You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Waya, kuma ki ciko ki murmure sosai, idan kuma kin shirya cigaba da zama ana yi miki gori shikenan".

Ruma ta tuna iskancin da su Fauziyya suka din ga yi mata, wai a kalli ?irjinta kamar plate, ga samha cikakkiyar mace, amma takawa ya aureta, ta gyara zama ta ce "To ita maman khadijan a ina take? Kuma yaushe zaki sai mini kokon nata".

Laila ta ce "Ni ban ce miki koko take sayarwa ba, garin kunun sabaya take sayarwa, amma ba a kano take ba, a zariya take, bayan federal palladan. Na daWe ina harka da ita, kuma na haWa mutane da ita sosai, na san ingancin kayanta. Zan yi waya da ita, a sayo, tunda tana tura kayanta ko ina, amma ba zan baki ba, sai na ga gwargwadon biyayyarki"

Rumaisa ta yi shiru tana kallonta, laila ta gama bayananta, rumaisa ba wani fahimta tayi ba, ita dai babban fatanta, a samo abun da laila ta faWa na yin kunu, saboda ta sha ko ya fito ta huta gori.

(*INA UWAR GIDA DA AMARE, INA WANDA SUKA HAIHU, KO SUKA YI YAYE, INA MASU RAMA DA SU KE SON JIKINSU YA MURMURE SU YI ?IBA, INA MASU YARA WANDA SUKE FAMA DA MATSALAR RASHIN GIRMA? SHIN KEMA MIJI NA YI MIKI GORI, KAMAR YADDA TAKAWA YAKE YI WA RUMAISA? SHIN KINA KUNYAR SHIGA CIKIN ?AN UWANKI MATA, SABODA RASHIN NONO, KO KUWA ?INKI NE BA YA ZANA A JIKINKI, SAI KIN HA?A DA CIKO? RAMA CE TAYI MIKI YAWA, KO KUWA YAYE YA SANYA NONONKI YA ZUBE KAMAR BANA MACE BA. TO ALBISHIRINKU! KUKANKU YA ?ARE, HAKA ZALIKA KAKARKU TA YANKE SA?A. MAMAN KHADIJAH TA SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYE, DA INGANTACCEN GARIN KUNUN SABAYARTA. BAYA CUTAR DA LAFIYA KO KA?AN, ZAI GYARA MUKU JIKI, YA CIKO DA NONO, INA WANDA SUKA YI YAYE, KO SUKE SHIRIN YI, KU JARRABA WANNAN GARIN KUNU, ZAKU BAYAR DA LABARI, MAMAN KHADIJAH NA NAN A GARIN ZARIYA, BAYAN FEDERAL PALLADAN, KO KU TUNTU?ETA KAI TSAYE TA LAMBAR WAYARTA 08033411249*

Iman kuwa a sitting room ta iske jabir, ya wani hakimce yana danna wayarsa, tun da ta shigo ya kafeta da ido, kamar yadda ya saba. Ta nemi wuri ta zauna, tayi masa sbiru.

"Wai dan Allah iman me na yi miki ne? Meyasa ki ka tsane ni haka?"

Cikin mamaki ta Waga kai tana kallonsa, ganin yadda yake neman ya raina mata wayo, ya fi kowa sanin abun da ya sanya, ba ta yin sa, amma yake ta wani basarwa.

"Ke shikenan abu ba ya wucewa a wurinki ne?. Son ki nake yi da gaske, aurenki zan yi, magana ta riga ta yi nisa, na samu amincewar ammi, takawa kuma kan ya dawo ma wata?ila an riga an yi".

"Amincewata da ta mahaifiyarka ba ta da muhimmanci kenan?".

Yayi murmushi ya ce "Amincewar hajiya wani abu ne daban, ke kuma a kowane lokaci idan mun yi aure komai zai wuce, dan Allah ki daina taurin kai, ke kanki kin san ba ki da wani rufin asiri, da ya wuce amincewa aurena, idan ba haka ba, duk wanda suka zo a baya sun tafi, sun kasa Waukar kasada. Ni a nawa ganin zaSe-zaSe ba naki bane ba iman, kamata yayi ki gode mini, da na ce ni na ji na gani"

"Ko ba ka yi Soye-Soye ba, na san ni ba kowa bace ba, abun da ka ke son gaya mini kenan, amma kasancewata ba kowa ba, ba shi yake nufin zuciyata ba ta da ?ancin ta so ko ta ?i wani abun ba, ina girmamaka a matsayin yayana, idan farincikin ammi in aureka shikenan, amma ni babu soyayya a raina".

Jabir ya ce "Haka ne, ammi ta yi iya ?o?arin ta a kanki, har keta billenta ta yi, ta nemi alfarmar Wan ta ya aureki, amma ya ?i hakan, dan yana ?yamarki, na cancanci ki gode mini ne iman, ba ki ?i ni ba a halin yanzu ba ki da zaSi, aure shi ne mafitarki, idan ba haka ba kuwa wannan kyawun barazana ne a gareki"

Sannu a hankali jabir yake gasa mata munanan maganganu, amma ta yi iya ?o?arin ta, ta din ga haWiyarsu, duk da yadda take ji, suna barazana ga zuciyarta.

Jin bugun zuciyarta ya fara ?aruwa, kuma numfashinta ya fara sama-sama, ya sanya ta tashi ta koma Wakinta.

Rumaisa na ta jin daWi, tare da fatan, Allah ya sa laila da gaske take, za ta sai mata abun nan, Iman ta shigo, sai dai ba sai an gaya mata ba, ta san iman Win a cikin damuwa take.

Rumaisa ta yi shiru ba ta ce mata komai ba, ita ma ba ta ce mata ba, ta je kawai ta kwanta a kan gadonta.

Mintuna talatin ammi ta shigo, tana faWin "Iman, ya ku ka yi da jabir ne, ba kya bani update?" Ta tarar da iman a kwance, kamar mai bacci.

Ammi ta ce "Iman ?an kwanankin nan baccin nan ya fara yawa, duk in da ki ka samu sai bacci? Rumaisa ko ta gaya miki wani abu ne?".

Ruma ta ce "A'a ba ta ce mini komai ba".

Ammi ta ce "To shikenan"

Da daddare rumaisa ta ce A Wakin iman za ta kwana, duk da ammi ta bata Waki, amma ta ce a wurin iman za ta kwana.

Cikin dare iman ta tashi ta yi salloli, sannan ta zauna ta Wauki wayarta tana dubawa, rumaisa na kallonta, a haka bacci ya kwasheta.

Da safe rumaisa na baccin safe, laila ta shigo da system a hannunta, ta tashi rumaisa.

Ruma ta buWe ido ta kalleta, "Kin manta hau zaki fara zuwa islamiyya ne? Tashi mijinki zai yi magana da ke"

Rumaisa ta kalleta ta ce "Da computer zan yi wayar?"

Laila ta dungurarwa da ruma computer a gabanta, tana kalla ta ga fuskar takawa.

Ta ce "Laaa video call a computer"

Yayi murmushi ya ce "Hi little mimi".

"Iyee daga zuwa turai har ka koma bature, irin...." Sai kuma ta kalli laila ta yi shiru.

Yayi murmushi ya ce "Ba ki tashi ba ne? Yau zaki fara zuwa islamiyya fa, ki tashi kiyi breakfast, ki shirya a kai ki"

Ruma ta yi mi?a ta ce "Shikenan weekends ma ba zan huta ba".

"Ki yi ha?uri, ina boy, bai tashi ba ko?"

"Eh, bacci yake shi da anty iman, kai har ka karya? Waye ya dafa muku abinci?"

"Har Waki aka kawo mana, na karya"

"To yaushe zaku fara taron?"

"Sai Allah ya kaimu anjima" ya Wan yi shiru sannan ya ce "Mimi meyasa ki ka bani abun da zai sakani kuka?"

Jiki a sanyaye ta ce "Ba dan kayi kuka na baka ba, ni ba dare ba rana, abun ci mini rai yake, amma ba na ce maka kar ka tambayeni komai a kai ba, sai anjima, bari na Wan ?ara rage bacci".

"Mimi tsaya ki ji".

"A'a gaskiya sai anjima" ta ture system Win ta kwanta.

Laila ta daki ?afar ruma ta ce "Ke wace irin mashirirciya ce ne?" Ruma ta yamutsa fuska ta kalli ruman.

"Ya tafi wata ?asar, kuna waya ki kashe? Babu wani abu mai jan hankali, ba rausaya murya ba karairaya, wai ce miki aka yi dan kika ?anwar maza, ki din ga abu kamar namiji, you are not romantic at all, mijinki matashi ne, kuma kema kin san yana da masu son sa, ko dai ki gyara ko ki ga abun da ba kya so. Ki tashi ki yi wanka ki zo ki karya"

Ta Wau system Win ta, ta bar Wakin, rumaisa ta zumSura baki sannan ta tashi.

Laila kuwa komawa tayi, tana jinjinawa takawa. "Takawa i salute your effort, Wannan matar taka, zan iya saka bulala in zaneta wataran, she's very stubborn, beside she's much more than how i expect, ba ta ji ga taurin kan tsiya".

Adam ya ce "Haba madam, duk ita kaWai, ki yi ta ha?uri kema, halinku ne ya zo Waya shiyasa ba kwa jituwa, da Waya daga cikin ku na da ha?uri, zaku zauna lafiya, idan ku ka saba shikenan".

"Anya zan iya jurewa? Ba ta ji fa"

"Tuba muke, ayi ha?uri dai".

Rumaisa ta shirya cikin dogon hijjabi, hatta jakar islamiyya da litattafai adam ya sai mata komai, sidi ya Wauke ta suka tafi makarantar.

Ya je ya gabatar da ita, mai makarantar ta ce ta san da zuwan rumaisa, aka kai ruma aji.

Mamki ne ya cika su kansu ?an ajin, ganinta sanye da hijjabi irin na islamiyyar, suna mamakin kar dai matar aure ce.

Mai makarantar ta gabatar da rumaisa a wurin malamar da take ajin, zungu-zungui ta wuce ta je ta zauna, tana jin haushin kallon da suke yi mata.

Ajin duk manyan mata ne, dan da yawa sun haifeta, wasu kuma sun yi ?anwa da ita sosai da sosai.

Aka yi lesson Win da za ayi a ka gama, har lokacin tashi ba ta kula kowa ba, sai da aka tashi suka din ga tambayarta ko matar aure ce ita, sai dai ta din ga bin su da ido, ta?i magana.

Sidi ya zo ya Wauketa, amma ta ce masa ita Worayi zai kai ta wurin mama, ya ce ai ammi ba ta sani ba, ruma ta ce ba ruwansa, idan ba zai kaita ba, ya ajiyeta ta je ta hau napep.

Haka ya juya kan motar suka tafi Worayi.

A ?ofar gidan yara suka tsatstsaya suna kallon uwar motar da aka kawota a ciki, har da ma?wabciyarsu shamsiyya a le?owa, tana Wagowa ruma hannu.

Ruma ta ce 'Lallai matar nan, saboda ta ganni a mota, har da Wago mini hannu, nan gaba a daidaita sahu zan din ga zuwa, in ga ko za samu masu kulani'.

Ta kalli sidi ta ce "Ba sai ka dawo Waukata ba, zamu yi waya da uncle Mahmud" ta shige cikin gida, bakinta Wauke da sallama.

Gidan shiru, sai Aliyu da yake girki a kitchen.

Ya amsa mata ya ce "Koma bamu san da zuwanki ba, daga tafiyar mijinki jiya, yau kin fara yawo".

Ta ce "Ai da yake ba wurinka na zo ba ehe" ta shiga Wakin mama, mai sunan baba yana kwance a kusa da mama, yana kallon tv.

Mama ta ce "Ke daga ina?".

"Makarantar matan aure wai ya saka aka kai ni, mai sunan baba ina kwana"

"Lafiya ?alau"

Ba ta tsammaci wata magana sama da haka ba daga gare shi ba dama, dan haka ta zauna ta ce "Mama jiya ya tafi fa".

"Haka Aliyu ya ce mini, ina mai gidan nawa, ina ?a ta iman, ki ka zo mini ke kaWai?"

Mai sunan baba Wan gyarawa yayi, yana jiran jin amsar da rumaisa zata bayar, a kan iman.

"Mama, ni in koma kenan?"

"Gaskiya dai, ba iman ba mai gidana, sai ke fitinanniya"

"Ai shikenan, gara na koma wurin ammi. Sabir yana nan ?alau, iman kuma gari ba daWi, tsoro nake ji kar ciwonta ma ya tashi"

A fuskar mai sunan baba ta ga razana, amma saboda azabar miskilanci yayi kamar bai san me suke faWa ba.

Mama ta ce "Subhanallah, me yayi zafi haka, yara ?anana da ku, har kusa abu ya dameku a rai".

"To ammi kin san familyn na su sai a hankali, sun takura mata da yawa, kin san ba ammi ce ta haifeta ba, sau kusan huWu ana yin?urin aurenta, wannan muguwar Mummyn tana hanawa, tana cewa mutane ba ta da uba, wai ammi ce garin tsince-tsincenta ta tsinto ta"

Cikin rashin fahimta mama ta ce "Ke kin sani a duhu, kina nufin ba ita ta haifi iman ba?"

"Hmm mama baki san bada?alar da ke cikin gidan nan ba" nan ruma ta warware mata komai, sannan ta ce "Yanzu kuma wannan jabir Win ya ce son ta yake zai aureta, ammi tana ta murna, tun da shi ya san halin da ake ciki, ita kuma iman ba ta son shi sam, akwai wani wanda take so daban, amma ba za ta iya gayawa ammi ba, saboda ammi ta amince jabir ya nemi auren ta, ba wanda ta gayawa sai ni abun tausayi, kuma tsoro take ji kar wanda take so Win, ya ji labarin ga a halin da take ciki ya ce baya son ta".

Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, lafiyayyiyar yarinya mai mutunci kamar wannan, babu wanda zai ce ba ita ta haifeta ba, ni cikin yaran nan, da da wanda yake da ?wari sosai, ai da an auro mini ita, to sai dai ba matar talaka ba ce, ni dai ina ?aunar yarinyar nan fisabilillahi".

Cikin son sai ta yi pressing Win mai sunan baba rumanta sake cewa "Bari kawai ammi, kuma fa baki ga uban samarinta da suke sonta a haka ba, masu kuWi ta ce ta daina soyayya, kawai ta zo ta fara son wani, amma ta?i gaya mini waye, ba ?aramin son sa take yi ba. Amma wannan jabir Win, ya biyo kai tsaye ta wurin ammi, kuma yana daf da zuwa wurin mai girma wambai, shi kuma wannan wamban ba Waga ?afa, dama yana ta yi wa ammi kashedi, ta aurar da ita ko ta mayar da ita in da ta Waukkota, cikin dare ina jin tana ta kuka".

Tsaki mai sunan baba ya yi ya tashi ya bar Wakin, rumaisa kuwa ta yi wani guntun murmushi, ta tura sa?on yadda yakamata.

Aliyu ya shigo da plate Win indomie, ya ce "Me aka yi masa na ga ya fita yana tsaki?"

Mama ta ce "Shi wannan sai an yi masa wani abu ma?".

Ruma ta ce "Za mu ci indomie"

"Ai ko mayya ce ke, sai dai ki ci kan ki"

Tashi ta yi ta koma kusa da Aliyu, ta ce "Dan Allah zan ci".

"Wai ke da mijinki yake ajiye miki komai, ki zo ki saka mini rani".

Ruma ta ce "Allah sarki mijina, ya tafi ya barni, papa saurayina"

Aliyu ya ce "Ke fa baki da kunya ko?"

Flashing aka yi wa Aliyu, ta le?a wayar ta ga an rubuta "Baby Hibba".

"Ohhh ni ?a su, yaya Aliyu soyayya?"

Ya harareta, ya kira wayar "Hello my haidar".

"KuWin wayar sun ?are ne ake mini flashing?"

"A'a ba su ?are ba, bana son ka Waga su ?are ne, kuma ka sake saka wasu, shiyasa na yi maka flashing"

Yayi murmushi ya ce "An taso daga tahfiz Win ne?".

"Eh, yanzu na shigo gida ma"

"To shikenan, in ajima zan zo in sake jin haddar. Bari yanzu abinci zan ci"

"To my haidar, ka gaida mama, ka ci ka ?oshi da yawa".

Rumaisa ta ce "A gaban maman ka ke waya da ?an mata?"

Da?uwa ya yi wa rumaisa, ta hau tafa hannaye.

"Yaya Aliyu, habiba ce ta koma sweet hibba?".

"Uban wa ye ya ce miki ita ce"

Rumaisa ta ce "Na rantse da Allah muryar habiba ce, munafuka, habiba take soyayya da yayana, ba tare da tana biyan subcidy ba, dole na je gidansu habiba, mama a gabanki ake soyayya?".

Mama ta ce "Ya ce zuwa za ayi ma ayi masa tambaya, nan da shekara biyu"

Ruma ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Su mai sunan baba ba su yi aure ba sai kai"

"Uban wa ye zai bari kansa ya kulle kamar su? Yaya Abubakar ma kuWin aure za a kai masa, yana gama service. "

"Innalillahi, yaya Aliyu habiban da ka ke zanewa saboda ni"

Aliyu ya doke mata ?eya ya ce "?ar rainin hankali ba, duk ke ki ka ja, na daki mata ta".

Mama ta ce "Too har an yi auren kenan" da sauri Aliyu ya Wau plate ya fice daga Wakin yana dariya.

Wani irin zullumi mai sunan baba ya shiga, ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya kasa gane tausayin iman yake ji, ko tashin hankali ya shiga jin wani na neman aurenta, wani irin kishi ne ya taso masa, tabbas ya fi jabir komai, sai dai jabir ya fishi kuWi, sannan kuma wa iman take so

Yaya usy ne yayi sallama, rumaisa ta tashi da gudu ta tare shi, ta ce "Mussaman saboda kai na zo gidan nan yaya usy".

Ya ce "?arya ki ke yi".

"Wallahi da gaske, zo mu zauna daga nan"

Ba tara da ta bari ya shiga ko wurin mama ba, ta ja shi kitchen ta rufe ?ofa, sannan ta ce "Yaya usy wani abu ne yake damuna, na ga kaine abokin shawarata, na ce bari na gaya maka".

Ya ce "To ina jin ki"

"Yaya usy, dama...dam..mm"

"Wai meye haka ne?"

"Kunya nake ji ne, amma shawara nake nema. Ka ga dama takawa ne kan ya tafi, yake yi mini abun da bai dace ba, kuma"

"Kuma me? Wane irin abu ne da bai dace ba".

"Yaya usy kiss yayi mini kuma, ba zan iya faWar sauran ba dai, kuma kaga bai dace ba, bana son mama ta gane, ya ce mini wai ai ba komai, in tambaya in ji, wai tun da ihu nake idan ya taSa ni, zai ?ara aure, kuma ni bana son ya yi mini kishiya. Dan Allah yaya usy ya zan yi, bana son Sata tarbiyya ta, idan mama ta sani za ta yi fushi da ni, kuma bana son yayi mini kishiya"

Ayshercool.
08081012143

Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels


Usman ya yi ?uri da ido yana kallonta.

"Yaya usy ba ka ce komai ba?"

"Ji nake kamar in kama ki in ma?ure mini wuya ne".

Cikin damuwa ta ce "Dan Allah ka yi ha?uri, ka rufa mini asiri"

"Ke dalla ware malama, ke yanzu duk zaman da ki ke yi, yake baki ci da sha, ya Wauki nauyin karatunki, shirme kawai ki ke tafaka masa, zuwa ki ke kiyi masa ?iri-?iri da ido, kamar gardi a cikin gida, ke kanki ba zaki taSa waye ba, abun da aka koya miki baki san idan kin yi aure ki waye ba, sai kayan hauka da rashin hankali"

"Ni fa yaya usy ban gane me ka ke nufi ba"

Usman ya ce "Idan bai yi miki kiss ba, wata zai je ya yi wa a waje?"

"Yaya usy, ku fa ku ka ce mini haramun ne, Allah zai ?ona ni idan na yi"

"Kuma sai aka ce miki har da mijinki? Ai gara ya ?ara auren, kuma ba abun da zai hanamu ra?ashewa da bikin, ki je ki yi ta shirmenki" Usman ya tashi ya bar kitchen Win.

Ta yi shiru tana tunani, ta yaya haka zai yiwu? Sun ce mata abu babu kyau, yanzu kuma an dawo an ce mata ya halatta ba tare da wani cikakken bayani ba. Ta basar da zancen ta cigaba da harkokinta.

Mai sunan baba kuwa rumaisa ta ha??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Wa shi da assignment mai wahalar gaske, domin kuwa kasa sukuni yayi, maganar ta din ga damun zuciyar sa, ya din ga jin tamkar yayi tsuntuswa ya je ya ga Iman.

Da wayar mama, rumaisa ta kira Mahmud a waya, ta ce ya zo ya Wauke ta, ta bashi adress Win gidan.

Yayyen ruma sun sha mamakin ganin Mahmud, basu san shi, ba sai dai wasu lokutan ta kan yi maganar sa.

Ya fi takawa sakewa da mutane wasu lokutan, dan haka nan da nan ya shiga cikin su Aliyu kamar sun saba.

Rumaisa ta ce "Daddy, ga Yasir, shi ne hacker shi ne ku ka yi waya da shi"

"Ki ka kuma ce mini hacker, ba zan sake yi miki wani abu ba"

Mahmud ya ce 'Rabu da ita, ai ni da kai muke aikinmu" ta nuna masa Abdallah ta ce "Ga masterna a wurin zane-zane, da shi nake koyi, duk da idan na taSa masa kayan zane, wataran ran?washina yake, amma a hakan Alhamdilillah na koya, dan haka shi zai yi mana zane, sonake kan papa ya dawo, mun gama komai"

Ya ce "Lallai team Win nan an haWa manyan ?wari a cikin sa, Allah ya dafa mana". Mama sam ba ta san a kan me suke magana ba, bayan la'asar sosai, sannan ya Wau ruma suka tafi gida.

Aikuwa ta sha faWa a wurin laila, wai ta tafi gida, ba a kira takawa an tambayi izninsa ba, ruma tayi mata banza, irin kan ki ake ji Win nan.

Kusan sati guda, laila ta saka ruma a gaba, ta hanata sukuni, gashi ta yi ta mata magana da turanci, komai ruma ta yi sai ta ci gyaranta.
Ta hanata kwana tare da iman, tare suke kwana a Waki tare da ita, gashi ta kasa ta tsare ta hanata video call da takawa.
Abu Waya ne yake yi mata daWi, kunun maman Khadija na sabaya da take sha safe da yamma, wannan kam tun da batu ake na ci, ruma tana jin daWin haka.
Ban da wannan, duk wani wanke-wanke da gyaran fata rumaisa ba so take yi ba.

Rumaisa na zaune tana shan kununta, ita da sabir, dan idan suna sha, kamar ya shiga cikin kofin, ko zama ba ya yi, yana tsaye ayi ta bashi yana lashe baki.

Laila sai video call take da mijinta, ga mijin ya fara manyanta, amma ta shagwaggwaSe, sai taSara take, tana ce masa baby, suna wani abu mai kama da iskanci a wurin rumaisa.

Rumaisa har le?awa take, ta sake kallon fuskar mijin, wai wannan gundumemen mutumin ne baby, 'TaS sukumbiya, wai baby taS' laila tana jin ta, ta?i kulata, su suke wayar amma ita take jin kunya.

Babu babban abun da yake bata mamaki, kullum da daddare sai sun yi video call, laila ta Wau kwalliya kamar zata biki, ta sha ?anan kaya, ta zauna a gaban waya ko system.

Yau kam da abun ya ishi kunnuwan rumaisa, ta saka hannu ta toshe kunnenta. Sai da laila ta gama wayar, sannan ta dubi rumaisa ta ce "Ba zaki iya ba ko, ni ?ar iska ce ni da mijina, shi ne ki ka toshe kunne?"

Ruma ta yi shiru. "Ban ce dole sai kin yi irin nawa ba, ni na yi shekaru a gidan aure, na saba da mijina sosai da sosai, ke nake fatan ki daina wannan shirmen, ki san me ki ke yi" ruma ba ta ji za ta iya abun da laila ke yi ba, a ganinta fitsara ce muraran, ga takura mata da take yi.

Da safe kan ta tafi makaranta, ta karSi wayar iman, ta kira Adam voice call.

"Budurwata"

"Papa" ta kira sunansa a shagwaSe.

"Ya aka yi?"

"Ni gaskiya wannan anty lailan ta takura mini, ta yi ta mini masifa, da na motsa ta yi mini faWa, duk ta bi ta saka mini ido".

Adam ya ce "Haba mimi, baki kira ni kin ji lafiayata ba, sai kawo mini ?ara, ke ma ta ce mini ba kya ji, taurin kai ki ke yi mata".

"Yi ha?uri ya kake?".

"Ban sani ba, tun da baki damu da ni ba"

"In ji wa? To yau saura kwana Wari da saba'in da biyu ka dawo, calendar ce da ni, kullim sai na yi marking kwanakin da suka rage ka dawo"

Adam ya ce "Wow, lallai kin damu da ni sosai, take care, kar ki makara"

"Ni kar ka kashe"

"So ki ke ki makara a school ko?"

"Hmm ka san me?" "A'a sai kin faWa"

Ji tayi kamar ta gaya masa zancen kunun da take sha sai kuma ta fasa.

Jin tayi shiru ya sanya ya ce "Akwai matsala ne?".

"A'a"

"To ki shirya a kai ki school kin ji budurwata, sai mu yi waya anjima"

Ruma ta ce "Video call nake so mu yi in ganka, amma wannan anty lailan ta hana, duk abun da zai sani farinciki ba ta so".

Ya ce "nima dokar nan ta isheni gaskiya, mutum da budurwasa a hanasu sakewa"

Ruma ta yi dariya ta ce "To saurayina, sai na dawo, kun gama taron yaushe zaka wuce karatun"

Ya bata amsa da "sai Allah ya kaimu jibi".

Da ?yar suka yi sallama, ta ajiye wayar ta tashi.

Wata irin kewar adam ce ke sake bijirowa rumaisa, ji take kamar sun shekara ba sa tare, tayi shiru tana tuna abubuwan da suka faru a tsakanin su, daga aurensu zuwa yanzu, a hankali ta yi ajiyar zuciya, ta tashi tana shirin makaranta.

Mai sunan baba kuwa tsayin lokacin nan, kullum sai ya Wau wayarsa ya ji kamar ya turawa iman message, amma sai ya kasa, ya duba chats Win su, ko zai ganta online, amma ya ga sam ba ta fiye hawa online Win ba ma, gashi sai yana tsaka da jimami, da tunanin ya zai yi, Aliyu ya zo yana kashe murya yana waya da habiba, wanda ba ?aramin ?ular da shi yake yi ba.

Mummy ba ta sake nunawa Mahmud fushi ko damuwa a kan abun da yayi ba, hasali ma ta?i yarda su sake Waukko zacen, kamar babu abun da ya faru, ta ?ar?ashin ?asa kuwa, tana cigaba da shirin, sake

Please Login or Register in order to submit comment