You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sha gabanta ta ce "Wucewa zan yi"

"Ki je ina?" Ya tambayeta.

"Ciki mana wurin Wana, ko ba ka gane ni ba ne?".

Ya ce "Na gane ki, sai dai an ce kar mu sake barinki ki shiga idan ki ka zo?"

Cikin mamaki ta kalli securityn ta ce "Waye ya ce kar a sake barina na shiga?"

"Takawa, shi ya ce kar ki sake shiga idan kin zo in ba shi ya ce ba"

"Kam bala'i, wai wannan wane irin mutum ne, shi wane irin azzalumi ne, idan har ba zan din ga shiga ba, ya bani Wana mana, ai dai ya san ba maula ce take kawo ni ba ko?"

"Ke da shi ne wannan, matsa daga nan"

Wata irin zuciya ta turnu?o rumaisa ta ce "Wallahi ba in da zani sai an bani Wa na, wallahi yau sai na shiga gidan nan, wane irin mugun mutum ne shi, ba shi da imani ba shi da tausayi, wallahi sai na shiga sai dai ku kasheni" ta yi maganar tana tunkarar gate Win.

Tare gate Win Waya yayi, cikin tsawa wani ya ce mata "Ki ka motsa daga nan sai na harbeki"

"To ka harbenin mana, sai me? Allah sai na shiga"

Gaba Waya ta rasa abun da za ta yi, ta fashe da kuka, saboda uwar wahalar da ta shawo, kan ta samu ta zo, amma ta tarar wai an hanata shiga.

Ta fi mintuna talatin a tsaye a rana tana kuka, Waya daga cikin masu gadin ya ce "Wannan wace irin jarababbiyar yarinya ce haka?"

"Kai ne baka santa ba, kwanakin baya ta taSa zuwa gidan nan, zata aikata fiye da abun da ta yi yanzu"

Kamar daga sama, ta hango shi yana tunkaro ?ofar gidan, sanye da ?anan kaya, kunnensa Waya da Bluetooth, fuskar nan tasa fayau ya yi ?iba abunsa, kan ya ?arasa gate Win rumaisa ta tashi da gudu, ta je ta ri?e rigarsa tana kuka.

Sororo yayi yana kallonta, "Shi ne kace idan na zo kar a sake barina na shiga, ka san da haka ka karSe mini yarona? To ka shiga ka Wauko mini sabir ba zan sake zuwar muku gida ba"

?aya daga cikin security zai yi magana, ya Waga masa hannu ya dakatar da shi, ya kalli rumaisa ya ce "Wane jaririn ki ke magana a kai?"

Waro ido rumaisa ta yi ta ce "Ni zaka rainawa hankali ka mayar mahaukaciya, wato ma baka san wane jaririn nake magana a kai ba, wallahi sai na Webo maka ?an sanda, ko kuma tun da kai ma Wan sanda ne, na san haWa baki zaku yi, al?ali zam je na gaya wa, kuma ka bani Wana ba zan sake zuwar muku gida ba"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, mu shiga ki ga Wan na ki, sakar mini rigata".

"Wallahi ba zan cika ka ba, ka gudu su hanani shiga" ta ?ara ri?e masa riga, suka nufi gate Win.

"Ranka ya daWe, YallaSai ya ce kar a sake bari ta shiga".

"Ni kuma na ce sai ta shiga, ko nima an hana ni shiga ne?"

Ya girgiza kai, suka buWe gate Win, suka shiga, sai da suka zo ?ofar shiga sashen ammi, sannan ta saki rigarsa ta shiga ciki da sauri.

Sai dai tana shiga babban falon ammi, abun da ta gani ya razanata.

Turus! Ta yi ta tsaya, Adam ta gani a zaune sanye cikin suit farare, da shi da ammi a falon, sabir a kan kujera yana barci.

Ta waiwaya ta kalli hanyar da ta shigo, sannan ta kalli in da Adam yake.

Ammi ta ce "Rumaisa daga ina haka?"

Ta ?arasa ta zauna, safarta tayi futu-futu saboda tafiyar ?afa, ta zauna ta ce "Tun safe nake tahowa, da ?yar na zo gidan nan, dan na ga sabir, amma da na zo aka hanani shigowa, wai ya ce idan na zo kar a sake barina na shigo, sai kuma na ganshi ya zo wucewa zai shigo gidan nan, tare muka shigo na bar shi a waje, amma kuma da na shigo na ganshi a nan a zaune, a waje da ?anan kaya na ganshi, amma kuma a nan na ganshi da wasu kayan". Tayi maganar tana kallonsa.

Adam bin rumaisa ya yi da kallo, yana mamakin anya kanta Waya, jin ta ce da ?afa ta taho, kuma yanayinta ya tabattar da hakan.

Ammi ta ce "Ohh Mahmud ya shigo gari kenan?"

"Waye Mahmoud? Ba shi na gani a waje ba kenan?".

"Ba shi ki ka gani ba" Ammi ta bata amsa.

Rumaisa ta gyara zamantaz tana shafan kan Sabir, sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce "Allah sarki, Allah ya sa idan na fita na ganshi na bashi ha?uri ban san ba shi bane ba, na yi ta masa masifa*.

"Amma rumaisa ba makaranta zaki je ba na ganki da uniform?".

"Makaranta zani, amma na kasa jurewa, ba bu abun da nake so sai in ga sabir, amma na zo wai an hanani shigowa, ban da dalilin sabir ma ni mai zai kawoni gidan nan, ina ga ma alhakin yaran mutane da nake cin zali ne ya kamani, Allah ya jarrabeni da son yaron da ake wula?anta ni a kansa, bakomai wataran sai labari"

Maimakonsa ammi ta ji maganganun rumaisa sun yi tsauri, sai ma wani irin tausayinta da ya kamata, lallai rumaisa tana cikin jarrabawa ta gaske saboda sabir.

Ammi ta ri?e hannunta ta ce "Rumaisa, babu mai wula?antaki a kan sabir, sabir Wanki ne, ki yi ha?uri zan Wau hukuncin da ya dace a kan Adam, amma daga yanzu duk lokacin da ki ke son ganinsa, akwai lambata a wayar mamanki, ki kirani ni kuma zan saka a kawo miki shi, ko na kawo miki shi da kaina, kin ga yanzu kin yi missing school, bari ya mayar da ke gida, tun da dama wurin aiki zai koma"

Rumaisa ta girgiza kai ta share hawaye ta ce "A'a, zan koma gida da kaina, kuma ba zan sake zuwa gidan ba, balle masu gadi su ci mutuncina a waje kamar yadda aka yi mini yau kamar ?ar maula" tayi maganar tana sake fashewa da matsanancin kuka.

"Kiyi ha?uri, in sha Allah hakan ba zata sake kasancewa ba, babu mai sake wula?anki a kan sabir, ko shigowa gidan nan, tun da gidanku ne, bari a kawo miki ruwa ki sha, ki ci abinci sai ya mayar da ke gida".

Ta girgiza kai ta ce "A'a na gode, dama sabir kawai nake son na gani, ban ci wani abun ba balle yayi tunanin ina fakewa da son ganin sabir ina zuwa kwaWayi".
Kalaman rumaisa ya tabattarwa da ammi rumaisa ba wauta da ?uruciya kawai ta iya ba, ta san mutuncin kanta, kuma tana girmama kanta.

Ta ce "Ai na baki ha?uri, kuma na gaya miki zan Wau mataki a kansa, kuma ko me zai ce ki rabu da shi, abun da ki ka yi masa a rayuwa bai isa ya biyaki ba, ladanki yana wurin Allah, tashi mu je ki sha ruwa ki sake karyawa, wannan tafiyar da ki ka yi na san kin gaji sosai" da ?yar rumaisa ta amince ta tashi ta bi ammi, dan tana ganin mutuncinta da darajarta, amma ba dan haka ba, sai ta ce ko iskar gidan ba zata sha?a ba balle ruwa, saboda cin mutuncin da aka yi mata.

Ammi ta kai rumaisa falonta, ta saka a ka kai mata abinci, ta fita ta bata wuri dan ta ci, ta dawo ta tarar da Adam a falo.

Rai a Sace Ammi ta ce "Ban ji daWin abun da ka yi ba ?warai da gaske, muzanta yarinyar nan da aka yi a waje, a kan me zaka ce kar a sake barinta ta shigo?"

Cikin ladabi Adam ya ce "Tuba nake, ba na yi haka ne domin Sata miki rai ba, amma yawan zuwanta gidan nan akwai matsala, bana son ta shiga cikin wani hatsari saboda ni ko ayi amfani da ita wurin cutar da waninmu"

Ammi ta Wan yi shiru ta ce "Ban ?i ta taka ba, amma a ?uruciya irin ta ta, da irin ?aunar da take nunawa gudan jininka bai kamata a Wauki wannan matakin kai tsaye a kanta ba, ba tare da bin wasu hanyoyi da ba zata ga an wula?antata ko cutar da ita ba. Tana da matu?ar wayo da kaifin basira, dan haka abun da ka yi mata dole ta kirashi da wula?anci da tozarci, kar ka sake yanke makamancin wannan hukuncin ba tare da izinina ba".

Ya risuna ya ce "In sha Allah"

"Ka biya ka fara ajiyeta a gida, ka sanar musu halin da ake ciki, don a saka ido sosai a kan ta ta daina missing makaranta, kuma kar ta sake yin wannan doguwar tafiya haka a ?afa ita kaWai"

Ya jinjinawa ammi kai.

Rumaisa ta fito, idanun nan sun yi ja ta ce "Ammi zan tafi".

"Maman Sabir har kin gama, bari ya mayar da ke gida" rumaisa ta kalli Adam sannan ta kalli ammi za ta yi magana, ammi ta girgiza mata kai ta ce "Ba'a jayayya da umarnin giwar galadima" Ammi ta yi mata maganar cikin gargaWi, haka ya tilastawa rumaisa yin shiru.

Adam ya mi?e yayi gaba, rumaisa ta dur?usa ta sumbaci goshin sabir, sannan ta bi bayan Adam.

Kamar yadda ransa yake a haWe, haka ita ma ta tsuke ta ta fuskar, babu alamar wasa da yarinta.

"Laa ka ga, bawan Allah" Adam ya ji maganar rumaisa, tsayawa yayi ya waiwaya bayansa, da gudu ya ga ta nufi jikin bishiyar dabinon da ke tsakiyar harabar gidan. Mahmud ne a tsaye yake waya, amma ya katse wayar ya zubawa rumaisa ido yana jiran ta ?araso.

Ta ?arasa tana Wan haki ta yi murmushi ta ce "Ashe ba kai ne shi ba?"

Mahmud ya ce "Shi wa?"

Rumaisa ta nuna masa in da Adam yake.

"Na zata shine da na ganka Wazu, idona ya rufe sosai da Sacin rai, ga gajiya kuma kuna kama sosai da sosai, dan Allah ka yafe mini na yi maka rashin kunya a gaban mutane"

Yayi murmushi ya ce "Kin ga jaririn naki?"

"Na ganshi, Allah ya saka maka da alkhairi da ban ganshi ba yau, da ina ga mutuwa zan yi. ?a na ne fa anty aisha ta bar mini shi, amma ya ?wace shi kuma wai ya hana ni shigowa gidan nan"

"Wace aishar?"

"Kai baka san ta ba? Kai ba Wan nan gidan bane?".

"Eh Wan nan gidan ne, amma bana ?asar jiya da daddare na dawo".

"Au ho, to in gaya maka sace ni aka yi a katsina, sai aka sato anty aisha matarsa, ta haihu ta rasu ta bar mini jaririn na kuSuto da ?yar, bayan na yi kwanaki ina wahala, amma ya ?wace Wan kuma wai idan na zo kar a sake barina na shigo, dan Allah wannan ba mugunta ba ce ba?"

Mahmud ya yi murmushi ya ce "Bai kyauta miki ba gaskiya"

"To kai baka taSa zuwa sashin ammi ka ga jaririn ba, au ashe fa ka ce jiya ka dawo, ba ka ga Wan nawa ba, mai kyau tubarkallah, ai na san ammi zata nuna maka shi ma, tunda a gidan nan ka ke"

"Eh a gidan nan nake, amma ni ba a sashinsu nake ba, ni Wan Mummy ne".

"Wacece kuma hakan?" Ta tambayeshi tana Wan gyatsine fuska.

"Babata ce, ko baki san mata biyu ne a gidan nan ba? Anyway na ga kamar jiranki yake yi, ki je kar ya zo nan wurin ya karairayaki, shi yafi masa komai sau?i"

Cikin fitsara rumaisa ta ce "Wallahi wuce nan, na gode sosai ba zan taSa manta taimakon da ka yi mini ba yau, kuma ka na da kirki fiye da wancan mutumin, dan Allah ka je ka ga Wana a wurin ammi, sunanshi Mahmud ana ce masa sabir" tana maganar ta yi gaba tana murmushi.

Turus Mahmud yayi ya bi rumaisa da kallo, Adam ya sanyawa Wan sa sunan Mahmud? Ya tambayi kansa, dan abun da mamaki.

Wurin motar adam ta nufa, da tuni ya kunnata, ya fito ya saka ana karkaWewa motar ?ura.

Ya ?arewa rumaisa kallo ya ce "Bawanki ne ni da zaki shanya ni ki tafi yawon surut?".

Ta kalleshi ta ce "Ba yawon surutu na tafi ba, godiya na je yi masa na bashi ha?uri. Ya nuna mini karamci saboda ni Wan adam ce bai koreni ba Wazu da na rasa nutsuwa ta ina kuka ba, ya taimaka mini na samu abun da nake so". Ta yi maganar irin ko maganar ta yi masa daWi ko kar ta yi masa bai shafeta ba.

"Tun daga lokacin da ki ka sake shigowa rayuwata, ki ke ta wasu irin halayya da son nuna lallai akwai wani abu a tsakanina da ke, ina Waga miki ?afa albarkacin yaron nan da kuma ?uruciyarki, idan ki ka cigaba da wannan abubuwan ki ka shiga trap Wi na zaki sha wahala na gaya miki, and as from today kar ki sake zuwar mana gida, abun da ki ka yi Allah ya baki lada, bana bu?atar sake ganinki a cikin gidan nan da sunan kin zo ganin yaron nan, idan kuma ki ka cigaba da zuwa zan nesanta shi da ke, nisantawa mai tazarar gaske da ba zaki iya cimm masa ba, dan haka idan ma wani abun ne a ranki ya sanya ki ke bibiyarsa, ki saka abun da na gaya miki a ranki. Idan har zaki cigaba da bibiyar yaron nan, za'a iya amfani da ke a cutar da shi, dan haka bana bu?atar sake ganinki a kusa da shi" yayi maganar cikin kashedi.

Cak ta tsaya ko ?wa?w?waran motsi ba ta yi, sai wasu irin hawaye da suke zubowa daga idonta.



Ayshercool

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

=?I? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*



*? 500 ne, via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*




"Meyasa baka Wau maganar mahaifiyarka da muhimmanci ba, har kake yi mini wannan barzanar a bayan idonta? Ko ba komai tana tausayina wata?ila ta san me nake ji game da sabir" ta saka idonta cikin nasa, wanda hakan ya sanya musu faWuwar gaba a tare, cikin jarumta da ?arfin hali ta daki motar Adam ta ce "Idan har bayan mutuwar anty aisha an yi umarnin a kashe sabir, na Wau duk wani riski Allah ya dafa mini na kuSutar da shi, kana tunanin bayan kuSutarmu ne wani zai haWa kai da ni a cutar da yaron da na Waukarwa babarsa al?awarin kula da shi? Wace irin zuciya ce a jikinka?"

Ma'aikatan wurin ne suka tunkarosu, amma adam ya dakatar da su, saboda rumaisa ta faWi wani abu mai muhimmancin gaske.

"Kai ka san abun da ya haWani da kai ai tun farko, kuma ban janye abun da nace ba, ba zan taSa janyewa ba kuma. Sabir idan ka ga dama ka kai shi bangon duniya, ka yi duk abun da kake ganin ya dace. Mara imani ban taSa tsanar abu a duniya ba kamar kai, ko ?an bindiga da na zauna a hannunsu wataran suna mutunta ni. saboda furucin da ka yi a kaina, wai a haWa baki da ni a cutar maka da Wa, na gode daga yau ba zan sake zuwar muku gida ba in sha Allah, in dai ni ?at halak ce mama ce ta haifeni su yaya usman ne yayyena ba zan sake zuwa gidan nan ba" ta Wauko maganar tiryan-tiryan ta ?arasa da shirme, tana kuka ta juya ta nufi gate Win.

Jikin Adam yayi sanyi, tabbas a abubuwan da ya faWa sun Wan yi tsauri.

Da sauri ta fice tana kuka, ta bi hanya, dan ko za a kasheta ba zata hau motarsa ba, wata irin wutar ?iyayyarsa ke cigaba da azalzalar zuciyarta, duk wanda zai yi yin?urin rabata da sabir, to babban ma?iyinta ne.

Sashin Mummy ya shiga yana Wan tunani, lokaci-lokaci kuma yana murmushi.
Mummy ta kalleshi ta ce "Bani labarin wannan murmushin, dawowar nan ta yi maka daWi kenan?".

Ya sake yin murmushi ya ce "Wata yarinya na haWu da ita da zan shigo, na fita yanzu na kuma ganinta, gaba Waya zubinta da character ta abun dariya".

Mummy ta kalleshi cikin nutsuwa ta ce "Ko ka fara soyayya ne?"

Ya ce "Soyayya kuma? Yarinya ce ?ar ?arama fa, amma abubuwan da ta faWa ya bani mamaki, wai ita ce ta dawo da jaririn nan da ake ta surutu a kai, na aisha turaki, wai ta zo ta ga Wan ta, ya ce idan ta zo kar a sake bari ta shigo. Yarinyar mugun ?arfin hali ne da ita, maganganunta sam ba irin na shekarunta bane, akwai shirme a maganganunta, amma akwai hikima a cikin shirmen na ta. Ba abun da ya bani mamaki kamar yadda ta iya ri?e rigata cike da ?warin gwiwa take tuhumata a zaton ta wancan gayen ne".

Cikin rashin fahimta Mummy ta ce "Wai kana nufin wadda ta zo da jaririn aisha a gidan nan? Ka ce yarinya ce ?arama?".

"Eh, wannan ai sai kun fi ni sani ku da kuke cikin gidan, ni ban san komai a kan zancen ba, kawai dai na san yarinya ce dan ta yi wutar duniya, ba za ta fi shekara sha uku ba, a nawa tunanin"

"What! Kana nufin ?ar shekara sha uku ce ta zo da jaririn da ake cewa na adam ne? Amma rainin hankalin mutanen nan yayi yawa, ta yaya ?ar shekara sha uku za ta kuSuto da jariri daga hannun'yan bindiga".

Mahmud ya Wage kafaWa ya ce "I don't know".

"Amma tsaya, yarinyar tana nan haryanzu ne, ina bu?atar in ganta"

"Mummy ki ganta ki yi mata me? No need dan Allah ki daina shiga sabgoginsu da bin diddigin sai kin san abun da suke ciki, shiyasa suke raina ki, ki ?yalesu su ji da matsalar su" yayi maganar yana mi?ewa.
Bin sa da ido mummy ta yi, amma da ta iya cewa komai ba. Sai mamaki da sake jinjina lamarin giwa da Wanta saboda zallar goge hadda, wai ?ar shekara goma sha uku ce ta kuSuto da jariri.

Rumaisa kuwa tafiya kawai take yi tana kuka, dan ta ji zafin maganganun takawa matu?a. Ta kusa titi kawai ta ji an dan?i hannunta, a fusace ta Waga kai, amma kan ta yi wani yin?uri ya fara janta, a fusace ta fara kokowar ?wace cikin tsiwa take cewa "Ka cikani me na yi maka?".

Ba zata manta fuskar sidi ba, wanda suka taSa kamota suka kaiwa takawa.
Bai saurare ta ba, ya buWe bayan motar takawa ya jefata, ya rufe motar, Adam ya sauke glass Win motarsa ya jinjinawa Sidi kai, sannan ya rufe glass Win motar ya fara ja.

"Malam ka tsaya in sauka daga motar nan, bana son ka kaini gidan ka sauke ni bana so" banza yayi mata ya cigaba da tu?insa.

"Na ce maka ka sauke ni, wai kai meyasa ka ke mini haka ne? Ka sauke ni"

Ganin bashi da niyyar kulata, ya sanya ta fara kiciniyar buWe motar, amma ta ji ?ofar motar a rufe gam.

Adam a zuciyarsa yake jinjinawa masifa da taurin kan rumaisa, da a buWe motar take haka za ta buWe ta ce za ta fita.
Ganin ba za ta iya buWewa ba, ta zauna ta cigaba da kuka tana ?anan maganganu.

Bai tsaya a ko ina ba sai ?ofar gidan su, mamaki take yi a ina ya san gidansu?.

Ko da yayi parking bai fita daga motar ba, sannan kuma bai buWe motar ba, rumaisa ta hau kiciniyar buWe ?ofar motar, amma ta ji a rufe.

"Ka buWe mini in fita" ta kai masa duka dan takaici.

Danna wayarsa ya hau yi, na wani Wan lokaci sannan ya buWe motar ya fita.
Sai dai ya kulle rumaisa a ciki, bai buWeta ba, bubbugawa tayi ta yi, amma ya fita ya tsaya ya ?i saurarar ta.

Aliyu ne ya fito daga cikin gida, yana ganin Adam ya faWaWa Murmushin sa, ya ?araso suka gaisa, rumaisa ba ta iya jin mai suke cewa, amma sun Wan jima suna tattaunawa sannan ya buWeta ta fito tana wani basarwa.

Wani mugun kallo Aliyu ya yi mata, sannan ya ce "Sai ki wuce ki shiga" ko a jikinta, ta yi gaba dan ita yau ko za'ayi manda?o da ita tun da bu?atar ta ta biya shikenan.

Wani wawan burki ta yi, da ta ga mai sunan Baba a ?ofar Wakin mama, yana gyara botirin hannun rigarsa.

Wani irin mugun yawu ta haWiye, ta fara takawa a hankali kamar hawainiya.
Fuskarta ?arara ta bayyanar da tsantsar tsoro da razanin da take ciki.

Aliyu ne ya yi sallama da shi da Adam, mai sunan Baba ya amsa ba tare da ya Wago ya kallesu ba, sai ma ja da yayi da baya ya basu hanyar shiga falon mama.
Bai kula Adam ba, shi ma bai kula shi ba, suka shiga Wakin mama da sallama, da gudu rumaisa ta bi su tana waiwayen mai sunan baba.

Mama ta faWaWa murmushinta tana yi wa Adam barka da zuwa.

Ya ce "Tuba nake mama, tun da aka bar asibiti ban samu na zo na gaisheki ba, abubuwa ne sun yi mini yawa ?warai da gaske"

Mama ta ce "Babu komai, ya gida ya hajiyar take? Ya kuma mai gidana".

"Duk suna nan lafiya, ta ce a gaishe ki"

Rumaisa ta kalleshi a ranta ta ce "Kalleshi,

Please Login or Register in order to submit comment