You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke yi a nan?"

Cikin kuka ta kira sunansa "Huzaifa"

"Na'am" ya amsa.

"Ka san wani abu?"

"A'a sai kin faWa"

"Yaya Usyy ne ya ce mini idan namiji ya taSani, zan yi ciki in haihu, kuma korata za ayi daga gidan nan, sai malam ya aikeni karSo masa chalk, da na kawo masa hannunsa ya taSa nawa. Na tambayi 'yan babban aji na gaya musu abin da yaya ussy ya gaya mini, suka ce eh haka ne wai ciki ne da ni, ka ga cikina ma ya fara kumbura yanzu ya zan yi bana son a koreni dan Allah ya zan yi" ta yi maganar har cikin zuciyarta tana rushewa da kuka.

Huzaifa a ransa ya ce 'Alhamdilillah, na samo maganinki'

"Tabbas Deluwa kin kwaso mana abin kunya, yanzu abin da zai faru shi ne, ki haWa kayanki a Soye, cikin dare na kai ki tasha ki bar gidan nan, dan idan mai sunan Baba ya sani sai ya jefa ki a rijiya"

Sake rushewa ta yi da kuka har da majina, ya yi saurin cewa "Sai mama ta jiyo kina kuka asirinki ya tonu ko?"

Ta goge hawanyeta ta ce "To ya zan yi?"

"Shikenan, zan rufa miki asiri, amma zaki din ga yi mini wankin uniform".

"Eh na yadda, amma dan Allah kar ka faWawa mama, bana son a koreni dan Allah"

Huzaifa ya yi wani murmushi cikin mugunta ya ce "To na ji, goge hawayen ba zan tona miki asiri ba"

Abu kamar wasa, ruma ko abinci ba ta iya ci, gashi kullum sai ta wanke wa Huzaifa kayan uniform.

Mama ta gaji ta ritsa ruma, har da bulala sannan ta zauna ta yiwa mama bayanin abin da yake damunta.
Mama ta yi salati ta sanar da Ubangiji, gaba Waya ruma ba ta da wayo, ga shegiyar tambaya idan kuma ka yi mata bayani yadda za ta fahimta, nan ma ta yi wata kwaSar.

Sai da mama ta yi da gaske, sannan Ruma ta yadda ba ta da ciki, dan har da nunawa mama cikinta wai ya kumbura Wa ne a ciki.

******

Ta na zaune a kan sallaya ta idar da salla, sai dai ta lula duniyar tunani, ba lazamin take yi ba.

Kamar daga sama ta ji ana kiran sunanta, ta yi firgigit ta dawo hayyacinta.

"Ohh Nusaiba, an gama girkin daren ne?"

Nusaiba cikin damuwa ta dubi Ammi sannan ta ce, "Ammi, tunanin me ki ke yi haka ne? kin san fa ba ki da cikakkiyar lafiya"

Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Nusaiba tunanin nan na dole ne, shi yake yin kansa, abubuwa sun yi mini yawa, bana son na nuna gazawata amma ni na san na gaza na kasa shawo kan komai, al'amura na ta ?ara dagule mini"

"Me kuma ya faru ne?"

"Mahmud, lamarinsa yana damuna, ga kuma yadda aka addabawa yarinyar nan a cikin gidan nan, ha?urina ya fara ?arewa, duk wanda ya taSa Iman ni ya taSa raina ya na Saci fiye da tunaninki"

Nusaiba ta gyara zamanta ta ce "Ammi, kin san wannan duk shirin Mummy ne, so take ki magantu ku raba abin faWa a cikin garin nan, ita take buga miki wannan wasan, ki ?yaketa kuma ki yi ha?uri ki Wauke kan ki daga Mahmud, ba ga takawa nan ba, mu da shi mun isheki rayuwa su je su ?arata mana"

Ammi ta girgiza kai ta ce "Nusaiba kenan, ba zaki gane ba, tashi maza ki je ki tabattar an gama komai, sannan ki kira mini Iman, ba na son zamanta ita kaWai"

Nusaiba ta ce "To shikenan Ammi, bari na je".

Sannu a hankali yake tafiya, tamkar ya na tausayawa ?asar da yake takawa, har wani rangaji yake kamar wanda ake yiwa kiWa.
Fuskar nan a murtuke babu annuri, in da ya sa a gaba kawai yake kallo, yake burin cinmma. Babu tsammani suka yi kiciSis a baranda, ba tare da Waya ya san Waya ya taho ba, kuma aka rasa wanda zai bawa wani hanya ya wuce.
Kallon-kallo suka yi na wani Wan lokaci, sannan ya lumshe idonsa a hankali ya buWe. "Banihanya"
Kallonsa ya yi irin kallon ba ka isa ba ya ce "Ni da kai waye ya tarewa wani hanya?"
Cikin tsawa da zafin zuciya ya ce "Ka bani hanya na ce"
Murmushin gefen baki yayi, tare da rausayar da kai, yayi taku biyu ya koma gefe ya bashi hanya.
Sai da ya ?are masa kallo, kamar ba zai wuce ba, sannan ya cigaba da takawa sannu a hankali ya wuce.
Ya waiwaya ya bi bayansa da kallo, yayi wani murmushi sannan ya ce "Zamu ga wanda ya fi iya buga wasan sa"
(A mini afuwa ban editing ba)
AYSHERCOOL
08081012143
[19/07, 8:42 am] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA
? ? ? ? ? ? ? ??

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing? YouTube channel Win
@Cool Hausa Novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro.




P13

Kwanci tashi asarar mai rai, ruma ta kammala primary school za ta shiga sakandare, sai murna take yi, sai dai babu abin da ya sauya a halayenta na rashin ji, ta hanasu sakat,a gidan, da an jima sai ta buga tsalle ta ce "Wooo ni zan shiga sakanni in dire"

Yasir ya ce "Ji banza, me aka yi da maza meye wata sakandare, ai yanzu aka fara"

"A'a bar ni na yi tsalle, na samu cigaba a rayuwa ta, Sakandire fa, zan shiga jss1 ai girma ya zo, yanzu ni ma zan yi tsayi tun da zan shiga Sakandire"

Usman ne ya mi?o mata kuWi ya ce "Yi sauri ki je wurin mai shayi, ki karSo mini madara zan karya"

?an Sata fuska ta yi ta ce "Mama fa ta hana ni zuwa wurin mai shayi, da mai kifi da mai nama"

"Za ki wuce ki je ko sai na zo kan ki?"

Ba dan ta na son aiken ba, ta karSa ta saka hijjabi ta fita, tama tafe tana shan farar ?asa, bakinta yayi fari tas, kai ka ce akuya ce ta dumbuji dusa.
Ko da ta isa rumfar, dandzon matasa ne a ciki, sun cika kuma galibi abokan yayyenta ne, ba wanda ta kula a cikinsu ta mi?a kuWi a bata madara.

"Rumaisa, ina Dambele?" Cewar wani matashi da yake ?o?arin kai lomar indomie.
Ta kalleshi ta ce "waye kuma dambele?"

"Ussy mana, na gidanku"

"Sai ka ce mini wani dambele kuma, kamar sunan rago, yana gida ya aka yi?"

"A'a ba komai, kawai na tambayeki ne, kin san Usman dambele wani Wan ball ne, shi ma haka ake ce masa a filin ball".

"Ni zaka gayawa dambele Wan ball me, ai sai dai na baka labari"

Kan kace me, aka Sarke da hirar ball a teburin mai shayi tare da ruma, yadda take bayanin ball ya isa ka gane ?anwar maza ce, gaba Waya ta manta da aike da aka yi mata, ta tsaya ana sharhi da ita.

A ?alla ta kai mintuna arba'in a wurin, ta manta da aiken gaba Waya, ga wurin shayin a ?ofar gidan su yaje, ya ci ace ta je ta dawo, amma babu ruma babu dalilinta.

Ba shiri Usman ya sanya riga, ya fito nemanta, 'yar muryarta kawai yake jiyowa, tana bayani, har da dukan teburin mai shayi tana mayar da yadda aka yi.

"Ke! Meye haka?" Firgigit ta waiwaya, ta ga Usman a tsaye a bayanta.

"Aiken da na yi miki kenan?"

Kame-kame ta tsaya yi, dan har ga Allah ta manta da wani aike, musun ball na Wibarta a rumfar mai shayi.

"Dambele yanzu nake tambayar ruma kai, ashe kana gidan ma, yarinyar nan ta burgeni, ta san ta kan ball abin mamaki, gaskiya na yarda ?anwar maza ce"

A ?ule ya ce "Kai dilla ware, wannan ai hauka ne, kawai kun saka yarinya a gaba, kuna wani surutu, meye ala?arku da ita?"

"Haba Usman, Ruma ai ?anwarmu ce"

"Ba wani ?anwarku, baku haWa ala?ar komai da ita ba, ke kuma wuce kan na saka ?afata, na kifa ki a wurin" sumi-sumi ta bar rumfar mai shayin ta nufi gida.

Ya bita gidan, ya dinga yi mata masifa, kamar zai cinye ta Wanya.

*****

"Hutawarki lafiya uwar Wakina ta kai na, jirgin sama ma?urar tafiya komai nisan ta"

Gyara zama ta yi ta dubeta ta ce "Bani labari, me ake ciki ne?"

"A'a, labarin bai gama nuna ba, amma ki bari ya ?arasa tukuna, amma fa gida ya ?ara hargitsewa, ina ta gwara kawuna ta ko ina, na hanata sukuni, kusan tun bayan da Mahmud ya sa ?afa yayi fatali da ?udurinta"

"Hajiya Jamila, idan har muka tafi a kan tsarin da muka yi da farko, to tabbas zamu cimma buri, sarautar ta bar gidanku har abada"

Hajiya Jamila ta yi murmushi ta ce "Ai hakan na fi so, gara ai ayi biyu babu, sai na yi mata kassarawar da zata bar gidan nan da ?afafuwanta, tun da dai na fuskanci asiri ba ya cin ta, gara ayi mutuwar kasko"

Dariya suka yi a tare, suna tafawa cike da duniyanci, tare da cigaba da tattaunawa a kan cikar muradansu.

****
Tamkar mai shirin zarewa, haka yake kai gwauro, ya kai mari a cikin katafaren falon, da ya sha ado da kayan alatu kamar ba za a bar duniyar ba.

Gefe guda wani babban mutum ne, zaune a Waya daga cikin jerin kujerun da suke falon, hannunsa ri?e da wani kwagiri, fuskarsa Wauke damuwa.

Matashin ya daki teburi ya ce "Daddy meye abin yi ne? Ka na zaune ba ka ce komai ba?"

Dattijon ya numfasa sannan ya ce "Ka bini a hankali, ina tunanin wani abu ne"

"Daddy ba mu da isasshen lokaci fa, you know am following your footsteps, idan aka Sata siyasarka, zai shafeni, mutum mai girma da daraja, kamar kai wannan Wan ?aramin alhakin zai kawowa barazana, gaba Waya gidajen jaridu, da dandalin sada zumunta, an buga labarin nan, kamar kai ka cancanci haka a ?asar nan"
Murmushi mutumin ya yi ya ce "Easy Khalifa, ai ja da baya ga zaki ba tsoro bane ba, shirin ya?i ne, haka zalika yaro bai san wuta ba sai ya taka, ka ?yale shi, a yanzu ba ta tasa ma nake yi ba, na zuba ido ne in ga wani mataki za a Wauka a kansa. Saboda idan ya matsa sai ya fasa ?wai, to ba ni kaWai za ta shafa ba, zata shafi manyan ?asar nan da dama, yaron tone-tonensa ya yiwa, amma yana daf da tona wu?ar da za ta yi ajalinsa"

"Ohh my God, Daddy sai wasu irin maganganu ka ke yi, amma haryanzu ba ka gaya mini menene mafita ba"

Alama ya yiwa Khalifa da ya je, Khalifa ya ?arasa gabansa ya dur?usa. Ya tallafo kan Khalifa ya yi masa raWa a kunne.
A take damuwar kan fuskarsa ta gushe, murmushi ya mamaye fuskar ta sa ya yiwa mahaifin na sa alamar jinjina da hannunsa.

****
Sati biyu kenan da fara zuwan ruma makarantar sakandare, kullum sai ta yi gugar kaya, wai kar ta je da ?azanta kamar ba 'yar sakandare ba, amma idan ta tashi dawowa tamkar ta yi dambe da kura, kayan nan du?un-du?un haka take dawowa da su.
Haka kawai yau zuciyarta ta raya mata, ta bi ta hanyar gidan mai unguwa, kasancewar a hanyar makarantar da take gidan yake.

A layin gidan mai unguwar, ta ga manyan motoci a fake, da alama wani abun ake yi. Hankalinta na kan lambun da ta taSa zuwa ta Webo mangwaro mai gadi ya ce mata Sarauniya, dan haka ba ta tsaya jin me ake a layin gidan mai unguwar ba.

Sai dai ko da ta ?arasa layin lambun, wasu manyan motoci ta tarar guda uku a ?ofar lambun.
Lelle?awa ta shiga yi, ta na haWiyar yawu, saboda yadda take iya hango cincirindon bishiyoyin mangwaro da yadda? suka yi 'ya'ya, ban da sauran 'ya'yan itatuwa.

"Ke uban me ki ke yi a nan wurin?"

Da sauri ta waiwaya, ta ga waye yake yi mata tsawa haka.
?an gidan mai unguwa ne dai, da ya taSa kamata.

"TaS dama kana nan?"

"Eh ina nan, yau ma satar ki ka zo yi?"

Ta tsuke Wan bakinta ta ce "Ba yayana ya ce kar ka sake ce mini Sarauniya ba?"

"Oho miki dai, ai Wiba ki ka yi ba a baki ba"

"Eh amma ai dai ya biya"

Cikin hanzari ya ce "Wai me ma ki ke yi a nan wurin ne?"

Ruma ta Wan ri?e haSa ta ce "Hmmm, ashe haryanzu ka na nan, ba ka cigaba ba, ni gashi har na gama primary na shiga sakandare"

"Ke dalla ware, tun kan a haife ki na yi sakandare na gama, fitsararriya wai wani ban cigaba ba, Sace ki bar nan wuri muna da ba?i"

Ta Wan yi ?asa da murya ta ce "Wai su waye suka zo, na ga ?ofar gidanku ma da mutane"

"Ban sani ba, ba zaki wuce ba sai na zane ki?"

"Dan Allah Wan uwanmu mangwaro zaka san mini, ka ga dai yau ba sata na yi ba ko?"

Dariya ya kwashe da ita ya ce "A ina na zama Wan uwanku?"

"Ai kai Wan uwanmu ne na Musulunci"

Girgiza kai ya yi, zai wuce ta ya shiga cikin lambun, amma ta biyo shi.

"Wai ke baki da hankali ne, na ce miki muna da manyan ba?i masu wurin ne suka zo"

Cikin ko in kula ta ce "To ni ina ruwana, koma suwaye ai mutane ne ba mala'iku ba, dan Allah in biyoka ka san mini, ni sai na je na tambayo mai unguwa ma, na san shi zai ce ka bani"

Ya ?arewa ruma kallo tsaf, a rashin hankalinta, tsaf za ta aikata abin da ta faWa, na zuwa tambayo mahaifinsa, gashi yana tare da ba?i, ya dubeta ya ce "Yanzu abin da za ayi, ki zauna ki jirani, bari ba?in su tafi sai na baki"

"To, bari na je na zauna, kuma idan baka fito ba, biyoka zan yi"

"Wallahi ki ka shigo, zane miki jikinki za su yi"

"Su waye wai?" Ta yi maganar tana sake le?a lambun.

"Kin ga tsaya, bari na je na samo miki" ya ?arasa maganar tare da shigewa cikin lambun.

Dandamalin wani gida ta samu, ta ajiye jakarta, ta Webi duwatsu ta hau 'yar carafke.
Tun 'yar carafken na Wauke mata hankali, har ta gaji da jiran Wan gidan mai unguwa. Ta zube duwatsun ta tashi, ta je ?ofar shiga lambun ta tsaya, ta Waga murya ta ce "Ka cika al?awari, zan shigo fa" magana ta fara ji ?asa-?asa na mutane, alamar za a fito, ba ta yi niyyar matsawa daga bakin ?ofar ba, sai da ta hango akuya na shirin watso mata litattafanta, ta ci, ta nufi wurin jakarta, ta Wau jakar ta na zagin akuyar, har da kiranta mayya mayuwanciya kamar tana magana da mutum.

Tana waiwayo wa, taga mutanen sun fito, sai dai kusan duk sun yi rawani, sai mutum Waya da suke takewa baya, shi kuma suit ce ma a jikinsa.

Da gudu ruma ta kwaso, ta tsaya daga baya ta ce "Laaa sarki ne wannan?" Jin 'yar shilar muryarta ya yi, tamkar busar wata 'yar sarewa a kunnensa, duk da akwai dandazon yara da suke wurin, galibi suna zuwa idan har ya zo, saboda ya kan basu kuWi. Har ya Wan juyo, zai waiwayo ya ga wacece a cikin yaran, bai juyo gaba Waya ba, dogon hancinsa kawai ta iya ganowa, ya Wauke kansa ya shige motar da aka buWe masa.

"Sarki ka ganni, ka juyo ka kalleni, ko dai ba sarki bane ba, na ga sarki ba ya saka ?ananan kaya ai"

"Ke! Hattara yarinya 'yar talakawa, ba a yiwa takawa karan tsaye"

Shiru ta Wan yi ta dube shi ta ce "'yar talakawa kuma, to wallahi gidanmu akwai abinci, mu ba talakawa bane ba, kuma ba gara ni ba ma, Idan mu ka je kallon hawa mandawari, mama ta ce mini masu irin kayanka bayi ne, sayar da su ake yi zamanin baya a karSi kuWi"
Kowa waiwayowa ya yi yana kallon ruma, ya yin da dogarin ya zabura ya yo kan ruma, aikuwa ta kwasa da gudu ta tayar da uwar ?ura, shi kuma ya bita yana a tare ta.

Da ?yar ruma ta kai gida afujajan, ta na ta haki kamar numfashinta zai Wauke, ta shige Wakin mama ta ?ule ta na ta sauke numfashi.

Mama ta biyo ta Wakin ta na faWin "Ke!ke ruma ke da waye haka? Yanzun ma tsokanar ki ka yo ko? Tun yashe aka tashi 'yan makarantar ku, amma Allah bai nufe ki da shigowa ba sai yanzu ko? Ba zaki fito ba ina yi miki magana?"

Sumi-sumi ta fito, tana waige-waige sannan ta mayar da idonta kan mama.

"Daga ina ki ke?"

Ruma ta Wan Sata fuska ta ce "Mama ba ko ina fa"

"Zaki gaya mini ko na bari sai ya shigo?" Cikin kiWima ruma ta ce "A'a, dan Allah kar ki yi mini haka, wallahi kallon sarki na tsaya, a lambun mai unguwa, shi ne wani bawa ya ce mini 'yar talakawa, shi ne" sai kuma ta yi shiru.

"Shi ne me?"

"Cewa na yi, ai gara ni ba baiwa ba ce, shi fa kayan bayi ne a jikinsa, wanda ki ka gaya mini Win nan ranar da muka je cikin gari kallon hawa, shi ne ya biyo ni da gudu"

Tafa hannu mama ta shiga yi tana faWin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un,?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? dama can na aike ki, na ce idan an tashi ki dinga zuwa wani wur?" Ta girgiza kai.

"Saboda tsabar rashin kunya da rashin hankali, ki ka tsaya kina cewa babban mutum bawa, daga yi miki bayani ranar, ke ba zaki taSa hankali ba ko? Ina ma ya kama ki ya yi miki dukan tsiya, na gaji da halinki ruma, ki na girma ki na sake shiga dawa, gaba Waya babu alamar hankali balle nutsuwa a tare da ke. Ki je ki cigaba da abin da Allah ya nufe ki da yi, Allah ya gani na yi iya yi na, ban yi miki irin wannan tarbiyyar ba Allah ya shiryeki"
Ruma ta yi shiru, tana sunkuyar da kai kamar gaske.

A Sangaren karatu, an samu sassauci daga halin ruma, kullum Usman ya na ba ta ?warin gwiwa, a kan kar abin da ya bata tsoro, duk wani abu da wani zai yi, ita ma za ta iya.
A makarantar islamiyya kuwa, tun da malam Habibu ya taSa hannunta garin karSar bulala ta daina bin sa, sai dai yau ta zauna a ajinsu, gobe ka ganta a wani ajin, Waukar magana kuwa ba ta fasa ba. Dan saboda tsaurin ido, har manyan 'yan matan nan haka take zagewa ta yi musu rashin kunya, ba abin da ya yi mata zafi. Kuma ku san ko yaushe ta na cikinsu, ba ta yawo da sa'aninta.

****
"Allah ya taimake ki Hajjaju Mummy"

Murmushi ta yi cikin isa da izza ta ce "Abin ?auna, ka yi breakfast Win ne?"

"Eh, na yi" ya yi maganar ya na zama a kusa da ita.

Ta saka hannu ta shafi sumar kansa ta ce "Mahmud, ya kamata a rage sumar nan"

Yayi murmushi ya ce "Haba Mummy, wannan sumar yadda ki ka ganta ki bar ta kawai"

"Hmm to ai shikenan, ya shirye shiryen komawa school?"

"Alhamdilillah, ina nan ina yi, very soon zan koma"

Fauziyya ce ta fito falon ri?e kofin shayi, ta kalli Mahmud ta ce "Yaya Mahmud, barka da safiya"

"Yauwwa, ina Ruky, ban ganta ba?"

Ta nemi wuri ta zauna ta ce "Ba ta tash ba, bacci take yi" ya kalli agogon hannunsa ya ce "By this time?"

Mummy ta ce "Ka san ta na karatun dare, dole ta yi bacci da safe"

Ya jinjina kai ya ce "Haka ne".

"Amm Yaya Mahmud, takawa ya dawo fa, yakamata ku haWu kan ka koma, kun daWe baku haWu ba" tsuke fuska ya yi, ya kalli Fauziyya ya ce "Yaushe ki ka fara tsara mini abin da zan yi a rayuwata? Ubana ne shi da lallai sai na ganshi? Na gan shi jiya mana so what?"

Mummy ce ta katse hirar, ganin Mahmud har ya Wau zafi ta ce "Is ok, ya isa haka, ku dai idan ya shigo ku je ku yi masa sannu da zuwa, bana son ?ananun maganganu irin na gidan nan".



Sannu a hankali yake danna system Win da ke gabansa, kamar ya na tausayaa mata, hannunsa Waya kuma ri?e da cup ya na shan tea, idan ba ka kalleshi sosai ba, zaka Wauka Mahmud ne a zaune.
Muryarta ce take dawo masa kunnesa, kamar a yanzu take magana *laa sarki ne wannan? Sarki ka juyo ka kalleni* ya tuna ?arfin hali da ta dubi Waya daga dogarinsa, ta ce masa bawa, koma dai wacece a muryarta ya ji akwai yarinta da kuma tsananin tsaurin ido, idan sarkin ne shi a haka zata yi masa magana kenan, ba girmamawa?
Iman ce ta fito daga sashin Ammi, hakan ya kaste masa tunaninsa, ta ?araso falon ta zauna, ta kalle shi ta ce "Barka da hutawa ranka ya daWe" tun Wazu Nusaiba take falon, tun da suka gaisa ta ja bakinta ta tsuke, ta kasa ce masa komai, shi ma kuma bai kulata ba, amma Iman na fitowa ya yi murmushi.

"Barkanki dai auta ta Ammi, kin tashi kenan?" Ta jinjina masa kai sannan ta ce "Once again Ya hanya, ya kuma ibada?"
"Alhamdilillah, ya karatun?"

"Ina nan ina ta yi Yaya, ka yi mini Addu'a kuwa da ka je?"

Ya jinjina kai ya ce mata "Sosai, ban yiwa kai na Addu'a da na yi miki ba, na so mu tafi tare da ke, amma na san Ammi ba lallai ta yadda, sai dai ku je umarar azumi ke da ita"

Iman ta yi murmushi ta ce "Nima ina yi maka addu'a sosai yaya, Allah ya kawo abin da Ammi take ta fata"

Nusaiba ta jinjina kai, da wani ne ya tsare Yaya da wannan maganar da ya shiga uku, to wa ma ya ga fuskar hakan, ai sai Iman Win.

"Iman, ai kuma zaku iya samarwa Ami abin da take burin, ku fito mana da tsayayyu, a wuce wurin kawai"

Iman ta Wan rausayar da kai ta ce "Sai dai Anty Nusaiba, amma ni dai kam sai a hankali " tayi maganar jiki a sanyaye.

Alama ya yi mata da hannu da ta zo.
Ta tashi ta tafi in da yake ta zauna, ya matsa kusa da ita, yayi ?asa da muryarsa ya ce "Na ji abin da ya faru lokacin ina Saudiyya, abin bai yi mini daWi ba sam, da Ammi ta yi shawara da ni, ba za ta yanke wannan hukuncin ba, ai Allah ke da rayuwar kowanne bawa. Ki Wau abin da ya faru a matsayin Mafi alkhairi, Allah ya tanadar miki mafi alkhairi, ni kai na example ne a gareki, dan haka mu cigaba da Addu'a gaba Waya" ta jinjina masa kai ta na share hawaye.

*******
Usman ne a zaune ya gama cin abinci, ya kalli Abdallah ya ce "Kai ka san wani hau da wannan Anas Win yayi mini yau?"

Abdallah ya ce "Sai ka faWa"

"Wai ni zai tara ya ce mini ya na son ruma, yarinyar da ko ciwon kan ta ba ta sani ba, ni kuwa na ci ubansa, sai kaWan na kikkifa masa mari"

Abdallah ya yi dariya ya ce "Ba abokin ka bane ba, na ga filin ball Win ku Waya ma"

"Dan abokina ne, sai ya ce yana son ?anwata, mahaukacin ina ne shi?"

"Amma wallahi yaya Usy ba ka kyauta mini ba, 'yan ajinmu na Islamiyya su yi ta labarin saurayi, ni kuma ba ni da saurayi, duk wadda ba ta da saurayi fa wai ba?in jini ne da ita, sai an kai ta wurin malamai sun yi mata Addu'a "

Abdallah ya ce "Saurayin uban wa? Ke ya zaki yi da wani saurayi, ko yake shi Anas Win ne ma mara hankali, shi ma irinki ne ai mara kan gado perfect match"

?an saroro ta yi ta ce "Wai Anas Win gidan mai taya?"

Abdallah ya ce "?warai kuwa"

Ta ce "TaS, Astagfirullah Allah ba irin wannan ba, kenan addu'a ta ba ta karSu ba, ina ta Addu'a Allah ya bani saurayi mai kyau, mai kuWi, mai ?arfi sosai wanda zai din ga goyani kamar girman brownstrawman na wrestling, kawai sai wani Anas ya ce yana so na, wata uwar ?eyarsa kamar sirdin keken baban su Ade, gashi siriri da kaWan ya fi taliya. Ina ga sai na ?ara dagewa da Addu'a ".

Usman ya ce"Ke, kina halitta ne da zaki din ga kushe wasu? Kin ga ki shiga hankalinki, ba ke ce baki da kamun kai ba, dole kowa ma ya ce zai ce yana son ki, kuma wallahi idan ba ki shiga hankalinki ba, sai na bashi ke"

"Allah ya kiyaye, wallahi ba zan aure shi ba, gashi ba?i ?irin kamar an rina shi".

"Ke zan ci ubanki na kuma jin kina kunshewa wani halitta, ke kyan ne da ke. Ni kullum fatana Allah ya baki miji na gari ko ya fi biri muni"

Please Login or Register in order to submit comment