You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rusa giwa, saboda ta yi alwashin sai ba?in ciki ya kashe giwa, in dai da ranta babu wani abun alkhairi da zai sameta, babban birinta yanzu bai wuce kassara rayuwar rumaisa ba, kasancewar ita ce babbar barazanar ta.

?angaren Jamil ma, yana ta neman hanyar da zai yi magana da rumaisa, dan ya sha zuwa makarantar su, ya tarar da sidi yana tsaye yana jira, kuma alamu sun nuna babu wanda ya san adam yana zarginsa, dan haka so yake ya tutsiye rumaisa, ya ji me da me ta sani.

Baba uwani ma kullum zaman War-War take yi, a kan kar rumaisa ta tona mata asiri, dan tuni mummy tayi mata fata-fata ta sallameta.

Ammi na ta yi wa iman bayanin cewa Jabir ya ce mata, yana jira mai girma turaki ya dawo, wambai ne zai nema masa auren iman, kuma ya bata tabbacin cewa ya shawo kan hajiya Lubabatu ta amince masa ya nemi aure iman, kuma yayi mata zancen haWa lefe ta ce masa wannan maganar su ce, su yakamata su tattauna.

Iman da ke shan kunun sabayar maman Khadija, dan ba a bar ta a baya ba, har ita ake sha, dan kuwa kogi bai ?i daWi ba, ta sunkuyar da kai tana sauraren ammi, ruma kuwa tana ta game a wayar ammi, kamar ba ta san me ake faWa ba.

Ammi sai ta yi zaton kunya ce kawai irin ta iman, ya sanya ta?i magana, Nusaiba kuwa sai za?al?alewa take yi, tana tsara yadda biki zai kasance.

Sallamar hajiya Lubabatu ce, ta katse musu hirar, Ammi ta amsa su kuma duk suka bita da kallo.

Ammi ta faWaWa murmushin ta, ta saka duk abubuwan da suka faru a baya, mussaman da Jabir ya ce mata ai ta amince da aurensa da iman, dan haka cikin murna ammi ta karSeta.

Sai dai ta turSune fuska ta ce "Giwa ba zama na zo yi ba, magana zamu yi dan Allah"

Ammi ta ce "To shikenan, ko zamu shiga daga ciki ne?"

"A'a ba wani daga ciki, magana zamu yi a buWe a fai-fai. Wallahi giwa ki ji tsoron Allah, idan har kina son gamawa da duniya lafiya, mace sai tsabar son kanki a zuciyarki. Kawai kin juya mini tunanin Wa, ki rasa da wanda zaki haWa shi, sai auren ?ar tsintuwar ki, yarinyar da ki ka ce kin san iyayenta, ki ka gaza nuna su har rana mai kamar irin ta yau, kawai dan ki cuceni, wato sarauta ta bar gidanku, idan Allah ya yi jabir ya samu sarautar galadima, kin dai aura masa ita, dan ku mallake shi sai yadda ki ka yi da shi, wato kowa ya rasa, wanccan ba lafiya ce da shi ba, kin san ba sarautar zai yi ba, Mahmud kuma tun da Jamila ce ta ri?e shi, ba zaki bari abun arziki ya same shi ba, tun da ba ke yake yi wa kallon uwa ba, sai ki ka lallaSa zaki aura mata Wa na, to ba zai yiwu ba wallahi"

Ammi ta ce "Dan Allah ki yi ha?uri Lubabatu, ki fuskance ni, Jabir fa shi ya kawo kansa, ya ce yana son iman, ba ni na takura masa sai ya auri iman ba, kuma shi ne ya bani tabbacin lallai kin amince wa auren nan"

"Ni ina na san ana yi, ana ?ulla mini kitimurmura, ina Wan sarauta ina auren shegiya da aka tsinto, wallahi ?ar tsintuwa ba zata samar mini da zuriya ba, idan ba haka ba a nemo iyayenta a nuna mini"

Tuni jikin iman ya fara rawa tana kuka, rumaisa kuwa ji tayi kamar ta mari iman, ba ta da kataSus, da an yi mata abu sai kuka saboda tsabar shagwaSa.

"Lubabatu shi Wa na kowa ne, iman kuma ?ar ku ce, meyasa lallai sun kun nuna mini, iyakata ne?".

"Ba wani Wa na kowa ne, idan na kowa ne ki aurawa adam mana, ko dai sarautar ki ka ?allafawa rai, sai kin mamaye komai, wallahi Wa na yafi ?arfin auren ?ar tsintuwa, ba?in halinki ne yake bibiyar ki da yaranki".

Tuni rumaisa ta hasala ta ce "Wai jabir Win banza Jabir Win wofi, me aka yi aka yi wani Jabir munafiki da shi, ban da ?addara ta Allah, ki kalli iman ki kalli jabir Win mana, wani sololo kamar an mari Wan akuya. Wai ku baku da wani buri sai ku zo kuna zagin ammi, me tayi muku?".

"Ke rufe mini baki, ko na zo na talitseki, ?ar matsiyata ban saka da ke ba, sa'arki ce ni?"

Ruma ta ce "Wallahi talitseni, dai-dai yake da taka kan Wan maciji, baku da magana sai ta sarauta, fir'auna ma ya mutu ya bar mulki, dan abun kunya, mijinki na can na jinya, ke da Wan ki kuna nan kuna fafutuka a kan wata sarauta, wannan ne abun alfahari dan za a aure shi? Idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, wallahi jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, ai ni idan mutum babban banza ne, bana ganin girmansa, tun ranar da muka je gidanki, ki ka ci mini mutunci nake ?ullace da ke"

Ammi jikinta har rawa yake, ta ce "Rumaisa ya isa haka, ku tashi ku shiga ciki" dan ammi ba ta taSa ganin ruma tana asalin tijara ba sai yau.

Laila ta ?araso falo ta ce "Ammi su shiga ciki su je ina? Rumaisa kin yi mini dai-dai, ai asara na ga matar da ta wofantar da mijin da ya gatantata lokacin yana da lafiya, yana ?asar waje yana jinya, tana nan tana shirme a gari, ita da Wan ta mara tarbiyya.
?ar wahala, tun da na sanki Lubabatu baki da al?ibla daga ke har Mummy, shiyasa rayuwa ta ?i yi muku yadda ku ke so, kuma albarkar Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da al?ur'ani, cigaba yanzu muka fara"

Ruma ta ce "Kuma in sha Allah, sai na dawowa da ammi Mahmud"

Laila ta ce "Dan Allah malama kwashi banzayen ?afafuwan ki, da aka saba bin bokaye, a bar mana part, kar a zuba mana masifa".

Hajiya Lubabatu ta nuna kanta ta ce "Laila har da su kaza a cin dan?o, ni ?ar ri?o za ta gayawa magana haka".

"?warai ?ar ri?o ba, ko nima zaki ce mini shegiyar ne? Ke sa'a fa ki ka ci, Jabir yana girmamani, da wallahi ashar zan WuWWura miki, zaki iya fita"

Su biyun duk suka ?ureta da ido, ba wanda ya fi Sata mata rai, irin cin mutuncin da rumaisa ta yi mata.

"Giwa a gabanki sirikarki suka ci mini tuwo ko, duk saboda wannan yarinyar, na faWa ba zan bari Wa na ya auri wannan yarinyar ba, da ban san asalinta ba, wanda ba na raba Waya biyu, ?ar gaba da fatiha ce, kuma zaku ga abun da zai biyo baya" ta fice tana huci.

Bayan fitarta, Ammi ta kalli laila ta ce "Laila mey....."

"A'a Ammi, daga ni har rumaisa ba wanda yayi laifi, nima fa ba son aurenta da jabir Win nan nake yi ba, saboda duk wani abu da ya shafi mummy, bana ?aunarsa na tsani matar nan kamar yadda na tsani mutuwata, ke kuma iman, idan aka kuma zuwa ana gaya miki magana, ki ka Sare baki kina kuka, ubanki zan ci, sokuwa kawai komai kuka, bayan kin san larurar da ki ke Wauke da ita".

Jikin Nusaiba duk yayi sanyi, ita dai tana yi wa iman sha'awar auren jabir, amma halin mahaifiyarsa ne sai a hankali, kuma wani point da ruma ta kawo abun dubawa ne, mutumin da mahaifinsa yake ?asar waje yana jinya, an bar shi shikaWai sai mai kula da shi, tilon Wan sa namiji kuma yana nan yana gararambarsa.

Sai dai ba a fi mintuna arba'in, da tafiyarta ba, wambai ya kira ammi a waya.

Suka gaisa, gabanta na faWuwa, ko wani abun hajiya Lubabatu ta je ta kitsa masa, sai dai ta ji ya ce mata "Mun yi magana da jabir galadima, idan turaki ya dawo, zuwa ranar lahadi idan Allah ya kai rai, zamu kai kuWin auren yarinyar wurinki iman wurinsa, ya ce mini kun gama magana, zamu sanya watanni biyu ne kawai auren"

Gaba Waya sai ta ji ya Waureta ta da jijiyoyin jikinta, ammi ta ce "To ranka ya daWe, Allah ya tabbatar mana da alkhairi"

Laila ta ce "Lallai ma jabir munafuki ne, yana sane da uwarsa ba ta so, amma yake maganar kai kuWi? Kodayake hakan shine dai-dai, ta auri jabir Win, mu ga ta tsiya, Allah ya tabbatar da alkhairi, ai Allah ya fi su"

Ammi ta ce "Subhanallah, Allah ya kawo mini ?arshen wannan fitintinu, ni abubuwan ma sun isheni, Addu'a dai nake tayi, Allah ya shiga lamarin nan, bai kamata a hukunta jabir, da laifin mahaifiyarsa ba, tun da shi mutumin kirki ne".

Ruma ko sunan jabir ba ta son ji, dan haka ta bar falon gaba Waya, ita zaman gidan duk ya isheta, gida kullum cikin tashin hankali da bala'i, an saka mutum Waya a gaba da masifa.

Harabar gidan ta fita shan iska, tana ta zazzagawa, tana kallon fulawoyi, ga sanyin la'asar, yanayin yayi mata daWi sosai.

Daga sashin Mummy ta hango jamil, ta tsaya tana kallon sa, su kullum suna gidan nan, kodayake ba abun mamaki bane ba, tun da ?an uwa ne, amma ita a wurinta duk wanda ya fiye zuwa wurin Mummy ba shi da gaskiya.

Ga mamakinta taga yana tunkarota, dan haka ta haWe rai zata juya ta tafi, ya cimmata da sauri ya ce "?an tsaya mana, yau Allah ya sa mun haWu, magana zamu yi"

Ta ?are masa kallo ta ce "Maganar me?"

"Magana a kan abun da ki ka cewa mjinki na kina zargina da kisan Aisha"

Ruma ta ce "Ba rami meya kawo rami,? Ni ban ce ka kashe anty aisha ba, kuma da mijina ku ke magana ba ni ba, dan haka babu ruwanka da ni"

"Amma ko menene ke ki ka kitsa misa, daga auroki ?ar mitsitsiya da ke, kin rikita mana zaman lafiya family"

"Dama can ba zaman Allah da annabi ku ke yi ba, kuma na faWa Win, idan kana da gaskiya, maiyasa a da baku damu da anty aisha ba, sai yanzu kake damun baban sabir, wata?ila ma da kai ake haWa baki ake Sata masa suna"

Jamil ya ce "Kin san me ki ke faWa kuwa?"

"Malam danginmu babu mahaukaci, ban yi gadonsa ba, kuma babu ?an shaye-shaye"

Jamil ya ce "Ni fa jami'in tsaro ne, zan iya amfani da kakina wurin ladabtar da ke, da tursasaki a kan kiyi bayanin abun da ki ke Soyewa".

"To meya hanaka yin hakan tuntuni? Ka yi mana, amma ka sani na san da batun saka sunan anty aisha, a matsayin magajiya da mai girma turaki ya yi, a kan filin sa, da wani kamfani da haWin gwamnatin tarayya suka karSa jingina, ake amfani da shi, ana bashi wani kaso, na kuWi, wanda kai tsaye yake shiga asusun anty aisha. Ka ga idan baka kiyayeni ba, zaka tsinci talatarka a laraba"

"Wa..ww..waye ya gaya miki wannan maganar? Kenan adam saboda wannan maganar, ya fara tunanin Wora zargin sace matarsa a kaina?"

Rumaisa ta ce "Kai ma kenan saboda ka wanke kanka daga zargi, ya sanya ka ?ir?iri cewa ya kashe matarsa yayi tsafi da gangar jikinta?"

Mamakin rumaisa ne ya mamaye shi, ya ce "Kuma aka ce miki ni ne na yaWa wannan maganar? Me ki ke nufi ne?"

Ruma ta yi murmushi ta ce "Ba ina nufin kai ne ba, kawai na yi tunanin, kowaye ya saka aka sace anty aisha, shi ne ya yi wa mijina sharri, ni ba ?ar sanda ba ce ba, amma ?ar baiwa ce, garkuwa da aka yi da anty aisha shiri ne, kuma idan ba ka da hannu, kar ka damu kanka, sai dai ita rayuwa, iyawa ce, abu ?ailalan zaka yi, ya jefeka cikin masifa a gaba, har ?arshen rayuwarka, ka sani iya wuya ina bayan mijina, kuma kar ka sake tunkarata da wannan maganar"

Dafe kai Jamil yayi, ya ja da baya,gaba Waya ya ma rasa ta ina zai fassara maganganun rumaisa ne? Ta hargitsa masa zance cikin zance wace irin yarinya ce ne haka? Kamar ana controlling Win ?wa?walwarta da remote?.

Lokacin da rumaisa ke daf da shiga sashin ammi, taga laila ta fito da sauri, ta yi wa sidi magana, akan ya kawo mota, zasu tafi asibiti iman ta suma.

Da gudu ruma ta shiga sashin ammin, iman na kwance a in da ta barta Wazu tana bacci, ashe daga haka ta suma, ammi na ta magana amma shiru.

A gaggauce suka Wauketa, tuni ammi zuciyarta ta karaya, saboda yadda jikin iman ya saki, kuma Ammi ta Wora alhakin hakan a kan hajiya Lubabatu, da ta zo ta yi mata wannan cin mutuncin.

Ammi ta ce Rumaisa da Nusaiba su zauna a gida, ita da laila suka tafi kai iman asibiti.

Rumaisa ta kasa zaune ta kasa tsaye, lokaci lokaci ta din ga jan uban tsaki ta ce "Allah ya tsinewa babar jabir Win nan, da bata san darajar Wan Adam ba, daga ita har shi wawan jabir Win, mara zuciya"

Nusaiba ta ce "Ya zaki din ga zaginsa, shikuma me yayi miki?"

"Ba ruwanki da ni, ai naga take-takenki, ke kike goya masa baya, ke ki aure shi mana" duk da Nusaiba ta girmi rumaisa sosai, dan ta girmi iman ma, amma haka tayi shiru ta kasa magana.

Sai dare laila ta dawo, suka tashi gaba Waya suna tambayar laila ya jikin iman Win.

Laila jiki a sanyaye ta ce "Da sau?i, sai dai jini ya hau, zuciyar ta kumbura, amma ta farfaWo ta samu bacci."

Ruma ta ce "Anty laila dan Allah a fasa auren nan mana, ko dan ceto rayuwarta"

"Ai ni zan fi so yi auren nan, dan nuna mata iyakarta, kuma magana tun da ta riga ta je gaban wambai, rusata ba abu ne mai sau?i ba, mutumin nan ba ayi masa wasa".

Rumaisa ta rasa abun sa yake yi mata daWi, ji take kamar ita ce a halin da iman take ciki.
Nusaiba ce ta shirya, ta tafi asibitin, dan taya Ammi kwana da iman.

Yau sai ga rumaisa da tashi cikin dare tana sallar dare, tana yi wa iman da yayanta addu'a, idan da alkhairi Allah ya sa mai sunan baba ya auri Iman. Dan ta san mai sunan baba, akwai zafi, amma mutum ne mai kyautatawa da tausayi, kuma ba ta taSa ganin abun da ya damu da shi sosai bayan ita da mama ba sai iman.

Da gari ya waye, laila da rumaisa suka je duba iman, suka kai musu abinci.

Iman ta farfaWo, amma ta yi pretending, bacci take yi, saboda ba ta son magana, dan numfashinta sama-sama take yin sa.

Ammi da Nusaiba suka koma gida, an yi sa'a ruma da anty laila an Wan fara shiri, sannan laila ta sarawa tsagerancin rumaisa, mussaman jiya, da ga tsigalewa hajiya Lubabatu.

Wayar iman na hannun rumaisa, dan yanzu wayar kamar ta su ce su biyu.

Rumaisa ta kira mama ta ce "Mama dan Allah ki zo ki duba iman, ba ta da lafiya muna asibiti"

Mama a duk lokacin da ta ji an ce iman ba ta da lafiya, hankalinta yana tashi, mussaman da ciwonta yake mai hatsari.

Bayan ta gama wayar ta dubi laila ta ce "Anty laila".

"Na'am".

"Wai yaushe zan yi video call da papa ne?".

Laila ta ce "Sai lokacin da ki ka fara bin umarnina"

"Anty laila dan Allah, so nake na ganshi"

"Kin fiye taurin kai ne, sai lokacin da ki ka fara yarda zaki yi abun da nace miki ba gardama"

"To me ki ke so na yi?"

Ta ce "Ba wannan ba ma, so nake mu bashi mamaki, sai kin fi haka kyau da cika, ke baki ga yadda jikinki ya fara yi ba ne"

Ruma ta ce "Na gani, kullum idan na je wanka ina dubawa, idan sun fara girma".

Laila ta yi dariya ta ce "Ashe dai kina son su fito".

"Wallahi ina so"

"To ki mayar da hankali da cigaba da shan kununki, bayan sabayar maman Khadija ma, akwai maganin maman ilham, shi kuma a iya fito da nono yake aiki, baya sanya ?iba, haWinta haWi ne mai kyau Wan mambila ita ma.
Rumaisa daga lokacin da mace tayi aure, zama bai ganta ba, shekaruna a ?alla talatin da huWu, amma kalleni kamar ?ar ashirin da biyar.
Bana zama, abu ba sai ya lalace ake gyara shi ba, garkuwa ake yi kafin ya faru, nan gaba kina haihuwa kina shayarwa, dole zasu ran?wafa ko su zube, amma idan ki ka tattala su, ki ka kula da su, tsaf zaki yi ta haife-haifenki, ba tare da kin sirewa miji ba.
Kuma ba ina nufin ki je ki sai abun da baki san menene ba ki sha, ba haka nake nufi ba, duk abun da na baki kiyi amfani da shi, na san kyansa da ingancinsa, kuma na san da me aka yi shi.
Kin ga maman Khadija na ta haWin kunu ne na sabaya, da yake gyara jiki, ya sanya ?iba da gyara fata, kuma kowa na iya sha.
Ita kuma maganin maman ilham, akwai matan da suna da ?iba, basa bu?atar yin ?ibar, gyaran nonon kawai suke so, ita maganinta haWe-haWe ne, na natural abubuwa, ba shi da side effect kayanmu ne na islamic da saiwoyi masu kyau, ake kawo mata daga mambila ta haWa.
Ya ki ke gani, idan mutum ya haWa garin kunun sabayar maman Khadija, da kuma maganin gyaran nono na maman ilham?
Rumaisa ita mace ba ta zama ba gyara, dan haka so nake ki cika kiyi kyau, kan dawowar takawa".

Ruma ta yi shiru sannan ta ce "Ni fa na zata kawai amfaninsu a shayar da Wa, ashe mutum gori ake yi masa idan bashi da su"

Laila ta ce "Sosai makuwa, shiyasa ake son gyarawar ai, kuma gori ba iya na mata ba, har na miji, wanda ya fi kowanne takaici ba, miji yayi miki gori dan baki da su, ko kin bari sun lalace"

Ruma ta sake gyara zama ta ce "To ita ma na maman ilham Win zaki sai mini?"

"Eh mana, mai ze hana? Ki din ga biyayya kawai, mun gama magana da ita ma".

Cikin farinciki ta ce "Allah ya sa su fito kan papa ya dawo, kin san me? ce mini fa yake, wai nasa yafi nawa girma, wai nawa kamar girman wake, daga baya kuma wai kamar murfin jarkar faro".

?yal?yalewa da dariya laila ta yi ta ce "Rabu da shi, kan ya dawo zai sha mamaki, sai ki rama. Ai tun da akwai kunun maman Khadija, da kuma haWin maman ilham, an wuce wurin, kin wuce gori mutuniyar".

"Allah ya sa anty laila, to zasu kai kamar na samha? Su Fauziyar nan, wai a dubi samha ta fini komai amma ya aureni, idan nawa suka fi nata, ai ba zai aureta ba ko?"

Laila ta ce "Wannan kuma effort Winki ne zai sanya, ya aureta ko ya fasa"

*INA MASU SON WUCE GORIN KISHIYA, DA NA MIJI, KAI HAR MA DA NA ?AN UWANKI MATA, TO KU GARZAYA KU GWADA KUNUN SABAYAR MAMAN KHADIJAH DA KE ZAUNE A ZARIYA, BAYAN FEDERAL PALLADAN ZARIYA 08033411249, KU TUNTU?ETA KAI TSAYE TA LAMBAR WAYARTA*
*HAKA ZALIKA KU HA?A DA MAGANIN MAMAN ILHAM MAI TULA-TULA, MAGANINTA INGANTACCE NE, WURIN BIYAN BU?ATUNKU, BA TARE DA CUTAR DA LAFIYARKU BA, KU TUNTU?ETA TA LAMBAR WAYARTA 0813 561 3021 TANA NAN A KAWO ROAD KADUNA*
*HAJIYATA KAR KI BARI MATA SU SHA GABANKI, SU RIGAKI MALLAKAR MAGANIN MAMAN ILHAM, DA NA MAMAN KHADIJAH, MACE SAI DA GYARA, SUNA TURA KAYANSU KO INA A FA?IN A NIGERIA, HAR MA DA ?ASASHEN DA MUKE MA?WABTAKA DA SU*

Bayan sallar azahar, mama ta je ta duba iman, jikin da sau?i, amma dai tana jin jiki sosai.
Laila kuwa mama ce ta burgeta, saboda yadda take komai nata a nutse, gashi tun da tazo, rumaisa ke tsokanarta take son sakata magana, saboda kamar kakarta ta mayar da ita.

Mai sunan baba ya dawo daga kasuwa, ya tarar mama bata nan, abun da yafi komai Sata masa rai kenan, dan haka ko abinci ya?i ci, ya koma ?ofar gida ya zauna.

Ya kai awa guda da rabi sannan mama ta dawo.

Mama kamar ?a da uba, a wajen ta fara yi masa bayani, dan ta san ba shi ba, hatta sauran ?a?anta, ba sa son su dawo su ga bata nan, amma na sa yafi yawa.

"?anwar mijin rumaisa aka kwantar a asibiti na je dubata, daga nan na wuce mandawari na sada zumunci da ?an uwana"

"Wacce daga ciki?"

Mama ta ce "Wadda ka ke tsoratawa mana, iman, ciwonta ne ya tashi, ban ma tarar da hajiyar ba, sai wannan yarinyar, da wata yayar mijin rumaisan".

"To ya jikin nata?"

"Jiki Alhamdilillah, amma dai har na taho bata buWe ido ba"

Mama ta Wan yi shiru tana nazarin mai sunan baba, sannan ta shiga gida.

Mama na shiga gida, umar ya ciro wayarsa ba tunanin komai ya kira wayar Iman.

Sai dai rumaisa ta Wauki wayar.

"Ina me wayar?".

"Mai sunan baba muna asibiti fa, ba ta da lafiya, ba ta tashi ba haryanzu"

Ya katse wayar ya tashi, duk da yunwar da yake ji, ya shiga gida yayi alwalar magariba ya fito.
Ya gama yanke koma menene, yau sai ya je ya ga jikinta, dan gaba Waya hankalinsa ya tashi.

Bayan kowa ya tafi, ya rage daga iman sai nusaiba, laila ta ce za ta je gida tayi wanka ta dawo, ba sai ammi ta kwana a asibitin ba, su kwana ita da iman da Nusaiba.

Tun kan ya shigo, gabanta ya tsananta faWuwa, ba tare da ta san dalilin hakan ba, sai dai ba tare da tayi tsammani ba, ta ji an murWa ?ofar yayi sallama.

Da sauri iman ta fara kiciniyar neman hularta, dan kanta ko Wan kwali babu, ba ta taSa zaton mai sunan baba, ko da wasa.

Nusaiba ta ce masa "Ina wuni"

Ya amsa mata a ta?aice kamar yadda ya saba.

Ba tare da fargabar komai ba, ya je gaban gadon, ya zauna a kan kujerar da ke gaban gadon.

Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "Yaya umar ina wuni"

"Ban ganshi ba" ya bata amsa. Kamar yadda yayi tsammanni, ta Wago ta kalleshi, ta mayar da kai ta sunkuyar.

Ya waiwaya ya kalli nusaiba ya ce "Can you excuse us?" Ba musu Nusaiba ta tashi ta fita.

Mai sunan baba ya kalli iman ya ce "Meya sameki?" Yayi maganar kamar Wan sanda na tuhumar mai laifi.

"Bani da lafiya"

Jin shiru bai ce komai ba, ya sanya ta sake Wagowa, ya zuba mata ido, yana jiran ta bashi amsa, dan wadda ta bashi ba ta gamshe shi ba.

"Zuciyata ce take kumbura"

"Meyasa?"

"Nima ban sani ba"

Ya ce "Kin sani"

Shiru ta yi tana wasa da yatsunta.

Ya ce "Well, Allah ya sauwwa?e, kin san condition Winki, bai kamata ki din ga wasa da lafiyarki ba, and na ji rumaisa ta ce You are getting engaged very soon, Allah ya sanya alkhairi"

Kawai ta fashe da kuka, yayi ?uri da ido yana kallon ta, dan bai san me zai ce mata ba.

Tayi me isarta, sannan ya ce "Auren ne ba kya so?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Meyasa ki kai shi gidanku, idan ba kya son shi?"

Iman ba ta san ya aka yi ta tsinci kanta da yi wa mai sunan baba bayani ba "Bana son shi, mamansa ta ce ba zai auri wadda ba ta da asali ba, gashi ya riga ya kai maganar wurin wambai"

"Idan ba kya son shi, wa ki ke so?"

?agowa ta yi a hankali, suka haWa ido, jikinta yayi sanyi yayin da mai sunan baba yaji tsigar jikinsa tana tashi.

"Kuka ba ya maganin matsala, Addu'a ce magani, Allah na iya canza komai within seconds"

A sanyaye ta ce "Labarina ba zai canza ba yaya umar, yarinya ?ar tsintuwa"

Ya mi?e tsaye ya ce "Zai canza, put your trust on Allah, Allah Ya ?ara lafiya" tabi bayansa da kallo, wata irin ?aunarsa na ratsa zuciyarta.

Yayin da shi ma yake jin matsananciyar soyayyarta da tausayinta a nasa ran, ji yake tamkar kar ya tafi, sai ta samu cikakkiyar nutsuwa ta kwantar da hankalinta.

Yana daf da kaiwa ?ofa, Jabir ya buWe ya shigo.

Ayshercool
08081012143


Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please =?O?



Kallon-kallo suka shiga yi, tsakanin shi da umar, sai dai babu alamar mai sunan baba zai bashi hanya, sai jabir ne ya kauce masa ya bashi hanya.
Mai sunan baba

Please Login or Register in order to submit comment