You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi sannan ta ce "Yanzu shikenan, kin fasa fitar kenan?"

Iman ta Waga mata kai alamar eh. Ta ja hannun Iman suka bar falon.

****

Cikin rarrashi mama take magana, "Ruma, aiken ki nake son yi, amma bana son ki je ki yi mini shirme, ko ki tsaya a in da ban aike ki ba"

"In sha Allah mama, ba zan tsaya a ko ina ba, fiii zan ware dogayen ?afafuwana da bala'in gudu na je na dawo"
Mama ta ce "Wane irin gudu kuma? Kalen ki watasar mini da kayan aiken, ki tafi a hankali, ki yi sauri ki je ki dawo"

"In sha Allah zan yi sauri, na je na dawo"

Mama ta gaya mata in da take so ta je, tare da abin da za ta kai, ruma ta sauya kaya ta saka hijjabi, ta fita yi wa mama aike, ta ?uduri aniyar za ta je ta yi sauri ta dawo ko dan ta farantawa maman.
Tashin farko ta bi ta cikin unguwa, tana tafe tana kalle-kallenta, duk wani lungu da sa?o idan ta bi sai an kira sunanta, dan kusan kowa ya santa.

A ?ofar wani shagon aski ta ga keken Huzaifa, hakan ya tabattar mata da yana cikin shagon.
Murmushi ta yi ta nufi ?ofar shagon askin, da sallama ta buWe ta shiga cikin shagon.
Duk maza ne a ciki, ga Huzaifa ya zauna a kan kujera za ayi masa aski, jin sallamar mace ya sanya dukkansu suka juya suna kallonta.

"Ohh Huzaifa yau Allah ya yi zaka cire wannan sumar kenan? Kuma wallahi aka yi maka askin 'yan iska kai da mai sunan Baba"

A ?ule Huzaifa ya ce "Ke uban me ya kawo ki nan? Ba ki ga shagon aski bane?"

"To ni ina ruwana da wani shagon aski, ba dai mutane ne a ciki ba, keken ka na gani a waje na san kana nan, na ce bari na le?o na ganka"

"To na ji na gode, fita ki bar wurin nan"

"To sai ka tsaya na gama kallon kalandar askin nan, sai na tafi " tayi maganar tana ri?e ?ugu, tare da zubawa kalandar ido.

"Ni wannan yarinyar ba ke na taSa rabaku faWa da wasu yara ba, kun dawo daga makaranta?" Cewar wani da yake zaune shima yana jiran askin.

"Eh nice, me na yi kuma?"

Ya ce "A'a gane ki kawai na yi"

"To yanzu da ka gane ni lada nawa aka baka?"

Mai aski ya ce "Deluwa, dan Allah ki yi ha?uri, wurin nan duk maza ne, ki je aiken da aka yi miki, ko kuma in saka a ri?e mini ke na yi miki aski"

"Aikuwa da sai ka kasa zaman ?orayi, sai na saka yayyena sun kakkaryaka sun zubar, ni zaka yiwa aski?"

Huzaifa ya mi?e tsaye rai a Sace ya ce "Bi ?ofar da ki ka shigo ki fita"

Ta Wan kwaSe baki ta ce "Huzaifa ba ayi maka gwaninta, daga ziyara?"

"Ki fita na ce, wallahi na zo in da ki ke sai na gwara kan ki" ja ta yi ta tsaya cike da taurin kai tana kallon idonsa, hakan ya ?ara tunzura shi, yayi kanta amma suka ri?e shi, ta fita da gudu daga shagon.

Tana fita ta yi ?wafa, ta tura keken sa ta ji bai rufe ba, keken ya fi ?arfinta, amma ta haye ta yi gaba.

Wani ya le?a shagon askin ya ce "Huzaifa ?anwarka ta Wau keken ka fa ta tafi"

Da sauri ya mi?e ya le?o, ai tuni ta kusa ?arshen layin, ya san ko da ya bita ba zai cimma ta ba.
Kawai yayi tsaki ya koma ya zauna, zuciyarsa na tafasa, 'yan???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? cikin shagon suka din ga dariya, kowa na tofa albarkacin sa a kan halayar ruma.

Haka nan tun da ruma ta fita, mama ta kasa nutsuwa, kawai dai gata nan ne dai, ta fara dana sanin dalilin ma da ya sanya ta aiketa.

Tun tana saka ran ta ga ta ina za ta shigo gidan, har ta fara fidda rai, yanzu ba ta fiye Waga hankalinta ba, idan ruma ta fita makaranta ko aike ba ta dawo da wuri ba, sai dai fargabar mai za azo ace mata ruman ta aikata.

Aikuwa ilai, tana cikin wasi-wasi sai ga sallamar wata matashiyar budurwa da wata yarinya, yarinyar bakinta a fashe, jikinta duk kwata ga fasashshiyar roba, da sauran gari a cikin ta, yarinyar sai kuka take, yawu da jini yana zuba daga bakinta.

Cikin kaWuwa mama suka gaisa da matashiyar yarinyar, mama ta hau tambayar ba'asi.

Babbar ta ce "Dama cewa aka yi na zo gidan su na faWa, ruma ce ta taho a kan wani ?aton keke kashe gardi, ta taho da gudu, ?anwata ta karSo ni?a, ta bugeta da keken ta faWa kwata, ita ma ta faWi a gefe, ta tashi ta karkaWe jikinta ta hau keken ta gudu, kuma ba iya ?anwata ta buge ba, tun da tana tafe tana faWuwa a kan keken"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ya Allah kai ka jarrabeni, Allah ka dube ni, ka bani ikon cin wannan jarrabawa" mama ta kamo hannun yarinyar da aka jefa kwatar, ta wanke mata jiki, ta basu dubu Waya tare da basu ha?uri ta ce zata zo har gida ta basu ha?uri.

Gwaggo kuwa ta hau masifa "Wallahi mutanen maraya ba ku da kara a kan Wa, yanzu saboda wannan Win aka wani aiko yawon kan ?ara, ai Wa na kowa ne, kuma fitinar maraya ai daban take"

Kamar mama za ta yi kuka ta ce "Ba wnai fitinar maraya, dama can haka ake fama da ita, a ina ta samu keken da ta hau ni da na aiketa wuri daban, kullum sai ruma ta sakani asarar kuWi da yawon ban ha?uri, nan gaba idan ba ayi wasa ba, sai wasu sun kai ?ararmu ga hukuma"

"A'uzubil'ahi kina uwa ba zaki faWi alkhairi a kan yarinyar ki ba, ?uruciya ce, kowa da irin ta sa" mama ba ta kuma cewa komai ba, idan ta biyewa zuciya, za ta iya musayar yawu da Gwaggo, wanda ba za ta so hakan ba.

Huzaifa ya shigo a kumbure yana bala'i "Mama! Ina ruma take wallahi yau sai na tattakata, sai na ci mutuncinta"
Mama da take a ?ule ta kalle shi ta ce "A ina ka ganta?"

"Mama shagon aski fa ta bini, na koreta shi ne ta Wauke keke na ta gudu, ni sa'an wasanta ne ita duk wani halin zubar da mutunci ta iya"

Mama ta safe kai ta ce "A ina da ta samu keken kenan? Za ta gane ba ta da wayo da Baba zan haWata bari ta dawo"

"A'a ke wace irin uwa ce, wannan mugun Wan na ki, haka kawai ya kassarata a'a ban lamunta ba "

Huzaifa ya harari Gwaggo ya ce "Wallahi ko ba a gaya masa ba, da hannun nawa zan ci ubanta, sai na girgiza ?ashin ha?ar?arinta "

Har gefin magariba babu ruma babu alamarta, tun mama tana jurewa, har ta saka aje a nemo mata ruma.

Aliyu Allah ya bawa sa'a, ya ganota a wata tawagar 'yan d.j, ana biki an kunna d.j, ta shige tsakiyar manyan mata, ana rawar sabada, ta gantsare sai rawa take, tana wani juye-juye sai ka ce an saka mata batir, ga ta a shafe ba gaba ba baya ama sai karkaWa jiki take.
Cikin 'ya'yan Mama, Aliyu Ustaz ne, ba shi da ra'ayin wannan abubuwan, amma yau a saboda ruma, sai gashi a tsakiyar mata, ya samu bayan ruma da take ta juyi, ya tsula mata tsumagiya.
A zafafe ta ?andare ta juyo, a zaton ta yaron mai D.J ne ya daketa, dan dama yana ta korar yara daga cikin filin rawar ta?i tafiya. Ba kuma rawar kawai take yi ba, har da satar kuWin li?i tana sakawa a cikin hijjabinta, sai ta gantsare tana rawa idan aka li?o sai ta wayance ta Wauke kuWin.

Cak ta tsaya tana kallon Aliyu, ta Waga kai ta kalli yadda gari ya yi duhu.
"Sannu 'yar makaWa, aike da aka yi miki kenan ko? Fita ki wuce mu tafi"

Kasa magana tayi, a take tayi saranda, da jin za ta iya Waukar kowane hukunci, saboda ita kanta ta san ta tafka ta'asa.
Ta janyo keken Huzaifa, da Allah ya sa ba a sace ba, ta hau turawa, Aliyu ya haske keken, tayoyi duk sun sace, dan Wayar ma fashewa ta yi, ga kaca ta zube keken duk wani gurin ya lotse, adon fitulun da ya yiwa keken kuwa, suma wasu duk sun fashe.
Yana tafe yana kallon ruma, yana tunanin anya ruma mutum ce, fitinarta ko su da suna kamarta ba su yi haka ba, su dai akwai dambe kamar zakaru, kamar su cinye juna, amma rashin ji a gida, rashin ji a unguwa rashin ji a makaranta wannan sai Ruma ?ANWAR MAZA.

A ?ofar gida suka tarar da Uamar, yana tsaye yana waya, tana ganinsa ta fara kuka, tana cewa "Kashina ya bushe"
Aliyu ya ingiza ?eyarta zuwa cikin gidan, da sauri Huzaifa ya taso, dan ta kekenaa yake yi, sai dai yana kallon keken ya san ko a wurin 'yan gwan-gwan wannan keke ba zai daraja ba, kamar yayi shekara da shekaru.
A ka rasa wanda zai ce mata komai, duk suka zubo mata ido.

Mama ta ce "A ina ka ganota?"

"Ga ta nan ku tambayeta"

Cikin muryarsa mai razanata musamman idan ba ta da gaskiya ya ce "Daga ina ki ke?"

Jikinta ya hau rawa ta ce "Dan Allah mai sunan Baba......

"Daga ina ki ke fa kawai na ce?"

Gwaggo ta ce"Ya zaka razanata da wannan muryar ta ka, ka tambaye ta cikin nutsuwa mana"

Huzaifa ya daWe bai ji abin da yake shirin sanya shi kuka ba irin yau, ya kasa ko tari tun bayan tozali da kekensa.

Rarraba ido kawai take tana kokowa da numfashi, ganin yadda kowa ita yake kallo yana jiran amsarta.

Wata irin gigitacciyar dan?a Uamar ya yiwa kunnenta, ta kurma ihu, ya janyota har tsakiyar tsakar gidan, ya dungurar da ita, ya naWe hannun rigarsa cikin tsawa ya ce"Ina ki ka je da aka aike ki?"

Cikin kiWima da razani, ruma ta wassafa komai, ba ta Soye ba ciki har da zuwa wurin aski da yadda ta Wau keke tana tafe tana faWuwa, duk ta gurje gwiwa, da yadda bayan ta dawo daga aike ta tsaya wurin 'yan bikin da ba ta san suwaye ba ma, tana rawa tana satar kuWin li?i.
Sai a lokacin ta faWi har faWa suka yi da yaron dj yana ce mata shegiya Sarauniya.
"Yanzu ina kuWin da ki ka Webo Win?" Yayi maganar yana mi?a mata hannu.
Aikuwa ta zura hannu a rigarta, sai ga kuWi, a ?alla idan aka ?irga sun kai dubu uku da Woriya.



(SORRY FOR THE LATE UPDATE, AYYUKA SUN YI YAWA NE, INA GODIYA DA TARIN ADDUOI DA ?AUNAR DA KU KE WA BOOK ?IN ?ANWAR MAZA)

Ayshercool
08081012143
[13/07, 9:01 pm] JAKADIYAR AREWA: ?ANWAR MAZA
? ? ? ? ? ? ? ??

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing? YouTube channel Win
@Cool Hausa Novels, domin samun daWaWan litattafan hausa na sauraro.






12

Mai sunan Baba ya kalleta a tsanake ya ce "Sata ki ka koma yi kenan ko?"

Ta girgiza kai da sauri ta na zazzare ido.

"Ba zaki buWe baki ki yi mini magana ba?"

"A'a Yaya wallahi ba sata nake yi ba"

"To idan ba sata ba, me ki ka yi, kin san su masu bikin ne, ko kuma sun sanki, idan ba sata ba baki suka yi, ko nan aka aike ki?" Ta girgiza masa kai.

Ya ce "Good, tashi ki je ki yi alwala ki yi salla, zan gauraya da ke, tashi maza ina jiran ki"

Huzaifa da yake ta huci, ya cika ya batse kamar ya sha yeast ya ce "Wallahi yau sai na lallasaki, za ki gane baki da wayo"

Gwaggo ta ce "Ku dai din ga ha?uri yarinya ce, ?uruciya ce kawai take damunta"

Huzaifa ya yi ?wafa ya ce "Ba ?uriciya da yarinta ba, Allah ya sa Wanyar ?wa?walwa ce a kan ta da ba ta nuna ba, sai na lallasata na koya mata hankali"

Duk da tana cikin tashin hankalin rashin sanin hukuncin da za ta fuskanta, hakan bai hanata murguWawa Huzaifa baki ba, tana harararsa, duk da laifin da ta tafka masa.

Daga shiga banWaki alwala ta tsiri kashi, duk dan ta Sata lokaci kar ayi mata hukunci mai wahala, ta na fitowa, Umar ya ce a tsakar gida za ta yi sallar, dan haka ta Wau hijjabi ta tayar da salla.

Ita kanta ba ta san adadin raka'ar da ta yi ba, kawai yin sallar take cike da zullumi, a sujudar ?arshe kuwa kai kace neman gafara take ko bacci tayi, amma babu Waya nazari kawai take.
Haka ta idar ta saka addu'a, abin da ba ta saba ba, ko sallar ta yi sai mama ta yi ta faWa sannan take zaman yin addu'a.

Ganin ta?i sallame addu'a ne ya sanya Umar yi mata wani irin kallon, da babu shiri ta shafa addu'a ta tashi.

Ya ce "Oya, kamun kunne"

Cikin marairaicewa ta ce "Dan girman Allah Yaya.....

"Shut up! Zaki abin da na ce ko kuwa?"

Jiki a sanyaye, ta dur?usa ta kama kunnenta, nan da nan jikinta ya hau rawa, ta fara gajiya ta saka kuka.

Gwaggo ta ce "Kai ina mace ina wannan goho, kai meyasa ba ka tsoron Allah ne? Ke tashi dalla wannan wace irin azaba ce?"

Ruma ta ce "A'a Gwaggo, ba zan iya tashi ba sai ya ce dan Allah ku tayani bashi ha?uri"

Mai sunan Baba yayi shiru, ya ?i kula Gwaggo, ta dubi mama ta ce "Ke ba zaki saka baki ya ce ta tashi ba, tun da ni ban isa ba?"

Mama ta ce "Ba haka bane Gwaggo, ai gara a din ga hukunta ta idan ba haka ba, sangarta da rashin jin da zata yi sai Allah ruma ba ta ji sam" ?arshe mai sunan Baba ya tashi ya bar gidan ma gaba Waya ruma kuma ko da wasa ba ta tashi ba daga kamun kunnen, sai dai ta cika musu gida da koke-koke da magiya.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah mama ki saka baki, na tuba na bi Allah, dan Allah ki bashi ha?uri ya ce in tashi"

"Babu ruwana, ba dai ba kya ji ba, ai na gode Allah da ya bani waWanda zasu hukunta ki idan ki ka yi ba dai-dai ba, kuma kar ki sake kiran sunana"

"Wayyo Allahna na shiga uku, wallahi mama zan iya rasuwa, kaina da wuyana ciwo suke yi mini, bana son na mutu yanzu, bana nafila karatun Alqur'ani ba kullum nake yi ba, gashi ina yi miki abin da ba kya so, bana son na mutu yanzu ban tuba ba, wallahi mama zan iya rasuwa a wurin nan"

Yasir ya ce "Ba ki jigata bane ba, da ki ke iya wannan surutun"

Gwaggo ta ce"Ji min kafirar yarinya, ba nace ki tashi ba kin ?i, ni babu abin da ya ?ular da ni, irin wannan goho da ya saki kina 'ya mace, kema da azababben taurin kai na ce ki tashi kin ?i".

Ruma ba ta kula Gwaggo ba, sai cigaba da rusa kuka da tayi, tana magiya da neman taimako.

Cike da ?uluwa Yaya Aliyu ya ce"Ki yi mana shiru dan ubanki, tun da ba wani ne ya aike ki ki aikata abin da ki ka yi ba" haka ruma ta ja bakinta ta tsuke, tana kuka ?asa-?asa dan wasu lokutan yaya Aliyu ma ba daga nan ba wuri8iya tsare gida da hukunci, dan daga yaya Umar sai shi a zafi.

Har mai sunan Baba ya dawo ruma tana nan tana aikin kamun kunne, tana yi tana faWuwa tana tashi.

Sai da ya dawo sannan ya ce ta tashi, kuma ya ce mata washegari za su gauraya.

Tana mi?ewa tsaye jiri ya kwasheta sai amai, Gwaggo ta fito da sauri ta kama ruma, kanta sai juyawa yake saboda azabar wahala.

A zaune ta yi alwala tayi sallar isha'i, ko abinci ba ta nema ba, ta kwanta saboda galabaita, cinyoyinta sai azabar ciwo suke yi mata, dama da fari suna ciwo saboda hawan keke, gwiwoyinta na raWaWi saboda duk ta ?uje su saboda keke, yanzu kuma ga kamun kunne, jikinta kamar an mata duka haka take jin ta, a take wani irin wahalallen bacci ya kwasheta.
Sai dai kwana ta yi da wani irin zazzafan zazzaSi, wanda ita kanta ba ta san ya hau ta ba, jin surutan ta ya yi yawa a baccin ne ya sanya mama zuwa ta taSa jikinta, ta ji da zafi sosai.

Duk da mama a ?ule take da ruma, haka ta fita ta Webo ruwa ta sanya Wan ?aramin towel, ta din ga shafawa ruma ruwa a jikinta.
Tun asubar fari kuwa, ruma amai ne ya tasheta, saboda har a lokacin jiri take yi.
Yanzu ma a zaune ta yi sallar asuba, ta nemi wuri ta kwanta.
Tun mama na basar da ita, har kuma ta fara damuwa, Gwaggo kuwa ta samu wuri Waya ta zauna sai mita take na masifa a kan mama tana gani aka bawa ruma gwale-gwale amma ba ta ce komai ba.

Bayan gari ya gama wayewa, Gwaggo ta karya ta yi haramar tafiya, sai dai a lokacin ruma ta samu bacci, dan a galabaice take. Gwaggo ta ce kar a tasheta, Abdallah ya tafi rakata tasha, suna ta murna zasu huta, dan dama Gwaggon ta ishe su,? ruma ce kawai take son zamanta a gidan.

Mama ta tashi ruma, ta matsa mata a kan lallai ta ci Abinci, ta na ci tana kuka ta Wan sha tea kaWan ta kuma kwanciya, sai dai ko mintuna goma ba ayi da cin Abincin na ta ba, ta tashi ta cigaba da amai.

Ba shiri mama ta ce Aliyu ya zo ya kai ruma chemist a dubata.

Da ?yar take iya tafiya, suna tafe tana kuka, har sai da ran Aliyu ya fara Saci, amma ya shareta suka cigaba da tafiya a hankali. Cikin sa'a kuwa suka tarar ya fito, kasancewar asabar ce, ranar ba ya zuwa aiki.

Ya na ganinsu cikin kulawa ya ce "Subhanallah, 'yar gidan mama yau ke ce ba lafiya?" Ita dai ba ta iya magana ba ta nemi wuri ta zauna. Aliyu ya zauna ya rungumeta, saboda ?o?arin faWuwa take yi.

"Meya sameta haka?"

Aliyu ya ce "Ina ga zazzaSi ne dai, da amai ta fara jiya"

Bakinta bai mutu ba, ta ce "Kamun kunne aka sakani, kusan awa goma shine ya sani rashin lafiya"

"Subhanallah, waye ya saki kamun kunne kuma?"

"Mai sunan Baba ne"

"To ki yi ha?uri, yanzu dai zan Wibi jininki na yi miki gwaji, in duba meye ya haddasa zazzaSin"

?iban jinin da za'a yiwa ruma, tamkar za a cire mata ido, ta dinga kurma ihu, tana fizge-fizge, ga ta da shegen ?arfi, da ?yar Aliyu ya ri?eta aka Webi jinin nan.
Kuka har da majina, Aliyu ya dinga dungure mata kai yana zaginta.

Ya gama gwaje-gwajen da zai yi mata, ya ce "Malaria ce ke damunta, dan haka akwai bu?atar ayi mata allurai, da kuma magunguna"

Ruma ta yi masa zuru da ido, tana jiran ta ga a ina za ayi allaurar.

Ya haWa alluransa ya nufo ta, ta mi?e tsaye.

"Ke malama ki tsaya, dan ba zaki sake wahalar da ni ba"

"To a ina za ayi mini allurar?"

Mai chemist ya ce "Ai a baya ake yin ta"

"Wai bayana" tayi maganar tana nuna bayanta.

Nasiru mai chemist ta ce "A'a a mazaunai"

"Suwaye mazaunan?"

Aliyu ya haWe rai ya ce "Ke juya ki tsaya ayi miki allurar nan mu tafi, kin san sarai a in da za ayi".

Ta ri?e skirt Win ta gam ta ce "Ni wallahi ba zai ganni ba"

Aliyu ya fizgota, ya ri?eta da ?yar suka danneta suka yi mata, Aikuwa ta din ga zunduma ihu, kamar sun mata wani abu.

Haka aka gama yi mata treatment, suka taho gida, ban da uban kuka babu abin da take yi.
"To subhanallah, ko me aka yi mata kuma take wannan uban kukan haka oho" mama ta yi maganar tana fitowa tsakar gida.

Aikuwa suna shigowa, ta nufi mama tana kuka.

"Meye haka, kukan me ki ke haka,ki ke Sare baki?"

"Mama yaya Aliyu ne da Nasiru mai chemist"

"Suka yi miki me?"

"Bayan ya Wibar mini jini, kuma suka buWe mini tsiraici na aka yi mini allura"

Mama ta ce "Subhanallah"

"Mama ba ke ki ka ce Wuwawu tsiraici bane ba, amma har da Yaya Aliyu ya ri?e ni, Nasiru mai chemist ya ganni, wallahi ban yafe ba"

Mama ta girgiza kai, ta ?iftawa Aliyu ido sannan ta ce "Haba Haidara, ya zaka yi mini haka, dan me za'a buWe mata jiki ayi mata allura?"

Aliyu ya ce "To mama ai larura ce, ko a addinance ba haramun bane".

Cikin masifa ta ce "To shi yayana ne da zai ganni? Har da taSani ya yi mini allura a wurin"

Aliyu ya ce "Sa'anki ne ni, uban me za a kalla a jikin naki?"

"Wallahi ba zan taSa yafewa ba, Allah ya jijjigo bala'in duniya da lahira ya Wora masa, tun da ya ganan mini tsiraici na"

Mama ta ce"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wace irin Addu'a ce haka, kar in kuma ji, baki san larura ba?"

Aliyu ya ce "Sakarya, kamar ba tsairaicin ki ka je kina kaWawa a gaban mutane ba jiya"

Umar ya shigo Wakin mama, suna magana, bai kula ruma ba amma dan ya duba jikinta ya shigo.

Tana kwance ga zafin ciwo, ga na takaicin allurar da aka yi mata, zafin allaurar bai dameta kamar ganinta da mai chemist ya yi.

Sai da yamma mama ta sakata ta yi wanka, ta canza kaya ta Wan ji ?warin jikinta.
Sai da ta kwana uku tana fama, sannan ta ware gaba Waya, sai dai rashin lafiyar da tayi ya sanya aka mance da laifin da ta tafka, kowa sai lallaSata yake, ban da Huzaifa.

Ta ware sarai har ta koma makaranta, kullum mama cikin nasiha take yi mata, tare da yi mata addu'a da fatan shiriya.
Tun daga ranar ruma ta daina bi ta hanyar chemist Win Nasiru, idan kuwa ta ganshi ko kallonsa ba ta yi, balle ta gaishe shi, a cewarta Wan iska ne tsairaicin ta ya kalla.

"Mama wai yaushe zaki haihu ne, babannin 'yan ajinmu sai haihuwa suke yi, amma ke ban taSa ganin kin haihu ba"

Mama ta ce "Ikon Allah, ba gaki na haife ki ba, ai ke ce auta ha zan kuma haihuwa ba, sai dai in kin girma kin haifa na Wauka"

"To ni yaushe zan haihun?"

"Sai kin girma kin yi aure"

Ruma ta Wan yi jimm sannan ta ce "To ni so nake na haihu, ina son ?ani ko ?anwa da zan din ga wasa da su"

"Ruma ki ka haihu yanzu ai a nemi tsari, sai an yi aure ake haihuwa"

"To gaskiya mama ni so nake na haihu yanzu"

Usman da yake jin hirar ta su ya ce "Ke, idan ki ka haihu ba aure tsanarki za ayi, a kore ki daga gidan nan da unguwar ma gaba Waya, shi ya sa ba a wasa da maza, ki ka bari namiji ya taSa ki to ciki zaki ki haihu, kuma korar ki za mu yi"

Waro ido ruma tayi ta ce "Amma ku kuke taSani?"

"Ai mu yayyenki ne, muharramanki ne mu"

Ruma ta dafe ?irji ta ce "Allah ya rufa mini asiri, ai da ban sani ba, taS idan aka koreni ina zani?"

"Oho miki dai, wannan damben da ki ke da maza ma, idan ba ki daina ba, sai dai ki ga kin haihu, kuma sai kin bar mana gida"

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "In sha Allah hakan ma ba zata faru ba, ai ni ban san hakan abin yake ba, Allah ya sa na yi tsawo na auri kyakykyawa mai kuWi".

Mama ta ce "Ke zan ci ubanki ke da kyakykyawa mai kuWin nan, miji na gari ake ro?on Allah, fitsararriya"

"Ni dai gaskiya bana son mummuna, mai kyau nake so"

"Ke dalla ware, da wannan munin za ki auri kyakykyawa?"

"Ni dai yaya Ussy, ka yi mini Addu'a, ka san wa zan aura a cikin 'yan ball".

Mi?ewa ya yi ya ce "Ba ni da lokacin jij wannan shirmen na ki".

Tun daga wannan lokacin, ruma take kaffa-kaffa, da gudun kar wani namiji ya taSa ta, saboda kar ta haihu a koreta ta shiga uku, kuma ta san idan aka koreta ba kuWin mota za a bata ba, balle ta tafi ko ?auye ne wurin Gwaggo.

Yau gaba Waya mama ta kasa gane kan ruma, tun da ta dawo daga makaranta yanayinta ya nuna kamar tana cikin damuwa.
Ba irin tambayar da mama ba ta yi mata ba, amma ta ?i gayawa maman dalilin damuwarta ta, ta ce cikinta ne yake yi mata ciwo kawai

Mama ta aiki ruma sayen maganin sauro, ta je ta sayo, ta dawo ta tsaya a soro tana kuka.
Huzaifa ne ya sameta a soron tana kuka, dan sai da ya Wan tsorota.
"Ke me ki

Please Login or Register in order to submit comment