You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muguwa kamar Mummy, saboda waWan nan dalilan Adam yake jin ba zai iya auren mace sama da Waya ba, idan uwar Wa ta mutu kuwa, ya ce majaifiyarsa zai bawa ri?on Wan sa, babu wanda zai bawa ri?on Wan sa.

Tun Samha tana Soye son da take yi wa Adam, har ta fito muraran, shi kuma sam ba ta ita yake yi ba.

Maman Samha ta shiga ta fita, ta na son a aurawa wani ?aninta Aisha, Turaki ya ce ba zai bayar ba. Abun ya ?ular da ita sosai da sosai.

Babu tsammani, Ammi ta je ta samu wambai, yayan Sharif ta ro?e shi ya nemawa Adam auren Aisha.

Aka yi ta surutu, wai za ta aura wa mahaukacin Wan ta marainiya, dan zalinci, Aisha ta ce ta ji ta gani.

Ammi ta yi haka ne, dan Aisha ta samu sassauci, saboda azabtarwa da ake yi mata, kuma turaki ya ?i ya mata ita gaba Waya.

Samha tamkar za ta yi hauka, ta tsinewa Ammi da Aisha ba ta san iyaka ba, ta kuma lashi takobin ganin bayan Aisha, ta ?uduri aniyar ko da bala'i sai ta auri Adam.

Mummy ta ja ta a jiki, ta din ga rarrashin ta, tare da zigata da bata goyon baya Wari bisa Wari.



Ayshercool.
08081012143


What's app only please =?O?

Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu bu?atar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book Win. Kar ku manta da subscribing YouTube channel Winmu na Cool hausa novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ?anwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel Win*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please =?O?


Da fari saboda dagewa da neman magani, Adam ya Wan samu sau?i, dan ya kammala karatu ma, ya samu aiki a hukumar DSS, kuma ya shiga aiki da ?afar dama.

Yanayin larurar Adam, da abubuwan da suka faffaru da shi, ya sanya mai martaba yake matu?ar jan sa a jiki, da kwantar masa da hankali, haka zalika turaki da galadima, iyayen nan maza duk suna ?aunarsa, kusan halinsa Waya da mahaifinsa, amma har ya fi babansa taurin kai wasu lokutan, amma akwai Wa'a da ladabi.

Hakan bai ishi Mummy ba, ta din ga bi? wurin matayensu, tana Sata Ammi da ?a?anta, da har sai da wasu suka fara jin haushin Adam a cikinsu.

Bayan auren sa da Aisha, ciwo ya cigaba da tashi lokaci zuwa lokaci, sannan kamar yadda ammi ta din ga yi, haka Aisha ta din ga Sari, ciki ba ya zama a jikinta, ga ?annensa suka sakata a gaba, su je har gida su yi mata rashin hankali, su ci zarafinta ga Samha ma a gefe ta sakata a gaba, da makirci da sharri kala. Sannan still daga can gida mahaifiyar su samha ma, ba ta ?yaleta ba da sharri, da haWata da Turaki, wai ba ta Wauke ta uwa ba, komai sai dai ta yi ita da giwar galadima.

Idan Aisha ta samu ciki, da zarar zai zube, sai ta yi magafrki da adam, yazo mata da dogayen ha?ora, da kuma farata ya kafa kai a mararta, sai dai da safe ya tashi da zubar da jini.

Adam bayan shigarsa Dss akwai cakwakiya daban-daban, sai dai ya tsaya kai da fata a kan gaskiya, ba ruwansa da cin hanci, da shi da Jamil suka shiga aikin, amma ya fi Jamil karatu, dan haka rank Win sa ya fi na Jamil.

Akwai aiki da ?o?ari, hakan ya sanya shi zama sannane, mussaman da yake kama da mahaifinsa sosai.

Bashi da aiki bankaWa, da tonawa mugwayen ?asa asiri. A tone-tonensa, ya tono Usman wakili, da irin yadda yake yi wa ?asa Sarna, ya sako shi a gaba, a hukumar wasu suka goya masa baya wasu kuma suka ?i.

Ba ?aramin ragewa wakili mutuncin yayi a idon mutane ba, ya cigaba da fafatawa, amma aka ?i bashi goyon baya, a hukunta wakili. Shi kuma ya?i sakin aikin, ya cigaba da bin diddigin sa, babu irin jan kunnen da ba a yi wa Adam ya ?i ji.
Ya koma ya bankaWo wata tawaga, da suke yi wa kansu la?abi da SMOKE, sai dai an kasa gano suwaye a ?ungiyar smoke, sai dai ana ganin miyagun ayyukansu, duk wani shige da fice na miyagun kwayoyi, da makamai ta hanyar da ba ta dace ba, suna da hannu a ciki, za kuma kaga tambarinsu na haya?i, an rubuta THE SMOKE.

Bincike a kan Smoke, ya sanya ya sararawa wakili, bai kuma waiwayar wakili ba, sai da ya ji ?ishin walili zai tsayar da Wan sa takarar senator, shi kuma za a Wauke shi vice president, su yi takara, da Wan takarar da zai tsaya shugabanci ?asa.
Wannan dalilin ya sanya, Adam sake saka wakili a gaba a karo na biyu.

Nan da nan sunan Adam ya shahara, shi ma ya haWa tasa tawagar, da lauyoyi, da ma'aikatan Efcc, da ?an jarida da suke da burin yi wa ?asa aiki saboda Allah.

Iman kuwa tun kan ta kai shekaru goma, take samun masu cewa suna ri?o.

Iman tana girma samari kamar me, nan ma Mummy ta ?wafe a ranta, ya sake mayar da jita-jita a kan Iman sabuwa dal. Na cewa shegiya ce ba wanda ya san iyayenta.

Saurayin babbar ?ar Mummy, Surayya, Wambai ya haWata da wani babban mutum, amma yana ganin Iman ya ce shi nan duniya wannan jar yarinya yake so.

?arshe dai aka yi biyu babu, Surayyan ta yi aure, amma Mummy ta kai sunan Iman wurin bokansu.

Manyan mutane duk wanda ya ce ya na so, sai ace masa shegiya ce, sai zance ya lalace, a ?a?an mai martaba, Waya shi ma ya li?e Iman yake so, Mummy sai da ta yi dalilin da ya sanya, babar yaron ta hana zuwa da iman gidan. Yawan gorin da ake yi mata, ta daina shiga cikin mutane.

Ammi tana tausayin Iman, ga larura ga tsangwama.

Iman ba ta da wata ?awa, kullum tana manne da Ammi, ko Nusaiba, sai kuma uwar Wakinta Aisha matar takawa.

Duk wannan abubuwan, Ammi ba ta taSa nunawa Mummy wani abu ba, kuma ba ta saka wa zuciyarta wai wani ne yake yi mata wani abu, kawai ta saka wa ranta jarabta ce daga Allah.

Sai dai har a lokacin Ammi ba ta daina son Wan ta ya dawo gareta ba, ta kasa jurewa ta je ta sanar da wambai, dan Allah ya shiga lamarin gidansu, ya sasanta mata yaranta, ko Mahmud ba zai dawo hannunta ba, ya din ga zuwa in da take.

Wambai ya yi ta faWa ya ce laifin Mummy ne, da ta raine shi a haka, amma ta nuna ita ba laifinta bane, yayi musu sulhu, amma suna zuwa gida, ta sake hure masa kunne.

Cikin ikon Allah, Iman kan ta yi candy, wani ?anin abokin Adam ya fito zai auri iman, Wan babban gida ne sosai da sosai, aka saka rana tana kammala sakandare ayi biki, ta cigaba da karatu a gidansa, dan Ammi ta fara tsorata da mazan da suke bin Iman.

Adam kuma shekara huWu da aure, ciki ya gagara zama a jikin Aisha, ciki na ?arshe da ta samu, Ammi suka yi shawara a kan Aisha ya je ta yi rainon cikin a saudiyya, wurin wani wan Ammi da yaki zaune a can shi da matarsa.

Ya ce karatu za ta tafi ?arowa ?asar waje, aka din ga surutu a kai, ya ce babu mai tsara masa rayuwarsa, tun da matarsa ce.

Iman kuma watan da za a yi biki, wanda zai aureta ya aiko a karSar masa kayan aurensa wai ya fasa.
Hankalin ammi ya tashi, ta aika a tambaye shi dalili, iyayensa suka ce su manyan mutane ne a ?asa, ba za su karSi sirika da ba ta da asali ba.

Ammi ta sha kuka, laila da ba ta ?asar ma, abun ya ba?anta mata rai, ta cewa Ammi visa za ta yi wa Iman, a tura mata ita can, Ammi ta ce ba mai rabata da ?ar ta sai mutuwa ko aure.

Ammi ta yi shawara da baba uwani, a kan ta bata shawara ko ta ro?i Mahmoud ya auri Iman, dan ta lura wannan mugun tabon da Mummy ya yi mata, ba zai bari ta auru ba, baba Uwani ta ce ai ita babarsa ce, dan haka bakomai.

Daga nan ta kwashe ta je ta gaya wa Mummy.

Ammi ta keta billenta, ta je ta samu Mummy, ta ce mata dan Allah ta na son yin magana da Mahmoud, ta ce mata za ta turo shi.

Sai dai kan ya je, Mummy ta zauna ta kitsa masa, tare da sauya masa tunani.

Ammi ba zata iya tuna rabonsa da sashinta ba.

Ta ro?e shi Allah ma'aiki, ya auri Iman, ko ita kaWai ce alfarmar da zai iya yi mata a rayuwa a matsayin ta na mahaifiyarsa.

A take ya ?e?ashe ?asa, ya cewa Ammi shi ma ba zai auri ?ar da ba ta da asali ba. Ba?in cikin abun da Mahmud ya yi mata, ya sanya ta kamu da hawan jini, saboda ta yi kuka ba kaWan ba, ta shiga damuwa.

A lokacin Adam ya je umara, ya ga Aisha, cikinta ya girma sosai, ana ta addu'ar Allah ya sa ta haife shi lafiya, bayan ya dawo ya samu labarin, abun da ya faru tsakanin Mahmud da Ammi, ya din ga yi wa ammi mitar meyasa za ta ro?i Mahmoud ya auri Iman, ita kuma gani take ba ta da wata mafita sai wannan.

Ammi sai da suka kwanta da Iman a asibiti, dan ta so Al'amin saurayin da ya fasa aurenta, haka zalika ta so ta samu Mahmoud, duk da yana cikin waWanda take bala'in jin tsoro, saboda dukan da yake yi mata da hantara idan sun haWu.

Kuma zance ya fita a dangi, Giwa ta na neman kai da shegiyar ?ar ta, ta?i auruwa, kuma ta karya billenta ta nemi alfarmar Wan ta, ya?i yi mata.

A zahiri za ka ga ammi kullum cikin fara'a take, amma ?asan zuciyarta, tana cikin damuwa da tashin hankali a kan iyalanta.

***
Gaba Waya jikin rumaisa ya yi sanyi, ta rungume Iman da take ta sharSar hawaye, ta rungumeta ita ma ta fara kukan, ta kasa rarrashinta.

Sai da suka yi mai isarsu, danna rumaisa ta din ga share mata hawaye ta ce "Ki yi ha?uri Anty iman, tun da dai ammi ta san iyayenki, meyasa za ki damu dan an ce miki baki da iyaye? Ki fuskanci rayuwarki kawai, kuma in Allah ya yarda zaki auri miji na gari, wanda zai kula da ke, ki daina kuka"

Ta yi maganar tana sharewa iman hawaye, Nusaiba ta yi sallama a Wakin, suka amsa, ta Wan yi turus tana kallonsu, yanayinsu ya nuna mata akwai wani abu, amma ta share, ta ?arasa ta Wau Sabir da ya yi barci, ta fice daga Wakin".

Jabir kuwa rai a Sace ya koma Wakin Ammi, ya dubi ammi ya ce "Ammi, dan Allah idan ban takura miki ba, ina son mu yi magana ne".

Ammi ta ce "To" ta tashi ta bar Wakin, Adam ya bi su da kallo.

Falonta suka koma, Ammi ta ce "Ya aka yi ne?"

Ya Wan sunkuyar da kansa ?asa, sannan ya numfasa ya ce "Ammi wani abu ne ma daWe ina son in gaya miki, amma na kasa ban sani ba ko zaki bani dama".

"To ni Win ba?uwar ka ce? FaWi ina jin ka".

"Dama..dama game da Iman ne Ammi, dan Allah idan babu wani a ?asa yanzu, ni a bani mana, ina son ta".

Ammi ta ce "To fa! Babbar magana, ya aka yi ba ka gaya mini tun da wuri ba?".

"Ina jin nauyi ne Ammi".

"To meye na jin nauyin ban da abunka, ka san yanayin da take ciki, ta daina saurarar kowa ta daina bawa kowa dama tunda abubuwan nan suka faru, amma na yi mamakin da baka taSa faWa ba".

"Ammi Iman ai ?anwata ce, na daWe ina Soyewa ne, yanzu kuma na ga yakamata na faWa, wata?ila dama rabona ce".

"Haka ne, amma ka san dai case Win da yake kanta, kuma babu lallai hajiyarka ta yarda, na san ba za ta amince ba".

Jabir ya ce "Ammi zan shawo kan ta, in dai kin amince shikenan, idan har ba a cikinmu ba, haka zamu zauna mu cigaba da zuba ido, kowa ya zo ya fasa, Saboda wani dalili mara tushe, ina ga ni Win na fi dacewa, na san abun da yake faruwa da ita".

Ammi ta ce "Na yi farin ciki sosai Jabir, Allah ya tabattar mana da alkhairi, ai kai Wana ne, na gode da ?o?arin share mini hawaye ni da marainiyar Allah, Allah ya biya ka".

"Amin Ammi, na gode sosai, ina ga zan yi wa mai girma wambai Magana, a nema mini aurenta, zan yi ?o?ari ya shawo kan Hajiy??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ata ma".

"To, Allah ya ji she mu alkhairi, ya sanya albarka na gode sosai" Ammi ta ji tamkar ya yaye mata kaso mafi rinjaye na damuwarta.

Da ta koma wurin takawa, ya kalleta ya ce "Ya dai na ga kina fara'a?"

"Ina ruwanka?"

Yayi murmushi ya ce "Tuba nake".

Ta zauna ta ce "Kai ban gaya maka ba"

Ya tattara mata hankalinsa.

"Laila za ta shigo cikin sati Mai zuwa"

Ya waro ido ya ce "Yanzu muka gama magana a waya, amma ba ta gaya mini ba".

"Oho muku dai".

"To ta koma ba ma so, ba ta zo lokacin rasuwar aisha ba, ba ta zo ta ga Wan ta ba, na yi aure ba ta zo ba sai yanzu?"

Ammi ta ce "Ai ka san yanayin aikinta a can, amma ta ce za ta daWe sosai idan ta zo, yaran ne za su koma da wuri, tare da babansu idan ya zo, shi sai next month in Allah ya kaimu zai zo".

"To Allah ya kawota lafiya, gashi ni zan yi tafiya. yauwwa Ammi, mai girma turaki ya kirani, ya ce mini mai martaba ya tura mu wakilcin taro, kuma da na dawo zan je course Win nan ta watanni shida, kin ga ba zan wani daWe tare da ita ba".

"To sai ta zo Win dai tukuna".

"Ammi, ina Jamil ne? Ban ?ara ganinsa ba fa, tun da ya tafi Waukko Rumaisa".

Ammi ta ce "Ni ma dai na yi mamaki, ka san da ta zo ta ce wai ?in hawa motar ta yi, saboda ta san yana jin haushinta, ina ga saSani suka samu, ya ji haushi, mukullin motar ma, Sidi ya bawa ya kawo".

Yayi ajiyar zuciya ya ce "To ai ba da ni suka yi ba, ni kaina ba na son surutun nan na ta, ita ba ta iya kara ba ko kaWan".

"Ai ?uruciyar kenan, sai dai ayi ta sakata a hanya, ni maganar da ta faWa ne a kan Jamila, nake jin tsoron kar ta koma kunnenta, bana son tashin hankali da masifarta, in da na gode wa Allah ma, ba a gaban wani ta faWa ba"

Takawa ya ce "Ina tsoron wannan bakin na ta a cikin masarautar nan, sai dai Allah ya shirya".

Can Waki kuwa, suka gama koke-koken su, ita da Iman, kamar wata babba haka ta yi ta rarrashin iman.

Can Iman ta ce "Anty rumaisa ba zaki kira mai sunan baba ki yi masa godiya da ya ya je gida ba?".

Ta yamutsa fuska ta ce "Godiyar me kuma?"

"Dubiya da ya zo mana".

"Ba ki san halin gayen nan ba, ba lallai ya gode, kina ganin yarfani ya yi dan na ce zan raka shi, wai na je na kula da mijina, yanzun ma zai iya yarfa ni".

Iman ta ce "Ba haka bane, yakamata ki yi masa godiya, idan yana gida ma sai ki gaisa da su mama, ko yana zama yayi dare a waje?".

Rumaisa ta kalleta ta ce "To mai sunan baba da mace ne, da an shigesu, ba shi da wasu abokai fa, daga makaranta sai kasuwa, sai gida, su wani ball su wani abubuwan abokai, ko yawo duk ba ya yi, da dai yaya usy ne ko gadanga na mama yaya Aliyu, mama da kanta take fita yawon nemansu wataran"

Iman ta yi murmushi ta ce "Kowa da halinsa kenan, ga wayar ki kira shi"

"Sai dai ke kira shi"

"In kira shi in ce masa me, na gaya miki ya ce na daina kiransa".

Rumaisa ta ce "Gaskiya idan na kira shi, ya yi mini wula?anci sai na rama a kan ki".

Iman ta bata wayar ta ce "na yarda".

Sai da wayar ta kusa katsewa sannan ya Waga, alhalin wayar na hannunsa, yana kallonta, ya din ga fatan Allah ya sa muryar iman zai ji, ba ruma ce ta kira ta dame shi ba.

"Hello mai sunan baba"

Sak yayi da ba Muryar iman ya ji ba.

"Ya aka yi?"

"Amm dama, kiranka na yi na ji ya ka je gida, na gode sosai"

"Yayi" ya faWa a ta?aice yana ?o?arin kashe wayar.

Ruma ta ce "Dama Iman ce ta ce, na kira ka na tambayi ya ka je gida?"

Da sauri Iman ta ce "Kai Anty rumaisa" ta yi maganar tana karSe wayar ta kashe.

"To me na yi kuma?".

Cikin shagwaSa iman ta ce "Meyasa zaki gaya masa haka, kar ya zaci wani abun fa".

"Wani abu kamar me?"

Iman ta ce "Bakomai" ta tashi tsaye ta ce "Ki kwana a kan gadon, ni sai na kwana a kan katifa a ?asa".

Rumaisa ta kwanta ta ce "Ai ba kara zan yi miki in ce a'a zan kwana a ?asa ba" Iman ta yi dariya, ba ta sake cewa komai ba, ta yi shirin baccinta ta kwanta.

Har kusan ?arfe biyun dare, rumaisa idonta biyu, rabon da ta ci karo da abun da zai hanata bacci, tun farkon shigarta hannun kidnappers, daga baya kuwa baccinta take yi, sai lokacin da ta kuSuta da Sabir.

A hankali ta tashi zaune, ta na jin kanta duk ya yi mata nauyi, tausayin wa ma yakamata ta ji ne?.

Ta kalli in da iman take barci, ta girgiza kai 'Allah sarki Iman, a yadda ki ka bani labari ke yanzu gaba Waya ba ki da uwa ba ki da uba, sun rasu ba zaki taSa ganinsu ba har abada, ba a san in da za a ga dangin su ba, ba ki da wa ba kuma ki da ?ani ga larura. Ashe ni kukan daWi nake, na ban san babana sai a hoto, wannan ke ce marainiya.
Allah sarki ammi, ashe da gaske mama take da take cewa aure Wan ha?uri ne, ni na zata kawai abinci ake ci ayi bacci, amma a ?wace mini Wa a bawa kishiyata, wallahi sai dai ayi masifar da za ayi kowa ya huta.
Ga Wan ta ba shi da lafiya, Wayan kuma an raba shi da ita, kamar yadda dai mama take sonmu a ?wace mata Waya daga cikinmu, ko kuma kamar ni a ?wace Sabir ya auri ?anwar anty aisha ya bata. Kam bala'i wallahi da sai dai kowa ya rasa'.

Ta dafe kanta, abubuwan ba da ita suka faru ba, amma ta ji sun dameta, ammi tana da kirki fiye da tunani, amma meyasa aka tsaneta?.

Ta tashi ta sauka daga kan gadon, ta zauna a ?asa ta yi shiru, abun duniya duk ya dameta, ?arshe a nan ?asa ta yi bacci.

Mai sunan ba tun da ruma ta ce masa Iman ce ta ce, a kira shi, yake jin wani irin nishaWi a ?asan zuciyarsa, dan ?o?ari yake ya hana hakan tasiri a zuciyarsa, dan ya?i yadda ya sallama cewar ya faWa soyayya, haryanzu tantama yake yi.

Da asuba bayan sun yi sallar asuba, rumaisa ta je ta gaida ammi, ta tarar da ammi na salla, ga sabir ya farka, yana kuka. Ta hau kan gadon, ta Wauke shi, ta bashi ruwa ta kwantar da shi ta hau yi masa wasa, daga haka kuma suka yi bacci gaba Waya.

Wajen ?arfe bakwa, ammi ta tashi rumaisa, ta ce ta je ta yi wanka, ta shirya ta je ta duba takawa da ya kwana a Wakinsa, ta zo a kaita makaranta.
Gaba daya ba ta sanya ran zuwa makaranta ba, a zaton ta tun da bashi da lafiya, ba bu zuwa makaranta.

Ta je ta yi wanka, ta karya, sannan ta tafi Wakin nasa.

Ciwon kwana Waya, amma idanunsa sun yi zuru-zuru.

Ta ?arasa kujerar da yake zaune, sanye da ashe Win jallabiya ta ce "Sannu ka warke?".

Ya kalleta ya ce "Ina kwana?" Gatse yayi mata, amma cikin ko in kula ta ce "Lafiya ?alau, ya jiki?"

Jawota ya yi ya zaunar da ita, ya tsura mata ido sannan ya ce "Baki san gatse ba ko? Ban isa ki gaisheni ba?"

Ta ce "Auu, wai dan ban gaishe ka ba, na Wauka kawai gaisheni ka yi, to ina kwana?"

Yayi shiru bai amsa ba yana bin ta da kallo.

"Ai ka ga matsalar, mutum ya gaisheka, ka ?i amsawa wai sai an yi maka irin taka". Bai ce mata komai ba ya cigaba da kallonta.

"Barka da wannan lokaci ranka ya daWe, na sameka lafiya?" Ta yi maganar tana risunar da kai, kamar yadda ake yi masa.

"Ki tashi ki je, sidi zai kai ki makaranta".

Ta tashi ta amsa masa da to, tayi waje.

Sai dai a harabar gidan, ta haWu da Mahmud, yana shirin fita.

Gaisawa suka yi, ya ce "Ya mai jiki?".

"Ai ba zan amsa ba, sai ka je ka duba shi"

"Anya zuwa dubiyar nan kuwa? Taho mu je in kai ki makarantar, ya sunan makaranta"..

Sunan kawai ta gaya masa ya gane, ta buWe motar ta shige.

Sidi ya taho da sauri, ya ce "Ranka ya daWe, jiranta nake giwa ta ce zan kaita makaranta ne".

Mahmud ya ce "Mayar musu da mukullin, zamu tafi tare" ya ja motar suka tafi.

Suna tafe a hanya, tana zuba masa shirme, yana biye mata.

Can ta ce "Kai ina son mama a rayuwata daddy, a duniya bayan Allah da Manzonsa, ba abun da nake so kamarta, dama ban san babana ba, amma mama dai kam, Allah ya tsundumata a aljanna. Allah ya bani abun da zan shagwaSa ta, in ta sai mata abubuwa".

Ya ce "Amin, sai ki yi ta mata biyayya da addu'a".

"Ai ina yi mata, har da ammi ma dukkansu yi musu nake yi, mutane su yi ta hantarata wai ba na ji, har da yayanka ma hantarata yake yi wataran amma dai ya na da kirki wasu lokutan, idan na yi masa laifi sai ya yi mini banza. Ammi ka ga da mama da Ammi, da yayyena, da Anty Aisha da Sabir, da mai girma turaki, da gwaggo, da iya, da malam habibu na islamiyyarmu, da barde Wan bindigar da yake bani abinci, da Bashir abokin takawa da ya tsinceni, da Iman kai duk wanda suke yi mini mutunci a rayuwa, kullum sai na yi musu addu'a da fatan alkhairi"

Ya ce "wonderful, gaskiya nima a taimaka a sakani a ciki".

"Eh zan saka ka, amma kai wa ka ke yi wa addu'a, tsakanin Ammi da wannan matar?" Shiru ya yi jikinsa ya yi sanyi ya kalli rumaisa.

"Daddy, duk yadda nake son Sabir, da anty aisha na raye, duk wahalar nan da na sha, ba shi da kamarta, kuma dole ne ya bita, to kamar haka ne fa, kai da wannan matar, duk rashin ji na, Mama sai dai ta yi ta cewa Allah ya shiryeni, amma kai har ka saka Ammi ta yi maka kuka, kana da kirki amma ita ba ka yi mata meyasa?"

A dai-dai nan, ya iso ?ofar makarantar su, bai amsa mata ba, yayi shiru.

Ta ce "Yauwwa, ya batun baba uwani, ta je kuwa?"

Ya girgiza mata kai ya ce "A'a, kuma ban ji mummy ta yi maganar ba, ina ga ba ta kai ga faWa mata ba"

Ta buWe motar ta ce "Shikenan sai an jima, na gode sosai Daddy" ta nufi cikin makaranta.

Sosai maganganun rumaisa suka ratsa shi, baya samun wanda zai din ga tattauna maganar nan da shi, yana ji a jikinsa abubuwan nan da suke faruwa, tamkar juya sama ne a ?asa, gaba Waya abubuwa basa tafiya daidai, amma jin sa yake, tamkar an Wora masa dutse, kuma kamar a cikin wata kurku yake da ruhinsa ya kasa samun salama.
Ranar da ammi ta zubar da hawaye, saboda ya ?i auren iman, ji yayi kamar zuciyarsa tana ci da wuta, ya daWe yana ganin abun a idonsa, amma ya ji farincikin mummy shi ne a gaba, dan haka wannan bakomai bane ba.

Sosai Adam yake masifa, jin wai mahamud ya Wauki rumaisa zai kaita makaranta.

"Takawa, ka sakawa zuciyarka salama, dan Allah ka yi ha?uri mana".

"Ammi kin san ba shiri muke ba, idan ya kitsa mata wani abun fa? Ko ya bugi cikinta ta saki baki tana zuba, meye haWinsa da matata? Yarinyar nan ba cikakken saiti

Please Login or Register in order to submit comment