You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta huce abin da ya yi mata.
Duk wani hoton Adam yake kan account Win Jabir, sai da Jabir ya sauke shi, ?arshe ma yayi blocking Win ruma, bayan yayi reporting account Win ta an rufe mata shi.

Abdallah ya ce "Sai dai ruma ta yi ha?uri, dan wani wurin za shi, amma mama ta ce ya daure ya kaita, dan ruma a zahiri damuwa ta nuna da rashin lafiyar Hauwwaliya.

Ba dan ya so ba ya tasa ruma a gaba zuwa mandawari, Hauwwaliyarma ta samu sau?i, bayan sun gaisa da mutanen gidan, Abdallah ya ce da yamma zai zo ya Wau ruma.

Hauwwaliya ta yi ta murna da ganin ruma, dan rabon da su haWu tun wancan zuwan.
Bayan ruma ta Wan jima, ta fara ?o?arin aiwatar da abin da ya kawota.

"Hauwwaliya, ina ne gidan Galadima ne?"

Hauwwaliya ta ce "Wai makaranta?"

Ruma ta yi tsaki ta ce "Galadiman kano"

"Wanne?"

"Au biyu ne?"

Hauwwaliya ta ce "Ai akwai Galadima na yanzu, wanda ba shi da lafiya yana Germany, sannan akwai gidan Galadiman kano wanda ya rasu"

Ruma ta ce "Wanda ya mutun"

Hauwwaliya ta yi dariya ta ce "Ke ai wan baban su Janna ne, jikar turakin nan da muka je gidan su biki ta bamu kaya, kuma yayan Galadiman kano na yanzu ne duk fa 'yan uwa ne, sarautar ba a rabawa a bawa bare dole sai su"

Ruma ta yi tsaki ta ce "Ni fa ba nasaba na tambayeki ba, ina ne gidan na sa"

Hauwwaliya ta ce "Shi wa?"

"Ke wai ya ina magana kina raina mini hankali, maganar wa muke ne?"

"To ke meye ala?arki da su da ki ke tambayata?"

Ruma ta ce "Assignment aka bamu a makaranta"

"Aka ce me?" Ruma ta Sata fuska ta ce "Hauwwaliya, ni zaki wula?anta?".
Hauwwaliya ta kwashe da dariya ta ce "Yi ha?uri, Galadiman da ya rasu gidansa a bayan gidan sarki yake, wani ?aton gida gari guda, baki ga katangar gidan ba, doguwa sosai a nan dai gidan yake"

"To kin san 'ya'yan gidan?"

"To meye ala?ata sa su da zan san 'ya'yan gidan, suma 'ya'yan gidan duk a cikin assignment Win suke?"

Ruma ta yi murmushi ta ce "A'a dan Allah in anjima mu je, ina son in ga dokuna"

Haka ruma ta din ga lallaSa Hauwwaliya, suka tafi yakasai, har family house Win su Takawa.

Ruma ta yi mamakin girman gidan, ya fi na Turaki da suka je rannan, suka gama yawonsu suka koma gida.

Yau ma sai magariba sannan Abdallah ya Wauketa, suka koma gida, sai dai tun da suka koma gida, ruma take tunanin ta ina za ta ga Takawa, dan ta ?udirce a ranta ba zata ha?ura ba.
Sai dai gate Win gidan na su kawai girmansa abin mamaki ne, babu wata 'yar kafa da za ta bi ta shiga, ga masu gadi a zaune a ?ofar gidan, da alama shiga gidan ba zai zama abu mai sau?i ba.

***
Tun da Samha ta koma gida, take tunani a kan abin da Khalifa ya zo mata da shi, dan ba abu ne mai sau?i ba. Amma duk tunanin da ya kamata ta yi ta yi, shikaWai me mafitar da ya rage mata, dan takawa hankalinsa sam ba ya kanta, idan har ba kawar da ala?ar nan ta yi ba, to ita da Adam sai dai kallo daga nesa, haka zalika sai ta yi ?o?ari wurin takawa su Hajiya Jamila burki a wasu Sangarorin dan idan suka nakasta shi, to ita suka yi wa.

***
Mama ta zauna ta tattauna da yaranta, a ?arshe suka amince da a sayar gonar mahaifinsu ta can katsina? a garin ?an?ara, domin yin hidimomin da suke gabansu, masu registration ayi musu, masu exam a biya musu, masu bu?atar jari duk ayi musu. Sannan still akwai filinsu da aikin gwamnati ya bi ta kai, za a basu diyya.
Sai dai mama ta ce ita tsoron garin nan take ji, kawai ayi waya su sayar Wan abin da ya samu da na diyyar a aiko musu, can dangin babansu suka hau mitar cewa mama ta mallake yaran ba ga son su je in da suje, ?arshe aka yanke Aliyu zai je.
Yaya Abubakar ya ce "Dan Allah mama idan zai je, ya kai musu ruma, tun da dama exam za su yi, su yi hutu, ko a samu su daina surutun nan da suke yi na rashin zumunci, rabon da aje da ita garin fa tun yaye, rannan da na je baki ga mita da faWan da suka din ga yi ba, wai kin fiye son 'ya'ya, wayar da muka yi da baba Habu shekaranjiya a kan biyan diyyar nan shi ma ba ki ji faWan da ya yi ba".

Mama ta ce "Ba ?i nake ba, ka san halin rashin jin yarinyar nan shi nake tsoro, ga yanayin garin babu lafiya".

"Mama ai a cikin ido ake tsawurya, in Allah ya yadda babu abin da zai faru sai alkhairi"
Mama ta ce "To, Allah ya sa"

Ruma ta ji dadin batun tafiya da ita garin mahaifinta, amma gefe Waya ta fi son sai ta tafkawa takawa Sarna, sannan su tafi yadda zai nemeta ya rasa.

***
Zaune take a kan kujerar da ke gaban mudubi, tana ta shafe-shafen turare, ?amshi duk ya gauraye Wakin, sannu a hankali ya tako gabanta yana kallonta.

"Mutum kwalliya sai ka ce aljana" dariya ta yi har sai da dimples Win ta suka lotsa, ta ce "To idan ban kwalliya ba me zan yi?"

Ya saka hannu ya fara jan kumatunta ya ce "Kai na yi missing kumatun nan naki sosai da sosai" Sata fuska ta yi tana sake tura kumatun, shi kuma ya cigaba da ja yana dariya yana faWin "My Chubby girl".

***
Tun da aka ce za ayi tafiyar nan da ruma, mama take mata nasiha da ja mata kunne a kan tafiyar da za ayi da ita, a kan nutsuwa da kama kanta, musamman saboda rashin tsaron da yake garin.

Gaba Waya Instagram sun yi banning account Win ruma, dan haka yanzu ba ta hawa Instagram Win sam.

Mama har mamaki take, duk wanda ya ce za shi cikin gari sai ta ce za ta bishi, mama dai ba ta yi magana ba, ta cigaba da zira mata ido, ta gano sintirin me take yi haka a cikin garin nan.

Yau ma haka ta dage sai ta bi Aliyu, Allah ya taimaketa ya tafi da ita.

Bayan sun je, ruma ta faki ido ta fice, ta tafi gidan Galadima, domin aiwatar da abin da ta yi niyya, ta samu napep daga nan mandawari zuwa cikin yakasai.

A ?ofar gidan ta tsaya, tana kallo tana tunanin ta ina za ta shiga? Cikin dakiya ta tunkari ?ofar gidan, masu gadin suka zubo mata ido su ga iya gudun ruwanta.

Gadan-gadan ta nufi shiga, wani Wan sanda yayi mata tsawa ya ce "Ke wurin wa ki ka zo?"

Ta Wan yi jimm sannan ta ce "Wurin wani"

"Waye wanin?".

"Sunanshi Adamu"

Wado ido suka yi gaba Waya suna kallon ruma "Ke! Baki da hankali?" Saroro ta yi tana tunanin me ta yi kuma?

"Ke haka ki ka ji ana kiransa da shi, zaki zo ki faWi wannan sunan haka? Zaki bar wurin nan ko sai mun saka dogarai sun zane miki jikinki"

"Ai ni ban san me ake ce masa ba, dan Allah ku barni na shiga"

"Ke, ba a zuwa gidan nan sai da izini, wuce ki bar nan ko ki jira idan kin nemi izini sai ki shiga".

"To a wurin wa zan nemi iznin?"

?aya daga cikin su ya ce "Ke bar nan ko na yi miki duka a wurin nan, ji mini shegiyar 'ya da baki fil-fil kamar robot"

Ta kalleshi ta ce "Ni ba shegiya bace ba, ka daina zagina" tayi maganar idonta ?yar a cikin nasa.

Girgiza kai kawai yayi, dan idan ya tunzura sai ya ji?awa yarinyar nan jikinta.

Ta samu wani Wan tudu ta zauna, tana kallon hanya. Suka kunna sigari suna sha, ruma ta kallesu ta taSe baki a hankali ta ce "An yi asara"

"Ke ki ka kuma hararata sai na miki duka, ki tashi ki tafi ko?"

"Ni dai ba a kanku nake ba, ku ?yaleni mana" ta yi maganar tana kawar da kai, tana ji a jikinta ko zata wuni a nan, sai ta ga abin da ya turewa buzu naWi.

Wata dattijiuwa ce ta nufo gidan, suna gainta da fara'arsu suka fara mata magana "Baba Sabuwa, kin dawo?"

"Wallahi kuwa, kun ganni sai yanzu ya aiki?"

Suka amsa mata da Alhamdilillah.

Ruma ce ta taso da sauri tana faWin "Baba" baba sabuwa ta tsaya ta kalli ruma ta ce "Yarinya ya aka yi?"

"Dan Allah gidan nan zaki shiga?"

Ta ce "Eh, a gidan nake aiki"

"Kin san wani Adamu a cikin gidan?" Hangame baki baba Sabuwa ta yi, tana waige-waige da fatan Allah ya sa wani bai ji ba.

"Ke 'ya ta ai ba a faWar wannan sunan a gidajen sarautar kano, takawa ake ce masa, eh na san shi"

Ruma ta yi ?asa da muryarta ta ce "Dan Allah abu zan baki, ki kai masa, so nake na ganshi an hanani shiga, amma dan Allah ki bashi wannan takardar hannu da hannu babata"

Baba uwani ta ce "To shikenan, amma in ji wa zan ce masa?"

"Idan ya ga takardar shi zai gane, dan Allah ki bashi "

Baba sabuwa ta ce "to shikenan, zan bashi in Allah ya yarda".

"Ku kuma da baku barni na shiga ba kwa ci kanku"

"Zo mu baki sigari " Wayan ya faWa cikin iya shege.

"Sai dai uwar sigari" ta faWa a hankali.

Tutsiye Baba sabuwa suka yi, a kan lallai ta basu takardar nan su duba, kar a shiga da wani mugun abu gidan, amma ta ce ba zata bayar ba.

Baba sabuwa, hadima ce a cikin gidan ita ma, ita ce shugabar hadimai a Sangaren Mummy, kuma tana Waya daga cikin masu bata rahotanni a kan abubuwan da suke wakana a gidan.
Tun da baba sabuwa ta shiga gidan, take tunani ta kai wa uwar Wakinta takardar su fara dubawa ko kuwa? Sai dai mummy ba ta nan, dan haka ta sanya takardar a Wan tofinta, ta cigaba da ayyukanta.

Ruma kuwa jinta take wasai, kamar an yaye mata wata damuwa da take damunta, tana komawa maman su Hauwwaliya da yaya Aliyu suka rufeta da faWa, dan babu wanda ya san ta fita, ko a jikinta kasancewar yau tana lissafin sa?onta zai je in da take so, sai Addu'a take Allah ya sa baba Sabuwa ta bayar da sa?onta. Aliyu ya tasa ta a gaba zuwa gida, suna tafe yana ?are mata zagi.

Wajen ?arfe biyar takawa ya tashi daga aiki, a gaggauce ya nufo gida, dan yau bai samu zuwa gidan ba sai yanzu.
A gate jami'an tsaro suka sanar sa shi zuwan wata yarinya, da take son ganinsa amma suka hanata shiga gidan, suka sanar masa da ta ba wa sabuwa takarda ta ajiye masa.

Bai kawo komai a ransa ba ya shiga gidan, yana tunanin wacce yarinyar ce haka?.

Yana yin parking ya wuce sashin Mummy, ko da ya shiga falon, Fauziyya ya tarar, jiki na rawa ta yi masa sannu da zuwa.

Bai amsa ba ya ce "Kira mini Baba sabuwa" ta mi?e tana tunanin me yasa yake neman Baba sabuwa a yammacin nan?.

Baba sabuwa ta risuna tana gaishe shi, ya mi?a mata hannu ya ce "Bani sa?ona" babu musu ta fito da takarda ta mi?a masa. Ya juya ya fice.

Fauziyya ta ce "Sabuwa, takardar mecece?"

"Wallahi wata yarinya ce ta tsareni a ?ofa, ta ce a bashi ban san yarinyar ba ma"

"To meye a ciki?"

"Ai kin san ba iya karatu na yi ba"

"Kuma da baki iya karatun ba, mai ya hana ki kawo mini, tashi dalla usless" Sabuwa ta tashi cike da haushin tsawar da Fauziyya ta yi mata, duk da ba yau ta fara ba.

Bai tsaya duba takardar ba, ya jefata a cikin jakarsa ya tafi wurin Ammi.

Gaba daya ya manta da takarda, sai washegari da daddare yana neman wasu takardu, takardar ta faWo.
Ya buWe takardar wasu 'yan ?ananan rubutu ne, marasa kan gado a cikin takardar, bai yi zaton rubutun zai karantu ba sai da ya fara karantawa, duk an gwamutsa Capital da small latter's.

*Da farko dai zan fara da yi maka Allah ya isa, dan da alama baka da ?anne mata shi ya sa ka yi mini abin da ka yi mini. Kamar yadda ka saka aka nemo ni, nima sai da na gano gidanku. Ka saka aka Wauko ni, ka zageni kuma ka ci mini zarafi, to wallahi ban yafe maka ba taSa mini nono da ka yi, ina ta kaffa-kaffa da mutuncina, ina kula da kaina amma ka sha?oni hannunka yana taSa wurin, kuma bayan idan namijin da ba muharramin mutum ba ya taSa shi ciki yake yi, to wallahi Allah ya isa ban yafe ba, kuma idan ciki ya sameni sai na kwaso maka yayyena mun zo har gidanku na gaya wa mamanka abin da ka yi mini, kuma na faWa an saci kuWin talakawa an je karatu ?asar waje. Mu zuba mu gani daga ma?iyiyarka? RUMAISA MAHMUD ?AN?ARA ?ORAYI TUNGA ?ANWAR MAZA Kazo ka kasheni*

Zuruu takawa ya yi yana bin takardar da kallo, zuciyarsa na sake karkata ga ruma aljana ce. Ya maimaita sunanta *RUMAISA!* Tunani ya tafi yi, ko ya ga wani abu mai kama da nono a ?irjinta ranar da aka kai masa ita.

Ta yaya aka yi ta gano gidan su har ta kawo wannan takarda? Rubutun nata cike yake da wauta da ?uruciya.

"Zan ?ure miki gudu, zan gane idan ma ba mutum ba ce, da ni ki ke zancen" ya maimaita wasi?ar nan ya fi sau goma, babu abin da ya fi ?ular da shi irin wai ya taSa mata nono, duk da bai ri?e cikakkiyar suffarta ba, amma shi ba ya tunanin akwai wani nono a jikinta.


Mama ta haWawa ruma kayanta cif, da zummar gobe da sassafe za su tafi ita da yaya Aliyu, yau kuma Alhamis za ta je za su yi exam ta ?arshe, haka kurum mama ta ji ba ta son tafiyar nan da ruma, amma ta bar hakan a alhini, kasancewar ruma ba ta taSa nisa da ita na kwanaki ba, ga kuma rashin ji irin na ruman.

Uniform Win ruma sun sha guga, karin nan ya tsaya WoWar Abdallah ne ya goge mata su, sai ?amshi take, sai dai kamar kullum tana tafe tana zira hannu a aljihunta tana ciye-ciye.
Kamar a mafarki ruma ta ga an wanketa da ruwan kwatamin ruwan sama da aka yi ya kwanta, ?azantar ruwan har fuskarta. A gigice ta tsaya cak, ta buWe idonta, dan ta ga wani mara mutuncin ne ya ci mata zarafi haka?

A hankali ya sauke glass Win motar, suka yi ido huWu da Rumaisa. Bakinta mutuwa yayi ta ma kasa magana gaba Waya.

BuWe motar ya yi ya fito yana ?are mata kallo.

"Ko zaki rama ne, ko da yake ba ki da abin ramawa ai, banbancin talaka da mai arziki kenan, na ga sa?onki, abin da ki ka ce na taSa Win ni ban ganshi ba ranar, shi ne na biyoki yanzu in duba in gani ko akwai".

"Wai kai Wan iska ne?" Tayi maganar ba tare da jin nauyinta ba, ga babban mutum kamar Takawa, saboda ya kaita bango.
Maganar ta dake shi, amma ya ce "Eh shi ne, yayyen naki maza da ki ke ta?ama da su, sai na kamasu na rufe, kuma na rushe gidan na ku, na ga ta tsiya".

Karo na farko da ruma ta tsaya aka sakata kuka, hawaye ya wanke mata fuska.

"Wallahi sai ka yi dana sanin abin da ka yi mini, daga yau ba zaka sake yi wa wani abun da kayi mini ba, ba dai ta?amarka kuWi ba, to ni nan Rumaisa kai da kuWin naka da sarautar ta ka sai ka dur?usa mini a kan gwiwoyinka, kuma ka saka a ranka nice nan abokiyar gabarka" tayi maganar har da dukan ?irjinta.

Girgiza kai ya yi, ya buWe motarsa ya shiga, ta dur?usa ta Webi taSon wurin ta fara watsa wa motarsa, ya taka reverse ya sake wanketa da taSon wurin ya tafi.


(*ALHAMDILILLAH, TIRKA-TIRKA, YA KUKE GANIN ZATA KAYA A TSAKANIN RUMAISA DA TAKAWA? WACE IRIN LARURA CE DA TAKAWA, KUMA MEYE ALA?ARSA DA MAITA DA HAJIYA JAMILA TA FA?A? YA ZATA KASANCE? WANE DEAL NE KHALIFA YA SAKA SAMHA? MEYE TARIHIN GIDAN SU TAKAWA, DA ASALIN GABARSA DA ?AN UWANSA. ME ZAI FARU IDAN RUMA TA JE KATSINA??? WA RUMA ZATA AURA, SHIN ZA TA NUTSU KO KUWA? KAR AYI BABU KU, MAI BU?ATAR BOOK2 YA TUNTU?ENI TA LAMBAR WAYATA 08081012143 YA YI PAYMENT*


Ayshercool
Whats app only, ban da kira Please =?O? 0808101214




[8/22, 11:40 PM] Maman Aslam: *Na gamaku da zatin Allah kar wanda ya haWa mini document Win littafina, mallakina ne, nike da alhakin amfani da abina yadda nake so, kar wanda ya juya mini abin ta kowacce siga, duk wanda ya haWa mini document Win littafi ya fitar ban yafe masa ba! Kuma ina fatan Allah ya bi mini hakkina!*
*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*

*AYSHERCOOL*




Cikin damuwa Huzaifa ya dube shi ya ce "To me ka gani da ba ka yarda da shi Win ba?"

Cikin sanyin jiki Yasir ya ce "Wallahi kawai, ni mutanen cikin motar ne ba su yi mini ba"

Tsaki Huzaifa ya yi ya ce "Ka fiye matsala wallahi, dan Allah kar ma muje gida ka yi wannan zancen ka Waga mata hankali" Yasir bai kuma cewa komai ba, suka tafi gida, sai dai shikaWai ya san abin da yake ji a jikinsa.

Ruma kuwa da suka tafi, sai kallon hanya take, tana murmushi dan tun da take, ba ta taSa tafiya mai nisa ba, kuma ta yi sa'a a wurin taga take, dan haka take ta le?e tana murmushi. Sai dai tun shigarsu, Aliyu ya lura da Mutanen da suke zaune a? gaban su, tun da suka hau motar mutanen suke waya da wani yare, wayar ta?i ci ta?i cinyewa, gashi ba mai iya fahimtar abin da suke faWa a wayar.

Ruma kuwa sai surutu take wa Aliyu, kamar an jefeta a ka, ta ce wannan ta ce wancan. Aliyu dai bai tanka mata ba, sai Adduoi yake yi yana cigaba da kallon mutanen da tsarguwa da wayar da suke ta yi.

Ruma ta Wauko wayar nan ta wurin Yasir, ta din ga Waukar kanta a hoto, ga wayar duk a ragargaje amma sai Wagawa take tana hoto, har da hoton hanya Wauka take, ta hau yin videon cikin motar tana Waukar mutane.

Ko da suka bar gari suka shiga jeji, sai wannan mutane suka ce wa direba ya sauka daga kan kwalta, ya tafi ta gefen titi kan burji, ba tare da musu ba kuwa direban ya bi umarninsu, kuma aka rasa wanda zai yi magana a kan hakan kowa yayi shiru.

"Wai ya na ga ana bin gefen titi, ga kwalta WoWar a lailaye?" Ruma ta yi maganar har sai da kowa ya waiwayo yana kallonta. ?aya daga cikin mutanen ya yi murmushi amma ba wanda ya kulata.

"Ke uban wa ki ka ji yayi magana, sai ke hazi?a mazaru?s, kar na sake jin bakinki ko na make ki" Aliyu yayi mata maganar cikin kashedi. Tura baki ta yi ta kawar da kanta gefe. Sai dai ba aje ko ina ba, ruma ta fara cewa Aliyu ita fa wannan zaman motar ya isheta.

"Wallahi idan baki kiyayeni ba sai na zane miki jikinki, ni na yi dana sanin tahowa da ke, babu wanda ake jin bakinsa sai ke? Ki rufe mini baki na gaya miki"

Kamar zata yi kuka ta ce "To ni fa na gaji ne, kuma yunwa nake ji, su wannan mutanen na gaba, ba tun da muka taho suke waya ba suke surutunsu, babu wanda ya damesu sai ni zaka ce na ishi mutane, ni wallahi yunwa nake ji ulcer ta zata tashi"

Ri?e kunnenta Aliyu ya yi ya ce "Yi mini shiru, a gidan uban wa ki ke da ulcer?"

"Cikina ne ya fara ciwo, yunwa nake ji"

"Wallahi zan zaneki idan baki shiru ba" haka ruma tayi shiru tana ?o?arin goge hawaye.

Sai da suka zo wani ?aramin ?auye, mutanen nan suka ce a tsaya, nan ma direban ya bi umarninsu ya tsaya, kowa yana son yin magana amma yana tsoro.

Aliyu ne ya fara fusata ya ce "Direba ya na ga an tsaya? Mu da muke sauri?"

Direban ya ce "Dan Allah ku yi ha?uri, wani sa?o za su karSa mu wuce, yanzun nan ba daWewa zamu yi ba in sha Allah"

Aliyu ya ce "Amma ai ba a haka, sai a nemi alfarmar na mota ba a tsaya kawai ba, wannan shiga hakki ne ai"

Sai da Aliyu ya yi magana, sannan sauran mutanen cikin motar suma suka fara ?orafi a kan abin da aka yi.
Yayin da mutanen suka yi shiru ba su kula kowa ba.

Sun kai mintuna sha biyar, sannan wasu mutane suka ratso cikin dajin? a babura, mutanen suka sauka, suka karSo wata uwar jaka, sannan suka dawo motar. ?aya daga cikin su ya dubi ruma cikin gurSatacciyar hausar sa ya ce "Ke ki ka ce ki na jin yunwa ko?" Ta Waga masa kai alamar eh.

Ya bata wata ba?ar leda, ta karSa ta ce "Na gode" Aliyu ya bi ruma da kallo dan ya rasa me yakamata yayi mata, kawai ba ta san mutum ba ya bata abu ta karSe.

Gasashshiyar kaza ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ce a ciki, da ruwan roba, ta waro ido ta ce "Laa yaya kaza ce"

Ya harareta ya ce "Mayya, tun da baki taSa cin kaza ba, idan ki ka ci sai na miki dukan tsiya"

Ta Sata fuska ta ce "To in mayar masa, in ce ka hanani ci?" Banza yayi mata, ganin bai kulata ba ya sanya ta saka hannu ta hau cin abarta.

Da ta ci ta ?oshi ta Waure sauran, ta kwanta a jikin Aliyu ta hau bacci.

****
Lafiya Adam ya sauka a Abuja, ya sauka a hotel Win da zai zauna na kwanaki biyu, dan ba ya son a san da zuwansa, shi ya sanya ya sauka a hotel, sai dai gabansa ya tsananta faWuwa ya rasa dalili, ya kira Ammi ya kai sau uku, amma ta ce masa komai lafiya babu wata matsala.
Da yamma ya shirya ya ce bari ya Wan fita ya je wurin abokansa, ko ya Wan rage damuwar da ya rasa meya haddasa masa ita.
Sai dai yana fita harabar hotel Win, ya ji kansa ya wani sara, yayi ?o?arin basarwa? ya fita, amma ya kasa ?afarsa ta yi masa nauyi ya ji yana nema ya faWi, a hankali ya juya ya koma Wakin da ya sauka, ya nemi wuri ya kwanta, saboda yadda yanayin jikinsa ya sauya tamkar zai fita hayyacinsa.

***
Ruma na farkawa daga baccin da ta yi, ta cewa Aliyu kashi take ji, shi kuma ya ce sai dai ta ri?e kayanta sai sun sauka, don ko zata yi hauka ba zai saka a tsaya ba, ba zai bari ma ta yi kashi a daji ba.
Ta din ga matse ?afa tana nema ta yi masa kuka, har sai da ta fara janyo hankalin mutanen da ke motar.
"Wai kai ba ka ga yarinya bace ne? A tsaya ta yi mana" cewar Waya daga cikin mutanen da Aliyu ya kasa yarda da su.

Aliyu ya ce "A'a ba zata yi ba, idan mun je in da zamu ta yi" ya bawa mutumin amsa yana tsuke fuska. Ai bayan batun kashi ta cigaba da kuka, ita fa zai zubo, kuma ta gaji da zaman motar nan. Kan Aliyu ya yi magana motarsu ta yi faci, a tsakiyar jeji.

Fasinjoji suka din ga tsaki suna mita, masu ruwa suka Waura alwala kasancewar azahar ta yi, suka yi salla.

Wanda ya bawa ruma kaza ya kalli Aliyu ya ce? "Abokina tun da an tsaya gyara motar, ka shiga da ita ta samu wuri ta biya bu?ata mana".

"?an uwa ai na gaya maka ba abin da zata yi sai mun je, ?yaleta ?arya ma take ba wani kashi da zata yi"

Kowa yayi salla amma banda wannan mutanen, ana ta fafutukar sauya taya, tabbas da a gari motar nan ta lalace, da ba abin da zai hana Aliyu ya canza musu mota, saboda bai yadda da mutanen nan ba, shi ya san me ya gani, kuma yana tsoro yayi magana su cutar da su.
Aliyu yana salla, ruma ta tsaya tana ta ?arewa dajin kallo tana Waukar hoto da akwalar wayarta kamar abin da ta fito yi kenan.

"?an uwanmu ku ba kwa sallar ne?" Ruma tayi maganar tana

Please Login or Register in order to submit comment