You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ku yi sallama, ai bai kamata ku tafi babu sallama ba".

"To ai yaya Aliyu ya ce bai mutu ba, har ya tashi"

"Haba rumaisa, idan da kara yakamata ki je ki duba shi, ko dan albarkacin sabir Winki".

Usman ya ce "Sai ka lallaSata ma, wuce mu je, kuma saura mu je ki yi rashin kan gadon naki, ya saka dogarai su saita miki zama".

Suka Wunguma zuwa Wakin da takawa yake, suka tarar ammi na zaune a kusa da shi, ta ri?e hannunsa, tana share masa hawaye.

Ammi na ganinsu tayi murmushi ta ce "Kun fito? Yau ban ?araso mun gaisa ba rumaisa, hankalina ne a tashe"

Ruma ta dur?usa ta gaisheta, ta amsa mata cikin girmamawa.

Usman ya ce "Ki yi masa sannu mana"ta dubi Adam za ta yi masa magana, amma gabanta ya faWi, ganin gaba Waya idonsa ya koma ba?i, yana fitar da haya?i.

Mannewa ta yi bayan usman, tana le?o shi, taga ita yake kallo, amma idonsa yana ta haya?i, kallonsu take yi, tana jiran ta ji wani yayi magana a kan idon takawa, amma ta ji babu wanda yayi magana da alama su ba sa gani.

"Ba zaki yi masa sannun ba?"

Ta sunkuyar da kanta ?asa ta Wan zuro kai ta ce "Sannu, Allah ya bada lada" tayi maganar a rikice dan a razane take, bata taSa ganin idon mutum a haka ba.

Bashir ya ce "Ladan me kuma rumaisa, shi da ba shi da lafiya?".

"Au ba lada ba, Allah ya warkar da shi"

Usman ya ce "Yau kuma meke damunki ne?"

Mama ce ta kwance Sabir daga bayanta, mai sunan baba ya karSe shi,? ya ?arasa gaban gadon Adam ya ce "Allah ya ?ara lafiya, ya ji?an mamansa, kamar yadda ka bu?ata ga yaronka, Allah ya raya shi, Allah ya biyaka Wawainiyar da ka yi da ?anwarmu". Adam ya karSi Sabir, yana ?o?arin mayar da hawayen idonsa.

A rikice ruma ta ce "Ban gane ga Wan sa nan ba, da shi zan tafi ai, ni anty aisha ta bar wa shi" tayi maganar tana nufar Adam, amma mai sunan baba ya tare ta ya ce "Juya mu tafi" karo na farko da ta tsaya ta saka idonta a nasa ta ce "To ka karSo mini Wana".

"Ni nake magana ki ke mayar mini?".

"Haba mai sunan baba, ya za ayi a ?wace mini yarona, dama abun da aka shirya kenan? Mama ki saka baki" ta dubi Ammi ta ce "Dan Allah ku bani yarona, na sha wahala kan mu tsira tare, idan aka ?wace mini shi, mutuwa zan yi, wallahi ina son sa sosai, Wan uwanmu yaya bashir, dan Allah ka karSo mini Wana"
Gaba Waya sai tausayin rumaisa ya kama su. Ammi ta ce "Kina ji ruma, ki kwantar da hankalinki, babu mai rabaki da yaronki, zamu je a kai shi cikin dangi ne, kuma in sha Allah za a din ga kawo miki shi ki ganshi".

Rumaisa ta fashe da kuka ta ce "Da na san haka ne, gara na zauna mu mutu a dajin, da da wannan mutumin ya ce in tafi ba zan tafi ba, gara a harbeni, kwanana biyu ba ma bacci ni da sabir, saboda sanyi yana kuka, kwanana uku ina bulayin hanyar da zamu dawo, kuma a ?wace mini shi bayan mun sha da ?yar, ba anty aisha ba sabir Wina. Dan an ga ni yarinya ce za a ?wace mini Wa" Mai saunan baba ya dan?i hannunta zai yi waje da ita, tana kuka tana mi?a hannu tana "Dan Allah ku bani sabir Wina" tun da ruma ta fara kukan nan tana zuba, ko Waga kai Adam bai yi ba ya sunkuyar da kansa ?asa.

Kuka sosai rumaisa take yi, tamkar an ce mata mama ta mutu, bashir ya rakosu yana ?o?arin rarrashinta, amma mai sunan baba ya ce ya rabu da ita, ya buWe mota ya sakata, amma sai mi?a hannu take taka kuka.

"Ki rufewa mutane baki, idan an baki Wan ya zaki yi da shi, ke wace irin yarinya ce da ba a isa a gaya miki, ko ki rufe mini baki, ko na casaki a wurin nan" mai sunan baba yayi mata wata irin tsawa mai razanarwa.

A gigice ta ?an?ame mama tana ?o?arin haWiye kukanta, amma ta kusa ?warewa saboda kuka, ga hawaye ga majina har da yawu, saboda kuka.

Ammi na tsaye tana hango rumaisa yadda ake fama da ita, wani irin tausayinta ya kamata. Allah kenan ya karSi uwar yaron, kuma ya sanya soyayyarsa mai tsanani a wata zuciyar.

A hankali ta juya ta koma Wakin da adam yake, yana rungume da jaririnsa.

Ammi ya dube shi ta ce "To me ka yanke? A ganina mu bari nan da ko kwanaki biyu ne ka gama warwarewa".

Adam ya girgiza kai ya ce "Ammi, ba zan taSa warkewa ba, barin lamarin ina sake jinkirta loka8, abubuwa caSewa za su cigaba da yi, daga nan gidan turaki zan wuce, zan je na sanar masa da laifina gaba Waya duk hukuncin da ya yanke a kaina shikenan".

Cikin damuwa Ammi ta ce "Kana ganin hakan shine mafita?".

"Ammi dole ita kaWai ce mafita, na yi zaton aisha tana raye ne dama, shi ya sanya nake ta jinkirtawa, amma na yadda ta rasu yanzu, yanzu zan fara fuskantar mai girma turaki, daga baya kuma sai na fuskance ?alubale na gaba".

Ammi ta Wan yi shiru yana kallon ?asa, daga bisani ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shin, Ubangiji Allah ya yi mana jagora baki Waya "

Ya amsa da amin.
Bashir suka shigo tare da likita, likitan ya dubi adam da yake rungume da jariri ya ce "Allah sarki rumaisa, gaskiya ta sha?u da yaron nan, ba ka kyauya ba da ka ?wace mata Wa" Adam ya sunkuyar da kai ba tare da ya iya yin magana ba.

"To Yanzu me yake damunka, zan rubuta maka teses na yi reviewing file Win ka, na ga vitals Win ka duk normal".

"Sallama nake so" ya faWa a ta?aice.

"Meyasa zamu sallameka? Dole mu ri?e ka zuwa gobe in Allah ya kaimu mu ga abun da hali zai yi".

"Ba zaku hana Allah zartar da hukuncin sa ba, ku yi ha?uri tafiya zan yi " duk yadda likitan nan ya so lallaSa adam ya Wa zauna, amma ya?i ammi ta ce ya basu sallama kawai, suna da issue a gida.

Haka kan likitan ya rubutawa adam sallama, da yayi tunanin ya kira jabir su tafi tare, sai ya ga babu wani amfani ma da jabir Win zai yi masa a halin yanzu, dan haka kawai ya share suka tafi.

Suna tafe a mota, yana kalon sabir da yake ta ?amshin turare, yana wasa da hannunsa, har da farar hoda da kwalli mama ta shafa masa, ba ayi masa aski ba, dan haka suma ta cika masa kai, ga ta a cike ba?a siWik, har ta ?asan hularsa ta fito, ga gashin girarsa a hankali yana tofowa.
?asan zuciyar Adam yana ta fargaba da tunanin, yadda zai fuskanci turaki.

Har gidan turaki bashir ya kai su, sai dai shi ya tsaya a mota, su kuma suka shiga.

Da fari ta ?ofar turakar turaki ta harabar gidan, Adam ya shawarci Ammi su shiga, amma sai suka tarar da ita a rufe, dan haka dole suka bi ta cikin gida.

Falon ba kowa sai hadimai, suna ganin Ammi tare da Adam, cikin rawar jiki suka gaishe su, aka tafi nema musu iso wurin matar gidan.

Ba su jima a zaune ba sai ga mama ta fito cikin ta?ama, ta dubi Ammi ta yi murmushi ta ce "Giwa, yau ke ce a gidan namu?"

Ammi ta ce "Ni ce, kin san Waurowa take a Waure al?ali, ya gida ya iyali?"

"Alhamdilillah, takawa magajin takawa, dan kujerar galadima ta yi maka ?an?anta babbar kujera muke fata" tayi maganar tana kallon jaririn hannun Adam.

Ta sake cewa "Ina ku ka samo Wa?"

Adam ya ce "Dan Allah idan babu damuwa, muna neman iso wurin mai girma turaki idan yana nan"

Ta Wan jinjina kai ta ce "Yana nan, bari ayi masa magana".

?anwar Samha ce ta fito sumayya, ta gaida Ammi tare da takawa, ammi tambayeta ina samha, ta ce mata ta je abuja.

Mama ta fito ta ce "Bisimillah, ku shigo"

Ammi ta tashi, tana gaba adam na bin ta a baya, suka shiga falon turaki.

Yana zaune a falonsa, gefensa ga Alqur'ani a ajiye, da alama karatu ya idar.

Ya kallesu yayi murmushi ya ce "Maraba da manyan ba?i".

Ammi ta risuna ta ce "Barkanmu da wannan lokaci"

"Barka dai, ya iyali ya kuma rayuwa"

Ammi ta amsa da Alhamdilillah, maimakon mama ta fita ta bar Wakin, sai ta nemi wuri ta zauna.

Turaki ya kalli Adam ya ce "Takawarka lafiya, ana lafiya?"
Adam ya jinjina kai kawai, amma bai yi magana ba.

Ammi ta gyara zaman ta ta ce "Allah ya baka nasara, wata muhimmiyar magana ce ke tafe da mu, amma kan in ce komai, zan fara da neman afuwa sannan a sassauta mana hukunci"

"Babu laifi, ku muke sauraro".

Adam ya tashi a hankali, ya tafi gaban turaki ya dur?usa, ya Wora masa Mahmud a kan cinyarsa".

Turaki ya rungumi sabir ya ce "Masha Allah, ina na samu Wa, Wan kyakykyawa Masha Allah?".

"?an wurin aisha ne" takawa ya faWa jiki a sanyaye.

Turaki ya faWaWa fara'arsa ya ce "Ikon Allah, uwata yaushe ta haihu?, yaushe rabona da ita?"

"Allah ya baka yawan rai, ha?i?a ni mai laifi ne, kuma a shirye nake da karSar hukuncin da duk ka zartar a kaina. Wannan jaririn Wan wurin aisha ne matata, kamar yadda aka kai ruwa rana da surutu a kan karatu da nace zata tafi. Duk ba wannan ba ma, maganar da nake maka, yanzu haka fulani ba ta duniya, ya rasu" Adam yayi maganar kansa a ?asa hawaye na gangaro masa.


Ayshercool.

paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu bu?atar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*




Haka suka cigaba da ?ulla mugunta kala-kala suna dariya.

Wunin yau Samha ba ta bi ta kan wayoyinta ba, sai yanzu ta nutsu, ta Wau wayoyinta ta kunna, ta ajiye su a kan gado, ta shiga wanka. Daga shigarta wanka zuwa fitowar ta missed calls sun fi goma sha.

Mamaki ne ya kamata, tana shirin duba missed calls Win, kiran Fauziyya ya shigo wayarta. ?an Sata fuska ta yi ta ce "Wai lafiya ake yi mini wannan kiran kamar mara gaskiya?".

Fauziyya ta ce "Ke dalla can, idan ma wani rabon ne har ya wuce ki baki Waga waya ba, kawai kin wani kashe wayoyi".

"Ke karki Waga mini hankali, hutu na zo yi dan me za a dameni? Ina jin ki"

Fauziyya ta ce "To, ai ni zancen ne ma ban san ta ina zan yi miki shi ba, abun farinciki zan ce miki, ko kuma tashin hankali da jimami, ko kuma abun Waure kai?"

Samha ta Wan juya idonta ta ce "Fauzi, zan kashe wayata fa".

"Katangar da ta daWe da tsaye miki, ta hanaki cikar burinki ta rushe".

"Kamar yaya kenan?".

"?anwarki ce ta mutu"

Mi?ewa Samha ta yi, ji ta yi kamar ba ta ji dai-dai ba, wai ?anwarta ta mutu.

"?anwata wacce? Wace ?anwar tawa?"

"Ahh, wacece ta sha gabanki ta hana cikar burinki na auren yayanmu, aisha Wazu aka ce wai ta rasu a wurin haihuwa, a garin da ta je karatu, amma an dawo da jaririnta, amma dai kamar akwai wani abu da ake Soyewa ba a son a sani".

Wata iska samha ta fesar ta ce "I hope ba ?arya ki ke yi mini ba?".

Samha ta ce "Ana ?arya da mutuwa ne? Ki tambayi wanda ba sa yi miki ?arya sai ki tabattar".

"Am sorry, ba haka nake nufi ba, zan kiraki" ta kashe wayar ta cillata kan gadonta, ta hau sintiri a Wakin.

To murna za ta yi ko kuwa jimami, wata zuciyar ta ce "Ke ina ki ka gata jimami, damar da ki ka daWe ki na jira, Allah ya kawota a sama ki tsaya wani jimami? Yanzu hanya ta mi?e miki fetal, aiki kaWan ya rage miki".

Wayarta ta rarumo, sai dai ta rasa wa za ta kira ma, jefar da wayar ta yi, ta janyo akwatinta ta hau shirya kayanta, ko ba ta samu jirgi ba a mota zata koma gida gobe.

A daren ranar babu wanda ya runtsa a iyalin ammi, mussaman ita, da a kunnenta kishiyarta da facalolinta ke jifanta da miyagun maganganu.

Sabir kuwa tuni mama ta aike da shi gidan wata 'yar garinsu da take aure a kano, matar kamar ?anwa ce a wurin ammi, dan haka aka kai sabir can, duk surutun da aka din ga yi ba ta faWi in da sabir yake ba.

Washegari ma haka aka Wora zaman makokin aisha, samha kuwa tun da sassafe ta taho kano, sai dai ta rasa wani mood yakamata ta shiga, na farinciki ko akasin haka? Duk yadda ta so ta ji lamarin ya ratsata ta kasa, babban fatanta Allah yasa da gaske Aisha ba ta raye.

Sai da ta isa gida ta tarar da tarin mutane, sannan ta tabattar da gaske aisha ta mutu, tun daga waje ta fashe da kukan ?arya, dan kar a fuskanci wani abu, kai tsaye ta nufi cikin gidan tana kuka kamar gaske.
Nan yan makoki suka din ga rarrahinta suna yi mata nasiha a kan aisha addu'a take bu?ata ba wannan kukan da take yi ba.
Abu kamar gaske, Samha ta din ga kuka tana tumami, ana rarrashinta da ?yar ta yi shiru, ta tafi Wakin mamanta ta kwanta ta samu bacci.

Sai bayan la'asar sannan Hajiya Asama'u ta shiga Wakin ta tashi Samha.

Ta dubi Samha ta ce "Ke yanzu Samha dan aishar ta mutu ki ka zauna kina wannan uban kukan kamar ni na muty? Yarinyar da ta hanaku rawar gaban hantsi a wurin mahaifinku, har wani kukan mutuwarta zaki yi?".

Samha ta Wan duba bayan mama, ta ji babu almar wani zai shigo, sannan ta dubi mama ta ce "Mama na dole ne, ko ba kowa ba wasu san da cewa ina son Adam, idan har na nuna ban damu ba, wasu ma ai sai su ce ina murna da rasuwarta ne, nima na dole ne kukan, amma mama ya aka yi ta mutu wai? Sannan ina Wan da ta haifa Win?"

Mama ta kwaSe baki ta ce "Mhmm, su suka san me suka yi mata dai, wai can in da ta tafi karatun a can ta zo haihuwa ta rasu, jiya nan suka zo da jaririn, ammma sun ?i fito da shi yanzu, tun jiya ake fama amma Giwa ta?i faWar in da yaron yake sai Soye shi take sai ka ce ciwo".

Samha ta jinjina kai ta ce "TaS a nan aka yi mata sutura kenan?".

"To waye ya ga gawarta, wai a can london Win ta mutu aka binneta, haka suka ce fa, ni ko yaushe ta yi cikinma oho, na ga dai tana can tana karatu, to can ya bita yayi mata cikin? Ko kuwa da cikin ta tafi Allah masani, saboda wata lalacewa ma, ita ya turata karatu ?asar waje, ya zo yana nema ya haikewa iman".

Samha ta girgiza kai ta ce "Mama ba haka aka yi ba, batun iman wannan wani abu ne da Mummy ta shirya shi, amma yadda abubuwan ne suke wakana, akwai wani abu a ?asa, amma dai bari na yi wanka na sauya kaya".

Ta tashi ta Wau wayarta ta shiga banWaki, lambar Khalifa ta nemo, ta kira shi, sai da ta kusa katsewa sannan ya Wauka.

Ba sallama ba komai ya ce "Ya akwai labari ne?"

"Eh kusan haka, Allah ya yi wa matar adam rasuwa ne".

"Na ji labari" ya katseta.

"A ina ka ji?".

"Kin manta fitacce ne shi? Labarin duk ya karaWe dandanlin sada zumunta".

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Haka ne, sai dai an ce a can london wai aka binneta, ba a kawo gawarta ba, sai jaririnta kawai".

Da sauri khalifa ya ce "What? Jariri kuma? How a wace ma?abartar aka binneta a London Win? Suwaye suka halarci jana'izar ta a can?"

"I don't know, nima abun da na zo na tarar kenan" ta bashi amsa.

Khalifa ya yi dariya ya ce "Shikenan, kin zo mini da labari mai daWi, wannan ma wani abu ne na ya?ar adam".

"Amma dai ina fatan ba cutar da shi zaku yi ba, sannan ina son cire hannuna a contract Win nan, tun da ma dai wadda ta hanani rawar gaban hantsin ta mutu, ina ga na samu chance"

Khalifa ya ce "Haka ki ke gani?"

"Eh mana, babu abun da yayi saura ai"

"Ba zai yiwu ki saSa yarjejeniyar mu haka kanki tsaye ba, dole ki kammala mini aikina".

A fusace samha ta ce "Kai saurara, ba fa 'yar ka ba ce ni, ka daina yi mini magana da isa kana bani umarni, ka kiyayeni" da haka ta kashe wayarta tana tsaki.

Kwanaki uku aka yi aka watse daga makokin aisha, sai dai adam sam baya hayyacinsa, kana kallonsa ka san a tashin hankali yake, ko abinci baya iya ci, haka yake tafiya gidansa, ya zauna ya saka kayan aisha a gaba yana kallonsu.
Ranar da suka rabu ya tuna, da zai yi tafiya, lokacin kwananta biyu da dawowa tana yi masa magiyar ya barta ta yi tafiya, ya din ga jan kumatunta yana yi mata dariya ya ce "Cikin nan naki ya sanya kumatunki ?ara cika, kuma sun fi daWin wasa a haka" kwaSe fuska ta yi za tayi masa kuka ta ce "Dan Allah ka mayar da maganata serious please ka bari na je".

"Ki bari idan na dawo da kaina zan kai ki, kin ji fulanina".

Kamar ?aramar yarinya ta shiga turza ?afarta za ta yi kuka ta ce "Dan Allah kar ta mutu ban je na dubata ba".

Ya Wan tsuke fuska ya ce "Bana son rigima fa, ke ba ki ga yadda cikinki ya tsufa ba, kin san hatsarine ki fita a san kin dawo, a sirri fa na bari ki ka dawo, tun da kin kasa ri?e kanki, sai kin dawo wurin mijinki"

BuWe baki ta yi ta ce "Ni haka nace maka?"

Dariya yayi mata ya ce "Idan ma baki ce ba, yanayinki ya nuna ai, tun da ki ka dawo ko waje ban le?a ba, soyayya kala-kala kawai nake sha, ki yi ha?uri jibi zan dawo in sha Allah sai na kai ki"

Idonta ne ya cika da hawaye, amam ya mayar da abun jokes, ya cigaba da ja mata kumatu yana kashe mata ido.

Da ya zo nan a tunaninsa ya dur?ushe a kan gwiwoyinsa, yana kallon kujerar dressing mirror da ta zauna, suka yi wannan abu, da washegari ya ga message Win ta na ban ha?uri, a kan ba zata iya jiran dawowoarsa ba jikin kakarta ya tsananta da yawa.

Ya dinga zubar da hawaye yana surutai a hankali, wata irin kewarta tana ratsa shi.
Wani abu ne mai kama da bacci ya Wauke shi, kawai sai ganin rumaisa ya yi a kan kujerar, tana zaune tana ta yi masa dariya, 'Sarki mai koriyar alkyabba, ka Wananiba dokinka" tayi? masa maganar tana murmushi, daga bisani ta taso ta nufo shi, tare da mi?a masa hannu, ya mi?a hannunsa zai ri?o nata, kawai yayi firgigit ya farka yana kalle-kalle. ?an tsuke fuska ya yi, ya tuna yadda ya din ga fama rumaisa tana yi masa gizo a baya, da ?yar ya daina ganinta, kwatsam yanzu ma ta cigaba da yi masa gizon, ba dan ya ganta tare da 'yan gidansu ba, to da babu shakka zai gazgata cewar aljana ce ita.

Kusan kwanaki ukun nan, rumaisa ta ?i sakin jikinta, kusan kullum cikin kuka take a kan a dawo mata da jaririnta, tun mama tana ta tata har ta gaji ta ?yaleta, abinci ma sai an yi kamar za a zaneta sannan take ci. 'yan islamiyyarsu tawaga guda suka yo, har da malamansu suka sake zuwa dubata, amma mirsisi ta?i kulasu, ta?i magana.

Kwanaki huWu da sallamar su, mama ta ce wa usman yakamata su je gida su yi wa ammi gaisuwar rasuwar aisha.
Mai sunan baba na jin jaka ya ce bai yadda ba, kar su zata wani abun suke nema a wurnsu, tun da sun yi musu gaisuwar a asibiti ya isa.

Mama ta ce "Kai ka san ba zamu je wurinsu domin neman wani abu ba, amma dai-dai gwargwado sun yi Wawainiya da ?anwarku, kuma babu laifi dan an bisu gida an kuma yi musu gaisuwa, shi ne abun da yakamata ai, tun da rashi suka yi. Shi dai mai sunan baba ba haka ya so ba, amma babu yadda ya iya haka ya ha?ura ya ?yalesu.

Mama ya shirya ya saka rumaisa ta shirya, ta ce usman da Aliyu suka raka su, ruma sai murna take ko ba komai, zata ga Sabir, sai jin daWi take yi, ta shirya cikin riga da hijjabi, sannan ta kawo face mask ta saka.
Usman ya ce "Meye kuma na rufe fuska?".

"Bana son a din ga kallona duk in da na je"

Ya ce "Ko kuma baki da gaskiya ba, ko kin yi wa wani laifi"

"Haba yaya usy, yaushe na dawo da zan nemi maganar ma".

Yayi murmushi ya ce "Ashe kina sane ki ke neman maganar"

Gyara zaman hijjabinta ta yi, ba tare da ta sake magana ba suka tafi.

Gidan galadima kuwa, ammi ta karSo sabir, su iman sun kewayeshi suna kallonsa, yaron ha?urinsa har yayi yawa, ba ya kuka sai ya ga dama, sai dai yayi ta bacci.
Babu in da ya bar adam, kamarsa Waya sak da adam, an yi masa wanka an shirya shi, nusaiba tana bashi madara a feeder.

Iman ta ce "Allah sarki rayuwa, Allah ya yi wa anty aisha rahama, mun ci buri sosai a kan haihuwar nan, duk da yadda ake Soyewa ba a son a san da cikin, amma tayi buri a kan cikin, kusan kullum sai ta turo mini hoton siyayyar da ta yi wa baby".
Ammi ta ce "Rayuwar duniyar kenan, amma ba zan taSa manta yadda aisha ta mutu ba, Allah ka kawo mana tsaro a ?asarmu, ka ?ara kiyaye al'ummar musulmi" suka amsa da amin.

Adam ne ya yi sallama, suka amsa gaba Waya, su iman suka shiga gaishe shi, bai iya amsa musu ba sai jinjina musu kai kawai da yake yi.

Ya dur?usa ya gaida ammi. Ammi ta amsa masa tare da tambayarsa ya ha?uri.
Muryarsa a raunane ya ce "Alhamdilillah"

"Allah ya yi mata rahama, Sannan a cigaba da ha?uri duk mai rai mamaci ne". Ya jinjinawa ammi kai, tare da zura hannunsa a aljihunsa, Saboda vibrating da wayarsa ta fara.

Bai san mai lambar ba, amma ya Waga tare da yin sallama.

Aliyu amsa sannan ya ce "Aliyu ne yayan rumaisa, mun zo mu yi maka gaisuwa ne, mun shigo cikin gidan bamu san ina zamu bi ba, a wurin bashir na karSi lambarka".

Adam ya ce "Ok babu damuwa, bari na zo gani nan" ya mi?e ya ce "Ammi ina zuwa".

Rumaisa kuwa ri?e ?ugu tayi tana ?arewa harabar gidan su takawa kallo, ga motoci gefe guda kuma ga burgar dawakai, ko ina sai manyan bishiyu da ?anana, sai kalle-kalle take kamar 'yar ?auye, ga dogarai suna ta shiga suna fita, suna kaiwa da komowa a harabar.

Rumaisa ce ta fara hango adam ya nufo su, ya rame sai uban wuya, da dogon hanci, idon nan nasa jawur ya ?araso in da suke yana yi musu sannu da zuwa.
Risunawa ya yi ya ce "Mama sannu da zuwa, ya gida?".

Cikin kulawa mama ta ce "Lafiya lau, ya ?arin ha?uri?"

"Alhamdilillah"

Haka ya bi su usman duk suka gaisa, amma bai kula ruma ba, ita ma ba ya kula shi ba.
Ya ce "mu shiga daga ciki"

Rumaisa dama tun da ya zo yana fara magana, ta wani juya ?eya, irin ba ta ma san yana wurin ba, sai dai kamar yadda ta ga ya rame, haka shima ya ga tayi rama, ta fi cikowa kwanaki uku baya da aka sallameta daga asibiti.

Yayi musu jagora zuwa ciki, rumaisa ta gwalala ido, ganin kayan alatun da ke falon ammi, ya wuce da su babban falon, ya ratsa da su zuwa falon ammi, wanda bai kai wanda suka baro ba.

Yayi musu iznin su zauna, ya kira Waya daga cikin barorin ammi, ya ce a karSi su rumaisa. Ya ce "Bari na yi wa ammin magana".

"To ina Wana yake?" Ta yi maganar ba tare da ita kanta ta yi niyyar maganar ba.

Banza yayi mata bai kulata ba, sai da ya juya zai bar falon, sannan ya ce "Na kai shi koyo yadda ake gaida mutane"

Aliyu ya ce "Ai da abun duka ka samu ka zaneta wallahi, mara kunya kawai".

Adam yana barin falon, rumaisa ta mi?e tsaye, ta sake zama a kan kujerar ta

Please Login or Register in order to submit comment