You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaki yi Yabi. Ni yanzu son nawa mijin
nake yi? Amma na yarda kaddara shi ta zaba mini. Dan haka na yi hakuri nake yi masa
biyayya, duk da shi din ba duka yake sauke hakkin da shari'a ta gindaya masa ba.
Amma na sani ina rabo mai girma a wajen Azza wa jallah".
Na tsananta kallonta domin gaskiya ta fa'da. Har zuwa yanzu da ta zarce shekaru
goma da aure bata son mijinta, ni shaida ce akan hakan, amma kuma ha'kuri da
biyayyar da take yi akan sha'aninsa mai yawa ne.
Ta numfasa ta ce "Yabi ba kya yarda da Tijja
Yaya Bulkachuwa. Su kuma maza da kike ganinsu komai zaki yi musu na kyautata wa
matu'kar ba kya mutunta shinfidarsu, to fa komin kokarin ki a banza ne a idonsu.
Saboda haka ki d'auki matakin gyara a tsakaninku."
Na nisa na ce "Baya gamawa da wuri Yaya Ummi. Ni gaskiya bazan iya ba."
Ta ce "Ahab dama da labarin neman auren da yake yi ya riske ni, sai da na ce na
tabbatar ke ce silar k'arin auren sa. Ai sai ki yi tunda al'amarin kishiyata bai
saka kin k'yamaci kishiya ba".
Wani irin abu ya soki k'irjina, ban san mene ne ba. Amma gaba'daya ji na yi tamkar
zan shid'e.
Na rushe da kuka mai tsananin gaske.
Ta ce "Ai indai kika cigaba da tafiyar da shi a hakan, tabbaskuka na gaba. Ba ki ga
Bilkin da yake zuwa wajenta ba, gansamemiya ta yi biyu da rabin ki."
Da rawar murya na ce "Me za'a yi da mai BAK'AR TA'ADAH irin ta Tijjani. Aure ko
rufa wata biyu ba'a yi ba har ka fara neman wani auren. Na rantse Yaya Ummi sai dai
a tsine mini. Amma bazan taba zama da wata macen a k'arkashin ikon Tijjani ba".
Ta sake ru'ko hannuna ta ce "Idan kina son ki zauna lafiya, ki yi sana'arki, ki
cigaba da tallafa mana. To ki zauna lafiya da mijin ki, ki daina gudunsa, ki yi
hakuri da shi watarana sai ki ga kun kai ga babban bigire. Ni fa na dauka ma ciki
ne da ke. Jiya nan na je gidan Ubaida na tarar tana ta kwarara amai. Da kaina na
rakata asibiti aka tabbatar ciki ne da ita. Kin ga kuma ai kanwar ki ce duk
k'uruciyar ki ai kin fita a haife. Jabir din da kike ta kulafacinsa matarsa wata
tara ta haihu. Sai ke ce zaki zama shasha wacce bata san me yake mata ciwo ba. Da
ace kin kwantar da hankalinki da wata'kila ke ma da na ki cikin a jikinki".
Kunya ta rufe ni, na ce "To yanzu dai ki fa'da masa ya bar ni na yi sana'a ta."
Ta ce "A yanzu bazan yi masa magana ba. Idan kin canja kin daina gudunsa, bai bar
ki ba, sai na yi masa magana. Amma yanzu ai ke ce zaki fara zuwa da gyara".
A sanyaye na ce "To".
Amma k'irjina tamkar ya fa'do a dalilin nauyin da yayi akan batun tsohuwar budurwar
Bulkachuwa wacce aka kai masa ku'din aurenta aka k'i karb'a. Tun lokacin ya fita a
harkarta amma ita take ta nacin ya yi hakuri.
Tijjani da ya yi bakam yana sauraronsu. Ya saki gauron numfashi yana k'ara ganin
hankalin Ummi. Sai dai mamakin da ta bashi a ina ta ji yana zuwa wajen Bilki?
Shi yasan tunda aka yiwa su Baban Marina wula'kanci bai sake taka gidansu ba har
yau. Idan Ummi ta fa'di hakan da nufin yiwa Yabi barazana. Ya tabbatar liki ta
b'allo masa.
Duk yadda Yabi take kirarin bata son sa amma kuma kishi take yi akan lamarin sa ba
ka'dan ba. Duk da dai ya yi amanna kishi dabi'arta ce.
Amma ya tabbatar wannan maganar sai ta ri'ke ta a ranta.
Ya saki gauron numfashi yana fatan a sami dai-daito a tsakaninsu.
Tsawon lokaci yana sauraronsu, yana jin irin yadda Ummi take ta wasa shi tare da
ban baki a madadinsa. Wanda hakan ba k'aramin kaunarta ya k'ara ji ba.
Jin tana haramar tafiya ya sanya shi mike wa ya maze tamkar bai ji me suke fa'da
ba.
Da murmushi ya ce "Ummilolona ke ce da sassafen nan?"
Ita ma da walwala ta ce "Eh Yaya Bulkachuwa barka na je nan gabanku ka'dan, shine
na biyo na gaisheku ko na yi laifi?"
Da sauri ya hau girgiza kai tare da fa'din"kin yi daidai Ummi. Allah ya bada ladan
zumunci".
Ta ce "Ameen."
Ya bita suka fita da kafarsu. Wata'kila har gidanta ya rakata domin ya jima bai
shigo ba.
Hadari ya hadu mai k'arfin gaske. Daidai lokacin ya dawo tamkar jifa.
Sai da ya rufe k'ofar d'akin da yake yi mini isa, ya rufe tagogin falo.
Sannan ya shigo d'akina. Na kalle shi na dauke fuska domin haushinsa ya sake kama
ni sosai.
Ya zauna a gefen gadon ya sanyaya murya ya ce "Albarkacin zuwan Ummi na ajiye
fishina. Na huce, komai ya wuce".
Na yi kamar ban ji ba. Ya matso jikina sosai ya ru'ko ni, na fizge a fusace na ce
"Bana son ka huce Tijjani. Domin dai ni bana ha'da sabgata da marar imani bare kuma
tausayi."
Ya sassauta ya ce "me na yi na rashin tsoron Allah Asiya?"
Murya na rawa ina shirin kece wa kuka na ce "Ban da ka tabbata baka da tausayi
mene ne zai sa ka jajibo aure alhalin ko wata biyu baka rufa da yin auren ba. Mene
ne hakan inba rashin tsoron Allah da rashin imani ba?."
Ya sake matsowa jikina ta yadda bayansa na shafar cikina.
Ya yi k'asa da murya ya ce.
"Wallahi Asiya Toro tsoron Allah nake ji sosai. Shine shaidar hakan. Asalima saboda
ina tsoronsa ya sanya na fara neman auren. Ya zan yi? A d'an zaman da muka yi ya
kamata ki fahimci bazan iya ri'ke kaina alhalin ina ganin ki, muna kwana gida d'aya
ba.
Ke kuma gaba'daya kin bijire , kin k'i saurara ta, tunda ba sona kike yi ba. Sanin
zan iya fa'dawa halaka ya sanya na samu wata bazawara mai gajeran buri muke
tattauna wa. Idan Allah ya yi zan aure ta. Kin ga shike nan na magance tashin
hankalin da yake tsakaninmu, sannan na samu mafita daga hatsarin fa'dawa zina da
aurena".
Yana rufe baki ba zato na mik'a hannuna na d'auko wata doguwar robar mai ta
kokobota. Na kwad'a masa a goshi. Ina kwada masa tare da ce wa "Allah ka yi mini
tsari da mugun k'ullin da yake zuciyar wannan bawan naka. Bilhiillazi kana da
fitina Tijjani."

✍️

*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered,
Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan
farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon
yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.

*Assalamu alaikum Bayin ALLAH, kun san ce wa FREE PAGES na littafin ƘALUBALEN
RAYUWA ya ƙare? Wanda cigaban littafin KUSKUREN SO na? Kun san dai yadda na
nishaɗantar daku a labarin Nafeesar Sufyan? Kuma dai kun san yadda na nishaɗantar
DAKU a littafin ISHARA labarin Zainabun Sameer? Littafin ƘWAƊAYI fa? Labarin
Zainabun alamaramma? Na san baku manta RAHEELA MAI ƊAN BUJE ta cikin littafin
RUGUNTSUMI? Jamaa na rubuta kun karanta kuma kun shaida, alƙalami ne da babu
tantama a cikin shi, Jamaa yanzu ma tafe da nake da ɗaya tankar dubu, salon na
daban ne? Ba zan so ya wuce ku ba, shiyasa na maku promo ku biya 300 madadin 400
kacal ta wannan hanya 9994468172 Access bank fiddausi musa tare da shaidar biya ta
08036953516 ko 07042277401, domin mu tafi tare, na maku alƙawari, labari ne da zai
tsaya zukatan..*

53&54.
Ta ko ina nake jifan sa, gaba'daya na hargitse dakin.
Da k'yar ya samu ya ri'ke ni ya dauke ni caraf ya d'ora a cinyar sa ya rungume ni
tsam tsam.
Gaba'daya na shige jikin na yi luf, sai kukana kawai yake tashi, wanda na shagwaba
da kishi ne.
Cikin rad'a yake ce wa "So ki ke ki illa ta ni ne?"
Da k'arfi na ce "Eh. Wata'kila dan ka ga kana da kyau ne ya sanya kake ganin ko
wacce mace ka ce kana so, ba zata tankwabar da kai ba. To gara na rugurguza ka.
Tunda ni kyaun naka bai rud'e ni na makance akan ka ba"
Ya sakar mini wani irin nishi a kunne, sannan ya dan cizar mini shi ka'dan. Yar na
ji jikina ya amsa. Na fara fizge fizgen bazan yarda ba, sai nima na cije shi a nasa
kunnen.
Shi kuma ya dinga dariya yana cakuma ta son ransa.
Babu zato ruwa mai k'arfi ya goce.
D'akin ya yi duhu saboda ko ina rufe yake gudun kada ruwa ya shigo.
Wannan yanayin ya sake susuta Tijjani. Ni kuma na dinga koke-koken jan rai. A
ki'dime yake rarrashina.
Fa'di yake "ki yi ha'kuri I will be soft and gentle."
Ni kuwa sai botsare wa nake yi. Tare da ce wa "Ni dai ba da'de wa zaka yi ba."
Da rawar murya ya ce "Nà yarda amma idan kika cije ni, ko kika yi mini
fallashasshen kuka. Ki tabbatar kina cikin komar mala'iku".
Na yi shiru. Amma zuciyata sai harbawa take yi. Domin har zuciyata nake jin tsoron
al'amarin.
Ina ji ina ga ni, ya shiga yin yadda ya ga dama da ni.
A farkon tafiyar gaba'daya na kankame jikina ina sauraron jin matsanancin zafi.
Amma ga mamakina sai ban ji ba. Har na sakankace na saki jikina. Wanda hakan ba
k'aramin dadi ya yi masa ba. Ya k'ara haifar masa da kuzari mai yawa.
Dan haka lokacin da ya shafe yana abu daya, bai dame ni ba.
Bayan ya nutsu. Ya rungume ni yana ta faman sakin kalaman yabo da soyayya.
"Asiya da hakan kike yi mini, to me zai sa ma na yi fishi da ke? Bare har na yi
tunanin k'arin aure. Na gode sosai, Ubangiji ya sanya albarka a rayuwar ki
gaba'daya."
Na yi shiru. Amma zuciyata sai kai kawo take yi akan abin da nake son amayar wa.
Na kasa jarumtar ha'diyewar murya babu amo na ce "Yo ni ai tunda wula'kanci ka
shiryo mini daga yin aure za'a ka fara neman wani dan kawai ka nuna wa duniya bani
da wata kima a idonka. Wallahi ba zama zan yi ba. Zaka wayi gari ne ka ga na bace
maka."
A diririce ya sake ru'ko ni sosai tare da ce wa "Kar ki tayar mini da hankali dan
Allah.
Na fasa, dama dan na rasa yadda zan yi ne. Amma yanzu indai kin daina yi mini
abubuwan da kike yi. Wallahi bazan sake tayar da maganar ba. Ke ko hanyar da ta bi,
bazan sake bi ba".
Cikin kuka na ce "Daga baya ke nan. Wadanda suka ganka kana zuwa tadi ai tuni sun
san baka son Yabi. Dan haka kuwa ba yarda zan yi ba. Ka je ka cigaba da abin da
kake yi, ni ma zan samu mafita Wallahi".
A raunane ya ce "Bana son kukan ki Asiya! Amma sai ki ta yi mini, dan kawai ki
gigita ni. Ban iya yaudara ba. Na ce miki, na fasa, na janye, to ba shikenan ba?"
A zabure na ce "Ba shike nan ba".
"Da azama ya ce "To fa'da mini yadda za'a yi, me kike so na yi dan ki gamsu?"
Na dinga gunjin kuka da na tabbatar yana jijjiga shi.
Ya dinga shafa kaina, yana fa'din " Sorry Asiyata! Na ce bazan sake ba, ki yi
ha'kuri da gaske na fasa. Dan Allah mu rufe maganar nan haka. Me kike son ci na
dafa miki?"
Na fara kokarin fizgewa daga rugumar da ya yi mini, amma na kasa.
Cikin tab'ara na ce "Bazan ci ba. Yau kwana nawa rabon ma da ka tsaya ka saurare ni
akan maganar abinci. Ko na ci, ko kada na ci ai babu ruwan ka".
Ya sake sassauta murya ya ce "Wula'kanta ni fa kike yi. Ta ya ya zuciyata zata ji
da'din kyautata miki? Yanzu kuwa ai komai yi miki zan yi da kaina".
Na cuna baki na ce "Abar maganar abinci. Ka tashi tunda ruwan ya tsaya, ka kwaso
kayanka da ka kai mini wanccan d'akin dan kawai kana nema na da jidali".
Ya zabura ya tashi. Ya lalubo jallabiyarsa ya d'ora akan gajeran wandon bai ce
komai ba ya fice.
Ya kwaso su tsab. Ya mayar dasu inda suke.
Ya juyo ya ce "Na kwaso, shike nan?"
Na bata rai na ce "Ba shike nan ba. Kada mu samu sabani ka sake yi mini hakan.
Tijjani ba ruwanka da d'akin can. Nan ne dakinka. Idan kuma zaka dinga fitina ta
akan dakin to ka sani zan tattara kayan gadon na mayar maka can din. Tunda nan
d'akina ne da shari'a ta ce ka bani shi tilas. Idan anan nake sana'ata ban shiga
cikin dakin ba, ai na tsira ko?"
Ya yi wani irin murmushin da na fahimci mai harshen damo ne.
Ya numfasa ya ce "Namiji ai ba yi masa shamaki a gidansa. Dan haka mu zauna lafiya
mu mutuntata juna shine kawai. Amma bazan yarda ina tattala ki, ke kuma ki ce zaki
dinga wula'kanta ni, sannan kuma na yi miki yadda kike so." Ya girgiza kai ya ce
"Ba haka Tijjani yake ba. Ba kuma zai zama hakan ba".
Na kura masa ido na tabbatar iyakacin gaskiyar sa ya fa'da. Na rasa me zance masa
domin na tabbatar duk bala'ina. Idan ya kunsa mini ba'kin ciki daya tak kwana zan
yi na yini cikin ba'kin ciki mai tsanani.
Dan haka sai kawai na buge da sake fashe wa da kukan.
Daga inda yake tsaye, ya ce "Allah dai ya taimake ni ki hau ko na samu sau'kin
wannan rikicewar da gangan. Idan kina ganin baby a hannunki wata'kila kya daina yi
irin wannan sakalcin."
Yana rufe baki na fara nuna kaina cikin kuka ina ce wa "Tijjani ni ce sakaliya?"
Kafin ya amsa mini na rausayar da kai na ce shike nan na gode da wannan tukuicin".
Ya taho da sauri yana kuma dariya. Ya rike k'afafuna ya ce "Ina nufin sakaliyata
fa".
Na yi tsuka na juya.
A sanyaye ya ce "Bana son tsuka Asiya. Amma na yafe miki, ban yi fishi ba".
Daga hakan ya koma ya fita. Na tabbatar kuma kicin zai shiga. Ni dai daga nan barci
ya sure ni.
Sai bu'de ido na yi na ganshi ya yi wanka ya shiraya tsab. D'akin ma ya cika da
kamshin turaren nasa.
Yana daga jikin sif din yana saka links ya ce "Yanzu dama zan tashe ki, na kai miki
ruwan wanka".
Ban ce komai ba, na tashi, na daura zani a kirji sannan na saki zanin gadon na
sauko.
Ya kalle ni babu riga a jikina. Ya ce "Asiya Toro a gabana babu riga. Sai na sake
ganin ki wata yar kwaila, a hakan tamkar ba zaki iya komai ba. Nan kuwa al'amarin
da yake tare da ke azimin ne".
Na cuna baki na ce "Ai ni na gode Allah ma da aka baka yar mitsil din. Kai da rusa
rusan mata sai kallo daga nesa. In juninka cusawa mutum takaici ne. Har abada kai
da zunduma zunduman mata".
Ya murmusa duk da dai yana kokarin shanye dariyarsa.
Ya ce "Wato baki ji da'din yabon da na yi ba, sai kika dauki abin da bai yi miki
da'di ba, kika yi raddi?"
Na share, na dauki tawul na fice abina.
Na dawo na tarar da shi ya gyara gadon tsab. Ya share dakin. Na kasa hakuri na ce
"Tijjani wai a ina ka iya gyaran gado ne, tunda kullum dakinka na gida a hargitse
yake, sai asarrariyar can ta gyara maka shi yake yin fasali".
Ya dauko mai yana murmushi ya tarar da ni a bakin gadon. Na yi kamar na hana shi
shafa mini mai din sai na fasa kuma.
Domin a dan zamanmu na fahimci yana matu'kar son ya shafa mini mai, kafin na sanya
komai a jikina.
Ina ji ina ga ni ya dinga shafe ni da sunan shafar mai wanda ni kaina ina matu'kar
jin sakon nasa a dukkan jikina.
Yana cikin murzar tafin kafata. Wanda kafin ya zo kafar ya shafe mintina sha biyar.
Murya dakushe tabbacin so yake ya koma ruwa ya ce "Nasiba ce asarrariyar Asiya?"
Na fizge kafata na tashi. Na ce "Ina dalilin gatsa sunan matar wani ne Tijjani?
Kusan mintina ashirin da yin maganar ashe duk yadda na barka kake yin yadda kake so
da sunan shafar mai, zuciyarka na tunanin suntumemiyar halitta ko? Wallahi bazan
iya da bala'in ka ba Tijjani!
Ganin da gaske na fitittike, zan birkice masa.
Jikinsa na bari ya ce "Allah ya baki ha'kuri, na yi kuskure. Sai dai ya kamata ki
mini shaidar tun ma kafin a mini babban alherin ba ni auren ki ai na fita a dukkan
sha'aninta. Bare kuma yanzu da take matar wani. Dan Allah mu bar maganar, bana
sonta. Ki yi hakuri."
Ya dauko mini wata riga ya ce "Ga gifts din ki na zama matar aure, tun first night
dinmu nw so baki, to bata iso a lokacin ba."
Cotton yar kanti. Gaba'daya rigar tafi dacewa da yara y'an shekaru goma. Domin har
da teddy wacce aka yi jakar goyo da ita. Sannan da hula irin mai malafar nan.
Kalar ruwan hoda (pink )da yarfin filawa mai ruwan lemon tsami (lemon green) ce. Ba
karamin kyua ta yi ba.
Ya mik'o mini sabon pant. Ya ce na saka miki?"
Na juyar da fuska. Ban amsa ba. Sai da na shanye kunyar na na ce "Tijjani da gaske
dai kallon yarinya kake mini. Ban da haka wannan rigar ai ta yiwa Iklima ka'dan
bare ni. Kasan kuma Anas ne yake bina ba ita ba."
Kai-tsaye ya ce "Na sani. Sha'awa ta bani, shine na yi kundubalar d'auko miki ita,
rabin ku'din na bayar. Abokina yake kawo su daga China. Ta kusa dubu ashirin, sonta
nake yi, saka kawai".
Na ce "Tsakani da Allah da atamfa ka siyo mini, yanzu wannan ina zan saka na je da
ita?"
Ya ce "Ba dan ki sa ki fita na siyo ta ba. Dan ki saka mini na kalle ki a yadda
nake son ganin ki ne".
Ganin ya b'ata fuska ya sanya na juya na saka pant din. Ina juyowa ya bani sabuwar
breziya yar mitsil kalar wando da alamu set ne tare suka zo. Ban ce komai ba na
kar'ba. Ina ayyana wato ya riga ya gama gane wacce zata yi mini. Domin duk na
lefena sun yi mini yawa duk da k'ananu ne sai dai ko nan gaba. Domin da na aikawa
Gwaggo akan ta bayar, dawo mini da su ta yi, ta ce nan gaba zasu yi mini na
adanasu.
Sai da na shafa hoda na goga jan baki kalar ruwan hoda.
Sannan na zura rigar. Ta shige ni tsab. Ta d'an zarce guiwata da ka'dan, kasancewar
ba ni da tsayi. Ya ce "Wow This is Asi beauty lady".
Na dan yi murmushi. Ban ce komai ba. Da kansa ya sa mini hular ya d'auko sabon
turare a cikin kayansa da aka rubuta Active woman. Ya bu'de ya hau fesa mini.
Kamshin turaren jikinsa da wanda ya fesa mini suka hadu suak bige ni. Suka isar da
wani irin sako akan Tijjani a cikin zuciyata.
Shi kuma ganin na koma masa wata yar yarinya kankanuwa ya sanya ya sure ni. Ya yi
falo da ni. Yana ta sakin maganganun da suke da nauyin bayyana wa.
Komai da barin jiki yake yi mini. Ya ajiye ni akan kujera ya ce "Bari na kawo miki
abincin Little Angel."
Har cikin zuciyata na ji da'din sunan. Duk sunayen da Bulkachuwa yake fa'da mini
babu wanda na ji dadinsa irin little. Domin ya dace da ni k'warai da gaske.
Shiru shiru bai dawo ba. Sai na yi kamar na leka shi, sai kuma na fasa.
Can sai gashi da tray da ya jero kayan abincin.
Da walwala ya ce"Sorry little na bar ki ke ka'dai, ga shi babu wuta bare kallo ya
hana ki gundura da zaman jiran kukun naki"
Na k'yal-k'yale da dariya na ce "Wai kai ne kukun?".
Cikin gamsuwa ya ce "Ba ki aminta ba? To mene ne aikina ban da na fita na yi aiki
tukuru dan na nemo miki abin da zaki ci.
Idan kuwa ina gida, idai baki bata mini rai ba. Still aiki zan miki dan na hutar
da ke shiga kicin kullu yaumin".
Na murmusa ba tare da na ce komai ba, domin na yarda da dukkan zuciyarsa ya ke yin
maganar.
Ya bu'de kwanon abincin ga mamakina sai ganin fanke na yi subu-subu sun soyu sun
bada kala mai daukar hankali.
Na kalle shi da mamaki na ce "Tijjani yaushe ka iya fanke haka?"
Ya saki murmshin jin dadi ya ce "Ki bari sai kin ci sai ki tambayi na iya ko kuwa
makwaki na yi".
Na sauko ya ha'da mini shayi mai madara da milo. Shi kuma ya zuba bak'i.
Muka fara cin fanke wanda ba karamin dadi ya yi ba. Na kalle shi na ce "Ya yi da'di
sosai. Na ji har da k'wai da madara ka saka. Maimakon ka bar madara ka zuba a
shayinka."
Ya rausayar da kai ya ce "Ke dai ki sha my little".
Ya kashe mini ido sannan ya ce "Ai ina ganin amfaninta. Addu'a nake yi sosai na
samu damar da zan daina siyo miki ta sacet. So nake kullum ki sha ta ruwa gwangwani
guda. Ta yadda ba zaki dinga gazawa da al'amarina ba".
Kunya ta yi matu'kar kama ni. Na sanya dukkan hannuna na rufe fuskata, ina wani
irin murmushin da bansan ta inda yake bullowa ba.
Da k'yar na cigaba da cin abincin bayan ya ce "Duk a wajen Baba na koyi girki.
Yadda kika ga Aliyu da Nasiru suna hidima irin ta y'ay'a mata nima irin wannan
goyon ta yi mini.
Kullum fa'di take yi, tunda bata samu mace ba, ba zai yiwu a ce ba zamu tallafa
mata da kaomai ba.
Kullum cikin fa'da mana take yi mu koyi aikin gida dan wataran mu taimaki iyalinmu.
Annabin Rahma da yafi kowa daraja yana tallafawa iyalinsa. Ba mallakewa ba ne dan
namiji ya yiwa mace hidimar girki, wanki, ko ta shara ba. Amma kuma ta ce "Ban da
wanke wanke wannan na yan daudu ne".
Muka k'yal-k'yale da dariya domin kuwa munsan kawai ra'ayinta ne amma babu aibu
idan mutum ya yi. Ya ce "rigar nan fa ta yi miki kyua my little. Tamkar na dauwama
ina kallon ki".
Na murmusa ka'dan tare da ce wa"Thank you" a gayance.
Na marairaice na ce "Ya maganar tomfirint din?"
Cikin nutsuwa ya ce "zuwa wani satin zan kai ki da kaina".
Na fa'dada murmushi na ce "Na gode Tijjani".
Ga mamakina sai na ji nauyin gatsa sunan da na yi, ta mamaye ni. Karon farko da na
ji hakan a rayuwata.
Na lura shi kuma yana cikin maza yan ka'dan da basu damu da a fa'di sunansu kai-
tsaye ba.
Tas muka cinye fanken.
Na kwashe kayan dan nasan idan ya mike zai kwashe ne.
Na kai wajen wanke wanke na ajiye.
Na koma wajensa na ce "Wai da yaushe ka yi kwabin ne?"
Ya nisa ya ce"kina barcin gajiyar da na tara miki. Ni fa duk kallon jaruma nake yi
miki. Ashe a tsiwa da dambe da sana'ar k'unshi kike da jarumtar".
Na girgiza kai na ce "oh haka ka ce? Ai shikenan next time zaka gane ashe dazu ba
karamin jarumtar na yi ba".
Ya jani jikinsa ya ce "Kin san bana wasa a wannan fannin tsokanar ki nake yi, idan
akwai abin da yafi jarumta kin yi dazun".
Na kalle shi cikin nauyi nauyi, kunya kunya na ce "ka ji tsoro?"
Da sauri ya ce "Na ji".
Bai fita ba sai da ya dawo daga sallar azahar.
Muka ci abincin da tare muka yi da shi.
Sannan ya fita zuwa gidan Alh Ado Naira zai yi musu gyaran satellite tunda aka kawo
wuta suke ta yi masa waya.
Kamar ana jiran ya fita aka fara zuwa lalle da kitso.
Shike nan muka shirya da Tijjani. Wata irin soyayya yake gwada mini mai wuyar samu.
Da ya ga na canja fuska zai fara susuce wa, ya dinga jaye jaye magana, ko fita ya
yo sai ya dawo. Matu'kar ban ware masa ba, ba zai samu nutsuwa ba. Ni da kaina na
sani an jarrabe shi a kaina. Domin gaba'dayana a tsaye ban fi iya ruwan cikinsa
ba. Duk zafin ransa baya son mu yi fa'da. Cikin rarrashi yake tafiyar da ni.
Komai da rawar jiki yake yi mini. Kullum safiya ya wajaba kansa share duka gidan.
Ya sa tsintsiya ya wanke band'akin, sannan ya tashe ni na yi wanka. Mafi yawa da
safe da burodi muke karyawa. Dan haka shayin ma sai dai na gan shi a filas ya riga
ya dafa.
Da nutsu sai na ga ne tunda na daina gudunsa a shimfida shike nan ya tattara dukkan
hankalinsa a kaina da lamarina.
Baya taba yin dare a waje.
Ana idar da sallar isha zai dawo ya rufe gidan shike nan sai gobe.
Idan kuwa uzziri ya yanko masa sai ya bugo waya ya sanar mini yana waje kaza. Na ce
to tare da addu'ar ya dawo lafiya.
Ranar da yan rikicin suke kusa kuwa, na botsare masa idan ya dawo.
Ya yi ta barin jiki wajen rarrashi na.
Tuni muka fara jarrabawa har mun kusa kammalawa. Da kansa yake kai ni. Idan mun
gama sai na yi masa waya ya zo ya dauke ni.
Muna tsaka da jarrabawa Nazira ta haifo d'anta lafiyayye.
Dan haka zarya nake yi tsakanin makaranta da gidanta. Har aka yi suna yaro ya ci
sunan wan mahaifin mijinta Ahamd. Ni da kaina na lank'aya masa Abid.
Sosai na yi mata hidima ita da yaronta.
Ranar suna wanda a lokacin watan Maijidda biyu da haihuwa, y'arta Sajida ta yi
gubibi da ita.
Tana hannuna ina

Please Login or Register in order to submit comment