You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi da abokansa sun dawo daga idi, ko gida ba su zo ba, ya zauna an fito da abinci sun haWu suna ci, kuma kin hana hakan"

Ajiyar zuciya ya yi, yana hamdala da ba wancan zancen ta yi ba.

Mama ta ce "To wannan abun ne ki ke ta zuzutawa, ai shima ya zo ya Wau abinci ya fita da shi sun ci tare"

"To mama sai aka ce ya je ya zauna a ?ofar gida yana cin abinci ai rashin kamun kai ne, kuma ke ki ka ce rashin kamun kai ne fa".

Mama ta ce "To shikenan, za a yi masa faWa".

"To mama kiyi masa faWan mana yanzu"

A fusace ya ce "Ke wai ni sa'an ki ne?"

Umar ya ce "Maganinku kenan da ku ke wasa da ita"

Can ta sake gyara zama ta kalli mama ta ce "Mama, kin san wani abu?"

"Ke na gaji da wannan shirmen naki fa" mama ta faWa cikin ?osawa.

"Mama ba shirme zan ba, Wazu na ga Habiba a masallacin idi, da tsofaffin kaya na ganta".

"To ina ruwanki? Kin ga ina rabaki da sabgar munafurci amma ba zaki dai na ba ko?"

Jiki a sanyaye ruma ta girgiza kai ta ce "Mama so nake a bata kaya Waya a cikin kayana" gaba Waya juyowa suka yi suna kallon ta jin abin da ta ce.

Huzaifa ya ce "Kina da hankali kuwa?"

"Amma dai ka san tun da nake ni ba mahaukaciya ba ce ko? Mama dan Allah a bata ita ma ta saka sabon kaya"

"Rufewa mutane baki, mara zuciya nan babarta ta zo ta ciwa mutane mutunci, amma ki ka cigaba da shishshige mata, ba za a bayar ba Win" Aliyu ya faWa yana zaro ido.

Mama ta girgiza masa kai, ta dubi ruma ta ce "Allah ya kaimu gobe, sai ki zaSi wanda zaki batan"

Murmushi ruma ta yi ta ce "Na gode mama, Allah ya saka da alkhairi, to zaki Wan zuba mini naman kazar ita ma na kai mata ta ci, na san su basu yanka kaza ba".

Yasir ya ce "Dama ta yaya zasu yanka, wannan babar ta su tana kiwon kaji kamar su kasheta, amma ba zata yanka su ci ba, bayan talauci har da son zuciya"

"Ka daina zagar mini babar ?awa dan Allah"

Mama ta ce "Kin ga, tashi ki wuce ki je ki kwanta"
Ta mi?e ta shige Waki, mama ta mayar da idonta kan Aliyu ta ce "Aliyu, kar ku hora yarinyar nan a kan halin rowa, duk rashin jin ta tana da tausayi da son taimako, idan har abin da za ta yi bai saSawa shari'a ba ku ?yaleta"

Aliyu ya jinjina kai. Ruma kuwa ji take kamar ta janyo washegari, ta kai wa habiba wannan kayan, ita ma ta saka ta ji daWi.

Washegari da wuri ruma ta yi wanka, ta yi kwalliyar salla da Waya daga cikin kayanta, ta zauna ta Waukarwa Habiba set Waya na atamfa har da ribbon da abin hannu.
Mama bata hanata ba, ta ?ulle mata nama ta bata ta kai wa Habiban.
Har zata Wauka ta fita, ta tsaya ta ce "Mama, dan Allah idan ta yi kwalliyar zamu je gidan 'yan ajinmu mu yi wasa".

Mama ta Wan Sata fuska ta ce "Amma dai kin san babna son wannan abun ko, ba na son yawace-yawace"

Ta Wan marairaice ta ce "Dan Allah mama, kin san bana yawo, daga aike sai makaranta, yanzu fa salla ce".

"Shikenan, na ji, saura kuma ki je ki zauna sai an nemo ki, ina da ina zaku je?"

Ruma ta lissafa mata, mama ta yi ajiyar zuciya ta ce"Yanzu ?arfe goma da rabi, kar ki wuce sha biyu, idan ki ka wuce abin da zai zo biyo baya ba zai yi miki daWi ba".

Cikin murna ta ce "Mama da wuri zan dawo in sha Allah " ta yi waje ta na murmushi.

Kai tsaye gidansu Habiba ta nufa, ko da ta je ta yi ta sallama, shiru ba a amsa ba.
Tsayawa ta yi a tsakar gidan ta cigaba da sallama.
Sani ne ya le?o yana amsawa, yana ganin ruma yayi saroro ya ce "Ke uban me ki ka zo yi mana a gida?"

Hararsa ta yi ta ce "To ina ruwanka ai ba wurinka na zo ba, ba yayana yayi maka tsakani da ni ba, babu ni babu ba, ko kuma na kira shi, ya zo ya ?ara kumbura maka fuska"

Tana tsaka da maganar, sai ga babar Habiba ta fito daga banWaki, tana ganin ruma ta tsuke fuska ta ce"Ke me ki ka zo yi mini a gida?"

"Gurin Habiba na zo"

"Da izinin wa ki ka zo wurin Habiban?"

Habiba ce ta fito daga Waki, hannunta ri?e da kwanon tuwo da miyar kuka, tana ganin ruma ta ce "Laaa ruma, kin dai na zuwa makarantar allo "

Ruma ta ce "Ba na ganki a masallacin idi ba ki ka ?i kulani"

Habiba ta ce "Wallahi ruma ban ganki bane ba? Ya salla?"

"Lafiya lau, wurin ki na zo, zo ki ji?"

Mamaki ya cika babar su Habiba, ta ri?e haSa ta ce "Habiba, wato cigaba da shiga sabgar yarinyar nan ki ka yi ko?"

Habiba ta girgiza kai ta ce "Wallahi Ummanmu ba kulata nake yi ba, na daWe ma bamu haWu ba".

Ruma ta mi?owa Habiba leda ta ce "Kawo miki na yi, ki zo ki karSa ki gani"
Babu musu ta ?arasa ta karSi ledar, taga Winkakkiyar atamfa ga abin hannu da ribbon, sai kuma ?ullin nama.

Habiba ta ce "Ruma wannan na waye?"

"Naki ne, in gaya miki, kayan salla na? kala goma sha biyu da hijjabai, har da abin hannu da sar?a, shine na ce bari na kawo miki Waya, ki saka mu je yawon salla".

Babar su Habiba ta ce "Ba ta so ba zata karSa ba, bana son shishshigi, ba ta kayanta ce muku aka yi tana bu?ata? Ita ma tana da kayan salla"

Idon Habiba ya cika da hawaye ta ce "Wallahi Umma bani da kayan salla, ina son kayan dan Allah ki bar ni na saka".

Ruma ta ce "Dan Allah Umma ki bari ta saka, mun shirya ai mun dai na faWa, dan Allah ki bari ta saka"

Umma ta kalli yadda Habiba ta rungume kaya tana kuka, wai tana so, haka ta ?yaleta. Habiba ta shiga Waki ta saka kayan, aikuwa tamkar dan ita aka Winka su suka yi mata kyau.
Sani ya din ga ce wa habiba mara zuciya.

Abin ka da ?uruciya, tuni habiba ta shirya a cikin kayan, duk da babar Habiba na jin haushin ruma, hakan bai hanata rawar jiki wurin raba naman kazar da ruma ta kawo ba, fan kuwa an daWe ba a haWu ba.
Daga haka suka fita nasu yawo.

Tamkar awakai haka suka dinga yawo, kusfa kusfa gidajen ?awayensu, wasu a haWu a rabu da su ?alau, wasu kuma a ?are da faWa. Ruma ba ta tashi tuna kashedin mama ba, sai bayan azahar tana ta gararanbarta a gari.

A suwkane ta nufo gida, tana ta tunanin yadda za ta kare kanta a wurin mama, dan ta san zuwa yanzu ana can ana nemanta kamar kuWin guziri.

Yaya Usman ta hango a tsaye a jikin wata mota, ya sha kwalliya, shi da abokansa, da alama fita za su yi.
Da gudu ta ?arasa in da yake tsaye ta ce "Yaya ussy, me ka ke yi a nan?"

"Ban sani ba, wuce ki tafi gida, ki kai aiken da aka yi miki" abin da ya faWa ne ya sanya ta fuskanci kamar mama ba ta neme ta ba, dan haka ta ce "Dan Allah ina zaka?".

"Zamu Wan fita chilling ne"

"Meye chilling kuma?"

Ya haWe rai ya ce "Cewa na yi fa ki tafi gida ko?"

"Dan Allah ka yi ha?uri, zan bika dan Allah"

"Ke wai ni sa'an wasanki ne? Ba zaki wuce ki tafi gida ba?"

Ta sake marairaice wa ta ce "Dan Allah Yaya"

Ri?e rigarsa tayi tana kallonsa kamar za ta yi kuka. Tunawa ya yi da haushin ?in tafiya da ita zai iya sanyawa ta tona masa asiri.

Yayi ?asa da murya ya ce "To ki je ki tambayo mama, idan ta yarda sai mu tafi"

"Wallahi na san idan na tafi, tafiya zaka yi"

"Shegiya sai ka ce mayya, idan na tafi da ke a ina zan saka ki motar ba space" yayi maganar a ?ule.

"Sai na zauna a cinyarka" duk yadda ya so ya yakice ruma, ta?i ta nace, gashi ya san zai sha kunya, idan har ruma ta tona masa asirin yana waya da budurwa, dan ya san sai dai ya kasheta bayan ta faWa zare idonsa ba zai hanata faWar abin da ta yi niyya ba.

Haka ya sakata a motar, dama ta abokinsu ce, ita kaWai a cikin maza, sai zaginta yake, amma ko a jikinta, ya sakata a gefensa.

Abokansa sai dariya suke masa, suna "Ka ga ?anwar maza, suke mulkin amma dole a biki ko ba a so" ba wanda ta kula a cikinsu suka tafi.

Wurin sha?atawa suka je, duk abin da suka ci sai da suka sayawa ruma ita ma ta ci, da ta ji ta ?oshi ta kalli Usman ta ce "Yaya ussy, a samo leda a Waure mini sauran na tafi da shi gida"

"Saboda kowa ma bashi da hankali kamar ke? Wallahi baki isa ba" ba dan ya ji daWin fitar ba, ya azalzali abokansa suka koma gida, saboda yadda ruman ke ta zubar masa da mutunci a idon abokansa.

Ko da suka je gida, mama a kiWime take, tun sha biyu ake nemanta ba a ganta ba.

Bin su da kallo mama ta yi, ta dubi Usman ta ce "A ina ka ganota?"

"Nima a hanya na ganta bayan la'asar, zamu fita da abokaina, ta nace sai ta bini, na kira Aliyu a waya na gaya masa muka tafi da ita".

"Ku ka je ina?"

"Wurin wani cin abinci ne, ni da su Isma'il ne"

"Kuma ita kaWai a cikin maza Usman, ka san tun yaushe yarinyar nan ba ta gidan nan, ka ga tashin hankalin da na shiga kuwa? Wallahi yau sai kin ci ubanki"
Abdallah ya ce "Wallahi mama ko ba ki daketa ba, sai na zaneta yau, ki yi mata bugun shekararriyar dawa, yarinyar nan ta ci a bata gado a Asibitin mahaukata".
Mama a tsananin fusace ta janyo ruma, ta din ga turjewa tana ihu, mama ta zaro bulugari ta dinga bugunta da shi tana kurma ihu tana neman taimako.

Mama ba ta saba tarbiyya da duka ba, amma idan ta kai bango jikin mutum yana gaya masa, sai da Usman ya ?waci ruma da ?yar a hannun mama.

Tun daga ranar, mama ta ce ba zata bata sauran kayan sallar baz gashi an aiko mata da kayan salla daga can garin su, ga dangin mahaifin su ma, sun Winko mata kaya, sun aiko mata da su, duk mama ta ce ba zata sake sakawa ba ta gama kwalliyar salla.
Washegari ta na ji ta na gani mama ta shirya, ta tafi cikin gari, ta bar ruma a gida.

Gidan duk ya yi mata babu daWi, sai faWace-faWace take da su Yasir.
Suka gama suka fice suka bar ta a gidan. Ta ji babu daWi rashin tafiya da ita da mama ba ta yi ba, gaji da zama ta tashi tana neman abun yi.
?akin 'yan mazan ta shiga, ta fara gyara musu ta ci karo da shaddar yaya Umar ya sa?aleta.
Wani tunani ta yi, ta kwaso shaddar ta fito da ita tsakar gida. Ta zuba ruwa a bokiti ta tuttula omo ta zunduma shaddar nan a ciki, ta koma ta cigaba aikin gyaran Wakin.
A ?alla shaddar nan ta kai awa biyu a ruwa, ruma ta fito ta jagwalgwala ta shanya. Ai kuwa shaddar nan gaba Waya ta daina wannan shining Win da take yi saboda azabar omo.

Aka jima, ya haWa wuta a dutsen guga, ta hau goge masa ita.

Abdallah ne ya dawo, ya tarar da ruma ta du?ufa tana guga.
Ya tsaya yana ?o?arin gane me take gogewa.

"Wai meye wannan ki ke gogewa haka?"

Ta Wago ta kalleshi ta ce "Kayan yaya Umar ne, na ga ya sa?ale su a Waki, na san wankewa zai yi, shi ne na wanke masa nake goge masa".

Abdallah ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ruma da me ki ka wanke shaddar nan haka?"

"To za ayi wanki ba da ruwa da omo bane?"

"Uban waye ya ce miki ana wanke shadda da omo?" Ai suna cikin maganar ruma ta ?one gaban rigar.

Dafe kai ta yi ta ce "Innalillahi, na shiga uku, Abdallah ya zan yi na ?ona masa shadda?"

Abdallah ya ce "Maganinki shegen karambani, kya san mai zaki gaya masa"

Hannu ruma ta Wora a ka ta dinga kuka, dan ta san yau kashinta ya bushe, sai yadda Allah ya yi da ita.

Haka mama ta dawo ta tarar da ita, tana ta uban kuka, Abdallah ya gaya mata abin da ta aikata.

Cikin kuka ruma ta ce "Dan Allah mama ki bashi ha?uri, yau na san na mutu wallahi, dan Allah mama kar ki bari ya dakeni ko ya saka ni punishing".

"Ba ruwana, ai nima ba jin maganata ki ke yi ba".

Abu kamar wasa, har bayan la'asar ruma ba ta ci ko Abincin rana ba, sai kuka take yi.

Huzaifa ya ce "Ni ne mutum na farko da zai sanar da mai sunan Baba wannan taSargaza da ki ka aikata masa"

Duk da mama a ?ule take da ita a kan laifin da ta yi mata jiya, amma hakan bai hanata saka ruma ta ci abinci ba, amma ruma ta?i ci sai aikin kuka. Ita kanta mama na tausayawa ruma hukuncin da zata fuskanta a wurin Umar idan ya dawo ya tarar da Sarna da ta aikata masa, sai dai ita ta janyo kanta, rashin jin ta ya yi yawa.

Mai sunan Baba bai dawo ba sai bayan sallar magariba, tun da ya shigo ta sake takurewa tana uban kuka.
Ya dube ta, cikin kakkausar muryarsa ya ce "Kukan me ki ke yi?"

Huzaifa ya gyara zama, ya wassafa masa Sarnar da ta aikata.
Duk da babu isasshen haske a tsakar gidan, ta tsorata da kallon da ya yi mata.

"Dan Allah yaya ka yi ha?uri, ba a son raina na aikata hakan ba, wallahi kawai niyyata na baka mamaki, na wanke maka na goge maka ban san haka abin zai zama ba"

Kalmar ta bashi mamaki sai da ta saka Aliyu dariya, ya ce "Lallai kin bashi mamaki kam"

Yadda ta firgice ne, ya sanya Yasir ya ce "Dan Allah yaya ka ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yi ha?uri, kuskure ne, tun da tsautsayin nan ya faru ba ta ci Abinci ba"

"Zaka Wau hukuncin da zan yi mata kenan?" Yayi maganar ba tare da ya kalli Yasir ba.

Yasir ya ce "Eh ni ka hukunta ni a madadinta, a tsorace take"

A Wan tsawace ya ce "Tashi ki Wauko mini kayan na gani"

Sumi-sumi ta tashi ta je ta Wauko kayan, ta mi?a masa.
Ya karSa ya duba, gaba Waya kayan sun tashi daga aiki, jikinta sai rawa yake yi.

"Tun da ki ke na taSa saka ki wanki?" Ta girgiza kai.

"To Meyasa ki ka wanke nawa kayan?"

"So nake nima na yi abin arziki, ban zaci zai zama na tsiya ba"

Ya girgiza kai ya ce "Zubo mini Abinci" ta tashi tana ta tsuma, ta je ta zubo abinci ta kawo masa tana kallonsa.

Ya karSi Abincin, ya ajiye a gabanta ya ce "Ci Abinci"

Fuska duk hawaye ta ce "Dan Allah ba zaka saka ni kama kunne ba?"

Ya girgiza mata kai ya ce "Ba zan saka ki ba" yayi maganar yana Webo Abincin ya kai bakinta.

"To ka ha?ura?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

"To dan Allah ka yi ha?uri, tsautsayi ne"

"To, ci abinci" sai a lokacin ta ji ranta ya yi sanyi, har ta fara cin abinci, babu wanda bai yi mamakin yadda mai sunan Baba ya ?yale ruma ba, basu taSa kawo zai rabu da ita ba.

Sai da ta ci ta ?oshi sannan ta ce "Me sunan Baba"

"Na'am"

'Dan Allah ka yi ha?uri, zan karSi kuWina na wurin mama sai na saya maka wata "murmushin gefen baki ya yi ya ce 'To Shikenan".

Bayan yaya Umar ya fita, Huzaifa ya lallaSa ya bi ruma Waki yana cewa "Ruma, wace addu'a ki ka yiwa mai sunan Baba ya ?yale ki ne? Zo ki gaya mini"

Usman ya ce "Wallahi nima na yi mamaki duk Sarnar nan da ta yi masa ya ?yaleta"

Babu wanda ta kula a cikinsu ta kwanta tana yiwa Allah godiya.


Hidindimun Salla suka wuce, aka koma makaranta, ruma ta koma makaranta, sai dai fafur ta ?i zaman ajinsu, wai malaminsu baya son ta, wani malam Habibu Wan mai makarantar ta li?ewa, duk ajin da za shi ya yi ?ari sai ta bishi, gashi ta ma?alewa Auwal, yaya sama yaya ?asa haka take kiransa saboda yana sayen tsami gaye da goriba ya bata.

Yanzu ma 'yan ajin su Yasir suna jiran malam Habibu ya zo yayi musu ?arin Alqur'ani, sai ga shi ya shigo shi da ruma.
Yasir yana ganinta ya tsuke fuska, dan tun wancan hansfreen da ta yi masa a gida, ya hanata zuwa ajinsu, amma sai gata.
Malam Habibu ya zauna, ya ce ta shiga cikin mata ta zauna. Aikuwa ta shiga ta zauna, ta nutsu kamar gaske aka yi ?arin nan aka idar.
Aka zo kowa yana biyawa, aka zo kan Yasir shi ma ya biya, sai cewa ta yi 'Inyee ashe ka na ja, hmm da ba ka iya ba wallahi da sai na faWa a gida, in ce kai ma baka iya karatu ba"

Dariya 'yan ajin suka hau yi suna kallon Yasir, ya sunkuyar da kai yayi mata shiru.

Kowa ya gama biyawa, ruma ta ce "Malam nima zan karanta"

Ya ce "To bisimillah"

Abun mamaki sai ga ruma ta karanta shafi guda, duk da tana yi ana cin gyaranta, amma ta kai shafi guda, ba ?aramin mamaki ta bawa Yasir ba, yarinyar da ta ce ita gejinta aya biyu kawai.

?ari biyar malam Habibu ya bata, tare da jinjina mata, dan babu wanda bai san ruma ba ta ja ba.
Da ya kammala ?arin ya ce ta ta so su tafi, amma ta kalli yadda Yasir ya haWe rai ta ce "Malam ni ka bar ni a nan ajin"

Malam Habibu ya ce "To shikenan, duk malamin da ya zo ace masa ruma ajiyata ce, sanna ba ruwan kowa da ita kar a takura mata"

Suka ce to.

Yasir kuwa kamar ya zo ya rufeta da duka, dan ba zata taSa zama shiru ba.

Ruma ta shige cikin 'yan mata, suna hirarsu, ita kuma tana shan farar ?asarta, amma duk tana jin me suke faWa.

Yau har aka tashi tana ajin su Yasir, sai da aka tashi ta bar ajin.

Ta je ta samu tsohuwar da take sayar da kayan yara a a ?ofar makarantar, ya titsiyeta wai sai ta bata farar ?asa kyauta.
Duk shegen son kuWi irin na iya, sai da ta bawa ruma farar ?asarar nan, saboda shegen surutun ta da nacin tsiya.

Ta karSi farar ?asarta ta yi gida, haryanzu makarantar nan ba ta da ?awaye, a cewarta Waliban ba su yi mata ba, kuma ba komai bane su Waliban sa'aninta kowanne ya mayar da hankali a kan karatunsa ne, ita kuwa ruma 'yar abi yarima a sha kiWa ce.

Tun da ta je gida take tafa hannu tana masifa, "Wallahi an mini laifi a gidan nan, kuma sai kowa ya hallara zan faWi me aka yi mini" jin kowa ya shareta ya ?i kulata ya sanya ta ce "Mama yanzu dan Allah abin da ake yi mini a gidan nan ya dace?"

"Da aka yi miki me?"

"Mama a gabanki 'ya'yanki suke ce mini ?waila, amma baki taSa hana su ba"

Mama ta dubeta ta yi murmushi cikin manyance ta ce "To ba ?wailar bace ba?"

Ruma ta buWe baki ta ce "Au mama har da ke?"

Aliyu ya ce "To meye dan an ce miki ?waila, ai ?wailar ce"

Ruma ta ce "Kutt, ?waila fa wadda ba ta da nono kenan?"

Aliyu ya ce "Innalillahi wannan gingimemiyar maganar fa"

Mama ta ce "ke waye ya gaya miki haka?"

"'yan ajin su Yasir ne suke faWa, matan nan ina jin su da kunnen nan nawa, sun zaci bana jin su"

Mama ta ce "To ke nonon ne da ke da ba za ace miki ?waila ba?"

"Mama gori dai ake yi mini kenan? Sai in je wurin Mai furar nan na bakin hanya, na sayo nonon, na zo na ?ulla a leda na dinga sakawa" cike da takaici mama take bin ruma da kallo, ta ma rasa me zata ce mata. Usman yana tsakar gida, sai ?ya?yata dariya yake ?asa-?asa lamarin ?anwar nan ta su sai Addu'a kawai.

Aliyu ya ce"Ke da ki ke ?anwar maza, me zaki yi da wannan abun? Ki yi zamanki a haka ai sai kin fi kyau"

Ta ce "Kuma fa haka ne" ta cire rigar islamiyyar, daga ita sai vest, ta sinsina rigar ta kuma cewa "Mama, dan Allah yaushe zan fara warin hammata, ina son idan na cire riga na sansana na ji tana Wan warin nan da ?amashin turare "

"Fitar mini daga Waki dan ubanki, shashasha mara al?ibla fita ki bar mini Waki".





AYSHERCOOL
08081012143
[08/07, 4:58 pm] JAKADIYAR AREWA: ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?ANWAR MAZA
? ? ? ? ? ? ? ??

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing? YouTube channel Win
@Cool Hausa Novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro.

*A TAIMAKA AYI SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL ?INA NA COOL HAUSA NOVELS, KO IN KOMA POSTING SAU ?AYA A SATI =??*

10




?an tsayawa ruma ta yi tana kallon mama, cikin sangarta ta ce "Mama wai me na yi to?"

"Ban sani ba fitar mini daga Waki, mara kan gado, ni ba dan a gida na haifeki ba, cewa zan yi an canza mini 'ya, idan an yi gabas sai ki arta ki yi arewa, me ake da wani wari ban da rashin kan gado irin naki?"
Tsayawa ruma tayi tana kallon mama tana wasa da gashin kanta.
"Ba zaki fita ki bar mini Waki ba, sai na taso kan ki?"
Fitar ta tsakar gida yayi dai-dai da shigowar Yasir, da shi da Huzaifa.

Yasir ya aika mata da wani irin mugun kallo ya ce "Me na ce miki game da zuwa Ajinmu?"

Ta murguWa baki ta ce "Ni wurinka na zo, ai ba wurinka na zo ba, ni da malam Habibu muka zo"

"To uban me ya hana ki je ajin su Huzaifa?"

Huzaifa ya yi caraf ya ce "Wallahi ta zo mana aji, sai na mata dukan tsiya, ta zo Win ta gani"

Hararsu ta dinga yi, tana cewa wallahi sai ta je.

Bayan Huzaifa ya canza kaya, ya shiga Wakin mama ya Wau jakarta.
Ruma ta Waga murya ta ce "Mama, ga Huzaifa nan ya Waukar miki jaka"

Ya ce "To munafuka"

"Wallahi ni ba munafuka ba ce, mama Huzaifa zai satar miki kuWi"

Huzaifa ya ce "Mama aron naira Wari zan Wauka"

Mama ta ce "Ajiye mini jakata, ba zan baka aron ba, idan ka Waukar mini kuWi ba bani ka ke ba"

"Dan Allah mama ki bani, zan baki wallahi"

Daga kitchen mama ta ce "Ba zaka ajiye mini jaka ba sai na zo Wakin nan?"

"Mama wallahi bai ajiye miki ba"

A fusace Huzaifa ya ajiye jakara, yana yiwa ruma kallon banza, kamar ya kai mata duka haka ya fice.

Ruma ta ce "Dana sani na bar shi ya Wauka, nawa nake bin mama ba biyana take ba"

***

Yau za a rufe makarantar su ruma a tafi hutu, yau za ayi spelling B da aka bawa su ruma.
Sai bin malaminsu take tana ce masa ita fa sai an sakata a cikin masu spelling B.
Malamin ya ce "Ki kwantar da hankalinki, zamu san yadda za ayi".

Azabar nacin ruma sai da ya sanya aka sakata a cikin masu spelling B, amma aka ce kar ta yi magana.

?arshe dai ruma ce ta taimaki 'yan ajinsu, gaba Waya kalmomin nan babu wanda ba ta haddace ba, ruma ta bawa malaman makarantar su da Waliabai mamaki, dan ko bata takardar da aka yi, tsabar naci ne ya sanya a ka bata.

Ai kuwa ruma ta samu kyaututtuka sosai, karo na biyu a rayuwarta, da ta samu wani abun arziki a saboda harkar karatu.
Aka bata litattafai kaya guda, da kayan koyon karatu.

Ruma baki har kunne ta je gida, mama ta ganta da kaya ni?i-ni?i.

"Ke wannan kayan na menene?"

Ruma ta zubewa mama kayan ta ce "Mama, duk nawa ne a makaranta aka bani"

"Meyasa aka baki?"

"Wannan takardar da aka bani ce a makaranta, kowa ya ?i koya mini, na je na yi ta yi da kaina, shine fa aka yi yau na samu wannan kyautar"

Mama ta ce "Hmm, ai shikenan"

"Mama wai na ga kamar ba ki yadda da bayanin da na yi miki bane?"

"Eh to kusan hakan, dan abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa"

Cikin rashin

Please Login or Register in order to submit comment