You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce "Wayyo laushi, Innalillahi kujerar nan ta ji katifa yasin, kujerar masu kuWi daban take, har na tuna wata kujera da na gani a gidansu wata 'yar ajinmu, kujerar nan duk ?ashi, sai soso duk a waje, na ?usa ta kusa tsarge mini mazaunai"

Usman ne ya talle mata ?eya ya ce "Gaisuwa fa muka zo, ki ke yi mana surtu, shashasha" shiru ta yi ta sunkuyar da kanta ?asa kamar ta Allah.

Mama ta ce "Rumaisa yaushe ki canza halaye zuwa na banza ne? Dama haka na koya miki rashin gaida mutane ko?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a ki yi ha?uri"

Aka zo aka din ga jere musu kayan abinci kala-kala, da na sha, ita dai rumaisa burinta ta ga Sabir.

Adam ya je ya tarar da ammi ta aiki su Nusaiba, daga ita sai sabir a Wakin, ya ce "Ammi kin yi ba?i".

Ammi ta ce "Suwaye, na ce duk wanda yayi gaisuwa ya tafi ina son hutawa ne".

Rasa mai zai cewa ammi yayi, dan ko sunan rumaisa ba ya son kamawa, ya ce "Yarinyar nan ce, da mamanta da yayyenta suka zo yi mana gaisuwa".

Cikin rashin fahimta ammi ta ce "Wace yarinyar kenan?"

"Wannan yarinyar da ta zo da Sabir" Sabir Win ma da ya faWa ji yake kamar ya kwafsa, kasancewar rumaisa ce ta sanya masa sunan.

Cikin fara'a ammi ta mi?e tana faWin Allah sarki.

Adam ya karSi Sabir a hannun ammi, da niyyar ya gwanyawa rumaisa, suka fito falon.

Ko ammi ba ta kalla ba, ta mi?e tsaye tana jiran Adam ya ?araso ta karSi Sabir, amma ya canza hanya ya yi wani wurin. Ai ba su ankara ba rumaisa ta bi bayansa da gudu tana "Ka tsaya in Wauke shi, ka zo ka bani Wana".

Ayshercool.


paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu bu?atar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*



Da fari bayan bayyanar rumaisa, mama ta zaci ruman nutsuwa ta Wan ratsata, amma ina sai ta ga akasin abun da ta yi tsammani, halinta yana nan yadda yake, Aliyu na ?wala mata kira amma ta rufawa takawa baya.
Murmushi ammi ta yi ta ce "?yaleta, shi ma dai neman magana ne ya sanya ya Wauke shi zai fice, da na san haka zai yi da ban bashi sabir Win ba".

Usman ya ce "Ai gara da ya hanata, ?in gaishe shi ta yi, sai tambayarsa ina Wan ta dan ba ta da kunya"

Mama ta girgiza kai ta ce "Rumaisa ai sai fatan Allah ya shirya. Hajiya ina wuni ina gajiya?" Ta yi maganar tana mayar da kallonta ga Ammi

Ammi ta ce "Lafiya lau Alhamdilillah, ya gida ya iyali?".

"Kowa lafiya ?alau, ya kuma ?arin ha?urinmu".

"Ha?uri mun gode Allah"

Mama ta ce "To Allah ya sa ta huta, Allah ya rahamsheta"

Ammi ta amsa da "amin ya rabb, ya jikin rumaisa kuwa ina fatan ta wartsake gaba Waya"

Mama ta ce "Jikinta dai da sau?i, amma ta?i sakin jiki kullum kuka ita sabir, yau ne ma ta Wan saki jiki har da hira da ta ji an ce za a zo gaisuwa".

Ammi ta ce "Allah sarki rumaisa, Allah dai ya bata ha?uri"

Hira suka Wan shiga taSawa da mama, har ammi take Wan gutsura mata kaWan daga cikin halin da take ciki, na dangane da ?alubalen rasuwar aisha, daga ita har adam, haka nan ammi take jin yadda da mama a cikin ranta.

Rumaisa kuwa bin adam ta cigaba da yi, tana cewa ya bata Wan ta, amma yayi banza da ita ya cigaba da tafiya.

"Wallahi idan ba ka tsaya ka bani Wana ba, sai na yi maka ihu na tara maka mutane" bai ko tsaya ba balle ta sanya ran zai kulata. Kan ta ankara tuni ya sulale ta wata ?ofar ta neme shi ta rasa.

Komawa ta yi falon da ta baro su mama tana kuka.

Duk suka bita da ido, ammi ta ce "Rumaisa lafiya? Menene?"

Cikin kuka ta ce "Ba guduwa yayi da sabir Win ba, ina ta ro?onsa ya?i kulani, ya bi ta wata ?ofa ya gudu"

Ammi ta ce "Subhanallah, takawa fa wasu lokutan ba shi da girma sai na jikinsa, bari kan ku tafi zai zo har nan ya sameni"

Mama ta ce "Rabu da ita, yanzun nan zamu tafi, can gida ina ta ba?i, yan dubiya da jaje"

Ammi ta ce "Allah sarki, na zata zaku wunar mini, baku ci komai ba fa"

"Wallahi karki damu"

Rumaisa ta ce "Dan Allah mama mu Wan jira ko zai dawo ".

Aliyu ya ce "Ba in da zai dawo, ba dai ke fitsara ba, gara ayi maganinki ai"

Ammi ta yi murmushi ta ce "Yauwwa, dan Allah wata alfarma nake nema, idan Allah ya kaimu jibi, ina son a kawo mini rumaisa, za'a kaita wurin turaki, mahaifin aisha, abun da zai hana a kaita yanzu, haryanzu yana karSar gaisuwa kuma yana cikin alhini, amma ya bu?aci ya ganta, ko zuwa jibi ne in Allah ya kaimu sai ko turowa na yi a Waukota".

Mama ta ce "Yayyenta za su rakota in Allah ya yarda, babu wata damuwa Allah ya yi mata rahama, ai ko bai nemeta ba ya ci taje ta yi masa gaisuwa "

Ammi ta yi ta yi wa mama godiya, da kanta ta raka su har harabar gidan, rumaisa kuwa sai kuka take yi, ammin tana bata ha?uri, tare da yi mata alwashin hukunta adam.

Ko da suka taho hanya, mita ta cigaba da yi tare da cewa da ta san ba zata ga Sabir ba da wallahi ba zata bi su ba, dan ita saboda sabir ta je.

Su Aliyu ne suka tanka mata, mama kuwa shiru ta yi mata, sai da suka je gida, ta dirar mata da faWa, faWan da tun da ta kuSuta daga hannun yan ta'adda ba ta yi mata irinsa ba, sakamakon rashin hankalin da ta yi wa takawa yau.

Takawa kuwa ya kai awanni uku bai dawo ba, har wayarsa ammi ta din ga kira, yana Wakinsa ya kulle kansa da shi da sabir, sai da ya daidaici su ruma sun tafi, sannan ya mayarwa da su iman sabir, ya fice ba tare da ya bari ya haWu da ammi ba dan kar ta yi masa faWa a kan abun da ya yi.

Yana fita gidansa ya wuce, ya je ya kulle kansa, ya kashe wayoyinsa, dan baya ko son jin motsin wani a kusa da shi.
Rainin hankalin da rumaisa ta yi masa ne ya faWo masa a rai, ta?i gaishe shi, amma ta biyo shi tana kiran ya bata Wan ta, wani gajeren tsaki yayi ya nemi wuri ya kwanta tare da lumshe idonsa.

Da magariba mama take bawa su Abdallah labarin yadda suka yi a gidan su takawa da suka je gaisuwa, da abun da rumaisa ta yi, suka yi mata caa suna yi mata faWa, ita gaba Waya faWan da suka yi mata bai dameta ba kamar takaicin rashin ganin sabir, ji take da zata ga Adam ta sha?e shi ta huta.
Mai sunan baba da yake jin hirar ta su bai ce komai ba, ya kalli in da rumaisa take ya ga sam hankalinta baya kan faWan da suke yi mata, baya raba Wayan biyu ya san ba zai wuce tunanin Sabir take ba.

Gyaran muryar da ya yi ne ya sanya su waiwayowa suna kallonsa.

Cikin kakkausar muryarsa ya ce wa rumaisa "Ki nemo uniform Win ki kafin ranar monday in Allah ya kaimu, zan je mu yi magana da shugaban makarantar ku zaki koma makaranta" turus rumaisa ta yi, dan har ga Allah ita ba ta ?aunar makaranta a ganinta kawai salon uzzurawa rayuwarta ne.

Usman ya ce "Amma mai sunan baba bai yi wuri ba? Yakamata a bari ta gama warwarewa"

"Ba wata warwarewa da zata kuma yi, makaranta za ta koma, daga boko har islamiyya" yadda ya yi maganar very serious, ya sanya kowa jan bakinsa ya tsuke, rumaisa ji ta yi kamar ta fasa ihu, dan ba ta ?aunar makaranta ko kaWan.
Daga bisani ta ajiye tunanin komawa makaranta, ta sanya tunanin yadda za ta yi ta ga Sabir a gaba.

Samha ba irin tunanin da ba ta yi, a kan yadda za ta samu burinta ya cika a kan Adam, tun da yanzu dai wadda za ta zame mata matsalar ta kau, so take yi ta samu wata kafa da za ta sanya ace ta maye gurbin aisha a wurin Adam.
Ko da ta je ta yi wa mahaifinsu gaisuwa baya walwalar da zata sanya ta kawo masa zancen abun da yake ranta.
Rashin samun mafita ya sanya ta shirya ta tafi gidansu takawa, wurin babbar aminiyarta Fauziyya.

Bayan da Samha ta gama gaya mata abun da ke ranta, Fauziyya ta ce "Lallai Samha kina da matsala, a wannan yanayin da ake ciki, ana tsaka da jimamin mutuwar zaki ce ga bu?atar ki, ai wannan sai ace ma ke ki ka kasheta".

"Allah ko? Wallahi na rasa yadda zan yi ne Fauziyya, yadda ki ka san in Waura mana auren da kaina, wata dama ce fa da na daWe ina jira, kawai sonake na yi amfani da ita ko ta yaya".

Fauziyya ta ce "Aikuwa kwaSarki za ta yi ruwa, ke kin san yadda mai girma turaki yake ?aunarta, daga mutuwarta ki zo masa da kina son mijinta, ashe kuwa kin taro aradu da ka".

Samha ta yi wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta ce "Hmm ba dan idon mutane ba, ai mu mutuwarta abun farinciki ce a garemu, ko banza mayi 'yan ci mu samu ya din ga yi mana kallon 'ya'yansa mu ma. Yanzu dai ba wannan ba, fauzi meye abun yi?"

"Yanzu ai baki ga ta neman abun yi ba, har sai Allah ya sa an kammala zaman makokin nan, ki ga in da mai girma turaki zai sanya gaba"

"Zan iya jiran nan kuwa Fauziyya, kar na sake rasa wannan damar?"

"Aikuwa idan ba zaki jira ba, zaki jawa kanki magana"

Samha ta Wan yi shiru sannan ta ce "Haka ne, yanzu tashi mu je sashin su takawar na ga jaririn dai".

Fauziyya ta ce "Saboda me, da an so mu ganshi ai ba za a din ga Soye shi ba".

Samha ta ri?o hannunta ta ce "No, kar ki yi mini haka mana, ai duk cikin salo ne shi ma, dan Allah taso?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
".

Haka Samha ta lallaSa Fauziyya suka tashi suka nufi part Win Ammi.

Hadiman ammin suka tarar suna ta aikace-aikace, Fauziyya ta yi musu umarnin da su yi musu iso a wurin ammi.

Mintuna biyar, sai ga hadimar ta dawo, ta ce su shiga.

Kamar na kirki haka suka shiga a kame, a falon sashin suka tarar da ammin a zaune, suka gaida ammi, suka sake yi mata gaisuwa sannan Fauziyya ta ce "Ammi, dama zuwa muka yi mu ga jaririn, tun da Allah ya sa aka yi rasuwar nan babu wanda ya ganshi"

Ammi ta Wan yi shiru sannan ta ce "Akwai dalili ne, bashi da cikakkiyar lafiya shiyasa ba a son kowa ya din ga Waukar sa, amma bari in sa a kawo muku shi".

Wayarta ta Wauka ta kira iman a waya, ta ce mata ta zo da sabir falonta tana son ganinta.

Daga cikin bedroom Win ammi iman ta fito, nusaiba na biye da ita, sai dai kallon da samha ta yi wa iman, ya sanya iman saurin kawar da kanta gefe.
Ta ?arasa gaban ammi ta ce "Ammi gani".

"Ina sabir Win? Su Fauziyya ne zasu ganshi".

Iman ta ce "Ammi bacci yake yi, kuma kin san likita ya hana Waukarsa, sai dai mu shiga su ganshi a? net

Nusaiba ta ce "A net Win ma dan dai su ne, amma ba shi da cikakkiyar lafiya" da ?yar samha ta danne fushinta, suka bi su iman Wakin ammi, Sabir yana cikin net Win sa sai bacci yake yi, yayi ?alau da shi.

Samha ta kwaSe baki, dan haka kurum ta ji ta tsani Wan, ta ce "Ammi bari mu je, idan ya ji sau?i sai a bamu mu Wauka".

Ammi ta ce "Ku yi ha?uri fa, likita ne ya saka wannan dokar"

Fauziyya ta ce "Bakomai ammi, Allah ya raya shi" da haka suka fito, suna fitowa Fauziyya ta ce "Aikin banza da ki ka takura mu je, gashi nan a wula?antamu a banza ai"

"Ke ni ba wannan ba, zuwa na yi da niyyar in nuna nafi kowa ?aunar yaron, amma ina ganinsa na ji na tsaneshi wallahi, wai meya hana ya bi uwarsa ya mutu ne shi ma?"

"Aikuwa ki ka kuskura aka gane ba kya son yaron nan, ke da Adam har abada" Samha ta ja tsaki ta ce 'Dole zan daure zuwa lokacin da burina zai cika, shegen yaron kyau kamar ubansa, na so da wani yayi kama ace Wan shege ne ma, tunda ba wanda ya san ta na da ciki, duniya kowa ya san ciki baya zama a mahafairta kamar rariya haka take"

"To ni dai shawara nake baki, kar ki Sata rawarki da tsalle, ki iya takunki"

"Ohhh Allah, to shikenan zan bi komai a sannu, amma a wannan karon adam ba zai kuSuce mini ba"

Bayan fitar su Fauziyya kuwa, bin su iman da kallo ammi ta yi ta ce "Mai ya sa zaku hanasu Waukar yaron nan, suma ai Wansu ne"

Nusaiba ta ce "A'a ammi, ta idonka daban ta bayan idonka daban, dole ayi kaffa-kaffa da sabir, ba kowa ne ma yakamata ya din ga zuwa wai ya zo ganinsa ba, kin san komai ammi".

Ammi ta jinjina kai ta ce "Haka ne, Allah ya iya mana"

Suka amsa da Amin.

Rumaisa kusan tun da suka dawo daga asibiti, sai ta yi mafarki gata a wurin su sule, ta yi ta zabure-zabure, tana ihu, sai mama ta ri?eta tayi mata adduoi, gashi kullum ta zauna ba ta da zance sai na Sabir Win ta.
Duk tsananin surutu irin na rumaisa, ta ?i sakin jikinta ta bayar da labarin abun da ya faru da ita a hannun 'yan bindiga, da an fara zancen kuma sai ta yi shiru ta?i magana.

Yau shine ranar da suka yi, za a kai rumaisa wurin turaki, dan tun da safe ammi ta kira wayar mama, maman ta tabattar mata da za a kawo rumaisan.
Da safe bayan ruma ta cakali abinci, mama ta sakata tayi wanka, dan da fari taurin kai ta fara, wai ba zata je ba, sai da mama ta yi da gaske sannan ta shirya.

Mama ta kalleta a tsanake ta ce "Rumaisa" ta Wago ta kalli mama.

"Gaban babban mutum zaki je, kar ki je ki nuna masa halinki na rashin hankali, tsaf zai saka a zaneki, wurin mahaifin ita mai rasuwar za a kai ki, ya ce yana son ganawa da ke, saura ki je ki yi masa rashin hankalin naki da ki ka saba, ko kuma kina ji ana tambayarki abu, ki ?i bayar da amsa, ki ka dawo mini gidan nan sai jikinki gaya miki, ki ka kuskura ki ka yi rashin Wa'a zaki ga yadda zan yi da ke. Usman ka saka mini ido a kanta, duk abun da ta yi na rashin Wa'a ka zaneta tun a can"

Ya jinjina kai ya ce "In sha Allah" ita dai ba ta ce komai ba, ta tashi ta Wauko facemask Win ta ta saka, usman ya tasata a gaba suka fita.

Duk wanda ya gansu a hanya, sai ya tsaya ya sake jajanta abun da ya samu rumaisa, da masu son bugun cikinta su ji yadda aka yi, duk tayi mirsisi ta?i magana, kai ka ce shiriya ce ta zo mata.

Adam tun safe yana gida, yana jiran zuwansu rumaisa, dan ya kai su wurin turaki, amma ba su zo ba sai azahar.

Suna sanya ?afa a cikin falon, ?amshin turarensa ne ya fara dukan hancin rumaisa. A hankali ta Waga kai aikuwa ta hango shi a zaune, ya kashingiWa ya lumshe idanunsa.

Ammi ta faWaWa murmushinta, tare da yi musu sannu da zuwa. Sam rumaisa hankalinta ba ya kan su, ko gaida ammi ba ta yi ba, sai waige-waige take yi.

Ammi ta ce "Rumaisa ai kya bari mu gaisa, kan ki fara neman Wan naki ko?" Rumaisa ta dur?usa ta ce "Ina wuni?".

Ammi ta ce "Na ga dai hankalinki baya nan, bari yanzu zasu kawo miki shi".

Rumaisa na jin su suna cigaba da gaggaisawa, amma ta kasa zama, kawai jira take ta ga ta ina za a fito da sabir.

Usman suka gaisa da takawa, yake tambayarsa ya mama ya ce masa tana nan lafiya.
Kamar mai shirin zarewa, suka ga rumaisa ta tashi ta nufi Nusaiba, tana zuwa ta karSe sabir daga hannunta, nusaiba ta bi rumaisa da kallo, dan ba ta san wacece ba.

Ta rungumo sabir ta zauna da shi a wurin, kawai ta saka kuka "Sabir Wina, ka ganni, ka gane ni? Ka yi missing Wina ko? Kullum sai na yi tunaninka, kullum sai na yi mafarkinka, bana iya cin abinci ma kullum ina tunaka mai sunan babana, wallahi ina sonka sosai, ?wace mini kai aka yi" ta ?arasa maganar tana fashewa da wani irin kuka, da yake bayyanar da tsantsar damuwar da take ciki.
Abun ka da uwa, take jikin ammi ya yi sanyi, ta ji hawaye sun cika mata ido, tausayin rumaisa ya kamata, amma ta dake ta ce "Haba rumaisa, ai kowa ya san Sabir Wanki ne, babu mai rabaki da shi, ki daina kuka kin ji, nusaiba saka a kawo musu ruwa ma, da abun taSawa".

Nusaiba kuwa tsananin mamaki ne ya cikata, yanzu wannan 'yar yarinyar ce ta yo jigilar jariri har ta kuSutar da shi, iko sai Allah.

Sabir kuwa ?ura wa rumaisa ido ya yi, ko Wan Wauke kai ta yi, sai ya bita da ido kamar zai yi mata magana. Murmushi take yi masa, hawayenta na Wiga a kan kayansa ta ce "Ka gane ni? Na da muka taho tare daga dajin nan? To nice nan rumaisa mamanka, ka din ga ce mini ko mama, ko umma ka ji Wan albarka".

?an lumshe ido sabir yayi kamar zai yi barci, sai kuma ya washe mata bakinsa gaba Waya yayi dariya.

Cikin matu?ar farinciki ta ce "Yaya usy, yayi mini dariya wallahi, kalli ka ga ya gane ni".

Usman ya ce "A'a ba wani ganeki da yayi, bacci zai yi haka jarirai suke bacci".

Haka aka jere musu kayan abinci, ruma ta koma gefe ta?i cin komai, sai wasa da take yi wa sabir, shi kuwa takawa satar kallonta kawai yake yi, wata ajiyar zuciya da take yi, kai ba ka ce ba Wan ta bane ba.

Adam ya numfasa ya ce "Ina ga mu tafi, rana na cigaba da yi".

"Ni dai ku je ku dawo, kan nan na ga sabir sosai".

Ammi ta ce "Rumaisa, ai zuwan naki ne, ke yake son gani, ki yi ha?uri in Allah ya yarda da kaina zan din ga sawa a kawo miki sabir kin ji".

Kallonsa ta cigaba da yi tana kuka, Adam kuwa ya taso, yazo kanta ya dur?usa zai Wau sabir.
Ri?e shi ta yi gam tana kuka, ya saka hannu ya Wauke sabir Win ya bar ta da towel.

Ri?e towel Win tayi ta cigaba da kuka, ammi gaba Waya ta rasa me zata cewa rumaisa, sai da a ranta ta ji tsoron kar su shiga hakkinta wani ciwon ya kamata saboda ?wace yaron nan.

Haka nan sai ammi ta ji nauyin rumaisa, ta ma rasa me zata gaya mata ta rarrasheta.

Nusaiba kanta wani irin tausayin ruman ne ya kamata, ta tashi ta bi bayan Adam bedroom Win ammi.

Ya dubi nusaiba ya ce "Ku kula da kyau, kar a sake fito da shi, ina iman take?"

Jiki ba ?wari Nusaiba ta ce "Ta sha maganin mura ne, tana Wakinta tana bacci"

Ya mi?e mata sabir, sannan ya fito ya dubi usman ya ce "Mu je ko".

Ammi ta kasa cewa komai, sai ri?o hannun rumaisa, zuwa babban falo, ta ce "Rumaisa, ni dai ina kuma baki ha?uri, na san mu masu laifi ne a wurinki, amma ki yi ha?uri ki mayar da hankali a kan makaranta, in dai sabir ne bamu isa mu rabaki da shi ba, tunda Wanki ne"

Baba Uwani ce ri?e da tsintsiya a hannunta, ta biyo bayan ammi, ta washe baki ta ce "Uwar Wakina ba?i ki ka yi haka ne?"

Ammi ta waiwaya ta ce "Eh, dama ina nemanki" ta mayar da idonta kan rumaisa ta ce "Rumaisa, ki gaida mini da mamanki, akwai sa?onki a wurin takawa, ki yi ha?uri ki yi ta addu'a kin ji yarinyar kirki" rumaisa kawai jinjina kai ta kasa, ta bi bayansu takawa.

Usman har cikin ransa yake jin babu daWi kukan da rumaisan ke yi, adam kuwa jinjinawa azababben ?arfin halin rumaisa yake yi.

Ba wanda ya kuma juyowa tsakanin shi da usman, sai dai suka fita haraba wurin motar da za su hau, sannan suka waiwaya ba su ganta ba.

Usman ya ce "Kaii, ina yarinyar nan ta tsaya kuma?".

Adam ya ce "Bari na je na duba, ina zuwa "

Ya ja da baya ya koma in da suka biyo.

A zaune ya tarar da ita, bayan wasu bishiyu, ta cukuikuye a cikin hijjabinta, tana kuka mai Wan sauti kaWan.

"Ke!" Ya yi maganar cikin tsawa. Ta zabura ta Wago ta kalleshi, da sauri ta tashi tsaye.

A Wan ?ufule ya ce "Meye haka muna tafiya zaki ja ki tsaya? Sauri fa nake bani da lokaci".

Wani mugun kallo ta yi masa ta ce "To ina ruwana da rashin lokacinka, ni fa ba a son raina na zo ba in gaya maka, kuma wallahi babarku tana son bani sabir, kai ne ka dage ka ?wace mini Wa, kuma sai ka bani Wana ko ba ka so, ko kuma ka ga matakin da zan Wauka".

Adam ya ?are mata kallo ya ce "Idan aka baki shi, gaya mini da me zaki shayar da shi? Kalleki fa".

"To ai dai na ga ba shayar da shi ake yi ba, madara ake bashi, kuma idan na girma na zama babba sosai zan dinga shayar da shi".

Ya girgiza kai ya ce "An daina ba shi madara yanzu ai, ni nake shayar da shi, tunda na san nesa ba kusa ba, na fiki abun bashi, tashi ki wuce mu tafi".

AYSHERCOOL.
08081012143


paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu bu?atar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*


Shiru ta yi ta bishi da ido, tana nazarin maganarsa, ta yaya namiji zai shayar da jariri ita tun da take ba ta taSa gani ba, ko dai raina mini hankali yake?' ta tambayi kanta.

"Ki tashi mu tafi ina magana kina kallona" ta ji maganar sa cikin tsawa, da sauri ta tashi ta yi gaba ta wuce shi, ba tare da ta waiwayo in da yake ba ta mi?a ta tafi hanyar harabar gidan.

Usman na ganinta ya ce "Ke kuma ina ki ka tsaya, sai da ki ka saka a koma nemanki, wato dai ba ki ji abun da mama ta gaya miki ba ko?" Ta girgiza kai alamar a'a.

"Ba ki ji ba mana, idan muka koma gida sai na gaya mata" ita dai ta yi shiru ba ta ce uffan ba.

Adam ya ?araso ya nufo motar, rumaiss kallonsa take ta ga ?irjinsa a cike yake yadda zai shayar da yaro, amma ta kasa gane komai, kasancewar dogayen kayane a jikinsa.

Adam ya shiga ya kunna motar, usman ya buWewa ruma baya ya ce ta shiga, amma ya ga ta tsaya cak, ta zubawa gate Win gidan ido.

"Wuce mu je" usman yayi maganar yana tunkuWata cikin motar.

Cikin motar wani irin sanyi da ?amshin turaren Adam suka cika mata hanci, sai dai ta din ga jikinta wani iri, kamar wani mara daWi na tunkaro in da suke.

Adam ya kunna motar, ya nufi gate, sai ga motar Jabir ta shigo, jabir ya tsaya dai-dai in da motar adam take ya ce "Yaa ina zaka kuma? Daga gidanka nake".

"Eh wani muhimmin abu ne ya taso mini"

Samha ta ce "Barka da rana yaya" Waga mata kai kawai yayi ba tare da ya amsa ba, ya ce wa jabir "Ka jirani da daddare, zan nemeka in sha Allah"

"Ok, dama na je na kuma yi wa turaki gaisuwa, Samha ta ce idan nan zan taho zata zo ta sake yi maka gaisuwa".

"Na gode, zan je na dawo yanzu in sha Allah".

Tun da samha ta sanya idonta a na rumaisa, ta ji wata mummunar faWuwar gaba da fargaba, kamar ta san idon rumaisa amma ta manta a ina ta santa, gashi ruman ta rufe fuskarta da facemask, ita kanta ruma ba ta san yadda aka yi ta tsare samha da ido ba, ko ?iftawa

Please Login or Register in order to submit comment