You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita ma ta fuskanci tsananin da kika fuskanta? Ni fa dukkan y'ay'an
Babanmu ina sonsu da dukkan zuciyata".
Ta zaburo mini ta ce "Ban ce kada ki so su ba, amma ai wata kusan tafi wata".
Na yi dariya na ce "To kawai ki ha'da ni da Nazira da kuma Ubaida ki jamu a
jikinki, ki dai-daita su da ni. Shikenan Kinga kin samu k'anne uku aurarru tashi
guda.
Da sannu suma manyan sai su dawo cikinmu mu zama madaurin tsintsiya".
Ta yi gaba tana fa'din "To uwar Iyah! Ta ya ya zan ha'da shakikiyata da dan uba su
zama duka daya ne?"
Na k'yal-k'yale da dariya tare da fa'din "Yaushe zaki dawo?".
Ta ce "sai an kwana biyu".
Na zauna ina nazarin Yaya Ummi mutumiyar kirki ce, amma rashin adalcin da manyanmu
suke yi mata da kuma yadda kishiyarta ta jefa yan'ubanci a tsakanin y'ay'ansu ya
sanya ta k'yamaci dan uba. Na yi mata uzziri domin ita da yaranta suna fuskantar
zazzafan yan'ubanci.
Ina fatan watarana duka y'ay'an Babanmu mu zama abu guda, ina matu'kar son mu gane
girman nasaba irin ta uba daya.

*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA
KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA
KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*
***
Bai dawo ba, sai da ya sallaci Isha.
A falo ya tarar da ni, na yi wanka na zira doguwar riga cotton mai zuwa da mayafi
babba.
Na shafa turaren oudi(concentrate).
Ya kalle ni ya ce "Ranki ya da'de Asiyata".
Na galla masa harara na ce "Ba taka ba ce".
Ya murmusa ya ce "Ta Ummi ce shikenan?"
Na yi shiru domin so nake na fa'da masa abin da zai bak'anta masa rai.
Amma tunda ya saki maganar bari na k'yale shi sai idan ya sake katobarar cewa ni
tasa ce zan tabbatar masa ba tasa ba ce, ba kuma zan zama tasan ba.
Ya ajiye ledar hannunsa ya fita.
Sai gashi ya dawo da kananun bowls da kuma fork biyu.
Ya zauna kusa da ni.
Ya bude ledar kamshin hadadden balangu ta buge ni.
Ya juyo mini dauri guda ya turo mini gabana. Tare da robar yogurt madaidaiciya mai
sanyi, da kuma robar ruwa shima mai sanyi.
Sannan ya juyo nasa daurin. A hankali ya ce "Bismillah Amarya".
Ban kula shi ba. Na gama yaukina na dauka na fara ci. Sosai naman ya yi mini da'di,
sannan kuma mai laushi ne.
Na cinye tas na bu'de yogurt na fara sha. Rabona da abinci tun karyawar safe.
Duk da an kawo mini daga gida amma ban iya ci ba.
Ganin na cinye yasa ya turo mini nasa ya ce "Kara Asiya".
Na yi kamar ban ji ba.
A sanyaye ya ce "Ba kyau a yi magana mutum ya yi kamar bai ji ba".
Nan ma tamkar ba na wajen.
Ya yi k'wafa alamun ya k'ulu.
Ganin hakan ya sanya na tashi na bar shi na yi dakina ko kwanon da na ci ban kawar
ba, bare na kawar da nasa.
Ina shiga kuma na sanyawa dakin sakata.
Na cire mayafin rigar na haye gado na yi kwanciya ta.
Tunda na kwanta ban farka ba, sai da asuba shima kwakwasa mini kofa ya yi.
Kafin na fito tuni ya bu'de gida ya wuce masallaci.
Yau kam har na gama barcina na tashi k'arfe goma. Da na bu'de kofa na fito a zaune
na same shi akan barandar. Babu alamun gaggawa a tare da shi.
Yana ganina ya mike da sauri yana fa'din "Bari na janyo miki, na roba da sanyi, na
rijiyar kuwa dumi ne da shi.
Ya bu'de bandaki ya dauko botiki ta nufi rijiyar.
Na bishi da kallo. Mamaki nake yi dama Tijjani zai iya yin laushi haka?
Duk wula'kancin da nake yi ba ya fasa yi mini hidima.
Na sake bin kayan jikinsa da kallo. Alamu sun nuna ya yi wanka. Sabon yadi ne a
jikinsa amma ba alamun karin guga. Na tabbatar yadda tela ya ba shi hakan ya saka
su.
Na ja tsaki sosai. Dai-dai lokacin kuma ya zo daf da ni.
Ya ce "Asiya Toro wata rana za'a wayi gari a ga kin zama tsaka fa".
Ban kula shi ba, bare na tanka ya samu sanadin da zai jani da surutu.
Ya wuce ya kai mini bayin.
Na shiga na yi wankana na fito.
Yauma atamfa na dauko koriya Shar. Doguwar riga ce da ta manne a jikina.
Na gyara sosai.
Na gyara d'akin, na zauna. Ya yi sallamah na amsa a dole. Ya ce "Na shigo?"
Na ja tsaki, na kame bakina na tsuke.
Jim ka'dan ya shigo. Na daga kai na kalle shi. Fuska a daure na ce "Na baka izinin
shigowa ne?"
Da walwala ya ce "Tunda baki zabura kin ce kada ka shigo mini ba, ai nasan kin
kammala adana yan kananun abubuwan da kike yi mini k'yashin ganinsu".
Ba'kin ciki ya turnike ni.
Na murguda baki na ce "A a kiyasai ne k'arewar kankantar".
Ya zauna bakin gado ya ce "Ban da samun guri irin na ki Asiya. Ta ya ya zaki dinga
rufe mini kofa, kina hayewa gadon da ba'a siya miki ba sai saboda ni, ni kuma ki
bar ni da kwanan kasa. Kwana nake yi ina artabu da sauro. Amma ke babu ruwan ki, ba
kya gudun maleriya ta yi mini illah?".
Na ki kula shi, bansan me yasa yake bani haushi ba, baya burge ni ko ka'dan.
Ya sake yin k'asa da murya ya ce "Ki yi kokarin kyautata lahirarki Asiya. Babu
ruwan alkalami da cewar ba kya sona. Matu'kar ina kwana da ba'kin ciki ki sani kina
cikin fishin Ubangiji".
Na rasa me zance masa domin dai ya sako wanda ban isa na fa'di bak'ar magana a
kansa ba.
Kan tilas na share ban ce komai ba.
Ya tashi tsaye ya ce ki taso ki karya ga abin kari can a falo.
Bauchi zan je. In sha Allah ba zan wuce la'asar ba.
Za'a kawo miki abinci da rana. Ki shirya gobe zaki fara yin girki".
Sai lokacin na fashe takaicinsa da cewa "Ba zan yi ba.
Har abada ba zan dora tukunya saboda kai ba".
Babu damuwa a tare da shi ya ce "Babu laifi. Lokaci zai fayyace komai ai".
Ya juya ya tafi bai sake cewa komai ba.
Har shad'aya ina daki ban fita falon ba. Sai da cikina ya tsananta yi mini kartan
yunwa.
A dole na fita. Na tarar da waina a karamin flask. Sai kunu a jug. Daga dukkan
alamu siyowa ya yi.
Kan dole na zauna na karya.
Ina zaune har aka fara kiran sallar azahar. Na idar kenan sai ga almajiri yana
kwankwaso kofar shigowa wajena. Da yake ni ce a farko su kuma su Mama na can ciki.
Bamu ha'da komai ba, sai kofar shigowa gidan.
Da sauri na fita na bu'de masa. Ya mik'o mini flask din abinci babba mai kyau. Wai
wani ne ya bashi ya kawo wannan kofar.
Na kar'ba ba tare da na ce komai ba. Na sani abincin da ya ce za'a kawo mini ne.
Sai da na zauna a falo na bude na ga alalan gwangwani ya ji manja.
Da alamun kifi a ciki. Na ji wani iri a dalilin yunwa nake ji ba ka'dan ba. Ni kuma
bana iya cin alala na koshi. Tabbas an gyara shi ne dan a burge ni. Na rufe, ina
sake jin yunwa na taso mini gadan gadan.
Na yi shiru ina nazari. Sai na ji wayata na k'ara. Ina dubawa na ga Tijjani ne
domin ina da lambarsa tun lokacin kwamshina da muka fara dan gaisawa. Na ki amsawa
har ta katse. Ya sake kira ban dauka ba. Bai fasa ba, sai a karo na hudu na dauka a
fusace na kan ga a kunnena, bayan na danna alamar amsa wa.
"Yaro ya kawo miki abinci?"
"Eh".
Na fa'da a gajarce.
Ya ce "kin ci na safen kuwa?"
"Wai ni kam jinjira ce ne da zaka dinga mini tambaya tamkar kankanuwar yarinya?
Idan ma ban ci ba ai cikina ne ko? Tunda baka shawarce ni akan abinda zan ci ba, ka
ajiye mini wanda ya yi maka".
Ya nisa ya ce "Asiya Toro kenan!
Cikin kuka na ce "Komai zaka ce Allah na ganinka ai".
A sanyaye ya ce "Kukan na menene Asiya?"
Na sake tsananta kukan na ce "Akan me za'a kawo mini alala? Ni bana ci".
Ya tausasa murya ya ce"Alalan gwangwani ne, saboda ke har kwai da kifi aka saka a
ciki. Daga gidan abokina Abdul aka kawo miki fa, kema kuma kinsan matarsa mai
tsabta ce".
Da kukan na ce "To ni ina ruwana, ni dai ba zan ci ba, kuma yunwa nake ji tunda
kunun ma ban iya sha ba, ya riga ya yi sanyi k'arara."
Ya diririce ya ce "Ki yi ha'kuri bari na sa a kai wa Ummi macaroni da kayan miya
sai ta daho miki yanzu. Hakan ya yi miki?"
Na yi shiru. Ina harara tamkar yana wajen.
Ya sassauta ya ce "Please mana Asiya ki ce to".
A shak'e na ce "Yanzu d'aya da rabi. Idan ya wuce uku da rabi bazan ci ba, gara
yunwar ta kashe ni".
Ya dinga fa'din"Na gode sosai, bari na saka a kai mata yanzu. In sha Allah ba zai
wuce hakan ba."
Ya katse wayar.
Na ri'ke wayar, haka kawai sai na tsinci kaina da mamakin yadda Tijjani yake rawar
jiki a kaina. Gashi tunda na zo ban ta'ba yi masa wani alheri ko da ta magana mai
da'di ba ce.
Yadda ya lank'awasa harshe yana rarrashi tabbas yana yi ne tunda ga kasan
zuciyarsa. Na fara gasgata sona yake yi ba sha'awa ba.
Mintina biyar a tsakani ya sake kira.
Na dauka bayan ta kusa tsinkewa.
Da sauri ya ce "An tafi kai mata. Na ja mata kunne, na ce ta bar komai ta girka
miki, tunda Nina sanya ta. Biyu da rabi zan aika a karbo mini. Dan haka zuwa uku
za'a kawo miki in Allah ya yarda".
Na yi shiru. Ya numfasa ya ce "Asiya ba ki ce komai ba".
"A hankali na ce "Ina ji ai"
Ya yi kasa da murya ya ce "Me zan taho miki da shi?"
"Bana bu'katar komai na ka".
A sanyaye ya ce "Shikenan, amma na siyo miki abin da nasan zaki yi murna".
Na kyabe baki tare da fa'din "Hmm to ya yi".
"Baki ce na dawo lafiya".
A gajiye na ce "Tijjani ni na aike ka ne? Ka dame ni, in ta nine ma kada ka dawo".
Kada na dawo Asiya? Saboda ke na yi tafiyar fa! Amma idan na dawo zaki ga ni".
Ban bashi amsa ba na kashe wayata.
Na ajiye ina jin wani irin abu da bansan menene ba yana mamayata.
Uku saura na ji ana buga k'ofar.
Na zari hijabi na nufi k'ofar.
Yaro ne ri'ke da madaidaicin flash.
"Gashi in ji wani a waje".
Ya fa'da a hanzarce da alamu sauri yake kada ya yi latti tunda kayan Islamiya ne da
jikinsa.
Na kar'ba na tura kofar.
Kicin ma fara shiga na dauko plate.
Sai lokacin na lura da kwalin taliya, macaroni da galan din mai dana manja.
Sai wani katon bokiti sosai mai murfi. Na bu'de na ga garin masara ne a tankade.
Daga kantar kuwa an jere robobi masu dauke da kuka, kubewa daddawa da yaji.
Sai kunshin bakar leda mai dauke da Maggi da onga da kuma gishiri.
Na yi tsam da raina. Ina jinjina wannan kokarin. Na sani Kuma Babanmu baya irin
wannan al'adar domin shima baya bari a dorawa ango hidima mai yawa.
Na tabbatar a kaina aka fara irin wannan hidimar ni din ma saboda Tijjani ya yi.
Daga can gefe na sake hango buhun gishiri a cike amma kuma d'aure bakin aka yi. Na
saka hannu na ta'ba na ji don na tabbatar ba gishiri ba ne.
Ina tabawa kuwa na gane shinkafa ce a ciki.
Na girgiza kai ba tare da na furta komai ba.
Na dauki abin da zan dauka, na fice.
Na zauna ina cin abincin da ya yi mini da'di ya ji kifi da albasa.
Na bu'de fridge ga mamakina sai n ganshi cike da pure water da lemon fanta da coke
da kowanne zai yi shida.
Take na fahimci katon daya ya siya aka hada masa kaloli.
Na dauki ruwa da lemo na rufe.
Ina ci ina nazarin yadda Tijjani yake ta rawar jiki a kaina.
Wayata ta hau kuwwa. Kamar ba zan dauka ba sai kuma na dauka din.
Da sauri ya ce "Network dina ne ya dauke. An kawo miki abincin, kin ci?"
A shak'e na ce "Ni ban ci ba, yaji ya yi yawa, ga shi salam babu gishiri ko maggi
ne oho".
Ya diririce ya hau fa'din "haka Ummi zata yi mini? To a kawo miki yoghurt. Kafin na
dawo na miki girkin da kaina".
Na yi shiru.
Cikin rarrashi ya ce "Pls Asiya Toro".
Na tunzura na ce "Ai da zaka bar Toron baka tuna da cikina ba. Saboda bani da
daraja. Akan me yanzu zaka fitine ni da buge bugen waya da tambayar na ci abinci ko
ban ci ba. To bazan ci ba, idan na mutu ma ai baka da asara."
Ya harzuka ya ce "Botsarriyar yarinya kawai! Ana taro ki, kina sake nausawa, to kar
ki ci din. Allah ne shaidar na yi bakin kokarina".
Ai kuwa na zunduma ihu tamkar gaske. Na katse wayar.
Ya dinga kira amma naki d'agawa.
Ya kira ya kai sau biyar ina gani ban dauka ba.
Daga can sai ga text message.
Kamar bazan bu'de, sai kuma na bu'de din.
"Asiya Toro ki ji tausayina! Ki daina mini irin haka. Kinsan yadda zuciyata take
bugawa a dalilin kukanki da kin daukar kirana?
Ki yi ha'kuri bazan sake yin tafiya na barki hakan ba. Kuma indai na iso lafiya da
kaina zan dafa miki komai kike so".
Jikina ya yi sanyi. Tsawon lokaci na kasa gane yanayina, tausayi ya bani ko kuwa
mene ne?
Na bu'de what'sapp na ga anan ma ya turo mini sakonni.
Na kasa bu'de wa domin bana son na sake jin fiye da kasalar da nake ciki.
Da yamma lis sai ga shi ya dawo. Na bu'de masa kofa ya shigo dukkan hannuwansa
ri'ke da ledoji.
Ban yi yun'kurin kar'ba ba. Da walwala ya ce "Asiya Toro babu oyoyo sai kallo mai
kama da harara?"
Na gintse fuska na yi gaba, na bar shi.
Ya biyo ni falon dana shiga. Ya ajiye mini a gabana.
Ya fita da sauri sai gashi ya kinkimo kwanon satellite ya ajiye a tsakar gidan ina
hango shi ta windo.
Da'di ya yi matu'kar kama ni. Domin na kagu na fara kallo.
Ya sake fita ya dawo rungume da kwali a kirjinsa da na yi zaton receiver ce. Dayan
hannun kuma leda ne.
Na yi maza na gyara zamana na yi kamar harkokina kawai nake yi.
Ya shigo da sallama na amsa a hankali.
Ina mamakin yadda Tijjani yake da yawan sallamah.
Ya zauna a kasa a gabana tamkar uwargida da yaronta. Amma girmansa da cikar
haibarsa ya sanya bai yi kama da yaron gida a gabana ba.
Tunda ni din yar mitsil ce.
Yanayinsa yafi kama da na wadda yake neman a amince masa, a gamsu da lamarinsa.
Da barin jiki ya tashi ya dauko roba a kicin, da yar wuka hadi da bowl karami irin
plastic din nan mai k'wari.
Ya debo ruwa a cikin robar. Ya shigo, ya bu'de ledar da tafi kusa da ni.
Apple ya ciro guda biyu ya wanke a cikin ruwan, ya saka su a bowl din tare da yar
wuk'ar ya miko mini ya ce "Fara da wannan Asiya. Ki rage yunwa kafin na gama miki
abincin.
Maghariba ta kawo kai sai na dawo daga sallah zan d'ora miki. Me kike son ci?"
Ban kar'ba ba, ban kuma tanka ba.
Ya ce "Ki kar'ba mana, me yasa kike yi mini haka ne?"
Yadda ya yi maganar a dan tunzure, bansan ya aka yi ba, na tsinci kaina da mika
hannu na kar'ba.
Ya sassauta ya ce "ko na yanka miki?"
Ban amsa ba, illah hannu da na saka a cikin robar na wanke.
Sannan na dauki Apple din na fara gutsura da bakina.
Ya zuba mini ido yana kallon yadda nake cinsa cikin yanga tamkar me cin magani.
Ya murmusa ya ce "Yabi yanga".
Karon farko da kunne ya ji ya kira ki da Yabi.
Na dauke kai na ce "Tsabar adawa da kake yi da hajjina shine ba zaka ce Yabi ba.
Yau kuma da bakinka ya subuce ka fa'da din sai da ka ha'da da bita da k'ullin
yanga?"
Ya fashe da dariya sosai ya ce "Kamar kinsan subutul kalam na yi. Tun fil'azal nafi
son ce miki Asiya domin sunan na matu'kar burge ni. Yanzu kuma tunda Jabir haka
yake ce miki, na sake kauracewa sunan. Bana adawa da hajjinki, amma fa bazan kira
ki da Yabi ba.
Ina fatan na samu damar da zan kai ki sauke faralli Asiya. Sai ki zama Hajiya ta
sosai tunda hakan shine burinki."
Na dauke kai, na gutsuri apple na ce "Da wanne ku'din zaka kai ni Makkah?
Ai indai ina tare da kai babu wani alherin da zai same ni, bare alheri irin na zuwa
Saudiyyah".
Tsawon lokaci ban ji ya ce mini komai ba.
Na juyo da kallona gare shi. Na ga jikinsa ya mutu. Duk kuzarin da ya zo da shi ya
gudu.
Gaba'daya ya zama tamkar an kwara masa ruwan sanyi.
Ni kaina sai na ji jikina y mutu lakwas.
Tsawon lokaci muna haka tamkar masu zaman makoki.
Da k'yar ya yun'kura ya mike ya ce "Na tafi masallaci".
Na bishi da ido, ina jin abin da nake ji a kansa na sake mamaya ta. Na kasa gane
tausayi yake bani ko kuwa menene?
Nasan dai ko ka'dan babu digon sonsa a raina.
Da zai dawo ya shigo da k'aramin gas (3kg).
Daga bakin kofar falon ya tsaya bayan ya daga labule ya ce "Me zaki ci Asiya?"
A hankali na ce "Ni na koshi, akwai macaronin nan a kicin".
Bai ce komai ba. Ya saki labulen.
Da kansa ya zubo abincin.
Sai dai wannan karon a kujerar nesa da ni ya zauna. Bayan ya dauko ruwa da lemun
coke.
Na kalle shi tamkar wani mai wadata ya hakince ya saka ruwa da lemu a gaba.
Ya kammala, ya dube ni bayan ya ha'diye fishins ya ce "Ki dinga jin tsoron Allah
Asiya. Yanzu abin da kika yi ya yi daidai kenan? Ki saka na k'ira Ummi na balbale
ta da sababin bata yi mini aikin da na saka ta da kyau ba. Ashe ma kin ci kin cika
cikin ki, tsabar fitina, da son ki tayar mini da hankali shine ya sanya kike kuka
da fa'din abincin bai yi da'di ba?".
Na zum'bura baki, na kasa cewa komai.
Ya yi k'wafa, bai ce komai ba.
Ya sauko ya zauna kan kafet din ya bu'de reciver ya ce "Gashi na siyo miki."
Ganin ban amsa ba ya sanya ya cigaba da bude ledojin da ya shigo da su. Kusan duk
kayan abinci ne dangisu shinkafa, taliya da macaroni. Sai katon din indomie da
kayan shayi. Sai kuma leda mai dauke da sabulun wanki da su omo, makilin da maganin
sauro na kunnawa.
A hankali ya ce "Ku'din da abokaina suka ha'da mini ne na siyo miki settlite da
gas, shine na karo kayan abinci dan mu dan tura sosai kafin su kare."
Na juyar da fuskata na ce"Madallah".
Ya yi sororo murya a dakushe ya ce "Ba zan yi wani abu da niyyar na sanya ki farin-
ciki ki nuna mini kin ji da'di ba Asiya?"
Cike da iyashege na fara wage baki, dukkan hakorana a waje, ga idona na zazzarosu
tamkar mai motsi a k'wak'walwa.
Ina yin hakan, ina cewa "Na yi murna Tijjani. Ka burge ni Tijjani, na ji da'di
Tijjani".
Sannan na dawo yanayina na zuba masa ido na ce "shike nan?".


*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a
kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu,
nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*
✍️
*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA
BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES*.
*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.


*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki
da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*

*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin
register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*

Ya girgiza kai, bai ce uffan ba, ya tashi ya kwashi kayan abincin ya nufi kicin da
su.
Ina hangen sa ya dauko farantai ya juye kayan miya da ya barsu a tsakar gida.
Ashe har da doya guda uku manya. Sai da ya jide ya adana komai.
Sannan ya daga murya ya ce "Zan je sallar isha."
Bai jira amsata ba yasa kai ya fita.
Na tokara na dauro alwallah dan nima na sallaci isha.
Na idar na jima a zaune sannan na shiga daki na yi shirin wanka.
Na fito na shirya a nutse. Na dawo falo da nufin na sha ruwa. Aka dawo da wuta. Na
kalli receiver dokin a ha'da mini ita ya kama ni.
Ina tsaye na gan shi ya dawo, na tsinci kaina da lekensa ta windo.
Na ganshi da bargo irin mai sau'kin ku'di da kuma pilo guda daya.
Kai tsaye dakin da kayansa suke ciki ya shiga da su.
Na dan ji wani iri. Na tsinci kaina da tambayar kaina da cewar wato bai damu sai ya
zo dakina ba. Duk da k'arancin shekaruna ni din ma'abociyar karatun littafan Hausa
ce mussaman da nake da babbar waya nake karatun littafan online. Ina ganin yanayin
yadda angwaye basa daga kafa a wannan fagen. Sannan da yawa an yiwa kawayenmu aure
da muka kammala k'aramar sakandire, muna jin labarin zumudin angwaye.
Amma shi wannan ko oho. Nan da da nan zuciyata ta baci a dalilin na hakaito*BAKAR
TA'ADAR* Da ya saba yake yi!
Na ji tsanarsa ta sake tsananta a zuciyata.
Na dinga jan tsaki. A haka ya shigo ya same ni. Ya miko mini leda ya ce "Ga shi".
Na juya baya ba tare da na kalle shi ba, bare na kar'ba.
Ya iso kusa da ni ta yadda muke jin hucin juna.
Kamshina ya mamaye wajen, da ace yana shafa turare da sun cakude sun bada kamshi na
mussaman.
Baya wari, amma kuma ana dan jin tsamin maza ka'dan a tare da shi, wanda rashin
tu'amalli da turare ke sababawa.
Takaici ya sake k'ume ni. Hawaye ya cika mini ido.
Ya nazarce ni. Ya nisa ya ce "Wai menene haka kike mini? Tsabar tsanarsa sai na ji
hucin bakinsa mai bashi ne. Zuciyata ta taso na ji tamkar na sheka amai.
Na fa'di kan kujerar da bayana na fashe da kuka sosai.
Ya matso da sauri da nufin rike ni, na k'walla k'ara sosai. Ya yi maza ya janye
hannunsa ya fasa.
Ya sassauta ya ce "ki daina yi mini irin haka Asiya. Ubangiji ya sanya mini k'yamar
na ji kukanki. Fa'da mini me nake yi miki?"
Tsawon lokaci yana dakon amsa ta.
Ya kosa da shiruna ya ce "Ki yi ha'kuri komai zai dai-daita mana".
Cikin matsanancin kuka na ce "Wallahi ba zai daidaita ba. A hakan ne komai zai dai-
daita?
Dube ka dan Allah! Ni gaba'daya baka burge ni".
Ya murmusa ka'dan, ya mike ya ce "Wata rana zan burge ki In sha Allah".
Har ya kai bakin kofa ya ce "Ki ci nama ne, idan kuma ba zaki ci yanzu ba, ki bu'de
shi domin akwai albasa a ciki kada ta lalata shi. Ki kara ha'kuri Asiya".
Ina ganin ya fice na dinga kuka sosai mai dafa zuciya.
Ina jinsa yana ta kiciniyar jawo ruwa a rijiya.
Bayan kamar mintina talatin ya dawo ya zauna kusa da ni. K'amshin sabulun wanka
kawai na ji a tare da shi ba na turare ba.
Cikin rarrashi ya ce "Kuka har yanzu Asiya?
Ba zaki yi hakuri ba! Ko wanne bawa da kaddararsa, ba ke ka'dai ba ce, ki tsananta
addu'a."
Cikin kuka na ce "Addu'a sau milyan nawa zan yi?
Ai kaine matsala ta ni kam."
Ya yi shiru can ya ce "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!
Na mike da sauri na bar shi a wajen.
Ina shiga d'akin na rufe kofar da k'arfin gaske.
Na jima kafin barci ya sure ni.
Bansan yadda ya kare a inda na bar shi ba.
Washagari kuwa tunda na yi alwallah da asuba da na rufe kofata har shad'aya ina
kwance duk da ba barci nake yi ba.
Sau biyu yana kwankwasa k'ofar. Amma na share shi.
Ban fita ba sai wajen shabiyu da rabi.
Shima uzzirin shiga band'aki ne ya uzzira mini. Kan dole na yi shirin wanka.
Na fito na tarar da shi a saman katanga yana ta daura kwanon setelite.
Ya ha'da zufa sharkaf. Na ja tsaki na shige band'aki.
Abin mamaki sai na tarar bayan robar band'akin da take a cike. Ya cika mini botikin
wanka ya ajiye a inda ya saba ajiye mini.
Na yi shiru ina wasi-wasin yadda saurin fishi

Please Login or Register in order to submit comment