You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

guda, suks zo yi wa mama jaje suka gabatar da Adduoi, tare da yi wa mama al?awarin za su cigaba da addu'a da karatun Alqur'ani har zuwa lokacin da Allah zai bayyana rumaisa.

Rumaisa kuwa a hankali ta motsa, ta fara ?o?arin buWe idonta, amma ta ji goshinta yana mata zafi, a hankali ta kai hannu goshin ta ji ya kumbura, ga busashshen jini ta shafo.
Cikin ?arfin hali ta tashi zaune, sai dai wani irin jiri ne yake Waukarta, saboda azabar yunwa, ga zafin dukan da aka mata da bakin bindiga.

Wani narkeken mutum ta gani, yana zagaya su, yana ?are musu kallo.

"Ke a ina aka Waukko ki?" Yayi mata maganar cikin tsawa. Ba ta kai ga bashi amsa ba, ta ga mutumin da ta bawa gyaWa a kasuwa.
Yayi saurin kawar da kansa da ga kallon ruma.

"Ke ya ina miki magana kin mini shiru?" Yayi maganar cikin muryarsa mara daWin ji.

Gefe guda ta ja, ta tan?washe ?afarta, tana jin yadda take jan numfashi da ?yar.

A fusace ya saka hannu ya fizgo ruma, amma ta ta?ar?are iya ?arfinta ta fizge hannunta ta ja da baya tana huci. Kallon kallo suka shiga yi, tsakanin shi da rumaisa.

Yin?urawa yayi zai maketa, mutumin nan ya shiga tsakaninsu, ya ce "Yi ha?uri, yarinya ce"

"Ban gane yarinya ba, bani bindiga kasheta zan yi"

Ya girgiza masa kai ya ce "A'a, da alama ubanta wani ne, za a samu kuWi a hannunsu, ka bari mu karSa sai a kasheta".

"Ni bani da uba" tayi maganar cikin ?warin gwiwa.

"Ina magana kina saka baki? Zan ?yaleshi ya kashe ki" da ?yar ya shawo kan mutumin ya ?yale ruma.

Ya Wauki wata leda ya jefa mata, buredi ne a ciki sai ruwan pure water. Tamkar ta shekara ba ta ci ba, haka ta dirarwa buredin nan, tana ci tana yin?urin amai.

Tana zaune tana cin abincinta, tana kallon yadda ake karSar lambobin waWanda aka Wauko su tare, ana cinikin nawa za a biya a karSesu kamar wasu dealer kaya.

Mutumin nan dai na Wazu, ya zo kan ruma ya ce "Bani lambar babanki".

"Dama ana zuwa kabari da waya?"ta tambayeshi.

"Kamar yaya?"

"Na gaya maka bani da uba ya mutu ai"

"Bani lambar wani Wan gidanku"

Rumaisa ta ce "Ka ga nifa gidanmu in dai kuWi zaka ce musu su kawo, basu da shi,? sai dai ku yi mini abin da zaku yi mini"

Ya ?are mata kallo ya ce "Haka ki ka ce?"

"Eh"

Ya mi?e tsaye ya ce "Biyoni".

Ayshercool.

Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*


Gaba Waya suka bi ruma da kallo, ita kuma ta ?are masa kallo ta ce "in biyo ka mu je ina?".

"Cewa ki ka yi sai dai ayi miki duk abin da za ayi miki, abinda yakamatan zan miki ai".

Ruma ta ce "Koma mene ka yi mini a nan ba in da zani"

Mutumin da yake ta ?o?arin bata kariya ya fara fusata ya ce "Wai ke wace irin yarinya ce?, duk yadda za ayi a kare mutuncinki a rabu lafiya ana yi, amma ke sai ka ce baki san ciwon kanki ba, ke kin san me zai miki Win ne ki ka tura baki kina cewa ayi miki koma menene?".

Cikin kuka ta ce "Ta ina kake kare mutuncin nawa, da kuka haWamu maza da mata kuka rabo ni da 'yan uwana, yanzu ka gama cewa a kasheni, wallahi babu in da zani daga nan, koma me zaku yi mini ku yi mini ni na gaji"

Su kansu waWanda aka kamo su tare da ruma mamaki suke yi, yadda take rashin mutuncinta yadda ta ga dama.

?aton nan ya sanya ?afarsa iya ?arfinsa ya taka ?afar Rumaisa, ta ri?e kanta ta yi wata irin ?ara, ba ta warke daga waccan azabar ba ga wata ana gana mata, ji ta yi kamar ya karyata, saboda azabar da ta ji, dan ?ato ne na gaske.

Mutumin da haryanzu ba ta san sunansa ba ya ce "Ina ga daga yanzu ba zan sake magana ba, su yi miki duk abin da zasu yi miki, akwai dalilan da yasa nake baki kariya, amma tun da ke na fuskanci baki da hali, duk abin da aka yi miki ke ki ka saya, idan baki nutsu ba haka zaki ta shan ba?ar wahala, kina raye amma na lahira sai yafi ki jin daWi, ki cigaba mara kunyar banza".

Fuska duk hawaye cike da dakiya ta ce "Eh ayi mini Win, ku kasheni daga nan sai me?, wallahi ba zan daina magana ba sai kun gaji kun kasheni, kuma ba lambar wanda zan bayar a gidanmu, ku da Allah ba zan yafe muku ba, ba laifin da na yi muku kuke cutar da ni, Allah ya saka mini duniya da lahira".

BuWe baki yayi yana kallon rumaisa, ga fuska duk busashen jini, amma sai kwaroroto take ba tare da ta na tsoron ayi mata wani abu ba.

Aikuwa ?aton nan ya dinga takata da ?afarsa, yana dukanta tana ihu tana "La'ila ha illa anta, subhanaka inni kuntu mina zalimin" shine kawai abin da take maimaitawa, dan idan ya takata ji take kamar ana buga mata itace, ko wani nannauyan ?arfe.

?ayan kuwa yana kallo bai kuma cewa komai ba, sai da ?aton nan yayi mai isarsa ya ?yale ruma, ba dan ta yi shiru da bakinta ba, sai dai ihun ma da ?yar take iya yin sa saboda ta galabaita. Haka kowa ya zura mata ido yana kallonta, duk wurin ita ce ?arama sauran duk da girmansu, amma tafi kowa baki da rashin mutunci.

A gigice mama ta dafe ?irjinta, hawaye na zuba daga idonta, mutane na ta bata ha?uri, amma a zuciyarta take jin kamar wani na faruwa da rumaisa, mussaman da zuciyar ta ta ta tsananta bugawa.
Idan ka ga mama sai ka zata wani ciwon tayi, duk da ba mace ce mai ?iba dama, amma ba ramammiya bace ba, tana da kumarinta, amma lokaci guda duk ta zube sai tsawo.
Ba ta iya cin abinci sai su Abubakar sun yi da gaske, da rarrashi da ban baki, ake samu ta Wan sha abu mai ruwa-ruwa. Duk wata walwala da ake a gidan nan suka dainata, bacci kuwa sai dai Sarawo, babu mai iya yin sa yadda yakamata a gidan.

'yan uwa da abokan arziki ana ta shige da fice, ana yi wa mama jaje tare da addu'a Allah ya baiyyana ruma.

Habiba ce ta faWo gidan su rumaisa a gigice, ta din ga kallon yayyen rumaisa da mutanen da suke zazzaune, can ta hango mama, ta ?arasa wurinta da gudu, ta zube a kan gwiwoyinta "Mama, wai da gaske an sace ruma?"

Mama ta ?ura mata ido, amma ta kasa magana.

Ma?wabciyar su ruman ce ta ce "Eh da gaske ne, yanzu ku je ku yi ta yi mata addu'a, Allah ya bayyanata cikin aminci, ya tsareta a duk in da take".

Rushewa da kuka habiba ta yi, tana wata irin sheshshe?ar kuka, gaba Waya ta gigice tana wani irin kuka.

A fusace mai sunan Baba ya ce. "Dalla ku fitar mana da mai ihun nan, da wane zamu ji?"

Aliyu yayi saurin cewa "A'a ba haka yakamata ayi ba, akwai sha?uwa a tsakanin su, bai kamata a hantareta ba"

Aliyu ya fita ya je ya samu Habiba, ta haWa hawaye da majina tana kuka, ya tuna faWace-faWacensu na ?uruciya tsakaninta da rumaisa, kullum cikin sintirin kan ?ara ake, da yadda yake zaneta ita da yayanta a kan ruma, amma yau ta tayar da hankalinta saboda Satan ruma.

Hannunta ya kamo ya ja ta gefe yana rarrashinta, amma babu alamar za ta yi shiru, duk jijiyon kanta sun Waga idonta yayi jawur saboda kuka.

"Kiyi shiri kar kanki yayi ciwo, sannan addu'a zaki taya mu, Ubangiji Allah ya bayyana mana ita, ki daina kukan, mu je na raka ki gida"

"Allah ya sa kar a kasheta, Allah ya sa ta dawo gobe" ta faWa tana sake fashewa da kuka.

?walla ce ta cika idon Aliyu, domin kuwa dauriya kawai suke yi, ya wayance ya ce "Amin ya Allah, dan idan kin yi salla ki din ga sakata a addu'a kin ji"
Habiba ta jinjina kai, tana cigaba da share hawaye. ya saka ta a gaba ya rakata gida, amma yanayin tashin hankalin da take ciki, zai tabbatar maka da ta kaWu sosai da Satan ruma.

Hauwwaliya ma da take a zaune tana jinyar karayar da ta yi kafin tafiyar runa, ita ma haka ta burkice, dan da har tana mitar ruma ta tafi ba ta zo ta dubata ba balle su yi sallama, sai labarin an yi garkuwa da rumaisa suka ji.

Hatta malamansu ruma na makarantar islamiyya da take gallaba, gaba Waya suka shiga damuwa, makarantar kanta kamar ana zaman makoki, saboda babu wanda bai santa ba da halinta. Ita kanta tsohuwar da take sayar da kayan yara a makarantar, da suke yawan faWa da ruma sai da ta yi kuka, dan wataran idan sun yi faWa wata ran suna shiryawa, dan idan ruma ta zo da abinci wataran tare suke ci, duk rashin jin ta akwai shiga rai.

Takawa yana kwance a ?aton falonsa a kan doguwar kujera, yayi zurfi sosai a cikin tunanin da yake yi, abubuwa da dama sun yi masa yawa, gaba Waya ya rasa wace matsalar yakamata ya fara tsayawa ya nemi mafita a kai, duk matsalar da ya tunkara, sai abubuwa sun ?ara taSarSarewa.

Wani irin zazzafan zazzaSi ne ya kama ruma, saboda wahalar da ta sha, ga azabar cizon sauro da kuma sanyi suka haddass mata zazzaSin.
Babu wanda yake ta tata, balle ya taimaka mata, tuni wasu aka fara bayar da kuWin fansarsu, idan sun ga dama su bayar da mutum, idan ba su ga dama ba su karSi kuWin sannan su kashe mutum su ja gawar zuwa bayan wani babban dutse da yake nesa kaWan da in da suke ajiye mutanen su yar gawar ba tare da suturta gawar ba.

Ruma na kwance ta takure tana ta rawar sanyi, ga azabar ciwon jiki, saboda dukan da ta sha, wasu mutane suka zo a kan babur, wanda aka goyo hannunsa Wauke da ?atuwar jaka, ta Waga ido dan ta ga su waye, wa za ta gani, dattijon bafullacen nan, da ta haWu da shi har ya rakota gida a garin su Gwaggo.

Kallonsa take, amma ya kawar da kai kamar bai taSa ganin ruma ba, ya basu jakar, shima suka bashi wata jakar ya hau babur Win aka bar wurin da shi. Tunani ta shiga yi a kan abubuwan da ya gaya mata, da kuma tunanin meye ala?arsa da wannan mutanen? Kenan duk shiri ne?" Idonta ya sauka a kan lambar dake jikin jakar, sak irin lambar jakar da aka nuna mata bullet a ciki lokacin da za su zo katsina!

Guntun tsaki ta ja, a lokacin da ihun wani mutum ya dawo da ita hayyacinta, kan ta gano dalilin da ya sanya mutumin yake ihun, sai ganin abu ta yi a jikinta kamar an watso ruwa, jinin mutumin ya Sata su an kashe shi.

Gaban ruma ne ya tsananta faWuwa, ta ma rasa wani halin yakamata ta shiga, tashin hankali ko kuma fargaba, ga jikinta babu daWi, ta fara fidda rai da samun mafita.

A hankali ta tashi zaune, ta ?arasa gaban wanda ya kashe mutumin, ta kalleshi ta ce "Dan Allah nima ka kasheni"

"Saboda me zan kasheki?"

"Na gaji da zaman wurin nan, dan Allah ku kasheni nima" tayi maganar cikin magiya.

Ya kwashe da dariya ya ce "Ai ke zaki yi mana amfani,? ko zamu kasheki sai mun koya miki hankali tukuna, dan ba zaki taSa barin hannunmu ba, an jaddada mana mu kula da ke, bakinki ba shi da linzami, ko mun karSi kuWin fansarki kashe ki zamu yi".

"Idan kuma baku karSa ba fa?" Ta tambayeshi.

Ya bata amsa da "Nan ma kasheki zamu yi"

"To ku kashe ni, dan ba wanda zai baku kuWin fansata, bamu da kuWi talakawa ne mu"

Dariya yayi, ya cigaba da busa sigari, ya share ruma.

***
"Daddy, ina ganin kamar yadda nace ka bar komai a hannuna, komai ya kankama, kawai mu cigaba da abin da muka saka a gaba"

Senator usman wakili ya girgiza kai ya ce "Ni fa haryanzu a raina ban gama gamsuwa da shirin nan naka ba Khalifa"

Khalifa ya gyara zama ya ce "Please Daddy, ka yarda da ni, ba zan baka kunya ba kamar yadda na yi maka al?awari zan cika, Ni dai na riga na saka rai, bana son damar ta wuce ni".

"Ni kaina ba zan so damar ta wuce mu ba Khalifa, amma yaron nan yana da taurin kai da nacin tsiya, bana tunanin zai ?yalemu, ina matu?ar jin tsoron kar ya tona mana asiri"

Khalifa ya Wan girgiza kai ya ce "Amma daddy, sauran members Win naku ma sun san abin da ake ciki?"

"Sun sani sarai, abin da nake tunani, akwai masu bashi goyon baya da haWin kai a kan ya kawo ?arshena, ba wannan ne ya fi Waga mini hankali ba, ina tsoron ya bankaWo mu, dan ko last week na ji yana Abuja ku san kwanansa bakwai a can".

Cikin damuwa da tashin hankali Khalifa ya ce "To yanzu shikenan daddy, babu wani abun yi?"

Usman wakili ya kwashe da dariya ya ce "Abun yi kai, ka zuba ido kawai yaro, babu wani abu da zai iya, muna da wani shiri a ?asa".

"Allah daddy, shirin menene?"

"Kar ka damu, idan ya tabatta za ka gani, kaima ka je ka cigaba da naka ?o?arin zan gani idan zaka iya zama magajina"

Khalifa ya yi murmushi ya ce "To shikenan daddy, ba ka da matsala da ni"

***
Iman ce zaune a falo, an saka mata lalle ja, tana ta kwaSe fuska za ta yi kuka, wai ita ta gaji ammi sai mita take ta ce "Aikuwa kina tashi sai ranki ya Saci, ku kamar ba mata ba mutum yayi ta fama da ku a kan ku dinga ado".

"Ammi fitsari fa nake ji" tayi maganar a shagwaSe.

"Yi a nan a wanke".
"Mhmm ammi zan yi kuka fa ya matseni".

"Ki bari na zo na sameki a wurin nan kin cire lallen nan, ki ga yadda zan yi da ke".

Jabir ne yayi sallama, Ammi ta amsa ya ?arasa cikin falon yana kallon iman.

Kan nan nata babu Wan kwali, gashin kanta sai Waukar ido yake ya sha mai, ta tufke shi. HaWe rai ta yi ta kawar da kai, ya zauna suka gaisa da Ammi, daga nan ya hau zuba kamar an kunna shi, amma hankalinsa ba akan hirar da suke take ba, a kan iman take da ta basar kamar ba ta san da zamansa a wurin ba.
Ganin ba shi da niyyar tashi ne ya sanya Iman tashi, dama a iya hannu aka saka mata lallen, ta wuce Wakinta.

Ko da ta koma Wakin zama tayi tai shiru, tana tunanin irin balahirar da jabir zai jefata a ciki muddin ya ce yana sonta, kuma yadda yake da ammi babu abin da zai hana ammin amsawa, dan kamar Wa shima ta Wauke shi.

Baba uwani ce ta yi wa ammi ?arya a kan zata je ta dawo, ammi ta bata izinin fita.
Tana fita ba ta tsaya ko ina ba, sai harabar gidan ta tabbatar da babu wanda ya ganta ta yi wuf ta faWa sashin Mummy, ta Sarauniyar hanyar da ta saba bi.

A Waki ta iske Mummy, Mummy ta dubeta cikin mamaki ta ce "Uwani, me ki ka shigo yi nan da yammacin nan sai an ganki".

"Allah ya huci zuciyarki uwar Wakina, Allah ya baki yawan rai, wani labari ne nake tafe da shi, ban sani ba ko zai yi daidai da abin da ki ke son ji ba".

Mummy ta numfasa ta ce "Ina jinki".

"Dama wani al'amari nake ta sanyawa ido, in tabattar da shi, amma ina hasashena yana daf da zama gaske, Jabir naku na gidan Galadima mai ci a yanzu, kamar shi ne yake sinsina iman, akwai alamun yana daf da cewa yana sonta".

Wani uban tsaki Mummy ta ja, "To ni ta ina hakan ya shafeni, ni abin da na saka ki ki yi mini kenan? Ki saka mini ido ki kawo mini labari a kan abin da ya shafi ahalin gidan nan kin kawo mini maganar bare wadda ko gashi ba ta da shi a cikin gidan nan, ni ina ruwana na saka ki aikin samo mini maganin da suke yi wa wancan uban ciwon Adam amfani da shi, amma haryanzu shiru kin tsaya kawo mini shirme"

Baba uwani ta du?a ta ce "Tuba nake, Allah ya huci zuciyarki, Allah ya sanyaya ruhinki".

"Tashi ki bani wuri, kar ki sake zuwa in da nake idan har baki kawo mini abun da na ce ba".

"In Allah ya yarda ba zan dawo ba sai da sa?onki, tuba nake".

Kwanki goma kenan da sace ruma, amma babu wani labari a kan ta, tun mai sunan Baba yana buga waya ko da wani labari, har mama ta ce yayi ha?uri ya daina kiran wayar.
Shi kansa dagaci ba yadda bai yi ba ayi sulhu, su faWi abin da suke so a basu su sako wanda suka kama, amma suka ce ba zasu bayar ba, yayi musu maganar rumaisa amma suka ce su ba zasu iya gane wata yarinya da suka Wauka a gidansa ba.
Ruma kuwa sai gwada musu halin take na azabar taurin kai da rashin kunya, wataran ta yi borin amma sun ?i su kasheta kamar yadda take fata, sannan suka fara yi mata horon yunwa, basu cigaba da takurata a kan sai ta bayar da lambar wanda za a kira a gidansu ba, suka ?yaleta sai dai tana ganin azaba, idan ta ishesu da rashin mutunci, da kan bindiga suke dukanta.
Duk jikinta yayi tsami, ta fita hayyacinta kamar ba ita ba, ga rashin lafiya da take ta fama, wasu ko ba a kashe su ba wahala ce take kashe su a wurin, ruma ta fara sanya ran ita ma wahalar ce zata yi ajalinta.

Tun ruma na iya addu'a har ta fara sarewa, tayi kukan ta kira maman har ta ha?ura ta zubawa sarautar Allah ido.

Tana nan kwance kamar matacciya, ta ji wani irin ?amshin turare mai daWin gaske ya gauraye wurin.

Wata mata ce take kuka, amma kamar iyayi matar take a cikin kukan, ruma ta Wago da ?yar ta kalli matar.
Tsohon ciki ne a jikin matar, duk da ruma ba ta san kan ciki ba, amma yadda cikin matar yayi girma kana gani ka san ta kusa haihuwa, matar na sanye da wani irin farin leshi mai Waukar ido da hankali, mai Wauke da golden a jiki, hannunta zuwa kunnenta duk gold ne. Kai da gani ka san ba a wahala take ba, gata fara sol kamar ba ta shiga rana, sai kuka take ?afarta na ta zubar da jini tana haki.

"Rufe mana baki, ko mu harbeki a ciki" suka yi mata tsawa toshe bakinta ta yi da hannunta ta zauna tana kuka, tana ?arewa wurin da taken kallo.

Tausayinta ne ya kama rumaisa, ita wannan ?aton cikin na matar ne yafi ba ta tausayi. Ita kuma ko a ina suka Waukota oho?.

Fatar matar duk tayi burWun-burWun, tayi jaa, alamar ?wari duk sun cijeta a hanya kan su ?araso.

Ayshercool.


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

=?I? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*.



Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*

https://youtube.com/@CoolhausaNovels?si=Uv_ZJT91QMMuaNxG
Ku yi subscribing YouTube channel Win mu domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro.


Cikin ?arfin hali da kuka, matar ta ce "Dan Allah ku yi ha?uri, ku tausaya mini halin da nake ciki, ku sallameni, ko dan halin da nake ciki, cikina saura kwanaki kaWan na shiga wata tara, dan girman Allah ko nawa ku ke so ku kira gidanmu, za su baku ku sake ni".

"Ke ki rufe mana baki, ke zaki gaya mana abin da zamu yi?"

"Ba abin da zaku yi nake gaya muku ba, taimaka mini zaku yi, dan Allah ku duba halin da nake ciki"

Banza suka yi da ita suka cigaba da abin da ya dame su.

Ruma tana fama da kanta, amma sai bin matar take da kallo, ?arshen tausayi matar ta bata. Galibin waWanda aka Wauko ruma da su, da waWanda ta tarar an sallami wasu, wasu kuma an kashe su, sannan kuma kusan kullum akwai wanda mutanen za su kawo.

"Ki yi ha?uri ki daina kuka, ki yi addu'a" ruma tayi maganar cikin sanyin jiki.

Matar ta kalli ruma ta share hawayenta, ta ce "To, Allah ya kuSutar da mu, sun kashe mini direbana ma, ya iyalinsa za su ji?" Tayi maganar cikin kuka.

Ruma a ranta ta ce "Lallai wannan 'yar gata ce, har direba ne da ke"

A haka dare yayi, matar nan na ta kuka, abinka da farar fata ta koma jawur saboda kuka.
Suna nan a? zube a wurin kamar shara, ga wata irin iska da ake yi mai sanyin gaske, ga yunwa na damun ruma ga ciwo, dare ya

Please Login or Register in order to submit comment