You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutane, da mahaifinsa, hakan ya saka kowa Addu'a yake yi mata, a kan Allah ya bata na ta ita ma.

Laila ce ke satar jiki, ta Waukko wa ammi Mahmud, ta kawo mata shi ta ganshi, duk yadda laila ta sha?u da Sharif, sai da yayi mata rashin mutunci a kan Waukar Mahmud ta kai wa Ammi, ya ce kyauta halak ya bawa Jamila Mahmud.

A haka Ammi ta haihu, wannan karon ta samu ?ar budurwa, ta yi ta murna, aka saka mata suna Khadija sunan mahaifiyarta, sai dai duk da haka tana kewar Wan ta, Adam tun yana kuka, yana tambayar ammi Mahmud, har ya daina.

Jamila ta toshe duk wata kafa, da zata sada Ammi da Mahmud, Ammi ta yi wa Sharif kuka, ta yi masa magiya a kan a din ga bari ta na ganin Wan ta, amma ya ce wai Jamila za ta tambaya.

Sai dai jaririyar nan ma ba ta yi tsawon rai ba, ta koma ga Allah.

Abubuwa suka yi wa ammi yawa, depression ya nemi kamata, amma a lokacin ba a waye da ciwon ba, aka mayar da ita gida, wai aljanu ke damunta.

Kamar wasa, Jamila ma ta samu juna biyu, wanda tun da ta same shi take iyayi, da sanabe da fele?e, ranar kwanan Bintu, sai galadima ya bata ha?uri, wai zai kwana da Jamila ba ta da lafiya.

Ammi ba ta taSa tanka masa ba, dan a lokacin ta mi?a wa Allah lamarinta, ta rungumi laila da Adam, ta cigaba da ri?on abun ta, gefe tana zuwa makaranta.

Facaloli suka din ga ziga jamila, suna ce mata uwar magaji, ai yadda aka tsallake yayyen sharif ya yi sarauta, haka? za a tsallake ?a?an bintu na ta su yi sarauta.

Sai dai Allah mai yadda ya so, tashin farko ta haifi mace, ta din ga ?unci tana ba?in ciki, kwanan ?ar uku ita ma ta mutu.

Nan ta din ga yaWa cewar, Bintu ce take bawa bokaye ?a?anta su cinye, shi ne wannan karon ta haWa da tata ?ar, tun da dama ?ar gidan malaman tsubbu ce.

Duk wannan abun da ake yi, Sharif bai daina ?aunar Wan sa takawa ba, sannan ya na Waukar Adam ya shiga da shi wurin Mummy Jamila, amma fa ba zai Wau Mahmud ya shiga da shi wurin Ammi ba, wai kar ta tayar da rigima ta ce sai an bata Wan ta. Shi kansa ya na mamakin yadda aka yi yake yi wa giwarsa wasu abubuwan kamar ba shi ba.
Iyayen ammi suka yi ta bata ha?uri, da nuna mata dama aure, sai an yi ha?uri ibada ne, ta yi ha?uri da Wan nan Allah ya bata wani.

A kwana a tashi, ciwon ajali ya kama mai martaba, shi ma Allah ya karSi abun sa, al'umma shi ma sun ji mutuwarsa sosai da sosai, bayan rasuwarsa maimakon a naWa sarki a 'ya?an sa, sai aka naWa ?anin sa.
Hakan ba ?aramin fitina ya ja ba, dan sai da zumunta ta taSu.
Shi kuwa Sharif, ba sarautar ce ta dame shi ba, rashin babban masoyin sa mahaifin sa ya fi damun sa, kuma wanda aka naWa uba ne a wurin sa, dam tare suka rayu a wurin mai babban Waki kan ta rasu, shi yana Wan ?arami sosai, shi ne yake yi masa komai, kamar Wan sa, kuma idan ya kwaso rigimar sa shi ne mai taya shi, shawo kan mai babban Waki da marigayi, dan haka shi duk Waya ne a wurinsa.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, bayan wannan haihuwar da Mummy ta yi, sai da ta shekara uku, sannan ta haifi wata ?a macen, bayan sun gana Sata Ammi a cikin masarautar, da zancen ta na yi mata asiri. Sai dai ba haka ta so ba.

Ba wani armashi haihuwar ta ta, dan zuwa yanzu babu jinsin da giwa ba ta haifa ba.
Adam ya kai shekaru biyar, Mahmud huWu da watanni, hatta makaranta, Jamila ba ta yadda an saka su Waya ba da Mahmud, idan Adam da Mahmud suka haWu kamar su cinye juna, har Mahmud ya fara fita ya je sashin Ammi wurin adam, duk da bai san ba mummy ce mamansa ba, Ammi ta kama shi ta rungume ta yi ta kuka.

Baba Uwani ta yi ta bata ha?uri, ta Wauke shi ta mayar da shi, dan kar galadima ya shigo ya gani, yayi mata faWa. A irin haka Jamila ta fara amfani da baba uwani, ta bata kuWi tana sakata kawo mata rahoton abun da yake faruwa a sashin Ammi, duk da ammin na iya ?o?arin ta wurin kyautatawa baba uwani.

Wataran Adam ya shiga sashin Mummy, ya na neman Mahmud, kuma ya ga ?anwarsu, dan yana son yara. galadima na ganinsa ya yi murmushi ya tashi tsaye daga kashingiWen da yake yana cewa "Maraba da kai babana, abun ?aunata kuma magajina, galadima Wan galadima kuma jikan sarki, jikan manoma da malamai"

Sai da kirarin da galadima yake yi, ya bawa Adam Win dariya, wani dun?ulallen ba?in ciki ya tokarewa Mummy zuciya, galadima magajin galadima? Wato ita ko oho, wato har ma ya sa ran Wan sa zai yi sarauta, nan ta yi alwashin idan da ranta sai dai ayi biyu babu.
Tun daga nan ta fara turawa Mahmud a?idar tsanar Adam, wai babansu ba ya son sa takawa yake so, dan haka ya daina kula shi, shi ma ba son sa yake yi ba.

Labari ya iske ammi cewa, fulanin nan su ade sun tashi, Ade ta bar sallahun a gaya mata tashi ya kama su ba shiri, sun bar wannan rigar sun yi gaba.', za su koma mahaifarsu.

Ammi sai da ta je har rigar ta tabbatar wa da kanta, ta sha kuka sosai da sosai, yadda ta saba ta sha?u da Ade da ?an rigar, kamar danginta.

Rayuwa ta cigaba da tafiya, Jamila ta sake haihuwa, amma still ?a ma ce, sai da ta ji tamkar ta mayar ta ce ba ta so.

A wannan lokacin sarkin da yake ci, mahaifiyarsa ta na raye, dan haka ammi a wurinta take samun sassauci. Mai babban Waki ta wancan lokacin da ta ri?e shi, ita ma ba ita ta haife shi ba.

A wannan karon, shi ma Sharif ?arara yake nuna son Adam, saboda soyayyar da yake yi wa mahaifinsa, da yadda mahaifin nasa, ya nuna masa ?auna.

Jamila kuma ta yi alwashin rusa soyayyar nan, da cigaba da ba?antawa giwa, domin rama abun da ta yi mata, na fara auren Galadima.

Duk yadda ta so raba Mahmud da Adam, ba ta yi nasara yadda take so ba, duk da Mahmud ya fara yadda da abun da take gaya masa, sai dai duk yadda take korar Adam idan ya zo wurin Mahmud ya kasa zuciya.

Tuni Mutanen masarautar, wasu sun fara Wauka, tare da kiran Adam magajin galadima, har da masu ce masa galadima ?arami, ko kuma magajin takawa, idan ?an kan zagi suka yi masa wannan washin, haka galadima zai ta yi musu kyauta.

Hajiya Lubabatu ta samo musu wani hatsabibin boka, malam na kan dutse, suka je wurin sa a kan suna son a nakasta Adam, yadda ba zai moru ba, kuma a saka gaba da ?iyayya tsakaninsa da Mahmud, yadda wuta da ruwa ba zasu jitu ba, haka suma sannan a saka wa galadima tsanar Adam.

Bokan ya ce "Sai an kai masa Adam, saboda ya san aikin da zai yi a kan sa, sannan a taho masa da jinin Mahmud a sirinji.

Ta koma gida, ta saka galadima a gaba, wai tana son ta je garinsu, za ta tafi da Adam, galadima ya ce bai yarda ba, ta haWa baki da malaman makarantarsu Adam, ta je ta Wauke shi a makaranta, aka sha?a masa wani abu ya suma, suka tafi da shi wurin boka, tare da jinin Mahmud.

Bokan ya zu?i jinin Adam, ya haWa da na Mahmud, ya zuba wani abu a ciki, jinin ya rabu biyu Waya ya yi ba?i, Waya ya yi ja, ya mayar da jinin jikin Adam, ya bata sauran jinin, ya ce ta yi girki da shi, ta bawa Mahmud da galadima su ci, ya raba su.

Ta ce ai ba iya nan take so ba, so take a haWa shi da ciwon, da zai nakasa, nakasa ta har abada, da ba zai yi sarauta ba.

Nan ya yi wani ?ulumboto, ya saka wani abu, ya huda wuyansa, ya zu?i jinin Adam, ta wuya, ya zuba a wani abu, ya ce "Ramin da na yi a wuyansa, ta nan aljanar za ta din ga shan jininsa duk shekara, sai dai babu wanda zai iya hudat, Sannan zan yi wani abu da sauran jininsa, duk shekara za a din ga samun mahaukacin doki, ayi masa, zan haWa laya da sunansa, wadda za a kai ma?erar da ta shekara goma, a binne, sannan zan saka wannan aljanar, ta zuba masa jinin mahaukaciyar kura a jikinsa, an nakasta shi, nakasa ta fili da zahiri, iya rayuwarsa wannan aljana za ta cigaba da kula da komai, tun da an bata jininsa, sai dai loka-lokaci, za ta din ga bu?atar wani abun" ya wassafa musu abun da za su bayar, suka bayar sannan suka tafi gida.

Ammi ta kaiwa Adam, yana bacci, wai biyo ta yi ta hanyar makarantar su, ta ga an tashi shi ne ta Waukko shi yayi bacci a mota.
Ammi ba ta kawo komai ba, ta karSe shi, ta yi mata godiya, sai dai tun ammi ta na saka ran adam ya tashi, har tsoro ya kamata. Sai dai bayan ya tashi ba baki, sai dai kallo.

Hankalin Ammi ya tashi, ta gaya wa galadima, hankalinsa ya tashi suka tafi asibiti aka ce lafiyarsa ?alau, ya ce idan zuwa washegari, bai yi magana ba, za a kai shi babban Asibiti, ko ?asar waje ne a akai? shi, sai da daga haka washegarin, tunanin galadima ya sauya, ya ce wai ta ?yaleshi shakiyanci ne.

Abu kamar wasa, sai da Adam ya yi wata tara, ba magana, ga wani irin bacci, mara kan gado, ammi ta dage addu'a, ta kai shi gidansu wurin mahaifinta aka dage da ro?on Allah, sannan ya dawo yake magana.

Gaba Waya galadima ko a jikinsa, ya daina nan-nan da shi, sai dai abun ka da Wa da uba, soyayyar ba ta dishe duka ba, wataran idan ya gan shi ya na jin daWi.

A lokacin Mummy ta haifi Fauziyya, mutane ana ta shigowa, Ammi da laila da adam, sun je ganin jaririya, Adam na ganin Mahmud, ya nufi wurin sa yana kiran sunansa.

Sai dai Mahmud ya hankaWe Adam, sai da ya faWi ?asa, ai yana tasowa, sai idanunsa suka koma kamar na mahaukaciyar kura, yana wani irin gurnani, ya sha?e Mahmud.
Ammi hankalinta ya tashi, duk wanda ya je raba su, sai Adam ya cije shi, kowa ya ya?ushe shi, sai jini ya fita.

Da ?yar Ammi ta ri?e shi ta na yi masa addu'a, ta ja shi ta tafi da shi sashinta, tana kuka ita da laila, tana tunanin menene ya samu adam?.

Sai dai haka ya wuni yana wannan gurnanin, kamar kare.

Mummy kuwa bala'i ta din ga yi, wai za a kashe mata Wa, dama adam Win maye ne, ya tsotsa a wurin uwarsa, ko kuma a garin yawon bin bokaye, Wan ta ya haukace.
Magana ta din ga yawo a fada, galadima ya je har sashin Ammi, ya din ga yi mata faWa, wai ita ta sangarta Adam, har yake yin?urin kashe Wan uwansa.

Halin da ya tarar da Adam Win sam bai dame shi ba.

Tun daga nan, idan faWa ya haWa Adam da yara, sai ya burkice, ya na gurnani, da cizo, idan kuma yayi cizo sai jini ya fita, wanda wannan jinin aljanar take sha.

Wani lokacin idan ana ziga wutar ma?erar nan, haka yake jin ta a cikin jikinsa, yayi ta ihu ya na fuzgar fatarsa, ko kuma idan mahaukacin dokin nan, yana dara, sai ya ji tamkar ?ashin sa ake takawa.

Idan kuwa shakara ta yi, lokacin shan jinin nan ya yi, ya din ga suma kenan, har ammi ta fitar da rai da shi.

Mummy ta din ga tsorata Mahmud a kan Adam, da sai da ta kawo, ba mai kallon wani, juya masa bayan da mahaifinsu ya yi, ba ?aramin tsaye masa ya yi ba a ransa.
Sai dai ya je ya saka Ammi a gaba, ya yi ta kuka, abun da ake yi musu da tare shi da Mahmud, yanzu sai dai ayi wa Mahmud shikaWai, hakan ya sanya ya ?ara tsanar Mahmud!.

Ro?on Allah da neman magani, da Ammi ta dage a kai ne, ya sanya ya samu sassauci har ya koma makaranta.

Lokacin da za su shiga jss1, Mummy ta saka aka kai Mahmud boarding, aka raba shi da gidan baki Waya, dan yanzu galadima baya iya ?etare maganarta.

A hankali aka Wan fara sakin jiki da Adam, cousins Win sa suke wasa da shi, kasancewar makarantar su ma Waya.
A gidan su jamil, gidan turaki wanda yake wa ga sharif, akwai ?ar sa Waya da ya Worawa so shi ma, bayan mahaifiyarta ta rasu, mai suna Aisha yake kiranta da fulani, sai dai a bayan idonsa, babar su jamil, ta tsani yarinyar, kamar ba ?ar sarauta ba, saboda azabtarwa daga yayyenta, da kuma uwar ri?onta.

Tun ana yi a bayan idonsa, aka dawo yi a gaban idonsa, ba ya iya cewa komai, wasu lokutan ranar juma'a sai Ammi ta aika a Wauko mata Aisha, a kai mata ita, ta yi mata kitso, ta saka ayi mata lalle, tana son ?a mace, laila kuma ta riga ta balaga.

Ana haka Ammi ta haifi nusaiba, ta din ga murna, ta samu ?a mace, da wata salla suka je gombe, a nan yayan Ammi yake ce mata, ya wuce ta rigar su ade, ya ga kamar da mutane.

Nan da nan Ammi ta Wau hanya ta tafi, sai dai ta je ta tarar da wata kyakywar bafulatanar yarinya, da ciki.

Suka gaisa da Ammi, take tambayarta, ina su Ade.

Yarinyar ta ce "Ade kakata ce, sun yi gaba, ni daga yaye aka bar ni a wurin yayan babana, to sun tashi zasu tafi can iyaka, in da tushenmu yake, ni dai ban san sunan wurin ba, to mu ma can zamu tafi, da ni da yayan babana ne, da matarsa sai maigidana, sauran ayarin da muka taso tare sun yi gaba, ni kuma na yi nauyi, shi ne aka ce mu zauna in haihu, sai mu tafi, yayan babana ya san in da suke, ina son in ga Ade, kakata".

Ammi ta ce "Allah sarki, Ade kam tana bani labarinki, ta ce mamanki ma tana wata riga tana aure ko?"

Yarinyar ta jinjina mata kai.

"To ina mijin naki da matar yayan baban naki?".

Ta ce "Sun tafi kiwo, ita kuma ta je yin itace".

Ammi ta din ga murna ta ga jikar Ade, kasancewar za su yi kwanaki a can, ya sanya kusan kullum sai ta je, har suka saba da matar yayan baban ade.

Ammi ta sha mamaki, irin yawon da fulanin nan suke da shi, sun yi sanani sun hayayyafa, sun shafe shekaru a wurin, kuma su tashi su yi wani wurin kamar wasu iskokai.

Mijin yarinyar ma, mairamu yana matu?ar girmama Ammi, su yi ta Waukar nusaiba suna yi mata wasa.

Ammi kar ta tafi ta bar gida, dan ?arfin zaman na ta ma, ayi wa Adam Addu'a ne, da nema masa magani.

Bayan Ammi ta koma Kano, tana yawan yin waya, a kan aje a gano mata jikar Ade.

Sai dai aka kira Ammi, daga garin su, aka gaya mata, an kashe mijin mairamu, an kore dabbobinsu, kuma an rasa yayan babanta da matarsa.

Kasancewar ammi ba laifi, tana faWa aji, ta saka aka kai report wurin ?an sanda, amma ba wani labari, Mairamu ta tayar da hankalinta, a gidan su Ammi aka yi wa mijinta sutura, aka rufe shi.

Ita ba ta san kowa ba, sai mijinta da yayan babanta, in da suka baro, duka suka taso, ayari sun yi gaba sun bar su, dan su har a lokacin ba ruwansu da abun hawa, kuma ba ta san in da za aje ba, dan ta na da ?uruciya sosai abun da ta ri?e a in da za su je kawai shi ne kan iyaka, nan ne tushensu.

Saboda tsabar damuwa, ta fara na?udar dole, aka kwasa aka kaita asibiti, ta haifi yarinaya kyakkyawar gaske, jawur da ita.

Ammi ce ta yi mata role Win uwa da na uba, dan ba zata manta karamcin Ade ba.

Ta tambayeta sunan da za a sakawa ?ar amma ta ce ta saka mata duk sunan da take so.

Ammi ta ce "Ta saka mata Khadijah, sunan mahaifiyar ta, kuma ?ar ta da ta taSa rasuwa, amma take ce mata Iman".

Ta din ga rarrashin mairamu, tana bata tabbacin, za ta yi ?o?ari a nemo in da ?an uwanta suke, kuma a lokacin waya sai gidan manya, balle a sameta hannun bafulatanin daji.

Haka Ammi ta din ga sintiri tsakanin kano da gombe, mahaifiyar laila da ammi ta ri?e, ta cigaba da Wawainiya da Mairamu, dan a lokacin suma iyayen duk babu.

Sai dai har watanni uku, babu labari a kan in da ?an uwan mairamu suke, ga ?uriciya kuma ta yi ta fama da rashin lafiya, ?arshe Allah ya yi mata rasuwa.

Ammi ta yi kuka sosai da sosai, ta ce sai yayarta ta bata Iman, ya ce ba zata ba, sai ta nemo iznin mijinta.

Ammi ta yi wa galadima bayani, ya ji rauswar yarinyar, kuma ya san Wawainiyar da Ammin ke ta yi, dan haka ya ce ta Waukko ?ar, dan ya san soyayyar da ke tsakanin Ammi da Ade.

Ta zube har ?asa ta din ga yi masa godiya.

Ta je ta Waukko Iman, a lokacin kuma ta riga ta yaye Nusaiba, ya ce ko magani za ta yi, da ruwan nono zai dawo ta shayar da iman, yayarta ta ce kar ta shayar da ita, ta na da ?a?a maza, ba ta san me gobe za ta yi ba.
Haka ta ha?ura, ta Waukko iman, ta zo tana bata madara.

Kowa ya ga Iman sai ya tankata, saboda tsananin kyan da take da shi, gaya jaririya, amma gashinta irin na larabawa, mai tsawo.

Nan ma mummy ta samu na yi, wai Ammi saboda jaraba, an yarda ?ar shege ta Waukko wai tana so, kamar ?ar jari bolan ?a?a, Wan kowa ma sai ta Waukko ta ce za ta ri?e, da ganin kyan wannan yarinyar, an san shegiya ce.

Aikuwa aka yadda, wasu lokutan ammi har mamaki take, yadda sirrikanta ke fita.

Jamila ta hurawa galadima wuta, a kan lallai ya sa ammi ta mayar da ?ar nan, duk dan ta cusa wa Ammi ba?in ciki.

Ya kuwa je ya samu Ammi ya ce bai yarda da ri?on ?ar ba, sai da Ammi ta dangana da wurin sarki, da mai babban Waki a kan su saka baki.

Mai babban Waki ta ce "Dan Allah idan ma ?ar tsintuwar ce, ita ta na so, ?ar ta yi mata kyau Tubarkallah".

Da ?yar galadima ya amince, bayan mai martaba ya yi masa ta tas, a kan abubuwan da yake yi.

Iman ta fara girma, ga fari ga kyau, ga uban gashin nan, kullum tana tare da laila da su nusaiba, ga Aisha idan ta zo, amma muddin ta sake suka haWu da Mahmud, Fauziyya ko ru?ayya, to tabbas sai ta yi kuka, saboda cin zali.

Sai dai duk da haka, ?a?an jamila na shiga wurin Ammi, kuma ba zaka ce ba nata bane ba, sai dai suna tsoron laila, dan suka yi mata rashin hankali ubansu take ci, duk da ana yi mata gorin ba gidan ubanta ba ne ba, ta kan ce musu, Jamila ma an ri?eta ba a gidan ubanta ba, dan ita har da Mummyn ma yi take yi, duk yadda Mummy ta so ta saka Galadima ya kori laila abu bai yiwu ba.

Adam kuwa yau fari, gobe tsumma, kusan kullum cikin rashin lafiya, idan ciwon nan ya tashi kuwa, haka zai ta burgima yana ihu, yana neman abun da zai ri?e ya samu sassauci, makaranta wasu lokutan sai dai a jingine ta.

Sashin Ammi ya zama wurin faWi tashin yara, wannan ya shiga wannan ya fita, ta koya musu karatu, ta yi musu girki, mai assignment ta yi assisting Win sa. Mummy ta yi ta jawa iyayen yaran kunne, a kan su yi hankali da yaransu, kar mahaukacin Wan ta ya kashe musu ?a ?a, amma yaran sun riga sun sha?u da ita.

Idan har Mahmoud yana hutu, Mummy ta din ga kitsa masa abun da zai je ya gaya wa galadima takawa ya yi masa, idan ya gaya masa, ba bincike haka zai hau Adam da faWa, har ta kai ammi ta ce masa, kar ya sake hantarar mata Wa, da wanne za su ji? Rashin lafiyarsa ko faWan da yake yi masa.

Dan haka a duk lokacin da Adam ya san Mahmud yana nan, ba shi da sukuni, saboda faragabar abun da zai je ya ce ya yi masa, kuma hakan ya sanya Adam ya tsani Mahmud sosai da sosai.

Adam ba ya jin daWin hantarar da ake yi masa, mussaman idan aka shiga da shi taro.

Kasancewar da shi da Aisha, da Iman, ?addarasu na kamanceceniya, ya sanya ba shi da wanda yake ?auna sama da su.

Ya dai girmesu sosai, amma ya na jin daWin rayuwa da su, a haka Wan wani attajiri ya ce yana son laila, ba yadda Mummy ba ta yi ba, a kan kar abun ya yiwu, amma hakan ya ci tura, laila ta yi aure ta bar ?asar.

Daga baya Mahmud ya samu labarin, Ammi ce ta haife shi, amma bai taSa jin hakan a zuciyarsa ba, a ganinsa da ita ta haife shi, Meyasa ba ta son sa sai wannan Adam Win.

Idan ciwon Adam ya tashi, daga Ammi sai Aisha ko Iman, suke iya zuwa wurinsa, duk da ya taSa Waga Iman ya yi cilli da ita, sai da ta suma, amma tana farfaWowa ta fara kiran kakawa, lokacin ba ta gama iya faWan sunan sa ba.

A lokacin iman ta yi ta rashin lafiya, aka kasa gane me yake damunta, sai da ?yae, wai zuciyar ta ce take kumbura, Ammi ta tashi hankalinta, tana tunanin ko tsangwama ce ta sanya ta haWu da ciwon zuciya da ?uruciyarta.

Kwatsam rannan galadima ya yanke jiki ya faWi, ya fara rashin lafiya, nan ma Mummy ta ce Ammi ce, ?arshe dai Ammi ce ta yi jinyarsa, sai da ya kusa rasuwa, ya din ga neman yafiyarta, da ta takawa, dan bai san yadda aka yi, ya din ga wasu abubuwan ba.

?a da uba sai Allah, bayan rasuwar galadima, Adam ya yi kuka, ko ba komai mahaifinsa ya nuna masa ?auna, a baya, Mahmud ma ya Wimauta da wannan babban rashi da aka tafka a gidan sarautar.

Mummy ta din ga dariya, dan ta san dai ba za a bawa takawa sarauta ba, na farko yaro ne, kuma ga larura. Dan haka Waga likkafar mahaifin jabir ya zama galadima.

Tana ta murnar tun da Adam ba shi da lafiya, nan gaba ko za a bayar da sarauta, Wan ta za a bawa Mahmud, amma aka tunatar da ita, yanzu babu Galadima, giwa za ta iya duk mai yiwuwa ta karSe Wan ta, dan haka ta ce dole ayi biyu babu, ya din ga kwaWaitawa ?awarta Lubabatu, Wan ta jabir yayi mulki, nan gefe tana kuma turawa Mahmud ?iyayyar Adam tare da tura masa son mulki, amma sai dai sam, shi kamar mahaifinsu ne, bai damu da sarautar ba, duk da Adam ya fi gado kamanni da murWaWWen hali na mahaifin su.

Adam yana girma ciwo yana Wan raguwa, dan a haka yayi karatu, abu ne mawuyacin ciwon ya tayar masa a waje, Sai a gida.

Ya sha?u da Nusaiba da Iman sosai, musamman iman da yake ganinta kamar wata ?ar ?aramar mage mai kyau, ya cafata nan ya cafata can, sai dai duk da hakan suna girmama shi sosai dan akwai tsare gida.

Gefe guda, Samha ta ?allafa rai, tana ta nuna masa so, amma mahaifiyarta ta dankwafeta, saboda rashin lafiyar Adam.

Yayin da shi kuma ya fi karkata, ga Aisha, duk a lokacin bai san son ta yake yi ba, muraran Samha da mahaifiyarta, da kuma ?an uwanta ke nunawa aisha ?iyayya, ganinta suke kamar ba ?ar uwasuu ba, mussaman yadda turaki yake tausayinta, komai sai ya ce 'yar marainiya. Sanin sassauci ta sai idan Adam ya je gidan ya Waukkota, ko Ammi ta aika a Wauko mata ita.

Abubuwan da suke yi wa Aisha, ya sanya Adam ya fara tsanar mahaifiyar su Samha, Saboda ganinta yake

Please Login or Register in order to submit comment