You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba.

Tun magariba, ruma taga mama ta kwaSa lalle kaya guda, ba ta kawo komai a ranta ba, ta cigaba da harkokinta.

Sunanta da mama take kirane, ya sanya ta san asuba ta yi, ta yin?ura zata tashi, ta ji motsin leda a ?afarta, ta tashi zaune amma ta ga hannunta da ?afarta duk leda.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, mama me ya sameni?"

"A ina?"

"Wannan ledar mecece?"

Mama ta ce "Ahh, ruma ai ba ke kaWai ki ka san ta kan tsiya ba, na sai miki kaya ba godiya ki ka raina, na biya kuWi ayi miki lalle ki ka ?i zama, ai da ni ki ke zancen, kina wannan shegen baccin na yi miki dungulmi da shi zaki yi sallar, tsohuwa ta faWa kwata ba, irin wanda nake yi, kuma kitso ma gidan Hanne zan saka Huzaifa ya kai ki, tayi miki zane huWu ba dai ba kya ji ba, ai daidai nake da ke, ina sane nake kawar miki da kai".

Ruma ta kalli yadda aka ?unshe mata ?afa har ?wauri, ga hannayenta kuma ana batun ay???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i mata zanen Hausa guda huWu a ka tayi salla, ta tuna uwar rigar da zata saka a matsayin kayan ssllarta, ta Wora hannu a ka ta zunduma ihu.

DAN ALLAH MASU NEMA DAGA FARKO KU DINGA TAMBAYA A GROUP KO DUBA WATPAD KO AREWABOOKS NA GODE

AYSHERCOOL
08081012143
[03/07, 2:14 pm] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA
? ? ? ? ? ? ? ??

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing? YouTube channel Win
@Cool Hausa Novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro.
Ku yi following Wina a arewabooks a kan account Wina na ayshercool7724
Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode

*Ina mi?a sa?on godiya, ga waWanda suka yi mana ta'aziyya na rashin uba da 'yar uwa Naima Suleiman (Nimcyluv) ta yi, muna fatan Ubangiji Allah ya ji?ansa da rahama.*

*TA?ABBALALLAHU MINNA WA MINKUM, INA TAYA AL'UMMAR MUSULMI BARKA DA BABBAR SALLA, UBANGIJI ALLAH YA KAR?I IBADUNMU YA MAIMAITA MANA*




P8

Da rige-rige Usman da Abdallah suka shigo Wakin, suna tambayar meyafaru da ruma take wannan uban ihun.
Kallonta Usman ya yi, ya kalli mama ya ce "Mama meya sameta ne?"

Mama ta ce "Ku tambayeta mana, ba gata nan a zaune ba"

Abdallah ya ce "Ke menene?"

Nuna masa hannunta ta yi, tana sake fashewa da wani uban kukan.

"Wannan ledar ta meye haka a hannunki, kamar wata miskiniya"

?are baki tayi, ta cigaba da kuka iya ?arfinta.

"Dalla ki rufewa mutane baki, kiyi mana bayanin menene?" Usman ya daka mata tsawa.

"Ba mama ce ba"

"Me maman tayi?"

"Ta yi mini lallen tsofaffi wai tsohuwa ta faWa kwata ina bacci, wallahi dariya za ayi mini idan aka ganni da shi".

"Kuma saboda baki da mutunci, ki ke mana wannan uban ihun da Asubar nan, ke dai ba zaki yi hankali ba ko?"

"Wallahi mama ba ta sona, ban san meyasa ta tsaneni ba, wayyo Allah na"

Abdallah ya ce "Allah ya ?ara, a wannan shegen baccin naki, har aka yi miki lallen baki sani ba".

Mama ta ce "Ki tashi ki kwance lallen nan kiyi salla".

Ko motsi ruma ba ta yi ba balle ta tashi.

Abdallah ya ce "Wai wane irin lalle ne tsohuwa ta faWa kwatar ne?"

Cikin kuka ruma ta ce "Irin fa wanda mama take yi a ?afarta"

Dariya ce ta ?wacewa Abdallah, ya ce "Haba mama, ya zaki yi mana haka?"

Mama ta ce "Hukunta ta nayi, duk rashin jin da take yi ba ta zaci ina da hanyar hukunta ta ba, na bada kuWi ayi mata abin arziki na zamani, amma ta?i zama, ai da ni ki ke zancen, kuma ajima da kaina zan kai ki kitso zane huWu za ayi miki".

Sosai ruma take kuka, Usman kuwa ficewa yayi ya cigaba da sabgarsa, Abdallah ne ya kaita bakin rariya, ya tayata ya cire ta wanke, aikuwa hannunnan yayi jawur, lalle ya kwanta WoWar hannunta da ?afarta.

Da gari yayi haske kuwa, Huzaifa ya ga lallen rumaisa, ya zauna ya sakata a gaba ya dinga yi mata dariya, har da kifawa, wai hannunta kamar kuturwa.

Ko Abincin safe ruma ba ta ci ba, sai kuka da goge hawaye, wajen ?arfe goma na safe, mama ta sakata a gaba zuwa gidan kitso.

Kamar yadda mama ta faWa, kitson hannu biyu aka yiwa ruma, gashi ta sha azaba a wurin mai kitson, saboda da ta ?i tsayawa, mama na dukanta, matar kuma ta matse mata kai a tsakanin cinyoyinta, ga kitson azabar zafi tamkar za a zaro ?wa?walwarta saboda yadda matar ke jan gashin.
Ko da aka gama kitson, ruma ta haWa gumi ga hawaye da majina saboda azabar zafi, mama ta sakata a gaba suka tafi gida.

Ruma da ta kalli hannunta ranta yake Saci, saboda hannun ganinsa take kamar ba nata ba.

Har ana gobe salla ruma bata farin ciki, ji take ina ma ace an fasa sallar idi wannan shekarar, saboda wannan yankan ?auna da mama tayi mata.
Har bata son a aiketa, dan idan ta fita ta ga yara sun sha kitso da ?unshi, sai ta yi kuka, saboda yadda ta ?arfi ita aka mayar da ita zamanin mutanen da.
Yanzu haka tana tafe a hanya, zuwa aiken da mama tayi mata, ta gaji da tafiya ga Sacin rai, ta samu wuri tayi zamanta a kan wata baranda, tana share hawaye.

"'Kukan me ki ke yi ne haka, ba aiken ki aka yi ba?"

Ta Waga kai taga mai maganar, Auwal ne, na makarantar islamiyya da ta yiwa bori rannan.
Shiru tayi masa tana tura baki.

"Meyasa ki ke kuka?"

Mi?ewa ta yi tsaye tana faWin 'Babu komai"

Ya Wan girgiza kai ya ce "Ina Yasir?"

Cikin ?un?uni ta ce masa bata sani ba, tayi wucewarta.
Mamaki ne ya kama shi, duk in da ta ganshi ko ba zai kulata ba, sai ta yi masa magana, amma yau tayi masa wula?anci.

Aiken da bai fi tayi shi a mintuna ashirin ba, sai da ta shafe awa biyu da rabi, ta koma gida Aliyu sai da ya murWe mata kunne, saboda yadda ta je ta daWe.

Da safiyar salla kuwa, an kai ruwa rana da hajiya ruma kafin tayi wanka, dan cewa ta yi ba zata je idi ba.
Huzaifa kuwa musamman ya ?i shiri da wuri, sai ya ga shigar da ruma zata yi yayi mata dariya.

Ta na kuka, mama ta watso mata wannan atamfa da ta zauna ta dinga kushewa.

"Mama dan girman Allah ki barni na saka tsofaffin kayana, wallahi bana son kayan nan".

"Ni ki ke gayawa ba kya son kayan nan, zaki saka ki wuce ko kuwa?"

Za ta tsaya gardama Aliyu ya yi mata tsawa, ya ce ta Wau kayan ta saka su wuce sallar idi.

Ga lalle dungulmi, ga kaya Winkin mutanen farko, ga kai babu kitso mai kyau, ba yari ba sar?a? koma kamar 'yar ?auye.
Huzaifa kamar ya shiWe don dariya.

"Yarinya kin yi kyau kamar bafulatanar ?auye" Yasir ya yi maganar yana dariya.

"Babu ruwanka da ni Yasir, zan maka rashin mutunci wallahi".

"Na kuma jin bakin ki sai na Sarara da ke, maza wuce mu tafi" Aliyu yayi Maganar yana nuna mata hanyar fita.

Usman ne ya mi?o mata sabon hijjabi ya ce "Gashi nan ba dan hakinki ba".
Ajiyar zuciya ta yi, ko ba komai hijjabin zai taimaka mata ta rufe wannan buhun Winkin, tun da hijjabin dogo ne.

KarSa tayi tana yi masa godiya, ta saka suka tafi idi.

********

"Masha Allah, looking take away my beautiful angel" Ammi ta faWa tana kallon Iman.

Murmushi iman tayi ta ce "Ammina, an yi salla lafiya"

"Alhamdilillah my dear, ina fatan dai an yi mini Addu'a"

Murmushi ta yi ta ce "Ba dole ba Ammina"

Wata matashiyar budurwa da ke zaune a kan kujera, ta Wago ta ce "Wai mu Ammi baki ganmu bane?"

"Na ganku mana"

"Ai shikenan Ammi, wannan wariyar launin fata tayi yawa, mu shikenan ba za ki dinga kallanmu ba, sai wannan mai kama da bafulatanar dajin" cewar Waya yarinyar.

Ammi ta ce "Kun dai ji kunya, da ku ke kishi da ?anwarku"

Iman tayi musu gwalo ta ce "Iya wuya dai, nice ta gaban goshin Ammina"

'Ta mayar da ke ciki, ko a saka ki a zanin goyo a baki Nono, ?arshen ?auna"

Ammi ta girgiza kai ta ce"Allah ya shirye ku, Iman ki je ki shirya direba zai kai ki gidan zinariyar Galadima, ki kai musu Abincin salla".
?ata fuska Iman tayi ta ce "Ammi"

Kan ta ?arasa maganar, Ammi ta Wora yatsanta a kan lips Win ta ta ce "Shhhh, bana son musu, tana ta complain ba kya zuwa" ?an gyaWa kai Iman tayi ta ce "Shikenan Ammi, bari na shirya"

*****
"Ke ba zaki ta so ki fara kai tuwon nan ba"
Ruma ta kwaSe fuska ta ce "Dan Allah mama ki yi ha?uri, ki bawa su huzaifa su kai wallahi idan na fita dariya za ayi mini"

"Ni nake aiken ki, ki ke cewa na aiki wani ruma, ni ko ruma?"

"A'a mama ba haka bane ba, wallahi dariya yara suke yi mini" tayi maganar hawaye na taruwa a idonta".

"Tashi ki wuce ki je aiken da aka yi miki" Usman ya daka mata tsawa.

Jiki na rawa ta tashi, ta Wau kwanukan da mama ta zuba tuwo, ta fara kai wa.

A hanya ta haWu da wasu 'yan makarantar bokon su, cikin fara'a Wayar ta ce "Laa ruma, ya ki ke ina kayan sallar ki?"

Ruma ta kalleta ta ce "Ji masifa, to ba ni da su, ba a Winka mini ba"

"Daga tambaya sai masifa?"

"Eh, ina ruwanki da ina kayan salla na, tsirara ki ka ganni?" tayi maganar tana saye hannun ta a cikin hijjabi.

"Kutmelesi, ruma meye wannan a ?afarki?" Gaba Waya suka kalli ?afar ruma, da take sanye da silifas Wan madina, ga ?afa tayi maroon da lalle, kasancewar ruma ba? iya Waurin zani ta yi ba, zanin ya Wage har ?waurinta, kuma hijjabin bai gama rufe ?afar ba.

"Kutmelesi, wane irin lalle aka yi miki, lallai mai lallen nan ta cuceki, kut kamar ?afar tsohuwa"

Dariya yaran suka kwashe da ita suna sake le?a ?afarta.
Cikin takaici, ta juya zata tafi, amma wata za?a?urar yarinya, ta biyo ruma tana Wage mata zani.
Mai jiran ?iris ya samu a sarari, tuni ruma ta yi watsi da kwanuka, ta fara sana'ar ta ta dambe.
Kasancewar a ?ule take dama, ta rasa in da zata sauke fushinta, dan haka ta zage ta kama yarinyar nan ta dinga jibagarta kamar Allah ya aikota.
Suna cikin damben Allah ya bawa yarinyar sa'ar ketawa ruma hijjabi, hakan ya ?ara tunzura ruman, ta danne yarinyar tana duka.

"Wannan yarinya an yi jarababbiya, duk in da ta tsuguna sai dambe, sai ka ce annoba" cewar wani mai awo a gefe, da bai raba su ba sai zance.

?agowa ta yi cikin masifa ta ce "Wallahi ni ba annoba bace ba"

Ta du?a ta cigaba da dambenta.? ji tayi an yi sama da ita, ta fara kokowar ?wacewa tana kai duka.

"Zaki nutsu ko sai na kakkarya ki" yaya Aliyu ne ya tsare ta da ido.

"Dama abin da ta aiko ki kenan?" Ta yi shiru tare da sunkuyar da kai.

"wuce mu tafi, dage uwar faWa"

Haka ta kwashi kwanukan, da yagaggen hijjabinta a hannu ya tasa ta a gaba, zuwa gida.

Mama na ganin ruma ta shigo tare da Aliyu, a yadda ta shigo kawai mama ta gane halin ta je ta gwada a waje.

"Damben ki ka je ki ka yi kenan ko, mara kintsi?"

Wage baki ruma tayi zata fara yiwa mama bayani, amma mama ta katseta ta ce "Ban tambayeki ba ruma, ki je ji yi tayi, bakin mutane kawai ya ishe ki"

Gefe ta koma ta zauna, tana jin yadda ba ta gamsu da dukan da ta yiwa Hauwwa ba, saboda dariyar da suka yi mata.

Yaya Umar ne ya fito daga Wakin su, cikin wata dakakkiyar shadda dark blue, ya karya hula sai ?amshi yake zubawa.
Tsuruu ruma ta yi da ido, tana jiran ya sauke mata masifa, tun da ya ji ance ta yi dambe.

Nufota ya yi, ita kuma ta ?ura masa ido ko ?iftawa ba ta yi.

Ya kalleta ya ce "Na canza miki ne?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a ka yi kyau ne"

Murmushi ya yi, ya mi?a mata leda ya ce "Je ki ka gwada wannan" da sauri ta tashi, ba tare da sanin meye a ciki ba ta karSa ta shiga Waki.

Doguwar riga ce ta shadda kalar kayansa, da mayafi da sabon takalmi da yari da sar?a.
Ko da ta saka ta fito ba ?aramin kyau ta yi ba.

"Mama kin ganni, na yi kyau"

Aliyu ya ce "Saboda son kai, shine ku ka yi kaya iri Waya babu ko labari"

Cikin tsananin farin ciki ta ce "Yaya Ussy, kalleni dan Allah na yi kyau?"

"Eh to, babu laifi sai ki ka zama kamar budurwa, duk da ?waila ce".

Cikin tsananin farin ciki, ta faWa jikin yaya Umar tana murna "Yaya na gode sosai, Allah ya saka maka da alkhairi ya sa ka gama da duniya lafiya"

Ganin yadda take murna ya sanya shi yin murmushi na gefen baki ya ce "Allah ya sa ki daina rashin ji".

"Iyee, lallai mai sunan Baba, ni sai ka haWani da atamfa kala uku, amma kai da ?anwarka ka yi muku kaya iri Waya, wato an fi son ta a kaina" mama tayi maganar cikin sigar wasa.

Murmushi ya yi, dan ya san halin mama da barkwanci wasu lokutan.

Mama ta shiga Waki, ta fito da wata ?atuwar leda, ta mi?awa ruma ta ce "Gashi nan, ba dan halinki ba, kayayakin da suka yi miki ne, na wannan sallar na?i nuna miki dan in hora ki"

Rikicewa ruma tayi, dama suna yi mata Winke-Winke, amma sallar bana bata san sun yi mata ba, dan a ?alla ta tashi da kaya ku san dozen, banda hijjabai da abun hannu da sauransu.

"Wayyo Allahna, dama kuna so na haka? Duk nawa ne wannan mama kin ga fa duk nawa ne"

Gaba daya suka kewaye ta suna murmushi, ganin yadda ta rikice tana murna.

Bin su ta dinga yi Waya bayan Waya tana yi musu godiya, tana zuwa kan Huzaifa ya wani maze ya ce 'Kar ki damu, wannan fa bakomai bane ba, idan har zaki dinga biyayya".

"Ba zan yi biyayyar ba, na san ma ba uwar da ka saya mini, duk gidan nan waye ya kai ka talauci da son banza?"

"Laaaa, ke fa ba a abin arziki da ke ko?"

"A'a yi ha?uri mama, shi Win ne zai Sata mini rai, yanzu a cigaba da zuzzuba tuwon ina kaiwa, amma wallahi duk in da na san ba za a bani kuWi ba, sai dai Yasir ko Huzaifa su kai"

Haka tayi ta rabon Abinci cikin annashuwa, gidan da aka bata kuWi tayi ta murna, idan ba a baya ba tayi ta jin haushi.

********
Ba zata iya ?ayyade rabonta da gidan nan ba, dan haka ta Waga kai take ta na kallon sauye-sauyen da aka yi a gidan.
Ya ?awatu, duk da ginin yana nan a yadda yake, amma an yi wa gidan gyara sosai.
Da haka ta ?arasa cikin ?aton falon da ke cikin gidan.

Hadimai ne ke ta kaiwa suna komowa a cikin tangamemen falon, suna aikace-aikace.

?aya daga cikin hadiman ce ta kalli Iman da fara'a ta ce "Maraba da zuwa".

Iman ta ce "Yauwwa sannunku da aiki, Ummma fa?".

"Tana cikin turaka, bari ayi miki iso"

Babu jimawa hadimar ta fito, ta kalli Iman ta ce "Bisimillah, ta ce ki shiga"

Bayan hadimar Iman ta bi, zuwa turakar Ummma.
Shigarsu Wakin ke da wuya, gaban Iman ya faWi, bisa tozali da mutanen da ba ta son ko haWa hanya da su, ba dan jinin Ummma bane su, to tabbas da kai tsaye zata iya cewa mutanen da ba ta ?auna.

FaWaWa murmushi Ummma tayi ta ce "Masha Allah, Iman dama talaka na ganinki?"

Murmushin ya?e iman ta ?a?alo, ta dur?usa a kan gwiwoyinta tana gaida Ummma.

Cikin mutuntawa Ummma ta amaa mata, tare da tambayarta ya Ammi.

"Hajiya Iman, manya manyan 'ya'ya a gidan Galadima, ya kike ya school?" cewar wata matashiya da ke zaune a gefen Ummma.

Ko ba a gaya mata ba, ta san da biyu budurwar ta yi wannan maganar, ta dake ta ce "Lafiya lau Anty Soafy, an yi salla lafiya?"

"Hmm lafiya lau, irin wannan ado haka, Ummma wannan leshin kamar irin sa Khairiyya ta saka ranar kamunta ko?" Tayi maganar tana ?arewa Iman kallo.

Umma ta ce "Eh irinsa ne"

"Wow, it worth 120k fa, lallai autar gidan Galadima, kin ri?e wuta".

Iman jin ta take tamkar a kan wuta, dan haka a gurguje ta ce "Ummma dama abincin salla ne, Ammi ta ce na kawo miki, kuma nazo mu gaisa, bari na tafi".

"Kai Iman tun da wur haka, ke dai ba kya son mutane, shikenan bari na baki barka da salla".

"A'a Umma, ai na girma da barka da salla" iman tayi maganar tana mi?ewa .

"?aniyarki, tsaya ki karSa mana" girgiza kai iman tayi, ta fice daga Wakin da sauri.

Har ta kai tsakiyar falon, ta ji an ri?e mata jaka.
Ta waiwayo tana kallon wadda ta ri?eta.

"Duk na san kin ci kin ta da kai, Ammi tana ji dake, na san kina da kuWi baki rasa komai ba, amma yakamata ki karSa tun da kin san baki da gado a cikin dukiyar gidan Galadima?"

Cikin rauni Iman ta ce "Anty Soafy me kuma ya kawo wannan maganar?"

Cikin ko in kula Soafy ta ce "Yau aka fara gaya miki irin wannan maganar ne, ai gara a dinga yi ana tuna miki, ko ba haka ba?" Ta fizgi jakar iman, ta saka mata kuWin, ta sa?ala mata jakar a kafaWarta ta koma ciki.

Gwiwa a saSule, iman ta nufi fita daga falon, tuni idanunta suka cika da hawaye, sai dai tana fitowa ya sha gabanta, ya ?ureta da idanuwansa.

?o?arin ratsewa take ta wuce, amma ya ce "Me ta ce miki ne, har ta saka ki kuka?"

Girgiza masa kai tayi alamar bakomai.

Yayi murmushin gefen baki ya ce "Anyway, kin yi kyau sosai a outfit Win nan, ashe yayanki yana Saudiyya babu ko sallama?".

"Uncle J, am sorry sauri nake, Ammi na jirana" daga haka ta wuce ta bar shi a wurin a tsaye.

**********

Zuwa yamma mama ta saka ruma a gaba sai sa ta cire shaddar nan, dan idan ta bar ruma da ita sai shaddar ta fita daga hayyacinta.

Kwanukan da aka Sata, Yasir ya tattara yana wankewa, mama ta ce "Ke, shiga Wakinsu ki dudduba mini idan da kwanukana, cokula ko kofi, duk ki fito mini da su, dan na san hali, sai a kai mini kwano Waki a ?i fito da shi"
Ruma ta tashi ta nufi Wakin samarin nan, ba tare da ko sallama ba.
Usman ne a kwance yana waya, kuma da alama da mace yake wayar.
BuWe baki tayi, ta tsaya tana kallonsa. Zumbur ya tashi zaune, ya katse wayar ya ajiye ya haWe rai ya ce "Zo nan" ba musu ta ?arasa in da yake.

"Me ki ka ji?"

Ta ce "A ina?"

"Ina tambayarki kina tambayata? Nace me ki ka ji?"

"Wallahi ban ji komai ba, kawai dai na ji ka ce....." Sai kuma ta yi shiru.

"Ba zaki faWa ba sai na taka ki?"

Ta tura baki sannan ta ce "Na ji ka ce, wai kwalliyar ta tayi kyau, kamar farin wata".

"Sai kuma me?"

"Shikenan na ji wallahi "

"To na rantse da girman Allah, idan ki ka sake ki ka faWa, wallahi sai na yi miki dukan tsiya, ?anwar abokina ce ba wata ba"

"To ai ni dama ban ce zan faWa ba, mama ce ta aikoni" daga haka ta shiga duddubawa mama kwanukanta.

Aikuwa ruma ta fito da kwanuka a hannuta tana faWin mama "Kin ga kofin ki, an sha fura a ciki sha zumamu ya siWe miki kofi tas, har Sera ya fara ci. Kin ga plate Win ki har da sauran alalar da ki ka yi tun sati biyu da suka wuce".

Yasir ya ce "To munafuka, uban waye ya saka ki wannan sharhin?"

Mama ta ce"Ai ba ?arya ta yi ba, ku yi ta kwasar mini kwanuka kuna kaiwa Wakin ku, sai na bi na tsinto abina, ?azaman banza kawai"

Mama na tsaka da mitar sai ga Aliyu ya shigo, ya ce "Ina ruma"

Ta ce "Gani"

"Yo sauri, abokaina ne na filin ball suke tambayata kina ina, shi ne suka biyo ku gaisa, saura kiyi wani haukan da zaki zubar mini da mutunci ".

Murmushi ta yi ta ce"A'a ba zan zubar maka da mutunci ba, bari na sako gyalena"

Yana maganar ya fice, Huzaifa ya ce "Mama ke ba a zo gaishe ki ba, sai wannan yarinyar lallai ruma".

Ta fito daga Wakin mama da sauri, ta kalli Huzaifa ta ce "Ka yi mini Addu6, Allah ya sa su bani kuWi" tana gaya masa ta kwasa da gudu ta fita waje.

Da fari gaishe su tayi kamar nutsatsiya, suka amsa mata cikin mutuntawa.

"Ya makaranta ya rikici2?"

Ta ce "Makaranta lafiya ?alau, amma ni bana rikici" suka din ga jan ruma da hira ita kuma tana zuba, Aliyu sai hararta yake amma ta cigaba da zuba.

Dariya suka dinga yi mata, suka babbata barka da salla, ko Wan cewa ba zata karSa Win nan ba tayi ba, zuruf ta mi?a hannu ta karSe tana godiya.
Wani mugun kallo yake wa ruma, amma ko saurararsa ba tayi ba.

Ta duba a cikin kuWin da aka bata, akwai Wari biyu da ta tsufa sosai, ta kalli wanda ya bata ya ce "?an uwanmu Wan canza mini wannan, ba zata karSu ba" buWe baki Aliyu ya yi yana bin ruma da kallo.

Aikuwa ya karSa ya canza mata wata, ta ce ta gode ta shige gida.

"Mama kin ga abokan yaya Aliyu sun bani, kuma sun ce suna gaishe ki"

Mama ta ce "To madalla"

"Mama gashi ki ajiye mini, ki Wora da lissafi, idan kin manta ni ina sane da lissafin, dan Allah mama kar na zo karSar kuWina ki fara ce mini, abubuwan da ki ke mini ba da kuWina ki ke yi mini ba, wallahi mama da za ayi lissafi ban san iya adadin kuWin da nake bin ki ba"

Cikin gatse mama ta ce "To Anty ruma, ki zauna ki lissafa duk kuWin da ki ke bina, na biyaki"

"Dan Allah mama da gaske ki ke?"

"Eh mana" murna ta dinga yi tana cewa 'Ai mama kuWin da nake binki, sai ma zauna musamman na yi lissafi, tsaf sai na zama attajira da kuWin nan, unguwar da muke zuwa a bani kuWi ai da yawa"

Yasir ya ce "Ba zaki taSa hankali ba".

Aliyu ne ya shigo rai a Sace yana hararar ruma.
Kawar da kanta tayi gefe ta?i kallonsa.

"Dole ki kawar da kai mana, yarinyar nan ana bata kuWi ta karSe, wai har da cewa wai wata ba zata karSu ba, da yake ke ki ka basu ajiya"

"Yaya ba kyau mayar da hannun kyauta baya fa"

"Zaki mini shiru, ko sai na mareki, mara kai kawai"

A ranta ta ce "Ohoo dai, tun da Allah ya sa na karSa".

Bayan sallar isha'i yaya Umar ya dawo, duk sun daddawo suna gida, ana ta hira.
Ruma tayi gyaran murya, ta kalli Yaya Usman ta ce "Mama kin san me?"

Mama ta ce "A'a".

Usman ya zubo mata ido, kowa ya yi shiru yana sauraron wani shirmen zata faWa.

Ayshercool
08081012243

(INCLUDE ME IN YOUR PRAYERS PLEASE =?O?)
[05/07, 5:40 pm] JAKADIYAR AREWA: ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?ANWAR MAZA
? ? ? ? ? ? ? ??

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing? YouTube channel Win
@Cool Hausa Novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro.

P9


Wani irin kallo Usman yake mata, amma ta basar ta ce "Mama kin san me yaya Usman ya yi?"

Mama ta ce "A a sai kin faWa"

Usman ya ce"Haka muka yi da ke ruma?"

"Oho ni dai bana munafurci da rashin gaskiya, duk abin da aka yi mama bata nan sai na gaya mata, ba zan ga ana ba dai-dai ba mama bata sani ba na yi shiru".

Kamar ya yi kuka ya ce"Amma haka muka yi da ke?"

Mama ta ce "Gaya mini ina jin ki"

Ruma ta kalli Usman ta ce "Sai dai ka yi ha?uri fa, amma wallahi sai na faWa a gaban kowa da kowa, ba zan zuba ido ana abin da ba dai-dai ba"

Ba dan ya san idan ya yin?ura zai yi mata wani abu mama zata hana ba, da sai ya kife Ruma da mari, ya san idan ta Waga maganar nan akwai damuwa, zai sha faWa da mita.
Uwa uba ga Yaya Umar a zaune a wurin, kuma ba shi da tabbacin iya abin da ruma ta gaya masa ta ji, shi kaWai Win ta ji, dan kawai Waga kai ya yi ya ganta a tsaye lokacin da yake wayar.

Ta gyara zamanta sannan ta ce "?azu, da ki ka aikeni kai tuwo gidan mai ?uli, na ganshi a ?ofar gidan su wannan abokin nasa Yahaya,

Please Login or Register in order to submit comment