You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kare mata kallo. Na rasa gane da wa take kama a tsakanin itayenta
Jabir da Maijidda.
Saratu da Firdausi suka shigo. Ita Firdausi ta haihu. Saratu ce ta ke ja itama yau
ko gobe.

*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki
da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*

Na kallesu da murmushi na ce "Ni kam da wa Sajida take kama ne?"
Kafin na rufe baki Maijidda ta ce "Da Abbanta mana. Yo ko makaho ya shafa ai yasan
kama take da Honey. Shiyasa yake kara sonta domin kullum ya dauke ta sai ya ce mata
"Ta zabo uwarta da kanta".
Gaba'daya jikinmu ya yi sanyi domin kuwa kowa yasan neman magana kawai take yi.
Dan haka sai na mikawa Firdausi yarinya na shiga hidimar raba abinci. Amma k'asan
zuciyata ya yi nauyi akan lamarin Maijidda. Har aka watse ban sake yarda na zauna
a cikinsu ba.
Har dare duk mana gidan Nazira.
Muna zaune sai ga yaro ya zo ya yi sallamah ya ce "Wai Asiya ta fito su tafi".
Na kasa boye masa abin da Maijidda ta yi.
Tun a hanya na hau rattaba masa abin da ta yi mini.
Maimakon ya bi bayana ya fa'da mini maganganun da zan ji da'di. Sai ce wa ya yi "To
mene ne na bacin rai a ciki? Ke ma Ubangiji ya za'ba miki wanda yafi mijinta son
ki, to sai me kuma? Ki bar maganar nan inba so kike na ga ne kishinta kike yi har
yau ba".
Takaici ya kama ni goma da ashirin. Na kame bakina na yi dif. Amma na riga da na
harzuka k'warai da gaske. Ga mamakina sai kawai shi ma ya share ni. Muna isa gida
ya gama uzzirinsa ya yi kwanciyarsa ya rabu da ni.
Ba'kin cikin hakan ya sanya na dinga kukan sharbe. Bai ko motsa ba, bare ya nuna ya
ga ne halin da nake ciki. Da kaina na kwanta. Da asuba bayan ya dawo nan ma
kwnaciya ya yi bai nemi ni ba kamar yadda ya sabar mini. Ai sai kawai na fashe masa
da kuka mai sauti.
Ya janyo ni jikinsa ya ce "Yi shiru, na baki hakuri kin ga".
Cikin kuka na ce "Akan me zaka yi fatali da ni?"
Da rauni a muryarsa ya ce "Akan me har yau baza ki bar kishin Jabir ba? Kina
tunanin zan ji dadi idan na ga ne har yau ban yi nasarar shafe shi a ranki ba?"
Na yi shiru sai shesshekar kukana ne yake tashi.
Haka ya ajiye fishin nasa ya dinga rarrashi tare da shafata cikin nutsuwa. Daga
hakan kuma ya shiga yin abin da baya gundara da yinsa.
Sannu a hankali muke rayuwa. Duk yadda Bulkachuwa yake tarairaya ta, akwai abin da
yake mini wanda yake ci mini tuwo a k'warya.
Duk yadda na so na dinga saka mana kifi ko nama a cikin girkinmu ya k'i yarda. Idan
kuwa har na bayar aka siyo na girka to zai ci iya abincin ne ya bar mini nama ko
kifina.
Rannan da na nuna b'acin raina.
A zafafe ya nuna mini yatsa. Ya ce "Iya abin da nake da shi zan ba ki, ba kuma zan
zauna ki shiga cikin lamarin rik'on gidana ba. Ke dai tunda kina samun ku'di fiye
da ni, komai kike so ci akan abin da nake da ikon ba ki, ba zan hana ki ba. Amma ni
kada ki ajiye, ko ki ba ni, bana so".
Ganin da gaske baya so din, sai na daina. Iya abin da ya siyo shi zamu ci. Da na bi
yadda yake so, sai muka samu dai-daito. Domin duk ranar da ya ga kifi ko nama
alhalin ba shi ya siyo ba. To fa yini zai yi babu sukini da walwala. Sai dai wani
zubin na kan auni mangyada ko manja na zuba a galan din namu, ko na sayi ledar
maggi. Wannan bai cika fahimta ba. Tunda wani lokacin zai siyo gwangwani biyu a
leda ya juye a ciki.
Dan haka a duk lokacin da ya samu sararin siyo kwalba, kwanaki ka'dan nima zan sake
siya na zuba. To baya ankarewa da hakan.
Abin da na lura bai dauki maganar da aka yi na ce wa ba zai iya ciyar da mu ba da
sau'ki.


*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*

✍️
*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta
sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar
taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi
muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun
san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa,
mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai
soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan
littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan
numbers*
*08089965176*
*07084653262*

*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin
register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633

55&56.
Ranar asabar ya dawo da rana. Sai ga shi da macaroni guda biyu hakan ma taliya, da
shinkafa mudu guda. Sai sauran kaya danginsu maggi da sauransu.
Na karb'e shi da walwala kasancewar ba kasafai nake yin k'unshi asabar da lahadi
ba. Sai kitso ne yafi yawa a wadannan kwanakin, saboda ana hutun karshen mako.
Doguwar riga ce ta yadin material din *Umm Nihla collection*
*07020695644*
A lokacin kuwa watanmu kusan bakwai da aure.
Da na lura sai na ga kamar ba a cikin nutsuwarsa yake ba.
Na gabatar masa da ruwa da abinci.
A hankali ya ce "sai na dawo zan ci. Dauko mayafinki mu je gida".
Gabana ya takarkare ya buga. A ki'dime na ce "Me ya faru?"
Ya numfasa ya ce"Dada ce ta.."
Kafin ya karasa na katse shi ta hanyar saka salati mai tsananin gaske. Tare da ce
wa "Ta rasu?" Na fara k'walla ina cewa "Dada yau kwana ya k'are Innalillahi wa inna
ilaihir rajiun". Allah ka gafarta wa Dada!
Ya bu'de baki ya ce "Yaushe na ce "Ta mutu? Kin san yanzu damina ta tsananta. Ta je
zagaya wa ne sai shaddar ta rufta da ita. Allah ya sa an ji k'arar ruftawar, da ba
haka ba kam, da tuni ba wannan maganar ake yi ba. An ciro ta amma baki ga ba, duk
ta daddauje sosai."
Bansan ya aka yi ba dariya ta sosai ta k'wace mini.
Na dinga k'yal-k'yale wa. Ya yi sak'are yana kallo na. Can ya kasa jurewa dariyar
da nake faman yi babu k'ak'kautawa.
Ya kalle ni ya ce "Ban da dai lamarinki akwai k'uruciya mene ne abin dariya a ciki?
Dada fa na ce miki ta fa'da shadda. Da kuma rai ya yi halinsa me zaki yi?"
Cikin dariyata na ce "Kuka zan yi mana. Baban Kasuwa nake yiwa dariya da ya kasa
gyara band'akin gyatumarsa da take nuna masa soyayya ta daban shi da ahalinsa."
Gau na ji ya hambare mini baki. Ya d'aure fuska ya ce "Idan zaki iya yiwa k'anin
ubanki rashin kunya, to amma kuwa ba a gabana ba. Domin kawuna ne k'anin uwata na
kuma yarda k'aninta ne. Da zuwa na yi na dauke ki, ki gaisheta ganin kusan kowa na
gidan har Ubaida. Amma tunda zaki dawo da rashin kunyar ki, sai ki zauna ki yi ke
ka'dai".
Ya mike ya fice. Na bishi da gudu. Murya a marairaice na ce "Zan bika Tijjani dan
Allah".
Ya zuba mini ido yana yi mini kallo mai tsananin gaske. Na sani so yake na ba shi
hakuri, ni kuwa ban ga me na yi ba. Ai gaskiya na fa'da. Bayan haka ai ya buge mini
baki, dan haka na waske na k'i ban bada ha'kurin.
Kallon ya shige ni, na fara bubbuga k'afa. Ina ce wa "Saboda Allah me na yi maka?"
Ya jijjiga kai ya yi tafiyarsa, ba tare da ya ce uffan ba.
Ni kuwa da na hasaso Dada a masai sai na sake tuntsire wa da dariya.
Sai yamma lis ya dawo. Kai tsaye falo ya shiga. Na bi shi ina masa sannu. Na zauna.
Ya ce "zubo mini abincin".
Na fita na kawo masa, ban zauna ba sai da na dauko masa ruwa a fridge.
Sai da ya gama cin abincin. Sannan na kalle shi bayan na d'aure fuska na ce "Ya
jikin Dadan kuwa?"
Kai-tsaye ya ce "Da sau'ki. Amma ta samu tagarde a hannunta."
Na sake yin kalar tausayi na ce "Ayyah! Allah ya bata lafiya."
Ya amsa da "ameen" yana daddana wayarsa.
Can na nisa na ce "Tijjani wa ya yiwa Dada bik'in kashin da ta kwaso?"
Kamar ba zai yi magana ba. Sai kuma ya ce "Gwaggo ce".
Na zabura na dafa k'irjina na ce "Gwaggota?"
Kansa na k'asa ya ce "ita fa".
Kawai sai na fara kuka ina cewa "Na rantse da ina nan bazan bari ba. Duk yadda take
tsangwamar ta sai kuma ta zo ta yi mata irin wannan wahala alhalin tana da
y'ay'anta birjik?"
Kansa na kan wayarsa dai, ya ce "Ai da yake tana mutunta mijinta ne. Baban Marina
aikin ya kama, da yake ita mace ta gari ce, sai ta fanshi mijinta".
Na zabura na ce "Wallahi ba shi ya kama ba. Ina ce ga Baban Tsakiya nan, ga kuma
dan k'wai Baban kasuwa, dukkansu suna da matan auren kuma".
A fusace ya ce "To basu yi ba, ita Gwaggo ita ce ta yi domin tafi dacewa ta yi
aikin".
Na harzuka na ce "Ban gane ba Tijjani. Wato ita ce kaskantacciya kake nufi ko me?
Ai ba ita ce babba ba, ga Mama nan".
Ya dago ido cikin ido ya ce "Asiya na ce miki da ita aikin yafi dacewa shiyasa ta
yi d'in".
Na mike na ce "Wallahi aikin bai dace da ita ba kai ma ka sani. Y'ay'an cikinta ne
a hak'ku. Baba Maryo fa?" Ga mamakina sai na kasa ambato Baba ta Bulkachuwa.
Shima ya mike ya ce "jikinki na yi miki k'aik'ayi Asiya Toro. Bilhiillazi kika yi
gigin zaginsu a gabana sai jikinki ya fa'da miki. Bazan dauki wananan mugun halin
ba. Ke abu ba zai wuce a wajen ki ba? D'azu dukkansu sai da suka tambaye ki, amma
ke kin k'wafesu a cikin zuciyarki".
Na ja tsaki na ce "Kana yi mini dukan da jikina ya fa'da mini. Ka tabbatar kai ma
sai naka jikin ya fa'da maka. Domin kuwa dai ka daki aurenka tunda shine lasisinka
na dukan jikin nawa".
Ya kasa ce wa komai. Amma na lura ba k'aramin b'acin rai ya shiga ba.
Ya kewaye ni ya fice. Bai dawo gidan ba. Sai wajen goma. Ni kuma tuni na sake
fusata. Dan haka da ya dawo ya shigo d'akina ban ko kalle shi ba, bare nasan me
yake ciki.
Ga mamakina shima bai kalle ni ba, ya koma k'arshen gado ya kwanta.
Washagari ma da asuba ya fice, k'ofar d'akin ya buga da k'arfi. Wanda na gane
tashina ya yi dan na yi sallar asuba.
Ya dawo ya ajiye burodi. Ya ha'da nasa shayin ya karya ya fice.
Na yi abinci na ajiye masa na rana, amma bai dawo ba.
Da yake lahadi ne. Mutum biyu sun zo lalle, haka kitso ma mutum uku na yiwa. Kafin
la'asar babu kowa.
Duk da zuciyata babu da'di a dalilin yadda na lura Tijjani ya tsananta fishin da
yake yi.
Wayata na dauka na shiga manhajar WhatsApp. Sai ganin Umm Nihla ta yi posting
hadaddun materials daga Malaysia. Ina matu'kar son irin yadukan. Ba don komai ba,
sai dan basu da nauyi, sannan gasu da taushi, ga kuma sau'kin ku'di ainun. Abin
burgewa kuma basa kodou sai da ka gaji da su ka bayar.
Wani yellow da blue suka tafi da ni. Kai tsaye na ce mata ina sonsu. Ga mamakina
duk ku'din basu yi tsanani ba.
Ta tambayi a wanne garin nake? Na bata amsa da Toro. Ta ce to sai a saka miki a
motar Jos kenan?. Tunda kunfi kusa akan Bauchi.
Na ce "A a akwai sister ta Aisha Lame jakadiyar oriflame. Ita zaki aikawa zasu same
ni.
Ta yi mamakin cewar nasan Aisha Lame.
Na ce "To ai yar garinmu ce. Sannan muna da alaka ta wajen kakata da ta haifi
Babana.
Umm Nihla ta turo emojin mamaki ta ce "Ai kuwa Aisha na da kirki, kafin na bar
Nigeria a wajenta nake siyayyar kayan kwalliya da spices. Farashin kayanta mai
sau'ki ne ainun".
Cikin alfahari na ce "Ai ko anan haka ahalinsu suke, mutane ne masu kirki kwarai da
gaske. Nima da aurena ta bani kyautar fame wash. Yanzu kuwa na tura mata ku'din
wani zan siya saboda na gane muhimmancinsa".
Daga haka ta turo mini asusunta da zan tura ku'din.
Sai mamakin yadda duniya ta samu cigaba nake yi. Ina Toro amma na sayi kaya a
hannun wacce take zaune a Malaysia. Har na tura ku'din, ta tabbatar mini ta ga ni.
Nima kuma ina da tabbacin zuwa gobe zan ji Aisha Lame ta karba mini. Na saki gauron
numfashi.
Na fara lissafin ku'dina domin so nake na yi k'undubalar fara shafa man oriflame.
Idan nafi haka sheki da d'aukar ido zan fi daukar hankalin Tijjani fiye da yanzu.
Haka na lalubo lambar Aisha Lame cikin sa'a tana online, ita da kanta ta za'ba mini
Wanda yafi dacewa da farare. Itama take na tura mata ku'dinta. Na fa'da kuma za'a
kawo mata material d'ina ta ha'do ta aiko aiko mini. Muka yi sallama.

Yau ma sai bayan Isha ya dawo. Ban kula shi, shima bai kula ni ba.
Kwanaki uku muna fishi da juna. Abin na cina a zuciyata, amma na daure na matse na
share shi. Mussaman da bai shata mini layi da dakin sana'ata yadda yake yi a
watannin baya ba.
A kwana na hudu Gwaggo ta yi mini waya a lokacin ina tare da masu lalle.
Muka gaisa ta ce "Yabi ba zaki zo ki gaida Dada ba ne? Kaf yaran gidan nan kowa ya
zo ban da ke. Kuma kullum sai Tijjani ya zo ya duba ta. Amma daga ke har shi baku
yi hankalin ki zo ki duba ta ba. Sai ta mutu ki zo gaisuwa ne?"
Jikina ya yi sanyi na ce "Zan zo. Shine bai ce na zo ba".
Da sauri ta ce "Ke ma k'aramab niyya ce da ke. Nasan Tijjani ba zai hana ki zuwa
gaida Dada ba".
A sanyaye na ce "Ki yi ha'kuri zan zo In sha Allah".
Ta saki gauron numfashi ta ce "Ya dai kamata".
Sannan ta kashe wayarta.
Kamar almara ana idar da azahar ranar sai ya dawo.
Cikin sa'a na gama yiwa wacde nake sawa. Saura mutum biyu su kuma dama sai mun yi
sallah.
Ban yi abinci ba tunda ba dawowa yake yi ba. Ko cefane ne idan ya kawo mini. A
k'ofar gida zai bawa yaro ya shigo da shi, ya yi juyawarsa.
Na bishi falon. Murya a dakushe na ce "Sannu da dawowa".
Ya amsa babu walwala.
Sannan ya ce "yunwa nake ji. Me kika dafa?"
Na dauke kai na ce "Ban yi komai ba, tunda nasan cikina kawai zan yiwa".
Shima tasa fuskar a daure ya ce "To sai ki dora yanzu. Sauri nake yi kuma".
Ban ce komai ba, na juya na shiga kicin din. Na dora farin ruwa dan nasan ina da
miya a fridge.
Daga nan na nufi bayi dan yin alwallah.
Sai da na zuba makaroni sannan na yi dakinmu dan yin sallah.
Bayan na idar na shiga falon na dauko miya. Na tarar ta nuna. Na ta ce na dauraye.
Na dora miyar dan ta d'umama.
Na shirya a tire na kai masa. Bai nemi na zauna muci kamar yadda muka saba ba. Nima
kuma ban zauna di'n ba. Na tafi na cigaba da yin lallena.
Ya gama ya fita.
Har dare ina ta sakar yadda za'a yi a gobe na je na gaida Dada.
Muna kwnace kowa na k'arshen gado. Dukkanmu mun kasa barci da alamu akwai abin da
ya damemu. Ni dai nasan yadda zan fita gobe nake ta tufka da warwara.
Tsawon lokaci muna hakan. Sai kuma na ga ya mirgino ya same ni a jikin bangon da na
lafe.
Bai ta'ba ni ba. Amma ya mannu da ni sosai. Murya k'asa k'asa ya ce "Asiya Toro
idan muna fa'da ai bai kamata mu sanya aurenmu a cikin rikicin ba. Kawai mu yi
harkar aurenmu. Allah bar shi da safe muci gaba da gabarmu tunda bani da darajar da
zaki mini laifi ki bani hakuri".
Nan da nan na gano jarumtarsa ta kare ne. So yake mu kebe. Maimakon na yarda tunda
nima na kosa da gabar sai kawai na kwabse na ce "Sawa na nawa kuma? Ai tuni ka
sanya shi a ciki. Yau kwananka nawa da yin fatali da shi?"
Ya ru'ko hannuna a hanzari ya ce "To yau na cire shi Asiya. Mu shiryasu kin ji. Mu
din ma, ko yanzu kika bani hakuri mun shirya. Kin bata mini rai. Wai har ki ce
mini zan doki aurena. Ai ban zaci har yau ba kya sona ba Asiya".
Yadda ya yi maganr sai ta yi matu'kar ta'ba ni. Ban san me yasa yake yawan bani
tausayi ba.
Na numfasa na ce "Nima ai ka bata mini rai. Akan me zaka dinga duka na? Ko ka dinga
yi mini barazana da duka. Ai na dauka ko wani ka ga zai dokar maka jikin nan nawa
sai yadda karfinka ya k'are, ba wai kai da kanka ba".
Da sauri ya ce "Bilhiillazi ba wanda zai doke ki a duniyar nan na bar shi ya kwashe
kalau. Sai ko Gwaggo da Baban Marina. Amma kowa ye zan motsa k'wannjina a kansa. Ni
kuma ai ba haka siddan nake dukan ki ba. Sai na ga zaki kuskure. Sannan kuma ai ba
mai yawa nake yi ba".
Na cuna baki duk da a duhu ne na ce "To ni dai bana so, ka daina".
Da sauri ya ce "To. Amma kema ki daina yi mini taurin kai da rashin kunya. Idan na
ce miki ya isa, ko bari. To ki bari din kawai".
Ban amsa ba, amma na ji, zan kuma kiyaye.
Ya nisa ya ce "To me zaki ce mini?"
Na fara tirza kafa ina kukan shagwaba tare da cewa"Ai tunda ka buge mini baki
shikenan an yi zuza. Kuma ba sharri na yi musu ba. Gaskiya na fa'da.".
Ya ru'ko ni ya ce "Amma tunda raina ya baci, kuma har na fa'da miki ba, sai ki
rarrashe ni, ki kwantar mini da hankalina ba?"
Na dinga k'unk'unin ina fa'din "Ni ba wani rarrashin k'ato da zan yi".
Da yake bai ji me nake fa'da ba.
Ya jani jikinsa ya rungume. Ya dinga shinshinata tare da sakin maganganun masu
nauyi.
Ni kuma na cure jikina, na dunk'ule. Na dinga ja masa rai. Ban yarda na sallama
masa ba. Sai da na ce "Yaushe zan je na gaida Dada?"
Murya na rawa. Ya ce "Kina ce mini sorry gobe zan kai ki tun safe ki yini a can".
Da murna na ce "idan ban ce maka ba fa."
Ya ce "Zan kai ki, amma minti talatin tana cika zan tiso ki a gaba mu dawo gida".
Sanin da na yi da gaske yake yi, ya sanya na bu'de baki cikin walwala na ce "Ka yi
hakuri Tijjani".
Nan da nan ya sake rungume ni sosai ya ce "Thats my little girl. Na huce, na kuma
yafe miki. Daga Nan abubuwan da suka biyo baya masu nauyi ne. Domin Ni da kaina na
tabbatar na yi missing Tijjani da jagwalgwalonsa masu sanya ni tsumaye. Abin da ban
yi zaton zan yiwa Tijjani ba, sai da na yi masa a wannan daren. Wanda ba karamin
gigita shi na yi.
Da safe ya tashi ya dinga yi mini hidima da bare-bare. Ni kuma kunya ta yi mini
k'awanya.
Da wuri muka shirya ya kai ni gida da kansa. Ya kuma ce sai an yi sallah isha zai
zo mu tafi. Sai da zamu shiga gidan ya bu'de but din mashin d'insa ya fito da lemon
maltina guda biyu da lucozade shima biyu a leda. Ya mik'o mini ya ce "Ki bata".
Na kar'ba tare da cewa "Na gode! Ni ban yi tunanin na siya mata komai ba".
Bai ce komai ba, muka shiga gidan. Nan kuwa jakar hannuna cike take da omon viva
85kg zan bawa su Gwaggo. Da kuma alwar da zan raba wa kannena.
Tare muka gurfana da shi a gaban Dada muna gaisuwa cikin tausayi da alhini. Bansan
ai haka ta jigata ba. Kanta har a lokacin a suntume ya ke. Ga hannu a targade ya
sha nadi da bendeji. Ga fuska da k'afafuwa duk sun kuje sosai.
Duk yadda ta ji jiki, har jikin ya yi yaushi amma bakinta ras. Ta kalle ni ta ce
"Ai Yabi Allah ne yasa da sauran kwana a gaba. Gaba'daya ji na yi tamkar wadda
k'asa ta dare na afka. Kai wato wanda yake yawaita ro'kon Allah da neman kariya
daga tsautsayi da asara zai ga sassauci a lamarinsa. Ni nasan k'addara bata sauya
wa. Amma k'arfin addu'a yana rage zafinta. Na gode wa Rabbani da ya sanya ni cikin
bayinsa masu yawan ambatonsa masu kuma yawan gode masa."
Tijjani ya ce "Haka ne Dadarmu".
Ta muskuta, na kalle ta tausayin ta ya sake kama ni a dalilin nasan bata ji dadin
zaman ba.
Ilai kuwa kafin na yi wani abu. Sai cewa ta yi "Mai sunan manya matso ka gyara mini
zaman nawa. Gaba'daya a takure na ke."
Da sauri ya matsa cancakat ya cira ta. Ya ce "Asiya sa hannu ki gyara mata
zaninta".
Na gyra mata din cikin azama".
Ya mayar da ita ya tokare mata baya da filo mai tauri. Ta ce "Allah ya yi maka
albarka mai sunan manya. Allah ya tsare ka daga tsautsayi da asara. Allah ya sa
kafi karfin magauta. Ubangiji ya bu'de maka k'ofofin alheri".
Ya dinga amsawa cikin walwala.
Na k'ulu, wato Tijjani kawai zata yiwa addu'a.
Na daure na ha'diye ban fashe ba.
Can ta zuba mini ido. Sai kuma ta koma ga Tijjani ta ce "Mai sunan manya da alama
komai ya dai-daita. Wannan haske da sheki da cikar da Yabi ta yi ba iya na abici ba
ne kawai. Ana takar ta sosai gaba'daya ta fara bude wa"
Ba ni ba, hatta shi kansa maganar ta yi masa nauyi ainun. Ya yi maza ya sunkuyar da
kansa ba tare da ya ce uffan ba.
Ita kuwa ko a jikinta sai faman murmushi take yi tana fa'din "Alhandulillahi. Allah
kasa zan ga jininka kafin duniyata ta kare".
Na mike bayan na tura mata ledar gabanta na ce "Ga shi nan Dada. Allah ya k'ara
lafiya bari na tafi inda nima za'a yi nan nan da ni. Kin riga kin saba da hubbu
ra'as. Tunda muka zauna ba kya ta tawa. Sai mai sunan manya, mai sunan manya. To na
barku ku k'arata".
Ta k'yal-k'yale da dariya bayan ta ja ledar tana ce wa "Wayyo Yabi mai dogon hannu.
Da'dina da ke akwai ungo. Duk cikin jikokina na d'aki ke ce kika kawo mini tsarabar
dubiya. Ko wacce da sun zo da mijinta ta ga ya bani dubu ko dari biyar shike nan
sai ta ja ta tsuke. Wai suna nufin mazansu sun fanshesu. Har Nasiba haka ta zo mini
hannu na dukan cinya. Ita kam mijinta bai zo ba, bare ya bani.
Amma mijinki kullum ne. Sai ya kawo mini kunshin nama, ko lemo da ayaba. Ai yanzu
na ga ne biki mai zuciya a ke fa'dawa ba mai dukiya ba".
Na ce "Ke kuma Dada da son a baki ki ke. Ban da haka ina lafi ma da aka zo aka duba
ki?"
Na kalli Tijjani na ga ya kyafta mini ido, alamun na bar maganar haka".
Na sanya takalmi na ce "masa na yi cikin gida. Sai ka shigo".
Na tafi na bar shi tare da ita. Ina jin tana cewa "Ah yarinya ta yi bundum ta yi
cikar daki. Ni dama nasan ruwan wankan aure duk zai sanya muku nutsuwa."
A zaure muka yi kicibus da Yaya Anwar yayan Nasiba. Na gaishe shi da mutunta wa
domin shi d'in kamamme ne.
Ya amsa tare da ce wa "Yabin Bulkachuwa yau a gidan Marina? Tunda aka yi aurenku ke
ce ban ga kin zo ba. Bulkachuwa ya rufe ki ruf. Ma sha Allah! Allah ya k'ara ha'da
zuciyoyinku".
Kunya ta kama ni. Na wuce ban ce komai ba. Amma sunan da ya kira ni da shi ya sanya
mini wani irin shauki a zuciyata. Duk kame kamena na fara gasgata cewa na fara son
Bulkachuwa. Irin son nan mai shiga a hankali ya yi karfi mai tsananin gaske. Ga shi
wani irin kishinsa nake yi irin wanda ban ta'ba jin irinsa akan ko wanne namiji ba.
Kawai ina waske wa ne dan kar ya fahimci halin da na ke ciki. Tunda shima na
fahimci mai iyashege ne.
Ina shiga k'ofarmu aka dinga yi mini oyoyo tamkar ba Yabin

Please Login or Register in order to submit comment