You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zo ki
tuntube ta ki ji me zata ce akan hakan".
Ta zuba mini ido ta ce "Yabi a gidan kurkun kuka yi cikin ko a ina?"
Na fara nishi ina fad'in "Ki bari ta zo, ni ba iya bayanin nan zan yi ba. Dan Allah
ki zo ki cigaba da matsa mini kafafuwana".
Ta sake daukan salati tare da tafa hannu. Sai nanata iko sai lillahi take yi. Sai
ta yi shiru sai ta sake zabura ta d'auki salati tana ce wa "K'warzaba da jarabar
yaran yau ta kai kure wa. Ni Asma'u ina kallon zamani".
A kan dole ta cigaba da yi mini tausa. Tana yi, tana hirji domin ta shiga mamaki
mai yawa.
Da safe da Baban Marina ya shigo duba ni. A sanyaye ta ce "cikine da Yabi Alhaji".
Babu dar ya ce "Ma sha Allah! Ai rabo ba k'aramin al'amari ba ne. Allah ya raba
lafiya".
Ta yi galala ta ce "Alhaji na ga baka ka'du ba!
Ya murmusa ya ce "kad'uwar me zan yi bayan na gasgata Yabi tamkar yadda na gasgata
yunwar cikina. Ita tasan yadda ta had'u da mijinta. Tana da miji kuma dan na ganta
da ciki sai na bi ba'asi, akan me?"
Ta ce "To ai kowa yasan baya nan, sai kuma a ganta da ciki, kana jin yadda ake
daura mata magana haka siddan. Ina kuma a ganta da ciki".
Ya ja tsaki ya ce "Idan har kika daka bak'ak'en taadodin jama'a babu abin da zaki
yi. Ya mik'e yana ce wa "Sannu Allah ya raba ku lafiya."
Ya saka kai ya fice.
Satin su baba biyu sannan suka dawo, cikin sa'a ido daya ya budu. Daya ya mutu. Aka
yi murna da yi mata barka da arzikin da ta auna.
Babah tana zaune a dakin Gwaggo. Yayin da nake kwance akan k'aramin gadon. Na samu
sauki, amma jikin babu k'warai.
Gwaggo ta ce "ikon Allah Yabi dai ciki ne da ita."
Ta dauke kai ta ce "Ho ke kam yanzu kina neman baci da magana. Ina dalilin wannan
tuyar da kike yi ne. Nasan da shi tun kafin mu zo."
Gwaggo ta sake ce wa "ikon Allah sai kallo. Abin ne yake dafa ni. Wato kinsan komai
ke, shi yasa ta ce idan kin zo, na ji a bakin ki".
Babah ta mik'e ta ce "Sai ki yi ke kad'ai ina dalilin bin wannan diddigine haka?
Mace da mijinta".
Da mamaki Gwaggo ta sake ce wa "To wai a kurkun, a ina suke haduwa ni Ma'u!
Babah ta fice ta ce "A a nima ban sani ba. Sai ki tambayi mijin nata tunda ita kin
saka duk ta sururuce da kunya. Domin ke sai akan girman ki zaki baci da magana, sai
ki je ki gano shi, ki tambaye shi yadda aka haihu a ragaya ".
Ta fice da sauri.
A haka muka sake shafe sati biyu. Yaya Aliyu ya zo ya kwashi yara ya ce tunda ba
tafiya zamu yi ba, to ba zasu yi asarar karatunsu ba.
Na kuma gane Babah tana son ta zauna da Dada a dalilin ta damu da lalurar da ta
sami autarta.
Sannu a hankali na fara warware wa. Matan gidanmu sai nan ake yi da ni. Mama da
kanta sai ta tambayi abin da zan ci. Na tabbatar ta dad'e da ajiye makamanta. Amma
yadda nake tiritiri da rik'e musu gidan ya kara mini kima k'warai da gaske.
Ahalin gidanne dai idan muka had'u ko idan na fita da nufin zagaye ake bina da
kallon k'urillah da tuhuma.
Yara basa iya ce mini komai ba. Amma da kunnena na jiyo matansu Baban Kasuwa da na
Tsakiya suna gulmar cikin jikina suna fad'in "iyalin Tijjani bata yi shashanci ba,
ai a yi mamaki, irin fasadin da ya yi a doron kasa, sai kurum."
Na yi kamar ban ji ba. Domin a yanzu da nake fama da rashin Baban 2 mene ne bazan
yi hak'uri a kansa ba?
Baban Tsakiya kuwa fama yake da ciwon hawan jini. A dalilin mafi yawan y'aya'nsa
sun kangare. Dama dai Jabir ne mai dama, to a lokacin da yake da dama bai bari ya
taimaki kowa ba. Domin ko ni a farkon farkon rufe Baban 2 idan ya tura mini kudi
sai ya ce "Ba sai an ji ba".
Dan haka mafi yawa yanzu ba'a taimakonsa ko tausayinsa domin a lokacin da ya samu
ba wanda ya more shi. Sai aka yi mutuwar kasko.
Shi kuwa Baban Kasuwa manyan y'aya'nsa guda biyu na farkon mata ne. Amina sai
Maijidda. Kuma dukkansu a yanzu kowa fama take a gidanta bare ta taimake shi. Gara
ma Maijidda yanzu ne babu ta same su. Aminu na ukun sa'an Anas ne, yanzu suke
tasowa.
Gabadaya rayuwa ta yi juyin waina. Baban Marina da ake ganin babunsa a yanzu yafi
su rufin asiri. Abincinmu yafi na kofofinsu. Ba kuma kudi ya yi ba. A a Y'aya' ne
suka taso, muka hutar da shi fafutukar rayuwa.
Har yau kuma idan Baban Marina ya samu damar da zai yi mana wasiyya sai ya ce "mu
zama masu afuwa da manta sharri, mu kuma rik'e alheri komin kankatarsa. Ko waya ka
yi masa sai ya ce "Ba jarumta ba ne fad'a a tsakanin yan'uwan juna. Ba kuma tsoro
ba ne idan kai mai gaskiya ka janye ka barwa wanda ya karkace, masalaha ne da
takaita rikici.
Har ilah yau ba imani ba ne ka yi fatan ganin wani ya shiga mummunan yanayi duk
yadda ya zalunce kuwa. Mafi yawan sakayya yanzu tun a duniya Ubangiji yake fara
yinta. Matukar kana da gaskiya baka nufi kowa da sharri ba, to sai ka ga alheri
komin dade wa.
Iri iren wadannan nasihohin ne suka dagargaza mini tunanim son ganin su Baban
Tsakiya a halin tagayyara, na huce da su nake nema masu gafarar Ubangiji. Na gamsu
idan suna cikin tozarci dole dai jininmu ne kuma gidanmu daya.
Nazira akai akai take ziyarta ta. Mu yi hira, ta daho mini abinci, ko ba zata zo ba
sai ta aiko mini duk da gidan namu da abinci amma kullum sai ta ciko cooler ta kawo
mini.
Muna hira na ce "Adda Nazi wai ya ya Saiwowin dahuwar tattabaru din nan kuwa?
Ni dai na ga kyaunsu. Ya sabunta ni a wajen Baban 2 sosai".
Ta ce "hm kayya bari ke dai suna da kyau. Amma maigidan ne kuzarinsa ba mai yawa ba
ne. Na yi dariya na ce ke kuma babu s'auki."
Ta ce ba haka ba ne".
Na ce To zan karbo miki moringa tea ya dinga sha a shayi ko a lemo, zai sha?"
Ta ce "zai sha ba shi da matsa akan hakan. Amma dai Yabi kada ki saka na ba shi
abin da zai cutu ko ya hallaka ni"
Ta ba ni dariya ainun na ce "Kai Adda Nazi. Garin zogale ne fa sai sai saiwowi
marasa illah. Yana da d'an kudi amma yana da kyau ainun".
Ta ce shima a kano ne?"
Na ce "eh a wajen mai saiwowin ne duka daga Chad take kawosu. *08032773332*.
Ta ce "Tom shi ke nan. Na gode."
Sai da muka yi wata biyu. Muka koma BAUCHI. A lokacin cikin ya shiga wata na hudu.
Tun ina jin kunyar Babah har na hak'ura na ware a dalilin itama mita take yi. Wai a
sadda muka yi abin da muka yi, ban yi zaton zan ji kunya ba, sai yanzu?
Ranar da muka je Tijjani ya fahimci ciki ne da ni har ya yi k'wari ya kasa magana
ya tafi ya yi sujjud shukur. Babah ta koma gefe ta yi kamar bata wajen.
Ya dinga murna da yi mini addu'a. Gabadaya na danyace. Na ciko sosai. Duk wata ko
ban je gidan gwamnati ba, sai Hajiya ta kawo mini kudin envelope tare da nanata
basu manta maganar maigidan ba. Karamci kad'an na yiwa Hajiya, sai ya janyo mini
sanadin alheri mai yawa. Na kuma fahimci tausayina take ji da gaske. A haduwarmu
Allah kad'ai yasan adadin alherin da nake samu. Su Hamim ta mayar da su tamkar
jikokinta. Suna bata sha'awa. Kullum a cikin kawo musu suturu masu kyau take, ga
kayan wasa kala kala.
A haka rayuwar ta cigaba da garawa har na shiga watan haihuwa. A lokacin kamfani ya
sake biyan kudin filin Tijjani. Na yi siyyya mai rai da lafiya amma na kudire ba
zan yi Taron suna ba. Ya fad'awa Aliyu yadda za'a yi masa da kudinsa. Yaya Aliyu
Kuma Bai fad'a mini yadda za'a ba, Nima ban tambaye shi ba. Bayan ya ce a ware
wanda za'a yiwa Baban Marina da mahaifiyarsa hidima. Da ragowar yan'uwan. Ya ce
Aliyu ya dauko 250 ya yi wani abin.
Cikin ikon Allah watan Muharram da kwana bakwai na haifo yarinya sankaceciya. Jawur
da ita tamkar tsada. Wanda ya yi daidai da 1 ga watan goma miladiyya.
Babah ce ta karbi haihuwar domin cikin dare ciwon ya tashi. Kafin Aliyu ya zo da
mota tuni na haihu ta gyara wajen. Kawai mun je asibitin ne an duba ni. A daren
muka dawo gida.
Babah ta zuba yarinya ido ta ce "Ke kuma Aliyu kika debo?"
Na kalle ta. Domin ni fa bana gane kamar yara. Aliyu ba sosai suke kama da
Bulkachuwa ba, sai dai suna yanayi saboda jini d'aya. Ihisan ce suke kama da
Tijjani kwabo da kwabo shi yasa su Hanif suke matukar kama da ita. Dan idan muka
hadu kowa ita yake zaton ta haife su ba ni ba.
Washagari Babah ta d'auki jinjira ta kai wa Tijjani da kanta. Aliyu ne ya kaisu.
Tare da su Hamin da suke murnar sun yi KANWA tamkar su mayar da ita ciki.
Ya karbe ta cikin kunyar uwarsu. Ya zuba mata ido yana jin sonta da tausayinta na
tsaga shi. Zata girma babu soyayyar uba alhalin ba mutuwa ya yi ba. Ya tsinci kansa
da ce wa "Allah ka mini sakayya da duk wanda ya k'ulla mini sharrin da aka nesanta
ni da iyalina, na kuma rasa y'ancina.
Aliyu ya juya domin idonsa ya ciko da k'walla. Babah kuwa tuni take sharbe.
Domin ya bata tausayi k'warai da gaske.
Murya na rawa ta ce "yi mata addu'a ka kuma yi mata huduba.
Ya shiga jero mata addu'oin tsari da albarkar rayuwa. Ya Kalli Aliyu ya ce dauke ta
ka yi mata huduba da duk sunan da kake so."
Ya saka hannu biyu ya dauke ta ya yi mata kalmar shahada ya lakaba mata Hauwa.
Ya mikawa Babah ita yana fad'in sunan ki na zaba mata ".
Da sauri ta ce "Ba kuwa sunana zata ci ba. A saka mata Asama'u. Don Yabi tasan mun
san alheri, muna kuma gode mata.".
Aliyu ya ce "Hakane Babah. Ya sake sabuwar huduba ya rad'a mata Asama'u.
Maimakon ya bawa Gwaggo sai ta mika mawa Tijjani domin ta ga bai gaji da kallon ta
ba.
Ya ce "Aliyu rago nawa zaka yanka mata? Domin gabadaya kai ta kwaso, kamar da ta yi
da kai ta shahara."
Ya ce "Haka na ga ni, Babah ma ta ce ni ta kwaso. Biyu za'a yanks mata. Ana yaye ta
kuwa zan dauke ta".
Tijjani ya ce "Yabi kuka zata yi Aliyu. Twins ne naka. Kai na haifawa su, ga shi
nan kana ta tiri tiri da su babu gajiyawa. Ko yanzu idan kana so ka wuce da su,
amma wannan barta, ita ce zata debe wa Yabi kewar zaman jirana".
Babah ta ce "Uhum! Nan da nan ya kame bakinsa domin ya shafa'a da ita."
Sun jima kafin su tafi su bar shi cikin alhini. Yarinyar ta shiga ransa fiye da
twins.
Suna isa suka tarar da mutanan Toro. Gabadaya ahalin Baban Marina ne sai Dada.
Da murna ta fad'i sunan jaririyaya. Kowa ya yi murna take Yaya Salamatu ta ce sai a
kirata Husna. Na ce "To". Farincikin sunan Gwaggo ya zangwanyar da alhinin da nake
ciki.
**
Na Dade da gane Dada ba k'aramin son Bulkachuwa take yi ba. Domin sai yanzu na
fahimci kafatalin jikokinta tafi sonsa. Tunda bata iya boye son tagwaye. Ni kaina
na sake samun daraja ne a wajen ta saboda Tijjani. Kullum ta gan ni sai ta yi kuka.
Y'aya'nsa kuwa komai hannunta ya taba sai ta basu. Tana yi tana fad'in "Allah ka
yiwa mai babban suna abin da zato bai yi zatonsa ba. Wanda duk ya k'ulla masa
wannan salalar tsiyar Allahu ka dabaibaye duniyarsa da firgici da tashin hankali."
Kaitsaye Babah ta bawa Dada jinjira. Ta zuba mata ido tana kuka ta ce "Mai sunan
manya ya haifi Aliyu. Sai na tuna ranar da aka haife shi. Haka yake sak."
Aliyu da yake tsaye a bakin k'ofar ya ce "Dada ikon Allah! A gaban y'aya'na da
kannena kike maganar haihuwa ta?"
Ta ce "To uwaka ma bana yi zancen haihuwar ta bare kai".
Ya ce "Ai shike nan, dama ni ba wai kina sona ba ne . Yaya Tijjani ne na ki. Kin ga
da kin bini a hankali gobe dia na zo na kai ki wajensa."
Ta marairaice ta ce "A sannu ma zan bika Ali gadanga angon kilima".
Ya ce "Assha kin batawa amarya ta sunanta. Amma dai zan zo, ya hau gaishe ta.
Sannan suka gaisa da su Mama.
Ya ce "Ummi ni da ke waye babba ne?"
Ta ce "Mama fad'a masa".
Mama ta ce "Ita ce babba ranar sunanta aka haife ka".
Ta nuna shi da yatsa ta ce "To ka ji Wallahi ka kiyaye ni"
Ya rik'e kiirji ya ce "oh saboda Ikilima zaki dinga zare mini ido? Sannu gyambo
uwar son girma! Haka kike yiwa Yaya Tijjani?"
Ta ce "Ai shi yayana ne kuma duk da hakan girmama ni yake kamar me saboda ya yarda
surkuta gaskiya ne. Sai kawai kukan da take danne wa tunda ta ga jaririyaya ya
kwace mata duk da dai wasa suke yi.
Kowa ya yi k'asa da kansa ana taya ta kukan da take yi. Domin tun fil-azal idan
akwai amintattun da ba cikinsu daya ba a gidan Marina to Yaya Ummi da Bulkachuwa
ne. Akwai shakuwa da kauna a tsakaninsu mai yawa.
A sanyaye ya ce "Ki yi hak'uri ummilolo! Ai yana fad'in hakan sai kuwa ta sake
rushe wa da kuka na sosai. Don kuwa Bulkachuwa kad'ai yake ce mata ummilolo.
Daada ma ta bare baki ta shiga taya ta suka dinga yin sa kamar me. Da k'yar suka yi
shiru.
Aliyu ya tafi jiki a sanyaye. Yana fad'in ba zan sake zolayar ki ba Ummi har sai
d'an-uwan ki ya fito.
Har dare babu nishadi a tare da mu.


*Marubuciya Nazifa Nashe tana sabon littafi mai suna Gaskiyar lamari*
*Ku bibiye shi , babu jira, babu nadama*.
*Ku tuntube ta a wannan lambar*
*08033748387*.


*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta
sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar
taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi
muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun
san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa,
mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai
soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan
littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan
numbers*
*Tuni labarin ya fara nisa, yana kuma da dadi da darasi*.
*08089965176*
*07084653262*

*✍️

★ALKALAMIN JIKAR NASHE📲


*GASKIYAR LAMARI*
(New Book)


Wattpad @Nazeefah381.

Arewabooks @nazeefah.

*Kina bibiyar wannan kasaitattan labarin kuwa?*
*Babu jira babu dako, domin tuni an yi nisa.*
*Tuntube marubuciyaar wa wannan lambar*
*08033748387*


*INA MATUKAR GODIYA GA FANS DINA NA AREWA*
*NA JI DAD'IN YADDA KUKA YI SUPPORTING DIN RUBUTUNA. UBANGIJI YA KARFAFE KU, YA
SHIRYA ZURIARKU*.

*ZAN YI KEWARKU*
*GA WADANDA BASU BIBIYI LITTAFAINA NA BAYA NA, ZAN KAWO MUKU SU AREWA AKAN FARASHIN
MAI SAUKI*.

*Godiya kan godiya ga jama'ar what's app, mussaman wanda suka saka kudinsu suka
sayi wannan labarin*.
*Na gode sosai, bazan gaji da gode muku ba*.

*Yabo da jinjina ga y'an special wadanda nake basu ta private, na gode da
soyayyarku ga rubutuna.*


Sai washagari aka hak'ura da juyayyin rashin Bulkachuwa. Dada tun asuba ta yi
wankan tafiya gano shi. Tana yi tana fad'in "Allah a saukakawa wannan yaro. A
jibanci lamarinsa.
Ya ci arzikin ma'aiki. Ya ci albarkacim Shehu mai karama".
Da wuri ya kawo Iklima. Ya ce "Dada zan dawo idan an yi azahr zan kai ki gano mai
sunan manya."
Ta ce "Ina ce yanzu zamu tafi Ali?"
Ya ce "Ai yanzu baza su bari ma a gan shi ba."
Ta kyabe baki ta ce "Ina ce Ammar yana wajen? Ni da nake da kafa har a mini iyaka?"
Ya ce "Yi hak'uri, ki bari na dawo, tiyatar haihuwa zan yiwa wata mata karfe tara
zan shiga."
Ta rausayar da kai ta ce "Shike nan sai ka dawo, ya zan yi?"
Da ga dawo kuwa gabadaya suka rankaya ganin Tijjani. Ni da Babah kawai aka bari a
gida. Da ga can zasu biya gidan Iklima su bar ta a can.
Dada ta kalle shi ta ce "Mai sunan manya kana wuridin *RABBI INNI LIMA ANZALTA
ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN kuwa?"
Ya ce "Ina yi sosai, ina kuma ganin tasirin ta Dada. Komai ya saukaka mini, na samu
k'arfin zuciya da tawakkali, iyalina kuma suna cikin rufin asiri mai yawa ".
Ta ce "Hakane, Hakane! Cikin tausayawa.
Sun jima sosai suna shirin tafiya ta cewa su Yaya Ummi su yi gaba tana zuwa.
Yaya Ummi ta kalle shi da idonta da suka yi ja. Da rawar murya ta ce "Yaya
Bulkachuwa sai mun sake zuwa".
Ya yi mata murmushi ya ce "Ummilolona kullum sai kin yi kuka? Kamata ya yi ki gode
Allah ina rayuwa. Ban rasa komai ba sai y'ancina. Wanda duk ya zo kurku bisa
zalunci sai ya samu daukaka, so ku tsananta yi mini addu'a ba kuka ba".
Ta share hawaye ta ce "Allah ya nuna mini ranar da zaka fito Yaya Bulkachuwa sai na
yi azumi uku da ikon Allah".
Haka kawai ya ji ta bashi tausayi. Tun tana k'arama ta damu da shi ainun. Shima
kuwa idan aka dauke Ihisan da su Aliyu ba shi da wata yar'uwar da ta wuce ta. Ya
tabbatar ko bai auri Yabi ba, amincinsa da ita mai yawa ne. Sai aurensa da Yabi ya
sake girmama amincin nasu domin ya sani, tana son Yabi fiye da komai. Shiyasa ta
sake kaunarsa, ta kuma bada gudunmawar shawo masa kan Yabi matuka gaya.
Suka tafi, su mama duk jiki ya mutu, tausayi ya ratsa jikin kowa.
Sai da suka yi nisa Dada ta sassauta murya ta ce "Mai sunan manya wai anan din
akwai d'akin sirri ne, ko kuwa a ina kuke haduwa da Yabi?"
Kunya ta kama shi. Ya kasa ce mata komai. Ta ce "A a ba kunya zaka ji ba. Kawai ka
fad'a mini domin idan cikin jejin can kuke shiga a samowa jinjirar taimako domin
idan aka samu ciki da ranar Allah, kuma a fili irin haka aka yi tarayyar da ciki ya
shiga to fa wannan yaron ko yarinyar rashin kunyar da zasu yi sai ya gigita kowa".
Dariya ta k'wace masa. Ya yi kad'an ya gintse tare da ce wa "Ki yiwa Allah ki bar
maganar nan haka. Ki nemo mata taimakon ki kuma tsananta yi mata addu'oi kawai".
Ta saki ajiyar zuciya ta ce"Mai sunan manya abin ne yake ta bani mamaki to ta ina
kuke kebe wa ne? Ga yarinya nan ta kwaso Aliyu amma cikin ikon Ubangiji doguwa ce
sambal. Dazu ana mata wanka da na zuba mata ido gabobinta irin naka ne sak, haka
gashin kanta. Oh ni Binta. Kullum ina kuka da zullimin rashin ka ashe kai baka fasa
komai ba?"
Ya murmusa ya ce "Kina sauke mini dala'ilalul khairati kuwa?"
Da hanzari ta ce "Duk satin duniya kuwa. Ko wacce juma'a nake sauke wa. Kuma
hadiyya ce a kanka. Mai sunan manya na ga gurbinka! Dakina a bushe, babu kayan
shayi irin naka. Babu sabulai da turaruka irin naka. Ta hau kuka sosai. Jikinsa ya
yi sanyi. Ya ce su Baban Kasuwa basa siya miki ne?"
Ta ce "suna siya amma har sai sun k'are, kai kuwa kafin su k'are ka kawo wasu.
Sabulai da turare masu kyau ba masu s'aukin kudi ba. Amma yanzu fa?"
Ya ce "Ammar da Jabir basa yi miki ne Dada?"
Ta kyabe baki ta ce "Jabiru kam ai yanzu fama yake yi da kansa. Har ya gama samun
damarsa kuwa ban wani more shi ba. Kasan sun k'ullace ni akan ku. Wai nafi sonku.
Iyayensa kawai yake yiwa. To yanzu an yi mutuwar kasko, kowa ma ya rasa.
Shi kuwa Ammar yana yi mini bazan masa k'aharu ba".
Amma sai ta waiwaya ta sassauta murya ta ce "Da uwarsa muke raba daidai. Idan ba'a
hannuna ya bani kudi ba kuwa, basa zuwa mini".
Ya yi shiru, tausayinta ya kama shi ainun. Abin da ya fahimta Baban Marina da
mahaifiyarsa sun fi dukkan y'aya'nta yi mata biyayya da kyautatawa a gareta. Sune
kuma wadanda ta rayu tana nuna musu rashin soyayya. Komai sune a baya. Amma kuma
shi da kansa ya tabbatar Dada tafi sonsa akan kowa cikin jikokinta. Domin Ammar bai
samu sukunin yi mata raddi da fito na fito da ita ba. Da ace shine yake da
nutsuwarsa da bai san yadda zata ririta shi ba. Ya tuna sadda zai sadada ya kwashe
mata yan kobbonta da kayan amafaninta ya siyar. Bata yi masa fada a gaban jama'a.
Bari take sai dare ya raba kowa ya kwanta sannan ta shiga dakinsa su yi sababi,
tana yi kuma tana ce wa murya kasa k'asa mai sunan manya kada a gane halin da muke
ciki.
Shi kuwa sai ya bude muryarsa ya ce "Aji mana tunda sharri zaki k'ala mini saboda
kin washe ni. Duk yawan jama'ar gidan nan m, babu mai yi miki sata sai Tijjani!
Nan da nan zata bar maganar ta ce "Alfarmar shehu zaka bari. Darajar sunan da ka
ambata na yafe maka, Allah ya shirya mini kai, ya tsare ka daga hau da sharrin
zamani".
Ya nisa ya sake murmusawa ya ce "Ki yi hakuri zan fad'awa Aliyu ya dinga yi miki.
Ki kuma cigaba da yi mini addu'a Dada. Sannan ki yafe mini ta'adin da na yi miki a
shekarun baya.
Da azama ta ce "Wallahi na manta komai. Kuma menene baka yi mini ba da ka samu
dama? Aliyu kuwa ai shima a k'ullace yake da ni. Ya sha fad'a mini ina nunawa
uwarku butanci. Wanda sharri ne kawai, to wa zai haifi d'a ya ce baya sonsa saboda
Allah? Jiya kuwa a gidanka ya ce "Yasan nafi sonka a kansa. Sannan kasan matarsa
d'iyar Alhaji ce, su kuwa gabadayansu sun kwashe kayansu a gaban ma'aiki akan
sha'anina. Yabi ce kawai take mini sassauci, itama dan tasan ni da kai ba dai mutum
ba. Duk tsiyatakunta, duk yadda ka jarabtu a kanta, ba zaka k'i jin kaina ba, ba
zaka k'i ni ba!
Ta fad'a cikin sigar tausayi.
Ya saki gauron numfashi ya ce "Ki yi hakuri Dada. Za'a gyara. Yanzu ki daina
damuwa. Sannan kada ki koma Toro. Ki zauna anan BAUCHI ki dan huta. Idan jama'a sun
tafi zansa a kawo miki kaji Babah ta gyara miki, ki dinga cin abin ki. Idan sun
kusa karewa za'a sake soya miki wasu. Sannan yanzu a hanya za'a siya miki kayan
shayin ki, ki ajiye a wajen ki. Naki ne ke kad'ai kada Yabi ta yi miki k'auron
nata".
Ta yi maza ta ce "A a itama tana yi mini alheri, sannan tunda aka sakaye ka soyayya
ta sake kulluwa a tsakaninmu, kullum muka hadu sai mun yi kuka. Kasan yanzu ta yi
hankali. Gara na fad'i gaskiya ko ba haka ba".
Ya yi dariya ya ce "Ho Dada ta Yabi. Tsoron ta kike ji ne yanzu?"
Ta rausayar da kai ta ce "Uum kaidin mata mai yawa ne. Yanzun nan idan ta murde
kai ma sai ka juya mini baya a kanta. Barta dai tunda ta nutsu, kuma tana mini ya
kamata. A lallaba a tafi a haka, domin na riga na yi imani da kiararin da na ji
ubanta yana yi mata. Na ce wa ita kad'ai gayya ce a gidan Marina. Ko kasan kaf
zuri'ata babu mai ruwan kudi a hannunsa irin Yabi? Yadda na gasgata karamar Shehu
haka na gasgata kudinta na halali ne. Ka ga yadda ta mayar da dakin uwarta ne? To
ragowar matan uban ma duk ta yiwa dakunansu kwaskwarima lokacin auren Ubaida. Idan
ka ga bajintar da ta yi a auren kuwa sai ka rik'e baki. Matar gwamna har tawaga ta
turo su wakilce ta a bikin.
Kofarsu tafi ko ina haske da kyawu yanzu, kuma duk ita ce. Ko kai ma irin yadda
kake yiwa ubanta ai saboda ita ne. Yabi, Yabi duniya ce? K'aramar halitta sai
babban al'amari".
Ya kwashe da dariya ainun.
Ta ce "Allah kuwa. Mata ai yanzu sun ri'ka. Idan basa yin ka to mijinsu ma ba zai
maka kallon rahama ba".
Ya sake yin dariya ya ce "Duk zan fad'a mata ne".
Ta kyabe baki tare da ce wa "To hudawa cikinka wuka da kanka.
Ta jima kafin ta dingisa ta tarar da su a mota suka tafi.
**
*Watanni uku a gaba*
Zuwa lokacin Husna ta yi gubibi da ita. Shayarwa na matukar ciko da Yabi . Saboda
kirjinta suna cika, ita kam tana cikin mata kad'an da goyo yake karbarsu.
Bata da matsalar komai sai ta rashin miji.
Har zuwa lokacin Dada na tare da su.
Ba zato ba tsammani Aliyu ya zo ya kwashe su aka yi musu passport.
Sai da passport ya fito yake fad'a musu kudin hayar filling Tijjani ne. Shine kuma
ya ce Yabi da Dada su tafi su yi Umrah su yi masa addu'a."
Ai kafin ya

Please Login or Register in order to submit comment