You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai kai ba kurma bane ba, kuma ka na jina, jibi in Allah ya kaimu zan je duba galadima" sai a yanzu Adam ya Wago ya kalli Jabir ya ce "Ubangiji Allah ya tsare hanya, ka ce ina gaishe shi" Jabir ya girgiza kai ya tashi ya fice, dan halin Adam sai shi wasu lokutan.

***
Tun da rumaisa suka yi waya da ammi, take ta zuba ido ta ga ta ina za a kawo mata Sabir ta ganshi, danne zuciyarta kawai take yi, mussaman idan ta tuna da alwashin dabta yi wa Adam, a akan ba zata sake zuwa gidansu ba.
Ammi kuwa ta kasa ta tsare, ta ce lallai Adam ya Wauki Sabir, da shi da Iman su je a kaiwa rumaisa shi, ko awanni su yi tare ta ganshi, tun da dai an yi mata al?awarin yin hakan, a duk lokacin da ta bu?ata.
Tun da Iman ta ji za su je gidansu rumaisa, gabanta ya faWi, saboda tana matu?ar fargabar haWuwa da yayan rumaisa mai sunan baba, dan ita gaba Wayansa tsoro yake bata.

Adam dan dai babu yadda zai yi da ammi ne, ba zai iya bujerewa maganarta ba, amma a ganinsa tun da ya yadda da auren, wannan aika shin da ammin take, ba abun da zai janyo masa sai raini.

Da la'asar suka shirya, aka shirya Sabir suka fito domin tafiya gidansu rumaisa, Adam na gaba iman na bin sa a baya da Sabir. kasancewar Mahmud ?afarsa ta fara sau?i, ya fara yawonsa a cikin gidan, hango Iman yayi da yaron a hannunta, wanda ko ba a gaya masa ba ya san shi ne jaririn, haka nan ya ji ya kwaWaitu da son ganin fuskar yaron, tun da a yanzu, kansa kawai ya hango, mai Wauke da tulin suma ba?a wuluk.

Suna tafe a hanya Iman na yi wa sabir wasa, yana ta mi?a hannu yana son kamo sitiyarin motar.

"Iman" Adam ya kira sunanta.

"Na'am yaya".

"Abubuwa sun fara yi mini zafi, na san magana zata fara yawo a kan auren nan nawa, dan Jamil ya zo ya tutsiyeni na gaya masa idan maganar gaske ne, kuma na tabattar masa da gaske ne, abun da nake so da ke, dan Allah ku yi shiru da bakinku, kar wanda ya san wa zan aura, idan an yi auren sa ganta"

"Yaya kunya ka ke ji ace rumaisa ce matarka?"

"Ke rabu da ni kawai, banda rigimar ammi, ina ni ina wannan Yarinyar da a rayuwarta babu wanda ta raina kamar ni, kuma bana son a cutar da ita, Samha haryanzu tana son aurena, a wannan karon ma ba zai yiwu ba, shiyasa bana son kowa ya san wacece".

"In sha Allah yaya ba zan faWawa kowa ba, ammi ma ta gargaWemu a kan hakan"

Ya ce "Good, ku shiga ki kai mata shi, ni zan je gidan gona, wancan karon ban samu na je ba, saboda wani dalili " yayi maganar lokacin da ya yi parking.

Ta ce "To shikenan, sai ka dawo" ta sauka ta Wauki kayan rumaisa da ammi ta sake bayarwa a bata, ta shiga gidansu rumaisa da sallama.

Sai dai gidan shiru, babu alamar aksai mutane a gidan.

Iman ta yi sallama, sai dai muryar da ta amsa mata sallamar ce ta razanata. Kasa shiga ta yi, ta kuma kasa komawa baya.

Shi kuma bai kuma tankawa ba, sallama ta kuma yi, ya ce "An amsa a shigo mana" daga Wakin mama take jiyo muryarsa, kamar mai shirin arangama da horo, ta shiga Wakin.

Mai sunan baba ne a zaune yana cin abinci, mama kuma tana salla.

Cikin War-War, ta shiga ta zauna hannunta rungume da Sabir, kanta a ?asa ta ce masa "Ina wuni?"

Bai kalleta ba ya ce "Lafiya lau" Sabir ya ?urawa mai sunan baba ido, "Mi?o mini shi" yayi mata maganar cikin umarni.

Kai a ?asa ta mi?a masa Sabir, ya rungume shi yana cewa "My boy, ka ?ara girma Masha Allah" bai yi masa ?yuya ba, ya cigaba da cin abincin sa, iman ?o?arin satar kallon mai sunan baba take tana tsoro, shi kuma da ya lura da hakan, sai ya tsareta da idonsa tana Waga ido suka yi ido huWu, aikuwa ta razana ta sunkuyar da kanta.

'Yarinyar nan tana da hankali kuwa?' mai sunan baba ya tambayi kansa.

Mama ta idar da salla da addu'a, ta juyo tana yi wa iman sannj da zuwa.

Iman ta gaisheta mama ta amsa mata cikin sakin fuska, Iman ta ce "Ammi ce ta ce a kawo wa Anty rumaisa Sabir"

Mama ta ce "Allah sarki, yanzu za ta shigo daga islamiyya, ya babansa?"

"Yana lafiya shi ya kawomu, zai dawo ya Waukemu ma"

Mama ta kalli Sabir ta ce "Mutumin, zo mu gaisa mana" ya sake kwanciya a jikin mai sunan baba, yana cin hannunsa.

"Allah ka aika munafukinmu ?arshen nesa, mamarmamar, igiyar ?asa ko da lafiya ko babu mamarmamar" Rumaisa ta shigo tana wa?e-wa?enta, da ?an ciye-ciye.

Tana shiga falon mama sabir ta fara gani, ta buga tsalle zata Wauke shi, mai sunan baba ya ce "Fita ki yi sallama" sumi-sumi, ta koma ta yi sallama, sannan ta Wau sabir tana murna.

Ta kalli Iman ta ce "Anty iman sannu da zuwa, ya ammi?"

"Tana lafiya tana gaishe ki"

Babban abun da ya bawa mama mamaki, bai wuce yadda Sabir ya saki fuskarsa ba da ya ga rumaisa.

Rumaisa ta shimfiWa tabarma a tsakar gida ta ce "Anty Iman, dawo daga nan mu yi hirarmu, ya fi iska"

Haka yayi wa iman daWi, dan mai sunan baba ya takurata.

Rumaisa ta cire wandon uniform Win ta, daga? ita sai rigar uniform, ba hijjabi ba Wankwali, sai murna take yi.

"Anty Iman, bari na zubo mana abinci"

Iman ta ce "Wallahi a ?oshe nake"

"Ba kya cin abincin gidan talakawa dai"

Da sauri Iman ta ce "A'a wallahi"

Rumaisa ta ce "To kawai zan zubo ki ci".

Rumaia ta zubo wa Iman jallof rice, mai kyau har da nama, ta kawo mata ruwa, ita kuma ta Wauko tukunyar da aka yi girkin da cokali da yaji ta zo ta zauna.

"Anty rumaisa me zaki yi da tukunya kuma?"

"?anzon shinkafa zan ci ya fi daWi"

Iman ta zuba mata ido tana dariya, rumaisa ta din ga kankarar ?anzo ta na ci, Sabir ya din ga zura hannu yana nema ya ci shi ma.

Iman ta na cin abincin tana yi wa rumaisa santin abinci yayi daWi.

"Garadan mama ne suka girka, kuma ba wani daWi yayi ba kar su ji ki ziga su" hira suke yi sosai da iman.

Suna tsaka da hirar suka ji sallamar Adam a ?ofar shigowa gidan, suka amsa masa, mama ta ce ace ya shigo, mai sunan baba ya tashi ya baro Wakin mama, dan ya san nan zai shiga.

Adam na shigowa da rumaisa ya fara tozali, ta ta?ar?are tana kankarar ?anzon tukunya tana ci, kamar mayuwanciya, ga kuma abinci mai kyau a gaban iman, Sabir kamar zai shiga cikin tukunyar, yana son ya duntsi ?anzon ya kai bakinsa.

Ayshercool.
08081012143


PAID BOOK NE, ? 500 VIA 0009450228,AISHA ADAM JAIZ BANK SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143.




Sallamar Adam bai hana rumaisa cigaba da ta?ar?arewa tana ?wa?walar ?anzo da cokali tana cin kayanta ba, ba ta da niyyar tashi ma ta saya jikinta, abun da ya dameta kawai take yi.
Usman da tun zuwan iman yana cikin Wakinsu, ya le?a ta window, ji yayi kamar ya fito ya kifawa rumaisa mari.

Adam ya wuce su, ya shiga wurin mama, Iman ta kalli rumaisa ta ce "Anty rumaisa baki gaida takawa ba?"

Ruma ta kwaSe baki ta ce "Kin ga ya kulani ne?"

"Amma da kin yi masa magana zai kula ki"

Rumaisa ta ce "Wallahi ba zai amsa ba"

Cikin mamaki iman ta ce "Meyasa ki ka rantse"

Ruma ta ce "Mufa gidan nan babu mai kalar halin da babu, dan haka ko sau Waya na haWu da mutum zan gane halinsa, ni ba dan Sabir ba kuma a daina ce mini ?ar iska ba, ba abun da zai saka na aure shi, kuma dai ina son ammi ita ma ina jin maganarta, amma wannan mak faWan da zuciyar taS"

Iman ta ce "Wai ni, meyasa ba kwa shiri ne, wallahi takawa mutumin kirki ne sosai Anty rumaisa, ko wani abun yayi miki?"

"Hmm ba ruwanki a wannan faWan"

Iman ta ce "Haka ne, faWan masoya ne" aikuwa rumaisa ta ?ware da ?anzo jin abun da iman ta ce, "TaS lallai kin tafka saSo"

Iman ta kuma cewa "Allah Anty rumaisa, yaya Adam yana da kirki sosai, ki din ga yi masa uzuri, abubuwa sun saka shi a gaba, kawai kina ganinsa a haka ne, idan ki ka ji abubuwan da yake ciki sai kin tausaya masa".

Ruma ta taSe baki ta ce "Da zai gane da ya daina Waukar damuwowinsa a zuciyarsa, babu abun da zasu ?ara masa sai nauyin zuciya, ya din ga Waukar damuwowinsa a ?wa?walwarsa, ita ke da ma'aunin samar da mafita"

Mamaki ne ya kama Iman, jin rumaisa na wani lissafi, da ba ta gane ba.

"Ban gane me ki ke nufi ba".

"Kar ki damu, manta da ni kawai, bari na Wauko takarda da biro ki rubuta mini lambar wayarki, zan din ga kiranki muna hira".

Iman ta yi murmushi ta ce "Akwai jotter a jakata, bari na rubuta miki" Aikuwa ta rubutawa rumaisa lambarta, a lokacin rumaisa ta shagala da wasa da sabir, sai dariya yake yi.

A daidai lokacin Adam ya fito, mama ganin a yadda rumaisa ke zaune ba ?aramin ?ular da ita ya yi ba.

Iman ta ce "Anty rumaisa kawo shi mu tafi" a take jikin rumaisa yayi sanyi, ta sake rungume Sabir.

Mama ta ce "Ke bana son shirme, ki ba ta shi su tafi"

Kawai ta fara kuka, hawaye wani na bin wani, wanda a ganin adam kawai shagwaSa ce da wula?anci.

"Mama dan Allah a bar mini shi a nan, mu kwana tare" mama ba ta saurari rumaisa ba, ta karSi sabir ta bawa iman.

Wadda jikinta yayi sanyi, tausayin rumaisa ya mamaye mata zuciya.

Kallon ruma da take kuka Sabir yake yi, Iman ta ce "Ka yi wa maminka bye-bye"

KwaSe baki ya shiga yi, zai yi kuka, Adam ya karSe shi ya yi waje da shi, saboda haka nan ya ji tausayin su ya kama shi, wata irin Soyayya mai ban mamaki tsakanin yaro da zuciyar da ba ta uwassa ba.

Iman ta dafa kafaWar rumaisa ta ce "Anty ruma ki yi ha?uri kin ji, da kun yi auren nan, za a dawo miki da sabir Winki, ki daina kuka" ruma ta jinjina mata kai ta ce "Ki gaida Ammi, da wannan Win nan mai kamar da baban sabir"

"Tom za su ji in sha Allah"

Suna tafiya mama ta dirarwa da rumaisa faWa, mussaman a kan rashin hankalin da ta tafka, a gaban wanda zata aura ta ta?ar?are tana kankarar ?anzo tana ci, babu ko kunya balle kawaici, ga wannan koke-koken na babu dalili da take yi, a duk lokacin da aka kawo sabir.

Ita dai rumaisa a wurinta, ba ta Wau adam wani na mussaman ba, balle idonsa ya hanata abun da take yi, tun da duk gidansu maza ne, ita ba ta Wau abun da ta yi wani laifi ba.
Maganar Sabir kuwa, ta barwa ranta cewa babu wanda ya san halin da take ciki sai Allah a kan yaron nan, dan haka ta daina damuwa a kan mitar da ake yi mata.

Usman ya fito yana faWin "Bagidajiya kawai, wannan ai yawa ne ki ka yi, to wallahi nan gaba rainaki zai yi, sai la ce wata budurwar ?auye, ke ba wani class bakomai"

Abdalla da bai daWe da shigowa ba, ya tambayi mai ta yi, Usman ya gaya masa, ya ce "Kai yanzu har wani aji kake nema a wurin rumaisa, ai tun da suka ce za su aureta a haka, sai fatan Allah ya sanya su gama lafiya"

Ko a jikinta, an mintsini tattaura, abun da ya dameta kawai shi ne a gabanta.

***
Su Iman da suka koma gida kuwa, Ammi ba ta nan, Iman ba ta son ta fita ta koma gida ta tarar Ammi ba ta nan, gashi tare suka fita da Nusaiba, Kasancewar Sabir yayi bacci, da shi Adam ya tafi sashinsa ya kwantar da shi, Iman kuma ta wuce Wakinta.

Sai dai tana zuwa Wakin, ta yi tozali da Samha a tsaye, sai da ta razana ta ce "Anty Samha lafiya kuwa?".

"Ban sani ba, munafuka tsintacciyar mage da ba ta mage" cikin rashin fahimta iman take kallonta, dan ba ta san me ya kawo wannan maganar ba.

"Saboda tsohuwar munafuka ce, shi ne ki ka je ki ka cewa giwa kina son Adam, za a haWa aurensa da ke a maimakon ni, duk da irin kashedin da na yi miki ko?"

Kamar zata yi kuka ta ce "Ni kuma?"

"Ke Win fa, algunguma ni zaki yi wa pretending, to ki rubuta ki ajiye, gidan Adam kabarinki ne, yadda aisha ta shige shi ta bar duniya, duk wadda ta shiga bani ba sai ta bita, idan ba haka ba kuwa ayi babu, kowa ya rasa daga ni har ke, da ni ki ke zancen, zan yi maganinki ba?ar annamimiya"

Gaban Iman ya faWi da jin furucin da Samha ta yi, tana gama zazzage mata ta yi waje.

Jikin iman har rawa yake yi, saboda tsananin tashin hankali, da yadda hankalinta ya dugunzuma, a take rumaisa ta faWo mata, wato a zaton Samha Takawa ita zai aura, tausayin rumaisa ya kamata ya ruma za ta yi da wannan manyan al'amura ta ko ina, ga ma?iyan mijinta, ga tarin ?alubalen gidan, ga kuma masifar Samha, a kaf dangin nan babu wanda bai sarawa masifar Samha ba, an shakkarta sosai da sosai, saboda a tsaye take ba ta da kunya, yaya rumaisa za ta yi da ita, ita da take yarinya ?an?anuwa?.

Rasa abun yi ta yi, ta saSule ta zauna a kan gadonta, ?irjinta na cigaba da dukan uku-uku saboda tsananin fargaba.

Mintuna kusan sha biyar da fitar Samha, amma iman ta kasa kataSus, ?irjinta sai cigaba da bugawa yake yi.

Nusaiba ce ta shigo da sallama ta ce "Ashe kun dawo, bamu zaci zaku rigamu dawowa ba, mun je sai wa Sabir kaya, kin san ya kusa 6months, Ammi sai nuna mini irin kayan da za a zubawa amaryar takawa a lefe take, ya kuka baro ta?" Sai da Nusaiba ta kai aya, sannan ta lura kamar Iman a tsorace take.

"Lafiya kuwa?"

Iman ta jinjina mata kai ta ce "Lafiya lau"

Nusaiba ta ce "Kin ga idonki kuwa kamar mara gaskiya, ko wani abun ya faru a gidan da ku ka je ne?" Iman ta girgiza kai alamar a'a.

"Tsaya, ko jikinki ne ya motsa?"

Iman ta yi ajiyar zuciya ta ce "Babu ko Waya, cikina ne ya Saci zuciyata ce take tashi"

Nusaiba ta sauke numfashi ta ce "Har kin tsorata ni, bari na kawo miki anti acid, ina da shi a Wakina" iman ta jinjina mata kai.

Da Nusaiba ta fita ta sanarwa da Ammi iman ba ta jin daWi, ulcer ya tayar mata, a rikice ammin ta nufi Wakin Iman, ta je ta tutsiyeta tana tambayar ko jikinta ne ya motsa.

Kamar yadda ta yi wa Nusaiba ?arya, haka ta dake, ta Soye damuwarta, ta tabattarwa da ammi, ulcer ne kawai ya tasar mata.

***
Kwanciya ce ta isheshi, musamman da kwana biyun nan, a gida yake wuni saboda ?afarsa, amma yanzu ta yi sa?i sosai, kawai dai fita ce bai yi ba, gashi ya kusa komawa makaranta.

Kamar wanda aka tsikara, ya tashi ya fita falo, ya Wau lemon kwali mai sanyin gaske, ya koma Wakinsa, corridor ya nufa, ya buWe tagar a hankali, wata sassanyar iska ta dake shi, ya zu?e lemon tare da lumshe idanunsa.

Dare ne sosai, manyan security lights, sun haske ko ina na gidan, kukan tsuntsye na ta tashi, da ?anan ?wari, ga ?amshim furannin harabar gidan sun gauraye da sassanyar iskar da ke kaWawa.
Yanayin yayi masa daWi sosai, sai dai babu tsammani ya ga wani abu yana duddu?e, yana motsi ta jikin fulawoyin da zai sadaka da sashinsu.

Tsayawa yayi ya ?ura ido sosai, yanayin inuwar abun, kamar mace ce, dan har da lulluSinta.

Mamaki ne ya kama Mahmud, ganin maimakon ta shigo direct ?ofa, ta kutsa can ?arshen ginin da kai tsaye Wakin Mummy zai kai ka.

Bai yi wata-wata ba ya sauka, ya nufi sashin Mummy a hankali, sai dai bai buWe ya shiga ba.

"Kin shanya ni, tun Wazu nake zaman jiranki, amma baki zo ba"

Baba uwani ta risuna ta ce "Tuba nake Allah ya baki yawan rai, sawu ne bai gama Waukewa ba"

Mummy ta hura hanci ta ce "Ina jinki, bani labari, meke wakana da ki ke son ganina?"

"Allah ya baki yawan rai, labari ne nake tafe da shi, idan yayi miki daWi haka nake fata, idan bai yi ba ayi mini aikin gafara"

Cikin ?osawa Mummy ta ce "Hanzarta, ina jin ki"

"Takawa zai yi aure, sai dai alamu sun nuna kamar Iman zai aura, kuma zancen ya iske Samha ?ar wurin turaki, dan Wazu ta zo har wurin Iman Win ta yi mata kashedi da zafafan kalmomi, dan na laSe na ji komai"

"What? Aure kuma? A wannan karon kuma ita za a li?awa, ita ma ya cinyeta, lallai giwa ba ta tsoron Allah, amma na yi mamakin yadda aka yi Samha ta zo ba ta ?araso nan ba, kuma ba ta yi mini wannan bayanin ba, ko da yake ni kujera ce, ko dan zama za a neme ni, jeki na gode na ga yadda wannan lamarin zai yiwu"

Baba uwani ta ce "Godiya nake, na barki lafiya".

Mahmud ya so shiga Wakin Mummy, dan ganin wacece wannan, take zuwa a tsohon daren nan, amma ya fasa, ya lallaSa ya buWe ?ofa ya fita harabar gidan ya laSe.

Can baba uwani ta fito tana duddu?enta cikin duhuwar fulawoyi, ta nufi sashinsu ammi, tana buWe ?ofar, fitila ta hasketa, dan haka ya ganeta da kayan jikinta.
Hakan ya fallasa ma wacece ita, domin kuwa baba uwani kayanta ba Soyayyu bane ba, duk da tarin alkhairai da suturar da ammi ke bata, amma kullum cikin kaya Waya zuwa uku take.
Kan sa ya Waure da mamakin me take zuwa yi sashinsu, a wannan daren cikin siga ta rashin gaskiya

A hankali ya koma sashinsa, gaba Waya baya son wannan halin na Mummy, na bin diddigi da shiga abun da babu ruwanta, ya san ?arshe ba zai wuce rahoton wani abun ake kawo mata ba. Amma ya sha mamaki, idan har ace hadimar ammi ta kusa da ita, za ta aikata mata haka, to duniya kowa ma ba abun yarda bane ba.

***
Kwanci tashi asarar mai rai, mai girma turaki ya dawo daga aikin umara da ya tafi, duk da an riga an saba zuwa, amma ba a rasa ?an sannu da zuwa da su kan zo, domin yi masa barka da dawowa.
Ammi ba ta son takura masa, dan haka ta bashi lokaci, tare da sauraron abun da zai ce mata.

Duk da a nata Sangaren ta tsananta addu'a a kan lamarin sosai da sosai, tare da fatan tabattuwar alkhairin da yake cikin al'amarin.

?angaren Samha kuwa, da fari a iya tunaninta, za ta iya ji da lamarin, amma abun ya shallake tunaninta, kuma gaba Waya hankalinta ya karkata a kan Iman ce ake ?o?arin aurawa takawa, dan haka ta fara tunanin yadda za ta yi da ita, a ?arshe dai ta koma wurin Khalifa, domin samun mafita sannan ta je ta samu Mummy da zancen.

Mummy ta yi dariya ta ce "Yaro man kaza, ai na yi zaton ba zaki gaya mini ba, shi ya sanya na zuba miki ido na ga iya gudun ruwanki, ba shakka giwa wata irin murWaWWiyar mace ce, mara al?ibla, dan haka dole ki zage ki san abun yi"

Cikin damuwa ta ce "To ni yanzu Mummy ya zan yi?"

"Duk abun da ya kama ki yi, ko dai a kan Iman Win, ko kuma a kan giwa ko ma adam Win. A baya babu abun da ba mu yi ba a kan yarinyar nan, wanda hakan ya sanya duk ta rasa manemanta manyan mutane da suke zuwa wurinta, dan haka yanzu shine giwa ta yanke shawarar ?arshe na aura mata adam, shawara ta rage gareki, ko dai ki bari ayi auren daga baya ki san abun yi, ko kuma dai ki Wau wani matakin"

"TaS, ai wallahi da na bari ya aureta, gara uban kowa ma ya rasa, ni Mummy a cikin malamanki nake son ki haWani da wani, a watsa komai ko da kuwa yana nufin in rasa ta rasa kowa ma ya huta ne"

Mummy ta jinjina kai tana murmushi ta ce "To shikenan, zan yi tunani a kai kar ki damu"

"Mummy ba ni da dogon lokacin da zaki yi dogon tunani, dan Allah ki taimaka".

"Na ji zamu yi waya, ko zuwa sunday ne, akwia wani ?auye da nake zuwa, sai mu tafi tare"

Samha ta ce "To shikenan, na gode sosai Mummy".

Kusan sati guda da dawowar mai girma turaki, giwa har ta fara ?osawa, tana tunanin ko magana za ta yi masa, babu tsammanni ya kirata a waya ya ce zai zo.
Hakan yayi mata daWi, sai dai ta shiga fargabar da wacce zai zo, da nasara ko kuma babu?"

Kasancewar baba uwani na wurin, ammi ta yi waya da turaki, baba uwani ta saci hanya, ta je ta kira mummy a waya, ta kai mata rahoton cewar turaki zai zo, kuma da alama magana mai muhimmanci zasu tattauna, dan haka Mummy tace lallai ta sanya mata ido, ta naWo mata duk wani rahoto na abun da zai wakana.

Bayan sallar azahar, mai girma turaki ya iso gidan, kai tsaye ya sauka a sashin giwar da.

Hadimai suka shiga hidimar kawo kayan ciye-ciye, sai dai turaki ya?i magana a kan ha?i?anin abun da ya kawo shi, a lokacin da hadiman ke kaiwa suna komowa.
Dama tuni ammi ta hana Adam fita, ta ce lallai koma menene ya zauna ayi a gabansa, dan haka shima yana nan.

Ammi ta sallami hadimanta, Sannan ta nutsu ta fuskanci turaki.

Hakan ba ?aramin Satawa baba uwani rai yayi ba, dan babu damar samun rahoton da take son samu.

Ammi ta dubi turaki ta ce "Ranka ya daWe an dawo lafiya ya hanya? Ban samu shigowa ba, saboda ba na son zuwan nawa ya zama takura ko matsi a gareka, shiyasa ban yi maka sannu da dawowa ba"

Turaki ya ce "Kar ko damu, da ke da abun ya shafi zuriyar marigayi, dolenmu ne, kuma babu yadda za ayi ku zama takura a garemu.
Toh! Na zo da sa?onki, a can saudiyya ma na je gidan Wan uwanki mahadi, mun tattauna da shi sosai, kuma ya bayar da amanna sosai. Sai dai da muka dawo gida da kwanaki uku, mun sami wambai, in da ya nuna rashin amincewarsa da nuna za a sake zubar da darajar masarauta, ta hanyar auro wadda ba jinin sarauta ko tushen arziki ba, sai dai na yi iya yina na nuna masa ?ar gidan daraja ce da kuma gudunmawar da ta bayar.
Har ila yau ya gaya mana zancen da bamu ji daWinsa ba, ya kawo ?orafi sosai a kan ka takawa, ciki har da yin?urin taka Wan uwanka da mota, wannan lamari bai yi mana daWi ba, ya ce ya bayar da sa?o ka je, nan ma ka yi burus. Abun bai yi mana daWi ba, har yayi i?irarin babu shi babu kai, sai dai mun yi ?o?arin kwantar masa da hankali, in da har mai Wakinsa ta sanya baki, ta hanyar nuna masa tsaurinsa a gareka yayi yawa, shiyasa ba kwa shiri, amma dai duk da haka yakamata a din ga lura ana kiyaye wasu abubuwan, yanzu idon duniya a kan ka yake".

Ammi ta ce "Wallahi ranka ya daWe, abun da nake yawan gaya masa kenan, amma dai a cigaba da jaddada masa"

Turaki ya ce "Haka ne, akwai bu?atar a din ga kai zuciya nesa, akwai abun da yarinyar nan ta faWa mini a kan ka, wanda kuma tabbas haka ne ba ta yi ?arya ba, yana daga dalilan da ya sanya na yi amanna da auren nan sosai, nake yi muku fatan alkhairi".

Ammi ta ce "Allah sarki, Adam kuma ya sunkuyar da kai, yana murza zoben hannunsa.

"To, mun dai yi ?o?arin shawo kan wambai da ?yar, duk da yana nuna ba da yawunsa ba, amma ba wani abun damuwa bane ba zai sakko, illa iyaka kai takawa ka je ka same shi ka bashi ha?uri.
Magana ta gaba kuma, a sanar da iyayen Yarinyar nan, ranar juma'a zamu kai kuWin aure, kuma wata biyu zamu sanya rak, Allah ya tabbatar mana da alkhairi dan ba ma fatan a jinkirta wani abun ya zo ya gilma".

Ammi ta faWaWa murmushin ta

Please Login or Register in order to submit comment