You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau ba zata sake zuwa wannan makarantar ba da ake uzzurawa mutane.

Yasir kansa salati ya dinga yi da salallami "Dan girman Allah meyasa mai sunan Baba zai yi mana haka, ya saka yarinyar nan a makarantar nan ba a shawarce mu ba, wallahi mun kaWe"

"Oho muku, ku kwantar da hankalin ku, ni ba kuma zuwa zan yi ba, kawai ku bani Abinci"
Yasir ya dungure mata kai ya ce "Shegen ci kamar kazar hausa" suka sakata a tsakiya suna tafe suna zaginta, suka saya mata awara da ruwa ta cinye tsaf, sannan suka korata aji.

Ko da ta isa aji, tuni an gama karatun Alqur'ani, ana jiran wani malamin ya shigo.

"Ya aka yi daga zuwa fitsari ki ka daWe, gashi an gama ?arin Alqur'ani, sati mai zuwa idan Allah ya kaimu zamu bayar da hadda" cewar yarinyar dake kusa da Ruma.
Ruma ta kalleta ta ce "Ina aka biya Win?".
Yarinyar ta buWe Alqur'anin tana nunawa Ruma ta ce "Rabin shafi aka ?ara, gobe in Allah ya kaimu ma za a ?ara rabi, feji Waya kenan sati mai zuwa idan Allah ya kaimu sai ki kawo haddar".

Cikin ko in kula Ruma ta kawar da kanta gefe, alamar zancen yarinyar ma bai shigeta ba.

"Ya na ji kin yi shiru ne? Ki buWe sai na koya miki, idan fa baki iya ba babu ruwan ya sayyadi da sabuwar zuwa ce ke, zaneki zai yi".

Rumaisa da shishshigin yarinyar ya fara ?ular da ita ta ce "To a kasheni mana kar a barni da rai, ba cewa aka yi nan aji Waya bane ba, kuma sai a ?ara mini rabin shafi, kuma wai na haddace yo ta ina zan iya ni, nifa a makarantar da na baro sai nayi wata ina nanata aya biyu nake iyawa, wannan karatun ma na san ba zan iya ba sai dai ayi kwaWona da mai da yaji a cinye" galala yarinyar ta bi Ruma da kallo ta jinjina kai ba ta sake cewa komai ba.

Bayan an kaWa ?ararrawar tashi, malamin da ya yi mata interview ya kirata ya gaya mata cewar za'a fara karSar haddarta daga tushe, sannan za ta dinga yi tana haWawa da wanda ake yi musu a aji.
Da yake ma bata fahimci bayanin da yayi mata ba, hankalinta na kan ta tafi gida, dan ta san ba iyawa za ta yi ba, kuma ta gama yanke shawarar daga ranar ba zata sake zuwa ba sai dai Yaya Umar yayi mata abin da ya ga dama.

Ko su Huzaifa ba ta nema ba, ta nufi gida.
?a da uwa sai Allah, wuni gudan da mama tayi babu Ruma a kusa da ita duk sai ta damu, ta ji gidan babu daWi, gashi tana ta tunanin ko abinci Ruma bata tafi da shi ba, balle ta samu ta ci haka mama ta wuni sukuku.
Tana tsaka da tunanin Ruman ne, ta Waga kai taga Ruman a tsakar gida.

"Meye haka, babu sallama ki shigo ki tsaya?"

Ruma bata amsawa mama ba, sai kumbura baki da take yi, ta cire hijjabinta da jakar makarantar ta dungurar a wurin ta tafi kitchen tana dube-dube.

Ba ta saurari mama ba sai da ta ci ta ?oshi, Sannan ta dubi mama ta ce "Ni fa mama gaskiya ba zan sake zuwa makarantar nan ba".

"To ai ba ni zaki gayawa ba, wanda ya saka ki a makarantar zaki gayawa".

"Mama kin ga uban dukan da ake yi a makarantar nan kamar an samu bayi, kuma dan rainin hankali wai aka kai ni aji Waya ni za a kai aji Waya saboda raini, to wallahi makarantar malam babba zan koma ba zan iya ba"

Mama ta girgiza kai kawai, ta cigaba da aikin da take yi, Ruma ta saki baki ta dinga zuba tana cin alwashin ba zata sake zuwa ba.
Huzaifa ne suka yi sallama shi da Yasir, mama ta amsa musu. Basu kai ga zama ba suka hau mita.

"Mama dan Allah meyasa aka saka yarinyar nan a makarantar nan ba tare da shawarar mu ba? Kin san halin yarinyar nan tun a yau ta fara nuna halinta".

Ruma ta ce "Sha kuruminka ni ba komawa zan ba, daga yau ko za ayi ?uli-?ulina ba zan koma ba, wai saboda tsabar abu wai ?ari shafi guda, kuma wani satin ka kawo hadda, ni aya biyu nake iyawa waye zai yi wannan karatun taS ga uban duka wallahi ba zan sake zuwa ba

Yasir ya ce "Ai makarantar mu ba ta da?i?ai ba ce ba, ki koma inda ki ka fito ba zaki zubar mana da mutunci a makarantar nan ba".

Ba tare da sun san Umar yana gidan ba, yana Waki a kwance suke ta wannan zubar.

Tsuru-tsuru suka yi, musamman ruma da ta fi za?ewa, sai ganinsa suka yi ya fito tsakar gida.

"To dan ubanki ki daina zuwan kin ji ko, daga yau kar ki sake zuwa ki ga yadda zan yi da ke, kuma na gaya musu ba kya jin magana, idan har ba ki yi karatu ba su kama ki su zane ki"

Ruma a ranta ta ce "Ai wallahi sai na yi abin da za a koreni waye zai zauna ana jibgarsa kamar jaki"

Ya kalli su Yasir ya ce "Ku kuma, kune zaku dinga tsayawa a kan karatunta, ku zaku dinga koya mata dan da?i?iya ce, duk daWewar da ta yi tana zuwa makarantar allo ta kasa kawo izu biyu, sai karatun wani ta je tana iyawa, da?i?iya ki yi musu shirme na bayar da damar a zaneki"

Kawar da kai Ruma tayi gefe, Umar ya gama bala'insa ya bar gidan.

Yana ficewa daga gidan, Ruma ta dasa wa mama kuka, a kan lallai sai ta saka Yaya Umar ya cireta daga makarantar, mama ta ce babu ruwanta.

Ko da wasa Ruma ba ta sanya a ranta za ta yi wannan karatu ba, dan idan za a kasheta ba ta ma san in da aka ?ara musu Win ba, ta cigaba da sabgoginta.

Da sati ya zagayo zata koma makaranta, sai da a ka kai ruwa rana, tana kuka su Huzaifa suka sanyata a gaba zuwa makaranta, suna tafe suna zaginta suna mita an haWasu da ala?a?ai.

Yau mama ta bata kuWin makaranta, dan haka ta tsaya ta sayi goriba a ?ofar shiga makarantar.
Duk da babu malami a ajinsu, amma kowane Walibi ya nutsu sun haWa baki suna ta tilawa.

TaSe baki tayi, ta samu lungu ta zauna, ta kashingiWa tana cin goribar ta a nutse.
Shigowar malamin bai hanata cigaba da hangale baki tana gwaigwayar goribarta ba.
Ba ?aramin ?ulewa malamin yayi ba, tun a wancan satin ya lura ba ?aramar gaSuwa ce ba yarinyar.

Yayi mata alama da hannunsa ta je, ta tashi ta fito da jakarta da goribarta a hannu ta ce "gani"

Ya ce "Yauwwa, ta kan ki zan fara jin karatu yau, Wauko Alqur'anin ki ki karanta ?arin da na yi muku, sannan ki bani hadda" Wan waro masa idanuwanta tayi sannan ta ce "Gaskiya ban iya ba wallahi, karatun yayi yawa ina laifin aya Waya ko biyu"

"Koma gefe ki tsaya" babu ban ha?uri babu komai ta koma gefe ta ja ta tsaya.

Ya cigaba da sauraron tilawar 'yan aji, Ruma kuma ta mayar da hankali a kan cin goribarta, ya Waga kai ya kalli Ruma, wani irin takaici ya ?ule shi ko a jikinta abin da ya dameta kawai take yi, ya ce "Ke zo nan"

Ta ?araso ta tsaya, mi?ewa yayi ya Waga bulala zai daketa.
Ta ?walalo ido ta ce "Kar ka dakeni ba a dukana" bai saurari ruma ba, ya zuba mata a ?afarta har sau biyu.

Wani uban ihu ta ?wala, ta zube a kan ?afarta tana jujjuya kai.
Gaba Waya 'yan ajin suka yi shiru suna kallonta, sai a lokacin da ya daketa ya huce sai kuma ya sha jinin jikinsa ganin uban kukan da take yi.

"Wallahi ni sikila ce ba a dukana, shikenan ba zan iya tafiya ba" gaban malamin ne ya faWi, amma ya maze ya cewa 'yan ajin su cigaba da karatu.
A ?alla ruma ta shafe awa guda tana kuka babu ?a??autawa kuma ta?i tashi daga wurin, wai sikilarta ta tashi.

Abu kamar wasa magana har kunnen malamai, kasancewar malamin nasu, Wan ajin da suka yi sauka ne yake koyar da su, ba cikakken malami bane a makarantar.
Malamai suka taru a kan ruma, amma ta?i tashi wai sikila ce da ita, ba zata iya tashi tsaye ba.
Malamin nasu jikinsa sai rawa yake yana cewa "Wallahi bai san ba ta da lafiya ba"

Malamin da yayi mata interview ya ce "Kuma ni a form Winta yayanta bai rubuta tana da wani ciwo ba, ina ne gidanku?"

"Ni ba zan gane hanyar gidan ba, akwai yayyena a makarantar nan ku kira mini su su kai ni gida in ga mama zan mutu"

"Su waye yayyen naki?" Nan gaya musu ajinsu Huzaifa.
Huzaifa yana can yana karatu aka kirashi, yana zuwa ajinsu ruma ya ganta zaman dirshan malamai sun kewayeta.
Nan suka yi masa bayani, turus yayi yana kallon ruma yana son gano ko makircinta ne, dan shi a iya saninsa ruma ba ga da wata sikila, ban da zazzaSi ba ta ciwon uban komai, amma a ina ta samo wata sikila?.
Ya mi?a mata hannu ya ce "Taso in mayar da ke gida"

"Ni na kasa motss ?afata ciwo take mini" tayi maganar cikin kuka.

Huzaifa ya dur?usa ya ce "To hau bayana na mayar da ke" aikuwa ta ja jiki, ta hau bayansa ya Wau jakarta ya ce bari ya kai ta gida.


Sai da suka yi nisa sosai da makarantar sannan ya sauketa, aikuwa ta tsaya cak a kan ?afafuwanta.

Ya kalleta ya ce "A gidan uban wa ki ke da sikila?"

"To gani nayi za a kasheni da duka, naga a makarantar bokonmu ba a dukan wata me sikila, da na ji zafin dukan sai na ji kamar nima ina da sikilar".

Galala ya bi ruma da kallo, 'yar mitsila da ita amma ta iya makirci haka.

"To mu je ki yiwa Yaya umar abin da ki ka aikata"

Marairaicewa tayi ta ce "Dan Allah kayi ha?uri"

"Wallahi ba zan goyo ki a banza ba, ko ni sai na miki shegen duka yau" yana gama maganar ya dan?eta ya saSata a kafaWarsa dan zata iya ?wacewa ta gudu.






Ayshercool
08081012243
[22/06, 9:49 pm] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA
? ? ? ? ? ? ? ??

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES


https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing? YouTube channel Win
@Cool Hausa Novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following Wina a arewabooks a kan account Wina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.



*AFUWAN BAN EDITING BA*


P6

Iya ?arfinta take ihu, tana kiciniyar sai ya sauketa, amma yayi burus da ita, sai da ya je soron gida, sannan ya sauketa ya ja hannunta zuwa cikin gidan.

Aliyu ne a tsakar gida yana yiwa mama wanki, ya Wago ya kallesu ya ce "Ya dai, ya kake jan ta tana ihu, makarantar fa?"

Hauzaifa bai amsa masa ya tambaye shi"Mama tana nan?"

"Eh tana nan" Aliyu ya bashi amsa.

Jin ihun ruma ne ya sanya mama katse sallar walahar da take yi, ta fito tana tambayar lafiya.
Hakan yayi dai-dai da fitowar Yaya Umar, shi ma ya yi shirin fita. Duk suka zubo musu ido suna jiran jin ba'asi.

"Mama wallahi yarinyar nan ba ta da mutunci, daga sakata a makarantar nan ta fara tayar mana da hankali, yaushe yarinyar take da sikila ban sani ba?".

Mama ta Wan yi sororo ta ce "Wace irin sikila kuma?"

"To haka ta je ta ce wai sikila ce da ita, ta tashi tsaye ma ta ?i sai a bayana na goyota"

Yaya Umar ya kalleta ya ce "Ke meya sameki?"

Cikin in da in da ta ce "Dukana aka yi, kuma wallahi na ji zafi sosai shi ne na ce musu sikila ce da ni, na ga wata 'yar makarantar bokonmu ba a dukanta saboda sikila ce ita".

"Shi ne ki ke yiwa kan ki fatan ciwo saboda baki da hankali, ke dama za a zauna da ke baki yi abin da za a dake ki bane ba, me ki ka yi aka dake ki?" Yayi maganar cikin tsare gida.

Cikin kuka ta Wage ?afar wandonta, shatin bulala ya kwanta a kan fatarta, ta kalli mama ta ce "Mama kin ga fa, dan Allah a cireni wallahi ni ba zan iya makarantar nan ba, wai ban iya karatu ba shi ne aka yi mini wannan dukan, ni wallahi ba zan iya karatun nan ba, ga duka ga karatu mai yawa, da wanne zan ji?"

Cikin ts??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????awa Yaya Umar ya ce "Wuce mu je makarantar, sai kin ci ubanki yau, ai dama karatu aka turaki ba wasa ba"
A karo na farko ta yi wa yaya Umar gardama tana kuka, ta ri?e hannun Huzaifa, ta Suya a bayansa.

"Ni nake miki magana ki ke Suya a bayansa, ba zaki fito ki wuce ba"

"Dan girman Allah kayi ha?uri, wallahi idan suka san ?arya nake, sai sun kusa kashe ni, wallahi duka ake na tashin hankali a makarantar nan" kuka take wiwi kamar wadda aka yiwa mutuwa, mama dai ta kasa magana.
Huzaifa kuwa janyota ya yi daga bayansa, ya ce Wallahi ba zai kareta ba sai dai ayi mata duk abin da za ayi mata.

Yaya Sadik ne ya fito daga Wakinsu, yana zuwa ya ture Umar, ya kamo hannun Rumaisa, ya wuce da ita Wakin su.

Suna shiga ya zaunar da ita, shima ya zauna ya Wan ?ura mata ido sannan ya ce "Auta, meke damunki ne, kullum sai an yi rigima dake an ce ba kya ji, ke ko haushi ba kya ji?"

Ta girgiza kai ta ce "Wallahi ina jin haushin yadda aka tsane ni kullum ace bana ji"

"To yanzu meyafaru, har aka dake ki ki ke cewa sikila ce dake? Kin san sikila kuwa meyasa ki ke fatan wannan ciwon?"

"Gani nayi za a kashe ni da duka, ni bana son a dake ni".

"Gaskiya ba ka kyautawa, dan me yarinya za ta yi laifi ka hana a hukunta ta, me kake ?o?arin koya mata ne?" Umar yayi maganar a mugun fusace.

Yaya Sadik ya waiwayo ya kalli Hussainin na sa, ya haWa hannayensa alamar ban ha?uri ya ce "Tuba muke, zan wa tufkar hanci in sha Allah, on behalf of her, ayi ha?uri gobe in Allah ya kaimu da kaina zan mayar da ita makarantar in basu ha?uri" gajeren tsaki Umar yayi yai waje, babu wanda yake masa katsalandan kamar yadda Abubakar yake yi masa, ya fuskanci idan aka biyewa Yayan nasa ruma tsiyarta zata tsula ba tare da an kwaSeta ba, da tayi laifi sai ya ce ?uruciya ce.

Wunin ranar kowa share ruma yayi, yaya Sadik ne kawai yake kulata, Huzaifa da yasir suka ?are mata zagi tsaf suka tsangwameta.
Ko a jikinta, tun da Allah ya sa ba a mayar da ita makarantar an ce ?arya take ba, hankalinta ya kwanta.
Washegari Yaya Abubakar da kansa ya rakata makarantar, aka dinga yi mata sannu ana mata ya jiki, ta basar ta dinga amsawa.

************

Sanye yake da fararen kaya ?al, fuskarsa sanye da fari siririn glashi, taku yake cike da ?asaita ya biyo wata doguwar baranda.
Sannu a hankali ya ?arasa gaban wata ?atuwar ?ofa, ya sa hannu ya murWata a hankali. A take ta buWe wani sassanyan ?amshi ya daki hancinsa.
Da sallama ya shiga ya mayar da ?ofar ya kulle, babu kowa a falon sai wata matashiyar budurwa tana saka turaren wuta.
Amsa masa tayi tare da faWin "Sannu da zuwa".

"Yauwwa 'yar aikin Ammi, ina ma'aikatan ne ki ke aikin da kan ki?"

Ta Wan kalle shi sannan ta ce "Nima 'yar aikin ce ai" yayi murmushi ya ce "Sorry idan haushi ki ka ji, ina Ammi?".

"Bacci take" ta bashi amsa lokacin da take cigaba da saka turaren wuta.

"Ba kowa kenan?"
Cikin ?osawa da tambayoyinsa ta ce "Duk sun tafi makaranta".

"Ke me ya hana ki je makarantar?"

"Ohh God, uncle J am sick shi ya sa ban je ba, Ammi idan kana son ganinta ka dawo an jima, ina fatan zan iya tafiya na gama amsa tambayoyin ka?"

Ya girgiza kai ya ce "No, saura Waya ina yayan ku?"

Tayi murmushi ta ce"Wannan tambayar ai kai yakamata a yiwa, i don't know " daga haka ta bi wata hanya ta bar falon.

Ya girgiza kai a hankali ya ce "Wannan yarinyar ta fi mai kora shafawa, izzarki tayi yawa"
Wayarsa ce ta fara ringing, ya zura hannu a aljihunsa ya ciro wayar.

"Ke nifa kin isheni, ni kaina ban san in da yake ba, anjima kuma kilisa zan fita, zan neme ki amma" daga haka ya kashe wayar, ya saka a aljihunsa ya fice.

*********
Ruma ta sha kashedi a wurin su Huzaifa, a kan ta shiga hankalinta a makarantar nan, dan ba ?aramin girmansu ake gani ba, halinta ba zai sa mutuncinsu ya zube ba.
Ta cigaba da zuwa makaranta, amma ba ta gane komai, idan Yasir ya zaunar da ita zai koya mata kuma, sai ta ce ita ta gaji ba ta so.

Ranar wata juma'a da yamma, Abdallah yana ta haWa kayan miya, za a kai markaWe, Yasir ya kalleshi ya ce "Abdallah kyanta na Wau hotonka kana haWa kayan miyar nan, na je na nunawa yarinyar nan mai awara".

HaWe rai Abdallah ya yi ya ce "A'a mai wake zaka nunawa ba mai awara ba"

Yasir ya yi dariya ya ce "Zaka ga mai wake, wallahi yarinyar nan ta mato a kan ka, kawai ka nutsu ku daidaita, wallahi shar da kai awararka zaka yi ta ci"

"Na rantse idan ba ka yi mini shiru ba sai na Sarar da kai"

Yasir ya ce "Yaya ba zan ?o?ari na tayata kafa gwamnatin ta ba, kullum sai ta kyauta mini".

Buut Ruma ta fito daga Waki ta ce "Yasir yakamata muje ka gabatar mata da ni, na dinga biyawa idan zan je makaranta".

Tsaki Yasir ya yi "To munafuka waye ya sako dake, na zaci ma bacci take wallahi "

Abdallah ya ce "Wallahi ko da wasa ki ka je, sai na kakkarya ki".

"To ni ce maka ma nayi zan je?"

"Ke dai ki ka sani gulayya" Yasir yayi maganar yana hararta.

"Wallahi ni ba gulayya ba ce" shareta suka yi suka cigaba da hirarsu, yayin da Ruma ta koma gefe tana naWar abin da suke faWa.

Kamar yadda a islamiyya ruma ba wani ja take ba, haka ma makarantar boko ba uwar da take ganewa sai wasa.
Ta na cikin top 10 na marasa ganewa a aji, sannan ta farko a sahun marasa ji.
Yau bayan an taso daga makarantar boko, ta biyo ta hanyar da lambun mai unguwa yake. ?aton lambu ne da ya kasance mallakin wani a babba masarautar Kano, wanda yake ?ar?ashin kulawar mai unguwa, ba kowa ya san da hakan ba sai WaiWaikun mutane.
Gaba Waya hanyar ba ta cikin jerin hanyoyin da zata bi su sada ta da gida, amma tun da ta ji 'yan ajinsu suna labarin mangwaron lambun ya fito yayi kyau, tayi alwashin bi ta hanyar dan ganewa idonta abin da suka gaya mata.
Aikuwa babu ?arya, lambun ?ato ne na gaske, wani wurin an kewaye shi da katangar bulo, wanu wurin kuma aka ?arasa kewaye shi da waya.
Akwai bishiyoyi kala-kala a ciki, wasu duk sun yi 'ya'ya kasancewar lokaci ne na damuna.
Mangwaron nan yayi 'ya'ya sosai gwanin ban sha'awa.
?atuwar ?ofar shiga wurin ta gani, babu kowa a wurin, dan haka kai tsaye ta kutsa a gaban wata ?atuwar bishiyar mangwaro ta tsaya, yanayin wurin yayi mata kyau sosai da sosai.

Ta samu dutse, ta dinga jifan bishiyar, suna faWowa tana Wiba, ta tara ta cika jakarta, sannan ta nufo hanyar fitowa.
Tana fitowa wani matashi yayi caraf ya dan?eta yana faWin "Alhamdilillah, shegiya Sarauniya ashe ku ne masu shiga lambun nan suna ?urguma mana sata".

"Ban gane ba wace iri Sarauniya me nayi maka?"

"Zaki ga me ki ka yi mini, gidan mai unguwa zan kai ki, ke saboda ?warewa ma, da ki ka sata sai ki ka biyo ta ?ofa zaki fita, kina 'ya mace kina sata"

Cikin rashin kunya Ruma ta ce "Wallahi ni ba Sarauniya bace ba, ta ?ofar nan fa na shiga, ba wanda ya haura gida ne Sarawo ba?"

"To da ki ka bi ta ?ofar, wa ki ka tambaya ki ka shiga ki ka Webo abibda ba naki ba?"

"A'a, to ni wa na gani a wurin, kuma ma naga ai bishiyar ta Allah ce, Allah ne ya fito da ita, kuma sai ace sai an tambayi wani sannan za a Wau abin da Allah ne ya fito da shi, kai iskar da ka ke sha?a wa ka tambaya ka ke sha?arta?" Saroro ya bi ruma da kallo, wata 'yar cukul da ita sai shegen surutun tsiya.

"Zaki yi bayani, sai na kai ki gaban mai unguwa"

"DaWinta shi mai unguwar ba shi da wutar da zai sakani, kuma duk in da za a je ai bishiyar Allah ce, kuma ka sakar mini hijjabi dan ni ba 'yar iska bace ba.
Bai ko saurareta ba, ya figi hijjabinta ya fara janta.
"Ka dai na ja na haka kamar wata akuya, ba ?aramin aikina bane na cire maka hijjabin nan na ?ara gaba.




Mama sai kallon agogo take yi, tana kallon hanyar shigowa, amma babu ruma babu alamunta.
Tsakar gida ta fito tana kiran Usman, kasancewar shikaWai ne a gidan, ya dawo da wuri bashi da lectures.
"Ka ga haryanzu yarinyar nan shiru ba ta dawo ba"

Usman Ya ce "wata?ila tana can tana rashin hankali a titi da ?awayenta, amma maybe ki ganta yanzu".

"A'a zunnuraini, shi biyu da rabi fa take dawowa amma kalli yanzu ?arfe Waya da rabi, hankalina ya kasa kwanciya"
Ya Wan yi shiru sannan ya ce "Kuma fa kamar ma ga 'yan makarantar su lokacin da nake hanyar dawowa, amma bari na je makarantar ta su" yana rufe bakinsa, suka ji ana ?wala sallama a waje.

Usman ya amsa, ya nufi ?ofar gidan, aikuwa yana zuwa ya tarar da an ri?o ruma, tana rungume da jakar makarantar ta, sai kumbura baki take, tana cika tana batsewa.

Kallon matashin saurayin yayi, ya ce "Bawan Allah lafiya, ya zaka ri?o yarinya haka kamar ka ri?o Sarauniya?"

Matashin ya ce "To kusan hakan ne, karSi jakarta ka duba ka gani"

"Ka saketa mana" yayi maganar a fusace yana fincike hannun matashin daga hijjabinta.
"Me tayi maka haka?".

"Nan matashin ya kwashe komai ya gayawa Usman"

"Wallahi ni ba Sarauniya bace ba, tun da ta ?ofar wurin na shiga kuma ban ga kowa ba, ai ba haurawa na yi ba"

Usman ya fizgi jakar ruma, ya buWe ya ga mangwaro ya kai takwas a ciki manya, nunannu da Wanyu, sai goba guda huWu.

Ya kalli ruma, sannan ya kalli matashin ya ce "Yanzu kai a kan wannan zaka dan?ota ka keto layi da ita haka? Ka taSa kamata ta shiga ta Waukar muku abu ne?"

Matashin ya ce "Ban taSa kamata ba, amma ana haura mana, ayi sata"

"To kuma sai aka ce maka nice nake yi, ni wallahi ban taSa shiga ba sai yau".

Usman ya zura hannu a aljihunsa, ya Wauko dubu Waya, ya mi?awa matashin ya ce "Na san dai abin da ta Wauka, bai kai na hakan ba, gashi nan na biya, kuma kar ka sake kiranta Sarauniya Please, ba halinta bane ba ba ta taSa yi ba, dan ka ci sa'a da na biyewa zuciya sai na kifar da kai, saboda yadda ka ri?o mata hijjabi, ka keto unguwa da ita, saboda Wanyen mangwaro"
Yana gama maganar, ya ingiza ?eyar ruma zuwa cikin gidan, suna shiga gidan ya dan?ota ya ?wace jakarta, ya dur?usar da ita ya ce "Oya tsallen kwaWo maza"

Waiwayo ruma tayi, ta kalleshi cikin mamaki, amma taga babu alamar wasa a tare da shi, cikin tsawa ya kuma cewa tayi tsallen kwaWo.

Mama ta fito tana faWin "Lafiya, me aka ce tayi, sallamar da ake kenan?"

Usman ya ce "?yaleni da ita mama" nan ruma ta kama tsallen kwanWo.

Duk yadda mama tayi a kan Usman ya gaya mata me aka ce ruman tayi, amma ya?i, sai dai ruma ta ci ?wal ubanta, dan ko mi?ewa kasa wa tayi.

Duk yadda mama ta kaWa ta raya, amma bai gaya mata ba, kuma babu wanda ya gayawa abin da ta aikata.

****
Islamiyyar su ruma, sanya mata ido suka yi, dan ba ta iya karatu balle kawo hadda, ko karatun aka zo sai dai a tsallake ta, dan ba iyawa take yi ba.
Malamin ajin ko sabgarta ba ya shiga, tun daga ranar da ya dake ta ta ce ita sikila ce. Yau dai ya kasa jurewa yace mata "Wai ke ba kya jin haushi yadda 'yan ajin ku suke karatu, amma ke ba kya iya wa?"

"To malam karatun yayi mini

Please Login or Register in order to submit comment