You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son ci na dafa miki?"
Ba walwala a fuskata na ce "Babu".
Ya matso ya durk'ushe tamkar mai neman gafara. Ya ce "Kin amsa kin yafe mini, kin
amsa kin rufe maganar me zai sa kuma ki basar da ni? Na ro'ki dan darajar Annabi ki
yafe mini, dan Allah. Shirun ki bala'i ne. Ki fa'di komai na zuciyar ki, zan
ha'diye, na sani ban kyauta ba, amma nima bansan me ya same ni ba."
Da kuka na ce "Tun yaushe kuke yin hakan?"
Da rawar murya ya ce "Ranar ne kawai, Wallahi shine na farko kuma na k'arshe
Asiya."
Na ce "Ban yarda ba. Ina ce dama kafin ranar ka ce mini ni bana danne ka yadda kake
so?".
Ya daburce ya ce "Billahillazi kawai na fa'da ne, amma ba dan ina yin wani abu ba
ne. Ki yarda da ni, ki bani wata damar, kada ki yanke aminci da yarda a tsakaninmu
dan Allah".
Ya fa'da hankalinsa a tashe matu'ka.
Ya ru'ko hannuna ya ce "Ki ji tausayina. Zuciyata zata iya bugawa idan kika cigaba
da share ni, na yi tuba a wajen Ubangiji, ke ma ga ni durk'ushe a gaban ki, ki yafe
mini"
Na kafe shi da ido hawaye na zuba. Shima ya zuba mini nasa da suka kada suka yi
jawur.
Da kuka na ce "Kana tunanin zan samu nutsuwa idan kuna rayuwa da it'a a gida daya,
kana ganin zan iya mance wa idan ina ganin gittawar ta?"
Ya yi shiru. Na ce "ko ina son na manta ba zai yiwu ba. Dan haka zan fa'da maka
gaskiyar magana. Sai dai ka zabi daya a ciikin ni da ita".
Ina rufe baki ya ce "wanne irin zabi ne wanda babu azanci a cikinsa? Ta ya ya zaki
ce na zaba a cikinku? Ai ke ce tawa, ke nake so, ke nake burin rayuwa da ke, ke
kike burge ni."
Da rawar murya na ce "Ita kuma tana baka sha'awa, kana son ka ji manyan mazaunanta
a k'asanka, kana son kama manyan non..".
Ya yi maza ya rufe mini baki jikinsa na bari irin na zullumi.
Ya ce "Na zabe ki, ke nake so Yabi Ubangiji ne shaidar ban so wata mace kamar yadda
nake son ki ba. Na kuma yi imanin ba zan so wata sama da ke a bayan ki ba."
Na goge hawayen idona na ce "muhimmi a gurina ka zama kamamme, idan har son da kake
yi mini bai yi tasirin da zai kange ka daga ta'ba haramun ba ai banzar wannan son".
Da rawar murya ya ce "Allah ka mayar da ni kamamme. Allah ka yafe mini, Allah na
tuba".
Tausayinsa ya kama ni yadda yake daga hannuwansa yana ro'kon da dukkan zuciyarsa.
Na nisa na ce "Mu fuskanci gaskiya. Idan da gaske sonka nake yi to akwai bu'katar
na baka gudumawar da zaka tsira daga fa'dawa halaka. Na yarda na kuma gamsu kana
sona. Nima kuma idan gaskiyar zan fa'da ina son ka. Amma na sani ban zo maka a
yadda kake fatan matarka ta zo maka ba. Na yi amanna jikina bana manyan mata ba ne.
Nan da shekaru goma ma ba zan yi girma shahararre ba. Dan haka ka aure ta kawai".
Ya zabura ya ce "Kinsan me kike fa'da kuwa?"
Idona ya sake cika da hawaye na ce "Na sani mana, kuma har cikin zuciyata nake
nufin hakan"
Ya sake ni ya na girgiza kai ya na fa'din bana sonta, bana burin na aure ta, ko ina
da halin k'ara auren ma kamammiya nake so wacce bata san namiji ba sai a kaina
tamkar yadda na same ki".
Maimakon na ji da'di sai na sake shiga rud'u.
Da rawar murya na ce "ka tabbatar ba budurwa ba ce? Ashe ba iya abin da na ga ni ya
gitta a tsakaninka da ita ba kenan?"
Cikin ido ya kalle ni da dukkanin gaskiyar sa ya ce "Na rantse iya abin da ya faru
kenan. Amma kuma duk macen da bata san namiji ba ai ba zata dinga shige masa ba. Ba
ni na je inda take ba, ita ta kawo kanta. Ko da ina son na ta'ba ta sai amince, kin
ga ni kuma ba dole na yi mata ba, da son ranta ne, na tabbatar bani ka'dai ta ke
yiwa hakan ba, ba ni ka'dai take sakarwa ba. Dan haka ina cikin nutsuwata bazan
auri shasha ballagaza ba".
Y'anmata kalubalenku abin da mijin Yabi ya fa'da shine gaskiyar magana, saurayin
nan da kike amince yake ta'ba ki ba zai aure ki ba, sai tsananin rabo. Idan rabon
auren ya rantse kuwa har ki tsufa a hannunsa ba zaki fita daga zargi da
wula'kancinsa ba.
Ba shakka wayewar da ta sanya kika bar shi yake lalube ki, to shifa a ballagaza
wacce ta saba cudanya da maza daban daban yake miki kallo. Sannan ticket din
kaskanci kika yankarwa kanki.
Ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali ya yi wanka.

*Cikakken labarin zai fara zuwa muku ranar 09/09 wanda a wannan ranar mahaifiyata
zata cika shekaru ashirin da uku da barin duniyar nan*.
*Dan haka zan yi amfani da wnanan damar dan ku taya ni mika mata addu'oin gafara da
rabauta a wajen Ubangiji*.
*Na gode sosai Ubangiji ya saka muku da alheri bisa soyayyar da kuke yiwa
rubutuna*.

*VIP 1K*
*REGULAR 500*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM*
*ZENITH BANK.*
*A TURA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAYIN 08032773332 KO KUMA 09069067488*
*NA GODE SOSAI*

✍️.



*ANTI KULSUM BAUCHI HOW FAR?🥰*
*KIN TUNA RANAR DA NA CE MIKI INA RUBUTU?😄*

67&68.
Na daskare a zaune, wato duk tantirancin namiji shi kamila yake so.
Duk yadda zaki sadaukar masa da komai da sunan soyayya shi fa a zuciyarsa ba haka
ba ne.
A yau na k'ara fahimtar darasin rayuwa. Na kuma k'ara gode wa Allah da na tsallake
sirad'in yanmatanci lafiya.
Na kalle shi cikin tu'ajjibi na ce "To ka sani Wallahi bazan zauna a cikin gidan
nan ba. Matu'kar kana son kwanciyar hankali da walwala to kuwa bana son gidan, ba
kuma zan zauna a cikinsa ba."
A rikice ya ce "Asiya kin san dai da yadda aka biya ku'din rabin shekara yanzu wata
guda tal muka yi, ta ina zan fara neman wani gidan?"
Ido cikin ido na ce "koma ta ina ne, na baka nan da sati if not Bilhiillazi bazan
ha'kura ba. Sai dai ka nemi ni ka rasa shike nan sai ta tattaro ta maye maka
gurbina."
Ya yi muk'us ya kasa zaburo mini.
Ya nisa ya ce "Haba little nan da sati me zan yi na samo ku'di? Kin san dai ba dawo
mini da kudin zasu yi ba, bare na kama wani".
Na ce "Sai na baka aro, ka karbi zobena ko dan kunne ka siyar, sai ka biya ni idan
ka samu hali".
Ban san ya aka yi ba kawai ya fara nuna ni da yatsansa cikin sababi yana fa'din
"Nafi karfin ki kama gida na zauna a ciki Asiya. Ba zan yi wannan lalacewar ba, har
abada da ikon Allah."
Na kafe shi da ido tsawon lokaci har ya fara kame kame. Na nisa na ce "Tijjani ni
kake yiwa wannnan shouting din?".
Na girgiza kai na ce "Ba laifin ka ba ne. Laifina ne da na yarda da afuwar da Malam
ya yi maka ba tare da na bayyana tozarta ni da ka yi ba. Afuwar da aka tilasta ni
na yi maka ne ya baka kuzarin yi mini sababi irin haka ko?
To Wallahi bazan zauna a gidan nan ba. Komai za'a yi da ni kuwa".
Na mik'e na bar shi, ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye shi. Domin ya ga na koma
Yabin Marina marar sassauci.
Ban jima da shiga d'akin ba sai ga shi ya biyo ni jikinsa a sanyaye. Ya zauna kusa
da ni ya tausasa harshe ya ce "Ke little ba ki fahimce ni ba ne. Ki yi hakuri, zamu
tashi, amma pls ba nan da sati daya ba dan Allah."
Na ce "To".
Ai kuwa nan da nan ya hau fa'din "Na rok'e ki fa Little. Ban son irin wannan to din
na ki".
Na share shi. Ya dinga jaye-jayen magana amma ban tanka masa ba.
Sai kuma ya bani tausayi yadda ya yi shiru ya rasa abin yi.
A zuciyata sai hango girman gatan da Ubangiji ya yiwa mazaje nake yi. Domin duk
girman laifin da zasu yi wa mace sai Ubangiji ya sanya hakuri da sassauci had'i da
rauni a zukatan mataye. Nan da nan mace zata yafe ta kuma manta musganwar miji.
Na tuna ranar da ya rufe mini gida dan kawai na je na na yi sana'ar da zan samo
masa ku'din da zamu rufa asirinmu. Amma har washagari yana sababin sai na tafi
gida.
Amma ni na fita unguwa na dawo na tarar yana shek'a ayarsa. Na girgiza kai domin
nasan da ace ni ya ga ni a cinyar Yaya J sai ya masa dukan mutuwa tunda ba
k'arfinsu daya ba. Ni kuwa zai yi wahalar gaske idan bai sallama ni ba.
Na kalle shi na ce "Na tambaye ka?"
Ya d'aga mini kai tabbacin eh.
A hankali na ce "Idan ni ka ga ni a cinyar wanin ka ya zaka ji?"
Ya ce "Wata'kila zuciyata bugawa zata yi, wata'kila kuma na had'u da mummunan hawan
jinin da zai kanannad'e ni."
Na sake zuba masa ido na ce "Amma me yasa baka yi zaton nima sakamakon hakan zai
iya samu na a dalilin ganin wata a jikin ka ba?"
Ya fara sosa k'eya. Da k'yar ya ce "Ban san ya aka yi hakan ta faru ba. Ni
gaba'daya am upset ma".
Na girgiza kai na ce "Hmmm".
Muka yi shiru sai kuma na ce "Kuma zaka zauna da ni idan ka gan ni a irin yanayin
da na gan ka?"
Ba ja in ja ya ce "Ba zan iya ba".
Na zuba masa ido ina masa kallo mai tsananin gaske.
Na kaurara murya na ce "Amma kuwa son zuciyar ka azimin ne Tijjani."
Bai yi inkari ba. Bai ce komai ba, na kuma tabbatar da dukkan zuciyarsa ya bani
amsar.
Kamar daga sama sai na ji ya ce "Mace daraja ne da ita sai wacce ta wula'kanta
kanta. Duk matar auren da zata bada k'ofar da wani namijin zai mata waya, ko
doguwar gaisuwa dama ai ba kamammiya ba ce. Ba kuma yadda za'a yi mijinta ya
gasgata ta. Bare kuma a ce har ya ga ni da idanuwansa, tabbas ba zai zauna da ita
ba, ko kuma idan ya ri'ke ta din ma bisa wani dalilin to fa har abada ba zata ji
dadinsa ba."
Na sassauta na ce "Amma shi namiji idan yana sharholiyarsa ko da kuwa a cikin gidan
aurensa ne dole ne matar ta yi hakuri ta zauna da shi ko?"
Ya kasa amsa mini.
Na zarce da ce wa "Ana rudarku da cewa duk abin da namiji ya yi ado ne, na mace ne
kaico. To ka saurare ni da kyau abin da zan fa'da ka sani sai dai zan sake yi maka
matashiya ne na kuma kafa maka hujja tunda yanzu ka sanya an tursasa ni na yafe
maka.
Laifin namiji baligi da na mace baliga a banagaren barna duk daya ne a fuskar
addini tunda duk hukunci iri d'aya Ubangiji ya zartar.
Al'amari irin wannan kuma bashi ne in ji Annabin Rahma. Idan mutum ya bata y'ar
wani, shima za'a bata tasa. Idan ka yi da matar wani, kai ma za'a yi da taka.!
Na kaurara murya na ce "Na yarda baka yi zina ba Tijjani. Amma kana kusantar ta.
Kana bin hanyar da ta bi. Ka sani kuma Allah da kansa ce wa ya yi kada mu kusance
ta, ba wai kada a aika ta ba. Ina ro'kon ka, ka daina kusantar ta bare tsautsayi ya
sanya ka fa'da yin ta da auren ka. Ina jin tsoro da zullumin kada na fara haihuwa a
b'ata mini yara. Ina cikin fargaba kada laifin ka ya jefa ni cikin had'arin a
lalata ni da aurena".
Ya zabura ya ce "To y'ar sarkin mugun fata da jawo bak'in alkaba'i."
Na kalle shi na ga ya shiga rud'u a dalilin furucina sosai. Kishinsa ya bani mamaki
ainun.
Ban ji d'ar ba na ce "Gaskiya na fa'da maka, wacce Annabi ne ya fad'a tun gabannin
kakaninmu su iso duniyar.
Bayan haka kuma ina son ka sani laifin da ka yi tabbas na ha'kura. Amma ina
tabbatar maka idan na sake kama ka da irin wannan laifin to fa ka sani ka kuma
ri'ke a zuciyar ka ba zan sake zama da kai ba Wallahi".
Ya matso kusa da ni ya rungume ni sosai yana fa'din "Da ikon Ubangiji bazan sake ba
Asiya. Ki taya ni addu'a. Ina kuma ro'kon ki sake hakuri, ki shafe wannan al'amarin
a zuciyar ki. Wallahi summa Tallahi iya abin da ya faru ke nan, kuma a wannan ranar
na ta'ba yin hakan, kada shaidan ya rinjayar miki ce war na saba yi din ne.
Na kuma fahimci Ubangiji ya so ni da alheri ne shi yasa ma asirina ya tonu."
Na saki ajiyar zuciya mai nauyi na ce "Shike nan Allah ya yafe mana gaba'daya."
Ya sake ri'ke ni sosai yana fa'din "Na gode sosai, Allah ya sanya ki cikin bayinsa
da yake kar'ba daga gare su."
Hawayen da ban san dalilinsa ba ya dinga zuba mini.
A hankali na ce "Ameen".
Shike nan muka rufe maganar. A ranar ma mutum uku suka zo lalle amma hakuri na basu
da gabatar da uzzirin ban warware ba. Domin gaba'daya na rasa karfin zuciyata.
Rauni mai yawa nake jin yana bina. Sannan wata irin karaya da al'amarin Tijjani ya
haifar mini da gajiya da kasala masu nauyi a zuciyata wanda gangar jikin ta rasa
k'arfi da kuzari.
Bai ce komai ba. Amma jikinsa shima ya mutu domin ya fahimci k'arfin halin da nake
yi iya gangar jikina ne kawai.
Da daddare ya ri'ke ni, ya dinga rarrashi, da ban baki irin wanda sai masanin
falsafa ne zai dinga harhada kalaman masu nauyi a mizanin masalaha.
Na amsa da ce wa "Na ha'kura da gaske."
Ya ce "To me yasa ba zaki y lalle ba Asiya? Na sani kuma ke ma kin sani, rufin
asiri ne mai yawa sana'ar taki take yiwa jama'a."
Murya na rawa na ce "Zuciyata ta karye, jikina babu k'wari."
Sai kuma na ke ce da kuka fiye da wadda na yi a gabansu Malam.
Ya kasa ce wa komai tsawon lokaci mai yawa ina kukan, shi kuma yana shafata tamkar
jinjira.
Na jima ina kuka bai hana ni ba. Har sai da kukan ya tsaya cak dan kansa. Na koma
ina ajiyar zuciya mai d'auke da shesshek'a.
Ya sassauta murya ya ce "Kin yi kuka Asiya da ikon Ubangiji ba zaki sake kuka akan
irin wannan al'amarin ba. Ki yi ha'kuri, wannan rufin asirin da kika yi mini, ni
ka'dai nasan yadda na sake jin ki a raina. Ni ka'dai nasan yadda girman ki da
nauyin ki suka yi mini rubdugu. Ke yarinya ce k'arama amma hankalin ki na manya ne.
Kin yi k'ank'anta kin tsunduma cikin irin wannan bak'in-cikin. Ina ro'kon Ubangiji
ya sanya wannan ne kukanki na karshe akan wannan matsalar a dukkan rayuwarmu
gaba'daya".
Na amsa da"Ameen" a hankali.
Murya babu amo na ce "Bana son wannan gidan, ba zan yi farin-ciki a cikinsa ba. Ka
samo mini wani ko daki daya ne zan zauna".
A hankali ya ce "Da ikon Allah zan samo miki, amma ki d'aure zuwa lokaci ka'dan kin
ji".
Na ce "To shike nan".
Ya dinga fa'din Na gode sosai my little. Allah ya bani dama da zan jiyar da ke
da'di mai yawa".
Na ce ni "Ka tsare mini mutuncina da naka da kuma soyayya da tattali nake so fiye
da komai".
Ya ce "zan miki Asiya, zan yi kokarin kiyaye ko wacce irin BAK'AR TA'ADAR da zata
sanya ki kuka. Yanzu yaushe zaki fara yin k'unshin dan na tabbatar kin huce kin
kuma yafe mini?"
Na shagwaba na ce "Sai ka yi al'kawarin ba zaka dinga yi mini sababi akan k'aramin
abu ba. Bana son shouting".
Ya numfasa ya ce "Zan dinga k'ok'arin ina yin fa'dan a hankali. Amma bazan yi
al'kawari ba, kin san wani lokacin ha'kurinmu k'wace wa yake yi, abin da zaki
fahimta shine sab'awa a zamantakewar aure ba k'iyayya ba ce, matu'kar kuskure ne
irin na zaman yau da kullum ko kuma sab'anin ra'ayi".
Na ce "Tom shike nan jibi zan fara yi In sha Allah"
Ya tsananta rik'on da ya yi mini yana fa'din"Thank you my little girl".
Daga hakan kuma ya shiga bai baye ni da zafaffar soyayya mai goge dukkan tsatsar
zuciya.

Washagari muka yini cikin nutsuwa da walwala mai yawa. Tun safe kuma na yi status
da cewar gobe idan Allah ya kai mu zan fara k'unshi.
Shike nan na ha'kurkurtar da zuciyata na manta komai.
Na rungumi mijina da sana'a ta. Illah iyaka na yanke mua'amala da Rafi'a.
Mahaifiyarta kuwa ban fasa gaishe ta ba, ban fasa mutuntata ba. Illah iyaka shiga
ne bana yi. Ita ma kuma Rafi'a din ta daina shigo mini.
Wata biyu da faruwar hakan na fara wani irin zazzabi mai zafin gaske. Domin kwana
nake yi mutsutsukun ciwon jiki. Gaba'daya ji nake tamkar ana kwankwatsa mini
kasusuwan jikina. Ga bana iya cin abinci.
Haka nake kwana ina yini cikin wannan halin. Sa'armu d'aya akwai kayan abinci tare
da mu. Sannan yana k'ulla lallen da siyar da ruwa. Babu matsalar babu sosai a tare
da mu. Kwana biyu ina ta shan maganin zazzabi da na rage rad'ad'in ciwo. Amma babu
sau'ki kullum gaba ciwo yake yi.
Hakan ya sanya shi fita ya yi buga bugarsa ya samo ku'di ya ha'da da wanda muke da
shi, ya kai ni asibiti.
Yini muka yi domin sai da aka k'ara mini ruwa. Aka yi mini gwaje gwaje.
Da yamma aka sallame mu bayan sun tabbatar ina da ciki na wata daya har da sati
biyu.
Duk yadda nake jin rashin kwarin jiki amma sosai na yi murna. Ni da Tijjani ban san
wanda yafi murna da zumudi ba.
Muna isa gida na dauki waya na k'ira layin Gwaggo.
Tana dauka ta ce "Yabi ya jikin dai?"
Da azarbabi na ce "Hmmm Gwaggo ashe duk wannan wahalar da murkususun da nake yi
ciki ne da ni!"
Ta yi shiru, sai kuma ta ce "Ni kika kira ki fa'da wa hakan Yabi? Wacce irin marar
kunya ce ke haka?"
Na yi sakare domin ni ban ga wani laifin ba. Ita ce uwata bani da wacce ta fita a
halin yanzu. Ita ce mafi kusa na tattauna dukkan farin-cikina da ita. Zan yi
kokarin na boye fa'da mata damuwar da nake ciki domin na yi amanna damuwata zata
tsayar mata da dukkan farin-cikinta ne.
Na sanyaya murya na ce "Gwaggo ki yi ha'kuri. Ina cikin murna ne. Kin san kwanaki a
gidan nan aka fa'da mini ce wa Tijjani ya gama zubar da yaransa a titi ni bazan
haihu ba. Sannan kuma ke da bakinki kika ce sai na haihu da ki zo ki ga muhallina".
Ta sassauta ta ce "To ba sai ki bari na fahimta ba, ko na ji a bakin yayarku ko
kuma Nazira".
Na ce "To sake yin hakuri Gwaggo ai yanzu na fahimta. Idan zan yi ta biyu, bazan
fa'da miki ba. Sai dai kawai a ce miki Yabi ta haihu"
Ta ja tsaki ta ce "Allah dai ya baki lafiya" tare da kashe wayarta.
Tijjani da yake gefe yana ta faman murmushi ya ce "Burinmu ya cika.
Yanzu fa'da mini sunan nawa?"
Na yi dariya na ce "Ai sai na haihu".
Ya girgiza kai ya ce "Kin ce da zarar kin samu ciki zaki fa'da mini fa".
Na ce "Haka ne".
Ya ce "To fa'da mini na ji".
Na murmusa ka'dan na ce "Abbanta".
Ya kwashe da dariya ya ce "Wanne irin suna ne wannan? Duk yadda kika kwadaita mini
zakuwar samuwar cikin a iya wannan sunan zan k'are?
Abbanta kuma. Wace ce?"
Na jingina a jikin kujerar na ce "Bebin mana."
Ya sake fa'dada dariyarsa ya ce "To idan namiji ne fa?"
Na ce "Ai kuwa sunan da zan fa'da maka mai wuyar samu ne indai namiji na haifo
tunda na fa'da maka mai kama da kai nake so".
Dadi ya kama shi ya ce "Allah ka kula mini da Asiya. Ka taya ni son ta, ka shiga
dukkan kasafinta. Duk al'amarin da zai dunfaro ta, Ubangiji kada ka bar ta da
iyawar ta.
Na ce "Ameen" a gajiye domin wai maganar da na yi har na gaji na fara haki.
Haka nake kwana da yini babu lafiya. Duk dare bama barci kwana muke muna fama.
Domin gaba'daya ni dai babu sau'ki. Kwana nake magogo. Haka kuma Tijjani baya
runtsawa. Tausa yake yi mini, da fifita idan babu wuta. Tin a lokacin muka fahimci
zama iyaye ba karamin al'amari ba ne. Duk yadda na zaku na samu ciki sai da na fara
sare wa. Murnata ta fara koma wa ciki dan tsananin wahalar da nake ciki.
Al'amura suka fara yi mana tsauri a dalilin ku'di ya fara yanke mana.
Haka da safe idan ya tallafa mini na yi wanka, ya shafe mini jiki da man zafi zai
fita ya dan yawata. Idan an yi sa'a ya samu aiki ya samo ku'di, zai siyo mini 'dan
abin kwadayi. Watarana kuma hakan zai dawo.
Baya kuma nisan kiwo, ko ya fita hankalinsa na kai na.
Sai na samu sau'ki, sai kuma jikin ya sake rikice wa.
Na fara gazawa. Rannan Baban Marina da ya zo duba ni, ya ga yadda na koma gaba'daya
na yi yaushi.
Ya bashi umarnin ya kai ni gida, ko shima ya d'an huta.
Bai musa ba kuwa washagari da hantsi ya dauke ni da jakar kayana ya kai ni gida.
Har da siya mini su maltina da madara da indomi da zan dan yi kwanaki ina ci. Wanda
na tabbatar ya ha'da da bashi.
Da k'yar na shiga muka gaisa da Dada wacce bayyana farincikin da ta yi a dalilin
samuwar cikin bata lokaci ne.
Ya kira Ikilima ta ri'ke ni zuwa cikin gida. Na sani kuma dan ya mutunta iyayenmu
ne ya sanya bai ri'ke ni da kansa ba.
Yadda Tijjani ya ha'do ni da shirgi da maganganuwana. Sai ka rantse har cikin
zuciyarsa yake nufin na zo na yi goyon ciki a gida.
Kwana na biyu a gida na fara samun sau'ki tamkar a gidana ciwon yake. Domin ina
barci, da safe kuma ina shan koko na ci dumame.
Sannan Gwaggo da kanta take daddana mini jikina. Har gasa mini jiki take yi da
tawul. Ga shi duk abubuwan da nake son ci na gargajiya ina samu.
Kwatsam ranar da na yi kwana uku sai ga shi ya ce shi ya gaji da rashina sai dai mu
koma gida.
Na tubure akan sai na ji k'warin jikina.
Shima ya kafe. Kuma wai ni ce zan ce ina son komawa gidana.
Nan da nan na rantse akan bazan fa'da ba.
Ya jijjiga kai ya ce "Shike nan tunda babu taimako da fahimta a tsakaninmu. Ni zan
fa'da wa Baban akan na gaji ina son ki koma dakinki. Dama kunya da nauyinsa ne suka
sanya na kawo ki."
Da yamma ya dawo akan na taimake shi mu koma gida. Ya kasa fa'dawa Baban zai tafi
da ni. Na ce "Ni dai na fi son zaman nan".
Nan da nan ya tunzura ya ce "Saboda bani da ku'di ko Asiya?"
Na kalle shi a razane. Ya ce "Haka ne mana. Inba hakan ba wace ce ta taba zuwa gida
dan bata da lafiya a gidan nan?"
Na ce "Ubaida bata dawo ba?"
Da hanzari ya ce "Amma duk jinyar da ta yi da ciki ai bata dawo ba. Sai da ta
haihu. Ke kuwa ai ba haihuwa kika yi ba. Idan ba gazawa ta aka ga ni ba. Mene ne
zai sa ayi mini wannan umarnin?"
Na sake kallonsa cikin tu'ajjibi na ce "Baban Marina kake fa'dawa hakan ko kuwa
wa?"
A tunzure ya ce "Asiya na ke fa'dawa saboda ita ce zata ce masa ta samu sau'ki."
Idona ya ciko da hawayen takaici na ce "To".
Daga hakan na k'ulle bakina ban ce masa komai ba.
Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi. Ya ce "Ya muke ciki?"
Ko kallonsa ban yi ba.
Ya gama zamansa ban sake kula shi ba.
Da daddare ma ya dawo, ban yarda na kula shi ba. Domin idan akwai abin da yake
b'ata mini rai da shi idan muna magana ya dinga sako babun shi ne. Na kuma lura
idan ban taka masa birki ba, ba wanye wa k'alau zamu yi ba. Tunda yana nema ya
mayar da ita sara.
Washagari sassafe sai ga Babah ta Bulkachuwa ta dira a gidan. Ina daga daki na ji
suna gaisawa da Baba. Ya ce " Hauwa kamar ba kwanaki ka'dan da suka shud'e kika zo
duba y'arki ba. Me ya sake dawo da ke kuma yanzu? Mata kuna da son sabgar yawo.
Ta ce "Ba hakan ba ne Yaya. Shi ne ya mini waya wai jikin Yabi ya yi tsananin da ka
ce ya dawo da ita gida. Sai ya ro'ki na zo na zauna masa da ita. Ni kaina hankalina
ba kwanciya zai yi ba idan ba zuwa na yi na ganta ba."
Baba ya numfasa ya ce "Ai shi Tijjani bai gamsu zan kular masa da iyali dan karan
kansa ba, sai ya zargi na yi masa fin k'arfi saboda y'ata ce?".
Ta diriri ce ta ce "Haba Yaya ni Wallahi har kasa na ji babu da'di."
Ya ce "To ki ji mana. Ban da dai ke ma kin banbanta ta ya ya zaki zo ki ce mini
"Zaki dauki matar Tijjani a gaba na?"

✍️

*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered,
Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan
farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa

Please Login or Register in order to submit comment