You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida, ya gaya wa Iman, ruma ce ta haihu.

Mamaki ne ya kamata, dan washegarin taron nan sun haWu a gidan ammi, ta ce mata haihuwarta da saura.

Nan da nan ta yi girki, jiki na rawa tare da mamakin haihuwar ruma, ta kira ammi ta sanar mata.

Ammi ta ce "Ba dai rumaisa ba, takawa ya ce da saura ai"

"Wallahi ammi da gaske nake, yanzu yaya umar ya shigo ya gaya mini".

Nan da nan aka cika asibitin, ?an barka, sai dai ba ganin jariri, rumaisa kuma ba baki, duk wanda yayi mata sannu, sai dai ta jinjina kai kawai, amma ta san halin tashin hankalin da ta shiga a haihuwar.

Mama ta kalli rumaisa ta ce "In ce dai ta bakin ki ka haifo Wan naki, yau mata sun ga ta in da ake haihuwa" ruma tayi murmushi kawai.

Da ?yar ta iya cin abincin ma, ta fara cewa ita a kawo mata Wan ta fa, saboda lokacin da ta haife shi, tana gani ana ta fama, ya ?i yin kuka yadda yakamata.

Abdallah ya sha tambaya a babbar headquarter Dss ta Abuja, dan sai da aka karSi zanen aka sa shi sake yin wani, suka yi iya binciken da zasu yi, babu ko shakka Jamil ne, Wanda dama already yana hannunsu, takawa yayi kamar ya gaya musu da sanya hannun wakili, amma tayaya meye hujjarsa? Rumaisa ce kawai ta ji sun ambaci wakili, idan da wanda zai faWi da sanya hannun wakili, to Jamil ne yakamata ya faWa.
Duk wani report na bincike lokacin Satan aisha da suka yi, sai da suka gabatar da shi a wurin hukumar, laifin Jamil ya zama biyu, da na tuhumar fitar da sirrin hukumar, da kuma haWa baki tare da yin garkuwa da ?anwarsa, ga kuma Satawa Adam suna da yayi.

Ko da ana nunawa Jamil zanen nan, da Abdallah yayi, sai da ya zabura, saboda tabbas ya san shi ne.

Adam ya ce "Jamil ka tabattar wannan kai ne? Jamil me muka yi maka ni da Aisha? Idan ma wani abun na yi maka, meyasa zai shafi aisha? Ka haWa kai da wakili ka cutar da ni?"

"Adam jin dalilin hakan ba shi da wani amfani a gareka, tun an riga an kama ni, sai ka je ka cigaba da rayuwarka, ka ?yaleni. A kan me mahaifinmu zai fifita aisha a kanmu? Kuma duk wani abu na cigaba, ko na masarauta sai dai ya sanya ka a ciki alhalin gani. Wallahi da na san yarinyar nan ta gane ni, da ban barta ta rayu ba"

Adam yayi murmushi mai ciwo ya ce "Na gode sosai Jamil, sai dai ka sani, duk da ciwon hauka da nake fama, na tsaya ga Allah, shiyasa nake cigaba, kuma na barka da Allah Jamil, Jabir ma har shi da duk wanda ku ka cutar da ni, kamar yadda rumaisa ta faWa, ta ce in bar ku da Allah, zan ga yadda zai yi da ku, na bar ku da Allah"

Takawa suka koma masauki shi da Abdallah, tare da Bashir.
Sosai suke bawa Adam baki, tare da bashi ?warin gwiwa.
A lokacin yake sanar da su abubuwan da wakili ya kira shi ya sanar da shi.
Sun girgiza sosai da sosai, Bashir ya ce "A gaskiya na girgiza, dama biri yayi kama da mutum, yadda aka kasa magance wannan Smoke Win. Amma ina ga kamar yadda madam ta faWa, ka yi ?o?arin gano wanda suka yi maka ma?ar?ashiya, amma hukunta su sai Allah".

Ammi ce ta kira Adam a waya, ta sanar da shi rumaisa ta haihu, sai dai yaron an saka shi a kwalba.

Adam kansa abun ya Waure masa kai, wace irin haihuwa ana zaune ?alau, ba tare da cikakken lokaci yayi ba.

Gashi bai bai gama da abuja ba, amma ya ce dole ya koma kano. Zai bar Abdallah da Bashir ko za a bu?aci wani abun, idan komai ya lafa sai su taho, shi kansa Abdallah abun ya bashi mamaki, a kan ya aka yi rumaisa ta haihu a wannan lokacin.

Sai dai cikin ?udura ta Ubangiji mai kyauta da ?ari, yaron da mimi ta haifa ya koma ga mahaliccinsa cikin dare, dama ana ta fama, ya?i kuka amma d girmansa ba ka ce bai kai lokacin haihuwa ba.

Aka yi shiru ba a gayawa mimin ba sai washegari da safe, aikuwa rumaisa ta dira rigima, ta din ga kuka, tun mama na rarrashinta, sai da ta ?ular da ita, ta fara zaginta.

Mama ta ce "Ba zaki rufe mini baki ba?"

"Mama baki san me nake ji ba ne"

Mama ta ce "Dan ubanki ?a?a biyu na binne, da zaki ce ban san me ki ke ji ba".

Ammi ta ce "Maman rumaisa ki yi ha?uri, yarinya ce kuma dole za ta ji babu daWi"

Aka naWo jaririn, aka kawo wa rumaisa, kamarsa Waya sak da Adam.

Sabir da yake zaune a kusa da rumaisa ya kalleta ya ce "Mimi, baby ya buWe ido" yayi maganar cikin yarinta.

"Boy babynmu ya mutu"

Ammi ce ta karSi jaririn, ana jiran shigowar adam, ayi masa sutura.

?arfe tara na dare Adam ya dira, ko gida bai je ba, kai tsaye asibiti ya taho,? ammi tuni ta sanar masa da rasuwar yaran, dan haka hankali a tashe ya ?arasa asibitin jikinsa duk a sanyaye.

Ya tarar tuni Ammi na can ita da nusaiba, mama tana wurin rumaisa.

Ya dur?usa suka gaisa, ammi ta tambaye shi ya ake ciki, ina Abdallah?.

Ya ce mata yana lafiya, yana tare da Bashir, akwai abun da zasu ?arasa.

Ammi ta mi?a masa jaririn, ya karSe shi ya buWe zanin, kamar mai bacci, kamar sa Waya sak da shi duk da jikinsa yayi fari, amma da gani ka san yaron fari ne.

Ya mi?awa ammi shi, ya ce "Allah ya sa mai ceto ne" suka amsa da amin.

Mama tuni ta tashi ta bar Wakin, ya ?arasa gaban gadon mimi, ya zauna a kusa da ita ya ri?o hannunta.

Kawai ta fashe da kuka ta ce "Papa babyna ya mutu, kuma ina son shi"

Ya rungumota jikinsa ya ce "Am sorry mimi, ni kaina na ji ba daWi, amma Allah ya fi mu sanin me ya dace da mu, kiyi ha?uri ki daina kuka"

Yayi maganar yana shafa bayanta, shi kansa ya ji mutuwar yaron, sun sanya rai da yaron sosai da sosai.

"Ko dai abubuwan da suka faru ne, ya sanya ki ka tashi hankalinki ki ka fara labor?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To shikenan, Allah ya bamu mai amfani, ya sanya wannan mai ceto ne, na sanya masa sunan mahaifina Muhammad, Allah ya bamu wani" rarrashinta ya din ga yi tana jinjina masa kai.

Iman ta shigo ita da Usman, Usman sai da ya sunkuyar da kai, kunya ce ta kama shi, ganin yadda takawa ke zaune ya rungume mimi yana rarrashinta, ga ammi a zaune.

Abun da bai sani ba shi ne, har abun da ya fi haka yi suke, ita ba abun da ya dameta bane ba, domin ita kanta bata manta lokacin da aka yi mata aure, ba shirmen da ba sa yi ita da marigayi galadima, dan haka duk taSrar da ruma take ba ta damunta.

Usman suka gaisa da Ammi, ammi ta ce wa Iman "Ina mai sunan baban?"

"?arfe takwas suka tafi Lagos shi da yaya mahmud, wai wani abu za su je su yi"

Ammi ta ce "To, ni yanzu Mahmud tsoro nake ji, kar ya sake Sallo mana ruwa, ba a gama da wannan tarzomar ba, kodayake tare suke da mai sunan baba, ba zai bari yayi wani rashin jin ba.

Aka sallami ruma daga asibiti, tare da jaddada mata yadda za ta kula da kanta, saboda Winkin da aka yi mata.

Mutane suka din ga zuwa barka, Adam yayi mursisi ya ce ruma ba zata tafi gida ba, gidanta za ta koma, a Waukko mai kula da ita.
Ya kafa hujja da mama ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba.
Gashi ya samu labarin su Huzaifa ne suka kawota asibiti.

Mai sunan baba kuwa lokacin da suka isa lagos, suka je gidan Alhaji Aminu, suka tarar yayi tafiya, Ade kuma ta koma Gombe!.

Ayshercool.
08081012143
*WANDA KU KA KARANTA MINI LITTAFI BA TARE DA KUN BIYA NI HAKKINA BA, BA KUMA DAN BAKU DA SHI BA, IDAN KUN SHIRYA BIYANA HAKKINA GA ACCOUNT NUMBER NA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK*





Mahmud ya ce wa mai sunan baba, bai kamata su yi sanya ba, idan da dama kamata yayi kawai su tafi Gomben su bita can.

Mai sunan baba ya ce "Tayaya ni ban san a ina take a gomben ba"

"Tambayar mutanen gidan zamu yi, ba zamu yi sanya ba"

Ba tare da wani Sata lokaci ba, mutanen gidan suka basu kwatancen in da Ade take, kasancewar sun san mai sunan baba.

***
Rumaisa kuwa gwaggo ce ta je zauna mata, saboda bi?i, mutane suna ta zuwa duba ruma tare da jajanta mata abun da ya faru.
Tana zaune a Wakinta, suna video call da laila, sai kuka take yi mata, wai babyn ta ya mutu.

Laila sai rarrashin ta take yi, tana kwantar mata da hankali, tare da jaddada mata, idan komai ya dai-daita, lallai ta nemi maman Khadija, da maman ilham ta gyara, duk da yaron ya rasu, akwai bu?atar ta gyara jikinta sosai.

Rumaisa ta ce "To anty laila, in sha Allah ai ina da numbern su, ina Yasir".

Laila ta ce "Yaya bacci yake yi bai tashi ba"

Ruma ta ce "Inyee su yaya manya, ina fatan dai ba ya miki rashin ji?"

"Ba wani rashin ji, rashin ji ai sai ke, wallahi na ji daWin zuwan Yasir gidan nan rumaisa, very kind and brilliant guy, darling ya yi masa registration ma, very soon zasu fara lectures, baki ga daWin da babansu ya ji ba zuwansa, su anam ma suna ta murna"

Ruma ta ce "Sai wani yabon sa ki ke yi"

"Dole in yabe shi mana, dole a sarawa mama, yaranta gaba Waya masu tarbiyya ne da nutsuwa, ke ce kawai mara ji"

Ruma ta ce "To nima papa yana yabona, yana sona a haka"

"Ai shi dama ba zai ga rashin jin da ki ke ba. Yauwwa mimi ya hatsaniyar gidan kuwa ta lafa?"

"Ina fa lafawa, suna can suna cigaba da tashin hankalin su, ni ina nan ina fama da kaina, da mutuwar Wa na, mummy sun watse da Hajiya Lubabatu, ashe Jabir lalata suke shi da ru?ayya, abun duk babu daWi mahmud dai ya rufe shi"

Laila ta ce "Lamarin gidan nan sai Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya sa mu dace kawai mimi, bari na bari ki huta"

"To anty laila na gode sosai"

Tana gama wayar, Gwaggo ta shigo da kunun kanwa, ta ce ruma ta sha.

Ruma ta ce ita wallahi ta gaji da wannan kunun kanwar, gudawa yake sakata.

"To idan baki sha ba nonon ya zube ki huta ai, gyara ki nake son yi, na bayar da dawa ma a ni?ota in she?a miki tuwo, ga yajin daddawar ki nan"

"Gaskiya gwaggo ba zan ci tuwon dawa ba, in haihu ki bani wani tuwon dawa taS. Kunu kuma ina da sauran sabayata, yaushe zan ta shan kunun kanwa cikina yana ciwo".

"Kya ji da shi dai, ana yi miki abun arziki kina na tsiya"

Haka rumaisa suke faWa da gwaggo, komai sai ruma tayi raki.

Yanzu ma Adam ne ya je ya tarar da ita gwaggo na ta masifa, kamar ta ari baki, a kan rumaisa ta tashi ta je ayi mata wanka, tun yamma ake dafa ruwan, amma Rumaisa ta?i yadda ayi,? ta ma?ale tana kuka, wai wallahi fatarta duk ta dahu saboda ruwan zafi.

Takawa ya shiga Wakin suka gaisa da gwaggo, ya dubi ruma ya ce 'Mimi meyasa ki ke da gardama ne?"

"Saboda ba ka ga uban tururin da ruwan zafin yake ba, da wanne zan ji, zafin haihuwa ko mutuwar Wa na, ko na ruwan zafi?"

"Ai ni kin san bana jin zafin ruwa, zo mu je" yayi maganar yana mi?a mata hannu, ba kunya ta zagaye gwaggo ta bi takawa.

Gwaggo ta saki baki tana kallon ikon Allah, daga rumaisa har mijinta ba su da kunya ko kaWan.

A banWakinsa ya haWa ruwa zafin dai-dai jikinta, ya taimaka mata, ta gyara jikinta ta yi wanka, sai dai rumaisa akwai langwai.

Suka fito ya bata abinci ta ci, sannan ya Wauki magungunan ta ya bata ta sha.

Ya kalleshi ta ce "Na gode sosai papa, ya ku ke ciki a abujan ne, yaushe Abdallah zai dawo?"

Takawa ya kwashe komai da ya faru ya gaya mata.

Tayi ta rarrashin sa, tare da bashi tabbacin, Allah baya barin zalunci, amma kar ya ce zai cigaba da dagewa sai ya ga bayan wakili, saboda yana da goyon bayan manyan ?asar.

Ya ce "Haka ne, in sha Allah na bar wa Allah"

Cikin dare rumaisa nono ya cika, ya takura mata da ciwo, saboda ba ta shayarwa, dan haka kwana tayi kuka, har da zazzaSi.

Gaba Way tausayinta ya cika takawa, su mata komai na su abun tausayi ne, ta haihu ta rasa Wan, amma akwai wani pain Win na daban.

Anty laila ya kira directly ya sanar mata, ta ce su yi ha?uri, da safe su kira maman ilham a waya, su sai maganin ta na gyaran nono, mace ko yaye tayi yana hana mata jin zafi, kuma baya bari nono ya lalace.

(0813 561 3021zaku iya neman maman ilham kai tsaye ta lambar wayarta. Haka zalika kar ku manta da haWin maman Khadija na sabaya
0703 777 7442)

Da safe har wurin ?arfe goma, sanna suka tashi ita da takawa, Gwaggo har ta gaji da jiran fitowar ruma ayi wanka, sai ganin ta tayi tsaf, ta sha wankanta sun fito ita da takawa. A kunyace gwaggo ta gaisa da takawa yayi musu sallama ya fita.

Yana tafiya Gwaggo ta din ga yi mata faWa "Saboda rashin gado, kina jego ki ka bi miji ku ka kwana tare ko? Ki cigaba da biye masa wani cikin zai yi miki ya bar ki wahala, tun jikinki bai gama ?wari ba, dama gashi kin ?i bari ayi miki jegon kirki, ki je ki ?arata".

"Ni fa gwaggo ke ba kya lallaSa ni kamar yadda yake yi mini, jiya har ran?washi na ki ka yi"

"An ?i a lallaSa ki, ku ?ara ina yin sati biyu zan gudu, ba zan iya baWala ba" haka gwaggo ta cigaba da mita, ruma kuwa ko a jikinta.

Turaki tun da aka watse daga taron nan kuwa, kwanansa biyu ya rufe kansa a turakarsa, yana jinyar zuciyarsa daga raWaWi da Wacin abun da iyalinsa suka aikata.
Wanda ya Wora alhakin hakan a kansa, da kuma rashin jajirtacciyar uwa ga yaransa, kodayake auren biyayya ne na haWi, duk cikinsu sharif ne kawai yayi tutsu, ya ce shi sai wadda yake so.

A kwana na uku, aka sanar da jikin galadima ya tsananta, dan haka ya shirya ya tafi jamus.

Mahaifiyar su Jamil kuwa ta sha kuka, duk wanda ta san zata kira, ta ro?i a saka baki a bayar da belin jamil, kowa ya?i.

Samha ba ta taSa zaton Jamil ne mutumin da wakili ya samu yake taimaka masa ba.

Ko da ta kira shi a waya, ya ci mata mutunci ya ce kar ta sake kiransa, shi yanzu ya samu biyan bu?atar sa ya san koba koma, yanzu Adam ya san su ba sa'anin yin ba ne ba!.

***
Su mahmud kuwa, basu wahala ba wurin kwatancen da aka basu, nan da nan suka isa gari da Ade take, kuma gidan ?anin nata sam bashi da Saci.

Ras ta gane mai sunan baba, ta din ga murna da zuwansa, sai dai ta din ga kallon mahmud, kamar ta san shi a wani wurin.

Babu Sata lokaci mai sunan baba ya wassafa mata abun da yake tafe da su, da kuma dalilin da ya sanya yake ta bibiyarsu tun a lagos, har biyo ta nan.

Ba tare da ya gaya mata waye mahmud ba, jiki a sanyaye ta ce "Adamu ne?"

Umar ya ce "Kin gane shi? Kin san Ammi?"

Tayi murmushi mai ciwo ta ce "Na san Bintu, bintu ?ar Wakina ce sosai da sosai, lokacin da tayi aure tana goyon yaronta na biyu, muka bar garin, nayi kewarta sosai da sosai, sai dai wasu dalilai ya sanya ko da muka bar garin ko sunan garin bana ?aunar ji"

Mahmud ya ce "Kin tuna jikar ki mairamu?"

Ade ta fashe da kuka, ta ce "Yarinyar da aka bar amanarta a wurin jauro, da dabbobin mu, muka yi gaba, ya iskemu ya ce: wai ?an fashi ne suka kai musu farmaki, an kasheta ita da mijinta, dabbobinmu ma duk an tafi da su, kamar wanda ya rufe mana baki, babu wanda ya ?aryata shi haka muka sha kuka. Bayan wasu shekaru yara suka fara fita neman ilimi, wasu suka zauna a riga, muna katsina a ka kai mana farmaki shekara uku baya, aka sake kashe mana ?an uwa, muka sake yin hijira, shi kuma jauro ya ce a can zai cigaba da zama, sai daga baya labari ya iskemu, ashe jauro Wan fashin daji ya zama, kuma shi ya kashe mijin mairamu ya gudo shi da matarsa, yayi asiri ya rufe mana baki. Wai sojoji sun kashe shi kwanan nan".

Mahmud ya ce "Kar ki ce mini mutumin da rumaisa ta zana ta ce yana kama da Iman kawunta ne? Shi ne ya kashe mahaifin ta?"

Ade ta ce "Waye kuma ima?"

Sai a lokacin suka warware mata abubuwan da suka faru bayan barin su garin.

Jiki na rawa ta ce "Kuna nufin Bintu tana raye? Ita ta ri?e ?ar mairamu?"

Mahmud ya ce "?warai kuwa wannan mijinta ne ma?"

Ade ta rikice da kuka, tare da yi wa Allah godiya, da kuma sanya wa Ammi albarka.

Ta ce "Wallahi yaro Bintu tana zuciyata, ka ga dai gani a cikin garin gombe, amma har yau ko tuna rigar da muka zauna bana yi, ko in hanyar garin take bana son ji, gaba Waya tsoron mutane nake ji, Jauro bai yi mini adalci ba, dan Allah ku tashi ku kaini na ga Bintu, naga abun da mairamu ta bari" nan ta din ga basu labarin kyawawan halaye irin na mairamu, na rashin magana da ha?uri, yadda ta rayu a gidan jauro, ana azabtar da ita, tun tana yarinya saboda kawaici suka baro ta, suka sauya riga, an yi mata aure sun taso tare suka ya da zango, ta haihu tukuna, amma jauro ya cuce su.

Ade ta din ga murna tana cewa amma ta ji daWi da malam umar ya zamana mijin jikarta.

Nan da nan ta saka a kira Alhaji Aminu, tare da ce masa duk in da yake ya dawo, ko kuma yazo ya tarar ta tafi kano, an ga jikirta a birnin kano, tun da ba a kaita kano dan Allah ba, yanzu dalili ya samu dan haka babu mai hanata tafiya.

Nan da nan riga ta Wauka, an samu ?ar mairamu a raye, ashe kan ta mutu ta haihu, aka din ga zuwa ganin mai sunan baba da mahmud. Sun sha karramawa kala-kala.

Washegari da wuri Alhaji Aminu ya sauka a garin, tare da jin batun tamkar almara, abun da ya faru shekaru kusan goma sha tara baya, yaya za ayi ace, wai an ga ?ar mairamu.

Sai dai ya tsinke da lamarin, bayan saukarsa mai sunan baba ya nuna masa hoton iman.
Alhaji Aminu ya ce "Malam Umaru, amma ka kasa gaya mini wannan abu, duk da ban wani san mairamu ba, amma wannan kamarta Waya da ade, kuma ba shakka jininmu ce, yanzu meye abun yi?"

Mai sunan baba ya ce "Idan ba damuwa, sai mu taho da iman Win da amm...

Ade ta ce "Wane mutum, da ?afar nan tawa ko a ?afa zan taka na je kano, na ga Bintu"

Alhaji Aminu ya ce "Da wace ?afar? ?afa duk sai saura? Ki zauna a shirya tafiya, sai a tafi gaba Waya "

Nan ya sake warware musu irin zaluncin da jauro yayi musu, ya din ga haWa kai da ?an bindiga ana cutar da su, wanda hakan ya sanya da yawansu suka tarwatse, da farko basu gano shi ba, sai daga baya amma an ce sojoji sun kashe shi.

Da daddare takawa ya ceea rumaisa, ta zo su tafi su kwanta, ta ce "Ba zani ba gwaggo ta ce idan na biye maka wani cikin zan samu, kuma wallahi haihuwa da wahala"

Dariya yayi ya ce "Ai shikenan"

Gwaggo ta kawo wa ruma abincin dare, ta ce "Yau ba zaki bishi ba?"

"Ai na gaya masa kin ce bamu da kunya, kuma idan na cigaba da biye masa wank cikin zan samu da suri"

Gwaggo ta Wora hannu a ka ta ce "Rumaisa ba ki da hankali? Ki ka ce ni na faWa, ashe halinki na wauta na nan, da wani idon zan kalle shi? Wallahi dole in tattara kayana in bar gidan nan"

Ruma ta ce "Ashe kuwa zaki maimaita masa abun da ki ka faWa mini, dan sai ya bi ba'asi"

Ta samu Wan kwali ta kwaWawa ruma a baya ta ce "Shashasha uwar wauta, shikenan zai daina ganin mutuncina".

**
Mahmud ya kira Ammi a waya, ya ce "Su shirya, su haWu a wuri guda, suna tafe da manyan ba?i zuwa kano shi da mai sunan baba.

Ba yadda ammi ba ta yi ba, amma ya?i gaya mata ko suwaye, ya ce amma muhimmancinsu ya kai ace har mai girma wambai ko turaki yana wajen.

Ammi ta ce "Turaki baya nan, ya je Germany wurin galadima, jikinsa ya tsananta, sai dai wambai"

Mahmud ya ce "Ba?i ne masu muhimmanci, har mimi muna bu?atar ta a wurin" Ammi ta din ga mamakin wane irin ba?i ne kuwa haka?".

Da ta sanar da wambai kuwa, ya ce babu laifi, a jira ?arasowar ta su, aji wani irin ba?i ne, ya ce idan sun iso a kira shi.

Ammi ta sanya aka yi ta Worawa da saukewa, duk da bata san wane irin ba?i ba ne, amma akwai bu?atar ayi girki.

Duk nacin ruma da iman, a kan son sanin suwaye ba?in, ammi ta ce musu ita fa ba ta sani ba.

Duk suna falon mai sunan baba ya yi sallama, iman ta tashi da sauri ta ce "Hero suwaye ba?in?"

Ruma ta gwale baki ta ce "Su hero manya"

Takawa ya ce "Umar kun bar mu a duhu kai da ?aninka, ku muke ta jira"

Yayi murmushi ya ce "Yanzu za su shigo" ya kalli iman ya ce "My yellow, yakamata ki bani tukuici kan ki ga ba?in nan fa" yayi maganar yana jan karan hancinta, a gabansu.
Kunya ce ta ka??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????mata ta ce "To me zan baka?"

"Saniya zaki sai mini" gaba Waya suka hau dariya, Ammi ta fito ta ce "Mai sunan baba kun sauka? Ina ba?in?"

Mahmud ne yayi sallama, sai Alhaji Aminu a bayansa ya ri?o ade, sai ?annenta guda biyu.

Sakin carbin hannunta ade tayi, ta ce "Ade" da ?arfi.

Jiki na rawa saboda tsufa Ade ta Wago ta kalli Ammi ta ce "Bintuna"

Da sauri Ammi ta ?arasa ta ri?o hannun Ade, hawaye ya wanke mata fuska ta ce "Dan Allah gaske ne ba mafarki nake ba, Ade ke ce a gabana? Ade ba irin neman da ban yi miki ba"

Suka rungume juna ita da ita.

Alhaji Aminu ya ?urawa iman ido, ya ce "wannan ce ?ar ta mu?" Kamar sokuwa haka iman ke bin su da kallo.

Mahmud ya ce "Hajjaju ga ?an uwanki, mijinki ya nemo"

Jiri ne ya fara Wibar iman, saboda ba ta san mafarkin nan ya cigaja da yaudararta.

Umar ya ri?e ta ya ce "Iman, calm down mana menene"

"Dan Allah ka tashe ni daga baccin, kamar ba zai faru a gaske ba fa?"

"Ba mafarki bane ba fa" yayi maganar yana zama tare da ita, saboda har numfashinta ya fara sama.

Alhaji Aminu ya ?araso gaban iman, ya ri?e hannunta, ya ce "?a ta ba mafarki bane ba, mu ne ahalinki" bayan gama kukan ammi ta ce Aminu haka ka girma sosai? Iman ga Ade da nake baki labari, wannan su ne ahalin mairamu"

An sha koke-koke, ?an aike ammi ta tasa, aka kira wambai, sai dai yaji kunya da nauyin abubuwan da suka din ga yi wa Ammi da iman, a kan rashin sanin wacece, wanda hakan yana da ala?a da zigar Mummy.

Nan Alhaji Aminu ya gaya musu cin amanar da jauro yayi musu, da ?iyayyar garin da ya sanya musu, suka kasa komawa, balle su binciki abun da ya faru gaske ne ko ?arya.

Takawa ya ce "Tabbas wannan mutumin shi ne rumaisa ta zana mini, ta ce da wa yake kama? Na ce mata iman, ta ce a yanayin da ta ganshi ne ya sanya ba zata taSa cewa ta ga wani mai kama da iman ba, kasancewar sa mutumin banza, dan har tattaunawa da shi ta yi"

Iman ta rasa mai zata cewa mai sunan baba

Please Login or Register in order to submit comment