You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mena yiwa Tijjani da zai mini irin wannan cin mutuncin
a rayuwata?"
Da taushi sosai ta ce "Nutsu ki ji ni! Shawara zan ba ki, ba umarni ba, kinsan
umarni wajibi ne ki mini biyayya. Ita kuwa shawara sai kin so za ki bi. Amma idan
kika bi zai fi miki alheri fiye da barin."
Ta nisa tare da ce wa "Duk runtsi kada ki ce mijinki ya sake ki matukar bai keta
haddi da alfarmar shari'a ko ta aure ba. Sannan ki yi dukkan iyawar ki, kada ki
nuna damuwa ko gazawarki a gaban mahaifin ki Yabi. Ya damu da halin da kike ciki.
Ki daure, ba abin da ba zai wuce ba, sai ikon Allah".
Na yi shiru illah kukan da nake yi mata tamkar zan shid'e. Cikin jarumta ainun ta
ce "Allah ya sassauta miki, ba komai kin ji. To ban da ma kin saka damuwa a ranki
ai bai kamata al'amarin duniya ya susuta ki irin haka ba Yabi. Kinsan kalubalen da
yake gaban ki kuwa?
Kwanciyar kabari kad'ai da muna saka ta a gabanmu da bamu bari kalubalen duniya ya
kidima mu ya shagaltar da mu yiwa kanmu tanadin kwanciyar da Ubangiji kad'ai yasan
adadin tsayin ta ba.
Me yasa kishi ya ke sawa mu manta Annabi ya ce mu yawaita sadaka, sallah da
istigifari. Domin ya hango mataye da yawa yan'wuta ne. Kuma tsananta kishi alamu
ne, na mace ta barranta kanta daga ayar da Ubangiji ya saukar. Wacce kuwa ta
barranta daga imani da ayar Allah. La budda tana cikin hatsarin kafirta matukar
bata gaggauta tuba tare da yin hak'uri cikin hukuncin da Ubangiji ya halasta ba."
Tsikar jikina ta zuba k'warai da gaske. Na sassauta kukan da nake yi. Ta sake
sassauta wa ta ce "Ki yawaita karatun kura'ani domin karanta shi kad'ai yana wanke
tsatsar zuciya. Ki yawaita sallah. Ki rungumi y'aya'nki da sana'ar ki. Miji kuwa
kada ki zalunce shi, kada ki tauye shi, kada ki hana shi samun nutsuwa da ke ko a
gidansa. Illah iyaka ki sassauta zazzafar soyayyar da zata saka ki halaka, ki kuma
halaka shi".
Na numfasa tare da ajiyar zuciya mai nauyi na ce "To"
Ta shiga jero mini albarka. Ta ce "Idan akwai abin da yafi albarka da yafiyar uwa
na roki Ubangiji ya yi miki da ke da zuriarki. Idan har Ubangiji baya juyar da
addu'ar uwa akan d'anta , to alafamar ma'aiki ba zaki wulakanta a wannan duniyar
ba. Duk inda rayuwa zata kai ki, komin tsanani zaki zama cikin rufin asiri mai
yawa. Da ikon Allah wani mahaluki ba zai ga gazawar ki ba Yabi".
Da rawar murya na ce "Na gode Gwaggo! Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana mai
albarka".
Na jiyo ajiyar zuciyarra alamun ta samu nutsuwa da yadda na karbi ban hak'uriinta.
Ta ce "Ameen, ina tagwaye?"
Na ce "suna makaranta".
"To ke me kike yi yanzu?"
Ta tambayar cike da soyayya mai yawa.
A hankali na ce "A zaune kawai nake Gwaggo ".
"Tashi ki yi nafila, ki daina bari wannan lokacin mai tsada na wuce ki, baki yi
salatul duha ba. Kinsan duk abin da Ubangiji ya rantse da shi mai falala ne, mai
daraja ne. Allah ya ce "Wad Duha!
Lalle ki yawaita neman gafara da rahamar Allah a wannan lokacin, Ubangiji baya
juyar da addu'ar da aka yi ta a wannan sa'ar sai dai jinkiri, ko ya mussnya maka
fiye da abin da ka roka alheri".
Na ce "To!Da budaddiyar murya.
Ina jin soyayyar Gwaggo na sake tunbatsa a dukkan sassan jikina. Kwalla ta zubo
mini wacce bata ciwo ba ce, ta tausayinta ne, tare da tausayin wacce duk bata girma
da uwa mahaifiya ba. Tabbas soyayyar uwa ita ce mafi kololuwa a wannan duniyar.
Muka yi sallama na tashi na dauro alwallah, na yi walaha. Akan sallayar barci ya
sure ni, irin wanda na jima ban samu yin sa ba.

Akai Babah take yi mini waya, tana tambayar lafiyata da lafiyar yara. Na dinga
mamakin yadda ta sauko. Na sani tana sona. Amma a kwanakin baya gabadaya ta canja
mini. Yanzu kuma ta dawo mini Babah tawa Mai kaunata. Na dinga mamakin haka, da na
ga kaina zai dauki caji Sau kawai nayi Hamdala a raiana tare da rok'on Ubangiji ya
sake tsare mu daga sharrin masu tofi a cikin kulle kulle.

Da daddare muna kwance a dakinsa yara suna dakinsu da yake cikin falona sun yi
barci.
Dukkanmu kowa tunanin zuci yake yi.
Ba abin da nake so irin na fice na bar gidan Tijjani. Tufka da warwara kawai nake
yi. Maganganun Gwaggo sun yi matukar karya lagona. Domin a da na kudire wa raina
daga ranar da ya shiga dakin Nasiba ya kwana da ita. Tabbas washegari zan bar shi,
bari na har abada tunda nasan Baban Marina zai bani masauki tare da kyakkwar
mu'amala a tsakaninmu.
Amma yanzu Gwaggo ta mini tilas din cigaba da zama ta hanyar rarrashi da dabara.
Na nisa na saki ajiyar zuciya.
Daidai lokacin ya ce "Sannu Asiya!
Ban kula shi ba, ya ruko ni, na yi bakam tamkar mai barci.
A sanyaye ya ce "Zullimi ne yake kama ni from no where! Samar mini da nutsuwa pls.
Dan Allah bude baki ki fad'a mini wata kalma da zan samu sassauci a zuciyata. Ina
daf da tarwatse wa Asiya".
Na ja tsaki mai tsananin gaske tare da ce wa "Tsuntsun da ya ja ruwa".
Ya sake rik'e ni ainun. Ya kasa ce wa kanzil. Ajiyar zuciya kawai yake yi. Murya
babu amo ya ce "Idan na mutu Asiya dan Allah kada laifina ya shafi twins. Ni kaina
bana gane kaina a wasu lokuta, kin ga da hantsi ko yamma sai na ji tamkar ana hura
mini huta a kirjina.
Da zarar wani aka jima kuma sai na ji duk yadda aka azalzale ni na je Toro sai kuma
na ji ke nake son na dawo ma ga ni. Ko dai na haukace ne Asiya?"
Da k'arfi sosai na ce "Tunda har kana banbance wasu alamuran da hamkalinka sarai.
Kuma ina nan akan bakana, ba zan zauna da kai ba Bulkachuwa. Ana kawo maka Nasiba
ka tabbatar na hak'ura da kai".
Jikinsa ya dauki rawa. Ya ce "Bazan iya rabuwa da ke ba. Haka kuma idan ban aure ta
ba, bazan tab'a samun nutsuwa ba. Ki taimake ni mana".
Na ce "zaka ga taimako ganin idon ka. Na rantse maka duk wani sababin duniya ka
shiryawa ganinsa. Hala dai ka manta Yabin marina ne Tijjani?".
Ga mamakina bai iya taso mini da masifar sa ba. Gabadaya jikinsa ya sake sosai.
Washagari na tashi da bala'i ko kallon inda yake ban yi ba. Na yarda da zancen
Gwoggo. Amma bazan iya samar masa da nutsuwar da ake so ba.
Ya je can ya k'arata da dibar albarkar sa, shi da masu goya masa baya.
A wannan safiyar ya mini magana yafi sau goma ban kula shi ba. Na ki yin girki. Shi
kuma ba shi da kuzarin da zai yi. Gabadaya ya koma Tijjanin farkon aurenmu. Ba na
yanzu da yake masife ni a dalilin ina adawa da k'arin aurensa.
Ya kai ya kawo a tsakanin dakinsa da nawa. Ya kasa fita bare na samu na d'an
sarara. Tunda gabadaya haushinnsa nake ji mai kama da tsana.
Sallah kawai yake fita. Da k'yar ya lallaba ya tafi dauko su Hanif.
Da gudu suka shigo. Na yi maza na hadiye damuwar da nake ciki na shiga yi musu
oyoyo tare da murmushin yak'e.
Na dora musu indomie, bayan na juye musu ruwan wanka. Na kammala yi musu wanka,
suka yi sallah.
Sannan na juyo mana indomie muka fara ci da su.
Hanif ya ce "Baban 2 sauko mu ci".
Hamim ya ce "Ba shi da lafiya ai marar lafiya ba ya cin abinci"
Takaici ya shake Bulkachuwa.
Ya daidai ta zamansa ya ce "Hamim baka tausayina ko kad'an?. Zaka ga tsiya, daga
yau Hanif zan dinga siyo wa abina tunda kai uwarka kake so kawai".
Da yake mai kwadayi ne sai ya marairaice ya ce "Na daina Baban 2 sauko mu ci to."
Bai sauko ba, ya koma ya zauna. Ba tare da ya sake ce wa komai ba.
Muka kammala da kansa ya saka musu yunifom din islmamiya ya rakasu waje ya dawo.
Ya zauna daf da ni ya ce "Asiya Tsakanin ki da mai rumfa me ya hana ki daukar
ciki?"
Na hassalo na ce "Saboda na gama haihuwar da kai, sai da wani".
Ai kuwa ina rufe baki ya cakume ni yana kokarin murde mini baki.
Na dinga zille wa, ina ture shi. Maimakon ya bar ni tunda ya ga kuka nake yi sosai,
duk da bai mini komai ba, kuka nake na takaicinsa da na aurensa.
Amma bawan Allah bai yarda ya kyale ni ba. Ya sure ni ya yi dakina da ni. Sai da ya
yi abin da yake so. Ya tara mini gajiya ya ce "Ya kika ji? Kin hana ni abinci, amma
kin dafa muku ke da y'aya'n ki, kun ci. Sai kuma na zarta ki k'arfi da kuzari."
Na ja tsaki na juya masa baya, bayan na ja mayafi na lullube jikina.
Da daddare ya fita ya siyo tsire mai yawa. Ya dafa shayi ya kawo falo.
Ya juye naman a plate ya ce mu sauko mu ci.
Shi da yaran suka ci. Ni kuwa ko sha'awar ci ban ji ba, duk da yadda k'amshin ya
cika wajen gabad'aya.
Washagari har wajen tara yana gida kamar ba zai fita ba. Kamar zan masa magana a
dalilin yadda ya bani tausayi, amma da zarar na tuna ba janye wa zai yi ya fasa
auren Nasiba ba, sai na ji tsanarsa na sake darsuwa mini.
Yana zaune sai waya ake yi masa babu kakkautawa. Kan dole ya yi shirin fita. Murya
babu amo ya ce "Zan fita Asiya sai na dawo".
Ko motsi ban yi ba bare na masa shi. Ya sa kai ya fice. Sai kuma ya dawo, ya gama
kame kame ya fita.
Mintina kusan talatin ya sake dawo wa.
Ya tarar da ni a zaune. Ya ce "Gabad'aya jikina bana jin dad'i. Ga shi fitar ta
zame mini dole. Kano zan je na kai kaya. Amma yau zan dawo komin dare in sha Allah
".
Na dauke kai na kasa ce wa A dawo lafiya.
Ya fita. Na ja tsaki tare da ce wa "Ka gama shige da ficen ka ba kula ka zan yi ba.
Azahar ta tayar da ni. Na yi sallah na d'ora abinci saboda yara.
A daddafw na yi shara na gyara dakin.
Na fito wanka su Hamim suka dawo.
Da yake alhamis ne babu islamiya.
Dan haka sai suka debe mini kewa, ban fada nazarin yadda zamana da Nasiba zai
kasance ba. Tunda a duniya bani da matsalar da ta wuce hakan.
Ban ankara da rashin dawowarsa ba sai wajen goma na dare. Yana wahalar gaske ya yi
dare. Idan kuwa hakan ta kasance sai ya bugo mini waya, ko da ni ban masa wayar ba.
Na fara tsorata da shadaya ta gota. Zuciyata na bugawa na d'auki waya na k'ira shi.
Abin mamaki wayar ta ki shiga, na dage da kira babu kakkautawa.
A karshe a ka ce a kashe take gabad'aya.
Na shiga zullimi sosai. Mussaman da ya tabbatar mini zai dawo komin dare.
Na rasa yadda zan yi. Na Kalli yara na barci. Hamim ya dora kafarsa jikin Hanif.
Hawaye ya tsinke mini domin yadda nake jin jiki da zuciyata suna bari, nasan akwai
abin da zai biyo baya marar dad'i.
Duk yadda na so na tashi na yi sallah kasawa na yi. Daren ya mini tsayi ainun.
Domin tunda muka dawo Bauchi bai tab'a tafiyar kwana ya barmu ba.
Na dinga kuka ina fad'in "Allah ka taimake ni ka dawo da shi lafiya."
Da asuba na cigaba da kiran wayarsa nan ma shiru.
Ina idar da sallaj na bugawa kaninsa Aliyu waya na sanar masa Tijjani bai dawo ba,
kuma wayarsa a kashe. Ya yi yunkurin kwantar mini da hankali. Na katse wayata na
kira Yaya Salisu na shaida masa.
Har karfe daya na rana babu labarin sa. Hankali dangi ya fara tashi. Da la'asar sai
ga Babah ta Bulkachuwa tare da Aliyu.
Kuka kawai muke yi ni da ita. Aka rasa mai bawa wani hak'uri a tsakaninmu.
Yayin da Yaya Salisu da Yaya Aliyu suka nufi Kano tun hantsi.
Tashin hankalinmu ya sake tsananta da la'asar ta yi babu wani tartibin labari akan
Tijjani ko motarsa.
Hatta Toro hankakula ya tashi ainun domin tabbas abu marar dad'i ya same shi,
mutuwa ko mummunar hadarin da aka kasa gane shi.
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai muke ta ambata ni da Babah.
Babu abin da yake sake tayar mini da hankali irin idan na kalli twins.. gabadaya
sun kasa sukuni. Duk fitinar Hamim ya zauna a gefe ya nutsu tamkar marar lafiya.
Maganganunsa da ya dinga yi mini a baya akan mutuwa suka dinga dawo mini. Na fara
kuka sosai ina ce wa "Sai da na sakankance ba mutuwa zaka yi ba shine zaka tafi ka
bar omu, me yasa zaka tafi yanzu alhalin zukatanmu cike suke da gilli da bacin rai
mai tsananin gaske?.".
Babah ta kasa ce wa komai illa hawaye da ita ma yake k'waranya daga fuskarta.
Ina cikin haka sai ga Yaya Ummi da Mama. Baban Marina ya turo su, su zauna da ni. A
dalilin bai san Babah tana tare da ni ba. Ganinsu ya sake rikitini ina sake gasgata
abu marar dad'i ya same ni. Ina kuka ina fad'in "Ni Yabi yaushe zan tsallake
damuwowi ne a rayuwa ta?"
Gabadaya na rikice, sai tausa ta suke yi, duk da Yaya Ummi ma kukan take yi sosai.
Sai dare Aliyu ya k'ira Babah. Murya babu sukuni. Ya ce "Al'amarin dai sai
hak'uri."
Abin da na ji ke nan na yanke jiki na fad'i ban sake gane komai ba.

*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Saiwowin maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
* Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki
da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*



✍️
*INA MUKU ALBISHIR AKWAI DUKKAN TSOFAFFIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA SALIHA
ABUBAKAR ZARIA*
*ZAKU SAME SU SOFT COPIES A HANNUNA.*
*SABO LITTAFIN TA ZAI ZO BA DA JIMAWA BA*.

*HAKA NAN AKWAI WASU DAGA CIKIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA HAFSAT C SODANGI, SUMA
SOFT COPIES*

*HAJIYA HANNE ADO ABDULLAHI?*
*MARUBUCIYAR WANKA DA GARI DA KUMA WACECE UWA?*
*TO ITA MA TAKANAS NA SAMO MUKU LITTAFANTA DOMIN KUN SANI TA YI RUBUTU MASU
MA'ANA*.
*LITTAFAN DA YAWA, AMMA AKWAI DISCOUNT DOMIN SO NAKE KU YI TA SIYAWA Y'AYA'NKU DA
KANNENKU LITTAFAI MASU DARASI DA MA'ANA*.

*BA DA JIMAWA BA ZAN ZO MUKU DA SU*.
*08032773332*.


Na farfado ne na gan ni ana k'ara mini ruwa sai fifita suke mini tare da kuka
dukkansu.
Baki na rawa na ce "Babah ni din musulma ce! Ki fad'a mini Tijjani ya rasu ne?"
Da rawar murya ta ce "Bai ce ya mutu ba Yabi. Amma dai akwai abin da ya same shi
marar dad'in ji, tunda har Aliyu ya jinjina lamarin".
Na fizge k'arin ruwan na zabura na ture su na tashi. Hijabi na raruma na yi hanyar
waje ba tare ma da na saka ba.
Yaya Ummi ta ruk'o ni tana fad'in "Ina zaki a wannan halin Yabi?"
Da kuka sosai na ce "Kano ba zan tab'a samun nutsuwa ba, matukar ban san halin da
yake ciki ba".
Fuskar kowa k'walla ce da tashin hankali. Hatta Mama jikinta a sanyaye yake ainun.
Da k'yar suka tirsasa ni na hak'ura na zauna. Sai ambaton Innalillahi wa inna
ilaihir rajiun kawai nake yi. A fili nake fad'in Allah ka kaddara mini na ga
dawowar Tijjani cikin gidan nan, ko da ba akan kafafunsa ba ne. Fatana ace yana
numfashi. Ubangiji ka rufa mini asiri ni da y'aya'na".
Ba abin da yake sake tayar mini da hankali irin yadda Babah ta kasa tsayar da
hawayen ta.
Akai akai take share hawaye babu kakkautawa.
Kwanaki biyu muna cikin wani irin zullimi mai tsananin gaske. Domin duk asibiti da
yake cikin Kano su Aliyu sun karade a kwanakin nan amma babu Tijjani babu labarin
sa. Kowa ya karaya. A ranar Baban Marina ya taho Bauchi tare da Gwaggo. Nasiha kan
nasiha suka shafe lokaci suna yi mini akan yarda da kaddara na yi hak'uri mu bishi
da addu'ar idan a raye yake Ubangiji ya tsare mana shi, ya kuma bayyana shi. Idan
kuwa rai ya yi halinsa to Allah ya sanar da mu, ya kuma jik'an sa.
Na rarrafa na fad'a jikin Baba cikin matsanancin kuka na ce "Sai yaushe zan huta,
yaushe ne zan ji dad'in da ake ta fad'in zai same ni? Gabad'aya walagigi yafi yaws
a rayuwata Baba! Kalli k'ananun y'aya'n Tijjani wa zai taya ni tarbiyarsu da
wahalarsu Baba?"
Muryarsa na rawa ya ce "Ubangiji da ya baki su shine jagoran da zai taya ki kulawa
da su. Sannan matukar ina numfashi ko y'aya' nawa kika haifa zan kula da su iyakar
yadda zan iya, tamkar y'aya'n da na haifa!
Yadda ya kare maganar da kuka ya sanya Gwaggo fara kuka duk kuwa da yadda take da
jarumta mai yawa. Kowa na falo kuka yake, hatta Mama kuka kuma na gaske ba na ganin
ido ba.
Tsawon lokaci muna kuka tamkar an tabbatar Tijjani ya k'are.
Hanif ya ce "Ku yi hak'uri" Hamim kuwa ya ce "Baban 2 zai dawo a motarsa bai b'ata
ba."
Gabadaya yaran sun rasa kuzari da karsashi a tare da su.
Da yamma mun idar da sallar la'asar Yaya Salisu ya kira Baban Marina da yake zaune
a cikinmu tamkar mace.
A sanyaye ya ce "Mun samu labarinsa, mun je mun gan shi".
Gabadaya dakin muka hau fad'in Alhamdulillah Alhamdulillah!
Sai dai Innalillahi wa inna ilaihir rajiun din da Baban Marina yake fad'i ya yi
matukar tsorata mu, mussaman ni da zuciyata tamkar ta fad'o k'asa.
Na kasa fahimtar bayanin da ake masa. Nasan dai na ji ya ce mun gan shi.
Gumi ya dinga keto mini. Ina tambayar zuciyata wanne ibtilai ne ya samu Bulkachuwa
irin haka?.
Sai da Baban ya ajiye wayar. Tsawon mintina bai iya ce wa komai ba. Gabadaya ya
jike da zufa.
A sanyaye Gwaggo ta ce "Alhaji fad'a mana halin da ake ciki kada zullimi ya karasa
kassara mu.
Murya babu amo ya ce "Yana hannun jami'an tsaro. Tun shekaranjiya suke tsare da
shi. Kuma damln tsabar raina talakan k'asa suka kashe wayarsa bare wani nasa ya ji
halin da yake ciki."
Na saki nannuyar ajiyar zuciya, da kuka nake fad'in Allamdulillah!
Domin sai na ji tamkar an dauke mini k'atuwar masifar da ta nannad'e ni.
Tunda yana da ransa komai mai s'auki ne. Domin ban fahimci ana iya yiwa mutum
talala ya zama ba shi da yancin yin komai a rayuwarsa ba.
Na kasa yin walwala a dalilin yadda Baban Marina ya yi laushi. Na tabbatar Tijjani
na cikin k'ak'ani ka yi.
*Toro*
Baban kasuwa da Baban Tsakiya zaune a gaban Dada da take kuka face face tana fad'in
"Ubangiji ka kare mai sunan manya, ka bayyana shi".
Baban Tsakiya ya ce "Ki daina damuwa sai ciwon ya tashi ne? An ce miki a gan shi.
Sai dai fitowarsa sai ikon Allah. Tunda laifin da aka kama shi da shi idan a wata
k'asar ne take za'a tabbatar masa da haddin kisa."
Hannun biyu ta d'ora aka tana kururuwa tana ce wa "Allah ka yi mini dan ma'aiki.
Alfarmar Shehu Amadu Tijjani mai karama ka saukakawa wannan yaro".
Baban kasuwa ya ce "Allah ne ya yi sakayya ya toni asirinsa. Wai Tijjani ya rasa
wadanda zai wulakanta sai mu? A fili yake nuna wa Yaya Sani ne kawunsa da zai yiwa
hidima. Akan idonmu zai ta d'orawa yara kayan abinci da kayan miya ana kai wa
kofarsa amma mu wayam. Wai shi mai suruki. Alhalin ba akan son ramasa ya bashi
auren iblishiyar yarinyar nan ba. Mune muka so a bashi"..
Baban Tsakiya ya yi k'uta tare da ce wa "Allah ke nan! Ai duk mai gilli mai son ya
wulakanta na gaba da shi ya dinga ganin jarraba ke nan."
Dada dai kuka take bil hakki. Domin tun farko tana son Bulkachuwa. Da ya samu
wadata kuma ya jiyar da ita dad'i duk da dai ce wa take yi bashi yake biyan ta.
Tunda dukiyarta da ya salwantar mata runduna ce babba.

Washagari muka dunguma Kano tare da Baban Marina. A babbar hedikwatar y'an sanda ta
bonfai muka tarar da shi cikin mawuyacin hali. Hawaye ya tsinke mini. Domin
gabad'aya ya fita a hayyacinsa. Babu alamun duka a tare da shi. Amma ya jigata
k'warai da gaske. Abin mamaki a wajen muka tarar da su Yaya Jabir ya zo daga Kaduna
da kuma Yaya Ammar yayan Nasiba. Duk da shi ma a BAUCHI yake aiki a gidan Yari.
Tunda su Yaya Salisu suka fada musu, suka bar komai suka biyo su Kano dan sanin
halin da Tijjani yake ciki.
Cikin tashin hankali Tijjani ya ke fad'in "Wallahi bana harkar. Ina gida aka mini
waya akan na biya na karbi sako a Wunti. Ashe wiwi da koken ce ga shi an kasa samun
lambar da aka kira ni da ita. Wallahi ba kayana ba ne, ba ni da alak'a da ita".
Ya fad'a idonsa ya kad'a ainun tamkar na rikakken mashayi.
Na rushe da kuka riris. Domin dai na riga na gane mun fad'a cikin garari mai girma.
Kallon sa na yi na gane iyakar gaskiyarsa yake fad'a babu alamun karya ko
kwaskwarima domin ya riga ya bani damar da na fahimci gaskiyar sa da kunbiya
kunbiyarsa.
Babah ta kasa magana, yayin da Baban Marina ya ce "Tijjani ka fadamana gaskiyar
magana, dan musan ta yadda zamu b'ullowa wannan azal d'in. Kasan wahalar da shari'a
ma laifi ne babba."
Murya na rawa ya ce "Wallahi gaskiyar magana na fad'a. Bana harkar, ba ni da alak'a
da kayan da aka kama ni da shi Baba".
Gauron numfashi Baba ya yi tare da ambaton "Subhanallah!
Baba ta kasa magana duk da idonta a soye yake babu alamun kuka. Na sani kuma tana
cikin damuwa ne mai yawa.
Na tsugunna a gabansa ya sassauta murya ya ce "Asiya na rantse miki ba ni da alak'a
da wannan al'amarin sharrin magauta na had'u da shi. Kaddarar da azal ce ta hau
kaina".
Na zuba masa ido tamkar ba a gaban iyayenmu muke ba. Shi ma ya zuba mini nasa,
tsawon lokaci muna kallon juna. A cikin wannan kallon na tabbatar Tijjani bai
aikata laifin da aka jingina masa ba. Na kuma gasgata shi akan gaskiya yake
amayarwa.
Ni na fara janye idanuwana da hawaye suka cika su taf. Da rawar murya na ce "Na
gasgata ka Baban 2! Ina baka tabbas din ko baka samu mutum daya da ya gasgata ka
ba. Ni Yabi na yarda bak'in k'azafi aka yi maka, tare da hak'a maka ramin mugunta.
Dan haka ina tare da kai cikin ko wanne bigire har mu ga me Ubangiji zai zartar
mana".
Daga hakan na fara kuka sosai. Yaranmu da suke jikinsa suka yi tsuru tsuru suna
kallon yadda nake kuka sosai, shi kuma ya susuce ido ya kad'a.
Sai lokacin Babah ta ce "Allah ya warware maka, ya bayyana gaskiyar al'amarin".
Yaya Ummi kuwa da Mama kuka suke yi. Gwaggo ce bata um bata um tunda ta yi jaje
cikin rauni da kasala bata sake iya magana ba.
Muna kallo da lokacin da suka bamu ya cika suka iza keyarsa hannunsa dauke da ankwa
tamkar kasurgumin mai laifi.
Ni dai har muka dawo BAUCHI ban iya daina kuka ba.
Tun ana bani bakin na yi shiru har aka zuba mini ido.
Maimakon mu yada zango a BAUCHI sai Baba ya ce a wuce Toro kawai.
A k'ofar gida muka tarar da su Baban Tsakiya. Na kalle su na gasgata ce wa Baban
Marina ne kawai ubanmu. Ba wanda ya bi bayan Tijjani ko na ahalinsa a cikinsu.
Dukkanmu a gaban Dada muka zube tamkar masu neman gafara. Tana kuka, matan cikinmu
muna yi, tamkar dai mutuwar fuju'a Tijjani ya yi.
*INA MUKU ALBISHIR AKWAI DUKKAN TSOFAFFIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA SALIHA
ABUBAKAR ZARIA*
*ZAKU SAME SU SOFT COPIES A HANNUNA.
*SABO LITTAFIN TA ZAI ZO BA DA JIMAWA BA*

Sai ta dauko salatil fathi sai ta rikice ta dauko ashafa da k'yar dai ta fara
karanta casa'a ta sauke ta. Tana yi tana ce wa "Rabbani a saukakawa mai babban
suna, a tausayawa wadannan y'aya' nasa".
Da k'yar Baban Marina ya hakurkurtar da mu aka daina kukan.
A dakin Gwaggo na yada zango. Dakin da nake matukar samun nutsuwa a cikinsa. Amma a
yau sai na ji ina cikin matsanancin kunci da zullimi domin sai nake ganin tamkar
ana shirin raba ni da Tijjani ne. Na ga tsayin wannan dare tamkar dai ace gawa ce a
dakin.
Ban yi barci ba. Karfe uku na ga Gwaggo ta fita ta dauro alwallah. Duk yadda na ke
cikin zullimi sai da na tuna irin wannan yanayin muka shiga a lokacin da aka zartar
mini da hukuncin auren Bulkachuwa. Yau kuma ina kukan bak'in cikin nisanta ni da
gidansa da aka yi.
Gwaggo tana shigowa da alwalarta, nima na zabura na mik'e na doro alwalar.
Muka dinga nafila muna shigar da bukatunmu. Ina kuka hannuwana na sama "Tijjani,
Tijjani kawai nake iya fad'a gabad'aya kaina ya kulle. Domin dawo da ni gida ya yi
matukar sake tsorata ni.
Me yasa za'a raba ni da dakina?
Kwanaki biyu kacal a gidan Marina na gane masu farinciki yadda na shiga cikin
garari sun rinjayi masu tausayi da rarrashina.
A k'ofarmu kam babu wanda yake takura mini ko habaici. Amma da zarar na fita da
NIYYAR zuwa wajen Dada sai na samu wanda ya yi mini yarfe ana mini habaicin dama
karyar arzikin da a muke yi ba mai

Please Login or Register in order to submit comment