You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gashi babu wahalar fa'da.
Na maze domin tsokanar ta zan yi, dan na ga reactions d'inta.
Na ce "Dada ki daina jan carbi fa, babu kyau Annabi ya ce mu yi da yatsun hannunmu
domin su mana shaida ranar gobe".
Ta b'ata fuska kamar ba zata yi magana ba, sai kuma ta kufula ta ce "Asiya tun
kafin a haifi Ubanki nake jan jarbi, duk wani sabon addini da kuke son kawo wa na
raini Wallahi ba zai yi tasiri a wajenmu ba".
Nasiba ta fashe da dariya yayin da nake jira ta tara mini gayya irin wanda ta mini
watannin baya, amma na ji muk'us.
Na jijjiga kai a raina sai fa'di nake "Allah ka sake bawa Yabi tsaron da ba za'a
dinga tozarta ta ba." Ta ja robar maganinta da Honarabil ya kawo mata na warwarewar
gajiyar tsufa da kara kuzari. Sai kuma na daidaita siga da bugawar zuciya duka daga
kamfanin G.H.T. Na murmusa ina tuna a wajen FASEELAT ba zai kai kudin da na ga ni
a manne a jikinsu ba. Na Santa a littafin Guduyo.
Nemi dukkan nau'in kayan ght daga gare ta cikin RANGWAME.
*07039269802*
Muna cikin haka sai ga Yaya J.
Ya sha kwalliya da wani farin yadi, d'inkin ya zauna masa sosai.
Ga kamshin turaren Dagmar ya baibayemu.
Cikin farin-ciki Dada take fadin maraba da Jabiru angon Maijidda".
Zuciyata ta buga da k'arfi, shi kuma ya dan diriri ce.
Ya waske da ce wa "Angon Dada dai, ai ke ce ta karfen".
Ta yi dariya ta ce "Yaudara ke nan."
Ya gaishe ta ta amsa da walwala tana tambayar amaryarsa.
Ya bata amsa da ce wa"Tana lafiya a gajar ce.
Ya shige cikin dakinta yana cewa "Zo mu yi sirri Dada".
Ta rarrafa ta bishi domin kuwa mutuminta ne baya rabuwa da kawo mata tsire da
turare.
Ita kuwa duk wanda zai mata ungo tana mutunta shi.
Muka ci gaba da hirarmu wacce galibi Nasiba tana fa'da mini ciwon da take ji akan
sharewar da Bulkachuwa ya yi mata.
Fa'di take "Dan Allah laifina ne?
Inda ya fahimce ni, da ya k'arfafa soyayyarmu ai komai za'a mini bazan kula kowa
ba, amma daga maganar fatar baki ya d'ife, ya ce kada na kuma shiga sha'aninsa. Da
yana sona ba zai yi irin wannan fishin ba."
Ta fa'da k'walla na zubo mata.
Jikina ya yi sanyi ainun domin kuwa Bulkachuwa ya riga ya yi rantsuwar ya yanke
hulda da ita.
Kamar daga sama na ji muryar Dada cikin karadi tana cewa "Ina! Jabiru ka zo da
*BAK'AR TA'ADAH* Mai wahalar tabbatuwa, ta ya ya zaka ha'da mini jikoki kishi? Dama
kuma ba jituwa suke yi ba.
Ha'kuri zaka yi da Yabi domin tuni ta samu miji ita ma, dattijon arziki irin
albarka."
A sanyaye na ji yo shi yana ce wa "Idan ban samu goyon bayan ki ba akwai matsala
Dada.
Kin sani Yabi nake so tun fil'azal. Amma saboda na yi biyayya ya sanya na karbi
auren Maijidda. Yanzu da nake son na cike wanccan burin nawa ba sai a taimake ni
ba?".
Ya dinga magiya, tamkar zai fashe da kuka.
Cikin kad'uwa ta ce "Jabiru ka zo da babban al'amarin da yafi Dutsen dala nauyi.
Bana jin iyayenku ma zasu amince maka, ka bar maganar nan tun baka tono wani bacin
ran ba".
Ba shakka ko nauyi ya ce "Ba zan barta ba Dada! Domin da zan iya barinta da ko ke
baza ki ji ba.
Idan ba zaki taimake ni ba, to ki mini adalci kada ki b'ata al'amarin a gaban
iyayenmu".
Ta ce "ita Yabi ta gamsu zata aure ka ka had'asu da Maijidda?"
Da sauri ya ce "Ina da tabbacin soyayyarmu ba zata yi zangwayenwar da babu alfarma
ko fahimta ba, ban tuntu'beta ba, amma ina da yakinin ba zata juya mini baya ba".
Tsawon lokaci sun yi jigum jigum, muma da muka bar maganarmu muka kashe kunne muna
jiyosu, jikinmu ya yi la'asar".
Nasiba ta ce "Tabbas soyayyar da take ta gaskiya kuma k'arfaffa ce ake yin afuwa da
sassauci a cikinta."
Na kasa cewa komai domin hausa ta yi cikin hikima. Da Bulkachuwa take.
Bansan ya aka yi ba, kawai sai ganinsa na yi ya fito ya fice a hanzarce.
Sai ga Dada ma ta fito cikin rashin sukuni.
Ta zauna jiki a sanyaye.
Ta kasa jure wa ta kalle ni ta ce "Yabi Jabiru zai ballo wani irin tashin hankali,
kada ki sake ki saurare shi.
Ki rike Alhaji nan yafi miki, ina tsoron abin da zai biyo baya."
Na yi k'uri ina kallonta a zahiri gaskiya ta fa'da tashin hankali zai iya biyo
baya.
Amma kuma a zuciyata sai nake ganin son zuciya ne kawai yasa ba zata goya masa baya
ba. Dan kawai Maijidda d'iyar shalelenta ne, kuma mawadacin gidanmu. Dan sai yanzu
na fahimci ba fa wai ku'di ne da Baban Kasuwa ba, kawai a gidanmu ne yafi kowa
wadata, saboda talakawa ne mu na sosai.
Me yasa a farko bata hana a bashi ita ba, tunda tasan ni yake so?
Me yasa a wanccan lokacin ba ta yi zaton hakan zai zama tashin hankali a dalilin
gaba da kullaci da zai shiga zukatan y'an gidan gaba'daya ba?.
Duk yadda nake da ba'kin jinin a cikin ya'nuwana sai da suka yi kishin abin da aka
yi mini, suka yarda ubanmu aka tozarta.
Tashin hankali tuni an shige shi ai, kawai sa'ar da aka yi Baban Marina mai
sassauci ne, shi yake ta tsawatarwa dan kada mu kullaci y'anuwansa ko muce zamu
rainasu.
Amma iyakacin wula'kanci da kaskanci an yi mana.
Ba kuma wanda ya k'alubalanci hakan sai Baba ta Bulkachuwa ita ma kuma bata da
power kamar Babanmu. Duk da a cikin rufin asiri take, dai-dai gwargwado tana dan
tagazawa wajen yiwa Dada hidima. Haka nan ita ka'daice kafatalin yan'uwan Babanmu
zata aiko da wani abu da sallah ta ce a bawa y'ay'ansa.
Wani lokacin sark'a da yan kunne, ko hijabai, ko y'an takalma masu sau'ki haka.
Dan ko sallar da ta wuce da hijabanta muka je sallar idi ni da Nazira.
Amma Baba Maryo uwarsu Nasiba da bata iya tsinana komai har a Dadan ma ita take
zuba mulki, haka nan komai aka yiwa Dada na dangin sutura ko wani abu mai k'yau
karshe sai ya zama nata ko na y'ay'anta, ita kuma saboda auta ce da ta shiga rai.
*BAK'AK'EN TA'ADODI* masu yawa na faruwa a gidanmu da dole duk kawaicinka sai
zuciyarka ta motsa sa'i da lokaci.

✍️

*Ina tallata muku kayan gyara na mussaman na mutanan Sudan da chadi*.
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin Tsumi da Zaki dafa da kanki, ki ajiye ki sha sosai ya ratsa miki jiki*
*Y'aya'n gadali na mussaman*
*Hadadden daka emergency*
*Tsumin kwakwa da zuma*
*Turaren matsi na tsugunno*
*Maganin sanyi sadidan na mara har ma da gabobi*
*Gumba*
*Goran tula syrup and fruits*
*Tsumin Goran tula na asali*
*Duk zaku same su da RANGWAME kuma na asali me ba karabiti ba.*
*Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*.
*Tuntube ni a wannan lambar*
*08032773332*

✍️


*BAKAR TA'ADA*
*NA*
*SURAYYA DAHIRU GWARAM*
*(MRS M.I.NASHE)*

*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}```
✏️
____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•



*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*


*Last free page*

*500regular page*
*VIP 1k twice pages*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim Dahiru*
*Zenith Bank*.
*Ko*
*7061488065*
*Surayya Dahiru Ibrahim.*
*Opay Bank.*

*08032773332*.

19&20.
Jin na yi shiru tsawon lokaci a dalilin tunanin da nake ta yi.
Ya sanya Dada ta ce "Yabi da alama zaki bawa Jabiru ha'din kai".
Na yi murmushi na ce "A a sai dai na yi imani Ubangiji ne yake shirya komai, dan
haka shi na barwa al'amurana ya yi mini zab'i.
Dama kuma ban k'ullace shi ba domin ba shine ya mini laifi ba, sannan Dada idan har
auren Maijidda da aka sanya ya yi ya bar ni, bai zama abin kaico da rikici ba, ashe
kuwa nawa auren da yake hak'ilon yi a yanzu adalci ne da tsantsar gaskiya".
Jikin Dada ya yi tub'us tabbacin tasan gaskiya na fad'a.
Da k'yar ta ce "Ana barin halak dan kunya Yabi".
Are yi murmushin da yake nuna ba wananan maganar.
Ta sake ce wa "Kuma yanzu wannan dattijon arzikin sai ki bar shi, duk dawainyar da
yake faman yi dake da dukkan dangin ki?"
Na sake murmushi na ce "To ai aure gaibu ne, sannan Allah ne ya gadar wa maza su yi
ta hidima da macen da suke so dan su ja ra'ayinta. Abin farin cikin ba rok'arsa
nake yi ba, haka nan wani nawa bai ta'ba rok'arsa ba."
Ta yi shiru ta rasa me zata ce kuma.
Sai ta hau addu'a da kamun k'afa a wajen Shehu kada zuri'arta ta rikice a dalilin
wannan al'amarin.
Har k'asan raina da al'amarin zai yiwu ba wani nauyin da zan ji, domin nawa ne aka
k'wace mini saboda kawai zuciyar ahalin gidanmu a cike take da gilli da ba'kin ciki
mai yawa.
Kwanaki biyu kullum sai na ga Yaya J ya zo gidanmu, kusan a nan yake yini, ba shi
k'ofarsu ba shi a wajen Dada.
Rashin sukunin da nake ga ni a tare da shi, ya tabbatar mini kasafin ya cud'e fiye
da zatonsa.
Bai kuma neme ni ba.
Kwanaki suka yi ta shud'e wa har aka samu kwanaki bakwai babu tartibiyar maganar
Yaya J.
Dama na sani mawuyacin abu ne su amince, sai dai dan ya ce zai iya ha'diye gatari
ne, shi yasa na sakar masa k'ota ko zai dace ya ha'diye, bayan ya sha kakarin
tagwaitakar riskar ajali.
Ina cikin wannan yanayin sai ga wani b'acin ran, gidan da Bulkachuwa ya tura su
Baba akai masa ku'din aure suka shafa wa idonsu toka suka ce basu san wannan
maganar ba, ba zasu dauki y'arsu su bawa wanda aka bulale a bainar nasi bisa
k'azamin laifi irin wannan ba, kuma marar tartibiyar sana'a.
A sanyaye su Baba suka dawo babu kuzari.
Dukkan iyayenmu ukun nan sun ji ciwon abin da aka yi musu. Amma ba wanda ya hango
irin wannan tozarcin mai ciwo suka yiwa Babanmu ta hanyar hana Yaya J aure na.
Shi kuma Baban Kasuwa ya dauki tasa y'ar ya ba shi.
A gabana Baban Marina yake yiwa Bulkachuwa bayanin halin da ake ciki, cikin alhini
da bacin rai.
Ba wata damuwa mai yawa ya ce "Babu damuwa Baba! Ban damu ba, domin an hana ni aure
a cikin gidan nan ma. Dan haka dan waje sun hana ni ba zai zama abin kaico ko
tashin hankali a gare ni ba.
Ciwon da nake ji daya ne! Da na yarda da hukuncin Allah. Na amince aka mini bulala
sai kuma na zama abin k'yama a idon al'umma.
A wauta ta imani na yi, domin na yi biyayya ga abin da Allah ya zartar ba tare da
bin ra'ayin turawa na yiwa hukuncin Ubangiji tawili ba.
Na sani na yi laifin da ku kanku na zubar da darajar gidanku, amma ina yiwa Allah
kyakkawan zato zai katange ni daga sake aikata wa tunda na yarda da hukuncinsa, na
zabi tereren duniya akan na lahira.
Matu'kar kuwa mutane zasu ci gaba da nuna irin wannan *BAK'AR TA'ADAR* Akan mai
laifin da ya d'aura d'amarar taubatun nasuha ba shakka zasu dauwamar da mutum cikin
b'ata, tunda idan ya dawo kan sahihiyar turba, ba zasu karbe shi ba, ba zai tsira
daga yamididinsu ba."
Baba ya kasa ce masa k'ala domin jikinsa ya yi sanyi da kalaman na Bulkachuwa.
Ni kaina da nake gefensu ina wa Baban Marina wanki ba k'aramin sanyaya jikina
kalamunsa suka yi ba.
Na sani gaskiya ya fa'da, hana shi aure da ake yi kuma ba shine mafita ba, illah
bashi lasisin sake dulmiya cikin zunubin da ake k'yamarsa.
Baya ga hakan basu taimaki y'ay'ansu ba, tunda dukkan y'anmata nasa da aka hana shi
auren su sonsa suke tamkar su bashi kyautar kansu, ashe kuwa idan ya so lalata
rayuwar yaran nasu cikin ruwan sanyi zai yi hakan, tunda Ubangiji ya kyautata masa
halittarsa k'warai da gaske .
Dan haka zai iya amfani da son da suke masa ya lalatasu a banza, idan kuma hakan ta
faru zai yi wahalar gaske ya karbi aurensu domin komin lalace war namiji baya son
lalatacciya. Cigaba aka samu ko tabarbare wa?
A wannan rana na fahimci ashe cikakken mutum ne mai nutsuwa, kawai sharholiyar ce
ta yi masa k'awanya.
Ya katse shirun da Baba ya yi ta hanyar ce wa "Baba na gode sosai, zan cigaba da
istigifari, idan al'amura suka sake daidaita mini zan fara sana'a, zan je
Bulkachuwa na nemi aure ina da tabbacin a dangin mahaifina ko nafi hakan lalace wa
zan samu mai k'arfin halin da zai bani aure tare da fatan auren ya zame mini
sanadin shiriya da bud'ewar arziki."
Ya mike ya tafi yana sake godiya sosai.
Ajiyar zuciya kawai Baban Marina yake yi, na lura ba k'aramin ki'dima ya shiga akan
al'amarin ba.
Murya babu amo ya ce "Yabi idan kina son Alhaji ki ce masa ya turo wakilansa, idan
kuma ba kya sonsa to ki fa'da mini zan sallame shi".
Na yi k'asa da kaina na kasa amsa masa, daga haka kuma sai ya fita, na bishi da ido
amma tunanin a yadda jikin Baba ya mutu murus akan al'amarin Bulkachuwa da ace Adda
Nazira ba ta yi aure ba, Babanmu na iya juya wa nak'asunsa baya, ya bashi auren ta.
A fili na furta "Alhamdulillah da Allah ya sanya ta yi auren ta ta barranta da
auren tantiri ma'abocin *BAKAKEN TA'ADODI*.
Haka kawai sai zuciyata ta buga da tsananin gaske, a dalilin ayyana wa da na yi,
wata'kila fa idan ban tsayar da miji ba, Baba yana iya cewa ya bashi ni.
Nan da nan na tsirtar da yawu saboda kyankyaminsa da ya taso mini.
Gashi dai zabgegen saurayi ne dogo cak mai murdadden jiki tamkar ya fito cikin
Kyawawan Tirkawa(Turkish).
Amma kwata kwata baya burge ni duk da farar fatarsa da bak'ar sumarsa, da suke
rudar y'anmata.
Asalima Y'ar tsama muke yi, sassaucin rikicinmu a dalilin kwamshina ne, domin sosai
yake yi masa alheri.
Ya karbi takardunsa, samun aikin ne dai shiru, amma ana saka rai tunda kwamshina
baya wasa kuma mutuminsa ne. Tuni Yaya Salisu ya samu aiki a asibitin Toro a
matsayin accountant na asibitin tunda dama bangaren ya karanta.
Yaya Rabi'u da Bulkachuwa ne shiru amma akwai kyakkawan zaton suma zai samo musu.
Wananan dalilin ne ya sanya ya daina tsokanata ta hanyar muzanta ni.

*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin
register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*

A fili na furta "dutse a tsakanina da Bulkachuwa ya Rabb".
Ina wankin ina jaddada wa kaina matu'kar Yaya J bai yi yun'kuri mai k'arfi ba, to
nan da lokaci kankani zan bawa kwamishina dama ya fito tun zuciyar Baba bata ayyana
masa wani al'amarin da zai iya kassara ni, ya dauwamar da ni a cikin ba'kin ciki
mai tsananin gaske ba.
Na kammala wankina.
Mama ta fito ta ce "Yabi anjima zan aike ki gidan Nazira".
A ladafce cikin murna na ce "To"
Domin kuwa ha'din baki muka yi da Naziran, saboda na yi ta tambayar Baba zani
gidanta yana hana wa, basan me yasa yake hana ni zuwa ba, amma bai ta'ba yin
k'orafin zuwa koyon sana'ar da nake fita ba kullum.
Duk kuwa da ce wa ake yi shargalle nake yi da sunan koyon sana'a.
Shiyasa Nazira ta ce wa Mama ta bani kwanuka na kai mata kar aba wa marar wayo ya
yi b'arinsu su yi lamba.
Tunda idan ita ce ta aike ni Baban ba zai hana ba, ba kuma zai tambayi aiken menene
ba.
Dan haka a gurguje na shirya na tafi.
Muna zaune ina bata labarin yadda muka yi da J.
Ta galla mini harara ta ce "um um uhum. Ashe dai Yabin bata san ciwon kanta ba. Har
wane ne Jabir kuma?
Idonta ya ciko ta ce "Allah ka sanya sai bayan raina zaki zama matarsa!.
Jikina ya sabe da rawa na ce " Addda Nazi!
Cikin gigita domin ban ta'ba ganin fishi mai yawa a tare da ita irin hakan ba, ita
din mai ha'kuri ce, mai kuma sanyin hali ce tamkar dai ba daga tsatson Mama ta duro
ba.
Murya na rawa na ce "mene ne na wannan mugun fatan Nazira?"
Idonta taf cike da hawaye ta ce "Da kin fahimci yadda na k'yamci al'amarin, da
baki zo gabana da wannan maganar mai bak'i tamkar zunubi ba.
Ban iya fishi ba, shi yasa nake kaffa kaffa da duk abin da zai ha'da ni rikici da
jama'a, domin ni kaina ina tsoron fishina ina kuma yawaita neman tsarin Allah da
shi.
Amma zan fa'da miki, matu'kar kina son ganin fishina da barranta kaina daga
al'amarinki to ki cigaba da yi mini wannan maganar da nake fatan ajalina ya riske
ni kafin ta wanzu".
Sai ta fashe da kuka sosai.
Cikin kuma kukan take cewa "Yanzu duk ba'kin cikin da aka cusa wa ubanmu, duk yadda
aka wula'kanta ki, dan ke ce asararriya har ki kalli dan Baban Tsakiya da sunan
soyayya irin ta aure?
Na rantse miki da Allah idan ace Jabir ne ka'dai namiji a duniya gara ki tabbata
babu aure, ko ni na mutu ki maye wa mijina madadina da dai Yaya Jabir ya same ki.
A haukanki Baban Tsakiya zai bar shi ne?
Ko kuwa kwantaccen tunaninki ya fa'da miki Baban Kasuwa zai bashi aurenki alhalin
tasa y'ar ce matarsa?
Kaico da wannan maganar da kika nufo ni da ita.
Nima cikin kuka na ce ",Takura mini ya yi shine na yi masa gatse dan ya shafa mini
lafiya."
Ta ja tsaki mai tsananin gaske tare da fa'din "Amma shine kike rawar jikin fa'da
mini, idan ba kya so me ya sanya zaki yi mararin sanar mini?"
Ta nisa ta zarce da fa'din "Idan zaki ha'kura da shi ki hakura Yabi. Domin Jabir ba
mijinki bane, na tabbatar duk sanyayyar zuciyar Baban Marina ba zai ta'ba bawa
Jabir aurenki ba, ban da dai ma mai k'arfin halin jure damuwa ne da kuma kawaici da
tuni bai ha'du da ciwon shanyewar barin jiki ba a dalilin abin da yan'uwansa suka
yi masa.
Ashe duk zafin ranki, da kishinmu da kike yi a banza ne a kuma fatar baki ce?
Wallahi matu'kar zaki nemi zama ahalin gidan Baban Tsakiya ki tabbatar kin fita
daga namu ahalin Yabi"
Ta tashi ta bar ni tana kuka sosai.
Jikina ya mutu wato ba k'aramin gaba ba ce ta shiga dangimu ba kenan? Duk ha'kuri
da kawaicin Nazira ita ce take fadin tsauraran kalmomi akan zumunta irin haka?
To idan har Nazira mai sau'kin hali da k'ullaci zata yi hakan to ina ga Yaya Ummi
shakikiyata kuma mai ra'ayin rikau?. Domin ita hatta zumuncina da Nazira adawa take
yi da shi tana ganin ita ce tafi kusa da ni, ita ta cancanci mu yi irin wannan
soyayyar, ta kasa fahimtar tazara mai yawa ce a tsakanina da ita, Nazira kuwa tare
muka taso tamkar tagwaye, kuma Ubangiji ya jefa mana soyayyar juna duk da k'unbiya
k'unbiya irin ta iyaye mata da kishi yake haifar wa.
Bare kuma mazan Gidanmu.
Yaya Rabi'u shine sa'an Yaya J tare suka taso, bayan jini da ya ha'dasu, abokanta
suke yi sosai, amma Yaya Rabi'u da kansa bayan an yiwa J aure da Maijidda na ji
yana fa'dar bai k'i wani a duniya har cikin zuciyarsa irin Baffanninmu ba, yana
kuma fatan kada a k'addara auren zumunci a tsakanin y'an k'ofarmu da tasu ila
yaumil k'iyamati.
A sanyaye na bita uwar d'akinta na dinga rarrashinta da k'yar na shawo kanta ta
ha'diye kukan nata tamkar yarinya y'ar k'arama haka ta koma mini.
Wannan yinin bai yi wani armashi ba tunda zuciyarta ta riga ta baci.
Har na dawo gidanmu a takure nake jin kaina, domin ban ji da'din yadda Nazira bata
sake mini kamar yadda nake so ba.
Na iso gida na tarar da Yaya J gurfane a gaban Baban Tsakiya kansa a k'asa da
alamun kuka yake yana fa'din yayi masa alfarma ya bar shi ya yi abin da Allah ya
hallata masa.
Ba sassauci ko nauyin ganina ya ce "Na gama magana idan baka gamsu ba, ka je ka
nemi wanda zai shige maka gaba, babu damuwa, amma fa babu albarkata a ciki".
Na shige da sauri, ina ambaton "Innalillahi wa inna ilaihir Rajiun".
Ina shiga gida sallar almuru kawai na gabatar na dauki waya na k'ira kwamishina na
ce "Baba ya ce ka turo waliyyainka".
Ya dinga murna yana sanya alheri da albarka, tare da addu'ar Allah ya sanya yadda
na aminta da shi, kada ya kunya ta a idona.
Na ajiye wayar ina mamakin ni kuwa a duniya me na tsare wa Baban Tsakiya ne?
Na dinga Jin haushin kaina yadda na makance ina son Jabir! A yau na yarda na gamsu
tazarar da take tsakaninmu tamkar tazarar sama da kasa ne .
Ba zan ce bana son Yaya J ba, domin kuwa ikon zuciyata ba'a hannuna yake ba.
Amma na yarda da maganar Nazira ko shi ka'dai ne namiji a duniya to haramun ne a
gare ni.
Bayan Baban Marina ya dawo gida bayan sallar isha a tsakar gida Inna ta shimfida
masa tabarma a dalilin zafi da ake fama da shi.
Ya kammala cin abincin da ta gabatar masa kenan.
Ya kalli ni duk da muna da tazara ya ce "Yabi zo nan".
Zuciyata ta harba da tsananin gaske.
Na matsa kusa da shi kamar yadda ya yi mini umarni.
Babu sukuni ya ce "Ya ya maganar Alhaji?"
Kaina a kasa na ce "Na isar da sakon na ka".
Ina rufe baki ya ce "Madallah da Yabi! Ubangiji ya tsare ki, ya sanya albarka a
dukkan sha'aninki".
Farin-ciki ya mamaye ni, na amsa da ameen da karsashi.
Ya sallame Ni.
Na shiga dakinmu na tarar da Gwaggo tana ta kulla siganta hankali kwance.
A zuciyata ina ta jinjina mata na yadda bata raina riba duk kanknatar ta.
Domin sigan nan mafi yawa sai ta yi ciko duk sadda za'a auno mata.
Idan na ce ta bari, sai ta ce da bata siyar wa, da ba zamu sha yadda muke so ba.
A hankali na ce "Sannu da kokari Gwaggo! Allah dai ya nuna mini ranar da zan hutar
da ke zaman kullin sigan nan dan kawai mu saka siga a koko ya ji".
Ta yi murmushi tana fa'din Yabi da dogon buri kike, dama ana wuce yin sana'a ne?
Na ce "Indai bata kawo ku'di ba.
Ta yi murmushi ba tare da ta ce komai ba.
Na bu'de baki zan yi maganar sai kawai muka ji sallamar Yaya Jabir a tsakar gidan.
Baba ya amsa masa tare da cewa "iso mana Jabiru".
Ya zauna a tabarmar ya gaishe shi cikin nutsuwa.
Baba ya amsa cikin sakin fuska tare da tambayarsa iyali da karatunsa.
Tsawon lokaci Yaya J bai iya cewa Baban komai ba.
Sai Baban ne ya ce "Akwai matsala ne Jabiru?".
Cikin rauni sosai ya ce "Baba so nake ka bani Yabi na aura".
Zuciyata ta buga, na yi matu'kar kasa kunne a kansu, ko kwakkwaran motsi bana son
yi.
Hatta Gwaggo tsaya wa ta yi tana saurare.
Murya da walwala Baba ya ce "Jabiru ka zo inda za'a yi maka komai, ina tabbatar
maka da a ce a wani wajen kake son auren da na je na nemo maka.
Sai dai da yake y'ar tawa ce shiyasa bazan iya komai ba. Kana da siffar da za'a
baka aure babu haufi. Amma akwai mishkiloli da baza su bari na baka Yabi ba.
Farko matarka da take hannunka itama y'ata ce da kanina ya haifa. Kasan kuma matan
yau basu dauki lamarin kishi da sassauci ba. Ha'dasu kishi zai iya ruguza komai ya
mayar dasu abokan gaba, sannan zuri'armu zata dare ne, wasu na bawa Yabi kariya,
wasu na bawa Maijidda.
Da ace Yabi ka fara aura, ka zo kana son Maijidda daga baya to ina tabbatar maka da
sai inda karfina ya kare, domin ina da tasirin da zan lank'awasa ta a zauna lafiya.
Amma tunda ka riga ka auri Maijidda a farko, dole a ha'kura da maganar Yabi dan a
samu a cigaba da lallaba zumuncin da ya dan yi saura."
Tsawon lokaci ban ji Yaya J ya ce komai ba tabbacin ba haka ya so ji ba.
Murya ba amo ya ce "Baba kai ne tsanin da nake ganin zan taka dan na samu cikar
burina."
Baba ya numfasa ya ce "Ai kuwa a wannan karon ba zan zame maka tsanin ba Jabiru.
Domin ina sane da yadda Mahaifinka bai amince maka ba, ka yi kankanta da yawa ka
jefa kanka a cikin manyan matsaloli, domin auren da kake son yi ba zaka samu
nutsuwa da shi ba tunda babu albarkar iyaye, sannan su kansu matan naka ba gode wa
kokarinka zasu yi ba, kullum zaka zauna ne cikin zullumin zarge zargensu."
Yana dasa aya Yaya J ya ce "Zan jure Baba, zan iya, da sannu Ubangiji zai hore
mini su gaba'daya.
Sannan ina fatan sanadin wannan auren ya zama silar daidaita al'amura a gidan nan".
Ga mamakina sai jin muryar Baban Marina na yi cikin kaushi ya ce "Jabiru ba zan
baka ba, na rok'e ka, kar ka kuma dosa ta da wannan tatsuniyar domin ko mak'oshina
bata je ba, bare ta shiga zuciyata.
Bana son na yi maka abin da zaka mini kallon marar kirki, ko na rashin inganta
zumunci, amma idan ka cigaba da dagewa to ba shakka zaka sha mamaki, domin kuwa na
riga na haramta soyayyarku a zuciyata, dan haka kai ma ka shafe ta domin ba rayayya
bace".
Bamu gama fita da mamakin maganganun Baba ba, Yaya J ya sake shayar da mu wani
sabon mamakin ta hanyar cewa "To Baba

Please Login or Register in order to submit comment