta kaya a
tsakanina da Dada.
Ta nisa ta ce "Ba kya jin magana ne, ban da hakan mene ne zaki dinga janyo wa tana
yi miki mugun fata?
Kinsan kuwa bakinta zai kama ki domin ita ma uwa ce a wajen ki".
Jikina ya sake yin sanyi, na dinga yin addu'ar Allah yasa na daina tanka mata akan
Shehu tunda mafi yawa saboda hakan take fusata.
Ta ke tsanata mini, har take yi mini
mummunar addu'a.
Washagari takwas saura muka d'unguma zuwa makarantarmu ta jeka ka dawo ta
gwamnatin jahar Bauchi.
Ajin mu hudu wato ss1.
Ko wacce tana cikin tsafta, duk inda muka wuce sai an kallemu wataran

Please Login or Register in order to submit comment