You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samu daidaito tsakanin iyalina".

Nusaiba ta ce "Allah ya sa".

Har ?ofar gida ya kai rumaisa, suna tafe suna tattaunawa a hanya, yadda za su fallasa baba uwani, domin sai an katse hanyar kaiwa Mummy sa?o, da samu hanyar dakatar da wasu ayyukan na Mummy.
Rumaisa ta sauka, shikuma ya tafi da shi da Sabir.

Sai wajen goma na dare, sannan takawa ya isa gida.

Rumaisa tana fallo tana kallon cartoon, kamar yadda ta saba.

Sallama yayi da kaya a hannunsa, ta tuna mama ta taSa cewa, a zamaninsu idan miji ya dawo gida da kaya a hannunsa, jiki na rawa suke tashi su karSa.

Cikin basarwa, ta tashi ta mi?a hannu za ta karSa, ya kalleta ya ce "Kin ci abinci ne?"

"Na ci a gida".

Ya ce "Dafo shayi cup biyu, ki sameni a Waki"

Ta jinjina masa kai, ta tafi kitchen.

Kan ta dafa ta dawo, har yayi shirin kwanciya, sai dai yana gefen gado, yana danna waya.

Ta ajiye cup da flaks Win, za ta fita ya ce "Zauna ki haWa mana"

Su ruma da yake ba kowacce bisimillah take wucewa ba, ta zauna ta haWa tea cup biyu.
Gasashshen nama ne, da ?aton bredi, ba kunya ta saka hannu tana ci, tana basar da shi, ita dole ba ta daina fushi ba.

Hannu ya sa, ya matse kumatunta ya ce "Can't you smile, or say thank you? Kin shanye mini alawar madara, kuma kina wani kumbura baki"

Tura baki tayi, ta cigaba da kora shayi, suka gama ciye-ciye, ta tashi zata kwashe kwanuka ta fita.

"Zauna zamu yi magana".

Ta zauna tana lashe hannu. Ya Waukko tissue, ya goge mata hannun.

Sannan ya dubeta ya ce "Cikin satin nan zan yi tafiya in sha Allah, zan yi sati biyu, idan na dawo kuma, zan je ?aro karatu, na tsawon watanni shida. Wannan asabar Win in sha Allah, za a saka ki a Makarantar islamiyya ta matan aure".

"Islamiyyar matan aure, salon su rainani, ba manya ne matan auren ba? Kuma wai ka tafi ka barni nikaWai?"

Takawa ya ce "Eh, sidi zai din ga kai ki yana dawo da ke makaranta"

"To sai in daina ganinka?".

"Kina son ki d???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?inga gani na ne?"

Ta ce "Eh mana, nafi son ka dinga kaini makaranta da kanka"

Yayi murmushi ya ce "Abokin gabar naki? Da ki ke yi wa rashin kunya?"

Tayi dariya ta ce "Ai amanarka aka bani, sai na gama sauke amanar, sannan zan rama abun da ka yi mini, dan ban manta ba, kuma kai ne ka ke sawa na yi maka rashin kunya ai wataran, amma dai ka yi ha?uri.

Wani irin murmushi yayi, yana jin daWin jirar ta su.

Ya Wora hannunsa a kafaWarta, kamar ?awarsa ya ce "Ban ha?ura ba, fitsararki ta yi yawa, ha?urina ya kusa ?arewa"

Ita ma ta Wora hannu a kafaWarsa ta ce "Allah ya sa kar ha?urinka ya ?are, ai da ban taSa sanin kana da ha?uri ba ma sai yau. Allah ya sa in yi tsawo in kamo ka a tsayi"

"Ba wannan nake so ba, ki yi girma ki biyani bashina nake so"

Ba tare da ta gane me yake nufi ba ta ce "Ai da na gama makaranta, na fara aiki, dubu goma ma zan baka".

"Zaki ga idan kin gama makaranta, na gaji, baby nake so, ayi wa sabir ?ani ko ?anwa"

Ta ce "Eh wallahi, nima ina so"

Yayi dariya ya ce "Are you sure?"

Ta ce "Yes" cikin murna.

Yayi dariya ya ce "zamu gani ai".

Ya Wan yi shiru sannan ya ce "Duk da na yi maganar a baya, amma yanzu zan sake jaddadawa, ki din ga iya bakinki, a al'amuran da suka shafi masarautar nan. Abu na gaba a duk lokacin da abu ya faru, idan nayi magana ko kina da laifi ko baki da laifi, bana son musu, idan baki da laifi, da kaina zan yi bincike in gane"

"Idan bani da laifin sai ka bani ha?uri?"

Ya ce "Ya danganta, ba sai lallai na fito kai tsaye na ce kiyi ha?uri ba, sannan a duk lokacin da wani daga familynmu, ya sake zuwa, idan har suka yi miki magana ta rashin kyautawa, kar ki kula su, idan na zo ni ki gaya mini. Sai kuma ala?arki da wancan yaron Mahmud, ina sake maimaita miki bana so, ki kiyaye abun da ba na so mu zauna lafiya".

Rumaisa ta ce "Gaskiya papa, ni ba kullum nake ?arya ba, maganar gaskiya ba za aci mini mutunci nayi ha?uri ba, tun da dama can Allah bai yi ni a cikin masu ha?uri ba. Sai kuma maganar daddyna, dan Allah meyasa ba ka son ala?armu?" .

"Ban ji na yadda da ala?ar bane, zai iya yin komai dan ya cutar da ni, dan haka ba zan so yayi involving Winki da Sabir ba. Mussaman da ki ka kasance abokiyar gabata"

Ruma ta yi murmushi ta ce "Amma ka yadda ka yi mu'amala da su Jamil ko? Kai baka san farincikin ammi ne papa? Ba zai cutar da kai ba, idan kuma kana son mu rabu, to ka rabu da su Jamil kai ma".

"Ala?ata da su daban...."

"Amma duk wata ala?a barin jini ce da ciki Waya, wai ba Jamil Win ba ne yake yekuwar sai ya bincike ka ba a kan Anty Aisha, haka son da yake makan yake? Maiyasa da tana raye basu damu da ita ba, sai bayan ranta har da barazanar zai yi bincike a kanka, wata?ila ma da saka hannunsa, shiyasa yake son ya ji ta ina kake binciken naka, ya ji ko asirinsa zai tonu, ka din ga wayo kamar ni mana"

Gaban Adam ya yanke ya faWi, kar maganar rumaisa ta zama gaske fa, gaba Waya jikinsa yayi sanyi, take ya ?aryata maganar rumaisa a zuciyarsa, ya san abun da ba zai taSa faruwa ba kenan. Ruma ta tashi ta ce "Papa sai da safe" ta kwashi kwanukanta, ta bar shi da tunani.

Haka ya kwana wa wayi gari, maganganun rumaisa na kai komo a kansa, idan ya ?aryata sai yaji abun bai kama zuciyarsa ba, kamar da wayo clue ta bashi, a kan binciken, idan ba rami meya kawo rami?

Washegari a wurin aiki, takawa da kansa ya je office Win Jamil, Jamil ya wani tsuke fuska.

Adam ya ce "Jamil lafiya kuwa? Tun da ka kaini gida, na ce ka Waukko rumaisa, ban sake ganinka ba"

"Me zan zo na yi maka? Dama kana sane ka tura ni Waukko fitsararriyar matarka, ta yi mini rashin kunya, tun da ka gama zubar mana da mutunci a idonta, ni zata kalla ta ce wai ba ?aunar aisha muke ba, ka je ka gama zazzage mata sirrinmu, meye amfanin dawo da abun da ya wuce? Adam turaki ya?i gaya mini komai a kan abun da ta gaya masa, dole na cigaba da bibiyarka da tuhumar ka akan dalilin Satan aisha bamu sani ba".

"Kuma ni ta ce maka na gaya mata?"

"Idan ba kai ba waye ya gaya mata? A ina zata sani ko ta ji? Kuma dole ka gaya mini abun da kake Soyewa, dan na fika kusanci da Aisha, ai jini ya fi ruwa kauri. Kuma zan cigaba da bibiyar yarinyar nan, sai na san gaskiyar abun da yake faruwa.

Adam ya haWiyi yawu ya ce "To shikenan, ai matata ce, na gaya mata Win, kuma Jamil kar ka fasa tuhumata da bibiyata, ka yi duk abun da zaka yi"

Ya daki tebur da ?arfin gaske ya ce "Kuma ina yi maka rantsuwa da Allah, idan wani abu ya samu matata, sai dai ayi mutuwar kasko da ni da kai, ka je ka cigaba da bincike a kaina, amma idan har zaka bibiyi matata ita za ta gaya maka abun da ya faru, ka shirya cewa watan faWuwarka ya tsaya, dan tana da ?wa?walwa fiye da lissafinka, kuma gaskiya ta faWa, a da baku damu da ita ba, kun cutar da ita meye na tayar da jijiyoyin wuya a yanzu? Idan ka matsa za ta saka ka a sar?a, kuma muddin ka faWo cikin suspect Wina, aikina zai bi ta kan ka"

Ayshercool
08081012143


Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please =?O?



A rikice Jamil ya kalli takawa ya ce "Kana nufin ni ne ke da alhakin yin garkuwa da aisha, kai ba a zargeka ba sai ni?"

Adam ya ce "Ni dama a can a cikin zargi nake, ban ce kai kayi garkuwa da aisha ba, amma abun da ka yi ya jefa ka cikin zargi, madalla da yarinya mai kaifin tunani kamar rumaisa" yana gama maganar ya fice daga office Win.

Wani irin gumi Jamil ya yakice, yana wani irin huci.

"Da ni ka ke zancen Adam, zaka gane ba ka da wayo, daga kai har wannan shegiyar yarinyar mai ?ulla mini jakar tsaba, saboda kaji su bini".

A daren jiya kuwa, Mahmud yawonsa ya din ga yi da Sabir, har da zuwa yawon ciye-ciye, ya sayawa Sabir kaya ba kaWan ba, soyayyar da? yakamata ya ji game da Wan uwansa Adam, shi yake ji a Sabir, koma ya ce fiye .

Ammi tana nan tana dakon dawowarsu, Nusaiba da Iman ma, duk suna tare da ammi, suna jiran dawowar Mahmud.

Wajen ?arfe tara da rabi, sai ga Mahmud, sidi ya biyo shi, da uban faggon kaya ni?i-ni?i, zuwa shashin Ammi, da da yake ji kamar wata ba?uwar duniya, amma yanzu the more yake shiga, the more yake zama familiar da wurin.

Mahmud ya nuna masa wuri ya ajiye kayan, ba tare da ya kula kowa ba, ya ?arasa kan kujera, ya kwantar da Sabir da yake bacci, ya dur?usa a gabansa yana ta shafa gashinsa, kamar ya tafi da shi, ya kwana a wurinsa.
Ya mi?e a hankali ya juya zai fita, Ammi ta ce "Wannan kayan fa?".

"Nasa ne" ya faWa a ta?aice ya fice.

A sashin Mummy ya tarar da Mummy ta rako Samha, tana ta rarrashinta, idonta yayi jawur, alamar ta sha kuka, ya san ba zai wuce ta gaya mata sa?on Adam ne ba, shiyasa take wannan kukan.

Sai da Mummy ta rakata har mota, sannan ta koma sashinta.

"Ina ka je ne? Tun sallar magariba baka dawo ba, baka kirani ba kuma, na san baka yawo da daddare".

"Na fita da Sabir ne"

A Wan razane ta ce "Waye Sabir?"

"?an mu da Adam ya haifa"

"Au yanzu dan rashin zuciya, har Wan sa ka je ka Wauka kana yawo da shi? Wurin giwar ka je kenan?".

"Sirikarta na saka ta Waukko mini shi, ina ?aunar yaron nan sosai da sosai"

Mummy a ranta ta ce "Lallai tsuguno ba ta ?are mini ba, akwai sauran rina a kaba, aikin malam na kan dutse ya fara sanyi"

Ya ce "Mummy, ya dai na ganki wani iri, akwai damuwa ne?".

"Damuwa akwaita Mahmud, ban gane maka bane kwana biyun nan, ka san dai a duniya bamu da ma?iya sama da giwa da Adam, yanzu kuma naga kamar ala?a ce tsakanin ka da matarsa, ko ka san yarinyar nan cewa ta yi wai ina yi wa Adam asiri?"

A ransa ya ce "Tom, hasashena ya tabbata, matar nan ta faWa tarkonmu"

"Na gaji da wannan rashin albarkar, nan ya zo ya gama yi mini rashin mutunci, a gabana ya ci mutuncin ?a?ana, saboda wannan hatsabibibiyar yarinyar, kuma ta ce wai ina yi masa asiri, a gidan ubanta ta ga asirin, zai maimaita a gaban mai girma wambai, dole ayi mini iyaka da ita".

Cikin ko in kula Mahmud ya ce "Amma dai idan ki ka kai ?arar wannan Yarinyar, za ace girma ya faWi, ra?umi da shanye ruwan ?an tsaki".

"Ba ita zan kai ?ara ba, shi Adam Win ita a wa, ina ruwana da ita, amma dole ayi mini iyaka da su".

***
Daf da la'asar, rumaisa ta shiga Wakin takawa, tana dudduba abun da za ta gyara.

Daga toilet ta ji ya ce "Waye a nan?"

Ta amsa masa da "Ni ce nan"

"Rumaisa duba drowern mirror, ki bani shaver".

Ta yamutsa fuska ta ce "Rumaisa kuma?"

Ya ce "Eh"

"Ba cewa ka yi mimi zaka din ga ce mini ba?"

"An?i ace mimin, mi?o mini da sauri"

Ta Waukko shaver Waya, ta tsaya a ?ofar banWakin ta ce "To shigowa zan yi?".

Ya ce "Eh mi?o mini"

"Au kai ba ka jin kunya, to ni ba zan shigo ba, zuro hannu ka karSa".

Ya ce "To ai ba tsirara nake ba, mi?o mini abu nake yi"
Ta tura ?ofar a hankali, ta Wan le?a, yana tsaye a gaban mudubin toilet Win, ya shafa wani cream a fuskarsa, da wata shaver a gabansa, ga wani towel Win a wuyansa.

Duk da haka sai ta ji wani iri, ta ?arasa a hankali, ta tsaya tana kallonsa.

Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Ya dai?"

"Bakomai, so nake naga me ake yi da shaver"

Ya Wan waro ido ya ce "Baki san me ake yi da ita ba?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Ba kya aski kenan?"

Rumaisa ta ce "Ni namiji ce da zan yi aske kaina"

Ya girgiza kai ya kerSi shavern ya ce "To tsaya ki ga me ake askewa da ita".

Aikuwa ta tsaya, ta zuba masa ido.

Ya kammala gyaran fuskarsa da ita, sannan ya Webo cream a wata container, ya shafa a hammatarsa da ta fara fitar da gashi, ba sosai ba.

A hankali ya sanya shaver yana cire gashin. Ta ce "Innalillahi, dama abun da ake yi kenan, to ni ya aka yi bani da shi, sai yaushe zai fito mini?"

Ya ce "Da gaske baki da shi?"

Rumaisa ta ce "Bai fito mini ba, kuma ina so, in ga ya fito mini da yawa, idan na Waga hannuna a din ga gano shi".

Adam ya ce "Saboda ?azama ce ke? Waye yake ado da gashin hammata, ?azanta ne to"

"Eh, amma dai ina son ya fito mini"

"Duk ranar da ya fito, ki ka bar shi, ni da ke ne, idan kin ga ya fara fitowa ya taru, ki yi mini magana in sake koya miki yadda zaki aske shi. Amma gashin hannta ba abun so bane, ba abun ado bane. I even wonder kin fara period but still a child"

Rumaisa ta ce "To ni dai Allah ya sa ya fito da wuri, sai ka sai mini shavern nima ko?".

Ya ce "To, jeki zan aske Wayan"

"Me?".

"Gashin" ya bata amsa kai tsaye.

"A ina yake shi kuma, ko na ?afarka, ga hannunka ma"

"A'a towel Win ?uguna zan kwance, nan ma akwai wani, shima ba a barinsa cirewa ake yi, idan ba haka ba mutum ya din ga wari, idan ya fito shima ki gaya mini a sayo shavern, sai in koya miki"

Yatsunta ta saka, ta toshe kunnunwata ta bar toilet Win, saboda ta daina jin abun da yake faWa, a tunaninta ai wannan abun kunya ne.

Ta fice daga Wakin sa, ta sauka ?asan bene.

Asiya da barira, suna ta yi mata sannu da gida, ta amsa musu tana gaishe su, sai dai ta lura da yadda baba Uwani ke ta wani kumbura fuska.

Ruma ta ce "Baba uwani, me nayi miki ne?"

Ta kalleta ta ce "Hmm tambayata ma ki ke yi?"

"Papa yayi mini faWa, ya ce kar na sake ai, ranar ma dan raina a Sace yake ne".

Asiya ta ce "Ranki ya daWe, wata jita-jita na jiyo, da na je karSo miki sa?o a wurin Ammi".

Ruma ta ce "Wace jita-jitar kuma?".

"Wai sa?o ya iske cewa, kin ce hajiya jamila, babar YallaSai Mahmud, wai tana? yi wa maigida takawa asiri"

Rumaisa na jin haka, ta san mahmud ne ya bayar da wannan sa?on, yana nufin baba uwani ta kai tsegumin, kuma shi ya saka ta faWa a gaban baba uwani.

Rumaisa ta waro ido ta ce "Ni Win, waye ya faWa? Ni harkar wa ma na shiga balle na faWi wannan maganar?" Ta Wan yi shiru sannan ta ce "Anya babu munafuki a sashin ammi? Idan ma na faWa, ai ba a gaban wasu bare na faWa ba, balle ma ban faWa ba. Amma ai ba ?arya nayi ba, idan ma na faWa, idan ta san ba ta yi, ai ba zata tsargu ba, idan kuma yin take, A'uzu bi kalaimatillahi tammat.

Tsuru-tsuru baba uwani tayi, tana ta ya?e baki ta ce "Ai uwar Wakina, asirin ma ba za a rasa yi ba, saboda abu ne na gidan sarauta, kowa kansa kawai ya sani, galibi ba Allah a ransu"

Ruma ta ce "Yauwwa, Aisya kin ji ko, barira ma kin ji, ga baba uwani ma ta faWa, mummy na yi wa takawa asiri, ashe bani kaWai na fuskanci hakan ba".
A rikice baba uwani ta ce "Ba haka nake nufi ba, ki yi wa Allah da ma'aiki kar ki ?ulla mini sharri".

"Ba sharri bane, ai ke ki ka faWa"

Rumaisa ta nufi hanyar satairs, cikin tashin hankali, da mamakin yadda jikar cikinta, take yi mata wayo, ta bi bayan rumaisa. Ruma ta tsaya ta waiwayo ta ce "Idan ki ka biyoni sai na gaya masa" ta juya ta cigaba da hawa.

Ta koma a sukwane kitchen, ta ce "Aisya, da ku za a haWu a ?ulla mini sharri ko?"

Barira ta ce "Ba wani sharri baba uwani, mu ba butulu ne irinki ba, idan baki yi wasa ba, an ?ulla miki kyakykyawan tarko kema, kamar yadda ake haWa baki da ke, ake cin dudduniyar giwa".

"In ji uban wa? Waye ya haWa bakin da ni?".

Asiya ta ce "Oho, a juri zuwa rafi da tulu...".

Barira ta ce "Wataran zai fashe".

Ruma kuwa daWi take ji, ta san tana daf da tonawa baba Uwani asiri. Ta shiga kitchen ta duba fridge, taga takawa ya kawo kaji, amma bai gaya mata ba. Ga kayan miya duk ya ajiye bai gaya mata ba, balle ta yi aikin su.

Tana aikin tana mita, ya zo ya tarar da ita a kitchen.

"To uwar ?orafi, menene kuma?".

"To ba kaine ka kawo aiki ba, kuma ba ka gaya mini ba".

Ya ce "No, su Aisya na ce idan sun gama aiki, su zo su gyara miki, sai ki Wibi naki, ki basu na gida".

Rumaisa ta ce "Saboda ni ban iya aiki ba ko? To Wallahi ina ?ar ?aramata, na iya gyara nama, ko kaza ko kofi, ni fa tun ina shekara uku mama ta ce nake kuka, a bani Sare maggi, da daka, na iya aiki sosai da kake ganina".

"To Allah ya baki ha?uri, idan kin gama, ki dafawa mama wani abun, ko mu saya a waje, mu je ki gaishe ta, dan ni ina zuwa mu gaisa".

Tsalle tayi a kitchen Win "Yeeee, zan ga mama, amma shine ka yi mini wayo, ka ke zauwa kai kaWai?".

"Eh, ai da yake maman tawa ce, ba taki ba, kuma a kyauta zan kai ki ba, da sharaWi".

Cikin mamaki ta ce "SharaWi kuma?"

"Eh sharaWi mana.

Ta ce "Na me?"

"Kiss zamu yi"

Ta kwaSe fuska ta ce "Kiss, iskanci fa kenan".

Ko a jikinsa ya ce "Eh, shi zamu yi".

"TaS wallahi a'a, ?azantar?"

Matsawa ya yi kusa da ita, ya sunkuyar da fuskarsa dai-dai tata, ta rintse ido ta kame jikinta.

Ya ce "Wai ke haryanzu kamar robot ki ke, ba kya jin komai ne?"

Ta sake kawar da kanta gefe, tana rintse ido.

Ya rungumota a jikinsa, ya kai fuskarsa tata.

"Wallahi idan ka yi mini zan yi ihu, kuma ma ba kullum nake yin brush ba, bakina wari yake" ba ?aramar dariya ta bashi ba, gaba Waya ta tsorata sosai.

Ya girgiza kai ya ce "Ki yi girki mu tafi da shi, idan an yi sallar magariba zamu tafi" yana fita, tayi ajiyar zuciya, tana ta sauke numfashi.

***

Iman ce zaune a gaban Ammi, ta tattara mata hankalinta, jin ta ce mata, akwai maganar da take son su yi mai muhimmancin.

Ammi ta ce "Iman, Jabir ne yazo mini da wata magana, wai yana sonki, kuma nan kusa yake son ayi komai a gama, baki ji daWin da na ji ba, kin ga shi na gida ne, kuma ya san duk halin da ake ciki"

Ras! Gaban Iman ya faWi, mussaman ganin yadda ammi ke murna da al'amarin.

"Ya ki ka yi shiru, ba ki ce komai ba?"

Iman ta ce "Ammi tsoro nake ji, kin san mamansa ba za ta amince ba"

Ammi ta ce "Iman addu'a zamu yi, Allah ya sa ta amince ya shige mana gaba, na san babu yadda za ayi"

Jiki a sanyaye Iman ta ce "To Ammi" daga haka ta tashi ta tafi Wakinta, ammi ta nuna goyon bayanta a kan lamarin, gashi ita ko kaWan, ba ta ra'ayin Jabir, hasali ma zuciyarta na tare da wani daban, da bai san tana yi ba.

Mai sunan baba yana Wakinsu yana cin abinci, yana jiyo tsalle-tsallen ruma a tsakar gida, takawa kuma yana tare da mama suna hira.
Haka kurum ya ji gabansa ya faWi, har sai da ya ji tamkar abincin da ya haWiya ba zai wuce ba.
A take tunaninsa ya kai kan iman, ya janyo wayarsa, ya shiga What's app Win sa, sai dai ba ta online, to idan tana online ma me zai ce mata?.

Ya taso ya fito tsakar gida, rumaisa ta zauna ta saka Yasir a gaba, suna magana ?asa-?asa.

"Yasir, kai ka san ta kan waya, na san kai gwani ne, hacker ne kai, hacking nake so ka yi mini"

Ya harareta ya ce "Ni ne hacker?"

"Yi ha?uri, wani abu zaka yi mini, wayarka zaka ara mini, zan haWaka da wanda zaku yi aikin tare, sirri muke so".

"Ke, bana son iskancin banza, haka kurum ki ja mini masifa, ke idan kin nemo magana mijinki zai fitar da ke, ni kuwa fa?"

Ruma ta ce "Ba irin wannan aikin bane, yaya usy ya san komai, tare muke shawara ma, papa zaku tayani mu taimakawa, amma bana son ya san halin da ake ciki, bari ya usy ya dawo, zan baka lambar Mahmud Win, ?anin mijina ne" gyaran murya suka ji a bayansu. Ruma ta waiwaya taga mai sunan baba a tsaye.

Da sauri ta tashi ta ce "Laa mai sunan baba ina wuni, ban san kana nan ba ai"

Alama yayi mata da ta je, ta ?arasa zuwa cikin Wakinsu, ya kalleta ya ce "Ina yarinyar nan, ta warke?"

Cikin rashin fahimta ta ce "Wace yarinyar?"

"?anwar mijinki?"

Ruma ta ce "Auu, Anty Iman, dama ba ta da lafiya ne?".

Ya ce "Never mind, je ki kawai".

"Tana lafiya ?alau, shekaranjiya ma mun je gidan, kusan kullum idan muka je, sai ta ce mini ina yaya Umar, ko ta bani wayarta ta ce....

"Fita ki bani wuri" ya katseta, saboda yadda ta fara zuba.

Sum-sum ta fice, ya nemi wuri ya zauna, yana tuhumar kansa meye ma na tambayar rumaisa.

Tamkar mata, haka suka din ga shewa da Usman ya dawo, ta baje musu abincin da ta zo da shi, ta haWu a cikinsu, suna ci.
Idan da sabo, takawa ya riga ya saba, dan haka ba ya damuwa ma yanzu, ya riga ya fuskanci irin ala?ar da ke tsakanin su, shiyasa a rashin su, take sauke masa duk wani kwandon rashin ji da take yi musu.

Sai ?arfe goma suka bar gidan, suka tafi gida.

***
"Jamila ina cikin damuwa, wai ni Jabir zai tunkara, ba tsoro ba kunya wai yana so in bashi dama ya auri ?ar da giwa ta tsinto iman?"

Mummy ta ce "Ni na san wannan maganar tuni, ba wannan ne ya dameni ba, lamari ya fara jagulewa, na fuskanci kamar aikin malam na kan dutse ya fara sanyi"

Cikin mamaki ta kalli Mummy ta ce "Kin sani fa ki ka ce? Amma baki gaya mini ba"

"Ban zaci abun har zai kai haka ba, ban Wauka da gaske zai yi maganar aure ba, amma na san ba wata matsala ba ce ba, zaki iya jajircewa a kan hana faruwar hakan".

"Lallai ma jamila, ke kin fi kowa sanin, ba zan haWa ala?a da giwa ba, ya auri ?ar ta idan Allah ya sa ya samu sarauta, su mallake mini Wa?"

"Lubabatu naki fa mai sau?i ne, nifa abubuwa sun fara sakwarkwacewa, dole a nemo sabon boka, duk da na bayar da aikin da aka bani na ?arshen nan, amma dole na nemi abun yi, akwai matsala".

Hajiya Lubabatu ta ce "Kin ga ni yanzu bana gane komai, sai anjima ma yi magana daga baya kawai"

Mummy ta ce "Dole in motsa in sauya taku, ban taSa samun matsala a abubuwan da nake ba sai a wannan karon, saboda zuwan wannan matsiyaciyar yarinyar, ?ar wannan abar daga zuwanta za ta hargitsa komai, Allah ya sa uwani ta yi abun da na sakata, yadda yakamata".

Wayar Mummy ta fara ringing, ta duba taga baba Uwani ce, ta

Please Login or Register in order to submit comment